Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

weeks_


Mubarak yana kwance yana bacci jalal ya hada kayanshi da basu set uku ba ya rubuta mishi short note


"Zan tafi weekend"


Ya ajiye ya tafi kawai, mubarak yana tashi sosai gaji beji dadin hakan ba at least ya rubuta contact dinshi ya ajiye mishi mana gashi bemasan daga ina jalal din yake ba, haka ya qaraci zamanshi na week end cikin kadaici da kewar jalal



Zaune yake cikin room dinsu abdul jalal yayi sallama ya amsa ba tare da ya kalleshi ba yasan fushine mubarak din yakeyi



Wanka yaje yayi ya dawo ya shirya,, magana yakeso yayi mishi amma besan same sai fara ba

"Muje class" wani kallo mubarak yayi mishi yayi murmushi tare da kawar da kanshi "me kace? Mubarak ya tambayeshi


Shuru be bashi amsa ba "abdul jalal ina takuraka ne? Kallonshi yayi da alaman tambaya "eh abinda nake nufi kenan saboda na fahinci kai ba bakason muaamala dani banason shiga rayuwanka idan ina takuraka ka gayamin zan kyaleka"


Murmushi kawai yayi danshi ba mubarak din ne matsalanshi ba kawai dai yana mamakin yanda mubarak ya gagara fahintar halinshi ne hakan


Kai nake sauraro,,, ahankali ya bude Bali yace "sorry" kallonshi mubarak din yayi ya kawar da kanshi yanaso yayi dariya


Dariya mubarak yayi "gaskiya baka kyautamin ba za kaje week end ae sae ka gayamin da wuri gashi saqon jaililah ma bakajemin dashi ba kuma dan wulaqanci ko contact dinka baka ajiyemin ba kawai ka tafi abinka"

Hmmm muje

Bazani ba dan yunwa nakeji,,, kallonshi yayi ya juya ya ajiye hand out dinshi ya fice, be wani jimawa ba ya dawo da coke a hannunshi ya bude jakan da yazo da ita ya ciro naman kaza da Ummi ta bashi ya miqa mishi ya karba

Sosai yaji naman saboda yayi mishi dadi

Bayan ya kammla ya boye sauran abdul jalal yana kallonshi ya wanke hannunshi suka fice


Kallonshi mubarak yayi "cool jalal waya soya naman dan Allah? " Ummi" ya bashi amsa ba tare da ya kalleshi ba


Allah na matsu na koma na qaracinshi, ko kallonshi jalal beyi ba yaci gaba da karatunshi



_After a weeks_


Exam sukeyi ba wanda yake wasa da karatu acikinshi

Tafiya suke ya biyo da mota da gudu ya watsa musu ruwa duk yanda mai karatu yake tunanin baci ran jalal ya wuce hakan sosai ya bawa mubarak mamaki ganin yanda ya wani hade rai ba tare da yayi magana ba, haka suka nufi hostel jalal sai faman cin magani yake


Yaune ranar da suka kammala exam mubarak zai wuce garin Kaduna jalal yace shi sai gobe zai tafi dan bayason mubarak ya bada komi a kawai jalilah


Okay gayamin shekarun jalilah,,, banza yayi dashi

"Wai jalal meyasa kakeji dadin kyaluwa ne? Murmushi yayi ya tashi ya fice


Zaune mubarak yake hanata faman jiranshi amma shuru ba wani labari kusan 1h kafin ya dawo

Kallon kayan hannunshi yake ya ajiye ya kwanta

Ledan mubarak ya diba yaga abayane da cosmetics

Sam jalal be kula da kallon da mubarak yake mishi ba

Tashi yayi ya hada kayanshi ba tare da tace dashi komi ba yaja akwatinshi ya fice ya dawo ya dauki wayanshi ba tare da tace dashi komi ba ya wuce abinshi cike da takaici


Murmushi kawai jalal yayi ya tashi ya hada kayanshi ya fito

Cike da mamaki ya kalli mubarak zaune yana amsa waya danshi a tunaninshi mubarak ya tafi kenan


Murmushin dole yayiwa mubarak yaje kusa dashi ya tsaya

"Baka tafi ba kenan?



Harara yayi mishi "malam meye damuwarka dani? Rana ta farko da mubarak yaga jalal yayi dariya tare da juyawa sosai ya burge mubarak "sorry na sanja shawara ne zan tafi yanzu"


Murmushi yayi tare da girgiza kai "bari driver yazo mu tafi" ido jalal ya zare "ina? Kafancen mana" dariya ya qarayi cike da qasa ita kamar wani jinin sarauta


Sorry baza muje tare ba gaskiya "meyasa? Nazarin ya shigayi "toh me zakayi kafancen wai kawai saboda tsaban son wahalar da kai? Kallonshi mubarak yayi "Allah ka gama duo wani tunani da zakayi sai munje tare murmushi kawai yayi ya nemi wuri ya zauna

Driver din ne yazo "ganshi inji hajiya tace na Baka wannan ya karba suka shiga ciki driver yaja suka dauki hanya



Da gudu ta fito "ya jalal oyoyo oyoyo" murmushi kawai yayi tayi hugging dinshi sam bata kula da mubarak har suka shiga ciki sai zuba mishi surutu take


Gaban baffa ya zube cike da girmamwa ya gaidashi "abdul jalal haka makarata ya maidamin dakai? Murmushi yayi baffa ya gaisa da mubarak tare da Santa musu albarka ta fatan alkhairi

Dakin Ummi suka nufa cike da murna ta tarbi mubarak suka zauna


Kallonshi jalilah tayi "ya jalal wannan ne mukayi waya dashi ko? Kai ya gyada mata

Umurni ummi tayi musu suje suyi wanka suzo suci abinci...........
[25/12, 13:21] Hassan Atk: 🤴🤴 JININ SARAUTA 🤴🤴





*Written by Hafsat MN*





IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_





21-25





Zaune suke a dakin ummi ta zuba musu dambu da taha musu zobo mubarak kam sai faman ci yake

Jalal ne ya fara kammalawa ya tashi ya koma kan kujera ya zauna

Da gudu ta shigo ta zauna kan jikinshi tadan kwantar da kanta "ya jalal me kakeyi? Be amsa mata ba yaci gaba da matsa wayanshi tana kallon abinda yakeyi

Kallonsu kawai mubakar yakeyi yana murmushi "ya jalal inzo ka gyaramin kaina sai muje wurin kitso? Kallonta yayi "yanzun ne za muje ke bikisan ina tare da gajiya bane? Turo baki tayi alaman fushi "toh ai gobe akwai school kuma banaso na tafi ba kitso" kidaizo in yi miki kalaba idan kinaso sai ki bari week end muje kitson"


Mamakin yanda yake magana mubarak yake daman Ummi ta gaya mishi jalilah ce kawai take sanyashi magana


"Ya jalal in kwanta? Aa ki zauna a qasa yanda za muyi sauri" bata ranta tayi tare da turo baki "Allah ni nafiso a kwance


Be kulata ba ta kwanta ta dora kanta saman lap dinshi ya fara yi mata


Dariya mubarak yayi "lallai cool jalal babba kake, wai da gaske ka iya? Dariya ummi tayi "ai har kunshi yi mata yake dan ni bazan iya rigimar jalilah ba ga baki daya ya batata da son jiki da fitina ga rikici akan abinda ba nata ba" dariya mubarak yayi yaci gaba da kallon jalal da yake faman yima jalilah kalaba har ya kammla tas kai baxakace jalal ne yayi ba ya hada wuri daya yasa mata ribbon "tashi kije kiyi wanka" ya wari nakeyi? Aa ban fada ba" aiko mubarak ya shiga dariya "jalilah kitsonki yayi kyau gaskiya" ai ya jalal din ne ma yau beso yimin mai kyauba da ka ganni kamar wata balarabiya " ta qarasa magana tana dariya aiko mubarak ya shiga dariya taje tayi wanka ta dawo


Kayan make up dinta ta kwaso ta zauna kusa da jalal "ya jalal ka banisu daya bayan daya ina shafawa kaji? Kai kawai ya gyada mata

Daya bayan daya ya riqa batasu tana shafawa har ta kammala kwalliya gashi tayi kyau sosai


Taje tasa kaya ta fito "ya jalal dauramin dan kwalina" ba musu ya karba ya daura mata


Cool kace kai na mace ne kawai,,, dariya sukayi shida ummi

Mubarak ai dolene ya koyi komi na mata dan shi ya dauka ma kanshi yanzu wa zaice jalilah jss 2 take? Ido mubarak ya zare dan shi Sam bega alaman hakan ba


"Amma ummi shekarunta nawa? 11 yeas "ummi yanzu fa 12 nakeda ko ya jalal? Kai ya gyada mata "toh kaji amma ko yaushe tana jikin jalal kamar mage


Dariya mubarak yayi






Duk yanda juwairiya taso ta qyale cool A J ta gagara saboda ruwan da ya watsa mata kuma ya kirata da sunan jahilah

Cike da takaici ta qaraso wurinshi tadaga hannu ta wankeshi da mari

Ranata farko da cool A J ya qare mata kallo ba tare da yace komi ba kawai ya bude motanshi ya dauko wayanshi yayi snapping dinta ya shige motanshi



Sam bata kawo komi aranta ba da dare ta shirya ta nufi class dan akwai assignment din da takeso tayi


Haskata akayi da fitila sai tayi murmushi " Salma Allah ki daina" haka har ta qaraso wurin da Salma take


Cikin zafin nama suka turata cikin motan sai zuba ihu take suka rufe suka tafi da ita


Sam bata fahinci idan suka nufa da ita ba kawai dai ta ganta a wani dan qaramin gida sun turata cikin wani daki suka rufe


Ba irin kukan da bata sha ba amma sukaqi budeta har gari ya waye


Cikin takunshi na isa yazo ya bude qofan ya shiga


Ahankali ta dago tana kallonshi idanunta duk sun kubura

Tsaye ta miqe da sauri tana nunashi


Ya nemi wuri zauna sam ba alaman wasa a tare dashi


"Allah ya isa tsakanuna dakai mugu kawai kuma wallahi idan har ka bari na fita gidan nan sai kayi Dana San in abinda ka aikata zakasan nu juwairiya ba kanwar kasa bace kuma danasan Kaine kasa aka kawoni nan da ban bata hawayena ba nayi kuka "


Murmushi yayi ya kira AK a waya ya shigo "kaida ka damu da mata ga wannan idan zaka iya hada jiki da wannan qazantar

Dariya AK yayi "gaskiya yau zan more" kada ka yarda tayi mana taurin kai idan kuma tayi zan turo wadan da zasu daure maka ita" dariya AK yayi

Cool AJ karma damu ai ba wani yawa ne da ita ba zan iya tafiyar da ita


Tashi yayi ya fice AK ya matso kusa da ita tayi murmushi "na roqi Allah tsari da sharrunka dan haka kasa ka bata likacinka dan bazaka iya yimin komi gara kawai kaje abinka" kallinta yayi ba tare da yaji yana iya dogon motsi ba ta juya ta nufi Inda take tunanin toilet ne


Cikin sanyi AK ya juya ya nufi inda cool A J yake

Cool AJ kabarta ta tafi kawai "eh zata tafi na kira wanda zai yanka hannun da ta mareni dashi tace yana kan hanya" ido AK ya zare ganin da gaske cool A J yake yanka hannunta zeyi


Cool A J ta cancanci wannan hukuncin amma ka yafeta


No ka daina wannan zancen bazai yuyu ta zauna da wannan hannun ba dan ba nata bane,,, kallonshi kawai A K yakeyi


Cool A J amma ka tausaya mata mana "tsaki yayi kawai ya tashi ya dauki wuqan da yake kusa dashi

Cool A J!!! AK ya kirashi da qarfi "kada ka aikata hakan kasan mai martaba bazai taba kyalekaba zeyi maka hukunci fiye da hakan kada ka soma

Tsaki yayi "wait, kai zaa yima hukunci? Kai ya girgiza amma kasan duk abinda ya shafeka ya shafeni ko?

Dakin ya nufa ya sameta ta kammala sallah

Kusa da ita yaje ya zare wuqan ya janyo hannunta cike da zafi tayi wani ihu

Suka shiga kokawa tana ihu har ta kaisu ga faduwa qasa
Iya karfi cool A J ya danneta tare da janyo hannunta ya fara yankawa

Cikin wahala ta furta "pls A J have mercy on me for God sake" cak ya tsaya yana kallonta duk ta jigata ga wani zazzafan hawaye da yake zuba a idonta

Rana ta farko da mace ta bashi tausayi

Kallonta yake cikin yanayin tausayi idanunta na rufe ga azaba ga nauyin A J

Ahankali ya tashi daga kanta tare da dagota

Hawayene suka qara zubo mata saboda yanda cool A J............
[25/12, 13:21] Hassan Atk: 🤴🤴JININ SARAUTA 🤴🤴





*Written by Hafsat MN*





IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_






26-30





Hawayene suka zubo mata sakamakon yanda cool A J ya janyo hannunta, haka ya riqa janta har suka fito wurin da yayi parking,,, cike da tanshi hankali AK yake kallonshi ya turata cikin mota ya rufe



Direct sai hospital ya kira family doctor dinsu ya gaya mishi yanason ganinshi


Zaune yake saman kujera Dr. Labaran yana kallonshi cike da alaman tambaya


"Stitching zakayi mata" ya fada tare da ci gaba da matsa wayanshi


"Meya sameta ne? Ni na yanka hannun saboda ta mareni dashi" kallon mamaki yayi mishi "abdul baka tunanin abinda zai biyo baya? Wanikallo ya watsa mishi "kayi mata abinda nace kafin na daina jin tausayinta dan wallahi burina na cire hannun ga baki daya" murmushi Dr labaran yayi ya fara yi mata stitching



"Ke tashi muje" ba musu tabi bayanshi suka fice direct sai cikin school ya nufa da ita ya nemi wuri yayi parking


"Ki gode Allah yaune rana ta farko Dana fara jin tausayin mace da wallahi keda hannu saedae ki gani a wurin wasu" kallonshi kawai take tana mamakin qarfin hali irin na A J


Kudi ya ciro ya miqa mata kallonshi kawai take ba tare da ta karba ba, murmushi ya sakar mata tare da zube mata kudin a jikinta "out"

Ahankali ta bude motan ta fice


Tsaki yaja tare da tada motan da qarfi ya fice daga cikin school din ya nufi gida direct sai dakin mami ya zube

Kallonshi "abdul daga ina haka? Mami wallahi school nake duk na gaji" murmushi tayi mishi "toh kaje ka huta ko? Murmushi yayi ya tashi ya nufi part dinshi ya zube wayoyinshi ya kunna sigari ya fara sha yana kurba giya har ya samu yin bacci



***********************************




Zaune suke shida mubarak sai faman surutu jalillah take zuba musu wani zancen ya kualata wani kuma yayi kamar beji ba sai dai mubarak din ya kulata


"Ya jalal kaga yanda gonar baffa yayi? Allah kadan ya rage na cire wani rake sai naji baffa yace jalilah muje gida yamma tayi,,, sai na cije yatsana nasan da kana nan Allah zakasa qarfi ka ciremin ko? Kai kawai ya gyada mata

Ya jalal ko za muje ne? Aa bazani ba,, turo baki tayi "Allah ni sai munje" ke wane irin fitinane kika qaro haka? Kuka taxa mishi ya aika mata da saqon harara ya aika mata ta tashi taje kan jikinshi ta zauna "ya jalal muje" wai ke kenan idan kinaso abu sai kinyi fitina? "Toh muje" tsaki yayi "je ki sanya hijab kizo" aa ya jalal bari nasa abayana" kai ya gyada mata tayi mishi dariya ya sakar mata murmushi

Kallonshi mubarak yayi "gaskiya kanaji da jalilah sosai fa" murmushi yayi "toh ai banida kowa sai ita" dariya mubarak yayi "har gara kai ni ni kadai mami ta haifa abba ya rasu bata qara yin wani auren ba bale na samu wani ko qanwa" murmushi yayi mishi


Kallonta mubarak yake har ta qaraso wurinsu taje jikin jalal ta zauna "ya jalal ummi tace a dawo da wuri" kai ya gyada mata suka tashi suka fice

"Yaya jalal kawo kudin madarar kuka, ya mubarak kaima zakasha ko? Eh zansha mana kawai ya bamu kudin mu siyo" dariya tayi tana kallon jalal ya dauko naira dari ya bata "toh Ku jirani anan kunji" dariya mubarak yayi tare da gyada mata kai


Sosai mubarak yayi mamakin gonakin da su jalal suke da komi yayi sosai gonar ta burgeshi suka shiga zaga gonakin

"Ashhh" da sauri suka juyo "menene? Bansan meye na taka ba, sunkuyawa yayi ya cire mata "sannu ya furta ahankali tare da shafa face dinta, kallon da mubarak yayi mishi ya sashi jin kunya ya juya yana murmushi yana juyo suka hada ido da mubakar ba shiri yayi dariya


Allah cool Jalal Kannada abin dariya,,, ai kai kake sanyani dariya Allah


Wannan irin so haka anya zaka iya bada auren jalilah ko? Kallonta yayi tayi dariya " toh kasan sae dolene tayi auren so pls zancen ya wuce" yayi gaba ya barshi shida jalilah



Zaune suke mubarak da jalilah suna shan rake jalal kuma yacin abinci

"Yaya mubarak bani labarin school dinku" kallonta jalal yayi tana shan raken
Jalilah ai ina gaya miki school tafi rake dadi" ido ta zare "school kayi bulala school fa akwai wahala amma rake akwai dadi idan fa ina shan rake har ni yake iska tana daukana


Tashi jalal yayi yana murmushi ya shige dakin ummi aiko mubarak ya shiga dariya harda riqe ciki


"Jalilah muje wurin ummi" suka tashi suka nufi dakin ummi

"Malam saboda Ku fa na dawo nan" wurin ummi fa mukazo

Kallonsu Ummi tayi tana murmushi " Ummi gobe nakeso na tafi" kallonshi jalal yayi suna hada ido ya kawar da kanshi yana murmushi

"Toh mubarak Allah ya kaimu goben" ameen ya amsa


Washegari driver yazo dauka mubarak su jalal sunyi miahi rakiya ummi ta hada mishi chin chin ta soya mishi zaki ta bashi ya tafi dasu

Kallonshi jalal yayi ya rufe idanunshi ahankali yana murmushi ya bude suna hada ido ya kawar da kanshi yana dariya cike da qasa ita shima mubarak din dariya yayi tare da daga mishi hannu suka fice sosai jalal yaji kewar mubarak haka mubarak din yakeji kamar yabar wani rabin jikinshi ne



Zaune take duk abin duniya ya isheta ga baki daya ba yanda Salma batayi da juwairiya ta gaya mata ina ta kwana kuma me ya sameta amma taqi da qarshe ma bacci ta shiga yi.................
[25/12, 13:21] Hassan Atk: 🤴🤴JININ SARAUTA 🤴🤴





*Written by Hafsat MN*





IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_






31-35





Bayan ta tashi daga bacci tayi wanka suka nufi class ita da salma dan gobe za suyi exam na qarshe su wuce gida


"Juwairiya ga mutumenki nan fa" ahankali ta dago suka hada ido da cool A J tayi saurin kawar da kanta taci gaba da karatun da take


Sigari ya shiga zuqa yana matsa wayanshi har ya gaji ya nufi gida


Bayan juwairiya ta gama exam ta hada kayanta suka nufi katsina ita da salma



Haka sukaci gaba da rayuwa har hutu ya qare kowa yayi shirin dawowa school



Tsaf ya sami dakin da alama jalal ya qaraso kenan, murmushi yayi cike dajin dadi ya sauke kayanshi ya nufi toilet yayi wanka


Tsaye yake yana kallon jalal wanda kallo daya yayi mishi ya kawar da kanshi yana murmushi " kai baka ganni bane? Ya fada yana qara hade face, dariya jalal yayi "toh ai ko kaine malam ibrahim bazaka wuce haka ba" dariya mubarak yayi ya sa kaya yazo ya zauna


Ina saqona? Kallonshi yayi da alaman tambaya "eh abinda ummi ta baka ka kawomin nake nufi" tashi yayi zai fita mubarak ya riqeshi " malam yunwa fa nake ji" kamar ba zeyi magana ba ya tsaya yana kallon mubarak " na gaya maka banason wannan kallon" murmushi yayi "2mnts pls" ya janye hannunshi daga na mubarak ya fice, be wani jimawa ba ya dawo mishi da coke ya bashi ya fitar mishi da naman kaji ya miqa mishi ya zauna ya faraci shi kuma jalal kwanciya yayi abinshi yana kwallon mubarak har ya kammala ya tashi ya wanke hannunshi ya dawo


Malam tashi dan Allah bacci zanyi,, sam jalal yayi kamar beji me mubarak yake fada ba ya shareshi "Allah nima fa na iya shariya gara kawai ka bini ahankali" kallonshi jalal yayi ya kawar da kanshi " malam zaka tashi kosai na tureka? Kallonshi jalal yayi da kyau sai kuma yayi dariya dan yasan mubarak bayada qarfin da zai tureshi "kalleni da kyau ba makusa ajikina" dariya yayi ya tashi ya koma gadon mubarak din ya kwanta


************************************



Mami dan Allah kada kice sai ya dawo gidan nan yana takurani ne,,, abdul wai me imran din yake mana ne? Ni ki barshi a gidansu kawai" tsaki tayi tare da girgiza kai ya tashi ya nufi fada



Gaisuwa ya miqawa sarki fadawa suka fara "an gaisheka magajin sarki" wani harara yayi musu ya nemi wuri ya zauna



Cikin muryar nan ta qasaita sarki mahmud ya fara magana "abdul jabbar munada baqi wadan da kaine zaka shige musu gaba a madadina har su kammala abinda sukazo yi su tafi" cike da girmamawa ya amsa tare da yiwa sarkin fatan yawancin rai ya tashi ya fice



Jakanshi ya janyo ya bude ya shiga fitar da kaya ko wace set biyu ne a hade wuri daya haka yayita fitar dashi tun daga manyan kayan har izuwa qananan kaya set goma sha biyar kuma duka iri daya haka ya fitar da shoe set goma sha biyu ko wane biyu iri daya ne sam jalal be kula da abinda mubarak yakeyi ba saboda hankalinshi yana kan waya

Mubarak ya kwashi set goma sha biyar da na shoe 6 yakai ya zuba acikin locker din jalal ya juya ya dauko system sabuwa ya zauna yayi connecting da nashi ya shiga copying abubuwa masu amfani

Kallonshi kawai jalal yake har ya kammala, kallon jalal yayi yana murmushi ya tura mishi system din "nasan koda na Santa mana films zaka gogesu ne shiyasa banyi ba mami ce tace a baka" wani kallo yayi mishi "amma na gaya mana banason irin wannan kallon ko? Kawar da kanshi yayi amma Sam ba alaman faraa a tare dashi,, kallo mubarak ya bishi dashi yana qoqarin sanja kaya alaman fita zeyi

"Jalal ina zaka? Ya tambayeshi,, be kulashi ba kawai ya fice



Kusan 1hr be dawo ba mubarak ya kirashi a waya yaqi dagawa shuru mubarak yayi yana nazari "toh ko kyautan ne ya bata ran jalal? Toh meye laifinshi dan yanason su kasan ce 'yan uwan juna"


Kwance yake kamar me bacci yaji shigowan jalal, ahankali ya bude idanunshi yana kallonshi yana qoqarin rage kayan jikinshi


"Jalal" ya kirashi ya juyo yana kallonshi "meyasa baka daga wayana ba? Shuru jalal be bashi amsa ba, tashi yayi ya nufi wurin da jalal din yake tsaye


"Nasan ba kowa yake jure hakan ba amma mami ta dauke kamar dan da ta haifa ni kuma haka nake jinka kamar wani bari na jikina sam banyi tunanin kyautar mami a wurinka zata sanya ka daina yimin magana amma kayi haquri ka karba saida ni inajin kunyar na maidawa mami kayan nace bazaka karba amma zan gaya mata ta kiyaye gaba"

Kallonshi kawai jalal yakeyi har ya qarasa zancenshi yaje ya dauki wayanshi ya fice


Kiran mami yayi a waya ta daga ya gaidata "befi 1hr ba da jalal ya kirani yana godiyan kayan nace kasa na qarajin godiya daga gareshi shine fa yayi shuru nace koda abinda yake buqata ne da sauri yace aa" ta qarasa maganan tana dariya "amma ai zaku samu week end kuzo Kaduna ko? Murmushi yayi "mami kinsan tunda na bashi kayan yake fushi na zata kayan ne suka bata mishi" dariya sukayi "toh kaida jalal din ne ai bazan shiga tsakaninku ba" haka sukayi sallama ya koma ciki


Kallonshi jalal yayi yanaso yayi dariya amma ya gimtse ya juya kawai yana matsala wayanshi, kusa dashi mubarak yaje "Allah bakada kirki jalal amma bari baji Allah bazan qara daukan miskilancinka ba saboda nine kawai kake yiwa" murmushi yayi yana qoqarin tashi "me kuma nayi? Tsaki mubarak yayi ya nemi wuri ya zauna "pls jalal ka rage wannan rashin maganar pls kaga fa ni dan uwanka ne dan Allah ka daina" kallonshi jalal yayi yana murmushi " mubarak bazan iya yawan magana yanda kake tunani" amma kakeyi da jalilah? Kawar da kanshi yayi yana murmushi ya tashi yayi shirin yin girki


Cool jalal kayi mana irin wannan jolof din da kayi ranar da mukayi csc,,, harara yayi mishi yaci gaba shirin girkinshi "sai fa kayi mana"


Girki yayi ya kammala "cool jalal ka dama mana kunu" tsaki jalal yayi ya Dora ruwan zafi ya cika flacks da ya ajiye mishi yaje yayi wanka ya dawo ya sami mubarak zaune ya cika plate da abinci ya cika cup da kunu sai faman ci yake,, ko kallonshi beyi ba ya shirya cikin irin kayanda suke jikin mubarak soaai mubarak yaji dadin hakan ya tashi suka fice


Kallonsu take har suka qaraso kusa da ita taji mubarak yace

"Cool jalal Allah dan kawai banayi ne amma kasan na cika iya girki........
[25/12, 13:21] Hassan Atk: 🤴🤴JININ SARAUTA 🤴🤴





*Written by Hafsat MN*





IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_





36-40






Tsayawa jalal yayi yana kallon mubarak yanaso yayi dariya "meye? Sai a lokacin yayi dariya kadan yaci gaba da tafiya


Kayi magana mana "no I don't hv anything to say" I know, mubarak ya fada tare dayin gaba abinshi


"Toh wai wannan waye? Anya sun taba haduwa ko?

Murmushi tayi ta tashi tabi bayansu,, sallama tayi mubarak ya amsa jalal kam ko juyowa beyiba yayi gaba abinshi " amm bawan Allah dakai nakeson muyi magana kuma ka tafi" juyowa yayi ya tsareta da ido ba tare da yayi magana ba

"Amm daman inaso nasan
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment