Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

tana fitowa ta nufi gado tayi kwanciyar ta Bata ce masa kala ba , shima haka yaje yayi wanka ya kwanta Kusa da i’ta cikin zuciyarsa yana tunanin anya ya mata adalci inda ya zubar da cikin nan! tunda ta nuna Masa kiri kiri tana son abinda mai'yasa bazai barta dashi ba Haka yayita tunani har barci ya daukeshi can tsakiyar dare ta tashi jin wani i'rin murd’i da cikinta ya mata tun tana daurewa har ta kasa “Farouq!!” dakarfi ta Kira sunansa cikin barci yaji muryanta da sauri ya farka “rauda lafiya?” lumshe i'don tayi kafin tace “ka zubar min da ciki hankalin ka ya kwanta!! ka zabi sabawa ubangiji ka ko Farouq Ashe soyayyar da kake i'kirarin kana min kariyace ba gaskiya ba!! ashe...” wani kara ta saka tare da dafe mararta wani mugum tausayinta ne ya d'arsu a zuciyarsa danasani da ladama ne suka Masa dirar mikiya a zuciyarsa ganin halin da take ciki ne yasa shi mikewa tsaye yana tunanin wani taimako zai bata “karka yarda kace zaka kaini asibiti ka barni na mutu a yanzun nafi kaunar mutuwata fiye da komai” shuru yayi yana kallon yanda take murkususu kusan minti talatin kafin ta sauk'e wani ajiyar zuciya da kyar ta i'ya mikewa ta nufi toilet wanka tayi tare da wanke kayan duk cikin karfin hali take yi tana fitowa ana Kiran sallah ganin Yana Nan yanda ta barshi ne yasa taja dogon tsaki bai ji zafinta ba a wannan karon domin yasan shi mai laifi ne ya caccanci fiye da haka .
Zame zanin gadon tayi shima sai da ta wanke cikin gida ta nufa tayi sanya tana dawowo tayi sabon shinfid'a kwanciyarta tayi tana tunanin mafita “Farouq in ka gama tsayuwa sai ka nufi masallaci” ajiyar zuciya ya sauk'e haka ya nufi toilet wanka yayi tare da alwala Yana fita ta Kira Ummanta a waya “hello mamana da asubar fari inna fatan lafiya?” cikin dakiya tace “ummana...” sai kuma ta saka kuka “a a subahanalillah menene kuma?” da kyar ta i'ya daidaita kanta “ya zubar min da ciki” mikewa umma tayi tare da barin d'akin kar Abbu yaji domin hankalinsa ne zai tashi amma abinda Bata sani ba tun sanda suke Magana yana ji haka yabi bayanta ba tare da ta sani ba “innalillahi wainnailahi raji'un Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan minha Astagfirullah Astagfirullah RAUDA ba abinda zance Miki sai dai ki d'auki Wannan a matsayin kaddara kiyi Hakuri ki Kara hakuri Insha Allahu zaki ga riban biyayya...” da sauri Rauda ta katseta da “umma !! Hakuri! riban biyayya duk ba gashi Nan Inna gani ba! Uwarshi bata sona sannan shima ya zubar min da ciki shik'enan ni bazan ga d'ana a duniya ba...” karban wayar Abbu yayi cikin sanyin murya yace “ki Kara Hakuri Rauda karki yarda kuma kice zaki zo Nan ki zauna tare da Mijinki” Haka sukayi ta tausarta da kalamai masu dad'i a Haka har ta hakura badan taso ba suna Gama waya tace “Allah nagode maka rabbi ka bani i'kon yin biyayya a karo na biyu”
Tana kwance taji ance “ke tashi ki fito ki wanke min kaya” gabanta ne ya fad’i bata san lokacin da tace “Hajiya b..a.b..banida lafiya” wani tsawar da ta daka mata ne yasa ta sauko babu shiri har ta manta da wani ciwo haka ta nufo cikin Gida nan taga tulun wanki hawaye ne suka gangaro mata babu yanda zatayi haka ta fara wanki tana matsan kwalla ga wani ciwo da cikinta ke mata Sajida ta fito a d'aki da sauri tace “haba haba Hajiya gaskiya abinda kike bakya kyautawa mai yasa kullun bakya son ganin farincikin yarinyar nan gaskiya bai dace ba ki sauya hali..” wani mari Hajiya ta mata cikin bacin rai tace “kar in kara ji kiyi magana idan kuma ba Haka ba sainayi mugun saba miki fita ki bani guri kuma karki kuskura kije kusa da i'ta”
daki Sajida ta koma tana tsaye jikin window sai kallon Rauda take tana share wayan fusk'anta..
Farouq ne ya shigo ganin rauda na shanya ya sashi tsayawa yana kallonta tunani yake Wannan kuma kayan waye bayan zanin gadon data wanke yasan Basu da wanki domin shi yake wanke kayanshi dana hajiya gudun Magana ma a toilet yake sai ya Bata ta fito ta shanya ... Matsowa yayi kusa da ita Nan ya ga kayan Hajiya jikinsa har wani tsuma yake tsaban bakin ciki da bacin rai “Rauda!” ko kallonsa batayi ba Haka ta karasa shanyan ta,koma taci gaba da wankinta karasowa yayi tare da saka hannunsa shima ya fara wankewa d’agowa tayi da jajjayen idunta “idan kana kaunar Allah ka cire hannunka in kuma so kake ka jamin wani magana to” hajiyace da karaso gurin cikin bacin rai tace “tashi a nan!” shuru yayi kamar bada shi take Magana ba juyowa tayi Gurin Rauda “wato kin kirashi ki nuna min kin gamadashi ko kai kuma zanci mutumcin ka in baka tsame hannunka a cikin nan ba” mikewa yayi cikin dacin zuciya yace “haba Hajiya gaskiya abin kike baki kyautawa Bata da lafiya fa” zaman dirshan Hajiya tayi a kasa wani ihu ta saka “umaru ni kake fad'awa magana akan wannan yar isk'an matar ka to wlh Bari na Kara jajjada maka karka kuskura ka ma wannan karuwan ciki aure zan maka in aura maka Yar mutunci kamila ba karuwa wanda tayi cikin shege ba abin takaici da bak'inciki ma kanin ubanta ne ya mata cikin wlh zanci mutuncinka in baka bar nan gurin ba wayyo an shanye min d’a” hankali a tashe yace “dan Allah Hajiya kiyi Hakuri” wani tsawa ta buga masa “tashi ka bari guri kafin na kwashe maka Albarka”
d'aura hannunsa yayi akai Yana kallon Rauda dake kuka kasa kasa gurinta ya nufa kamar zai rumgumeta tsayawa yayi yana tunanin mafita hannunta kawai yaja suka nufi d'aki kulle kofar yayi da sauri Hajiya ta zo jikin kofar tana bugawa “wlh umaru ka bud'e kofar nan kafin na Saba maka ke kuma zaki gamu dani basai kinyi haka bane zai nuna kin mallakeshi saina kara mishi mata Nan da lokaci kad'an”

_aikin banza na d'auka yanzun Zaki Kara mishi matar ashe dai nan da lokaci kad'an ne kai Hajiya ki kiyaye mu fa😏😏kafin mu tada aljanu🤣_

Shuru Farouq yayi yana kallon Rauda dake kuka cire da mararta matsowa yayi gareta cikin tashin hankali yace “dan Allah kiyi Hakuri” da kyar ta mike ta nufi kitchen binta yayi cikin rawar murya yace “zan miki” wani mugum kallo ta Masa kafin tace “me?” gas d’in ya kunna kafin yace “abinci” tsaki taja “banso ka fita! Mahaifiyarka na kiranka plz ka barni mana dame zanji wlh a halin yanzun ko fuskanka bana kaunar gani” jiki a sanyayye yace “kiyi hakuri Rauda...” cikin tsawa tace “da akayi me kaga Malam ka barni fa” fita yayi ya zauna a kujewa ruwan zafi ta zuba cup sosai tasha ruwan domin kishi take ji tana Gama shan ruwan cikinta yayi wani i'rin murd’awa durkuwasa tayi kasa tana murkususu ganin jini ne yasa ta sakin ihu take numfashin ta ya tsaya cak da sauri ya nufi kitchen d’in gass d’in ya kashe tare da yin kanta “rauda! rauda!!” inna ko numfashi batayi d'aukarta yayi yana jijjigata da sauri ya nufi kofa da i'ta Yana bud'ewa ya ci karo da Hajiya har yanzun tana tsaye ko kallonta baiyi ba ya saka rauda a mota yana Shirin tada motar Hajiya ta bud'e murfin motar gefen da yake cikin bacin rai tace “karka kuskura ka fita in kuma ba Haka ba saina tsine maka Albarka gwara ta mutu kowa ya huta” da sauri ya kalleta sannan ya kalli rauda Kara kallon Hajiya yayi cikin tashin hankali yace “hajiya .....” katseshi tayi da “kar ka yarda ka musa min..........

*Aysha J.B*


61_62 +

Kamar ya d’aura hannu akai ya fasa ihu haka yake ji, kallon rauda dake cikin halin rayuwa ko mutuwa yayi ganin har yanzun tana sume ga jini sai bin jikinta yake, kara kallon Hajiya saratu, yai still itama kallonsa take “maganarki bata kan hanya hajiya! Zan kai matata asibiti a cetomin rayuwarta domin inna bukatarta a duniyata! Ina bukatarta kusa dani bazan iya barin ta cikin wannan yanayinba” da k'arfi ya figi motar Hajiya na qwala masa kira lna! ran maza ya baci tuni aka bude masa get ya cilla hancin motarsa asibiti dake kusa dasu ya nufa da i'ta cikin gaggawa aka tarbesu daki na musammam aka bata yaso ya bisu Amma sai nurse ta dakatar dashi ,tsayawa yayi yana kaiwa da komowa da sauri ya koma mota ya d'auki wayarsa Alhj ya kira ya kora masa halin da ake ciki kwantar masa da hankali mahaifinsa yai ta hanyar sanar masa yana nan zuwa nan da kwanaki ..
Bayan kwana biyu sai da rauda tayi kwana biyu kafin tasan inda kanta yake cikin wanan kwanakin ko lekota Hajiya batai ba, Sajida ke sintiri da rana misalin shabiyu ta fara bud'e idonta tun tana ganin dishi dishi har ta bud'e ldon tarr da sauri Farouq ya matso tare da kama lallausar hannunta “baby rauda sannu kin tashi yajikin ina yake miki ciwo mai kike so sannu” lokaci d'aya ya jero mata tambayar binsa kawai take da ido ganin yanda ya rame ya zabge sai uban hanci da idunuwa tubarkallah d'an murmushi ta sakar masa a hankali tace “bana bukatar komai sai ganin mahaifana farouq dan Allah ka saukwake....” bata karasa maganar ba taga ya sunkuyar da kansa kasa hawaye tagani yana d’iga akan tattausar hannunsa dake rike da nata cikin tsananin tashin hankali yace “ki dubi darajan ma'aiki manzon Allah kiyi hakuri ki daina abatan saki wlh bazan iya rayuwa batare dake ba ina kaunarki rauda! Ina tsantsar sonki ina bukatarki tare dani dan Allah karki barni” ya karasa maganar Yana langwa'bar da kansa .. ..

wani mugun tausayinsa ne ya kamata da sauri sajida ta bar d'akin tana mai tsananin tausayin yayanta , kwananta biyar aka sallamesu tattali tarairaya soyayya kauna kulawa duk farouq ta nuna mata ya dage sosai yana kula da ita bak'inciki kamar ya kashe Hajiya ganin ko fita baya yi, tayi masifa tayi fad'a har tagaji ganin ko sauraronta baiyi ba,

rauda kan ta kasa kwantar da hankalinta domin kullun cikin kuka da rokon Farouq ya saketa take shima sai dai ya samata kuka duk lokacin da ta bukaci haka haka suka kwashi wata guda zuwa wannna lokacin rauda ta warke rass Alhj ma ya dawo sosai Hajiya ta shiga taitayinta amma tana ganin Farouq da Alhj sun fita Nan zata shiga gallazawa rauda tare da saka ta aiki mai wahala rauda duk ta rame ta susuce bata cikin nutsuwarta yau tunda ta tashi take jin bacin rai gashi kanta na mata wani i'rin sarawa shi kansa Farouq yau shakkarta yake ji ganin yanda ta had'e rai bai ta'ba ganinta cikin wanan yanayin ba Haka yayi shirinsa matsowa yai gareta tana kwance sai jan tsaki take i'ta kad'ai d'agota yai tare da d'aura k'ansa saman Kirjinta bin nonuwanta yai da kiss tare da fad'in “baby rauda nayi missing d'inki sosai plz ki tausaya min ko kad’an nayi mana tunda kin warke ina bukatarki” wani i'rin Kallo ta watsa masa kamar zatayi magana sai tayi shuru ganin yanayin da take ciki ne ya sashi manna mata hot kiss a lips dinta kwantar da i'ta yai “ilove you har kullun kaunar ki na dad'e ,qaruwa a cikin ,zuciyata inna sanki matata” kallonsa tayi kawai bare da tace masa komai ba.

Haka ya fita ya barta kwance fitarsa da kamar minti biyar saiga Hajiya ta banko kofar “shegiya fito kimin wanki, kin sami gado kin kwanta kamar gidan ubanki karuwar banza duk anbi an mallakemin d'a” mikewa Rauda tayi kanta a sunkuye suna tafiya hajiya na zungurar kanta sai zaginta take ran rauda ne ya Kara baci aii bata san lokacin da ta juyo a fusace ta danki wiyar hajiya cikin wani i'rin murya take magana “mun tara ki yayi yawa yau kin kaimu bango ita baiwarki ce da Zaki ringa azabtar da ita? ko jakarki ce i'ta?!” jikin Hajiya ne ya fara wani i'rin rawa sai gwale idanuwa take.

saukan bulala ta faraji a jikinta fiyat fiyat ta rasa ta inna bulalar yake gashi har yanzun rauda rike take da wiyarta wani ihu hajiya ta kurma sajida dake barci ta tashi da sauri waje ta fito iya kakarinta tayi dan ta kwaci hajiya abin ya gagareta i'ta wlh Aljanun rauda sun birgeta sosai taji dadi kuma da suka mata haka da kyar makota suka kwaci hajiya ai da mugun gudu ta nufi daki ta kulle kanta sai ajiyar zuciya da shafa wiyarta take "ashe daman mayyace ban sani ba cabb da sauran aiki gabana dan wlh bazan bar mayya da d'ana ta cinye min shi ba" sajida ce ta kira farouq yana tsaka da aiki jin abinda ke faruwa ne yasashi bari aikin babu shiri ya dawo gida rauda ya tarar tsaye kik'am idanuwanta sai jujjuyawa suke kai kana ganinta kasan wannan ba ita kad'ai bace cikin fargaba da tashin hankali ya kama hannunta amma ko didin ko motsi batai ba yin duniyar nan yayi su shiga d'aki abin ya gagara Alhj ya kira ya shaida masa halin da ake ciki cikin gagggawa shima ya nufo gida nan ya kira limamin anguwar rukiya aka fara mata kafin malam ya kai aya daya sun sun kai biyar da kyar dai suka barta bayan sun jijjigata sosai domin buka kanta ta ringayi da bango tana wani irin murkususu sai nannadewa take kamar wata macijiya kai koni sai da na tausaya mata domin a wannan lokacin ko kai mara imani ,ne muddin kaga halin da rauda ke ciki sai ka tausaya mata..

STORY CONTINUES BELOW


YOU'LL ALSO LIKE


ZEE 'YAR BARIKI
10.2K
150
this is a story about a girl who's leave with out parent,batada wani sana'a se karuwanci,she leave with one guy Called joeboy,suna zauna ne kuma rayuwar ma'aurata kawai...

NI KISHIYAR UWATA CE!
18.9K
286
labarine akan wani uba da yake haikema yarsa ta cikinsa a gefe Kuma qawarta take yaudararta take fadawa lesbian ga Kuma uwarta itama da take neman qawayenta qarshe yari...

YA JI TA MATA
57.3K
6.1K
Wannan labari me suna YA JI TA MATA shine littafina na uku.... Labarin wani saurayi ne Wanda bashida aiki sai zina, a cewar sa ba laifinsa bane Allah ne yayi sa hariji...

ALKAWARIN MU
14.4K
189
Labari mai cik'e da Zazzafar Soyayya tausayi Romacing nadama tare da darasin Rayuwa

Kiss Me Dangerous | ✓
7.2M
194K
[OLD VERSION] "You shouldn't point guns at people if you aren't willing to pull the trigger-Lola." The way he said my name was like he was somehow reprimanding...

MY BESTIE'S HUSBAND
33.3K
2.1K
MIJIN AMIÑIYATA Lbrn wasu aminai da suka kasance basa rabuwa sai kwanciyar bacci, aurene ya zamo silar rabuwarsu wanda daya tayi aure tabar daya inda mijin dayar ya rinq...
bayan sati uku

yanzun kan alhamdulillah rauda suna zaman lafiya sai dai har yanzun ta kasa kwantar da haakalinta kwance take kanta gefe daya na mata ciwo "FAROUQ ji nake kaina kamar zai fashe ciwo yake min" ta karasa maganar kamar zata zubda kwalla..
da sauri ya bar takardun da yake hadawa ya matso tare da jawota jikinsa gabansa ne ya fad'i ganin yanda ta kara wani cika da fresh a hankali ta zuba masa idanuwa taka kallonsa ganin tashin hankalin karara akan fuskansa "ciki kuma?" abida yace kenan ya dauka a zuciyarsa yai maganar ashe a zahiri ne, lumshe ido rauda tayi bata san lokacin da wani lallausan murmushi ya subuce mata ba , shafa sumar kansa tayi "ina farin ciki da sake samun wani cikin a wannan karo ko zan rasa raina bazan yarda a zubar min da ciki ba nima inna son yaya aure na yana tafiya shekara biyu kenan Allah nagode maka" cikin tsananin tashin hankali yace "plz ki tausaya min a zubar..." cikin ihu tace "wlh ta dade bata tsine maka ba, in har cikinan za'a zubar bazan taba yarda ba kome zai faru ya dade bai faruba" ta karasa maganar tare da mikewa dafen da kanta.

*******

kichin nufa ta rasa mai zata ci fitowa tayi ranta a cunkushe tace "plz farouq muje yawo mana tunda nazo ban taba fita ba kuma ina so insha cakulet" yanda tayi maganar ba karamin dariya ya bashi ba domin wani narkewa tayi tare da langwabar da murya "zo kij to" make kafad'a "a a kaina ciwo yake min" lumshe i'don yai kafin ya mike "ki shirya to" cikin murna tace "yauwa mai sunan uncle" da sauri ta bud'e akwatin kayan aurenta wanda tunda aka ajiye ko kallonsa Bata yi dad'i yaji sosai a ransa wani riga da wando ta saka wandon ya kamata sosai Haka ma rigan sanna ta d'auko abaya ta saka aki tsayawa yai Yana kare mata kallo ganin yanda tayi mugun kyau matsowa yai tare da kama kugunta nan ya fara juyawa da i'ta "kai gaskiya baby rauda kinyi kyau sosai anya baza aka fasa wanna fitar ba..." Da sauri ta fad'a jikinsa kamar zatayi kuka tace "dan Allah Farouq na..." da sauri yace "me kika ce?" lumshe masa idanuwa tayi "farouq na" matseta yai sosai a jikinsa wani sanyin dad'i na ratsashi wayyo yau shine rauda ta fad'awa haka gaskiya yaji matukar dad'i dan karamin gyaleta ya yane Mata kanta dashi hannunta sakale cikin nasa suka fita a cikin gida suka tarar da Sajida da sauri tace "matar yaya wannan k'yau? Bari na muku selp na tarihiri" murmushi rauda tayi shima murmushin ya mata.

Ahaka Sajida ta musu picture kala uku daya hannunsu na riƙe dajuna daya kuma ta kwanto Kirjinsa na karshen shine ya tsaya a bayanta tare da kwanto kansa saman kafad'arta hajiya dake d'aki sai jan tsaki take babu halin fitowa domin wani i'rin tsoron rauda take yanzun sai da ta tura musu hotunan ta Whatsapp sannan suka fita a d'an karamin motar sa sunje yawo sosai inda ya kaita tasha askr da yoghurt sun zaga gari sosai da yamma lis dazu dawo tace "muje sai nama Sajida tsaraba ko?" a wani babban gurin siyayya ya tsaya parking yai kusa da wani had'ad'd'en mota kurawa motar ido tayi tunda suka tunkaro gurin gabanta ke wani i'rin bugawa hannunsa ta kama suka shiga nan kallo ya dawo kansu matsowa yai sosai kamar zai shige jikinta ransa na wani i'rin zafi ganin yanda kowa ke kalle masa mata jaka ta fara d'auka sannan ta nufi gurin takalma shi kuma yana tsaye gurin agogo yana dubawa tana tafiya ta tare da ta lura ba wata yar karaman yarinya ce tazo da gudu tana kuka kamata yarinyar tayi tare da fad'in "mamy kinga Dady da momy wai baza'a sai min jakaba wai ni ba am mata bane" ta karasa maganar tana kuka da sauri rauda ta juyo ta kama hannun yarinyar gabanta ne yai wani i'rin fad'uwa idan ba gizo i'danunta ke Mata ba wannan yarinyar kamar uncle umar dinta lokaci d'aya taji kaunar yarinyar har cikin ranta sunkuyowa tayi tare da fad'in "yi hakuri yarinyata ya sunanki" murmushin daya Kara hargitsa tunanin rauda yarinyar ta sak'ar mata cabbb Allah na Kama i'rin i'rin a duniya yanzun murmushin ma sak uncle na? "sunana rauda" da sauri tace "what!!" Sai Kuma tayi murmushi "sunanmu d'aya" dariya yarinyar tayi sannan tace "dadyna yana cemin baby kuma kullun Yana cemin yana sona yana nuna min hoton wata mata wai aunty na ce tana da kyau sosai kaman ki" ta karasa maganar tana dariya ...

rumgume yarinyar rauda tayi tana jin wani sanyi a ranta farouq na bayansu sosai suka birgeshi wata matace ta karaso tana fad'in "ke rauda zonan mutafi kin barni sai nimanki nake baiwar Allah yi Hakuri ta tareki da surutu" bata fuska yarinyar tayi tare da fad'in "aunty fati ni bazan biku ba ga mamy na samu zata siya min jaka ko" ta fad'i Haka tare da matse rauda wayyo maganarsu ma d'aya? "Ey man yarinyata zan siya miki d'agowa tayi nan Fati ta kalleta gabanta ne yai wani i'rin fad'uwa ganin Raudan uncle a zuciyarta tace "taf a zahiri ma tafi kyau kai gaskiya dole mijina ya mace akanki Ashe haka kike da kyau?" kallon bayanta tayi taga bayanan wani ajiyar zuciya ta sauk'e murmushi rauda ta sak'ar mata tare da Mika mata hannun sannan tace "yarinyar ki tamin kyau abani i'ta" dariya fati tayi sannan tace "ba matsala na baki sai dai akwai surutu kamar aku ya sunanki"

"Sunanmu d'aya da yarinyata" rauda ta fad'a tana Kara kallon yarinyar Farouq ne yayi Gyaran murya nan suka juya da sauri Rauda ta matso tare da fad'in "mai sunan uncle kaga baby nan dawa ta maka Kama plz tell me?" Kallon yarinyar yai shima Yana murmushi "wow gaskiya tana min kama da uncle d'inmu" cikin happy rauda tace yauwa Farouq na Ashe ka iya ganin Kama" mamaki ne ya Kara Kama fati mai sunan uncle haka take Kiran Mijinta! Kenan har yanzun uncle na ranta? Allah sarki ...

Fati tace "to k'anwata mu zamu tafi rauda sauko muje ko dadynki na jira"

"nifa momy sai mamy nan , ta siya min jaka tunda kin ki siya min" da sauri rauda ta bata jakan data daukawa sajida "gashi yarinyata kina sona nidai Ina sanki" cikin murna yarinyar tace "lahhh nagode mamy nima inna sanki" kiss yarinyar tama rauda i'tama rauda ta Mata kiss fati kamar zatayi kuka dan tausayin rauda ajiye yarinyar rauda tayi tana Mata murmushi hancinta yarinyar taja tare da Mika Mata yar yatsarta "mamy kawo naki nima kimin haka dadyna yake min kullun sai yace baby ina sanki nima sai nace dady ina sanka" wayyo Allahna wani hawaye ne ya saukowa rauda durkusawa tayi taja Hancin yarinyar nan itama ta bata yar manuniyar yatsarta suna had'a yarinyar harda lumshe i'do tace "ina sanki new mamy" cikin kuka da dariya rauda tace "inna sanki yarinyata mai kama da ..." Sai tayi shuru a hankali tace "mai kama da masoyina ina sanshi kamar raina kullun kaunarsa kara daduwa take cikin zuciyata" farouq baiji abinda tace ba amma Fati taji kama hannun rauda tayi tare da mikar da i'ta tana share mata fuska "ohh sorry my sister duk kukan akan rabuwa da yartaki ce" murmushi rauda ta mata sannan tace "Baki fad'a min sunan ki ba sanna ga wayata ki mana pic plz.." dariya Fati tayi sannan tace "sunana Fatima" nan ta karbi wayar ta d'auke su hoto kala biyar masu kyau rauda tace "nagode sosai Aunty fati" yarinyar kuwa sai tsalle da murna take an siya Mata jaka kallon fati tayi sannan tace "Aunty fati nima na zama am Mata tunda mamy ta siya min jaka" rauda tace "yarinyata kice momy ba aunty ba" bata fuska yarinyar tayi "nifa ba momy na bace momy na tana hoton dady" dariya fati tayi k'arfi da yaji uncle uncle ya hana yarinyar tace mata momy sai aunty fati hakan na Bata mata rai matuka amma kasancewar macece mai tsananin hakuri sai ta jure kullun yana makale da hoton rauda shine yace i'tace mamanta wani lokaci sai dai ta musu dariya.. nan sukayi sallama yarinyar na d'agawa rauda Hannu tare da sakar mata murmushi haka rauda ta sake d'aukar wani jaka da takalmi da gyale suka nufi gida cikin ranta tana fad'in komai nasu irin d'aya harda murmushin ma ...fati na shiga mota tace "ka gudu ne" murmushi uncle ya mata sannan yace "inna tsaya za'a samu matsala banson ganin damuwarta da hawayenta kema shaida ce nasan Kuma tayi hawaye " da sauri fati tace "kamar kuwa ka sani wlh ta bani tausayi har yanzun fa tana sanka tsananin kaunar da take maka mijinta ma mai sunan uncle take ce masa" murmushi uncle yai tare da jawo baby jikinsa "raudata nima inna sanki sosai a inna ta miki kiss" nuna Masa tayi Nan shima ya Kara manna bakinsa ya mata kiss murmushi kawai fati tayi domin inda sabo ta saba tun tana jin haushi har ta daina jakar ya karba yace "baby zan ajiye miki" haka suka tafi daman hanyace ta biyo dasu...
63_64 +

Lokacin da yai parking motarsa duk jiki a sanyayye suka fito kama lallausar hannunta yai ganin jiri na niman kada , i'ta manna kanta tayi da kirjinsa lokacin d'aya ta fara jin wani mahaukacin barci lumshe i'don ta fara a hankali yace "barci
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment