Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels 24/07/2020 à 12:47 - Les messages envoyés dans ce groupe sont désormais protégés avec le chiffrement de bout en bout. Appuyez pour plus d'informations.
24/07/2020 à 12:47 - Vous avez créé le groupe “Mak'otan Aljana by RAHIMA”
24/07/2020 à 12:48 - Vous avez retiré Aishatuwalle
24/07/2020 à 12:51 - 👸🏻Princesse👸🏻: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__

*MAK'OTAN ALJANA*




😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈



_TARAWA DA RUBUTU TAWA_
*RAHIMA FALOLA*
_PRINCESSE_👸🏻

*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*👩🏻‍💼👩🏻‍💼👩🏻‍💼
*GODIYAR SU CE*
And now
*MAK'OTAN ALJANA*





🇳🇪 *TAURARIN NIGER*🇳🇪
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼





*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*



0️⃣1️⃣↪️1️⃣0️⃣

Mun kasance cikin babban gidan, gidan haya ne mai d'auke da d'akuna biyu da douche da gwadala (kitchen) sai d'an hilin gida karami, muna zaune cikin aminci da mugunta juna tare daidai gwargwado muna bawa kowa hakin shi.

B'angaren dama mu, a kusan mu akwai Naïma wada mijin ta ya rasu ya bar mata yara biyu duk maza (Moussa da Yahaya), ni kuma ina zaune da mijina da yara na uku( Abdullah, Nazifi, Firdaoussi).
B'angaren hagu kuma Ousama Soja ne sai k'anwar shi Lya'atou dake jami'a, kusa dasu kuma babu kowa à cikin gidan.

Idan aka mik'e kuma za'a samu ciki da falo da bayi sai d'an karamin tsak'ar gida irin namu nan ne mai gidan ke zaune, baida mata tsoho ne irin tsofin da suka ga jiya su kaga yau kuma suke sa ran ganin gobe (Daouda konDavid) dan duk rabin rayuwar shi a turai yayi ta, katon hiline wanda ya kunshi itatuwa masu duhu idan dare yayi.



Mukan fito tsakar gidan don yi hira lokaci lokaci dan gaskiya idan akace 'yan bariki to mune na k'arshe,mijina sai dare yake dawowa daga office, ita kuma Naïma koyawa take lycée ( secondary)dan haka ba kulum take zuwa ba, shi kuma Soja yakanyi sati biyu yana aiki amman idan aka ce maku ya sauko to yana gida ko k'ofar d'akin idan mun fito shan muyi hira ko tare da 'yan mata, shi kuma tsoho baya koami sai zaman kashe wando a kofar gida yana dara ( dame) irin ta nasaru, wani lokacin tare da Ousmane suke yi ana shan sigari.
Mukan zauna mu tsokani junan mu muna kalon yaran mu na wasa, wani lokacin tsoho David ke bamu labari gwagwarmaya da suka sha a turai, mukan tsokani Ousmane akan yaushe zaiyi aure shekaru na ja rayuwar mu muke cikin kwanciyar hankali kafin mu samu wata mak'ociya kusan gidan Ousmane da tazo ta hana mu shakat ta hana yaran mu shak'atawa.




A wata ranar asabar muna zaune dukannin mu a tsakar gida David yake sanar damu za'a samu bak'uwa, yana gama magana kenan sai muka ji tsayuwar mota sai gashi ana shigowa da kayan ta, ta shigo mun gaisa, ta wuce David ya bata clé (makuli)mu kuma muka ci gaba da hira, har Ousmane yana cewa ya samu wurin lab'awa kafin ya samu matar aure, nake cewa "haba dai Ousmane shekara 35 amma har yanzu ko kanwar ka da ke jami'a 25 gare data gama zamu wanketa", yace ina mama Lya sai kin samomin mata da kanki wada ta iya abinci da tarairaya miji kamar ki"
Mu duka muka sa dariya.
Can sai David yayi gyaran murya ya fara bada labari su a lokacin da suna tura kaza kaza......




Bak'uwa ta fito itama ana fira da ita sunan ta _FOURAIHA_ doguwa ce ajin karshe gata fara ga gashi.... tinda muka had'a ido da ita naji gabana ya fad'i n'a kauda kaina gefe hirar ma ta gundure ni na tashi na bar wurin.


Bayan sati da zuwan ta muna zaune nida Naïma muna hira nake ce mata, "wallahi kinsan wani abu?"
"Ina zan sani sai kin fad'a".
"Humm bak'uwa nan nidai ina jin wani abu gamida ita dan idan mukayi ido hud'u da iya gabana fad'uwa yake"

"Kedai maman Lya cikin abubuwa da canfe canfe Lamar wada ta girma wajen kakar ta"

"To shikenan tinda baki yar da ba"

"Kar kisa komai a ranki 'yar uwar kisa alkhairi"

"To shikenan"

Mun gama maganar kennan muna juyowa sai ga Fouraiha bayan mu ga alama taji duk abinda muka tatauna, gabana ya yanke ya fad'i!!!!!


Tayi wani munafinkin murmushi tayi mana sanu da gida.

Kusan goma da rabi na dare ina kwance da yake baban su Lya ya shigo a gajiye har ya kwanta ni kuma ina kwance saman salon (kujera) mai zaman mutum uku ina kalon wani film n'a Zombies abin ban tsoron kuma ina chatin da waya kawai saida naga wutar d'akin ta mutu, télé na nuno wata halita mai ban tsoro babu kyai gani ai da gudu nayi d'aki........









*(Ku biyoni domin jin ya zata kaya)*




















_PRINCESSE RAHIMA CE MAI K'AUNAR KU HAR KULUM_✍🏼✍🏼👸🏻👸🏻👸🏻
24/07/2020 à 12:51 - 👸🏻Princesse👸🏻: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALALA*
_PRINCESSE_





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*






🇳🇪 *TAURARIN NIGER*🇳🇪
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼






*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*



1️⃣0️⃣↪️1️⃣5️⃣


Da gudu nayi d'aki na kwanta, can nashi shuru kusan minti sha biyar har wani irin barci ya fara d'auka ta,harda mafarki.
Wai gani kwance na kasa komai Amman ina ji a jiki na kamar an rikeni, gashi dai dare ne sai farin wata daya ratso fenêtre (taga) ina so in d'aga daga kwanciyar da nake amma ina, sai na kalo k'ofar d'aki na wata mace doguwa ga tsayi cikin wata jar riga, gashi duk ya rufe mata fuska, ta ratso gini ta wuce ba tareda ta bud'e k'ofar ba, zuciya ta sai dukan tara tara take gashi na kasa motsi, macen ta tako tazo ta tsaya gaba na, na kasa motsawa ta rike wuya na ta d'oramin wuk'a tana yankawa amman baikai ga yankuwa ba.

Sai ihhuuuuu nake ina cewa "dan Allah ki bari mi nayi maki dan Allah ki bari"

Da taga wuk'ar taki yanka ni sai kawai ta shak'eni saida taga na dena lunfashi...


Ai da sauri na farka ina zufa ina sauke ajiyar zuciya...
Naje na d'ibi ruwa na sha na zauna salon (falo)ina maida lunfashin kawai sai naga matar nan bafa a mafarki ba aa zahiri ta shigo ta bango ta tunkaro ni nikuma na kasa motsi,abinda ya faru cikin mafarki haka ya faru sai ihummm nake shi ya tasheda mai gida na ya fito a guje "lafiya miya same ki?"


"Wani......"na kasa magana kamar an rufemin baki Haka ya jani muka koma d'aki ina ta k'ark'arwa kamar mai jin d'ari ni kuma duk a tsora ce n'a, haka muka kwana.



Washe gari mun fito zan je kasuwa na had'u da Naïma mun gaisa take tambaya ta lafiya jiya tana ta jin ihuu n'a?

"Hummm ki bari kedai nan dai na sanar da ita abinda ya faru"

"Lah wannan abu akwai ayar tambaya, nima fah banyi barci ba" cewar Naïma.

"Ke dan Allah mi ya faru?"


"Hummm ina correction de (gyaran paper d'in 'yan makaranta) nasan yara na sukaiawa biyu da kwantawa wai sai nake jin hira a d'akin su suna hira da shewa, nayi kira babu wanda ya amsa, ta tashi naje na kuna wuta amman gasunan kwance suna barci, na juwo nace gaskiya na gashi ya kamata in kwanta, ina bada baya kuma hakanan, na sake lek'owa amma shuru ai sai gaba na ya fad'i,sai akamin tsuki ina fitowa naji a kitchen pompo n'a zubar ruwa nace ko ruwa aka dauke yanzu aka maido bari naje na kashe, ina kashewa ana kunnawa,ai da gudu na baro kitchen d'in, na dawo wajen yara na na rungume su haka muka kwana dan tsoro kala kala aka bamu"


Nayi tagumi ina sauraran ta ohhh mu kuma wace irin masifa ce wannan....


Ashe bamu ga komai ba ya'zu ne za'a fara wasan......





*Kuyi maleji da wannan sai gobe insha Allah*





_DOMIN GYARA KO SHAWARA GA NUMBER NA +22792494512 🤗🤗_







*Princesse Rahima ce*👸🏻✍🏼🇳🇪
24/07/2020 à 12:51 - 👸🏻Princesse👸🏻: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALALA*
_PRINCESSE_





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*



*(INA JIN DAD'IN COMMENTS NAKU YAN SANI NISHAD'I BA'YI ZATON BOOK ZAI SAMU K'ARB'UWA HAKA BA)*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻








🇳🇪 *TAURARIN NIGER*🇳🇪
(Tsintsiya mad'aurin ki d'aya)✍🏼✍🏼






*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*





1️⃣5️⃣↪️2️⃣0️⃣



Muna cikin magana saiga Lya k'anwar Soja, zataje makaranta daganan ta biya kasuwa siyo kifi Soja yace gobe yana shigowa.dan jiya ba gida ya kwana


Mun gaisa take cewa mi ake rautaunawa itama taji. Muka ce kefah yarinya ce kiyi hankuri har ki girma, b'ata fuska tayi ita yaza'yi ace wai yarinya, ai taji gulmar wasu abubuwa masu ban tsoro ake, muke sanar da ita abubuwan da suka faru, ai sai ta bushe da dariya,"Kai maman Moïs baki rabo da abin dariya wallahi da keda kawar taki to ya za'ayi hakan takasan?"


Nace "kefah 'yar raini hankali ce ana gaya maki kice wai aa"


"Maman Moïs tace ki barta dai idan itace sai tayi fitsari a wando"


"Kudai ne baku rabo da abin dariya ni fah ban yarda da irin wannan abubuwan ba, kawai nasan ace mana a jami'a idan mutun ya gaji zai iya imaginé (imagination) abubuwa da dama kuma kwakwal wa take buk'atar hutu, ko kuma mafarki kuma nasan mafarki ba gaskiya bane"

"Kijin ko matsalar d'an boko kenan" inji Naïma (mamar Moïs,Moussa)


"Kidai barta idan abin yaje gareta zata gane"


"To yayuna n'a tafi kada na makara sai na dawo"


Munyi salama da ita ta wuce gaba, a bakin babban k'ofar gidan (get)suka had'u da Fouraiha tana shigowa suka gaisa, har ita Fouraiha ke tambayar Lya mitar mi take ne ita d'aya ?

"Hmmm ki bari nidan wad'ancan matan wai jiya basuyi barci ba"

"Ke dan Allah to mi ya hana su barci?"


"Wai tsoro akayi ta basu"
Nan ta kwashe komai da muka fad'a mata ta gaya mata.

"Kai haba kam eh lale sunji tsoro"

Sai Lya tace"ke nifah ban ma yarda da irin wannan abubuwan ba wani aljani, ko tsafi ko.... Nasan dai sciences technologies de tace kaza da kaza"


Fouraiha da taga surutun bamai k'arewa bane ta mata salama tayi gaba dan shirin daren yau....



Kicib'us mukayi da ita muna shirin fita babu wanda yayi magana sai ita ce ta gaida mu, ciki ciki muka amsa mukayi gaba.




Bayan Lya ta dawo daga jami'a tayi tuwan rana kifi ne da dankali turawa tayi hahin zob'o taci ta k'oshi har ta aikawa da mamn Moï da maman Firdaoussi, ita Fouraiha bata nan, kuma shi taci kafin ta kwanta tayi karatu sosai sai kusan sha biyu ta kwanta.



Ciki barci wajajen biyu dare naji ana buga k'ofar d'akin na kamar za'a b'aleta, mun farka nida baban Firdaoussi muka je baki k'ofar muna tambaya k'asa k'asa...
"Wane ne?"

"Maman Fido bud'e dan Allah wallahi ba lafiya"


"Lya kece miya faru?"

Duk a firgice take Kayan barci gare ta dogon wando da wata 'yar shimi, gashin kanta duk a barbaje, sai kuka take.

"Lya kiyi shuru ki gayamin miye daga ina kuma cikin wannan shigar?"



Cikin kuka tace "gida gida.... Tana nuna gidan su"

"Ki nasu ki gayami mike faruwa?"

"Gidan nan akwai aljanu"

Cikin mamaki nace "aljanu kamar ya?"


Nan fah ta fara zubar kamar k'any'an tana yi tana kuka, tana sanar dani abinda ya faru da ita.....


"Mama Fido ai kinga lokacin da na kawo maku abinda na dafa to dama kifi hud'u na siyo na dafa biyu na raba maku d'aya keda mama Moïs ni kuma na ci d'aya rabi da rana rabi cikin dare,to har na kwanta can motsi mutun ya tadani cikin kitchen kamar ana fasa wani abu et kuma wuta a kune"

"To ai ko ke daya ce ko soja ya dawo ne?"


"Aa ni d'aya ne wallahi, n'a tashi naje don na gani waye a kitchen, ina kaiwa k'ofar kitchen sai naga wuta ta d'auke, sai na kuna kuma kamai yana muhalin shi kamar ba kowa, kawai sai nace ko dan na gaji ne ko mafarki nayi"


"Nifah banga abin rudani anan ba"


"Koda na kashe wutar, ina komawa dakina d'ora kaina saman matashi (filo) keda wuya kuma naji komai ya dawo sabo ana abinci cikin kitchen na ji tsoro amma haka na kama hanyar kitchen ina kaiwa bakin k'ofar komai ya tsaya tchak!! Na shiga na na isko gaz kune, abun gasa kifi sama harda kifi d'aya a saman shi, saida na zabura dan nidai nasan kifi a frigo na barshi kuma na kashe komai, hata abin gasa kifi yana lak'e a katanga tare da manyan koshiyai"


"To!!!! Sai kika yi yaya?"

"Sai nayi kamar na tafi na kwanta na lab'e dan sai naga wane mutun ne kemin yawo da hankali, bayan na kashe gaz da wuta har abin suyar kifin na d'auke shi na rufe kinfi"


"Sai miya faru?"


"Kinsan mai na gani?"

"Ina zan sani sai kin gayamin"


"Hummm da ido na na ga wuta ta kuna kanta, abun suyar kifin ya tashi yazo ya d'ora kanshi saman gaz, wutar gaz ta kunan kanta, kashiyar juya kifin ta fito daga cinin ma'ajin ta tana motsa kifin da kanta"


"Ya salam!!!"

"Allah mama Fido saida nayi fitsari a wando vatare da nasan abinda ke faruwa ba, Can naga kifin yana kwashe kanshi cikin kwano da koshiya sai gaz ya kashe kanshi, kwanon yana yawo a sararin samaniya, wutar kitchen ta mutu komai ya tsaya,saiga kwanan ya fito yazo har a falo bisa table, sai ga télé (telenbijin) ta kuna kanta, télécommande (remote na chanza tashoshi wlh bansan lokacin da na fito ba ta fenêtre (taga)sai k'ofar gidan ki"


"Kennan k'ofar gidan ku rufe take?"

"Eh a rufe take"

"To muje mu duba"


Mun tafi tareda mai gida na, lale k'ofar rufe take mun bud'e mun shiga amman komai a mazaunin shi yake hata kitchen komai daidai, saida da aka tab'a gaz anji shi da zafi....

Muka ce mata to ba komai tace ina ira wallahi bazata kwana gidan ita d'aya ba, dole muka ce ta biyomu mu kwanta tare.....



*Washe gari....*








*Comment*
_and_
*Share*




_Domin gyara ko shawara ku tintub'i wannan number +22792494512 na gode_😇😇








*PRINCESSE CE*✍🏼✍🏼👸🏻
24/07/2020 à 12:52 - 👸🏻Princesse👸🏻: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALALA*
_PRINCESSE_





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*






*Ina ganin comment d'inku na gode sosai Allah yabar k'auna*




🇳🇪 *TAURARIN NIGER*🇳🇪
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼



2️⃣0️⃣↪️3️⃣0️⃣



*Washe gari*

Tinda safe Soja ya tadamu daga barci yana bubuga k'ofa taki budewa ko ina take yana zage zage dan bashi hankuri ko kad'an.


Ni na fito nace yayi hankuri ai gata nan wajen mu ta kwana.


"Tana ina?"

Lya ta fito daga cikin gida na duk a tsorace take dan tasan shi ba yada Wasa idan ya hau kad'an yake jira ya maketa.


"Kam uban can miye haka ? Daga gidan iban wa kike da wannan shigar?"

"Yi hankuri zo muje zamu zan sanar da kai abinda ya faru"

Mun shiga gidan su duk na gaya mashi itama ta maimaita mashi abubuwan da suka faru da ita daren jiya.

Mi zaiyi inba dariya ba kamar an aiko shi, "kar ki cemin da wannan shekaru naki kina irin wannan tunanin na yara, gaskiya kin bada ni"


"Wallahi grand frère (yaya) ni ba yarinya bace nasan abinda nake gayama ka ka yarda dani"


"Eh na yarda da ke, wuce ki chanza kaya jikin ki kar kuma nasake gani kina hana mutane barci"

"To grand frère....."

Bai bari ta k'arasawa ba, "ya isa wuce kije".


Soja yana girgiza kai ana cewa Lya ta girma mai irin wannna tinanin, dan shi bai ma yarda da irin wannna sirkulen ba bale wani aljani .....yana kalon mu a matsayin wasu tab'ab'i.
Ni kaina da Bata faru dani ba bazan yarda ba.
Haka muka ci gaba da rayuwa cikin tsoro da fargaba.

*Bayan sati d'aya*

Ousama Soja yayi dare a bakin k'ofa dan har David ya riga shi kwanta wa, idan yana so yayi waya da budurwa shi dake kasar waje haka yake zaman shi k'ofar gida, sabida lokutan mu ba d'aya, to haka ta kasance dashi a ranar, ya fara Waya kenan "masoyiya gani ina kalon sararin samaniya ga taurari nan gwanin kyau Amman basu kaiki kyau ba" Ousama mayaudari ne ga duk macen da shiga hanun shi, to wannan ranar dai abun bai je mashi yanda ya kamata ba.

Suna cikin waya sai tana tsinkewa réseau (network)na yankewa.
"Allô allô....(Hello hello) sai kiran ya yanke yana k'okarin maida kiran wata irin guguwa ta taso ta turnike shi,yana cikin kare fuskar shi guguwar ta tsaya koda ya bud'e idonanun shi ya hanko wata mace tana tunkaro shi cikin doguwar riga bak'a.

"Wake nan?wake nan?"

Cikin duhun dare bazai iya tantance wacece ba, haka ya cigaba da magana "ki tsaya anan wacece?"


Mace ta tsaya nesa dashi, koda ya ga haka sai yayi anfani da wayar shi ya kuna hitilar ya haska.........







(Wa zai gani?domin sanin yanda zata kaya ku cigaba da bibiya ta)


*Kuyimin uzuri wallahi ciwan kai na wuni dashi, ina barar adou'oinku*🤲🏻🤲🏻🤲🏻🤲🏻









*Comment*
_and_
*Share*






_Domin gyara ko shawara ku tintub'eni a wannan lambar +22792494512😇😇 na gode_









*PRINCESSE CE*👸🏻✍🏼
24/07/2020 à 12:53 - 👸🏻Princesse👸🏻: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALOLA*
_PRINCESSE_





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*






🇳🇪 *TAURARIN NIGER*🇳🇪
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼



3️⃣0️⃣↪️4️⃣0️⃣



Koda ya haska baiga kowa ba kawai sai yace barci yake ji,ya kamata yaje ya huta,ya shigo gida kenan baikai ga kawowa k'ofar gidan shi ba ya hangi macen d'azu tana kisanto shi, "ya akayi tazo har nan?" Cikin zuciya yake magana, wannan karon baiyi magana ba daya aza k'afa d'aya itama ta aza ai sai ya ari na kare sai gudu sai cikin gidan shi ya rufe k'ofa da gudu sai cikin dakin ya rufe duk ya jik'e da zufa ga tsoro duk ya mamaye shi, yana sauke lumfashi can ya juya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

2 Comments On MAKOTAN ALJANA
avatar
umar-faruq

1 year ago

Reply

Jazakallahu Khair

avatar
nana-2

1 year ago

Reply

Masha Allah Allah ubangiji ya qara basira yaushe zamu samu cigaban pls????yamin Dadi sosaii

Please Login or Register in order to submit comment