Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a gaban idanunsu sannan
mu umarce su da abinda muke bukata kuma mu
gargadesu cewa duk wanda ya tona asirinmu acikin
su shima mutuwa zai yi,koda jin haka sai Zauwadu

yayi dariyar farin ciki yace tabbas indai mukayi haka
komai zai tafi dai-dai to amma fa kasani idan muka
debo wadannan kudaden acikin sa'a daya asirinmu
zai tonu don a sannan ne shugaban dakarun zai
dawo,koda jin haka sai Imhal yayi tsaki ya mike tsaye
zumbur a fusace ya dakawa ALZauwadu tsawa yace
kada ka sake yimin tambayar komai har sai bayan mu
samu nasararr fita daga gidannan.Gama fadin haka
ke da wuya sai suka ji an kada kararrawar zuwa cin
abinci nan take dakaru suka fara bude kofofin
dakunan fursunonin,ana bude dakin su Imhal sai
suka wuce da sauri suka zama akan gaba suka riga
kowa zuwa inda masu dafa abinci suke suka shige har
cikin dakin girkin ba tare da dakaru sunga lokacin da
suka shiga ba,suna shiga suka iske masu dafa abincin
akan aikinsu kawai sai Zauwadu ya kama kan daya
daga cikin su ya murde ya yar da gawrsa a kasa,cikin
tsananin tsoro sauran ma'aikatan suka zube a kasa
suna rokon su ayi musu rai kawai sai Imhal ya dube
su yace idan kuna so ku tsira da rayuwarku ayau ku
zuba banju acikin abincin da za a kaiwa masu gadin
shugaban dakarun gidannan idan kuma kuka gayawa
wani wannan sirrin duk sai kun mutu lallai kuyi
wannan aikin cikin dakiku kadan,koda gama fadin
haka sai Imhal da Zauwadu suka fice daga cikin dakin
suna fita kuwa suka yi arba da wani babban badakare
akayi kallon-kallo nan take jikin badakaren ya bashi
cewar da akwai abinda suke shiryawa.
TO JAMA'A ANAN NAZO KARSHEN LITTAFI NA DAYA
.
Marubucin yace
SHIN SU IMHAL ZASU SAMI NASARAR FITA DAGA CIKIN
WANNAN KURKUKU
.
YAYA LABARIN TSOHO IMZANU DA MUZAIRA
.
SHIN SARKI GURZALU ZAI SAMU NASARAR HALLAKA
IMHAL A GASAR JARUMTA NA BIRNIN KISRA
.
Marubucin yace domin jin wayannan amsoshi sai mu
hadu a littafi na biyu
.
Nine Shuraih USman
Inkiya Shuraih 99% dana kawo maku
Nake cewa sai kun jini a Littafi na biyu gobe

RIJIYA GABA DUBU
Littafi na biyu 2
Na Abdulaziz sani m gini
Ebook creator Shuraih Usman
Ebook publish by http://hausaebooks.cf
.

Typing:- Ibrahim S combatant
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 2A
.
Da isar saiyaru cikin gidan kurkukun bayan ya wuce
kofofi goma sha daya sai ya wuce kai tsaye izuwa
dakin tuhuma yana ta murmushin mugunta,da isar sa
kofar dakin sai masu gadin dakin suka rusuna suka
gaishe shi,ko kallon su bai yi ba ya daka musu tsawa
yace Maza ku budemini kofar da sauri na shiga,cikin
hanzari daya daga cikin masu gadin yasa kuba ya
bude kofar ya kunna kai,ashe wadannan masu gadin
duk na bogi ne acikin shigar kayan dakaru suna daga
cikin dakaru guda ashirin din da Imhal suka zaba
domin su taimaka musu wajen samun nasarar
guduwa daga kurkukun.Da shigar saiyaru cikin dakin
sai yayi arba da Zauwadu zaune akan kujerar da aka
saba dora masu laifi an daure hannayensa da
kafafunsa da sarkoki ga badakare daya a tsaye akansa
yana dukansa da kulki har ya fasa masa baki da hanci
jini na suba.koda ganin haka sai saiyaru ya bushe da
dariyar mugunta sannan ya dubi badakaren yace
dakata haka yanzu kuma nine zanyi masa tawa
azabar,ya kai Zauwadu kayi sani cewa yau ne ajalinka
zai tabbata a hannnuna tunda har ka karya dokata ka
sake haddasa fada tsakanin fursunoni,hakika yau
gawrka rabon kifayen dake cikin teku ne.yana gama
fadin haka sai ya daga kulkinsa ya nufi Zauwadu da
nufin ya buga masa a kansa,ba zato ba tsammani sai
kawai wannan badakaren dake tsaye ya shammaci
saiyaru ya maka masa kulki akan kunnensa na
hagu,take saiyaru ya sulalae kasa sumamme.Koda
saiyaru ya farfado sai ya tsinci kansa a zaune akan
kujera wacce ake dora fursunoni idan za a yi musu
azaba an daure hannayensa da kafafunsa ta
baya,Imhal da Zauwadu na tsaye akansa sanye da
kayan dakaru,shi dai Zauwadu kayan saiyaru ya sanya
sannan ya sanyawa saiyaru nasa na fursunoni.Koda
saiyaru yaga haka sai ya tuntsire da dariyar mugunta
kuma ya turbune fuska yace kun bata lokacinku a
banza domin baku isa ku iya guduwa daga cikin gidan
nan ba,nan gidan mutuwa ne gidan da babu wani
fursuna da ya isa ya tsira da rayuwarsa koda kun
gudu sai an kamo ku an dawo daku idan ma sanyin
teku da halittun cikinsa basu hallaka ku ba.Koda
gama fadin haka sai saiyaru yaci gaba da kyalkyala
dariyar mugunta,cikin fushi Zauwadu ya daga katon
kulkin nan na saiyaru ya maka masa shi a ka,take kan
saiyaru ya fashe har kwakwalwarsa tayi fallatsi,koda
suka ga saiyaru ya mutu sai Imhal ya dubi Zauwadu
yace to fa yanzu duk nasarar mu tana hannunka duk
yadda za a yi kada ka kuskura ka bari a gane cewa kai
ba saiyaru banen,hatta muryarka sai ka karyar da ita
irin ta saiyaru tunda daman can kuna kama da juna a
fuska da yanayin jiki.Zauwadu ya risina ga Imhal yace
yakai abokina kuma shugabana a wannan gida na
darul maut,ina mai tabbatar maka cewa baza a taba
samun wata matsala ba daga gareni sai dai daga
sauran yan'uwanmu fursunoni guda ashirin wadanda
muka janyo cikin wannan aiki,ni dai alkawari daya
nakeso kayi mini,koda jin haka sai mamaki ya kama
Imhal yace wane alkawari kakeso nayi maka?koda jin
wannan tambaya sai Zauwadu ya sanya hannu acikin
aljihunsa ya dauko wata sarka ta dinare ya damkawa
Imhal a hannunsa yace,Wannan sarka ce ta matata
wacce muke tsananin son juna fiye da hangen mai
hange,a ranar da aka daura aurenmu da ita acikin
birnin kisra dakarun sarki Gurzalu suka zo su dubu
uku suka rufeni da masifaffen duka har sai da suka
sumar dani,ina ji ina gani aka Rabani da amaryata
SUHAILA aka sa mini sarka a wuyana,hannayena da
kafafuna aka tafi dani suhaila tana kuka da
ihu.Wannan shine asalin rabuwata da suhaila yau
tsawon shekaru ashirin da bakwai kenan,suhaila na
raye ko ta mutu ban saniba.ina son duk sanda ka
dawo cikin birnin kisra komai dadewa ka nemi
suhaila a unguwar Sharkas ka bata wannan sarka
idan har na rasa rayuwata a kokarin guduwarmu
daga nan,idan kuma na tsira da rayuwata to zan karbi
sarkata domin nayiwa suhaila alkawarin cewar indai
ina raye komai daren dadewa sai na dawo gareta
,amma idan ta ga an kawo mata sarkarta to bana
raye.Koda Zauwadu yazo nan a zancensa sai hawaye
ya zubo masa,Al'amarin da ya karya zuciyar Imhal
kenan shima yaji ya kamu da tausayin Zauwadu har
kwalla t acika masa idanu,nan take dai suka fito daga
cikin dakin tuhuma Imhal ya sanya sarkar suhaila a
cikin aljihunsa suka kullo kofar dakin ,masu gadin
dakin mutum biyu suka rufa musu baya.
Duk ta inda su Zauwadu suka zo wucewa sai ka ga
ana gaishe su sabo da ana zaton saiyaru ne,hatta
muryar Zauwadu ta amsa gaisuwar sai ta zama iri
daya sak da ta saiyaru,su kansu su Imhal sai da suka
cika da tsananin mamaki bisa yadda suka ji Zauwadu
ya iya mayar da muryar tasa haka,haka dai suka
cigaba da tafiya har suka iso dakin da ake ajiye
gawarwakin fursunonin mutum hudu da suka mutu a
sanadiyyar fadan da akayi a dakin cin abinci,kawai sai
Zauwadu ya bada umarni a debo gawarwakin a dora
su akan amalanke domin a futar dasu gaba daya daga
gidan a watsa a teku,nan take kuwa dakaru suka cika
wannan umarni daya bayan daya fursunonin nan
guda ashirin abokan aikin su Imhal suka dinga
shigowa cikinsu suna take musu baya.dama su duka
sunyi shigar dakarun gidan kurkukun,haka dai su
Imhal suka cigaba da tafiya acikin kurkukun suna tura
amalanken gawa ana bude musu kofofi,duk inda suka
zo da zarar anga saiyaru akan gaba sai kaga anbude
musu kofa da sauri har suka shige ta cikin kofofi
goma sha biyu na kurkukun kuma duk kofar da suka
fita sai an mai da ita an rufe.
Suna fitowa daga cikin kofa ta karshe sai suka yi arba
da dandazon dakarun dake tsaron gidan kurkukun,a
gefe daya kuma ga jirgin ruwa da ma'aikatan
kurkukun ke shiga idan zasu je karbo abinci ko wani
kaya acikin birnin kisra.Su dai masu gadin kurkukun
dakaru ne kimanin guda dubu arba'in,kuma ko
yaushe acikin shirin yaki suke dauke da muggan
makamai,koda suka yi arba da juna tsakanin su Imhal
da masu gadin sai aka tsaya ana kallon-kallo,in ba
don ma shugaban dakarun ya hango saiyaru akan
gaba ba da tuni ya baiwa yaran nasa umarni su afka
musu.
Cikin karamar murya Imhal ya matso daf da Zauwadu
yace dashi kada ka kuskura ka matsa kusa da dakarun
can,domin sai shugabansu ya gane cewa kai ba
saiyaru bane,daga nan zaka yi musu magana ka gaya
musu cewa zamu tafi watsa gawar fursunoni ne
teku.Koda jin wannan umarni sai Zauwadu ya daga
murya ya dubi shugaban dakaru yace ya kai Murwatu
kayi sani cewa yau an samu mutuwar fursunoni har
guda hudu,sabo da haka ina son ku bani jirgi na zuba
su a ciki sai na isa tsakiyar teku sannan na zubar dasu
domin na tabbatar da cewa sun zama abincin kifayen
ruwa.Koda jin wannan batu sai Murwatu ya turbune
fuska ya dakawa saiyaru tsawa yace,Kai saiyaru sabo
dame yau zaka zo mana da sauyin yanayin aiki? A
aikin tarihin gidan nan tsawon shekaru arba'in da
kafuwarsa ba a taba yin hakan ba,duk fursunan da ya
mutu daga nan ake jefa gawarsa cikin tekun,idan
baza ku iya jefa gawarwakin ba daga nan to fa sai dai
ku hakura ku koma da gawarwakin ku,duk wanda yayi
wani yunkuri cikin ku kuwa zamu far masa.
Koda jin wannan batu sai hankalin su Imhal ya
dugunzuma ,suka rasa abinda ke musu dadi domin
ga dukkan alamu sun sha wahalar banza kenan bisa
duk irin kokarin da sukayi suka samu nasarar fitowa
har kofar karshe ta gidan kurkukun DARUL MAUT.
Cikin tsananin damuwa da karayar zuciya Zauwadu ya
dubi Imhal yace ya kai abokina yanzu mene abin yi?
Imhal yace Bamu da abin yi face mu yaki su Marwatu
ko mu ko su!
Cikin firgici Zauwadu yace Baka da hankali ne,ta yaya
mu ashirin da biyu zamu iya yakar dakaru dubu
arba'in?
Imhal yace bamu da wani zabi wanda ya wuce
hakan,ko dai mu yake su ko kuma mu jefa kanmu
acikin tekun nan mu hallaka shine kadai gatan da
zamu yiwa kanmu,ya kai abokina kai sani cewa
faduwar gaba asarar namiji ce,yau ne za muyi yaki da
dukkan karfinmu na jiki da karfin zukatanmu,ko
mutuwa mukayi mun bar abin fadi.Ko kuwa ka zabi ka
koma cikin darul maut a cigaba dq gana maka azaba
har ka mutu tunda kasan cewa ko kadan baza ayi
mana sassauci ba tunda mun kashe saiyaru?koda
Zauwadu da sauran fursunonin suka ji wannan batu
sai nan take suka ji dukkan tsoro ya kau daga cikin
zukatan su.
Friends kuyi hakuri fa 2days kun jini shiru wallahi
mkaranta ne ya boyeni kuma makarantan ma boarding
Yanzu haka yaune na dan dawo gida
Shiyasa nace bazan dan yi maku post
Ammafa ban dauki alkawarin na gobe baRIJIYA GABA DUBU
Littafi na biyu 2
Na Abdulaziz sani m gini
Typing:- Ibrahim S combatant
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 2B
.
Lokaci guda su duka suka daga kulakensu,sannan
suka ruga izuwa kan dandazon dakarun suna masu
kurma uban ihu,ai kuwa suma wadan nan dakaru su
dubu arba'in sai suka zare takubban su suka ruga
gare su.ana haduwa aka kacame da azababben yaki. a
kofar gidan na darul maut.Kaico hakika idan mutum
yaga mutuwa muraran to fa sai inda karfinsa ya
kare,duk da cewar su Imhal yan kalilan ne a cikin
wadannan dakaru sai gashi suna ragargazarsu don
duk inda suka sa gaban su sai dai kag maza na
zubewa kasa alokacin da jini ke feshi da
fantsama,kuma ihun mazaje da karafkiyar karafa ta
cika dodon kunne.Koda aka samu dakika dari biyu
ana wannan gumurzun sai labari ya sauya sabo da
sarkin yawa yafi sarkin karfi,nan fa dakaru suka fara
samun nasarar saran jikin fursunonin nan,jikinsu na
darewa suna ihu amma sabo da naci gami da taurin
rai sunki su fadi kasa,a hakan suke cigaba da yaki.Sai
dai kaga jikin fursuna yayi kaca-kaca da sara da suka
tamkar yayi wanka a kogin jini amma shima bai fasa
ragargazar maza ba,wani lokaci ma har faduwa suke
kasa sakamakon jiri dake dibarsu amma sai kaga
suna mikewa tsaye suna cigaba da yakin.
Koda shugaban dakarun ya ga ana ta ragargazar
yaransa kuma ya kasa fahimtar bangaren dake
samun nasara a tsakanin mutum ashirin da biyu
kacal da kuma mutum dubu arba'in sai ya fusata
ainun ya kutsa cikin fursunonin nan da karfin tsiya
cikin tsananin kwarewar yaki ya dinga fillewa
fursunonin kawuna suna zubewa kasa matattu.
Kafin Zauwadu da Imhal su ankara da abinda yake
faruwa tuni ya kshe musu mutane goma sha biyu ya
zamana cewa saura goma kacal,koda Imhal ya juyo
yaga gawarwakin jama'arsu a kasa a lokacin da gaba
daya jikinsa ya rine da jinin dakarun da ya kashe sai
ya kwarara uban ihu ya kara kaimi yana mai cigaba
da sara da suka cikin tsananin zafin nama mara
misaltuwa sai gashi yana yiwa dakarun mummunar
barna.
Shima Zauwadu da yaga Imhal ya kara zage damtse
sai shima yayi koyi dashi suka haukace suna ta
daukar rayuka,Koda shugaban dakaru Murwatu yaga
haka sai ya daka tsalle sama kamar an cilla shi daga
cikin kibiya ya dira a gaban Zauwadu ya tare shi suka
ruguntsume da azababben yaki.
Wohoho! idan tsagwaron karfi ya hadu da kwarewa
akwai tashin hankali,kai koda ga dan kallo ma cikin
firgici da tashin hankali zai iya kallon wannan
gumurzun.Sai da Marwatu da Zauwadu suka shafe
dakiku masu yawa suna kaiwa juna mugayen hare-
hare na sara da suka basu samu nasarar komai ba.
A wannan lokaci kuwa Imhal ya samu nasarar bazar
da dakaru dubu ashirin a kas,ragowar dubu ashirin
din ma sun razana dashi ainun sun fara ja da baya
duk da cewa wasun su ya sassare su amma sabo da
naci sun ki hakura dada yi masa kawanya suke domin
suyi masa rubdugu
A bangaren Marwatu da zauwadu kuwa,lokacin da
suka fafata ainun suka ga babu wata nasara sai suka
ja da baya sukayi cirko-cirko suna haki da kallon juna
kamar wadan su zakaru,kowannensu na tunanin irin
dabarar da zai sauya don ya samu nasara akan
abokin yakinsa.kamar hadin baki suka zare
takubbansu suka daga sama lokaci guda suka rugu
izuwa kan juna suna kururuwa,koda ya rage saura bai
fi taku uku ba su hadu sai kowannensu ya daka tsalle
sama suka kaiwa juna mummunan hari.Cikin sa'a
Murwatu ya sokawa Zauwadu takobi a kahon
zuciyarsa,shi kuwa Zauwadu ya soka masa a gefen
cikin sa,suka rikito kasa a matukar galabaice jini na
zuba a jikin su.
Zauwadu ya baje a kasa wanwar ya kasa tashi yana
aman jini da karkarwar jiki,shi kuwa Marwatu sai ya
mike tsaye ya yage rigar jikinsa ya daure raunin cikin
nasa don tsaida zubar jini.
Koda ya dubi Zauwadu yaga yana kakarin mutuwa
kuma ya waiga yaga shima Imhal ya fara gajiya ainun
tsabar naci ne da tsananin juriya yasa yake cigaba da
yakin sai ya bushe da dariyar farin ciki ya dubi
zauwadu yace Ai babu yadda za ayi ku samu nasarar
guduwa daga nan har ku tsira da rayuwarku,shekaru
arba'in baya haka muke gadin gidan nan ku duka sai
kun zama gawa,saura Imhal shi kadai a tsaye shima
kuma yanzun nan zan koma na gama dashi kamar
yadda na gama dakai.
Koda jin wannan batu sai hawayen bakin ciki ya
zubowa zauwadu ya dubi gawarwakin 'yan uwansu
fursunoni dake kwance a kasa,kawai sai ya yunkura
cikin matukar karfin hali ya bushe da dariya ya dubi
marwatu yace,Tabbas mutuwa zanyi amma ko ba
komai na jagoranci fursunoni mun karya alkadarin
gidannan tunda gashi har mun samu nasarar fitowa
daga cikinsa alhali babu fursunan da ya taba
fitowa,ko ba komai kai marwatu zan mutu na barka
da tabon yankan takobina a cikinka.
Gama fadin haka keda wuya sai suka ji karar bude
kofofin kurkukun guda goma sha biyu gami da gudun
sawaye alamar cewa dakarun da ke cikin gidan sun
faarga da mutuwar shugabansu saiyaru wanda aka
bar gawarsa a dakin tuhuma don haka fitowa za suyi
waje su kawowa su marwatu dauki.
Koda Imhal ya jiyo sautin gudun dakarun daga cikin
kurkukun sai ya zabura ya falfalo da azababben gudu
izuwa inda su marwatu suke ya buda dakarun nasa
da karfin tsiya yana saransu da banke su kai kace
tamkar bai taba gajiya ba ko kuma a sannan kuma a
sannanne ma ya fara yakin.
Kafin marwatu ya juya ya tari Imhal tuni Imhal ya
dako tsalle a sama ya doki gadon bayansa,sabo da
karfin dukan sai da marwatu yayi tsalle sama ya bar
kan tsuburin gaba daya ya fada cikin tekun,koda
ganin haka sai ragowar dakarun nasa gaba daya suka
ruga zuwa bakin tekun domin su ceto rayuwar
marwatu.
Damar da Imhal ya samu kenan ya sunkuya ya dauki
zauwadu ya saba shi ae kafada ya ruga da baya izuwa
inda jirgin ruwa yake ya daka tsalle ya dirga acikin
jirgin ruwan ya warbar da zauwadu a ciki sannan
yasa takobinsa ya sare igiyar da ta daure
jirgin,aikuwa sai igiyar ruwa ta kada jirgi sai gaba.
a dai dai wannan lokaci ne dakarun cikin kurkukun
suka karaso kofar gidan a guje suna da yawa kuma a
sannan ne aka tsamo marwatu daga cikin tekun aka
dawo dashi kan tsibirin.
Koda marwatu ya kyalla ido ya hango su Imhal acikin
jirgi nesa kadan da tsibirin sai ya kwarara uban ihu
yace A ruga a debo karnukan gidan,nan take kuwa
aka je aka debo karnukan,Marwatu da karnukan tare
da wadansu dakaru kimanin mutum dari biyu suka
shiga wani jirgin dabam suka bi bayan jirgin Imhal.
Lokacin da Imhal yaga igiyar ruwa ta kada jirginsu
yayi gaba sa ya dawo inda ya warbar da Zauwadu ya
iske shi yana ta kakarik mutuwa bai mutu ba,Imhal ya
durkusa daf dashi ya kama hannayensa ya rike a
lokacin da hawaye ya zubo masa ya dube shi yace
"Haba ya kai abokina,sabo dame zaka tafi ka barni
alhalin gashi mun sami nasarar guduwa daga
kurkukun darul maut?" koda jin wannan batu sai
Zauwadu yayi kakin jini ya tofar sannan ya dubi Imhal
cikin karfin hali yace"ya kai abokina ina mai farin ciki
da ya zamana cewa kai kadai ka tsira da rayuwarka
daga cikin mu ba don komai ba sai don nasan cewa
ka samu damar da zaka cika alkawarin dake tsakanin
mu, duk ranar da ka riski matata suhailat ka bata
labari irin rayuwar da mukayi a cikin kurkukun darul
maut da yadda ka zama babban abokina kuma
masoyina alhalin da farko mun kasance makiyan
juna,ka sanar da ita yadda akayi muka samu nasarar
guduwa daga wannan masifaffen kurkuku har izuwa
sanda ajalina ya riskeni,ya kai Imhal idan kayimin
haka ka gama yimin komai,kuma cikin kabarina zanyi
bacci acikin kwanciyar hankali batare da bakin ciki ko
nadamar komai ba,sabo da ko ba komai matata tasan
cewa na mutu a filin daga a matsayin gwarzon
jarumi,ka sani cewa ba wani laifi nayi baaka kawoni
kurkukun darul maut face kawai na hana dakarun
sarki Gurzalu zalunci a watavrana sanda suka shigo
cikin gari suka kashe wani attajiri suka kwashe
dukiyar gidansa kaf,suna shirin kashe iyalinsa ne na
afka musu na ragargaje su suka gudu,nan take na
taimaki iyalan attajirin na kaisu tashar jirgin ruwa
suka hau jirgi suka bar garin gaba daya,tun daga
wannan rana sarki Gurzalu ya dinga farauta ta ina
buya har izuwa ranar da tsautsayi yasa aka zo aka
kamani ranar da na auri suhaila" kodaZauwadu yazo
nan a zancen sa sai yayi wa Imhal murmushin karshe
sannan idanunsa suka kafe gaba daya jikinsa ya
sandare ya zama gawa.Koda ganin haka sai Imhal ya
kwanta akan gawar zauwadu ya rungumeta yana mai
fashewa da matsanancin kukan bakin ciki kamar ba
zai taba dainawa ba, sai da Imhal yayi kuka har ya
gaji barci ya dauke shi bai sai ba,a lokacin da igiyar
ruwa ta ci gqba da kada jirgin acikin teku yayi ta tafiya
ba sassauci.
.
RIJIYA GABA DUBU
Littafi na biyu 2
Na Abdulaziz sani m gini
Typing:- Ibrahim S combatant
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 2C
Al'amarin su marwatu kuwa,wadan da suka hawo
wani jirgin tare da mugayen karnuka kimanin guda
arba'in sai suka nemi jirgin su Imhal suka rasa a cikin
tekun domin ya bace musu sakamakon iskar da ta ie
kadawa mai karfin gaske ce gami da hazon da ake yi
mai duhun gaske,amma sai suka cigaba da tuka jirgin
nasu a haka,sai da suka kwana uku suna tafiya a cikin
teku sannan suka iso bakin gaba a wata sakaliyar
safiya,ai kuwa suna isowa suka yi kicibis da jrgin su
Imhal a gefen tekun,cikin hanzari murwatu yasa aka
saki wadan nan karnuka suka ruga izuwa cikin jirgin
Imhal suna nemansa suna shinshine-shinshine,A
lokacin ne murwatu da dakarunsa suka iso gaban
jirgin suka caje cikinsa kaf amma basu ga Imhal ba
sai alamar jinin zauwadu da ya zuba a kasa wanda
har ya bushe,Kawai sai marwatu ya dago kai ya dubi
dakarunsa yace Duk yanda akayi Imhal yana nan cikin
dajin nan bai yi nisa ba amma abokinsa zauwadu ya
mutu domin babu mutumin da zai zubar da jini mai
yawa haka ya rayu,yanzuzamu bazama cikin wannan
daji duk inda Imhal yake sai mun riske shi mun kashe
shi,sai na cire kansa na tafi dashi izuwa darul maut
domin sauran fursunonin gaba daya su gani ya zama
gargadi a gare su don kada wani yace zai kara
yunkurin gudu anan gaba,kuma nasan cewa sai sarki
Gurzalu ya daukaka ni ya bani dukiya mai yawan
gaske sakamakon wannan gagarumin aiki da zanyi kai
inda hali ma a araye nake so na kamo Imhal domin
na mayar dashi cikin darul maut mu sake tsare shi
sabo da sarki ya fi son su sake haduwa a gasar
jarumtaka wacce za ayi a birnin misra nan da cikar
kwana goma sha daya,maza ku saki karnukan nan
subi sawun Imhal domin suna iya jin kamshin mutum
komai tazarar da ya basu kuma suna da karfin gudun
da bai isa ya tsere musu ba.Koda jin wannan umarni
sai dakarun dake rike da karnukan suka sake su suka
sake rugawa izuwa cikin dajin suna masu haushi da
falfala azababben gudu su marwatu suka bi bayan
karnukan da gudu.Marwatu na cikin yin gudu sai
raunin da ke gefen cikinsa ya motsa yaji wani
azababben zafi da zugi ya shige shi,bai san sanda ya
fadi a kasa ba,nan da na dakaru suka yanyame
shi,koda ya kwaye rigarsa sai yaga ashe dinkin raunin
ne ya farke,cikin tsananin takaici marwatu ya kwarara
uban ihu ya dubi dakarun yace Maza ku tafi farautar
Imhal kada ku dawo nan sai tare dashi,nan take kuwa
suka bi bayan karnukansu da gudu shi kuwa marwatu
sai ya bude jakar guzurinsa ya dauko zare da allura
gami da garin magani domin ya sake gyara rauninsa.
Al,amarin Imhal kuwa,a ranar da jirgin ya kawo shi
gabar teku sai ya dauko gawar zauwadu ya fito da ita
daga cikin jirgin ya nausa da ita izuwa cikin daji,sai da
yayi tafiya mai nisa ya iso gaban wani katon dutse
sannan ya sauke gawar ya haka kabari ya binne ta.A
sannan ne ya kurawa kabarin idanu yana tuno duk
abubuwan da suka faru a baya tsakaninsa da
zauwadu a cikin darul maut,kawai sai hawaye ya fara
zubo masa,yana cikin wannan hali ne ya jiyo sautin
haushin karnukan nan na darul maut,da yake yasan
irin haushin nasu kuma ya san tsananin gudunsu da
irin mugun horon da aka basu sai hankalinsa ya
dugunzuma ainun,kawai sai ya mike tsaye zumbur! ya
falfala da azababben gudu izuwa cikin dajin.
Imhal ya dage iya karfinsa da iyawarsa har yana tashi
sama yana shallake duwatsu da karyayyun bishiyoyi
da suka fadi kasa amma koda ya waigo sai ya hango
wadan nan karnukan suna neman cimmasa sai kawai
ya kara kaimin gudun,Ba zato ba tsammani sai yaga
wani katon rami mai tsananin zurfi a gabansa,kafin ya
iya sarrafa kansa ya cije sai karfin gudun nasa ya
rinjaye shi ya fada cikin ramin yana mai kurma uban
ihu.
Sa'ar da yayi kawai kawai kasan ramin cibiya ce ta
ruwan teku amma yana tsunduma a cikin ruwan sai
kansa ya bugu da wani dutse ya sume.
Su kuwa karnukan suna isowa bakin ramin sukayi
tirjiya suka fara haushi,sautin haushin nasu ya cika
dajin gaba daya,wanda hakan ne ya janyo hankalin
dakarun Marwatu suka rugo sashin da suke jin
haushin cikin matsanancin gudu,suna cikin gudun ne
suka hango karnukan sun kewaye wani rami suna ta
haushi,don haka suka kara azama don nufar inda
ramin yake.
Lokacin da dakarun marwatu suka iso bakin ramin
wanda Imhal ya fada sai suka iske karnuka a tsaye a
wajen suna ta haushi sai suka leka kasan ramin,ai
kuwa sai suka hango Imhal a kwance akan ruwa
kuma ruwan yana tafiya dashi ko motsi bayayi kamar
gawa.
Cikin gaggawa wasu daga cikinsu suka gangara kasan
ramin suka shiga cikin ruwan suka tsamo Imhal,suna
fitowa dashi sai suka ga yana numfashi don haka sai
suka yi sauri suka turmushe shi suka daure
hannayensa da kafafunsa da sarkoki sabo da sun san
cewa in har ya farfado baza su iya kamashi ba.
Nan take suka daure shi suka kai shi can inda
Marwatu yake zaune,da zuwan su suka iske Marwatu
a kishingide ya gama dinke raunin dake cikinsa ya
saka magani,koda Marwatu yaga dakarunsa sun
dawo dauke da Imhal a daure cikin sarka sai ya kamu
da tsananin farin ciki mara misaltuwa ya mike tsaye
zumbur!ya kwarara uban ihu irin wanda manyan
barade ke yi afilin yaki yayinda suka samu nasara
akan abokin gabar su,kawai sai yasa aka warbar da
Imhal gefe daya a kasa aka kyale shi har sai da ya
farfado daga suman da yayi.
Koda Imhal ya bude idon sa yayi arbuna da marwatu
zaune a gabansa yana yi masa murmushin mugunta
sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya yunkura da
nufin ya gudu amma sai ya kasa sakamakon sarkokin
da suka daure kafafuwansa da hannayensa
Nan take yaji wani irin bakin ciki ya lullube shi,ya
ayyana a ransa cewar da ma ya mutu a kokarin
wannan guduwa da yayi daga kurkukun Darul maut
da ya fiye NASA alheri.
Kawai said yaji marwatu ya bushe da dariyar
mugunta yana mai nuna shi da yatsa,daga can sai
marwatu ya fara yiwa kansa kirari yana cewa Nine sa
gudu maganin ki gudu,kuma nine sarkin darul maut
mai RIJIYA GABA DUBU,ya kai wannan takadarin
jarumi,kayi Sani cewa inda ba muyi nasarar kamoka
ba da sai Na kashe kaina sabo da Kaine kadai jarumin
da ya karya alkadarina,ya sami nasarar guduwa daga
kurkukun darul maut Wanda Na shafe shekara da
shekaru INA gadinsa,ban taba samun rauni ba a
rayuwata said wannan karon don haka idan muka
koma darul maut sai Na dandana mama azabar da
bantaba dandanawa wani fursuna ba sai Na shigar da
kai RIJIYA ta azaba mai GABA DUBU.Koda gama fadin
haka sai marwatu ya mike tsaye yaje inda jarumi
Imhal yake zaune ya shammace shi ya gabza masa
wawan naushi a fuska ,nan take Imhal ya sulale a
kasa sumamme.
lokacin da Imhal

4 Comments On RIJIYA GABA DUBU
avatar
mlm

1 year ago

Reply

Next please

avatar
khadija-1-4

1 year ago

Reply

??????

avatar
muhammad-musa

1 year ago

Reply

Good book

avatar
ismail-9-8

10 months ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment