Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yazo nan a
zancensa sai Imhal ya rungume shi suka fashe da
kuka tare tsawon yan dakiku suna manne da juna sai
daga can Imhal ya janye jikinsa daga cikin nasa ya
dube shi yace Ya kai Abbana kayi sani bazan yi maka
gardama ba bisa wannan shawara da kazo min da
ita,sabo da nasan cewa ni bansan abinda kasani
ba,domin duk wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka
tashi,yanzu sai mu koma bukkarmu mu debo
kayanmu gaba daya,Imzanu ya gyada kai yace Ai na
debo mana dukkan kudadenmu idan mun shiga cikin
gari mayi guzuri,cikin alamun tsananin damuwa
Imhal ya dubi imzanu a lokacin da idanunsa suka ciko
da kwallah yace Haba ya kai Abbana ko ba komai na
koma da baya ka nuna inda ka binne mahaifiya ta
nayi mata bankwana tunda rabona da ita tun ina
kankani,koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa
Imzanu ya dubi Imhal yace ka gafarceni ya kai dana
hakika naso nayi babban kuskure,zo muje na nuna
maka kabarin mahifiyarka,ko da gama fadin haka sai
tsoho Imzanu ya juya da baya suka koma izuwa can

gaban bukkarsa suka cigaba da nausawa cikin daji
suna bin wata hanya mai sarkakiya da yawa wacce shi
kanshi Imhal a iya tasowar shi acikin daji bai taba
sanin akwai wannan hanya ba,kawai sai tsintar kansa
yayi acikin wadansu dogayen bishiyoyi masu manyan
ganyaye wadan da suka sa dajin gaba daya yayi
duhu,bisa dole suka kunna wuta a jikin itace don
haska hanya,Imzanu ya cigaba da yiwa Imhal jagora
sai gasu a bakin kofar wani kogon dutse mai girman
gaske,da isowarsu bakin kofar kogon sai Imzanu ya
haska cikin kogon yaga lafiyarsa sannan ya juyo ya
dubi Imhal ya mika masa wutar itacen yace acikin
wannan kogon na binne mahaifiyarka,ka shiga ciki
zaka ga kabarinta sai kayi mata bankwana ni kam
bazan iya sake kallon kabarin ta ba domin idan na
gan shi zan tuno baya,kuma hakan zai iya jefani cikin
mugun hali,cikin matukar sanyin jiki Imhal ya karbi
wutar icen sannan uya kunna kai cikin kogon dutsen
yana shiga kuwa ya hango kabarin na mahaifiyarsa,ka
i tsaye ya tukari inda kabarin yake da isarsa gaban
kabarin sai ya durkusa a gabansa ya kifa kansa akan
kabarin sannan ya fashe da matsanancin kuka tsawon
yan dakiku yana cikin wannan hali sannan ya dago ya
kurawa kabarin idanu yace YAKE MAHAIFIYATA SABO
DAME ZAKI TAFI KI BARNI LKACIN DA NAFI
BUKATARKI FIYE DA KOMAI?ME YASA KIKA TAFI BAKI
FADI KO WAYE UBANA BA?SHIN HAKA KIKE SO
RAYUWATA TA KARE ACIKIN KADAICI, MARAICI GAMI
DA TAKAICI KAMAR YADDA TAKI TA KARE?WANENE
IMHAL?SUNAN DA KIKE AMBATA AKO DA YAUSHE?
IDAN HAR BAZA KI IYA BUDAR BAKI KI GAYA MIKI
AMSAR TAMBAYOYINA BA YANZU ZAN KASANCE MAI
SAURARON FATALWARKI KODA ACIKN
BARCINA,BAZAN TABA SAMUN SUKUNI DA
KWANCIYAR HANKALI BA A RAYUWATA HAR SAI NA
GANO ASALINA.
Koda gama fadin hakan sai Imhal ya sake kifa
fuskarsa akan kabarin ya dada fashewa da kukan bakin
ciki.
.RIJIYA GABA DUBU
Littafi na daya 1
Na Abdulaziz sani m gini
Typing:- Ibrahim S combatant
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 1C
.Sai da ya jima yana kukan sannan ya mike tsaye ya
fice daga cikin kogon dutsen yana waigen kabarin
yana zubar da hawaye,har ya isa bakin kofar kogon
zai fita sai ya waigo ya dubi kabarin yace Yake
ummata nayi miki alkawarin zan rayu acikin wannan
duniya komai RINTSI DA TSANANI har izuwa lokacin

da zan gano asalina na dawo har nan na sanar
dake,koda gama fadin haka sai ya juya ya fice daga
cikin kogon yana fitowa ya iske tsoho Imzanu a zaune
ya kishingida da jikin kogon har ya fara bacci sabo da
gajiyar yaar tafiyar da yayi,motsin takun sawun Imhal
ne yasa ya farka daga baccin cikin yanayin
damuwa,Imzanu ya dubi Imhal yace yakai dana kayi
sani cewa na gaji ainun kuma gashi tsufa yana tabani
ina ganin cewa yanzu bazan iya takawa da kafafuna
ba yanzu sai dai mubarwa gobe da safe amma yin
hakan yana da hadari,domin ina ji a jikina cewar
sarki zai iya turowa a kamaka domin ya tsareka a
kurkukunsa,don kada ka gudu kabar garin,kafin tsoho
Imzanu ya gama rufe bakinsa sai suka jiyo sautin
takun sawu daga can nesa,alamar takun sawu ne ta
mutane da yawa kuma inda suke aka durfafo,koda jin
haka sai Imhal yayi wuf ya suri tsoho Imzanu ya
goyashi a bayan sa ya daure shi tamau,sannan ya
ruga izuwa kan wata bishiya mai tsawon tsiya wacce
can karshenta ganyayene manya manya masu
duhuwa,kamar kadangare na hawa bango haka Imhal
ya dinga hawa kan bishiyar da gudu kai kace ba sama
yake hawa ba,cikin dakiku kadan ya isa karshen
bishiyar yayi lambo akan wani reashe,shi kansa Imhal
idan ya leko kasa baya iya jiyo motsin komai sabo da
nisa,A dai dai wannan lokaci ne dakaru acikin
bakaken kaya kimanin su dubu suka iso dai dai kofar
kogon dutsen da gudu,dukkanninsu suna rike da
tagobi tsirara kuma sun rufe fuskokinsu,koda tsoho
Imzanu ya hango wadannan dakaru sai ya sai
zuciyarsa ta buga da karfin gaske ya firgita ainun ya
fara kokarin tuno da wani al amari wanda ya faru a
shekarun baya,amma sai kwakwalwar tasa ta kasa
tuno komai.Dakarun masu bakaken tufafi na isowa
suka tsaya cirko cirko suna kallo kallo da waige
waige,nan dai shugabansu ya rarraba su izuwa gabar
da yamma kudu da arewa,suka bazama neman inda
su Imhal suke,har cikin kogon dutsen inda kabarin
mahaifiyar Imhal yake sai da suka shiga.A dai dai
wannan lokacine Imhal yayi kundunbala ya sallamo
kasa daga kan doguwar bishiyar,karar dirar kafafunsa
kasa ne yasa dakarun suka farga suka baro inda suke
da gudu,amma kafin su iso inda suka bari tuni Imhal
ya falfala da azababben gudu goye da tsoho
Imzanu,Wohoho!kafa me naci ban bakiba?idan zan ta
tarar da muje mu sai abinda hali yayi,duk tsananin
gudu irin na Imhal sai gashi wadannan dakaru suna
rufa masa baya har ma suna nema su cimmasa
amma sun kasa,koda dakaru suka ga an shafe dakiku
masu yawa sun kasa cimma Imhal duk da tsananin
nacinsu gami da horon da suka samu na juriya sai
suka fara zaro kibiya suna danawa akan baka suna

harbawa Imhal,Imhal na cikin gudu sai yaji kibiyoyi
suna wucewa ta samansa da gefensa,har ma sai da
wata kibiya ta karci gefen kunnensa jini yayi
tsartuwa,al amarin da yayi matukar girgiza
hankalinsa kenan ya kara karfin gudunsa,amma
abinda ya kara tayar masa da hankali shine,tunowa
da tsoho Imzanu wanda ke goye a bayansa wanda
ako da yaushe bisa tsautsayi kibiya zata iya zuwa ta
soke shi,koda ya aiyana hakan sai yasa hannayensa
ya juyo da tsoho Imzanu daga bayansa ya dawo dashi
gabansa ya ci gaba da falfala gudun da haka,kaico!
Tsautsayi ba a yi masa barci!Imhal na cikin wannan
azababben gudu ne kibiya tazo ta soke shi a duga
duginsa na kafar hagu take kibiyar ta ta nutse ta hudo
waje,Imhal ya kwarara uban ihu sakamakon tsananin
zafi da zugin da yaji,yayi taga taga kamar zai kife kasa
amma sai ya yunkura cikin zafin nama da tsananin
juriya ya take kafar a haka tana zubar da jini yaci
gaba da gudu.Naci damben kuturu!koda dakarun nan
suka ga Imhal yaki faduwa kasa yaci gaba da gudu
duk da cewar kibiyar ta soke shi a kafa sai suma suka
ci gaba da falfala gudu suka dada zubo masa ruwan
kibbau ba sassauci,Har Imhal ya iso daf da kafar cikin
gari dakarun basu cimmasa ba kuma babu wata
kibiya data soke shi amma fa yana jin mugun zugi
acikin kafarsa tamkar ya sare kafar da hannunsa ya
yar da ita.koda dakaru suka ga an iso cikin gari sai
suka samu lokuna suka shiga suka buya suka sauya
tufafin jikinsu suka sa irin na mutanen gari suka bude
fuskokinsu,sannan suka rarrabu suna masu dada ci
gaba da farautar Imhal.Imhal na shigowa cikin birnin
kisra goye da Imzanu sai ya fara sarewa yana jan kafa
da kyar,cikin hanzari ya doki kofar wani gida dake
rufe da hannunsa guda, take kofar ta balle ya kunna
kai ciki ya yunkura zai kwance Imzanu daga jikinsa sai
yaga ashe ya suma sakamakon wata kibiya data soke
shi a gefen wuyansa,cikin tsananin dimaucewa Imhal
ya sauke Imzanu kasa ya wangame baki zai rusa ihu
don a zatonsa Imzanu ya mutune,sai kawai yaga wata
tsaleliyar mata ta rugo da gudu daka can cikin gidan
ta dube shi tana mai yi masa inkiyar yayi shiru.
Sai da tazo daf da shi sannan tayi masa rada a kunne
tace tsohonka bai mutu ba,zan iya ceto rayuwarsa ni
likita ce,bari nayi sauri naje na batar da shaidar da
zata sa a gane ka shigo nan,maza ka shigar da tsohon
can cikin dakina ka kwantar dashi kada ka taba
shi,tana gama fadin haka sai ta dauki wani tsumma ta
ruga waje,cikin sauri Tsaleliyar matar taje ta goge
duk jinin kafarsa,daya zuzzuba a kofar gidan,sannan
ta sake rugawa izuwa cikin gidan ta mai da kofa ta
saka sakata.Faruwar haka ke da wuya sai ga
wadannan dakaru da suka biyo Imhal sun iso wajen

da gudu,gaba dayansu sai suka tsaya suna yin duru
duru suna waige waige da hange hange,suna jiran
karasowar shugabansu domin ya basu umarni bisa
abinda za suyi
Al'amarin Imhal kuwa,lokacin da ya kinkimi tsoho
Imzanu ya shige dashi izuwa dakin wannan tsaleliyar
mata a dimauce sai ya shimfide shi akan wani
babban teburi na katako,a sannan ne ya dubi ko ina a
cikin dakin nan take ya gamsu cewa daki ne na
likita,don babu komai acikinsa face tarkacen kayan
likitoci,kawai sai ga matar ta shigo cikin dakin da
gudu,ko kallon Imhal batayi ba ta ruga izuwa kan
tsoho Imzanu ta shiga yi masa aiki,nan take ta cire
kibiyar dake wuyan nasa,ta zuba wani garin magani
akan raunin nan take jini ya daina zuba,duk wannan
abu da take Imhal yana tsaye a gefe daya ya zuba
mata idanu kawai cikin tsananin mamaki,domin bai
san dalilin da yasa ta taimake shi ba alhalin gashi ma
yayi mata laifi ya karya mata kofar gida da karfin
tsiya,kuma gashi bata taba ganin shi ba sai yau,Bayan
gama shudewar dakiku dari da ashirin da gama yiwa
Imzanu magani sai ya farfado ya bude idanunsa,koda
ganin haka sai farin ciki ya lullube Imhal ya kama
yiwa matar godiya,A dai dai wannan lokaci ne suka ji
ana kwankwaso kofar gidan da karfi,Al'amarin da ya
tayar da hankalin Imhal ya yunkura zai zare
tagobinsa,sai matar tayi masa nuni da kada ya zare
tagobin,ta dube shi tace ka bani yardarka ina mai
tabbatar maka da cewa komai dadewa zaka dawo ka
iske mahaifinka a cikin koshin lafiya,maza kayi
sallama da tsohon naka zan nuna maka hanyar da
zaka bi ka fice daga cikin gidan nan ba tare da wani ya
ganka ba,cikin tsananin mamaki Imhal ya dubeta yace
wacece ke kuma sabo dame kika ce ci rayuwarmu
nida wannan tsohon nawa?matar tayi murmushi mai
taushi ga Imhal tace Ni na sanku fiye da shekaru
bakwai baya,kune baku san ni ba,kuma na dade ina
bibiyarku a duk sanda kuka shigo garinnan,tana gama
fadin haka ne suka ji anci gaba da buga kofar gidan
da karfin gaske,A guje matar ta kama hannun Imhal
ta jashi izuwa cikin wani dakin daban yana waigen
tsoho Imzanu yana hawaye,shima Imzanu ya bishi da
kallo yana zubar da hawaye,domin duk su biyun sun
san cewa abu ne mai wuyar gaske idan har zasu sake
saduwa da junansu,da shiga su Imhal cikin wannan
daki na biyu sai sukayi arba da wata rijiya a bude
wacce ta ciko da ruwa har baki,kai sai matar ta dube
shi tace kayi nitso izuwa can kasan rijiyar zaka samu
hanya wadda zata kaika har izuwa kogon Ishmal dake
can bayan gari,daga nan sai ka nausa daji kayi
kokarin ficewa daga nahiyar nan gaba daya,kada ka
kuskura ka dawo garinnan sai bayan anyi gasar

Jarumta a birnin misra koda gama fadin haka sai
matar ta juya da baya,cikin sauri Imhal ya ruko
hannunta,ta waigo ta dube shi cikin mamaki yace
mata mene sunanki? Matar yai murmushi tace mishi
sunana ZUMAIRA IBINI IMHAL.Koda jin wannan suna
sai idanun Imhal suka zazzaro ya kasa sakin hannunta
kuma a sannan ne suka ji anbugo kofar gidan da karfi
ta fadi rikica gaba daya,koda ganin haka sai matar
tasa kafarta ta doki kirjin imhal ya fada da baya cikin
rijiyar,kawai sai ya nutse izuwa karkashinta,cikin
hanzari matar ta juya ta koma baya da gudu.Tana
isowa falonta ta iske tsoho Imzanu zaune akan
teburin cin abinci yana shan ruwan Inibi kuma har ya
sauya tufafin jikinsa,kuma ya sauya kamanninsa
domin ya shafe gemunsa da sajensa da shuni kamar
bashi ba,wadansu karti kimanin su arba'in na tsaye a
gabansa daya daga cikinsu nayi masa
tambayoyi,kawai sai Zumaira ta dakawa kartin tsawa
ta dube su tace,su waye ku akan wane dalili zaku
karya mana kofar gidanmu ku shigo?koda jin haka sai
Dakarun suka waigo izuwa kan zumaira suna muzurai
kamar saci babu har sun zare takubbansu zasu afka
mata sai daya daga cikinsu ya daga musu hannu suka
dakata sannan ya matsa daf da Zumaira ya dubeta a
fusace yace muna neman wani saurayi da wani tsoho
mai furfura a gemunsa ki gaya mana gaskiya idan sun
ahigo gidannan kun boye su domin idan kuka yi mana
karya kuma mukayi bincike muka gansu sai mun
kasheku,koda jin haka sai Muzaira tayi guntun
murmushi tace ai sai ku duba ku gani,nan take katti
suka bzama ko ina amma basu ga kowa ba,sannan
suka fice daga gidan gaba daya.
.
.
RIJIYA GABA DUBU
Littafi na daya 1
Na Abdulaziz sani m gini
Typing:- Ibrahim S combatant
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 1D
.Muzaira ta dubi tsoho Imzanu kawai sai taji ya fashe
da kuka,al amarin da ya karya zuciyarta kenan ta
kamu da tsananin tausayinsa don haka sai ta dube
shi tace Ya kai Imzanu ka kasance mai gaskiya da
juriya acikin duk irin yanayin da ka tsinci kanka
aciki,koda jin haka sai Imzanu ya dago kai ya dubeta
cikin mamaki yace Ya akai kika san sunana?yayin da
muzaira taji wannan tambaya,sai nan take idanunta
suka ciko da kwallah sannan ta dubi Imzanu tace
Mahaukaciyar da kayi jinya acikin daji har ta haifi
wannan saurayi da kuke tare yayata ce uwarmu daya

ubanmu daya,kuma ita ce babba a wajen mahifinmu
wanda shine sarkin kisra na da,kafin azzalumin
sarkinmu na yanzu ya kashe shi ya hau kan karagar
mulkinsa.Gaba daya zuri armu sai da sarki GURZALU
ya kashe su,nice kadai nayi saura,nima albarkacin
karfin sihirin tsafin da nake dashine yasa na tsira da
rayuwata,Ba wani abune yasa yar uwata ta haukace
ba face a gabab idanunta aka kashe mijinta Imhal aka
yi masa yankan rago,sannan aka yanka iyayenmu da
dukkan zuri'armu,tana ganin wannan al'amari ne ta
haukace nan take,amma duk da haka sai da aka yi
mata yankan rago akasa dakaru sukayi badda kama
suka dauki gawarta suka kai daji suka yar,Abinda
yasa aka dauki gawarta aka kaita daji shine,Ramin da
aka haka aka saka gawar mijinta da ta sauran
zuri'armu ya cika.Duk abinda ya faru da yar'uwata
Shulaira na gani a madubin tsafina,kuma duk naga
irin dawiniyar da ka sha da ita shi yasa yanzu na
taimake ku na kubutar da Imhal,ina mai tabbatar
maka da cewa Imhal ya kubuta daga sharrin sarki
Gurzalu domin zai fice daga cikin garin nan gaba daya
ta cikin wata rijiya dake cikin gidannan.koda Muzaira
tazo nan a zancenta sai tsoho Imzanu ya cika da
tsananin mamaki gami da tsananin bakin ciki,daga
can kuma sai ya dubi Muzaira cikin alamun damuwa
yace Ke kuwa mai yasa tun yar'uwarki na raye a
wajena a daji baki ziyarce ta ba,kuma me yasa yanzu
baki gayawa Imhal cewar ke kanwar mahaifitarsa
bace?Muzaira tayi ajiyar zuciya tace Ai ina fita daga
cikin garinnan sihirin tsafina zai karye sarki Gurzalu
ya gano inda nake ya turo a kashe ni,dalilin da yasa
ban sanar da Imhal ni uwace a garshiba shine,idan
na gaya masa bazai tafi ba yanzu kuma idan yaki
tafiya ni dashi halaka zamuyi,koda jin haka sai
hankalin tsoho Imzanu ya tashi fiye da ko yaushe ya
rasa abinda ke masa dadi a duniya.
Lokacin da Imhal ya nutse izuwa cikin karkashin
wannan rijiya ya isa can kasanta sai ya kama laluben
hanya,nan da nan ya fara fita daga hayyacinsa
sakamakon rashin numfashi,amma cikin sa a sai yaga
wani kifi yas shigo cikin rijiyar ta cikin wata kofa,cikin
sauri ya kunna kai cikin kofar sai ya ganshi
akarkashin wani katon kogi,ciin sauri ya taso sama
domin ya shaki numfashi,aikuwa yana dagowa sama
yaji an gabza masa duka da kulki a fuska,take jini yayi
feshi daga cikin bakinsa da hancinsa nan take ya baje
a saman ruwa sumamme.
Sa'adda Imhal ya farfado sai ya tsinci kansa acikin
wani matsatstsen daki kwance a kas,gefensa ga wani
garjejen saurayi a zaune ya kura masa idanu,cikin
dimaucewa da mamaki imhal ya mike zaune zumbur
ya karewa dakin kallo tsaf,sannan ya dubi garjejen

katon saurayin dake gabansa yace,Ina ne nan?Yaya
akayi nazo nan?koda jin wannan tambaya sai katon ya
bushe da dariyar mugunta,maimakon ya baiwa Imhal
amsar tambayarsa sai ya mike tsaye ya damki
makoshin Imhal da hannu daya ya daga shi sama
tamkar ya daga sillan kara,sai gashi Imhal ya fara
kakarin mutuwa,kawai sai garjejen katon yaci gaba da
kyalkala dariyar mugunta sannan ya daga kansa sama
yana duban Imhal yace,Kai yaro yau ka shigo
kurkukun darul maut na birnin kisra,kurkukun da ba
a fita sai dai gawa ta fita kuma gashi kayi rashin sa a
ka shigo dakin dodon kowa a gidannan ZAUWADU,a
dai dai wannan lokacine sauran fursunonin dake cikin
sauran dakunan gidan suka kama lekowa dakin
Zauwadu domin suga mai karar kwanan da aka
kawo,ashe duk fursunan da aka kaishi dakin Zauwadu
kawai so akeyi a kashe shi,Ba zato ba tsammani kawai
sai Zauwadu yaji Imhal ya gabza masa mugun duka a
fuska da kafarsa guda,Sabo da karfin dukan sai da
Zauwadu yaga taurarin wuya bai san sanda ya
dimauce ba ya saki wuyan Imhal ya fado kasa yana
tari,koda Zauwadu ya shafa fuskarsa yaji jini sai ya
fusata ainun ya juya bayansa inda Imhal ke kwance
yana mai yin kururuwa kuma yakai masa mugun taku
da kafa,cikin bakin zafin nama Imhal ya goce ya
mirgina can gefe daya ya shammaci Zauwadu ya
buga masa kafa akan marenansa,take Zauwadu ya
sulale kasa sumamme,koda ganin abinda ya faru sai
gaba daya fursunonin gidan suka daina shewa da
dariya suka kame kamar gumaka sabo da tsananin
mamaki,Ba komai ne ya jefa fursunonin cikin
tsananinb mamaki ba face ganin yadda aka samu
jarumin da ya sumar da Zauwadu.Gaba daya
fursunonin dake cikin kurkukun suna tsananin tsoron
Zauwadu,kai ba ma fursunoninba su kansu dakarun
dakaru dake tsaron fursunonin shakkarsa suke
domin mutum goma basa iya ladaftar dashi sai dai
ashirinb zuwa sama,duk da cewa dakarun kartine
majiya karfin gaske wanda sai da aka zabo su,ko ya
ya wani abu ya hada fursuna da Zauwadu to fa sai dai
a sanya sunansa acikin matattu don ansan cewa
Zauwadu ya kashe shi sabo da zaluncinsa,karfinsa da
rashin imaninsa.Lokacin da Zauwadu ya farfado daga
dogon suman da yayi yaga Imhal a zaune acan gefe
daya kan shimfidarsa ya harde kafafu tamkarma ba
fada sukayi ba sai ya fusata ainun musamman da ya
waiga baya yaga gaba daya sauran fursunonin dake
cikin sauran dakuna sun zubo idanu suna
kallonsa,nan take zauwadu ya yunkura zai sake
afkawa Imhal kawai sai gani yayi Imhal ya daka tsalle
sama kamar dan biri ya dirga akan wuyansa ya shake
shi,duk da tsananin karfi irin na Zauwadu sai gashi ya

kasa kwacewa kuma idaninsa sunyi bulu-bulu sunyi
jawur sai gashi yana dukushewa kasa yana kakarin
mutuwa.Koda Imhal yaga Zauwadu na neman
mutuwa sai ya sake shi ya zube kasa magashiyan
yana numfashi sama-sama,take imhal ya nuna
Zauwadu da dan yatsa ya dubeshi yace idan ka kara
kawo miki wargi a karo na uku sai na kashe ka,Tun
daga wannan rana Imhal ya zama shugaban
fursunonin gidan gaba daya ya zamana cewa kowa
yana shakkarsa ana yi masa ladabi da biyayya.A
bangaren shugaban dakarun dake dake tsaron
kurkukun kuwa,sai ya dauki kiyayyar duniya ya dora
aka Imhal ya zamana cewa haka kawai sai yasa a
kama Imhal a daureshi a tsaye da sarkoki ai ta
dukansa da itatuwa har sai ya suma kamar gawa sai
dai fursunoni su zo su dauke shi suyi masa
magani,wani lokacin kuma ai ta gana masa bakar
azaba iri-iri wacce duk fursunan da akayiwa ita sai ta
zama sanadin ajalinsa amma sai gashi imhal yana
jureta,duk da tsananin juriya irin ta Imhal sai da ya
dinga ramewa yana yawan ramewa yana yawan
rashin lafiya sabo da tsananin wahalar da yake
sha,kai in ba don ma fursunonin suna matukar
kaunarsa ba kuma suna gadin rayuwarsa ba,da tuni
dakarun gidan sun kashe Imhal,komai rashin
tausayin mutum idan yaga irin halin da imhal ya
shiga sai ya tausaya masa,ba komai ne yasa
fursunonin gidan suke matukar kaunar jarumi Imhal
ba face zuwansa ya kawo adalci a tsakaninsu ya
zamana cewa mai karfi ya daina zalunta mara karfi,a
da,ko abinci fursuna ya karbo ya zauna zaici sai kaga
wanda ya fishi karfi yazo ya kwace ya hada da nasa
sai dai wancan ya kwana da yunwa,haka kuma akwai
fursunoni masau mugayen dabi'u na yin luwadi ga
wadan da sukafi karfi amma duk sai da Imhal ya hana
yin wadannan mugayen abubuwa,Zauwadu da ya
kasance babban makiyin Imhal sai da ya zamo
babban amininsa kuma abokin shawararsa.
.
RIJIYA GABA DUBU
Littafi na daya 1
Na Abdulaziz sani m gini
Typing:- Ibrahim S combatant
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 1E
Wata rana bayan an kama Imhal an kai shi wani daki
na musamman inda ake yiwa fursunoni azaba,anyi
masa dukan kawo wuka,sai aka dawo dashi dakin su
aka warbar dashi a kasa jina-jina yana numfashi
sama-sama kamar zai mutu,cikin dimaucewa
Zauwadu ya shiga yi masa magani,da kyar ya samu ya

tsayar da jinin da yake zuba a jikinsa,koda Imhal ya
farfado ya dawo cikin hayyacinsa sai ya bude
idanunsa dakyar ya dubi zauwadu yace Gobe idan na
samu karfin jikina da cikin dare zan gudu daga cikin
kurkukun nan,idan zaka iya bi na kazo mu gudu tare
mu tsira tare,koda jin wannan batu sai idanun
Zauwadu suka zazzaro ya kamu da tsananin tsoro ya
dubi Imhal cikin damuwa yace Ya kai abokina kayi
sani cewa tunda aka gina kurkukun nan tsawon
shekaru arba'in a baya ba'a taba samun fursunan da
ya samu damar guduwa ba daga cikinsa,ta ya ya kake
tsammanin kai zaka iya?ka dubi katangar gidannan
wacce ta kasance mai tsananin tsawo da kauri,Ta ya
ya zaka iya haurata ko fasata ba tare da anzo an
kamaka ba?ka dubi yawan dakarun dake rangadi a
harabar gidan nan a duk dare da rana,sannan ka dubi
mugayen karnukan da suke gadin ko ina wadan da
suka kasance manya tamkar kuraye sannan gashi sun
samu da horo na musamman na iya kama mai laifi
gami da tsananin karfin gudu gami da juriyar su.Idan
baka sani ba to ka sani cewa gaba dayan kurkukun
nan akan tsibiri yake,kuma shi tsibirin akan tsakiyar
teku yake,idan ma ka samu nasarar fita daga cikin
kurkukun nan ta yaya zaka iya ketare wannan teku har
ka tsira da rayuwarka?Ai dabbobin dake cikin tekun
nan ma kadai da sanyin teku sun isa su hallaka
ka.Tabbas wannan kurkukun yaci sunansa
DARULMAUT wato gidan mutuwa,duk fursunan da ya
shigo gidan nan ya san cewa ya shigo gidan
ajalinsa.Lokacin da Zauwadu yazo nan a zancen sa sai
kawai yaji Imhal ya bushe da dariya al'amarin da yayi
matukar bashi mamaki kenan ya kura masa idanu
kawai ya kasa cewa komai,daga can sai Imkal ya
nutsu ya dube shi yace Babu wani abu da bazai yiwu
ba a doron kasa,kawai abinda nakeso dakai shine ka
nemo mana kudade masu yawa wadan da zamu iya
siyan ma'aikatan gidan nan,babu abinda kudi bazai
iya yi ba.Koda jin wannn batu sai jikin Zauwadu yayi
sanyi ya sunkui da kansa kas ya fada kogin
tunani,Daga can sai ya dago kai ya dubi Imhal yace Ya
kai abokina ko na bika ko ban bika ba mutuwa zanyi
acikin gidan nan don haka gwara ma na bika din
tunda babu wanda yasan abinda zai faru gobe,naga
misali akan haduwa ta dakai,ban taba zaton za'a iya
samun fursunan da zai zo gidan nan ba har ya iya
kaini kas sai gashi ma kai ka kaini kas har da sumar
dani alhalin babu wan "DA" mai karfina kowa tsorona
yake,dukkan fursunoni da ma'aikata amma sai gashi
andawo andaina tsorona kai ake tsoro ana yi maka
ladabi da biyayya.Ko da jin wannan batu sai farin ciki
ya lullube Imhal ya rungume Zauwadu suka bushe da
dariyar murna tare.Daga can sai Zauwadu ya janye

jikinsa daga cikin na Imhal ya dube shi cikin nutsuwa
a karo na biyu yace Ya kai abokina kayi sani cewa da
dangari akan ci gari,a matsayina na fursuna da ya
shekara ashirin da uku a cikin gidan nan nafi kowa
sanin sirrin kurkukun nan acikin fursunoni domin
babu wanda yayi dadewata kuma nafi kowa sanin irin
ma'aikatan da ya kamata mu hada kai dasu wajen
samun nasarar wannan gagarumin aiki da mukeyi,Ina
nufin dole ne mu zubo ma'aikatan da na tabbatar da
cewa suna da kwadayin abun duniya,to amma inda
matsalar take shine ta yaya zamu iya samo kudaden
da zamu biya ma'aikatan su bamu hadin kai?Abu na
biyu shine,har yanzu baka gaya min yadda zamu iya
ketare tekun da ya zagaye gidannan bayan mun sami
nasarar fita wajensa ba?Sa'adda Imhal ya ji wannan
tambayoyi sai yayi murmushi yace abinda nakeso
dakai shine ka bini a sannu zamuyi komai daki-daki
da idanunka zaka ga amsoshin duk wadannan
tambayoyin da kayi min yanzu.
Abu na farko da nakeso mu farayi shine ina so mu
hada baki da masu dafa abincin gidan nan,su zuba
banju acikin abincin dakarun da suke gadin dakin
shugaban dakarun gidan nan,domin mu samu damar
shiga mu balle akwatin da yake ajiye kudin hidimar
gidannan aciki,na sani cewa akalla baza mu rasa
dinare dubu dari ba acikin wannan akwatin
wadannan kudade sun isa mu siye duk mutanen da
mukeso suyi mana aiki,Zauwadu ya gyada kai yace
tabbas zasu ishe mu,amma ta yaya zamu samu
amincewar ma'aikatan da suke dafa abinci su zuba
banju acikin abincin?Imhal yace baza mu iya yin
wannan aiki mu biyu kacal ba,dole sai mun nemi
hadin kan yan'uwan mu fursunoni akalla mutum
goma,cikin tsananin firgici Zauwadu yace idan muka
gayyato mutane cikin wannan aiki namu za a iya
samun rashin sirri a ciki,acikin mu za a iya samun
munafikin da zai zagaye ya tona asirin mu,Imhal ya
gyada kai yace ai ba kowa zamu tabo ba sai wanda
mukasan ya gari da zaman gidannan kuma yana da
taurin rai gami da sai da rai,haka kuma duk wanda ya
shigo cikinmu zamu gaya masa idan har ya tona
mana asiri aka kamamu hukuncin kisa ne akan
sa,koda jin wannan batu sai Zauwadu yayi murmushi
yace hakika kwakwalwarka tana aiki sosai to idan
muka samu mataimakan ta yaya zamu samu hadin
kan masu dafa abincin?Imhal ya sake murmushi a
karo na biyu yace ka sani cewa masu dafa abincinnan
fursunoni ne yan'uwanmu dole ne mu firgita su mu
kashe daya daga cikinsu

4 Comments On RIJIYA GABA DUBU
avatar
mlm

1 year ago

Reply

Next please

avatar
khadija-1-4

1 year ago

Reply

??????

avatar
muhammad-musa

1 year ago

Reply

Good book

avatar
ismail-9-8

10 months ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment