Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dauke shi a makofin kaddara . Inalillahi wainna ilaihir rajiun kai shattu ni yau ya zanyi Fatomo ban dauko ba an daukomun lailah haillah... Haba Fatima kiyi hakuri kaman yanda liman yace mun san kaddara ,kuma ko wani cikakken musulmi yayi imani da ita kiyi hakuri wannan shine kaddarar mu .cewan Abban Shatu yana girgixa kan takaici da damuwa idon sa ya sauya kala zuwa jah .

Don dole Umma tayi shiru tana girgixa kai kurum...nasiha da ayoyi da nafsi sosai Liman ya jawo maawa Oumma da Abba kamin ya mike su fice tare da Abba ,abba kam wurin sayar da maganin itacen gargajiyan sa ,amma duk taron mutanen nan ya kasa komai na sallaman su ,damuwa ya taru yayi masa yawa.

Jaririyar Yawindo ta fara gyarawa tsaf ,kamin ta dora mata ruwan zafi ya tafasa da magunguna ...sannan ta juye a bangaje babban na kwano takaishi bandaki .

Bin bayan ta shatu tayi ba tare da tunanin komai ba ,don ita fa sam ta manta waida wani abu shi wankan jego....Anan ne Yawindo ta gasgata abun da take sakawa a kwakwalwarta gameda Shatun...batace da ita komai ba har ta sirka mata ruwar ,ta fito tabar ta tayi wanka kaman yanda tasaba . Tunkan Shatu ta fito ta ke kyenkyesa mawa Oummsn nata abun da tagani dan gane da shattun na gasgatar mata cewar ba diyar ta bace .
Dai_dai mareeya na shigowa garken...kukan idon ta na ya kafe sai dariya Yawindo da gske ne Wannan jaririyar bana Shattu bane..? Cewar Mareeya fuskan ta dauke da murnan jin mgnan da yawindo ke fadi mawa Ammie .

Kwarai kuwa da gske ni nagani da idona ,Shatu tana nan da mutumcin ta na ya mace budurcin ta na tare da ita ... Wannan shine xancen karya!!"

Cewar inna wuro wato mahaifiyar jauro dake nufowa xuwa inda su Yawindo suke . Adai dai kuma Shatu na fitowa daga bandaki tana amsa Mareeya da cewa" wayace maki ba diyata bace?? Wannan jaririya diyatace... Kwa fadi dai gskiyar mgn Oummam hardo ta kuma katse su a karo na biyu.... Ni ba wani mgn ce mai tsawo ta kawoni wurin ku ba ,nazo ne ku ji kusani D'ana Hardo baxai Auri diyar ku ba...wacce tagama iskancewa ta yada budurcin ta a diniya ,aradu Hardo baxai auri Shatu ba na fadeku .... Habawa InnaWuri auren da aka daura tun shatu na shekara 8 a duniya a yau xakice kin warware saboda wannan dan karamin dalilin da zaa agano gskyar lamarin?.

Cewar Oumman shatu tana mikewa daga tsaye ,cike d kwantar da muryar ga innan Hardo.

A zafafe Innawuri ta juyo kaman zata bugi umman Shattu...wannan ne karamin dalili? Lailai ne fatima ,wato ke kika daure mawa yar taki gindin yin iskancin ta...ta zubat mana da mutumci d dangin mu allh ya saka mana ... Sai kuje ku raini yar shegen! Tana fadin haka ta fice fuuuuu... Kwallah ne ya hau kwarara a idon Umman shatu...wanda ganin hakan yasa shattun saurin shiga buka ,zuciyarta na mata zafi .

Zama tayi a saman wahalalliyar katifan ta ,tana kai hannu hadi da daukan jaririyar d babu ko kayan da xaaa samata babu ,sai wani farin zani irin ta fulani da aka rufeta dashi.... Ganin jinin dake fita saman goshin yarinyar yasata saurin kai..............



_*Littafin WALIJAAM na kudi ne kaman yanda kuka sani*_
_*Ga masu bukatar wannan littafi xasu na iya mgn dani ta wannan whatsap link din👇*_
https://wa.me/qr/7UGIAODZY3LON1

_Normal grp 200_
_Vip grp 500_
_Spc group 1k👌_

_Idan kati xaki turo MTN ne ._
_Idan kuma ta account ne ta nanan👇_
_0028799846_
_Farida Hashim Stanbic bank_

_Yan niger kuma zaku tura katin 500f ne kati na Airtel ta wannan number na kasa👇_
_+22797780373_
_Idan kuma Spc grp kk bukata 800f ._

_*Maman teddy🧸*_
*🐄WALIJAAM🐄*

_free page_
_11_12_
*_Ga masu bukatar wannan littafi xasuna iya mgn dani ta wannan link din 👇_*
https://wa.me/qr/7UGIAODZY3LON1
_FREE page na dab da karewa ,Ki tausaya ma yar mutan mallawa kar ki fitarmun da littafi idan kin siya ,kema kar ki karantamun idan ba biya kikayi ba don Allah._
*_SADAUKARWA GA DUK KANIN FULANI🐄_*
*Alheri writers asso.📚*
_________________________

" Shatu ne ta kai hannun ta tana shafan inda jinin ke zuba mawa yarinyar ,wanda bata lura dashi ba sai a wannan lokacin hannun ta tasa tana shafa inda jinin ke fita duk da bada yawa ne yakefita ba ,amma hankalin ta ya tashi matuka. Bata ankare da shigowar mareeya ba sai maganan ta da taji tana xama gyefen ta kamin tace " Shatu kiyi hakuri komai mai wucewa ne a rayuwa kum...wani wucewa ai wannan abun da ta jawo mawa kanta baxai ta6a bille mata ko ya haifa mata da mai ido ba ,kuma tayaya zai wuce mareeya? Ai sai kin fada mana inda kika dauko wannan diya sannan...Cewan Oumman shatu da shigowar su kenan bukan ita da Yawindo.
Aa Fatima kar ki manta da maganan liman mana komai fa kadara ce,kuma mun san wannan yarinya bata aikata wannan abun da ake zargin ta dashi ba...don haka mu bita ta lalama ne muji inda ta tsinto wanga jaririya.
Nisawa Oumman shatu tayi badon hankalin ta ya kwanta ba ,ta koma tana xama jarab a kasan tabarman kaba...amsan yarinyar Yawindo tayi tana kara gyarata hadi da nadeta cikin zani tana shafa mata mankade akan raunin da akaji mata garin dukan shatu da Oumma keyi . Sai da ta gama natsata sannan yawindo ta bata dafaffan kindirmo don ya dau cikin ta sosai ,sai wani yin nan nan da ita take kaman mejegon gskennan... Sai da Yawindo ta kammala ne sannan ta bar bukan hadi da nufan wurin liman . Wanda bata boye masa komai ba ta fadesa duk abun da ta gani akan Shatu da sanar masa cewan Wannan jaririya ba Diyar ta bace.
Hamdala Liman yayi kamin yayi saurin nufan Wurin sana'ar Baffa don ya sanar masa da komai .
Mutane ne tun daga nesan rumfan Baffa tankam ,dagani kasan sunyi babban bako . Amma da liman ya matsa kusa sai yaga abun da ranshi yayi matukar baci don mahaifin Hardo ne da shi kanshi hardon sun tsaya akan Baffa basuyi duba ga Mutanen da sukazo rumfar nasa ba suke tsitsaya tsiya da masifa hadi da cin mutumci .

Bazan Auri Shatu ba ni nama saketa ,taje ta auri wanda suka saba sheke ayansu har yayi mata cikin shege ya Aureta. Nidai bazan auri ragowa ba ,kuma wlh banyafe ba abun da akamun...cewar Hardo yana wucewa fuuuu yabar mahafin shi yana cigaba da zagi da cin mutunci .

Shikam Baffa dukar ds kai kurum yayi ranshi na masa wani irin suya ,a zuciyar shi yana ayyanawa cewan daga yau Shatu tabar masa gida. Hakuri ake baimawa Baffa gyefe guda kuma wasu na janye Baffan Hardo da yake abu kaman xai bigi Baffa. Kowa a wannan wuri tausaya mawa Baffa yake da wannan iftilain abun kunyar da ya same shi ,wasu na cewa a zukatan su wannan ai shine baka jawo ba an jawo maka.

Liman kam wucewan da Baffan hardo yayi yana kumfar baki da zage_xage yasa shi zama yaana fuskan tar Baffa da hankalin shi sosai ya tashi . Kayi hakuri Malam Yakubu ,kar kayi fushi ko kullatan diyarka ,anan ne agaban sauran mutanen ya kwashe komai yanda ya faru da abun da Yawindo ta sanar masa ya fada masu . Hamdallah duka wurin aka dauka ,wanda har a wannan lokacin Baffa baiyi sauka ba ,budan bakin shi cewa yayi tom liman ita wannan yarinya yar wacece a ina ta samo....??

Malam Yakubu na lura duk gabaki daya hankalin ka yagaxa kwanciya ,ni ina rokon ka abaimawa Yarona Auren Wannan yarinya ta wurinka daman na dade inason mu kullah haalaka wacce babu rabuwa a tsakanin mu ta har abada.

Wani irin tsit ne wurin ya dauka ,kowa yagaxa motsawa don jin mgnan da Alhji Jalingo ke fadi da bakin sa.... Cigaba yayi da cewa " kayi mun alhairai maban banta na rokeka Malam yakubu kabaimawa dan dana haifa Aishatu ko nima auren nata zai xama silar shiriyar nawa yaron. Don duk wacce ya kalli shatu yasan iyayen ta sun bata tarbiya kwarai ,shiyasa nake roka...Haba Alhaji Ai Shatu ya ce a wurin ka ,wlh kamin komai nima ,basai ka roki wani abu daga gareni ba alhji ,indai wannan abun kuwa nawa ne kasa mawa ranka tamkar naka ne ,don haka ni Yakubu na bai ma Yarona na wajen ka Auren Shatu.

Mashaallh Alhmdullillah...Abun da kowa ke fadi kenan a wannan wuri ,kamin Alhji jalingo yace " Nagode kwarai malam yakubu ,ina nima alfarma idan babu damuwa..... Cike da yabawa da hali da dattijanta ka ga dattako irin na Alhji Jalingo da bai nuna banbanci tsakanin talaka da mai Arxiki Baffa yace munaji Alhji .

Nisawa yayi kamin yace" yanda suka saki wannan yarinya anan wurin sakin wulakanci inaso ne adaura wannan Aure anan wurin a take..!!
**********
Fitan Yawindo ke da wuya ne Umma cike da fushi tafara rufe Shatu da balai ,kun sun zuciya idan fushi ya turnukota ,sam Umma batasan lokacin da ta dubi Wannan jaririya ba tace " idan baki fada mana inda kika samo wannan yarinya ba aradu sai nasa an dauketa an jefar ajeji can ta karata ko akaita gidan marayu bai wuce ai tsintota kikayi... Kuka Shatu tasa mai ta6a zuciya harda shashsheka gami da fara mawa Umma magiyan kan ta rabu da yarinyar amma Umma cike da fushi a zuciye ta fice daga bukan .

Tsawon lokaci shatu ta dauka tana xubda kwallah ,kamin tunanin yaxo mata ,mikewa tayi tana sa6a jaririyar ,don a cewan ta baxata yarda a cutar mata da Wannan yarinyaba sam ,amanan tace ,kuma ta dauki alkawarin ba zata fadi mawa kowa wannan sirrin ba.

Fakaitan idon Umma tayi ta fice daga wannn buka tana nufan hanyar barin wannan Ruga. Tana tafe tana kuka takaici na rashin fahimta n ta dakowa yayi ,kowa yakasa barin ta da y'ar ta. Ta daujika ta ke yankawa don koda an biyo bayan ta tayi badda hanya babu mai iya cin mata .

Tafiya tayi mai nisan gaske don har rana ta fara faduwa sannan ta yanko wani Babban titi da batasan ta inace ba.

Yanda ta rufe yarinyar rigib a bayan ts bubu mai cewa ba diyar tace ba...haka itama tasa lullubi ta rufe kanta rijib da shi.

Tafiya take kanta tsaye batare da tayi aune ba taji an riko hannun ta caraf. Wani irin faduwa ne gabanta yayi wanda tsoro sai da ya fito a kwayar idon ta.... Wasu irin murda_murdan rikakkun sojoji ta gani wasu a gaban ta wasu baya ,kusan su 4 ,fuskan su daure babu imani ko baa ce maka ba.

Kasa masu magana Shatu tayi don ko ina na jikin ta rawa yake ,don Yagwalgwal ta fadi mata su waye soja a nigeria matsayin su da martabansu.

Duk da tsoron da ya kamata sam bashi ya hanata cewa" ku din su waye..? Me nayi maku?? Me kukuso dani?? Basu bata amsa ba ,sai daya daga cikin sune yace da ita" meje gurun Leutanant zamu kai ki. Yayi mgnan yana tasa kyeyarta . Mamaki ne ya kamata waye shi wannan leutanant din ne? Me xaiyi mata kuma? .

A tsaye ta taddasu su uku kamsn yanda kullum suke ,idan kaga daya sai kaga biyun ,Anwar ,Abbas da Sadeeq .

Murmushi Abbas ya saki kamin yace " Anwar kaga yar fulani mai kyaukuwa ,a ina kika samo wannan kyaun haka ?! Yayi mgnan ga Anwar da kallo daya yayi mawa Shatu ya gane fuskan ta don baxai manta da ita ba ,wani irin tafasa zuciyar sa yake masa lokaci daya ,kaman a wannan lokacin ne sukayi case din da yahadasu da Shatun .

Kauda kansa yayi gyefe yayin da Sadeeq ne ya amsa shi da Allah yaasa yanda take da kyaun fuskan nan nata har daga ciki ma hakan yake . Wani wawan dariya Abbas yayi yana kai hannun shi hadi kokarin riko Shatu . Saurin matsawa tayi tana bin sa da wani irin kallo .

Murmushi ya saki irin na yan iskan nan yana wani shafa sajen sa da ya tattara ya tara na rashin kunya . Zaki zo nayi abun da xanyi dake ne ko ko sai na sa miki karfi .

Kina wani jah baya kaman baki saba ba,bayan fualin nan babu wanda ya kaiku iskanci ku fake da saida nono kuyi ta iskanci a gari ,matsawa yayi kusa da inda take yana dukowa hadi da dan rage tsayin sa kadan yana saisaitawa da nata cikin wani irin murya ta tatattu yace " koda akwai wanda bakyeso ya ganki ne anan wurin mu shiga daga ciki ...yy mgn da murya mai kama da rada yana kashe mata idon daya....Wani irin mari Shattun ta dauke shi dashi wanda batasan xata iya shi ba .

Ba Sadeeq ne kadai ya girgixa da saukar marin ba Har da Anwar da ya kauda masu da kai ,don a zuciyar shi godiya yake mawa Allah da ya kuma hadasu da wannan yarinyar ,yana farin ciki don bai ta6a son Abbs da wannan harkar ba sai ayau...yana addu'ar Allah yasa yaci ubann Shatu ,shiyasa ya juyq masu baya ,amaimakon yaji Abbas ya jefata moto sai kuma yaji saukar mari a kuncin Abbas wanda baiyi zato ko tsaanin hakan ba..................

_*Littafin WALIJAAM na kudi ne kaman yanda kuka sani*_
_*Ga masu bukatar wannan littafi xasu na iya mgn dani ta wannan whatsap link din👇*_
https://wa.me/qr/7UGIAODZY3LON1

_Normal grp 200_
_Vip grp 500_
_Spc group 1k👌_

_Idan kati xaki turo MTN ne ._
_Idan kuma ta account ne ta nanan👇_
_0028799846_
_Farida Hashim stanbic bank_

_Yan niger kuma zaku tura katin 500f ne na Airtel ta wannan number na kasa👇_
_+22797780373_
_Idan kuma Spc grp kk bukata 800f ._

*Don Allah kimun mgn ne idan kin san biyan littafi xakiyi ,wlh banada lokacin amsa hlo ,hi banadashi ....kawai ki tura kudin ki kimun screen shorting evidence of payment naki ta wannan number 08081202932 ,idan kati turo mun kaawai xan saki a paid grp inshaallh....*
*Kar ku manta free page na dab da karewa....*

_________________________
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR
Call 08066268951
_________________________
_FREE PAGE na dab da karewa don Allah don maaiki kar ki fitar mun da littafi a bati idan kin siya ,ke kuma don Allah kar ki jira isowar littafin da aka sata ba tare da sanin marubuciyar ba ,idan kkyi haka kaman kin xama barauniyar xaune ce! Don ma'aiki badon niba kar ki fitarmun da littafi idan kin biya ,ku kuma idan baku biya ba kar ku karanta mun littafin WALIJAAM Don Allah👏_
_*Masoya makaranta littafan maman teddy a yau gashi ta zo maku da wata dama na karatun littafan nata kaman👇*_
_Yar Aiki na_
_Bafullatanan ruga_
_Gidan kwarata_
_Siyasa taah_
_Zuma da madaci_
_Kwaryar sama_
_Dijama y'ar fulani_
_Y'ar maula_
_Y'ar waye_
_Da dai sauran su...A yau sun bude hanyar da zaku na samun audio na littafan a youtube channel nasu mai suna HUMAIRA NOVELS TV_

_*Maman teddy🧸*_
*🐄WALIJAAM🐄*

_free page_
_13_14_
*_Ga masu bukatar wannan littafi xasuna iya mgn dani ta wannan link din 👇_*
https://wa.me/qr/7UGIAODZY3LON1
_Ki tausaya ma yar mutan mallawa kar ki fitarmun da littafi idan kin siya ,kema kar ki karantamun idan ba biya kikayi ba don Allah._
*_SADAUKARWA GA DUK KANIN FULANI🐄_*
*Alheri writers asso.📚*
_________________________
"Shikam Anwar ne da yake zuba idon yaga Irin cin mutumcin da Abbas zai mawa Shatun , a zuciyar shi yana godiya ga Allah don bai ta6a farin ciki da iskancin da Abbas yake mawa mata ba sai a yau ,da ya tare Shattu ...wannan yasa shi ma juya masu baya ,yana jirar ji da ganin Abbas ya daga shattu ya wurga a moto sai dai kuma yaji abun da yazo masa unexpected da bai zato ko tsammani ba jin saukar marin da shattu ta wanke Abbas dashi . Ta6 Babban magana abun da nima kaina nace kenan ,Marin soja ai ba wasa ba. Wani irin huci Shatu keyi ranta na tafasa ,nan take ta juyo ga Sadeeq da shima ita yake kallo yayi mutuwar tsaye...
Shikam Anwar ji yayi kaaman ya shako Shatu ya kashe da duka don takaici nan take tsanan ta ya dada lunkuwa a zuciyar shi...ware_ware yayi da lulun idon shi yana bin Sauran yaran Sojojin da kowa ke aikin shi babu wanda yaga komai dake faruwa.
Nisawa yayi yana mai yin Hamdala a zuciyar shi .
Shikam Abbas mamaki ne ya hanaasa ce mawa shatun komai idon shi lokaci daya ya kada ,dama shi mutum ne mai bakar zuciya ,a fusace ya daga hannu yana kaiwa saaman kuncin Shatu ,amma sai Sadeeq da yagama tsorata da Al'amarin Wannan bafullatana yayi saurin rike hannun nasa ,kamin ya girgixa masa kai...wani irin fixgar hannun sa Abbas yayi daaga garesa kamin ya kuma damko Shatu a karo na biyu yana hadata da jiikin moton da take gyefen su ...wani irin kallo yake mata yyn da hadata dam wannan moton da yayi nan jaririyar ta hau ihu tana karawa ,hankalin shatu ya tashi matuka don a wannan lokacin ganin yanda Abbas yakoma kaman wani mayunwacin zaki yasata tsorata matukar gaske. Sadeeq ne yace dashi " Abbas ka cika ta matar Aure ce kada kayi mata komai da goyo a bayan ta...A fusace Abbs yayi mgnan ba tare da ya juya ya kalli Sadeeq ba da ce masa " allah yasa tsohon ciki ne a tare da ita wlh sai na yi abun da nagadama da wannan yarinyar yau...ai nayi burinn ace ma A gaban mijin ta nake da a agaaban shi xanyi mata fyade ".

Wani irin abune Anwar yaji ya daki kirjin sa lokaci daya da baisan dalilin hakan ba". Ihun da wannan jaririyar takeyi ne yake masa kai kawo a kwakwalwa...sam bai san lokacin da yayi saurin fincike Abbas daga jikinn Shatu ba da takasa motsa kanta sakamakon wani irin damka da tasha ,don har ya yarda mata da mayafi goyon jaririyar yarinyar na dab da faduwa kasa ... Kai Abbas rabu da ita Daddy ne ke kirana yanxu ". Jin yanda Anwar din yayi mgnan ba da wasa ba yasa Shi cika ta ,yana wani irin jan numfashi na zuciya tare da dafe kirjin shi dake halbawa kamar zai fito .

Komawa yy yana rintse idon tare da yi mawa zuciyar sa Alkawarin kota halin kaka sai ya keta mawa wannan bafullatanan hadin ta .

Itakam Shatu ganin ta samu ya cika ta da kyar ne tayi saurin gyara goyon bayan ta tana daukar mayafin ta tuni ta silale ta gudu ba tare da dukkan su sun lura ba . Sai Sadeeeq kadai ne yaga ta juya takoma ta hanyar da ta fito... Shiru Sadeeq yayi yana tunanin abubuwa kamin lokaci daya kwakwalwar shi ta bashi cewan Wannan Bafullatanan ba mutum bace ba ,aljana ce...

Sai a sannan Abbas ya bude idon shi da yakoma kaman an watsa mashi borkono don jah ,bin Sadeeq yake da wani irin kallo kamin yace " Allah kasa ifritu ce wlh sai na kyeta mutumcin ta .

Bin su da Kallo Anwar yayi kamin yace " Daddy na kirana har ya katse ban dauka ba akan wannan wahalalliyar bagidajiyar bafullatanan dajin . Mtswww tom me ma zakayi da itane Abbas ,mu wuce kawai yakamata a yau na koma gida saboda ina tunanin Dad ya dawo ". Huuuuummmm A tare shida Abbas suka sauke numfashi kamin su shige moton nasu suna bata wuta don ko wannen su ransa a bace yake . Shikam Sadeeq ran sa ya baci don kwartancin Abbas ya fara damun shi a cewan sa yanxu yafara kokarin jawo masu balai ,tun da yafara kokarin yin iskancin shi da mutanen 6oye .

*******

Shiru_shiru Mama tana xaman jirar fitowan Asma'u a dakin nata amma shiru bata fito ba. Mikewa Mama tayi tana nufar dakin nasu wanda ya kasance nasu ne itada Teemah . Mamaki ne sosai ya kamata ganin Asma'u na salla da tsakar rana wuraren 11am. Sakin labulen dakin tayi tana komawa inda take zaune hadi da daukar tray din shinkafan da take tsinta hadi da fidda shefin dake ciki .


Tsawon lokaci sai ga Asma'u ta fito sanye cikin wata doguwar riga roba da yake kama jikin ta ta yana karamin mayafi ...Abun ka ga mamaki da Mama tayine yasata cewa" Asma'u yau kece da Sallah bama na farillah ba Nafila??. Keko me kike nema haka har kika dawo kikasan Allah daya ne??. Cewar Mama tana kallon Asma'u da itama Maman take kallo .

Murmushi tayi kamin tace " Ohh mama kenan ,tom Teeema nake tayawa addu'a don samub miji kaman leutanant Anwar abune mai wuyar gaske . Yau zata sanar mawa Mahaifiyar sa da Abun dake zuciyarta game da d'an ta kinga kuwa sai da rokon Allah muyita jamata sura.

Wani dariya Mama tasa wanda ya 6ata ran Asma'u ,buden bakin Asma'u cewa tayi " kai Anya Mama kece kika haifemu kuwa ? Sam baki son ganin cigaban mu ,mudai gsky idan bakece kika aifo mu ba ki fadi mana kawai munema Uwar mu mu huta . Cewan Asma'u tana wani irin gallare gallare.

Wani irin murmushin takaici Mama tayi kamin tace" hmm banyi mamakin mgnan ki ba Asma'u don dama kunsaba fadimun abun da yafi hakan ,kuma koda nayi dariya naga shashancin kune da har kuke tunanin wai auren Wannan matashin sojan ,a irin wannan dabi'ar takuce kuke wannan tunanin tabdijam....hmmm Allah sarki na tausaya maku ,bakwa ganin mahaifinku ,mahaifiyar ku da kima har daa akwai wani mutumin arxiki da kirki da xaiso hada zuria daku kunyi gwari kam yara !! Mama tayi maganan tana ca6e baki ,kamin tace nice mahaifiyar ku Asma kije Allah ya shuryaku abun da nake maku fata kenan a kullum kuma akoda yaushe .

Uhmm Asma'u tace tana barin mawa Mama filin tsakargidan hadi da ficewa daga gidan tana wani irin tafiya da motsare botsaren jiki da duwawu ,kunsan dai Cat Walk irin tafiyan da takeyi kenan tun tana na iskanci yanxu ya zama mata jiki .
Da kallon shiriya mama tabita dashi har ta bar gidan kamin ta girgixa kai tana cigaba da tsintar shinkafan nata.

*******

A 6anagaren gidan Dr Haulat kuwa fada ne ya kacca6e tsakanin Teemah da Zabeena ,don tun isan ta ta tadda Dr Haula bata nan tana daya daga cikin Asibitocin ta .hakan yasa Teema ta zauna a falon nata ,nan itama Zabeena ta zauna ,a nanne suka hau yadawa juna da habaici da maganganu tsawon lokaci don dukan su sun san manufan su a cikin wannan gida .

Hmmm lallai wannan shine hausawa kece mawa iska na wahalar da mai kayan kara ,ina mutum ina gwarzona Anwar ? Hmm abun ma baa hadi sam....Waye ne mutum waye kuma ubanshi....uhmmm bari na baimawa kaina amsa na daya dai mutum dinnnan ba kowane ba face dan gidan talakawan likis...na biyu kuma uban shi ba kowane ba face cikakken misakin talaka wanda babu sana'a cikakke sai buba buga....hmmm uhmmm tom ina ke don allah ina Anwar ,Anwr nawa neni Zabeena... Kutumar ubannan Abun da Teemah tace kenan kamin ta daga ruwar dake glasscup din gavan ta tana wanke wa hadi da sheka shi saman fuskan Zabeena da tayi gigif ta mike daga tsaye ,don batasan da zuwan ruwan ba .

Itama Teeman mikewa tayi a fusace tana kallon Zabeena da take bun ta da kallon mamaki . Nine kika watsa mawa ruwa a saman fuska....cewan Zabeena cike da mamaki.

Wanii irin kallon sama da kasa Temmah tayi mata kamin ta ta6e baki gyefe tana mai cewa" kwarai kuwa kena watsa mawa ,kinsan duk sabo dameye nayi maki hakan ?? Saboda ambaton sunan Anwar da kikayi da mijin ki ,tom kisani wannan ruwan ruwa na watsa maki na gaba ruwar petir ne ko kalanzir zakiji a saaman fuskar ki na kyetta ashana na babbakaki ,wannan duknasaboda son da nake mawa Mijina Anwar ne??? .

Mijinki?? A yaushe ne Anwar din ya xama mijinki sauna? Cewan Zabeena tana fiddo da ido waje cike da bakin ciki . Kamin ta cigaba da cewa" wlh nikuma duk ranan da kika kara kirar sunan Anwar da mijinki sai na Kashe kin bar duniyar baki daya ....


Allah ko tom ko zaki kwatantan ta eiye? Cewan Teemah tana fito da ido hadi da matsawa kusa da Teemah

3 Comments On WALIJAAM
avatar
hannatu-8

1 year ago

Reply

Great

avatar
asiya-aliyu-5

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
asiya-aliyu-5

11 months ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment