Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akan cewar kada su kuskura su
bari ya tsere, idan kuwa ya gudu a bakacin ransu su
duka.
Gama tunani ke da wuya sai ya kamu da tsananin
bakin ciki ya fashe da matsanancin kuka, A karshe ya
kudiri aniyar cewa komai rintsi da tsanani sai ya jure
duk irin bala in dake gaban sa domin ya tsira da
rayuwarsa, ya koma gidan kurkukun darul maut ya
ruguje shi kuma ya kone wannan RIJIYA ta gaba dubu
domin a daina azabtar da al umma,Bayan nan kuma
yayi alkawarin cewar sai ya koma gidan Likiciya
Zumaira domin ya dauke tsoho imzanu su gudu
izuwa wata nahiyar daban inda da sannu zai cigaba
da bincike domin ya gano asalin iyayensa da
danginsa, haka dai Imhal yayi ta sakar zuci har dare
ya raba bai sani ba sannan bacci ya kawo masa
mamayar ba zato,
Kashe gari kuwa da safe aka sake kawo masa abinci
da abin Sha mai rai da lafiya ya kimtsa cikin sa,sai
bayan ya huta sosai sannan aka zo aka bude dakin
aka fito dashi a daure cikin sarkoki, aka nufi filin
gasar JARUMTA dashi.
koda aka iso filin gasar da jarumi Imhal a daddaure
cikin sarka, da jama'a suka yi arba dashi sai filin gaba
daya ya rude da shewa gami da tafi.
Gimbiya lamirat da Shumaira na hango shi sai su
duka suka mike tsaye, suka kura masa idanu domin a
wannan rana kyawunsa da siffar jarumtakarsa sun
bayyana a fili muraran,ita dai Gimbiya Shumaira nan
take taji ta kamu da tsananin kaunar sa,bata ma San
sanda ta kama yin murmushi ba a gareshi, ita kuwa
Gimbiya lamirat sai kawai taji zuciyar ta taci gaba da
bugawa da karfi, bugawar da bata San dalilin ta
ba,shin kiyayya ce ko soyayya ta janyo hakan? amsar
da ta kasa baiwa Kanta kenan.
Koda aka kawo jarumi Imhal tsakiyar filin gasar
wanda sama da dakaru dubu dari ne suka kewaye shi
rike da makamai don tabbatar da tsaro harma da
wadanda suka dana kibiyoyi akan baka, kawai jira
suke suga wani yayi ba dai dai ba yasha ruwan
kibbau, aka kwancewa jarumi Imhal dukkanin
sarkokin da ke jikinsa sannan aka bashi takobi da
garkuwa ya rike, nan fa Imhal ya fara waige-waige da
dube-dube domin ya ga abokin gwaninsa, amma bai
ga kowa ba,Alokacin ne sarki taryan ya bushe da
dariyar mugunta ya dubi sarki gurzalu yace,Yanzu
wannan Dan jarumin ne lake tunanin zai iya karawa
da gwarzo na abin alfahari na?Sarki gurzalu yace,Ai a
inda babu kasa nan ake gardamar kokawa, ina naka
jarumin ya fito su kara mu gani,Koda jin haka sai
sarki taryan ya daga kai ya dubi wani barde,take
barden ya daga wata katuwar gudumar danko ya daki
wani katon bandiri, karar bandirin ta cika birnin gaba
daya da amsa kuwwa, Faruwar hakan ke da wuya aka
bude wata katuwar kofa, sai ga sadauki Darwaz ya fito
cikin shigar yaki rike da takobi da garkuwa, Tunda
Imhal yazo duniya bai taba ganin mutum mai
tsananin tsawo, kauri, da murdewar jiki ba irin ta
sadauki Darwaz, nan take zuciyar Imhal ta karaya ya
fara tunanin cewa, ai bazai iya ba da wannan katon
domin da sadauki Darwaz ya karaso ya tsaya daf da
shi sai ya zama Dan mitsitsi akansa kamar an ajiye
dantsako a gaban shirwa, tun kafin a bayar da
umarnin a fara gasar sai Darwaz yasa hannu daya ya
make Imhal, saboda karfin dukan sai da Imhal ya yi
tsalle sama yaje ya gwaru da karfen da aka kewaye
filin gasar ya fado kasa Tim!yana aman jini,Koda
Faruwar hakan sai filin gasar ya rude da shewar
jama'a, Attajiran da suka shiga cacar kudi da sadauki
Darwaz suka kama murna suna ihu da tsalle domin
suna ganin cewar lallai jarumin sune zai lashe gasar
su kwashi tsabar kudi, shima sarki taryan sai ya kama
kyalkyala dariyar mugunta, ita kuwa Gimbiya
Shumaira sai hankalin ta ya dugunzuma ta rude
ainun ta kamu da tsananin tausayin Imhal, har kwalla
ta cika mata idanu.
Ba zato ba tsammani sai aka ga jarumi Imhal ya mike
tsaye zumbur! ya ruga da gudu izuwa kan sadauki
Darwaz sun ruguntsume da azababben yaki suna
masu kaiwa junan su SARA DA SUKA cikin tsananin
zafin nama da juriya da bajinta ta ban al'ajabi.
WAYE ZAI SAMU NASARAR WANNAN GASA
TSAKANIN JARUMI IMHAL DA SADAUKI DARWAZ?
SHIN SARKI GURZALU ZAI SAMU NASARAR KASHE
JARUMI IMHAL YA LASHE GASAR KAMBUN JARUMTA?
SHIN IMHAL ZAI CIKA BURINSA NA RUGUJE
KURKUKUN DARUL MAUT DA KONE RIJIYA GABA
DUBU?YAUSHE NE IMHAL ZAI KOMA BIRNIN MISRA
YA SAKE SADUWA DA TSOHO IMZANU KUMA YA SAN
'YAR UWAR MAHAIFIYARSA LIKICIYA MUZAIRA? Mu
hadu a littafin RIJIYA GABA DUBU 3 don jin cigaban
wannan kasaitaccen labari.
to jama'a zan Dan huta kafin Ku jini a cikin na uku
.
RIJIYA GABA DUBU
Littafi na uku 3
Na Abdulaziz sani m gini
Ebook creator:- Shuraih Usman 99%
Ebook publish by http://hausaebooks.cf

Typing:- Ibrahim S combatant
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 3A
.
Lokacin da jarumi Imhal da sadauki Darwaz suka
ruguntsume da azababben yaki a tsakiyar filin fadar
birnin misra wanda yan kallo sama da mutane
miliyan dari suka kewaye, sai filin ya cika da ihu da
shewar jama'a, nan fa kowa ya cika da mamakin
yadda Imhal ke iya kare hare-haren sadauki Darwaz
har yake mai da martani, sai da aka day lokaci mai
tsawo ana wannan artabu, daya daga cikin jaruman
biyu bai samu nasarar Koda kwarzanar jikin daya
ba,Al'amarin da yasa jikin sarki taryan yayi Dan sanyi
kenan, kuma ransa ya baci, bai San sanda ya mike
tsaye ba daga kan karagar sa ta mulki ya fara yiwa
jarumin sa kirari, abinda sarki taryan bai taba yiba
kenan a tarihin gasa da ake yi tsawon shekaru, Koda
sadauki Darwaz ya ga sarkin sa ya mike tsaye Daga
kan karagar sa yana Koda shi,sai ya fusata ainun ya
kara zage damtse iya karfin sa ya dinga kaiwa Imhal
Sara da suka da dukkan karfin sa,cikin wata irin
sabuwar jarumtaka mai tsananin zafin nama ta
BAZATO, Nan fa shima Imhal ya dinga yin iya kokarin
sa don kare kansa,amma sai ya zamana cewa dakyar
yake iya kare hare-haren, kuma baya iya mai da
martani, Koda ganin haka sai murna ta kama sarki
taryan ya dinga shewa, Ai kuwa sai jama'ar gari suma
suka dinga taya shi,ya zamana cewa babu mai yiwa
jarumi Imhal jinjina a filin, Duk abinda yake faruwa
sarki gurzalu yayi shiru yana guntun murmushi kawai
don yasan wanene Imhal, A gaba dayan filin gasar
babu wanda hankalin sa ya dugunzuma ainun bisa
ganin halin da jarumi Imhal ya shiga sama da
Gimbiya Shumaira, domin duk sanda taga an kai
masa wani mugun gari sai kaga ta kai da kai kamar
ita ake kaiwa, wani lokacin ma har mikewa take yi
tsaye zumbur! kamar zata kwalla ihu,ita kuwa
Gimbiya lamirat kawai tana kallon fadan ne,ba ta ma
San jarumin da take so ba acikin ranta, amma kuma
sanda ta tuno da bayanin da mahaifin ta sarki gurzalu
ya gaya mata cewar idan Imhal ya samu nasarar
lashe wannan gasar JARUMTA sai ya ga bayansu sai
ta ji ta tsani Imhal fiye da komai a duniya, domin
babu abinda take so sama da sarki gurzalu da
mahaifiyarta, ana cikin haka ne sadauki Darwaz ya
kara kuntata Imhal har ya matse shi a waje daya ya
hana shi matsawa, kuma ya cigaba da kai masa Sara
da suka na hauka ba sassauci, ai kuwa sai ya samu
nasarar dankara masa Sara a saman kirjin sa,take
Imhal ya kwalla ihu ya fadi kasa a lokacin da jini yayi
tsartuwa daga kirjin nasa, Koda Darwaz yaga Imhal
ya fadi kasa sai ya kai masa suka da takobi a ciki,
Cikin zafin nama Imhal ya goce ya doki marainansa
da kafa, kawai sai ji akayi Darwaz ya kurma uban ihu
ya fadi can gefe daya, a sannan ne Imhal ya mike
tsaye dakyar jini na zuba kirjin sa yana yin layi,Cikin
sauri ya cire wani yanki dake daure a goshin sa ya
daure raunin don ya rage zubar jinin, a sannan ne
Darwaz ya mike tsaye zumbur! ya kwarara uban ihu
bisa ganin ya samu nasarar yiwa Imhal rauni, A
sannan ne fa sarki taryan ya cigaba dakyakyata
dariyar mugunta, Koda suka had a idanu da sarki
gurzalu sai gurzalu yayi masa murmushin mugunta
ba tare da nuna karayar zuciya ba,Al'amarin da yasa
jikin sarki taryan yayi Dan sanyi, kuma ya daina
kyalkyala wannan dariyar muguntar,A wannan
lokacin Imhal ba karamin kokari yayi ba ya tsaya bisa
kafafunsa, don jiri ne yake dibarsa sakamakon jinin
da ke zuba daga kirjin sa kuma idanunsa suna
lumshewa yana gani dishi-dishi,Koda Darwaz ya lura
da irin halin da Imhal ke ciki sai ya bushe da dariyar
mugunta don yasan cewa yanzu ne zai gama da Imhal
farat daya.
Kawai sai Darwaz ya gyara tsayuwarsa, sannan
sannan ya sake zaro wata sharbebiyar adda a
bayansa wato ya hada makamai guda biyu a hannun
sa yana mai gyara tsayuwarsa gami da fuskantar
Imhal, A sannan ne fa filin gasar ya rude da shewar
jama'a, Attajiran da suke yin caca akan gasar suka
dinga yiwa junansu kirari, Kaso bakwai cikin kaso
goma na 'yana cacar duk sadauki Darwaz suka zaba a
matsayin jarumin su,kaso uku ne kacal suka yi
kundunbala suka zabi Imhal, tun da ake yin caca a
wannan gasar ba a taba zuba kudade masu yawa ba
irin na bana,Da yawa Daga cikin attajiran da suka
shiga wannan caca idan ba jarumin su ne yaci gasar
ba karayar arziki tazo musu kenan.
Lokacin da jaruman biyu suka fuskanci juna, sai filin
gasar yayi tsit! aka zuba Ido don ya ga wanda zai yi
nasara, saboda ansan cewa wannan gamon da za ayi
na karshe ne, Koda Darwaz ya ga shima Imhal cike
yake da burin neman sa'a, sai ya budi baki ya karanta
wadansu Dalasumai na tsafi guda biyu, kawai sai
Imhal yaga wata irin gagarumar iska ta kanannadeshi
tasa ya kasa Koda daga hannun sa,ko matsawa daga
inda yake, kuma sai Darwaz ya rugo izuwa kansa yana
mai daga makamansa sama yana ihu, Abin al'ajabi
shine, babu wanda yaga wannan guguwa wacce ta
kanannade jarumi Imhal face sarki gurzalu, domin
shine kadai yake da karfin ganin sihirin tsafin
Darwaz,Imhal yayi iya kokarin sa akan ya kaucewa
guguwar ya kasa,Al'amarin da ya dugunzuma
hankalin sa ke nan yana ganin mutuwa muraran,
Koda sarki gurzalu yaga abin da ke shirin faruwa sai
yayi nuni da hannun sa izuwa kan guguwar da ta
kanannade Imhal don ya kawar da ita ,amma sai nasa
sihirin tsafin ya ki yin tasiri, Take ya tuna cewar ai Yau
ya manta bai dauro gurunsa na tsafi ba ya barshi a
can cikin wata akwati a dakin da aka sauke shi,nan
take bakin ciki ya rufe shi ya sunkuyar da kansa kas
yana mai rufe fuskarsa don baya son Darwaz ya
samu nasarar kashe Imhal, A dai-dai wannan lokaci
ne hankalin Shumaira ya dugunzuma ainun bisa
ganin za a hallaka jarumin da taji ta kamu da
tsananin sonsa a Yau dinnan kuma farat daya,kawai
sai ji tayi hawayen bakin ciki ya zubo mata.Gaba daya
attajiran da suka zabi Imhal a matsayin jarumin su
suka zuba kudin su na caca akansa sai jikinsu yayi
sanyi, suka ayyana cewar asara tazo musu tunda
gashi suna gani an durfafoshi da gudu za a sare
shi,amma ko motsi ya kasa yi,Koda ya rage bai fi taki
uku ba kacal Darwaz ya iso kan Imhal ba sai ya daka
tsalle sama da nufin ya sare kan Imhal da makaman
dake hannun sa,wato takobi da adda, Kwatsam!ba
zato ba tsammani sai Imhal yaji guguwar da ta
kanannadeshi ta sake shi ta bace bat!t take ya samu
damar sunkuyawa ya kaucewa harin da Darwaz ya
kawo masa ,makaman Darwaz din suka sari iska,
kafin Darwaz ya juyo da baya tuni Imhal ya soka
masa takobi a gadon baya, takobi ta burma gadon
baya ta fito ta cikin sa ,Darwaz ya kwarara ihu saboda
tsananin zugin sukan da akayi masa ,sannan ya fado
kasa yana shure-shuren mutuwa, Ai kuwa sai
attajiran da suka zabi Imhal a matsayin jarumin cacar
su suka kaure da ihu gami da shewar farin ciki,
Gimbiya Shumaira kuwa bata San sanda ta daka tsalle
ba sama don murna ta kama kyalkyala dariya, amma
tana hada ido da sarki taryan sai taga ya kame,
saboda tsananin mamaki da takaici, fuskarsa ta
murtuke babu alamar annuri ko kadan, Sarki gurzalu
da 'yarsa Gimbiya LAMIRAT kuwa, suma sai farin ciki
ya lullube su suka kama yiwa Imhal tafi. Sauran 'yan
kallo kuwa kamewa suka yi kamar gumaka saboda
tsananin mamaki bisa ganin yadda aka gama
dajarumi Darwaz farat!daya, duk da cewar babu
kamar sa a karfin damtse da karfin sihirin tsafi a
garin,shi kuwa jarumi Imhal yayi matukar mamaki
yadda akayi ya tsira daga sharrin wannan guguwar
tsafin, Haka ma sarki gurzalu yayi wannan mamaki,
kuma hankalin sa ya Tashi, ya fara tunanin cewa lallai
akwai wani ma'abocin tsafi da ya taimaki Imhal daga
cikin'yankallo,don haka ya zama wajibi yayi bincike
don ya gano ko wanene, nan take ya ayyana a ransa
cewar yana komawa turakar da aka sauke su zai
daura gurun tsafin sa don yayi binciken.Ana cikin
wannan halin ne aka ga jarumi Imhal ya yanke jiki ya
fadi kasa,Koda ganin haka sai Gimbiya Shumaira ta
yunkura za ta ruga izuwa cikin filin inda Imhal yake,
amma sai sarki taryan ya ruko hannun ta yana mai
daka mata harara, take ta shiga taitayinta ta sunkui
da Kanta kasa cikin alamun kunya.RIJIYA GABA DUBU
Littafi na uku 3
Na Abdulaziz sani m gini
Typing:- Ibrahim S combatant
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 3B
.
A wannan lokaci ne sarki taryan ya umarci likitansa
yaje ya ceci rayuwar Imhal, a guje likita ya isa filin
gasar ya kama aikin sa na ceton rayuwar Imhal tare
da dinke masa saran da Darwaz yayi masa,nan take
aka dauke gawar sadauki Darwaz Daga filin gasar sai
sarki taryan ya ba 'yarsa Gimbiya Shumaira izuwa
cikin gidan sarautar, Al'amarin da yasa filin gasar ya
watse kenan, kowa ya kama gaban sa,shi kuwa sarki
gurzalu da Gimbiya LAMIRAT sai suka wuce izuwa
masaukin sarki gurzalu, shi kuwa jarumi Imhal bayan
likita ya gama dinke raunin da ke kirjin sa yasa masa
magani sai aka dauke shi aka kai Shi izuwa cikin
wannan daki mai kama da kurkuku aka kulle shi.
Lokacin da sarki gurzalu suka isa cikin masaukinsu
suka zauna, sai wata kuyanga ta kawo musu ruwan
inibi suka Sha,a lokacin da fuskar sarki ta cika da
annuri yana ta farin ciki amma sai yaga gimbiya
lamirat tayi shiru tana mai sunkui da Kanta kasa cikin
alamun damuwa, Gurzalu ya dubi LAMIRAT yace,
Yake 'yata,ina dalilin wannan damuwa taki? Koda jin
wannan sai lamirat ta kawo gwauron numfashi ta
ajiye sannan ta dube shi cikin alamun tsananin
damuwa ta ce,Ya kai Abbana akan wane dalili kake
farin ciki alhalin babban makiyin mune ya samu
nasara a wannan gasa? sabo dame kake son lallai
kayi wannan gasa da jarumi Imhal alhalin na gani da
idanunka cewar shi mutum ne mai tsananin sa'a?
shin baka tunanin cewa kana neman kayi ganganci ne
da rayuwarka akan jarumi Imhal? maimakon kai ceci
rayuwar sa kamata yayi kasa a kashe shi,ko a sirrance
ne kai bani dama a daren Yau nayi baddakama naje
har dakin da aka kulleshi na kashe shi.Kafin lamirat ta
gama rufe bakin ta tuni sarki gurzalu ya daka mata
tsawa har ta firgita taji hantar cikinta ta kada,ta Dan
na da baya kadan Daga kusa dashi, Koda yaga ta
firgita sai ya bushe da dariya, sannan ya dubeta cikin
nutsuwa da murmushi yace,Haba yake 'yata, shin kin
manta da ko ni waye ne? NINE FA MURUCIN KAN
DUTSE,WANDA BAN FITO BA SAI DA NA SHIRYA!
NINE SA GUDU, MAGANIN KI GUDU! KUMA NINE
BAKIN TAKOBI MAI RABA MASOYA! Ina mai tabbatar
miki da cewar na gama yin bincike a cikin halwar tsafi
na gano cewa idan har ba ta hanyar wannan gasar
jarumtaka ba,bazan samu damar hallaka shi ba,duk
da cewar na gwada jarumtaka ta da tashi,naga karfin
mu yazo daya, ai yanzu zanyi amfani ne da karfin
sihiri na,na hallaka shi a yayin da muke yin wannan
gasa,ni yanzu Abu daya ne ya shige min duhu, kuma
ba komai bane na fuskanci cewar akwai wanda ya
taimaki Imhal da sihirin tsafi a Yau lokacin da ake
wannan gasa,kuma bansan ko waye ba, amma
yanzun nan zan bincike na gane ko waye.Koda gama
fadin hakan sai sarki gurzalu ya mike tsaye ya shige
cikin kuryar dakin da ya kwana inda akwatinsa ta
ke,da Isarsa gaban akwatin wacce ta kasance katuwar
gaske mai nauyi, kuma wacce ke datse da katon
kwado,sai ya kurma uban ihu, Cikin firgita lamirat da
dakarun sa dake can kofar turakar suka rugo izuwa
cikin dakin, A dimauce LAMIRAT ta dubeshi tace,Me
ya faru ya kai Abbana kai kurma uban ihu haka?
maimakon ya bata amsar tambayarta sai ya juyo a
fusace ya fuskanci wadannan dakaru nasa masu
tsaron dakin yace, Bayan mun tafi filin gasar
JARUMTA waye ya shigo cikin dakin nan? Shugaban
Dakarun ya risina yace, Ya shugabana babu wanda ya
shigo, in baka manta ba kai da kanka na kulle dakin
da mukulli da zaka fita ,kuma yanzu ma da kai dawo
kai ka bude shi da hannun ka... Kafin badakaren ya
rufe bakinsa tuni Sarki gurzalu ya sare takobinsa cikin
bakin zafin nama ya fille masa kai, sai ga jini yana
tsiri izuwa saman dakin ta cikin jijiyoyin wuyan
badakaren, sannan kuma sai gangar jikin ta fadi kasa
rub da ciki,Faruwar hakan ke da wuya sai ragowar
dakarun suka firgita ainun suka dauke gawar
dan'uwansu da sauri suka fice da ita,A sannan ne
sarki gurzalu ya dubi lamirat a lokacin da idanunsa
suka kada suka yi jawur yace,Wani yazo ya sace min
gurun tsafina, maza ki tafi neman wannan barawo a
cikin garin nan,shine wanda ya taimaki Imhal a filin
gasa. Da jin haka sai LAMIRAT ta juya da sauri ta tafi
izuwa can bangaren da turakar sarki taryan take
domin ta sanar dashi abinda ya faru kuma ta nemi
izininsa akan tafiya cikin gari don farautar barawon
mahaifinta.
Lokacin da sarki taryan ya tafi da Gimbiya Shumaira
izuwa cikin turakarsa, bayan Angama wannan gasar
JARUMTA, sai ya tunkude ta ta fada kan wata
doguwar kujera, ya dubeta cikin fushi har muryarsa
na rawa yace,akan me Zaki so jarumin da yake fada
da nawa jarumin?sabo dame Zaki nuna soyayyar ki a
fili gaban jama'a ki zubar da kimarki da mutuncin
gidan nan?Shin kinsan irin makudan kudaden da nayi
asara a wannan gasa bisa kudin da na zuba a cacar
da mukayi ni da sarki gurzalu? Lokacin da sarki taryan
yazo nan a jawabinsa sai gimbiya Shumaira ta sunkui
da Kanta kasa cikin biyayya tace,ka gafarceni ya kai
Abbana, ka sani cewa a rayuwata ban taba son wani
da namiji ba a rayuwata ba face wannan bakon
jarumi, kai da kanka kayi mini tayin 'ya'yan sarakai
guda ashirin da uku a wannan nahiya amma nace
akai kasuwa, idan baka manta ba na gaya maka
cewar, bazan yi aure ba face na samu jarumi mai
tsananin sa'a da JARUMTA, kaga kuwa lallai babu
wanda ya dace dani face wannan bakon jarumi tunda
gashi sa'arsa ta bayyana a fili, tunda gashi ya kashe
jarumin da babu kamarsa, alhalin a zahiri bai isa ya
iya da shi ba.Yayin da sarki taryan ya ji wannan batu
sai jikinsa yayi sanyi, kuma hankalin sa ya
dugunzuma yayi shiru ya kasa cewa komai, kwatsam!
sai ga wani babban hadimansa ya shigo cikin turakar
sa,hadimin ya risina ga sarki taryan yace,ya
shugabana Gimbiya LAMIRAT 'yar sarki gurzalu tazo
yanzu, tace tana son ganinka cikin gaggawa, Koda jin
wannan batu sai mamaki ya kama sarki taryan tare
da Gimbiya Shumaira suka dubi juna sannan ya dubi
hadimin yace, he ka kace ta shigo,nan take hadimin
ya fita sai ga gimbiya LAMIRAT ta shigo fuskar ta a
murtuke babu annuri, kai da gani kasan cewa tana
cikin tashin hankali, LAMIRAT ta risina ga sarki taryan
tace,Ranka ya dade barawo ne ya shiga cikin
masaukin Abbana ya sace masa wani Abu mai
darajar gaske.Koda jin wannan batu sai mamaki ya
turnuke sarki taryan da Gimbiya Shumaira, sarki
taryan ya dubi lamirat yace, Tun da aka gina gidan
sarautar nan tsawon shekaru dari da goma Sha daya
ba a taba yin sata ba a cikin sa sai Yau,lallai ko wane
ne yayi wannan sata ya cika hatsabibin gaske, domin
nasan irin tsaron da yake gidan nan yafi gaban misali,
ko sarkin barayin aljanu yana shakkar yazo yayi sata a
nan, wai shin mene ne abinda aka satar muku? lallai
zan sa a tsananta bincike har a kamo wannan
barawo, kuma ki gayawa mahaifin ki cewar komai
kimar abinda aka sace masa zan biya shi.lokacin da
gimbiya lamirat taji wannan batu sai ta gyada kai
cikin alamun takaici tace,Inda zaka cika gidan
sarautar nan taka da darhami, baza ka iya siyan
abinda aka sacewa ubana ba,ni yanzu abinda ya kawo
ni gareka shine, ka bani izinin shiga cikin gari don
farautar wannan barawo, kuma ka bani dakarun ka
wadanda za suyi mini rakiya, wadanda suka San sirrin
birnin ka sosai, in yaso kayi naka binciken daga baya,
Koda jin wannan batu sai sarki taryan ya sake
kamuwa da tsananin mamaki, kuma hankalin sa ya
dugunzuma ainun, nan take ya tura aka kirawo masa
wani badakare mai suna DARHUS, ya dubeta shi yace,
maza ka debi jama'arka mutum dubu uku Ku tafi tare
da Gimbiya lamirat izuwa cikin gari, lallai ina son Ku
bincika gida-gida,lungu-lungu da duk wani sako da ke
cikin garin nan domin Ku gano barawon da yayi wa
mahaifin ta sata har cikin masaukin da na bashi, kada
Ku dawo gareni face kun kamo wannan barawo, idan
bakwa son Ku fuskanci fushi na.nan take DARHUS ya
risina yace, Angama, kawai sai ya juya da sauri ya fice
daga cikin turakar, Gimbiya lamirat ta bishi da sauri.
A wannan rana dai sai da hankalin gaba daya
mutanen birnin misra ya tashi, domin sama da
dakaru dubu arba'in DARHUS ya diba bisa jagorancin
gimbiya LAMIRAT suka dinga shiga gida-gida,unguw
anni da kasuwanni suna dukan mutane suna caje
kayayyakin su ana neman abinda aka sacewa sarki
gurzalu.RIJIYA GABA DUBU
Littafi na uku 3
Na Abdulaziz sani m gini
Typing:- Ibrahim S combatant
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 3C
.
Duk gidan da aka shiga sai an tarwatsa kayan ciki anyi
filla-filla da su kin a duk Inda aka riski bako tasa ta
same shi domin anfi tsananta bincike a kansa saboda
sai anfara yi masa dukan tsiya anyi laga-laga da shi
sannan ma za a fara tuhumarsa, Tun safe aka fara
wannan bincike amma har dare ya raba ba a ga
abinda ake nema ba,kuma ba a ga wanda ya dauke
abin ba,Bisa dole su Gimbiya lamirat suka hakura
suka koma gidan sarautar suka sanar da sarki
gurzalu da sarki taryan abinda ake ciki, nan fa
hankalin sarakunan ya kuma dugunzuma fiye da ko
yaushe, musamman ma sarki gurzalu wanda ya
tabbatar da cewar duk burinsa na duniya ya rushe
idan har ba a ga wannan Abu da aka sace masa
ba,nan fa sarki taryan ya sake dimaucewa bisa ganin
yadda hankalin sarki gurzalu ya Tashi ainun, don
haka sai ya sake baza dakaru izuwa cikin birni da
kauye kai har izuwa cikin dazuzzuka ma yace duk inda
aka ga wadansu baki a kamo su azo dasu Koda kuwa
sun kasance fatake ne masu wucewa,haka kuwa
al'amarin ya kasance aka yi ta kamo baki ana kai su
kurkuku ana kullewa, har sai da babban kurkukun
birnin ya cika fal sannan aka dinga kaiwa sauran
kananan gidajen maza da ke wurare da bam.A
wannan dare dai sarki gurzalu bai yi bacci ba har gari
ya waye bisa tsananin tashin hankalin da yake ciki.
Ba wani abu aka sacewa sarki gurzalu ba face
gurunsa na tsafi wanda shine kadai abinda ya dogara
da shi akan cewar yana bashi sa'a a gasar jarumtakar
da akeyi a birnin misra tsawon shekaru, abinda ya fi
razana shi shine, yanzu yaya zai yi da batun shiga
wannan gasa,ya sani cewa saura wasa biyar ga
jarumi Imhal su hadu a filin gasa su fafata, Koda yake
dai yanzu Imhal bashi da lafiya, dole ne yayi jinya ta
tsawon Koda kwana bakwai ne,kuma ya San cewa ko
babu wannan gurun tsafi a tare dashi ba ya shakkar
karo da Imhal domin Idan har bai samu nasarar
kashe shi ba sai dai ayi RAGAS indai da zallan karfin
damtse da kwarewar yaki za suyi fadan, babban abin
tashin hankali shine, barawon da ya sace gurun tsafin
sa ba karamin sihirin tsafi ne da shi ba tunda har ya
iya shiga har cikin masaukinsa ya sace gurun ba tare
da asirin sa ya tonu ba kuma tabbas zai cigaba da
taimakon Imhal a cikin wannan gasar jarumtaka da
ake yi har ya kai ga nasara.
Abinda ya fadowa sarki gurzalu a rai shine, yana da
zabi guda biyu rak! Ko dai ya koma can birnin Kisra ya
shiga halwar tsafin sa yayi bincike don ya gano ko
waye wannan barawo da kuma inda yake kafin a
cigaba da gasar JARUMTA, ko kuma duk yadda za ayi
ya gano barawon kafin gasar tazo kansa,nan fa sarki
gurzalu ya rasa hukuncin da ya kamata ya yanke,
Babu yadda sarki taryan bai yi ba don ya San abinda
aka sacewa sarki gurzalu amma abun ya gagara,
domin yaki ya gaya masa,Dama ya dameshi da
tambaya sai yace dashi, Abinda aka sace mini yafi
komai da kowa daraja a idanu naka wannan duniya,
tunda sarki taryan yaji wannan batu sai yayi shiru bai
kara yi masa magana ba.kashe gari kuwa tun kafin
hasken rana ya fito su Gimbiya lamirat suka sake
bazama izuwa cikin gari neman barawon sarki
gurzalu.
Al'amarin Gimbiya Shumaira kuwa,a wannan rana sai
ts rasa sukuni, domin ta kasa zaune ko tsaye, kuma ta
kasa yin bacci, ba komai ne ya janyo hakan ba face
duk sanda ta runtse idanunta bata ganin komai face
jarumi Imhal, nan take taji tunani da begensa sun
addabe ta kuma taji bata da sauran kwanciyar hankali
idan bata je ta gan shi ba,domin gani take kamar
mutuwa zai yi sakamakon wannan Sara da jarumi
Darwaz yayi masa a kirji, nan fa Shumaira ts fara
tunanin hanyar da zata ni taje ta ga jarumi Imhal a
can inda aka tsareshi, Samun wannan dama kuwa ba
karamin aiki bane saboda babu wanda yake da ikon
zuwa wannan wuri face sarakunan biyu wato sarki
taryan da sarki gurzalu domin dokar da aka kafa
kenan tun jiya da aka kai Imhal aka tsare, Koda
Shumaira taga tunanin yayi mata yawa ta kasa komai
sai ta fito daga cikin turakar ta,A wannan lokaci da ko
wanka ba tayi ba,kuma tana sanye ne da rigar bacci
wacce ke nuna dukkan siffofin jikinta, kawai sai ta
kama kai kawo a cikin harabar turakar ta ta inda
kuyanginta ke ta kai kawo suna

4 Comments On RIJIYA GABA DUBU
avatar
mlm

1 year ago

Reply

Next please

avatar
khadija-1-4

1 year ago

Reply

??????

avatar
muhammad-musa

1 year ago

Reply

Good book

avatar
ismail-9-8

10 months ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment