Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

"dan Allah ka rufamin asiri ai zan iya mutuwa na barka a maraye kaga kayi haquri kasa ka samu matsala saboda zan shiga damuwa ni kuma zan riqayi ahankali ba tare da na takuraka ba"

Tureshi tayi tana dariya "ya jalal dan Allah na rana daya ka dagamin qafa mana" dariya yayi "duk ranar da kika haihu promise you zan daga miki qafa"


Dariya suka shigayi ya janyota jikinshi yana shaqar qamshin jikinta ahankali ta shiga shafa jikinshi tare da lumshe idanunta tana shafashi ahankali


Sannu2 jalilah ta shiga wasa da machine dinshi tana shafawa ahankali sai faman jan numfashin shi yake kamar ze shide

Zamewa tayi daga jikinshi wanda sam jalal bayada karfin da ze riqeta tayi qasa kadan ta fara yi mishi socking sai famar mayar da numfashi saida ta tabbatar ya samu natsuwa ta dawo kan jikinshi ta kwanta tana murmushi

"Bazaka qara bawa baby na wahala ba" murmushi yayi cike da farin ciki


"Jalilah kin zama daya tamkar dubu banajin akwai namijin da ya kaini sa'a a duniya,,,, bansan dame zan sakawa su ummi ba,,, suka raineni suka bani tarbiya da ilmi suka zabamin mace ta gari,,,, Allah ne kadai zai iya biyanku"


Murmushi tayi tare da shafa face dinshi "ya jalal kai ka fada ni kuma nace me? Duk abinda su baffa sukamin ba wanda yafi tasiri arayuwa face mijin da suka auramin wanda nasan burin ko wace 'ya mace ta samu irinshi"


Murmushi suka sakarwa juna "Allah ya saka maka da alkhairi baffa da ka auramin jarababbiyar mace"

Duka ta kai mishi a qirji "yanzu waye jarabarshi ta bayyana? Dariya yayi tare da qara hugging dinta ahaka har bacci yayi awon gaba dasu




Washe gari kowa ya shirya zuwa wurin da yafi iyawa jalal yaje ya fitar da motan jalilah cikin qanqanin lokaci aka wanketa suka fito

"Wai waya baki wannan motan? Dariya tayi "bazan fada ba sai yanzu zaka tambayeni? Sorry gayamin dan Allah

"Hmmm wa kake tunanin zai bani wannan motan in ba ya mubarak ba" murmushi yayi aranshi yana tunanin ko mutuwa yayi yasan mubarak bazai taba bari wani abu ya shigewa family dinshi ba


Saida ya shiga ya tada mata motan ya bata taja ta fice kafin yaja nashi motan yayi gaba





*After a months*



Jalilah ta dawo daga school tana murna yau dai ta kammala ga cikinta har ya tsufa haihuwa yau ko gobe"



Zaune take part din ummi jalal ya shigo ya zauna kusa da ita "ummi bacci take? Kai ta gyada mishi


"Gani" kamar ya gaka? Ai naga kin kirani ne,,, a waya? Ta tambayeshi,,,, kai ya gyada mata


Ni ban kiraka ba gaskiya,,,,, kallon ummi yayi yaga bacci take ya juyo yana kallonta


"Saboda jarabanki har wayanki kika koyawa jaraban kirana? Dariya tayi "eh na koyar da ita kuma ummi tace bazan koma part dina ba saboda any time ina iya haihuwa kuma tafison akwai wani kusa dani wanda zai kula


"Biki gaya mata jarababben miji kike da bane? Ya jalal tashi Mu tafi kar ummi ta falka taji kana wannan zancen" dariya yayi ya taimaka mata ta tashi suka nufi part dinsu


Dariya ummi tayi "wannan zamanin da muke ciki Allah ka tsaremu yanzu wa zaice jalal zai iya wannan zancen dan Allah"


Jalal kam besan me ummi takeyi ba yayi gaba abinshi



*some hours ago*





Kwance suke jalilah duk ji take maranta na mata ciyo ta kalleshi "ya jalal taimakin nayi wanka dan Allah"


Tun jalilah na dauriya kada jalal ya fahinta har abin yazo yafi qarfinta sai faman zufa take



"Jalilah lafia? Duk yanda taso tayi mishi magana abu ya gagara ga baki daya hankalin jalal ya tashi da sauri ya nufi part din ummi ya sanar da ita



Cak jalal ya dauketa suka nufi part din ummi "jalal kaje ka kiramin assibi "ummi me zatayi? Banason fitina kaje ka gaya mata kuma dagacen kayi wurin sabgoginka kaji na gaya maka? Sam jalal bata iya musu da ummi ya tashi ya fice ga baki daya bata cikin natsuwa


Masjid ya shige yana ta faman gayawa Allah damuwanshi


Kiran mubarak yayi ya gaya mishi halinda ake ciki sam be bata lokaci ba yashigo gidan suka hadu

Sosai ya shiga kwantarwa jalal da hankali har ummi ta kirashi ta sanar dashi jalulah ta sauka "ummi jalilah fa? Lafia qalau suke da sauri ya kashe wayan suka nufi part din ummi shida mubarak




Mamaki ne ya cikasu ganin yara guda biyu wanda su daya suka sani kuma duka maza


"Wow cool jalal wannan job din naka yayi kyau wallahi" ya daga waya ya kira mai martaba ya sanar dashi ga baki daya kowa murna yake harda mai martaba yaje ganin yaran amma mami kam bata leqa ba



Ummi ce ta shirya taje wurinta "mamin abdul da nice naqi zuwa ganin jikanki da ya zama abin magana amma shuru ban ganki ba"


Murmushi yayi "ban samu time bane" murmushi ummi tayi "toh a samu time aje aga jikokina" kai ta gyada sukayi sallama ta fice............
[25/12, 15:52] Hassan Atk: 🤴🤴 JININ SARAUTA 🤴🤴





*Written by Hafsat MN*





IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_





196-200





Harara ummi ta aiko mishi ganinshi kwance kusa da jalilah "tashi ka fita" ummi dan Allah ina kikeso naje? Bazaka tashi ba sakina saba maka"

"Ummi dan Allah ki barshi mana bayada wurin da zashi fa" jalilah Allah zan bata miki"

Tashi yayi ya fice ya nufi part din mami ya nemi wuri ya kwanta


"Jalal lafia? "Ummi ce ta koreni" sosai ya bata dariya

"Kaje ka hanasu jego ko? Mami Allah ba abinda nayi kawai tace saina fita"


"Wai zai shiga tsakaninka da umminka yayi kunya"


"Jalal wane suka ka tanadarwa yaran? Mami mubarak yace wai sam sunan beyi mishi ba shine na barshi ya sanya wanda yayi mishi"

Murmushi tayi ai duk dayane sai ku jira kuji sunan da zai sanya musu



Yau ta kama ranar suna mai martaba yace ayi suna a masjid bayason wannan taron kallon mubarak baffa yayi yana murmushi "mubarak ya sunan da ka tanada musu? "Baffa hassan din shine Ibrahim khaleel husain din kuma shine Abubakar Sadiq" toh Allah ya raya mana su akan sunnah ya amsa da ameen

Harara jalal ya aikawa mubarak shima ya maida mishi

Murmushi mai martaba yayi sosai mubarak da jalal suke burgeshi


Sosai kayi walima yara kam sunsha kyaututuka sai dare jalal ya shigo part din ummi

"Me kazo yi? Ummi dan Allah wai me nayi ne da bakyason ganina? Au bakasan me kayi ba? Juyar da kanshi yayi yana kallon jalilah ta aiko mishi da sanyayyan murmushi


"Ya jalal kaci abinci ko? Yaje wurin juwairiya yaci abinci banason yawan surutu"


Haba ummi wa zaice ya jalal yana surutu kawai dai yanzu kin samu jikokine kin daina sonshi


"Jalilah zo kibishi kuje cen harda yaran" ummi toh me yake miki ne dan Allah? Tunda na haihu sai faman fushi kike dashi ni bazan ma qara haihuwan ba" ta tashi tabar yaran ta shige ciki


Kallon yaran yayi ya juya kawai ya fice


Kune masu dawowa ku daukesu ai


Mubarak ne ya shigo "ummi jalilah fa? Tana ciki


Shine zata bar yara ta koma ciki? Idan wani abu ya samesu fa?


"Gaskiya ne gara ta kula dasu" murmushi yayi "ummi dan Allah me cool jalal yayine yace kin tsaneshi ga baki daya ya daga hankalinshi"


Mubarak fitina kawai yakeji bazai bari su gama jego ba idan suka koma part dinsu ya cinyesu ai ba wanda zai hanashi


"Ummi dan Allah ki kyaleshi kinsan fa jalal baya jure kina fushi dashi ki daina dan Allah ummi" mubarak ai ba fushi nake dashi ba

Amma bazaki qara hanashi ganin yaran ba ko?

Murmushi tayi ganin mubarak yayi magana kamar zeyi kuka


"Mubarak da yara hudu amma baka daina ahagwaba ba" dariya yayi "ummi idan ina gabanku aimantawa nake dasu

Dariya tayi "toh Allah ya raya mana Ku" amin ummina" ya tashi ya fice


Zaune ya sami jalal "cool muje walid yana yiwa mami fitina Mu maidashi dan Allah murmushi yayi yaje ya karbo walid din suka nufi gidan mubarak


Tun daga wannan lokacin shiga part din ummi saboda fushi yake baffa ma a masjid suke haduwa


Yau jalilah ta cika 50days a part din ummi sam ba wani ganin jalal take ba hakan yana damunta shima jalal haquri kawai yake


Baffa ne ya tambayi ummi yaushe jalilah zata koma part dinta? Baffan jalal ka barni da jalal kawai fushi yake dani shine nakeso naga qaryan fushin"

Keda jalal din naki kuma Aisha? Ka barshi kawai sai yazo ya sameni



Bayan sallan isha jalal ya shiga part din ummi ya gaidata ta amsa "ummi gobe zanyi tafia" "toh" kawai tace dashi taci gaba da lazimi

Ahankali ya dago yana kallonta "ummi dan Allah ki daina fushi dani koda zan samu ci gaba a rayuwana"

Ni nace ina fushi dakai? "Ummi toh me nayi kika daina yimin addua?

Kallonshi tayi dakyau ga baki daya dariya yake bata "jalal wa nakeda Sama da kai da zan daina yimaka addua? Toh ummi meye laifin da nayi miki?

Murmushi tayi "bakamin laifin komi ba jalal saidai banason wannan damuwar da kake ciki" murmushi yayi ya dora kanshi saman qafanta ya kwanta

"Ummi su khalil fa? Nace su sarkin tsotso dai ai wannan badan sunan baffan jalal yake da ba da nace na fasan auren khalifa ne dai ba ruwanshi da nono saidai ko yaushe idan ba hannun jalilah yajishi ba ba zaman lafia" murmushi yayi


"Ya kwaso fitinar jalilah kenan? Ai Kaine ka bata jalilah dan ba wani damuwa tayi dani ba saboda kai

Dariya yayi daya tuna yanda suke rayuwa kafin aurenshi da jalilah


Fitowa tayi dauke da khalifa sai faman tsala kuka yake jalal yayi sauri ya karbeshi ya dorashi saman qirjinshi yana shafa bayanshi be wani jimawa ba yayi bacci


Sarkin tsotso bacci ake ne? "Hmmm ummi wallahi wannan idan banyi da gaske ba sai ya shanyeni ga baki daya"

Dariya jalal yayi "Allah ki daina yiwa baffana sharri"

Ya jalal baya qoshi fa,,, toh menene? Dama a tagwaye zaka tarar hassan yafi rikici


Harara ya aika mata wanda sam ita ba nufinta ta tsokani jalal ba

Dariya ummi tayi "ai zaman jalal da mubarak ne ya sanya jalal ya fara magana"

Allah ummi kamar kin sani haka nayita fama dashi a school


Haka suka sha fira sosai jalilah taji dadin ganin jalal


"Ummi gobe da wurin zan tafi kuma 2days zanyi"

"Ya jalal ina zaka? Dan tsaki yayi kafin ya fara magana "abba ne ya sanyani wani aiki kuma a qauye ne"

Ya jalal shine zaka zauna har tsowon 2days?

Jalilah aikin yanada yawa fa,,, kukan shagwaba ta fara yi mishi

"Jalilah bafa ko yaushe kike ganina bale yanzu kiyi fitina inaga kusan 5days ban shigo nan ba toh me akayi 2days"

Dakin ummi ta nufa tana kuka ya bita da kallo har ta shige ciki


Kallonshi ya mayar gun ummi "ai na gaya mana kai zakafi kowa shan wahalar jalilah saboda kai ka batata"

Tashi yayi yabi bayanta yana dauke da khalifa

Zaune ya sameta tana bawa khalil nono ya zauna kusa da ita ta juya mishi baya

Murmushi yayi "precious bikiyi missing dina bane?


Juyowa tayi tana kallonshi "ya jalal dan Allah kada ka kwana pls"

Jalilah meye abin damuwa aciki tunda biki koma ba

Ya jalal Allah zan koma yau


Dariya yayi "yi haquri aikin bana wuni daya bane" kai ta gyada mishi

Kallon khalil yayi wanda yake ta faman shan mono ya kafe jalilah da ido


Dariya yayi "khalil wannan wayon naka yayi yawa gaskiya"


Cire mishi nonon tayi a bakinshi aiko yasa kuka da sauri jalal ya maida mishi yana dariya


"Baffana gaskiya ka daina yiwa khalifa wayo kana shanye ga baki daya shi kuma sai faman bacci yake

Dariya jalilah tayi "ya jalal mami tace haka tayi fama da ya abdul har fada sukeyi da abba idan ta hanashi

Murmushi yayi yaci gaba da matsa mishi nonon

"Ya jalal haka ai sai ka sanya ya qware" wannan ai idan yafi haka bazai qware ba


Ya jalal tsaya ka gani ta zame mishi nonon ya shiga kuka ta fara lallabashi sai faman kuka yake

Kallonshi kawai jalal yake "precious yi haquri ki qara mishi kinji?

Ya jalal Allah baya qoshi

"Yi haquri precious qara mishi kadan"


Ci gaba da bashi tayi yana sha daqyar yayi bacci

Dariya jalal yayi "sannu da qoqari


Murmushi tayi ta karbi khalifa ta kwantar dashi ta juyo tana kallonshi "ya jalal yaushe zamu koma part din mu? Yaushe kike so?

Dariya tayi "yau nakeso" kai ya gyada mata..........
[25/12, 16:10] Hassan Atk: 🤴🤴 JININ SARAUTA 🤴🤴






*Written by Hafsat MN*






IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_






201-205






Ya jalal da gaske fa nake Allah na gaji da wannan rashin ganin naka "ba wani rashin ganina ki dai fadi abinda yake ranki"

Ya jalal idan har zaka riqa zuwa ko yaushe ina ganinka ka barmu anan kawai

Dariya yayi dan shi bega abi fushi anan ba "fushi kikayi? Dariya tayi "ya jalal Allah kai sai kayita faman fassara mutum" naji muje ki hadamin kayan da zan tafi dasu" ya jalal wai da gaske kake 2days zakayi?


Murmushi yayi aranshi yace 1week ma zanyi wallah,,,,,


"Jalilah kinga idan banje ba zaiyi tunanin kawai dan ba aikin baffa bane" murmushi tayi "Allah ya taimaka"


*8:30pm* jalal ya shigo wurin ummi suka gaisa yq nemi wuri ya zauna "ummi dan Allah ki bari jalilah tq koma part dinta yau"


Kallonshi tayi da kyau "jalal ba tafia zakayi ba?



"Ummi dan Allah ki barta ta koma" "jalal naga tafia zakayi idan ka dawo sai ta koma ko? Shuru yayi kawai ya daina kallonta


"Jalal tashi ku tafi sauki ne na nema muku nima ai bason zaman naku nakeyi ba"

"Aa bari kawai ayi yanda kika tsara" au fushi kayi kenan?

"Ummi ba fushi nayi ba kawai dai na sanja raayine"

Idan har ba fushi kayi ba ka hada iyalinka ku barni wurina nasha iska"



Kai ya gyada zuciyanshi cike da farin ciki dan yasan idan ba haka yayi ba ummi zatace sai ya dawo daga tafia

Tashi yayi ya nufi dakin da jalilah take ya sameta kwance direct kan jikinta yaje ya kwanta


"Ya jalal ina ka shigene haka? Wurin ummi mana


"Kinga tashi mu tafi dan Allah" ya jalal ka gayama ummi ne? Harda fushi saida nayi kafin ta amince


Dariya jalilah tayi "ya jalal Allah yanzu ya dace ka ajiye shagwaba ka girma fa yanzu "

Wane girma ne nayi? Yara nawa kake da? Mahmud da Mustapha"


Amma kuma kake shagwaba? Dariya yayi "Allah bari kiji koda jikoki nake da idan ummi na kusa bazan daina jin kaina yaro ba"

Dariya tayi "ni dai yanzu na girma gaskiya tunda har aisam ya zama saurayi" dariya sukayi naga yanda kika girma ai

Ai tashi daga kan jikinta ya daga "dauko khalifa sai muje"


Mamaki yake me mai martaba yakeyi tsaye kuma shi kadai


Wurinshi suka nufa "sannu abba" murmushi yayi ya karbi khalifa da yake hannun jalilah "wannan waye?

"Abba sadiq ne" murmushi yayi "masha Allah, aminina ka girma sosai fa" murmushi sukayi ya bata ya karbi khalil

"Malam Ibrahim bacci yake gashi sak kamar malam Ibrahim din"

Ya bawa jalal shi "abdul jalal sammako zakayi gobe? Kai ya gyada


"Allah ya taimaka" ameen suka amsa tare da juyawa suka nufi part dinsu


Kallo ya bisu dashi yana murmushi sai faman murmushi jalal yakeyi jalilah nayi mishi magana har suka shige ciki


Ajiyan zuciya mai martaba yayi yaci gaba da zaga gidan



Washe gari jalilah ta zubawa jalal ido taga ya kwanshi kaya da yawa "ya jalal wai har kwana nawa zakayi wannan uban kayan ai sunyi yawa"


Murmushi yayi "kinsan halin abba yana iya qaramin kwanaki kuma yana iya ragemin gara naje da shiri"


Ba wani qara maka da zeyi saidai ya rage maka


"Haka nake fata ai"


Rakiya tayi mishi yana dauke da yaran ga baki daya

Suka nufi parking space


Kallonshi cool AJ yayi yasa dariya sosai jalal ya hade rai


"Ya abdul lafia? Kusa dasu yaje ya karbi yaran "cool jalal wai da gaske 1week zakayi acen?

Kanshi ya dafe "1month zanyi"


"Ya jalal amma fa 2days kace zakayi" "jalilah 1week abba yace ni kuma na shirya aikin cikin 2days zan gamashi"


Kai ta gyada tana murmushi

Cool AJ kam dariya kawai yake dan yasan 1week jalal zeyi


Sallama sukayi cool AJ ya nufi part din mami da yaran

Kallonta yayi "wai ahaka zan tafi?



Dariya tayi taje tayi hugging dinshi tare da hada lips dinsu suka shiga kissing din juna

Daqyar jalilah ta samu ya barta ya tafi


Part din ummi ta nufa


Kallon yaran mami tayi cike da murmushi "abdul ina zaka da yara haka da sassafe?


"A hannun cool jalal na karbosu kinsan yau ne zeyi tafian toh na hadu dasu ne a parking space"



Murmushi kawai tayi aranta tayi mishi addua



Call din ummi ne ya shigo wayanshi ya daga "ummina kin tashi lafia? Murmushi tayi mishi


"Tafia ba sallama? Ummi na shiga naga kina bacci shiyasa Dana shirya na wuce dan banaso na tadaki"


"Allah ya tsaremin kai kuma kayi a hankali a kiyaye dokokin Allah"

"In shaa Allah ummi"


Sukayi sallama ya kira baffa


"Abdul jalal kana hanya ne? Eh baffa ya kafancen din?


Lafia qalau abdul jalal Allah ya kiyaye hanya ka kula sosai kaji? In shaa Allah baffa zan kula


Sukayi sallama ya ajiye wayanshi



Cikin 3hrs ya isa qauyen da mai martaba ya turanshi



Kallonsu jalal yake cike da tausayawa yanda suke rayuwa haka yaci gaba da zaga garin yana ganin abinda ke faruwa harda kwalla a idanunshi


Zama yayi acikin mota ya shiga lissafin kudin da yaga kamar suna buqata da kuma abinda mai martqba ya bashi


Call din mubarak ne ya shigo wayanshi ya daga cike da murmushi


"Amma kasan da nine bazanyi maka hakan ba ko?

Cike da dariya yake magana "me kuma nayi? At least idan bazaka samu damar zuwa ba sai kamin waya inje mana dan Allah yanzu idan ka dawo ka tarar na mutu kuma fa? Shikenan na tafi ba tare da munyi sallama ba?


Murmushi jalal yayi "sorry ba haka bane ka daina zancen mutuwa akanka pls"


Toh meyasa kayi haka? "Mubarak wallahi hankalina yakan mutanen nan ga baki daya tunda abba ya gaya mana halin da suke ciki duk da ba qarqashin masarautar abban bane hankalina a tashe yake wallahi"

"Eh daman nasan bazaka rasa abin fada ba abdul jalal mai imani"


Dariya yayi "mubarak rayuwar mutanen nake dibawa rayuwa ba ruwa ba abinci ai akwai tausayawa"


"Ka tausaya musu ni kuma ai ka jefani cikin halin jin yunwa dan bazanci abinci ba sai ka dawo"


"Allah ko jawahir ce tayi tafia bazaka qi cin abinci ba bake ni"

Dariya sukayi ga baki dayansu mubarak yayi mishi fatan alkhairi sukayi sallama ya ajiye wayan yaci gaba da aikinshi


Duk yanda jalal yake tunanin aikin sai yaga yafi hakan ga engineers suna qoqarin fara nasu aikin



Call din jalilah ne ya shigo ya daga "my heart desire" dariya tayi "ya jalal duk aiki ne haka?

Murmushi yayi "aiki yanzu na fara wallahi" zaa gajiyarmin dakai kenan? Murmushi yayi "bazan bari hakan ta faru ba ai"


Haka sukaci gaba da fira yana kallon yanda ake gudanar da aikin



Tsawon kwana 3 jalal ya samar da ruwa a qauyen gashi sai fama yake da rigiman jalilah akan ya dawo




Cikin tsari jalal ya bawa kowa hannun jari akan su nemi Sana'a yafi ya zube musu abinci idan ya ware kuma shikenan



Yau jalal ya cika kwana shida sai murna mutanen qauyen suke da abinda yayi musu ya shirya ya dawo cikin zaria


Kwance take Khalil yayi bacci khalifa kuma mubarak ya tafi dashi part din cool AJ


Ahankali ya shiga cikin dakin


Qamshin tularenshi taji ahankali ta rufe idanunta tana murmushi

Kwanciya yayi bayanta da sauri ta juyo tayi hugging dinshi "oyoyo ya jalal" dariya yayi ya qara hugging dinta ya fara kissing dinta................
[25/12, 16:10] Hassan Atk: 🤴🤴JININ SARAUTA 🤴🤴






*Written by Hafsat MN*





IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_






206-210






Sai faman dariya take shi kuma ga baki daya yaji jikinshi ya amsa saqon da jikin jalilah yake aika mishi



_some hours ago_




Zaune suke a parlour mubarak yayi sallama ya shigo ya nemi wuri ya zauna,,, kallonshi jalal yake cike da murmushi "na angel fushin ne har yanzu? Kai ya girgiza yana murmushi


"Meke faruwa ne? Ba komi ya bashi amsa

Kallonshi jalal yayi cike da nazari yayi saurin kawar da kanshi ya maida kan yaran da suke kusa da jalal din yana murmushi


"Mubarak" jalal ya kirashi

Kallonshi kawai yayi ba tare da yayi magana ba "gayamin abinda yake damunka"



Kusa dashi mubarak yaje ya zauna "ba abinda yake damuna kawai gajiya ne"

Kai jalal ya gyada yaci gaba da kallonshi sam ba wanda yake magana da wani daga cikinsu


Tsawon lokaci mubarak ya tashi kawai yana kallon jalal "zan tafi" kai ya gyada mishi kawai ya juya ya tafi jalal ya bishi da kallo




Zaune yake a gaban mai martaba ya bayanin aikin da yayi a qauyen sosai mai martaba ya sanya mishi albarka ya tashi ya nufi gidan mamin mubarak


"Jalal lafia naga kayi zaune ba magana?


Mami dan Allah taimako nakeso kimin,, me kake so jalal?


"Mami a rayuwa ba abinda yake sanya mubarak damuwa face abinda ya shafeki ko kuma mahaifinshi dan Allah ki sanar dani damuwarshi"


"Jalal yanaso yaje wurin dangin mahaifinshi ni kuma nace baxashi ba saboda basu damu dashi ba kuma basa sonshi dan ba wanda ya nemimu tunda mahaifinshi ya rasu"


"Mami dan Allah kiyi haquri yaje tunda sunzo ranshi yanason ya gansu kinga ya shiga damuwa sosai wallahi"


Jalal sam bazaije ba gaskiya gara ya haqura kawai

Mami dan Allah kada kiyi haka kiyi haquri kinga zai samu lada kuma baasan halin da suke ciki ba dan Allah mami kiyi haquri kada ya shiga wani hali


"Jalal banason nacin zance nace bazashi ba ko? Sunkuyar da kanshi yayi qasa tsawon lokaci yana zaune a gabanta


"Jalal kana buqatar wani abune? Kai ya girgiza mata

Toh ai ka koma ya fiye maka wannan zaman

Ta tashi ta shige ciki ya bita da kallo



Kusan 10mnts tayi aciki ta fito ta sameshi murmushi kawai tayi


"Jalal wannan nacin naka ko mubarak din beyishi ba"

Mami dan Allah kiyi haquri ki barshi yaje


Address din gidan su alhaji Mustapha azare ta bawa jalal "wannan shine address din gidansu mahaifinshi yaje Allah ya kiyaye hanya


Cike da farin ciki jalal yayi mata godiya ya fito ya nufi gidan mubarak


Kwance yake kan 3sitter ya rufe idanunshi jalal yayi sallama ya tashi zaune yana murmushi


"Daga ina haka? Jawahir fa? Murmushi yayi ya tashi ya kirata


"Cool jalal nake gani haka? Murmushi yayi "kawai kinje kin sanya yaro a daki kina koya mishi lalaci bayan shi jarumi ne"

Amma kasan nima ai raguwa bace


Eh hakane gaskiya shiyasa ko yaushe kina a kwance


Dariya tayi suka gaisa tayi mishi ya gajiyar zuwa qauye


"Ni zan koma dama naje karbo wani saqo ne kawai"


Rakiya mubarak yayi sam ba wannan wasan da yake tsakaninsu har jalal ya shiga ciki mota yana mamakin mubarak

Kallonshi "ajiyemin wannan ya bashi kawai yaja motanshi ya fice



Mamaki ne ya cika mubarak ya koma ciki ya kira maminshi ta gaya mishi yanda sukayi da jalal din


Shiryawa yayi ya nufi gidan mai martaba


Kallonshi jalal yayi ya kawar da kanshi yaje kusa dashi ya zauna yana murmushi


Tashi jalal yayi da sauri ya rikeeshi "ka tsaya muyi magana mana" fizge hannunshi yayi da sauri mubarak ya tashi ya riqeshi

Dariya jalilah tayi "ya mubarak daman wannan fushin da dakeshi Kaine ka janyoshi har ya shafeni?


"Jalal bansan me zan gaya maka bane shiyasa" fizge hannunshi yayi kawai ya nufi dakinshi


"Ya mubarak Allah nifa mamaki kuke bani" murmushi kawai yayi yabi bayanshi


Wuri ya nema ya zauna jalal ya tashi ya fito yaje kusa da jalilah ya zauna "ya jalal kayi haquri mana"

Yatsanshi ya dora saman lips dinta yana murmushi

Tsaye yayi kusa dashi "jalal meyasa bazaka saurareni ba kawai sai kayita faman fushi dani?

Tashi yayi ya kalleahi da kyau "me zaka gayamin? Ni dan uwanka ne kuma friend indeed amma ba in need ba ko? Toh kasa ka bata lokacinka nasan da hakan


"Jalal ya kake magana
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment