Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


WACE CE ITA MARUBUCIYA HAUWA
M.JABO
By Hauwa jabo 15:44 3 comments
[3:43AM, 4/25/2015] .: WAC CE ITA..?? 1 1⃣
Na Hauwa M. Jabo
Kiyi sauri ki sauko maigadi ya kusa zuwafa,
Daga saman icen wata siriyiyar yarinya kamar
bulala da qarfi tace mangoro nawa na tsinko?
Daga gefen wata yar lukutar yarinya tace guda 8
ne Amma uku basu nunaba. Yarinyar da take
saman ice tace yauwa.. haka naga ta diro
kaman biri daga saman iccen ni jabo da naje
gano muke WACE CE ITA? saida na firgita mace
haka ba tsoro na kalli bishiyar naga tsawonta
abinda yafi bani mamaki ya akayi ta hau bishiyar
ba tsani.? Kamin in waigo sai kawai na hangota
saman dayan bishiyar har ta Dane bishiyar, ta
fara tsunko gwaiba tana wurgowa qasa
qawayenta suna cabewa, da gani wayannan
yaran taqdiraine waima ya take hawan bishiyar
ba tsani?? Yau sai na kakkaryaku Dan
ubanninku! Matsiyata..!! Muryar wani dan tsoho
naji da alama shine mai gadin wurin Iffatu sauko
baba shehu.!! baba Shehu!! Haka suke fada
suna ihu, Timmm naji Abu siririyar yarinyar ta
fado na tsorata Dan na dauka ta karye Amma
inaaaa tana fadowa qasa ta dauki dayar gwaibar
ta basu daukaba ta filfila har ta wucesu koda ta
iso bakin qofar gonar taga baba Shehu ya kulle
qofa tashin hankali..... Kunsan baba Shehu ya
kulle qofa dole zamu tsallaka ne kamin yazo,
tana fada jikinsu na rawa, ke dijee kulllum ke
kike bamu matsala wallahi bazaki qara biyomuba
gashi ke baki iya gudu sabida shegun duwawun
nan naki. Mtswwww... Kuzo mubi ta chan ginin
yafi gajarta. Suka kwasa a guje suka samu suka
tsallakar da dije da yake ita rukayya irin ippatu
CE ba auki da kanta ta tsallaka duk da haka sai
da iffatu ta taimakamata. Juyowan da ippatu
zatayo ta hango baba shehu da gudunsa ya
kusa kawowa gurinta, ya wurgo mata sandarshi
amma bai sametaba, da yake gurgune sai ta
yanka a guje kamar fanka fil fil da ita, gurin ginin
yafi tsawo dama, na yanda ta iya baba Shehu
zai iya kamata, tana nisa dashi,taja baya sosai
tazo a guje sai kawai ta dane ginin saida ta hau
ta waigo tayiwa baba shehu gwalooo sannan ta
dira a qasa......
WACE CE ITA..?? 22⃣
Na Hauwa M. Jabo
Tana dirowq dijee rukayya kozo nan ta basu
umurni. Sukazo ina mangurona da gwaibata ?
Taki ko tamu inji dijee, ta wani harereta itama
dijee ta harereta ta jajayen idonta gasu qanana
itadai rukayya batace dasu komaiba tayi tsaye
dama sune hatsabiban dije da ippatu.
Ippatu ta rufe ido cikin tsiwa, abani kayana
kamin in lissafa uku. Ta fara lissafi daya biyu
uku itadai rukayya ta miqaa mata kayanta dijee
ko ta sakasu a Dan kwali ta gulle taci damara
da Dan kwalin. Bude idon ippatu ta kwashe dije
da mari dama sun saba. Suka fara danbe aka
tima dije a qasa dama batada qarfi sai rashin
kunya, dagyar rukayya ta rabasu Amma duk
manguron da gwaibar sun turmuje a qasa sai
guda biyu da gwaiba hudu suka rage. Ko
wannen su na fitarda numfashi daddaya. Amma
fa dije anji ji jiki kusan kullum sai sunyi dambe
da dijee Dan dukansu basuda kunya kuma
basuda haqurin juna gashi basu iya rabuwa da
juna.! Gamon jini da hali ita rukayya batada fada
biye take dasu kamar raqumi da akala duk yanda
akayi da ita chan takeyi. Ippatu ta baiwa
rukayya mangoro daya gwaiba daya ta riqe
mangoro daya gwaiba uku kaji adalci irin na
ippatu dije kuwa tahau tsini Dan bata bata
komaiba. Ta daure fuska muninta ya qara fitowa,
Sunkama hanya ana gaba da juna kowacce tabi
hanyarta ippatu na tafe tana shan magoro da
gwaibarta, Bala'eeeee wallahi ga bello mai kifi
chan, inji rukayya, Habawa baima hangosuba
Amma tuni sun yanki ticket suka fara gudu ba
tsayawa basu tsayaba saida suka daina
hangoshi suka fara dariya. Kamar basune sukayi
danbeba har sun shirya. Ippatu tana dariya tace
dijee kin tuna faduwar da bello mai kifi yayi suka
qara kwashewa da dariya suka tafa ai ranar
saida ya bani tausayi habadai, wallahi baibani
tausayiba kifinsa bala'en tsada sai shegen dadi
inji dijee, Dan yaga ana saye yake yiwa mutane
yanga. Shegiyarda sukamai saida ya qare suyar
kifi ya jera akan tire zaije talla kawai sukayo
tsokana aka biyosu suka zo a guje suka barar
mai da kifi kuma sukabi takai suka wuce ko
waigowa basuyiba shiko bello mai kifi dan jaraba
maimakon ya tsaya kwashe Dan kifinsa sai
kawai ya biyosu a guje, garin binsu ya fadi a
qasa ya huge bakinsa, sukam tuni suka bace
mai ko mai lafiya baya iya kamasu idan suna
gudu bare bello mai kifi daya tsufa. Dan ko dijee
bai mangalar duwawu idan ta saki qafa ba dama
bare rukayya mai kamar bulala, Nidai Jabo
bantaba ganin gyauyawa kuma Yan iskan yara,
marasa kunya ga tsokana da rashin tsoro irin
wayannan yaranba dije da ippatu ba, Dan ita
rukayya yar kallo ce sai zugasu da takeyi idan
sun samo su sammata ko ta musu gadi suyi
abinda zasuyi.
Suna dariya suna tafawa abinsu har suka iso
gida sai lokacin ippatu ta tuna da aikenta akayi
sayen daddawa da manja, ko shakka babu ta
xubar da kudin, ta kwance Dan kwalinta data
daure kudin amma ina tuni sun fadi, zakuwa
tashi qaniyarta idan ta koma ba daddawar nan
da manja ga uban shiririritan da tayi..
Maimakon ta shiga gida sai kawai ta kama
hanya tana tafe tana tunanin yanda zatayi da
saqon googo, kicibis taci karo da wasu yara
suna fada ta tsaya kallo suma aikensu akayi sai
taga sun yarda kidi naira ashirin da biyar ta
dauke ta qulle a habar zaninta. Yau wace rana
ippatu taga fada bata tsaya sayen fadanba da
walakin. Taje ta siyo manjanta na goma
daddawan biyar ta siyo kan kifi na biyar tana
tafe tanaci har taje ta dawo suna fada fadan
yanzu kuma na an sace kudin dayane ta
kyalkyale da dariya iron ta mugunta ta wuce
abinta.....
WACE CE ITA..?? 3 3⃣
Na Hauwa M. Jabo.
Ta wuce abinta koda taje gida ta rasa yanda
zatayi ta shiga Gidan ta fara labe labe. Ubanme
kikeyi anan ??muryar babanta taji ya mata
tsawa saida hanjin cikinta suka juya duk duniya
babanta kawai take tsoro ta fara kame kame,
bakomai baba sannu da zuwa. To wuce gida
munafukar banza ya tasa qeyarta suka shiga.
Malam ina ka tsintomin ippatu? wallahi tun
qarfe biyu na aiketa Dan nasan halinta
batadawoba sai yanxu, kaga har na qare tuwo!
Dan ubanki ina kikaje? Ta fashe da kuka wallahi
baba sai bayan la'asar ta aikeni ko minti uku
banyiba na dawo. LA ilaha illallahu Muhammadu
rasulillahi... Ihhatu "haka take kiranta Dan bata
iya sunan ba" kina nufin qarya zan miki? Kinma
saba bani kayana ta qwace manjanta da
daddawarta, baba ya juyo ya kalleta ina kika
samu kifi sai qarnin kifi kikeyi. Ta fuske kamar
gaske gidan su kulu mai daddawa suka
sammini.! Na dauka kin qara tsokano bello mai
kifine. Aah wallahi baba.!! Idan ta tashi zama ta
Allah sai ki rantse da Allah ba ita bace take
taqdiranci a hanyaba kamar wata waliyiya har
ma dai gaban babanta.....
*********************
Ippatu yarinyace yar kimanin shekara 11 duk
yanda zan muku bayanin ta idan dai ba ta muku
taqdiranci nata kungani da idonkuba ba zaku
gane WACE CE ITA ba, Sabida batada kunya,
batada tsoro ba tada ladabi ba tada mantuwa ba
yafiya haka take wata hargitsatsiyar yarinya da
ita. Gata qazama taqin qarawa, batasan
tsabtaba ko kadan haka batasan wankaba bare
wanki farace Amma yanxu tafi zainb khalifa baqi,
haqoranta Dan rashin wankewa har sunyi tsatsa
daga sama, daga qasa kuwa kamar an kwaba
laka an shafa mata idonta kuwa gasu Manya
Manya Amma sunyi jaa kamar na sister khade
qafar nan kuwa duk tayi wani iri Allah ne ya
tsareta qafar bata Faso da tuni ta farfashe Dan
su dijee tuni qafafunsu sun yayyage da Faso,
bata yawo da takalmi, a cewarta takalmi basa
barinta gudu. Mahaifiyarta sun rabu da
mahaifinta tun tanada shekara 6 tanada yayye
guda biyu maza duk mamansu daya, suna gurin
mamansu, itama babansu yaje gun mamar ne
akan dai ta bashi yayanshi, ta hana, dazai dawo
ippatu ta maqalemasa ya dauketa ba da son ran
mamarba, tana zaune gun kishiyar mamanta
gwagwo rabi, gwagwo batason ippatu ko kadan
ita kuwa ippatu ba abinda ya dameta harkar
gabanta take bata damu da asotaba kuma
gwagwo rabi duk abinda zata mata saita rama
cox bata mantuwa bata yafiya.! Shiyasa
hankalinta kwance bata tsoron kowa duk
qauyensu sai babanta kuma bata ragawa kowa
duk qauyen nan. An sakata makarantar boko har
uku ana korota sabida uban yara da takeci, a
makarantar allo ma Dan yana maqocinsune da
tini ya korota ippatu kenan....
WACE CE ITA..?? 4 4⃣
Na Hauwa M. Jabo
************
Ta dauki allo na tafi makaranta, gwaggo ko
kallonta batayiba Dan tasan ba makaranta
zatajeba wacce batason makaranta zata fita tun
qarfe biyu, za'a gurin jarabadai, allonta har
rubutun ya goge dan tsabar rashin zuwa
makaranta da takeyi tana fita taje bayan qyaure
ta boye allon ta sa mai bata tsayaba sai gidan
su dijee da yake dijee da rukayya gida daya suke
dagyar suka samu suka sulalo suka fito. Suna
tafe suna tadi duk yaran garin har Manya
tsoronsu suke dan basu bar kowaba, idan
babbane ya daki daya taron dangi sukemai ko
suyita jifarsa da duwatsu, basu tsaya ko inaba
sai rafi suna zuwa suka tube dagasu sai qajeren
wando rukayya dai ta fara girgar dangi dija ma
ya kunmo kai Amma basu kunyar kowa suka
fada ruwa sukayi iyo sosai kaman kifaye sun iya
ruwa kaman me suna ruwa suka hango baba
shehu mai gadi shima ya hangosu sunsan kamin
su fito ya iso sai dijee tace kar mu gudu idan
yashigo kamamu mu bashi ruwa mu danneshi a
ruwa.! Sun haqamai gadan zare, Baba shehu
dayazo sai yaqi shiga kaman yasan abinda suka
fada, ya kame guri daya kamar bai gansuba,
sukayi jira har suka gaji Amma yaqi tafiya sai
kawai suka yi shawara akan su nutse su tafi
chan nesa dashi su fito. Suka nutse a ruwa,
baka ganin tafiyarsu, saida sukayi tafiya mai
nisa sannan suka fito suka lallabo suka zagayo
suka saka tufafin su suka nufi gona satar
mangoro shiko baba shehu yanachan yana jiran
fitowarsu daga nutsewar da sukayi yaji shiru sai
abin ya bashi tsoro kardai ya kashe yayan
mutane!!! Tuni ya fada ruwan ya shiga lalube
Amma basu ba labarin su chan ya hangosu suna
gudu sun ciko zaninsu da mangoro da gwaiba
yau hadda lemu da basu cika diva ba sun debo.
Tsoro ya kama baba maigadi daganan baba
shehu mai gadi ya sallama cewa ba mutane
bane aljanun dajine ko Yan ruwa suke
addabarshi, dole ya nemo tsari karsu hallakashi.
Da sauri ya fito ruwan saida sukaxo Dan kusa
dashi suka kwashe da dariya sannan suka mai
gwalo suka gudu. Kaji hatsabibai....
*****
Tun daga ranar baba maigadi bai qara binsuba,
hasali ko kallonsu baiyayi idan suna abinsu, da
suka gane ya saka musu Idone sai suka maida
abin Sana'a kullum zasuje su debo sai suje su
wanke suje talla da sukaga basa ciniki sabida
baqin halinsu sai suka riqa daurawa rukayya
tallar rukayya kuwa akwai farin jinin talla, talla
ta karbeta nan danan suke saidawa gurin rabon
kudi suyita bala'e da danbe. Ba ranar da basa
fada kuma aranar suke shiryawa,.....
[4:50PM, 4/26/2015] .: CHI GABA....
WACE CE ITA..?? 5
Na Hauwa M. Jabo
********************
Yauma kamar kullum yan matan uku dije ippatu
da rukayya suna tafe suna labari suna shewa da
dariya da gani dai kasan basu da kamun kai
bare uwa uba tarbiya, laaaaaaaa dije kalli
malan garba da ya dakemu ranar.! suka waiga
gaba dayansu suka kalleshi, ippatu tayi tsaki
share shi mugun banza, dijee ta kalli ippatu
bazamu share shi ba,yakamata mu rama, mi
zamu masa mu rama kalli fa har yanxu tabon
bulalanshi, ta nuna hannunta, kawai mu
ramako ? Eh mu rama, Suka fara shawara
sharrin da zasuyiwa Dan saurayin malamin
makarantar allonsu, yayo wankansa na juma'a
zashi masallaci sallar juma'a baima kula
dasuba. har sun hada sharrin da zasuyi tunda
nanne hanyar sa kamin ya dawo daga masallaci,
sun nemi toka ta murhu sukaje Gidan da ake
daka taba gari irin wannan da tsofafi suke
sakawa a qasan lebonsu, suka siyo ta ashirin
suka siyo garin barkono na goma suka hada guri
daya suka ijiye suka samo bokoti daya suka
debo ruwan kwata mai shegen wari suka je
suka samo kashin shahu sabo suka kwaba da
kwatar nan suka labe gefen hanya, ippatu ta
dane bishiya kamar biranya, da bokitin kwatar ta
da suka dama da ruwan kashi, malam garba na
bullowa shida dije ta watso mai garin tokar
daidai fuskarshi, da suka yiwa hadi ita, ita kuma
ippatu ta watsomai ruwan kwatar daga saman
bishiya, daga kansa har qasa ta diro gasa suka
waske, idon malami sun cika da yaji ya sai ihu
yake yana Neman dauki,yana murxawa ga ruwan
wari a saman kanshi kamin mutane suji ihunsa
tuni sun gudu gidajensu. Kuma ba Wanda ya
gansu Amma sabida hatsabibancinsu duk Wanda
ya sami labari sai yace hatman aikinsu ne sun
koma gida duk ranar ba Wanda ya fita cikinsu,
wayanda tun safe idan sun fita gantali basa
dawowa sai guraren yamma shima Dan sunsan
idan sunyi dare akwai samarin da zasu
hallakasune shiyasa duk la'anarsu da dibar
albarkarsu basa fita gida da dare.
Ina ippatu? tana daki, Malam lafiya kashigo a
hargitse?? Inafa lafiya yarinya tana son tasa
xaman qauye nan ya gagareni..
Ke ippatu.!! Na'am baba, zonan mara kunya
yarinya, ku ne kuka jiqe Malam garba da ruwan
kwata kuma kuka zuba masa barkono a Ido ko??
LA ilaha illallahu Muhammad rasullullahi wallahi
tana taba hannu tana salati kaman gaske,
wallahi baba ka tambayi gwagwo yau duk ban
fita koda zaureba, Dan banida lafiya, ko goggo,??
to ubanwa zai masa wannan ta'addancin idan
bakuba gashichan ido sai Allah, kuma yace bazai
barwa Allah ba.
Salamu alaikum. Daga waje sukaji sallama koda
baba ya fito saiga yan sanda biyu an kamo dije
da rukayya akazo a tafi dani, ina kuka ina kiran
baba, amma saida yan sanda suka tafi damu
police station..
************
Kun Dade kuna addabar mutane a garinnan, ba
makhluqin da bai kawo qararkuba a qauyennan,
kun zama annoba jaraba a gari to zamu kulleku
har sai likita ya tabbatar mana da samun idon
malam garba, DPO yake wannan bayani wasu
ippatu, iyayensu sunyi sunyi abasu belin su
amma sunqi badasu aka kullesu suna kuka suna
basu bane!
DPO yasa an musu Dan karen duka tunda ba
wata sheida da take tabbatar da cewa su suka
aikata wannan laifin, kawai sanin hali yasa aka
tsaresu, sunji wuya matuqa, amma dukda haka
sunqi fada gaskiyane, rukayya ta gaji ta tona
asiri tace sune dije da ippatu duk wahalar da
suka sha sun qi aminta hasalima sun qaryata
rukayya ne, Dpo dayaga ba nasara kuma likita
yace malam garba ya samu sauqin idon sai aka
sakesu, aka musu kashedi mai tsanani, sunyi
wujiga wujiga dasu, tun suna police station suka
fara shirya sharrin da zasu yiwa dpo insun fito
kaji hatsabibai dpo ne next target dinsu.......
WACE CE ITA..??6
Na Hauwa M. Jabo
*********
Bayan sun fito da sati biyu sundan yi lafiya dan
iyayensu sun manna musu mari a qafafu basa
zuwa ko ina hatta makarantar allo, gari ya samu
lafiya two days,
bayan sati biyu kamar sun shiryu sun zama na
kirki, aka kwance musu marinda aka saka musu,
ranar da suka hadu da juna suka fara dariya
suna bada labarin yanda iyayensu suka musu,
bayan sun qare labari suka fara shirrin yanda
zasu yiwa Dpo su dau fansar dukanda yasa aka
musu da marinda ya riqa tsinka musu lokacin,
bayan iyayen su ba Wanda ya taba marinsu
saishi.!!
Sun shirya zuwa har gidanshi su fasa mai glss
din akwalar motarsa. Amma basusan yanda
zasuyiba, sun gargadi rukayya akan idan ta
kuskura ta qara tona musu asiri basu ba ita ta
amince, matsalar su daya kada a ganesu, sun
yanke shawarar fita da dare Amma suna tsoron
samarin garin.
Yauwaaaaaa ina yan matannan da muke tsokana
masu saka baqiin Abu da hijabi su kulle
fuskarsu?? Eh nagane inji dijee naji ana ce musu
wani Abu namanta sunan, yauwa mu samo irin
wannan abin da suke sakawa mu rufe fuskar mu
sai a dauka sune zasu makaranta sai muje mu
fashe mu dawo, kaji hatsabibai marasa tsoro.!!
Suka saka dariya sun sami wani tuggu da zasu
qulla, Matsalar su daya basu da niqab din nan
dijee akwai gyallen tatan gasara na Maman su
zata dauko sai su yagashi suyi niqab tunda
gyallen baqine haka kuwa akayi, suka tare yar
makaranta ita ta dauka dukanta zasuyi, sai taga
kawai sun karbi niqab dinta suna kalloyanda
yake, suka sa allura suka hada irinsa, kaji
shegun yara...
da dare suka fita sai unguwar su dpo suka shiga
har chikin gidansa batareda shakkun komaiba,
da qarafunansu da suka samo gun kanikawa,
suka ma glss din motar tamas tamas, da yake
dpo yana gurin aiki, matarshi tana islamiyya
yarane kawai suke Gidan wataqil suna bacci
sukayi operation din ranar har suka gudu ba
Wanda ya gansu,har suka iso gida!!
Labari ya chika qari, ya yadu a kowa yace da
dai da rana ne da sai muce su ihhatu da dijee
ne, Amma yanzu duk qauyen an yarda basu bane
barayine kawai suka masa wannan karen
aikin... uku bala'e kenan!! suna nasara aduk
aikinda sukasa gaba koda zasusha wahalane..
*******************
Yauda gobe ba wuya a gurin Allah abubuwa da
yawa sun faru a dan qaramin qauyen nan ciki
kuwa harda rasuwar mahaifin ippatu sanadiyar
hatsarin mota, yajee birni siyo kayan shagonsa
anan babbar mota ta bi saman motar su Allah
yayi mai cikawa.! Su ippatu an Dan natsu kadan
an rasa mahaifi, mahaifiya kuma dama batasan
duniyar da takeba coz ba rabuwar allah sukayi
da babantaba duk sharrin goggone, tunda tayi
wayo bayan babanta ya kwatota a hannun
mahaifiyarta bata qara saka mahaifiyarta a idoba
haka ma yayyenta..
Tun farko farko zaman haquri goggo takeyi da
ippatu, bare yanxu da ba mahaifin ippatu, sabida
haka ta yanke shawarar miqata birni wanke
wanke ko ta moreta....
[4:50PM, 4/26/2015] .: WACE CE ITA..?? 7
Na Hauwa M. Jabo
Tashin hankali ni kaina Jabo na tausaya
wayanda zasu dauki ippatu aiki gidansu kamin
su korota nasan zataci ubansu.!
Goggo kullum gori take mata har ta fara girgar
dangi a gida, amma ba mashinshini bare a aurar
da ita. Wazai kwasar ma kanshi jaraba. ippatu
da yar birni ce da sai anyi haddadiyar mace dan
komai Allah ya bata sak mamanta ta dauko
fulani gaba da baya sai ta hada da da duhun
babanta sai tayi Dan duhu farinta mai haske ne
da duhu gata qirar kalangu ga gashinan kamar
yakasheta amma ba gyara idan akayi kitson
sallah qarama sai babbar sallah ake tsefeshi,
tayi baqi Dan na tabbatar da tafi zainb khalifa
baqi sabida tsabar rashin wanka, qafafu duk sun
jeme haqora sunyi tsatsa da wata laka laka a
ciki idonnan sunyi ja duk jikinta tabone sabida
fadowa saman bishiya da akeyi a jijji ciwo, ko
saman Garu da ake dirowa ko a na gudu a fadi a
ji ciwo haka dai take masha Allah.....
*********
Goggo tayi magana da altine akan tanason a kai
ippatu birni aiki amma inaaaaaa altine taqi
aminta Dan tasan halin ippatu sama da qasa,
gaba da baya, altine taqi yarda har goggo ta gaji
da zuwa gidanta neman alfarma ta haqura,
ranar goggo taje suna maqotansu taga wata
mata daga birni tana maganar a nemo mata yar
aiki yarinya qarama mai qoqari da kuzari goggo
batace komaiba, Dan tasan idan ma tayi magana
anan mutane zasu fadi mugun halin ippatu.
Saida aka watse matar na fita goggo ta faki ido
ta bi bayanta, tajata gida tace tanada ya amma
batason kowa yasan zata kaita aikine zatace
takaita gun yar uwartane goggo tace yarinyar
marainiyace, tanason ta dan riqa samun abinda
zasu chi su rufawa kansu asiri, Amma batason
kowa ya sani, hakadai goggo yayita tsara matar,
ana haka saiga ippatu an dawo daga kogi tun
safe dataje sai yanxu tayi shudi daya, Koda
matar taga ippatu taga uban bokitin data dauko
saman kanta chike da ruwa ta tabbatar da cewa
ippatu Nada kuzari, kamar gaske ippatu ta gaida
matar ta wuce abinta matar kuwa ta amince da
ganin ippatu kuma tace baxata fadawa kowaba.
Matar da yake gidan biki tayi sanarwar anata
kawo mata yara yan mata amma Duk wacce aka
aiko sai tace musu ai ta samu bata fadawa
kowa cewa ippatu CE ta samuba har ta koma
birni,.!!
Bayan kusa sati uku da magana matar tazo ta
tafi da ippatu birni ta mata dinki kala biyu Dan
kar taje Gidan daga shigarta a koresu , aka hada
da yan kayan sallarta. Ippatu tayi kukan rabuwa
da qauyensu Dan batason zuwa aikin da
za'akaita sun rabu da dijee da rukayya sunata
kuka sai birni......
WACE CE ITA..?? 8
Na Hauwa M. Jabo
*******************
Bayan sun isa birni matar da nikaina Jabo
bansan sunantaba takaita gidanta, tasa tayi
wanka ta saka kayan da ta dinka mata, suka
kwashi hanya takaita gidan da zatayi aiki, ippatu
tunda ta shigo birnin sokoto take qauyanci ganin
sabuwar duniya ya hanata kula da fadan da
matar take mata bare ta mata rashin kunya,
data shigo gidan Alhaji Habib nan kallo ya koma
sama, gidane da idan na tsaya muku bayaninsa
zan bata lokacine, duk unguwar ba gidan da
yakaishi girma, ga lambu a gidan shuke shuke
manyan itatuwa swimming pool ne, gurin ijiye
motoci ga abubuwa nan kala kala, ataqaice dai
Gidan dai ya hadu, ippatu tana shiga palon
santsin tayis ya kwasheta ta xube qasa tiiiiim..!!
Wata Yar budurwa da matar gidan suka saka
dariya, taji haushin dariyar da aka mata ta daure
fuska abinta, badan yau tazoba da sai ta tsula
musu rashin mutunci su har sun isa su mata
dariya.!!?
Matar data kawota ta riqa hannunta suka
qarasa palon suka zauna, sanyin ac tuni ya fara
shigarta ta fara rawar dari sai qarar haqoranta
kikeji kakaf. kakaf, alhaji yace a kashe ac din
baquwarsu tanajin sanyi.! haba Abba wallahi
zafi akeyifa wani Dan saurayi ya fada yana
yatsina fuska alamar zafi! Alhajin dakanshi
yatashi ya kashe ac ya dawo ya xauna. Wacce
ta kawoni ta fara musu bayanina kamar yanda
goggo ta mata bayani, taji qaryarda goggo ta
zuba tayi yawa ta kasa haquri Dan ita ba'aqarya
gabanta, tayi charb ta chabke ta fara zuba,
goggo ba itace mahaifiyataba mahaifiyata sun
rabu da mahaifina tun ina qarama mahaifina ya
rasu shekara kusan biyu da suka wuce kum.....
Keeee, keep quiet mana ya fada yana mata
kallon wulaqanci, chikin tsawa ya fadi maganar
ta gane keep quiet dan lokacinda tana boko
kamin a korota Malaminsu yana yawan fadar
haka idan ana surutu kuma daya fada sai kowa
yayi shiru, shima malaminsu da qarfi yake fada
kamar yanda wannan ya fada, ta dallamai
harara hadi da yimai kallon banxa ta zubar.
Kaiiiii abba u see? Kaga yanda take kallona
kuwa,?
Farhaan yakamata ka riqa haquri mana, da
zuwan baquwa zaka tsaneta haka, kada ka
manta da ita zaka zauna.. farhaan ya juyar da
kai gefe gaskiya dady bana tunanin xan iya
zama da wannan, kalletafa!! wata kyakyawar
dattijuwa ta kalleshi wallahi kayi kadan wannan
itace ta qarshe ba chanji. Duk maganar. da
suke da englsh suke yinta, Ya bata fuska ya
tashi yabar musu guri yar qanwarshima ta bi
bayanshi suna gunagunai da turanci,
Matar data kawoni ta basu haquri tace kuma
kada in qara magana, ganin maganata kamar
itace ta haifarda rigima sai nayi shiru bawai dan
raina yasoba, taci gaba da musu bayani inajin
tana qarya amma ba halin magana......
Mujeee zuwa muji yanda iffat za'azauna a gidan
aiki, da wannan hali nata......M jabo
.......
[4:00PM, 4/27/2015] .: WAYE ITA..?? 9
Na Hauwa M. Jabo
Wacce ta kawoni Ta qare bayananta na qarya
dana gaskiya da goggo ta kitsa mata....
Kyakyawar matar tace Allah ya bamu ikon riqeta
yar marainiya da ita, dama yaron mune muka
nemowa mai aiki, duk wacce aka kawo sai su
sami sabani dashi kusan mai aiki 13 ana
kawowa suna samun sabani, shine yanxu yace
asamo mai qaramar yarinya tunda aikin nashi
bashida yawa yace bayason Yar cikin qari sabida
sauran daga qazamai sai barayi sai yan iska sai
marasa kunya da sauransu, shi kuma baya iya
zama dasu

Please Login or Register in order to submit comment