Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

18:15] Feedoh: ⚜ *BRILLIANT* *WRITERS* *ASSO* πŸ–Š






*XAMA* *DA* *KISHIYA* πŸ€¦β€β™€







*Story* ,,, *written*
*By* *feedoh*



*Dedicated* *_too*
*Brilliant* *asso*






πŸ…Ώ= *29*




Tun dasafe falmata Tah tashi tana gyaran gida farha taso tashi but tahanata tace takuma tayi bacci tahuta tass ta gyaran gidan sae kamshi mae dadi ketashi Koh wani lungu na gidan




Sae, 9 farha tafarka wanka tayi dogowar riga tasaka sae hulanta




Ah kitchen ta iske Anty ta bayan tagaesheta


Falmata ce takaleta badae wanka kikayi ma kanki bah baki jira nazo nayimiki dakaena



Kaii anty nafa iya yanzu fa nagirma yaci ace andae namin wanka



Tho fa auta zandaena tunda an girma
.



Humm antyna kenan me ake dafa muna



Kidae auta waenar flawa ce zanmuna sae ruwan Tea kobazaki ci ba



Zanci mana ae akwae dadi anty mae Sugar zakiyi Koh mae gishiri



Tho fa daman har kalla biyu NE tho wani kikeso


Mae Sugar nikeso


Tho angama autar anty

Kinga anjima sae inmuna dambu zakici



Ehh xanma ci dayawa but ba baba yaji zakimun ba Cux Koh mummy xata muna da miya takeyi but gidansu walida sukam da yaji sukeyi nikuma banaci yaji shiyasa kusunyi banaci





Tho fa karki damu bazan miki da yaji ba Kinji mae dadi zanmiki
Haka suke ta fira har tagama tuya waenar tafitoh dashi suka ci suka koshi




Sanan auta tace anty baci nikeji


Tho auta kije ki kwanta mana ae naga kinyi saurin tashi


Tho Anty sae anjima
Sae natashi


Tho ayi bacci lfy kar amanta ba ayi addu"ah ba



Tashi tayi tanufi kitchen around 10 ne dambun tafara shirin yi tace garan nayi yanzu insa nafuta nasan anjima fira kawae zamusha



Sanu sanu take aekinta har tagama ta gyara kitchen cikin kulla ta kwashe abinci takae dining


Falo tadawo taxauna tana mae futa gajiya har bacci yafara daukarta sae chan tajiyu salama kamar ah mafalki ae dasauri tamiqe tana ansa salama oyoyo sammy ashe dagaske zakizo



Uhmmm daman kizata wasa nike ne tho gashi din nazo


Ae Koh nafi kowa murna sanu daxuwa ya hanya kizauna mana



Sameera ce tazuna
Falmata ce tashiga kitchen juice da ruwa tadauko mata ah jug tire da cups


Sake gaesawa sukayi suna mae kewar junansu


Falmata ce tace ya Mijinki da yara


Lfy qalau suke yamace yana gaedaki


Ina ansawa
Lallai ma sameera kinsamu kwanciyar hankali jiyarda kikayi kibba kinyi fari infact ma harda kyau


Keeh falma bana son shairi abunda narame


Idanu falmata tazaro ahakan kika rame kice da kizamu madam kenan
.

Dariya suka kwashe dashi su duka




Sae chan sameera ta nisah tace falmata mike faruwa naga duk kin canza kamar ba keba duk danaga kina dariya nasan bae kae ciki ba duk wanda yaganki yasan kina cikin damuwa falma mike faruwa kika Mayar dakanki haka badae *zama* *da* *kishiya* ne tun yanzu yafara saki ah damuwa ba



Hmmmm sammy kenan zama da kishiya Koh jidali ae nikam ban mori xama da ita ba banhana nan gaba ba hawaye dake zubu mata tafara sharewa


Kusa da ita sameera tadawo hanunta takama. Tajata zuwa dakinta bisa gado suka zauna suna Kallon juna
Sammy tace plx falmata talk to me wat is going on


Nisawa tayi tace sammy zan fada miki komae kinji rayuwata nacikin wani hali narasa yazanyi dakaena xuciya ta zafi Koh ayaushe haka nikeji bazan rasa ciwon xuciya ba jifa duk yarda nakuma akan na Miji sae kace ba falmata ba



Nan ta kwashe labrin tun Randa aka kawo laurat gidan dayarda zaman su yakasance dazamanta da hajiya har xuwanta gida harta dawo da farha har kawowa yanzu da naseer yagujeta bae damu da cinta ba shanta ba bale lafiyata
Kuka mae tsuma rae tasaki duk wanda yaji yagani sae ya tausaya mata



Itama sammy din hawaye take tana mae mugun tausayin qawarta Koh ma tace yar uwata sae da tabari tagama kuka sanan takamu hanunta falmata gaskiya na tausaya miki nakuma yaba miki da jinjina miki irin kokarin dakikayi nadake xuciyarki kika yi hankuri *xama* *da* *kishiya* ahakan kuma fatana Allah yakara baki hankuri nasan wanan hankurin gobe xakici moriyansa



Falmata kiyi hankuri kinji dan Allah kidaena sa damuwa ah ranki kar kijama kanki wata lalura chan daban




Uhmmm sammy kenan


Aha abun mamaki wae duk wanan son da naseer ke miki za ace zae iya barinki bae damu dakeba gaskiya da sake



Hmmmm wani hawayen takaici tashare sameera shiyasa Koh naso nashiga damuwa sae Nayi tunani may be bayin kansa bane saboda nasan baqaramin aekinsu bane daga ita har uwarta da shedanu qawayenta
Nima nasan bayarda suka iya danine dasun sayaza suyi da tuni Sun fidani gidanan Koh Sun kasheni



Shiyasa sae wani lokaci bana ganin laefinsa akan abunda yakemin lura da lokaci guda ya canza



Hummm falma Kenan ke dakikayi wanan tunani Koh tho Allah yashige muna gaba kuma kidinga sa ah addu"ah Allah ya fitar dashi daga shairinsu
Dan nasan bazae wuce aekinsu ba



Uhmmm abun tsorona kar hankuri na yakare sammy xuciyata takusan bushewa



Uhmmm hakan ma bazae faru ba falma ke Mae hankuri ce hankurinki daga jini yake bazae iya canzawa ba hankurinki daban yake dana sauran mutane wallahi falmata nadade banga mae irin hankrinki ba tho koh ninan danike zaune wlh baxan iya yin hankurinki ba wlh da tuni nasan abunyi nakama gabana dan wlh bazan iyaba



Sammy kenan ke kikace nikam hankuri yazamu dole gareni ya zamto abincina Koh dayaushe




Falmata sae yanxu natabatar da *zama* *da* *kishiya* darasi ne,, da mutum xae koya dayawa


Nawa *zama* *da* *kishiya* ya banbata da nike sosae kowa haka zalika wasu na chan suna fama danasu zaman



Uhmmm sammy kenan Allah dae ya kyauta


Ameen falmata


But falmata in tambayeki mana


Inajinki sammy


Sae nike ganin Kamar cikine gareki


Ciki kuma haba ciki ah ina


Ah jikinki mana yanaga kinji tsoro ga kuma alamu Sun bayana ah jikinki



Mstwee nifa bawani ciki dake gareni Koh mummy haka tace nikam na ce mata banda komae



Tho inbada abunkii miye na boyu da bacen rain abunda yakamata kiyi murna kigodewa allah
Tho inda kince bakida yaushe rabonki dakiga period


Kusan, 3 to 4 month






*Feedoh* πŸ–Š
[9/3, 18:15] Feedoh: ⚜ *BRILLIANT* *WRITERS* *ASSO* πŸ–Š




*XAMA* *DA* *KISHIYA* πŸ€¦β€β™€






*Story* ,,, *written*
*By* *feedoh*



*Dedicated* *too*
*Brlliant* *asso*






πŸ…Ώ= *30*




Mstweee aman dae falma kin raena wayon mutane shine har kinada Karfin halin bude baki kice bakida ciki



Uhmmm wae dan na cemiki banga period ina ba na for some months shine xaki ce inada ciki
Halan kinmanta Koh ah ckul nakan kai irin wanan lokaci bangani ba har kudinga cewa banida lafiya inje asibiti adubani kwanciyarta ta gyara taciga da cewa shiyasa. Koh yanxu abun baeda meni ba kuma faruwan haka bazae sa nace ciki ne dani ba




Hummm falma kenan ae koh yanxu bakida lafiya kije asibiti adubaki narashin period inki akai akai Inkuma cikine musani



Dukan wasa falmata takae mata tunda ke kikamin shi ae dashine danafi kowa farinciki kodayake fa kesan ace masuyin iirin period ina ance suna dadewa basu haehu ba Koh kuma baza su haehu dayawa ba bazae wuce su haefa yara 1 xuwa 3 kodayake Allah masani



Shikam dae za ace Allah yazabamuna mafi alkhairi


Ameen ya rabbi tashi muyi sallah sae muci abinci koh



Tho limamiya kice har yanzu Hali bae canza ba yin sallah kafin liman yagama


Tho ae buqatar kirra akesonji bawae jiran sae yagama ba


Tho nidae jikeyi inajiranki



Mstwee aekaji irinta
Alwala falmata tayo sallah ta tagamayi azkar inta takeyin yanda tasaba


Chan tajiyu sameera nacewa dan Allah malama mutum fa ke jiranki nikam yunwa nikeji



Sae da tagama abunta sanan tamiqe tace basan mutun dole yajirani ba yunwa kuma Aekinsan kitchen



Atare suka fita fallo suka nufa falma ce tace wanan baccin na auta lafiya kowa barin intasheta hakanan
Sammy ce tana ina halan wlh yau dakin goga tashige wae anan xatayi bacci



Tho fa kice yau ita keda miji kenan



Kedae kika sani



Dakin tanufa sallah ta isko tanayi Allah sarki tace saman gado tazauna tajirata har Tagama sallah



Juyowa tayi tace anty ina wuni



Lafiya qalau auta yau Kinsha bacci kodae bakida lafiyane


Lafiyata qalau anty



Tho tashi muje hanunta takama suka nufi fallo
Jeki gurin anty ki kugaesa kinji
Tho



Gurin falmata tanufa anty ina Wuni


Lafiya qlw farha yakika baro mummy


Lafiya qalau take
Yauwa



Falmata ce tace rankiyadade ku taso muci abinci Koh anan zankawo
Uhmmm bari mu futar dake gamo zuwa muci anan hanun farha taja sutafi




Farha ce tace a ah ni anty anan zanci banason ci achan kafafu na basu kaewa kan kujera kuma dae bani walawa sosae
Dariya su duka sukasa falmata ce tadauko kayan abinci takawo gurinsu ah plate tasaka musu itada Sammy sanan tasaka ma farha anata plate tasaka mata stew



Sammy ce tace ba jellop kikayi ba naga kinsa mata stew
Ehh auta anty ce fa da stew tace takeso kega dole namata yanda takeso



Auta wanan xae isheki Ehh Anty indan bakoshi ba sae akara tho,,,, tashi auta tayi xata tafi daki sae sammy tace inazuwa farha anty daki xanje a ah kidawo kizauna mana




Kyaleta kawae auta yi tafiyarki jeki dauko lemo muma kidauko muna kinji
Tho Anty
Abincinta taje tadauko musu lemon ah gaban su ta aje sanan tadauki nata tawuce



Gaskiya training inki yana burgeni falma sister Kince fa inaga yaranki wlh harnaji taburgeni tanada hankali



Sammy kenan muci abinci kar ya hucce



Tho wlh abincinan yamin dadi ina ace nina iya abinci nan da kullum sae alhaji yabani kyauta



Ke banason shairi wlh ina dadin da abinci yayi


Hunmn falma kenan
Aha falma kinko karbo results dinki na ckul Ehh nakarbo tuntuni ya akayi halan



Daman alhaji yasamu qarin girma ne tahanyar sa ake daukar aeki ta jahar dinan
Wow natayaku murna Allah yasanya alkhairi


Ameen yarabi
Tho shine nikeson kikawo takadunki intafi dasu asamu miki aeki Koh nan gvmt. School dake shiyar ku



A ah Karma kifara sameera taya Zanfara aeki batare da sanin mijina bazaeyu ba



Matsalata dake kenan da anyi magana kice miji tho ina mijin yake wanda baedamu dake ba baruwansa dake kefa danzu da bakinki kike fadamin cewa abincinku yakare da babu kudin da yaya fahad yabaki da bakisan yazakiyi ba shine yanzu ina miki magana aeki kina min wanan zance tho miye amfanin karatunki kisani fa da kinsamu aekinan albashi xaki dinga karba kudi nashigo miki kidinga biyama kanki bukata basae kin tsaya jiran anmiki ba kihuce ma kanki takaici nidae inabaki shawara wlh ki tsaya ki nutsu kifita harka tunani naseer kiyi abunda xae fisheki nidae tawa shawara kinga tafiyata ga alhaji nakirana nasan ya iso barin intafi





Tho sammy nagode duk shawara dana yanke xakiji bari naraka ki Koh
Auta kifito anty ki zata wuce

Tho gani xuwa



Fita sukayi gurin motarsa sukaje gaeda shi falmata tayi tamasa ya kwana 2 dakuma aeki


Alhmdullah,,,yamae gidan yana lafiya lafiya qalau yake
Tho ah gaedashi

Insha Allah xaeji


Farha ce tafitoh tagaeda shi da fara"Ansa ya ansa Baby girl yasunanki


Farha sunana


Yauwa farha yakike
Lafiya qalau


Motar sa yabude yaciro kudi yabama farha yace gashi kisha sweet Koh

A ah nagode bazan karba ba juyin duniya yayi taki karba sae dayace dan Allah falmata tamata magana takarba sanan fa takarba tamasa godiya sosae.



Sosae yaji dadin yarda farha tayi yanason yara hakanan



Salama suka musu suka shiga mota harsun shiga sammy tace



Aha Plx falmata inkin yake shawara kisanar dani dawuri kinji



Ok insha Allah sammy
Allah ya kiyaye yakaeku lfy



Ameen







*Feedoh* πŸ–Š
[9/3, 18:15] Feedoh: ⚜ *BRILLIANT* *WRITERS* *ASSO* πŸ–Š






*XAMA* *DA* *KISHIYA* πŸ€¦β€β™€






*Story* ,,, *written*
*By* *feedoh*



*Dedicated* *too*
*Brilliant* *asso*






πŸ…Ώ= *31*






Bayan kwana 2 anty amina ce tazo ita da yaranta gidan falmata ziyara sosae taji dadin ganinsu hardae farha datasamu yara yan uwanta wasan su sukeyi



Anty ce da falmata suka wuce daki suna tautaunawa anty dae naqara bata hnkr sae chan falmata kecewa aha anty sameera qawata tace zatamin hanya gurin mijinta nasamu aeki but nikam nace a ah sae Nayi shawara taya xanfara aeki batare da sanin mijina ba




Kaicona amina wae nikam falmata wani irin sone kikema Naseer haka komae kice shi



Tho tsaya kiji inkice sae kintabayii ixini nasir tho ah ina zakigansa yaushe rabon dakiganshi ah idanu ki dan haka wlh kidauki aekina ki rike dan shine Jindadi ki Miye amfanin karatunki ba ae Koh shi nasir yau yaji ance kinsamu aeki dadinshi ne dan haka kidau waya ki kirata kice kiyanke shawara kinaso aekin fada sosae anty keyi dakarshe tace ba wallah naserr ba naserah




Sosae fada anty yabawa falmata dariya
Auw dariya nabaki Koh


A ah nidae bance ba anty

Wayanta tadauka takira Sammy bayan sugaesa tace Sammy batun aekinan inaso xanyi




Wow harnaji dadi wlh falma kin kwantar da hnklinki aekin kam kamar kinsamu alhaji nadawowa zanmasa bayani gobe zan aeko driver yakarbi credentials inki




Tho tawa nagode
Sallama sukayi ma juna




Anty ce takaleta koh kefa Murmushi tamata firansu suka cigaba dayi sae da yamma su anty suka tafi




Sammy tama mijinta bayani kuma ya yarda but yace gaskiya fita aeki bada izini mijinta baeyi ba but zan asamu mata na LGA ah bangaren health kinga zata samu albishi Mae yawa

Tho ae hakama yayi alhaji mungode sosae waya takira tama falmata bayani sosae taji dadi hardae dataji aekin bana fita bane ta aeko ankarbi takardun falmata abunka da harka Manya cikin sati guda akabawa falmata offer




Haka kwanaki nata tafiya karshen wata saega alert yashigoma ah waya na albashinta 50k murna mara misaltawa takeyi nantake takira sammy tamata godiya sosae itama jindadi sammy takeyi qawarta na cikin farin ciki nuna mata tayi bakomae sae anjima sukayi ma juna




Anty amina takira tamata albishir
Sosae anty amina tayi murna




Tashi tayi tashiga kitchen taga sunada sauran abinci



Fallo takuma ta iske auta kusa da ita tazauna tace auta kallo kikeyi
Ehh Anty



Auta albishirinki gobe kishirya xankaeki school kinji
Yeeeeh anty najji dadi Allah yakaemu

Ameen auta




Washe gari suka shirya itada auta wata privet ckull dake shiyarsu sukaje akasa dan ba nisa tace tunda ba abun hawa gareta ba Koh akafa kullun auta zata iya zuwa suntafi takaeta akamata interview sosae suka yaba da iri kokarin auta JSS1 sukace zasu ajeta school fees tabiya dakomae daya kamata tayi nan Take suka bata uniform da dae sauran school items sukace monday tafara zuwa tunda yau yakasance Friday short day


---------------------+----------
Ah kwana atashi ba wuya cikin Laurat yakae 9 month haehuwa yau Koh gobe




Falmata ce yanxu hankalinta ah kwance tarage sama kanta damuwa tabama Allah komae

Yanzu sae abunda tagadama ci Koh sha daga ita sae farha duk su canza suyi kyau abunsu hardae falmata tayi wani haske ga kibar datayi Masha Allah komae nata fresh



Bata dawani aeki sae girka musu abinci wani sa"in ma sau daya takeyi tarzace itakam farha daga boko tana dawowa ba hutawa tawuce islamiya itada da hutawa sae dare sosae takejin dadin zama da anty ta





Yau yakama alhamis tun safe laurat ta tashi da nakuda aka wuce da ita asibiti sae guraren 12 tasauka Koh shi sae da akamata CS
Tasamu yarta fara tasss da ita Masha Allah dae zae ace




haka duka dagi keta murna hardae hajiya da naseer baki har kune yakasa rufuwa Naseer kefadin alhmdillah yau Allah yanuna Min yarta ta cikina Allah yara yaki
Sae zuwa Safe aka salamesu su suka kuma gida sosae akebawa laurat kulawa kamar wata princess kayan barka su hajiya suka shirya kudin naseer yasha. Kashi




Falmata kam batasan miyar da suke Shaa ba
Sae ana jibi suna
Suna zaune itada farha suna kallo sae chan Farha tace aha Anty natuna yau ah makaranta ance mudinga sauraron News Koh zamu dinga karuwa hardae zuwa SS wae zamu farayin News ah assembly ground



Tho Masha Allah Tho yi maza ki canza chanel kinji nima kozan karo koda suka saka angama news in turanci na hausa akeyi
Tho auta kinga angama na turanci nahausa akeyi but Bari mubarshi koshi zamu karu
Tho anty




Sae chan sukaji anafadin ana mae gayantar ilahirin mutane gurin zane suna ran alhamis 9 nasafe ah masalaci juma'ah dake GRA,,, Birnin/kebbi

Nah Naseer aminu fakku da uwar diyarsa laurat A musa



Hotunansu aka nuno atare sae jariryar Baby dake rungume da laurat baqaramin kyau sukayi ba duk wanda yagani sae yaji Sun burgesu



Gaban falmata yafadi dumm dummm laurat tahaefu jibbi suna tabdi shine Koh akirani afadamin kodaya ke ina naga wanan matsayi hummmm Allah yaraya muku ayi bikin suna lafiya



Auta ce tace anty kina magana ne


A ah auta bacci ma nikeji kashe kayan chan muje mu kwanta


Tho Anty kayan takashe daki suka nufa sukayi shirin bacci



Gari yawaye but duk yarda tayi tacire damuwa takasa tana tunani harwani laefi tama Naseer da abun farin ciki yasamesa but Koh yakira yafada mata sae dae tajji Allah sarki rayuwa kenan



Hawaye yazubu mata Yah Allah kabani nawa nafuta da kurri da gorri
Farha ce tazo kusa tace lafiya Anty kike kuka waya tabaki Koh yaya naseer ne kidaena kuka kinji kiyi hankuri anty



Hawayen fuskarta ta goge shikenan auta nadaena kinji Murmushi tamata tace tashi muje kibiya harda ki inji inki iya iyaso anjima sae muyi home work dinki



Tho Anty mutafi
Haka sukaje falo suka zauna suna karatun atare




Bayan sungama ne falmata kicewa auta yau meza muci da dare.


Uhmmm muganiπŸ€”kimuna cikaka
Cikaka fa auta dariya falmata keyi sosae nikam ban iyaba bazan miki ba



Nikam anty kimin dan Allah bayada wuya mummy fa namin garin towo fa kawae xa kwaba aruwa sae toyawa



Ah Tho inbaya da wuya basae kije kiyi ba nikam yau kinjawo min aeki miqomin wayata nakira mummy in tambayenta dan gaskiya na Manta yanda akeyinsa




Wayar tamiqomata mummy takira bayan Sun gaesa take cewa Plx mammy ya akeyin cikaka (masan dutse)




Laaah nashigesu falmata ynx masan dutse kika Manta yanda akeyinshi ae Kinga ranata yau lokacin inda nace ku tsaya Koh kuyi abincin gargajiya yanada amfani sae kuga kamar bana sonko ae gashi yau




Dan Allah kiyi hankuri mummy wlh diyarki ce wae yau shi zamuci


Tho fa kinci albarkaci auta daba zan fada miki ba sae dae kikoya dakanki kuci kwabinku takarashe maganan tana dariya
Itama falmata dariya takeyi tace tho nagode mummy tunda zaki fadamin



Bude kunanyeki da kyau kiji.

Nabude mammy

*MASA* *DUTSE*
Xaki tankade garin dawanki Koh masara irin na towo ki kwaba sa daruwa tare da kukarki kadan kanwa kadan dan gishiri kadan sae albasa kuma zaki iyasa ataruhu inda kina ra"ayi
Zaki iya amfani da murhun Ice Koh na chacool kiyi amfani da marfin tukunya ta sanfara kixuba sae yayi sanan kisake juyawa kamar dae yanda xakiyi masa but kinayi kina shafa ruwa bazaki saka maii ba sae kingama
But yanxu daya kasance kundaena amfani da morhun itace sae na electric tho sae kiyi amfani da frying pand kiyi yanda nace bazaki sa maii ba sae kingama kintanada yajinki sae kibbi kishashafa bisa Koh kihade yajin da maii Kuna dangalawa Kuna ci ra"ayine




Hummm tho nagode mummy yanzu kuwa zanyi sae na aeko miki kema kici
Uhmmm nidae bani diyata mugaesa haka tabawa farha waya suka gaesa da mummy bayan sungaesa sukayi sae anjima




Kitchen suka nufa gabadae su aekita farayi cikin nutsuwa yanda mummy tace tayi,,,, daqet tasamu kingi garin masara dashi xatayi amfani




Sae around 6 suka gama wanka sukaje sukayi sae da suka gama salolinsu sanan suka fito fallo danci abinci



Abinci sukeci farha tace Wow anty yafayi dadi yafi wanda mummy kemuna gaskiya ke iya girki anty na




Auta na kenan ae kema xaki iya kinji



Tho anty


Yau ba batun kallo muje daki muyi Home work inki damun gama sae bacci Koh



Tho Anty

.
Suna gamawa suka wuce daki bayan H/W din sukayi shirin bacci




Asuba tagari yau takama alhamis tunda safe ta tashi duk da batajin dadi jikinta koda 10 tayi tagama komae fallo take xaune tana maejin kewar Farha ta matsu sudawo makaranta kozata sha labari balle yau babu islamiya





Har bacci yafara daukarta sae chan taji qara wayarta kamar karta tashi sae kawae Tah tashi



Gabanta yabada wani dummm dumm gani mae kiranta har kiran farko ya katse bata gama tunani ba tasake jin qara wayar


Still naseer ke kiranta...





*Feedoh* πŸ–Š
[9/3, 18:15] Feedoh: ⚜ *BRILLIANT* *WRITERS* *ASSO* πŸ–Š






*XAMA* *DA* *KISHIYA* πŸ€¦β€β™€





*Story* ,,, *written*
*By* *feedoh*



*Dedicated* *too*
*Brilliant* *asso*






πŸ…Ώ= *32*




Gabanta nafaduwa tadau wayar cikin sanyi murya tayi salama
Iyaxubillah abunda kunayenta najiyu
Da masifa yake magana ke my soul tahaehu yau suna kizo kuma yanxunan Koh aeki ne kya yi



Najji kawae tace takashe Waya




Wae kee anhaehu karkice banfada miki ba tho nah nawa mstwee dama baka fada ba


Wae my soul a ah ruhi dae mstww aekin banza bama inda zani balle kuyi tunani harna muku aeki
Wuri tasamu tayi zamanta ,,,,,sae kuma chan tayi wani nazari cewa yanzu kuma dazaran bataje ba za ace ina bakin cikine akan ni ban haehu ba hunmn mutane kenan




Jira tayi har farha tadawo sae su shirya su taffi
Farha ce tadawo bayan tahuta taci abinci tayi sallah sanan suka fara shirin tafiya cikin dogowar riga ta yan kanti ta shirya farha tayi kyau sosae sae dan qaramin hijjab da tasakamata
Itama cikin riga da zani na atamfa tashirya sae baban mayafinta tasaka kamshin tulare sukeyi duka




Fitowa sukayi suka kulle Koh ina sanan suka fita daedae kofar gidan mae napep ya ajesu gate tabude suka shiga hayanayi kawae kakeji yana tashi kofar Main fallo tashiga da salamata


Wasu suka ansa wasu kuma basu masan tayi ba
Gaeshesu tayi cikin ladabi tana mae cewa ashe ansamu qaruwa Allah yasa tho musulmi aka samu bata kai da rufe baki ba tajiyu murya hajiya nacewa Tho munafuka yar bakin ciki so kike asamu kafiri irinki koh



Aenan hankalin mutane gurin sukadawo gurinsu nibanmasan uban daya kawoki ba tundanzu akayi kiranki kizo aman dan kinraena wayon mutane sae yanzu nibanmsan meyasa aka fada miki ba mafarin kizo kicanye min jikka dawanan shegun mayun idanunki



Hajiya laurat ce tasauko a ah hajiya yanikejin hayaniya halan keda su waye ne



Humm kedae bari hajiya nida banzar yariyarnan ce bansan uban me tazoyi ba



Auw badae wanan ce matar naseer ba


Ehh itace daman bakisanta ba
Ehh Bawani santa ba sosae



Tho gatanan Mae kama da mayyu
Lalaikam aeta mafisu tho ga wuri chan sae tazauna kesan wulakanta bako ba kyau



Yan mata ga guri chan kizauna



Murmushi yaqe falmata tayi tace nagode


Hanun farha taja sukaje suka zauna kowa sae binsu da ido yakeyi abinci aka kawo musu but kallon farha kawae Tayi
Farha kuma tasan me haka ke nufi




Xaune suke saega uwar jego tafitoh cikin wata dankareriyar shada sosae tayi kyau sae gwala gwale dake yawo ah jikinta sae wani kyali takeyi kallo yakuma kanta kowa da albarkaci bakinsa yake fada



Zarah ce bayanta itama cikin shiga ta alfarma itace dauke da jaririyar




Suna saukowa kalonta tamaeda kan falmata a ah yaushe kikazo

Tundazu

Tho shine baki shigo ciki ba Koh bakin ciki ne yahanaki zuwa



Uhmmm laurat kenan muga Baby


Wahh Allah ya tsereni nabaki diyata kishafa mata bakin jini irin naki yanxu ae dakin dauketa ae kota girma shikenan haka za akorata gidan miji bata haehuwa tunda kin dauketa kinsamata bakin tambo




Murmushi tayi ohk shikenan yasunanta



Sunanta nadeeyah yan mata adon gari



Allah sarki suna mae dadi Allah yaraya ta




Ameen inda gaske kike




Uhmmm gawanan ae saya mata pampers
A ah mungode ae ba ace miki tarasa komae ba



Gurin zama Koh wacensu tasamu tazauna



Auta ce kicewa anty kitashi mukuma gidan mu tunda wanan gida ba asonmu suna cikin magana da farha sae ta jiyu su hajiya na magana hajiya laurat ce tace hajiya yarinyar chan kamar mae ciki duk jikinta ya canza duk wata alama ta ciki yanuna gareta
Hajiya Nasser tace haba hajiya ciki nayaushe da tanada rabonyi datayi ae



Wata tsohowa datake geffenan tace haba hajiya har kun bani kunya

Please Login or Register in order to submit comment