Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

๏ปฟ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€


*_'YAR CASKALE_*
( _Sanadin bakin uwa_ )

*NA*


*KHADEEJA USMAN*
*_(Real Tame Gari)_*



*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*
___________________________________


*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________



1โƒฃโžก5โƒฃ


*ALHAMDILLAH! ALHAMDILLAH!*


*_AM BACK AGAIN_*



*_Wannan buk d'in,sadaukarwa ne ga dukkan daukakin Marubuta na ๐ŸŒˆkainuwa writers asso...da Kuma masoya na a duk inda kuke a fadin duniya Allah ya barmu tare ya Kara Mana zumunci mu gudu tare mu tsira tare_*


_Hussain ATK da dukkan masu taya mu posting din litattafan mu muna matukar godiya Allah ya saka muku da alkhairi ya barmu tare_



_Ban yarda wani ko wata su juyamin littafi ta ko wacce siga ba tare da izini na ba,yin hakan zaisa mu samu matsala Dan Allah a kiyaye_


******

Sauri yakeyi kamar zai kifa,Dan ya na son yayi sauri yakai musu maganin.

Malam shu'aibu kenan,cikakken bakano,asalinsa shida iyayensa 'yan Kano ne, a unguwar fanshekara,ya na da Mata guda d'aya da yaransu biyu,Isma'il shine babba sai mace *MARYAM* wadda ita ce karama yanzu ake goyo.

Malam Shu'aibu da matarsa Huwaila,suna zaune ne a unguwar yamadawa,inda yake sana'arsa ta sayar da kayan marmari,dangin su lemo ayaba da dai sauransu.Huwaila macece Mai kirki da Sanin ya kamata,duk da cewar uban mijinta ya Dade da rasuwa,hakan yasa kullum Bata rasa abinda zata bayar tace akaiwa surukar tata,Dan malam Shu'aibu kullum Sai ya je gaida mahaifiyar tasa.

Matsalar Huwaila fad'a da rashin lafazi,Sam bakinta Dad'i,ba ga wani ba ,Baga 'ya'yanta ba,malam Shu'aibu yasha fama da ita akan muna nan lafazi akan yaranta,amma Ta 'ki dainawa.Yanzu haka Maryam na da shekara goma yayin da Isma'il keda shekara Sha d'aya,Dan babu wata tazara tsakaninsu,Dan irin haihuwar nan ce ta zamani.Yanzu ma Isma'il ne ba lafiya,shine ta kaishi asibiti ,magungu Nan da aka rubuto,su ne malam Shu'aibu ya ta fi siyowa.

Da sallamar sa ya shigo gidan,inda ya Fara jiyo hayaniyar ta tana fad'in"ai ke Kam anyi bak'ar matsiyaciya,ban San halinwa Kika kwaso ba,Danni kaf dangina babu Mai bakin Hali irin naki,sai dai ko can dangin ubanki Kika kwaso,ace yarinyar kullum sai kin Sani tsinin baki,da ace baki Yana Kara tsawo da yanzu nawa ban San inda yakai ba"

Yarinyar dake tsaye idanunta feke ta tsare uwar dasu,babu ko alamun tsoro tace" Allah umma ko yanzunma bakinki ya k'ara tsawo ba kamar sanda na ke k'arama ba,Dan yanzu Kinga yadda bakinki ya koma",ta kamo le'benta na sama Dana k'asa ta jawosu.

"Kinci kut......ta narka Mata ashar,Ni d'in ce bakina yake a hakan?"

"Wallahi umma da gaske nake"ta fada kanta tsaye ."Zakici ubanki ne ,na rantse da Allah yau saina kusa kasheki a gidan nan".

Jin abinda tace ne yasa Maryam din zumbura Baki ta nufi bakin kofa Dan fita daga dakin."wallahi Kika sake fita daga gidan Nan sai na farfasa Miki jiki,inba Haka ba shegiya uwata ta haifeni,Kuma jeki din in kina musu".

Babu alamun tsoro ko ta fita daga dakin tana zumbura Baki tana gunguni,inda tayi kacibis da babanta tsaye a inda yake jiyo diramar su.

Washe Baki tayi tana fadi'in ,"Lah baba! Sannu da zuwa,harka dawo daga siyen maganin?"

Kama hannunta yayi Yana fad'in"yauw 'yar baba,laifin me kikayi ne naji mamanki na Miki fad'a?"

"Kawai fa Dan tace na jire gida Kar naje ko'ina,shine fa Ni Kuma Ina Nan zaune sai zuwaira ta leko ta tsokaneni ,Wai an barni tsaron gida harda min gwalo,Niko na bita har gidansu na Kama bakinta nai ta naushi irin yadda Naga rannan johnsina yayi dashi da omega,shi ne fa jini har Saida yayi tsartuwa,wallahi baka gani ba baba,da kyar aka kwaceta a hannuna,ashe dai nima jaruma ce,shine fa aka zo aka fadawa umma ,shine takemin fad'a" .


Girgiza kansa yayi sannan ya shiga shafa kanta,"Maryam me yasa bakya Jin magana ne,anya kina son mu shirya kuwa? Kinga Ni bana son wannan yawan fadan da kikeyi sai kace ahlin shagon dambe,ke kenan make wannan jibgi wancan,to indai kina son mu shirya Kar in Kara Jin Haka kinji ko?"

"Zan daina Amma suma ka fada musu su daina cemun _'yar caskale_ "


"Naji duk zansa a tattara mun yaran in musu kashedi,muje maza kibawa ummanki hakuri".

"Tab ai yaseen nasan Dana Bata daban Bata ba sai ta dakeni ,gara ma inki bayar war" tana Gama fad'ar hakan tayi waje da gudu.


Girgiza kansa kawai yayi,Yana addu'ar Allah ya shirya Masa yaran Nasa,tare da matar tasa ma,Dan wannan abin na Maryam yasan yanada nasaba da bakin da Huwaila keyi musu,Dan tun suna kanana in sunyi Mata abu, kamar barna,sai dai kaji ta furta ,"Kai amma wannan yarinyar anyi tsinanniya,ko Kuma anyi matsiyacin yaro,da dai sauran irin wadan Nan kalaman marasa amfani,masu cutar da rayuwar yaranmu,su durkushe,in sun girma mu rasa dalili,alhali wani lokacin muke jifansu da wasu lafuza marasa dadi ,muna ganin kankantar su ko rashin tasirin su,Wanda wallahi komai kankantar zagi Yana taka muhimmiyar rawa a gurbacewar tarbiyar mu a yau.


Da sallama ya shiga dakin,inda ya isketa zaune tana yiwa Isma'il fadan yatashi ya sha farau-farau koya danji dama a cikinshi.

Saida yasami guri ya zauna sannan shima ya shiga lallabar yaron akan yasha,da kyar yasha kadan sannan ta balla maganin ta bashi, aikuwa saiga amai.


"Kut......."ta lailayo ashar ta makamai,bakin matsiyaci,Dan kaga Ina lallabaka,shine kake dada wani langabewa,to Dan kut.........kada kasha ka mutu ma,Kai Ni Allah ma yasa ka mutu In huta da jaraba,yaro inata bin kanka na rasa inda Zansa kaina duk saboda ciwonka,amma komai aka baka saika amayar dashi,ni a wahale Kai a wahale,Dan bak'ar k'eta,Kai ba jinjiri ba ba Kuma d'an yaye ba,to wallahi daga yau sai dai ka mutu ,idan na K'ara baka wani abu magani ko abinci Allah ya tsinemun".Ta karasa maganar tana huci.

Da kallo malam Shu'aibu ya bita,Bai ce da ita komai ba ya shiga lallaba Isma'il akan yatashi ya k'ara Shan kunun Koda kad'an ne yasha magani.

Itako ta shiga hada kwanuka tana gyaran gurin tana masifa.

******


Misalin Sha biyu na dare,bayan ya tabbatar Daya yaran sunyi bacci,Dan shima Bai Dade da shigowa ba saboda yanayin sana'ar tashi.A zaune yasameta tana kokarin kwanciya.

Saida ya samu guri ya zauna,kafin ya Kira sunanta,"Huwaila"!

"Na'am mallam".

"Ina son zamuyi magana dake,duk da ba wannan shine karo na farko ba,amma Kuma Zan iya cewa wannan shine kusan gargadi na karshe da zanyi Miki".

Ganin kamar Yana maganar ransa a d'an b'ace yasata nustsuwa.Ganin da yayi ta maida hankalin ta akansa yasa ya Fara magana.

"Wato abinda ke faruwa ne game da furucin ki Akan yaran Nan,anya kuwa Huwaila kina da hankali,kin San dafi da Kuma illar bakin uwa akan 'ya'yanta, mummunan furuci ko ba ga d'an daka Haifa ba,ai baida amfani,bare Kuma ace ga yaranki,tun yaran Nan na Shan nono nake fama dake akan ki gyara kalamanki akan su,amma abu yaci tura,yanzu furucin da kikayi dazu akan Isma'il,idan hakan ta kasance wakeda asara,Kinga nidai inada damar k'ara aure,duk da kuwa bani da tabbacin Zan Kara haihuwar,amma ai daga ni har ke bamuda wata matsala mun tabbatar.Dan Allah na rokeki Dan girman Allah ki gyara kalamanki akan yaran nan,ke bama su ba har wasu yaran daba namu ba,shi yaro na kowa ne,addu'ar shiriya yakamata mu dinga yi musu bawai mugun Baki ba,Dan Haka Ina son daga wannan lokacin Dan Allah ki gyara lafazinki kinji Huwaila ta".

Hawayen dake bin fuskarta ta share kafin tace"insha Allah malam bazan sake ba,nima sai bayan nayi sai abin yaita damuna,amma insha Allah Zan kiyaye".

"Yauwa Huwaila,Dan Allah a dinga kiyayewa kin San shi harshe dafi ne me zafi,dan Allah bana so kinji".

Gyada Kai tayi alamar toh,kafin ya jawo 'yar matarsa Yana me k'ara yimata nasiha cikin hikima.


*************************

Tsaye take ta rike k'ugu gaban Rakiya me dambu,tana fad'in"baba Rakiya!wallahi daga yau bazan Kara kawo Miki karar ummita ba, jikinta ne kawai zai fada mata,gara ma kija Mata kunne Dan yaseen idan na kamata lallasar tishin yaji zanyi Mata,Dan karki ganta ma da tabo kice ban fada Miki ba,ki tanaji na magani tun yanzu".ta karasa maganar tana murguda baki.

"Ke Maryam ki fita idona,Dan kaniyarki ni kikeyiwa rashin kunya,Dan wannan ba kashedin ummita Kika kawo ba,Ni kike jawa kunne a fakaice,Dan Haka anki ayi Mata fadan,ke ba'ai Miki fad'a ba sai ita,kinbi kin maida Mana Yara kamar jakai,kiyita lodar su kina musu bugun uwa da d'a,dama na fada duk ranar da abinki ya biyo takan ummita Ni Kuma ranar Zan gwada Miki Nima uwar zamani ce,shegiya fitinanniya".


"Kenan bazaki Mata fada ba ko?"

"Bazan yi matan ba,ta tsokane ki,gobe ma inta ganki Zan Kuma fad'a Mata ta tsokane ki,ai ba fin karfinta kikayi ba,Dan ma ita din saiwar sala ce, badan hakan ba,ai da inta rikeki ko kwacewa bazaki iya yiba,amma yanzun ma muje zuwa"ta karasa maganar tana bude tukunyar dambunta Dan ganin ko yayi,Dan so takeyi ta gama saboda yau ta d'an makara,dama yayar ummita ke fita dashi,wani Kuma ta sayar a gida,to yau Kuma gashi har ta shirya ita kawai ake jira,to iccen ne danye.


Kwaaaaaaaaaaa! Taji saukar ruwa saman tukunyar dambun,Wanda tsabar ruwan Daya tumbatsa,har Saida ya antayo waje,ya leme murhun,toka tayo futar burtu tayiwa fuskar Rakiya fenti,tare da yiwa dambu decoration,Dayake bakinta bude yake sanda ruwan ya sauka a murhun,gaba Daya bakinta ya wanke da toka,inda hakoranta sun rikide sun koma ruwan tokar.Wata iriyar ashar ta narko,wadda tasa sauran tokar bakinta da bata Gama jikewa da miyau ba ta feso kamar ta zuki sigari,aikuwa a sukwane tayo Kan maryama dake rike da bakin bokitin k'arfe na wanka,Nan ko suka kasa tsere.mijin Rakiya da dawowarsa kenan daga kasuwa,Yana kokarin kafe kekensa yaga maryam ta fito a guje Rakiya ta dafo Mata,ya bude Baki kenan da niyyar ya Kira matar,gefen bokitin da Maryam ta rataya kamar jaka ya daki bakinsa,Nan take ya wuntsila daga shi har keken Nasa sai gashi a kwata,shima maimakon ya Kira sunan Allah ,sai ji kake ya runtuma ashariya,Yana me shafo bakinsa da jini ke d'iga,aikuwa ya shiga kiciniyar mikewa,duk da kansa dake Sara Masa,Bai hana sa Mara musu baya ba.

Itako Maryam gudu takeyi iya karfinta,yayin da rakiya take biye da ita zaninta a hannu sai d'an under's din ciki Daya Sha bakar dauda.

Sosai Maryam ke shiga lungu da Rakiya ga Kuma mijinta a baya,Yara da Basu San dalilin gudu ba suka dinga binsu duuuuu suna son ganin me ke faruwa.

Itako Maryam ganin tafara gajiya gashi ta rasa gurin nufa kawai saita hango wata majallisar matasa,aikuwa ta nufi can tana fadin "ku taimakamin wayyo ni mahaukaciya ta biyoni",itako Rakiya Jin abinda Maryam ke fad'i yasata lailayo ashar tana Kara laftawa,tare da ikirarin idan har ta rik'e Maryam wallahi saita ga ta daina numfashi.Su kuwa matasan ganin yadda fuskarta tayi dumu-dumu da toka ga bakinta ya hadu ya hade,sai suka dauka da gaske batada lafiyar Nan ko sukayo kanta,ita ko Maryam ta labe tana mayar da numafashi.

Sosai matasan suka shiga kiciniyar rike Rakiya,aikuwa ta shiga fizge-fizge,su kuwa sun sami abin bukata,nan wasu suka shiga lagudar inda yai musu a fakaice.

Mijinta da karyo kwanarsa kenan yaga yadda ake tattabe matarsa,da sauri ya karasa ya shiga ture matasan yana zaginsu,nan suka kauce ita kuma Rakiya ta fashe da kuka tama rasa abinda zata yiwa yainyar nan,dan inta kamata saita ga ta daina numfashi........


_ina son inga comments din dazai girgiza ni_


*Alkalamin khady* โœ
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€


*_'YAR CASKALE_*
( _Sanadin bakin uwa_ )

*NA*


*KHADEEJA USMAN*
*_(Real Tame Gari)_*



*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*
___________________________________


*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________



*ALHAMDILLAH! ALHAMDILLAH!*


*_AM BACK AGAIN_*


6โƒฃโžก1โƒฃ0โƒฃ


Maimakon Maryam tayo gida data samu ta sulale,aikuwa saita bazama,itace wannan lungu,itace wannan layin,makaranta Kam yau islamiyya ta yafe ta,tunda dama yau asabar ba boko,islamiyyar yamma data safen duk yau bataje ba,tasan ko yau Mai kwatar ta gurin umma sai Allah,shine tace gara kawai ta cika laifinta ya cika cif ayi Mata dukan gaba Daya.(Illar sabawa yaro da duka kenan,komai yayi duka,hakan shi kesa yaro ya zabure yabar Jin tsoron dukanma,gara tun Yana d'an karamin sa ki Saba Masa da kallo ki banbance Masa dai-dai hakan zai fahimci kallon me yake nufi,kada kice komai yayi saikin daka,ki Bari ki Tara tukun,yadda idan Kika rikeshi yasan bazakiyi Masa da Wasa ba,zaiji tsoron gamuwar ku matukar kikace Zaki dakeshi.Allah yabamu ikon gyarawa amin.)

A can gida tuni labari yazowa Huwaila,aikuwa yaran Rakiya sunyi rashin mutunci,Dan cewa sukayi a Miko musu Maryam sai sun jajjaga ta,Dan sunji labari tasa uwarsu gudu a titi,Kuma tayi sanadiyar fadawar babansu kwata.Sai da Huwaila tasa aka kirawo Mata malam Shu'aibu yazo ya basu hakuri,da kyar suka hakura suka bar kofar gidan.

*********************
Ita kuwa Maryam tana Nan labe ta hango Rakiya da mijinta sun rungumo juna,Rakiya nata gunjin kuka,yayin da mijin keta Bata hakuri,Yana fado Mata irin nau'ikan azabar da zasu yi wa Maryam in sun kamata.Zugar Yara na biye dasu duuuuu! Kunsan Yara in sun samu abun kallo kiris suke jira.A hankali ko Maryam tayi tsulum ta afka cikin yaran ta wage murya da karfi tace,"mahaukaciya 'yar macukule! ,Take ko zugar yaran ta amsa suka maimaita,aikuwa harda tafi Nan ma wasu yaran suka Kara tittidowa,Nan da Nan ko Rakiya ta juyo,aikuwa idonta ya sauka Kan Maryam tana bada wak'a.Ai kuwa sata kwace tayo kansu,nan kuwa Yara suka watse,ta tsaya tana zage-zage tana neman maryam.Itako Maryam lungun gidan su taje ta labe, tana son shiga gida a ranta Kuma tana cewa mudun tsokanar ta Bai cika ba.

***. ******. ******. ***

Sai da duhun magariba ya gabato,sannan tasa kanta zuwa soron gidan,dayake soron biyu ne,Haka ta sadada ta leka, dai-dai lokacin ta hango umman nata na bude robar ruwa danta zuba a buta,aikuwa sai taga ba ruwan,ji tayi tana fad'in,"oh ni 'ya su,Kinga a shefa ba ruwa a robar Nan,Allah sarki Isma'il ,sabo da ka Saba zubawa na dauka yau dinma diba kawai zanyi ashe babu,Bari idan nayi sallah nazo naja ruwan duk da ba amfanin Jan ruwa da daddare,Amma ya zanyi" Haka taja ruwan guga Daya ta zuba a buta,ta shiga bandaki,bayan ta fito tayi alwala ta shige daki.

Maryam na ganin wucewarta ta shigo gidan tare da nufar gurin rijiyar,ta bude babbar jarkar ruwan ta shige,bayan ta jawo murfin ta Dan Dora aka ta zameshi tana Jin iska,take bacci ya kwasheta cikin kankanin lokaci.

Saida Huwaila ta idar da sallar,sannan ta fito Dan Jan ruwan,so takeyi taja da wuri dan ma yaza ma dole ne,da Sai da safe zata ja,to tasan bukatar ruwan na iya tasowa Kuma dole dai rijiyar za'a bude aja komai dare.

Tana zuwa ta bude rijiyar,Saida ta jawo ruwan sannan ta Mika hannunta ta Jaye murfin robar tana fadin" oh Kinga na Manta ma ban wanke robar ba,Haka dai zan hakura in zuba da safe a wanke,na ciccika Mana butocin kawai" dai-dai tana kwara ruwan cikin robar ruwan,Wanda yasa Maryam sakin ajiyar zuciya ta farka.


D'an jimm umma tayi,Dan saita ji kamar an sauke ajiyar zuciya Kuma daga cikin rijiyar,amma sai Kuma tayi tunanin Kila kunnenta ne,Dan Bata Saba Jan ruwan dare bene,yasa ta Jin hakan,aikuwa ta Kara zura guga tana cewa"yau Maryam Ina tausaya Miki ,Dan ban ma San irin bugun dazan yi Miki ba,laifi goma da ashirin,Allah ya dawo dake gidan kafin babanku ya dawo zanci ubanki,Dan nasan idan Yana Nan nace Zan dakeki hanawa zaiyi,dai dai ta jawo ruwan ta Kara antayawa cikin robar,Maryam ta Kuma sakin ajiyar zuciya saboda sanyi,kun San ruwan rijiya lokacin zafi.
Daurewa kawai umma tayi ta kara zura gugan,dan wannan Kar kam da gaske taji anyi ajiyar zuciya,hakan yasa zuciyarta Fara rawa amma wai ita jaruma saita dake,taci gaba da antya ruwan cikin robar,jin da maryam tayi ruwan na neman kawo mata wuya,yasata mikewa ta buga tsalle ta fito jagab da ita,ta zura a guje ta shige dakinsu.


Wata kara umma ta saki tare da karanta ayatul kursiyyu iya karfinta,tana nan tsaye Kuma ta kasa sakin gugan yana hannunta,irin d'an dutsen nan na rijiya ya rike gugan Nan umma tawage Baki tana kuka da neman agaji.

Mallam Shu'aibu da shigowar shi kenan ya hango matarsa na makyarkyata da sauri ya karasa Yana fad'in"subahanallahi! Huwaila waye ya fada rijiyar,bawai garin jarabar Taki Kika jefamin Yara rijiya ba,ya fada Yana fuzge gugan hannunta,Yana lekawa rijiyar,ganin da duhu ba komai zai gani ba yasa ya juyo a fusace Yana fad'in,kin mun shuru ki fadamin meyake faruwa!

Cikin rawar murya da tsoro tace 'matashiyar 'yar ruwa ce ta fito daga rijiyar ta shige dakina".

Tsaki yaja,kafin ya saki gugan ya nufi dakin yaran,a zuciyarsa Yana fad'in yaga ranar da Huwaila zatayi hankali.

A kudundune yasamu Maryam da kayanta jikakku,tunda yaga Haka ya tabbatar da itace tayiwa uwarta haka.karasawa yayi inda ta kwanta kusa da Isma'il ya tashesu duka,Nan Maryam ta shiga rarraba ido,Bai nuna Mata wani bacin Rai ba,yace ta tashi ta cire kayan jikinta,aikuwa ta mike ta canza ,Nan yake tambayar ta ko taci abinci,Nan ma tace mishi ah'ah ,yasan za'a rina,Dan haka ya fita dakanshi ya fita kicin ya zubo mata,yace taci Yana zuwa.

Yana fita ya tarar da Huwaila tsaye bakin kofar dakinta Taki shiga,Yana zuwa yaja hannunta ta shiga tittirjewa,ganin tana cijewa ya juyo yace "Wai miye haka ne Huwaila?ba fa na son sakarcin banza wuce muje,Dan Yara na baro wurin Ina son magana ne dake a gaggauce".

Ganin ya shige ciki Bai Kuma dawo ba yasa tayi shahada ta biyo shi,ta samu guri ta zauna tana waige-waige.

Bai kulata ba yace,"dama ba komai ya dawo Dani ba sai akan Maganar Maryam, Huwaila bazan boye Miki ba,komai ya faru da yaran nan kece sila, wallahi na tabbatar bakinki ne,gashi yanzu kin samu a damuwa,kullum maryama da kalar tsokanar da zatayo,a tsokaneta Kuma ta jawo magana Nan ma,ba babba ba yaro duk Kan me uwa da wabi takeyi,gashi Bata Jin tsoron ko mu iyayenta Dan kin Gama horar da jikinsu da duka,tasan bazai wuce muma dukanta zamuyi ba intayi ba dai-dai ba,Kinga yanzu abinda ya faru dazu,yanzu Haka maganar da nake Miki mijin Rakiya ne yaje da yaranshi maza manya har gurin san'ata sunce wallahi idon su idon Maryam sai dai wata ba ita ba,na rasa abinyi da kyar aka Basu hakuri suka bar gurin.To shine nake fadawa malam Garba abinda ke faruwa shine ya bani wata shawara yace in Kai Maryam almajiranta kawai".

Da sauri Huwaila ta d'ago ta kalleshi tace,"wace irin almajiranta Kuma malam ? Wai ma Isma'il kake nufi ko wa? Dan Naga dai shine namiji Kuma maza ake kaiwa almajirci ba Mata ba".

Murmushi yayi kafin yace ," Maryam dai nake nufi kamar yadda Kika ji,malam Garba yace babanshi Yana da almajirai Mata,idan yarinya ta gagara to shi ake kaima,sannan Kuma cikin yardar Allah sai kiga yarinya ta kimtsu ta samu ilimi,sannan bawai bara sukeyi ba,zamu had a Mata kayane kamar zata boading school,shima Kuma acan gidansa ana Basu abinci Dan suna mu'amulla ne kamar yaran gidansa,Ina gudun abinda Maryam zata jawo Mana ne Nan gaba in mun barta Haka.
Nanfa ya shiga gayawa Huwaila muhimmancin Kai Maryam makaranta.

"Naji malam na Kuma gamsu,amma kasan fa halin Maryam,kana ganin bazata iya dawowa ba?"

"Kada ki damu na shirya yadda za'ai tafiyar,Kuma yace min garin lungu ne can jihar jigawa ne".

"Shikenan malam, Allah yasa karshen wahalar kenan"

"Amin ya amsa,kafin ya mike Yana fadin ta hadawa maryam kayanta kala biyar,Dan da asubar nan zasu tafi a motar malam Garba.

Haka ko akayi Daya tashi dawowa ya tahowa da Maryam harda robar almajirai,dasu gari da dakaken kuli magi dadai 'yan wasu abubuwan bukata na 'yan makaranta๐Ÿคฃ.

*********

Asubar fari suka fito aka tashi Maryam Huwaila ta sallara mata wanka,itadai Bata cewa komai,ana shiryata ana Mata nasiha.

Gani sukayi malam ya fito da zundumemen buhu yace"maryama ta taho ki shiga Nan kinji"

Make kafada tayi alamar ah'ah,Nan ya shiga.lallabata harta yarda ta zura kafafunta tace"baba kasheni zakuyi?"

Zaro ido yayi yace "injiwa yace Miki kashe ki zamuyi?"

"Gashi Nan zaku je ku jefani a ruwa".

"Ah ah,madinan Nigeria zamu kaiki ki sauke farali,shiyasa muke son mu boyeki anan,kar Yara su ganki suce Suma sai anje dasu,bayan ke kadai ce 'yar gata...."

Bai gama ma maganar ba,yaga ta shige buhun tana fadin"to ummana Allah ya kaddara saduwar mu,nidai yau Zan hau jirgi" sai Kuma ta fitoda kanta tace,"to amma baba a maleji zani ko Kuma a booth,da Naga za'a Sani a buhu?"

"Ai a kujerar boye Zaki shiyasa,Dan Haka ma Zan yanka Miki inda Zaki dinga Shan iska bakida matsala kinji".

Komawa tayi tana fadin,baba k'ulle bakin buhun muyi sauri Kar jirgin ya tafi,amma Allah ya taimaki ummita,da nace wallahi saina mata dukan tsiya,amma yanzun ma idan na dawo indai ban manta ba saina dake tan".

Haka malam Shu'aibu ya daure bakin buhun,bayan ya yanka mata wani gurin,yace tasa hancinta dai-dai gurin,Dan ta dinga Shan Iska,Nan ya kinkime ta zuwa bakin motar.

Malam Garba ya bude musu gidan baya yasata, shima malam Shu'aibu bayan ya shiga,yayin da Huwaila ke tsaye tana musu sallama da addu'a Allah ya tsare,tana Jin ba Dadi rabuwa da 'yar tata,badan rashin lafiyar Isma'il ba da da ita za'a ,Amma tana musu fatan sauka lfy da Kuma fatan samun shiriyar 'yar tata,ance kowanne yaro da kalar kuruciyar sa,to ita Kam ta Maryam ta dabance.

Jin an tada motar Maryam ta saito bakinta saitin bular buhun tace"mama ke bazaki filin jirgin ba?"


"Eh Zan biyo ku daga baya kinji mairo ta,ta fada tana goge
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment