Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi mata aiyuka iri-iri,
kwatsam! sai ta hango wata kuyanga ta taho za ta
gifta ta gabanta,tana kallon fuskar kuyangar sai ta ga
ai bakuwa ce domin bata taba ganin fuskarta
ba.Al'amarin da yai matukar bata mamaki kenan
domin babu yadda za'ayi a kawo bakuwar kuyanga
cikin turakarta ba tare da an sanar da ita ba,Har
kuyangar ta gifta ta zata wuce sai Shumaira ta Sha
gabanta da sauri suka dubi juna,tsawon 'yana dakiku
sannan Shumaira tace, Wacece ke kuma yaushe aka
kawoki nan,muhallina ba tare da sani na ba?Koda jin
wannan batu sai kuyangar tayi murmushi cikin
alamun takama da yarda da kai tace,Ni ba kuyangar
ki bace hanya ce ta biyo dani ta nan,bani hanya na
wuce abina idan ba so kike ranki ya baci ba, Koda jin
wannan batu sai ran Gimbiya Shumaira ya baci bisa
ganin cewa tana matsayin'yar sarki amma kuyanga
tayi mata rashin kunya, kawai sai ta daga hannu da
nufin ta sharawa kuyangar mari,amma sai taji
hannun nata ya makale a sama ta kasa sarrafa
shi,kuma taji an matse hannun nata,wani irin mugun
zugi da radadi na shigarta bata San sanda ta fara ihu
ba,Abinda ya daure mata kai shine,duk ihun da take
yi babu mai jinya,asalima babu wanda yaga abinda ke
faruwa, nan take tsoro ya kama Gimbiya Shumaira ta
fara tunanin cewa,lallai wannan kuyanga da ke
gabanta ba mutum bace aljanna ce.
Koda ta ayyana hakan a cikin zuciyar ta sai ta dubi
bakuwar kuyangar cikin tsananin dauriya tace,Ki
gafarceni banyi dai-dai ba,kafin ta gama rufe bakinta
sai taji an saki hannun ta kuma ta daina jin zafin
komai, kawai sai ta sake duban kuyangar tace,"Ya ya
akayi kika sami damar shigowa gidan nan ,alhalin
babu wani aljani da ya taba shigowa tun farkon gina
shi? " sanda bakuwar kuyangar taji wannan tambaya
sai tayi murmushi tace,Ni ba aljana bace, mutum ce
ni kamar ke,idan har kina so kisan ko ni Wacece ki
kaini cikin turakar ki mu zauna muyi wata magana,
bayan hakan ne za kisan ko ni wace ce kuma zan
taimaka miki na kaiki har inda aka tsare bakon jarumi
ki ganshi ba tare da kin fuskanci wata matsala
ba,Koda jin wannan batu sai murna ta kama
Shumaira nan take ta kama hannun kuyangar ta ka ta
izuwa can cikin turakar ta,da shigarsu cikin kuryar
dakin kuyangar ta zauna tana mai yin hamma alamar
cewa tana jin yunwa da bacci, har Shumaira ta budi
baki za tayi magana sai ta dakatar da ita da hannu
tace,Kafin muyi maganar komai sai naci na koshi,
maza kisa a kawo min abin kalaci,Koda jin haka sai
gimbiya Shumaira ta kwalawa wata kuyangarta kira
tace da ita,taje ta kawo mata abin kalaci,Koda jin
wannan umarni sai mamaki ya kama kuyangar mai
suna SALIFAT, Salifat ta sunkui da kai kasa tace,"ya
shugabata me za kiyi da abincin kalaci yanzu alhalin
dazu na kawo miki kika ce bakya bukatar?" Shumaira
ta dakawa Salifat tsawa tace,"Ina ruwan ki,yanzu nake
bukatar cin abincin, maza kije ki dauko mini kafin
raina ya baci".Cikin hanzari kuyangar ta juya da sauri
ta je ta dauko abincin bisa faranti a cikin manyan
kwanuka guda biyu na dinare, kuyanga Salifat tazo ta
ajiye farantin a gaban bakuwar kuyangar amma kuma
ba ta ganta ba,bata ma San cewa akwai wani mutum
a cikin dakin ba face Gimbiya kadai,Koda kuyangar ta
ji kamshin abinci ya doki hancinta sai ta fado kasa
Daga kan kujera ta bude kwanukan abincin ta duma
hannu a ciki ta kama ci kamar wacce ta shekara da
yunwa, kafin a jima ta cinye kusan rabin abincin dake
cikin kwanukan biyu wanda a ka'ida mutum shida ne
ke iya cinye shi,tana gamawa ta dauki tambulan din
ruwan ta shanye shi tas ya zama ko digo daya bata
rage ba sannan tayi wata katuwar gyatsa,kai da gani
kasan cewa bata saba cin abinci mai daraja ba irin
wannan, A sannan ne bakuwar kuyanga ta mike tsaye
ta koma kan kujerar ta zauna sannan ta fuskanci
Gimbiya Shumaira ta dubeta cikin nutsuwa
tace,"sunana MUZAIRA, kuma ni 'yar uwar matar
sarkin Kisra ce na da,wanda sarkin yanzu ya kashe ya
hau karagar mulkinsa. "Koda jin wanne batu sai
Shumaira ta mike tsaye zumbur! cikin alamun tsoro
da mamaki, kuma jikinta ya kama tsuma tana mai
nuna MUZAIRA da dan yatsa bakinta na rawa tana so
tace wani abu amma sai ta kasa,Koda ganin haka sai
MUZAIRA tayi murmushi tace," kwantar da hankalin
ki ya ke Gimbiya Shumaira, ban zo nan dan cutar da
ke ba,sai domin na taimake ki kamar yadda nayi
alkawari,kuma kema ki taimake ni,wannan bakon
jarumi da kika kamu da son sa wato jarumi Imhal da
ne a waje na,domin MAHAIFIYARSA yayata ce,uwar
daya uba daya,kuma na biyo shi ne izuwa birnin
misra domin na ceci rayuwar sa a cikin GASAR
JARUMTAKAR da ake yi,Tabbas a dazu sanda ya fafata
da sadauki Darwaz, in ba don na kawo masa dauki ba
da tuni Darwaz ya hallaka shi da karfin sihiri, inda kin
lura za kiga cewar jarumi Imhal ya tsaya cak a waje
daya sanda Darwaz ya rugo da gudu izuwa kansa a
wannan lokaci wata guguwar sihiri ya jefo masa ta
kanannadeshi ya kasa Koda motsa hannayensa,nice
na kawar masa da guguwar a lokacin da saura kiris
Darwaz ya gama dashi.
Yanzu zan gaya miki wani babban sirri wanda ba ki
San shi ba,kuma labarin zai girgiza kwakwalwarki, da
farko dai nice barauniyar da ake ta nema a cikin garin
nan da kewayensa wacce tayi wa sarki gurzalu sata,
kuma ba wani abu na sace masa ba face wani GURU
na TSAFI indai yana tare da wannan grun tsafi babu
wani mahaluki da ya isa ya samu nasara a kansa,ko
ya iya cutar dashi, yanzu gashi Gurun ya dawo hannu
na, koda MUZAIRA tazo nan a zancen ta sai ta yaye
rigar da ke jikinta, take Shumaira tayi arba da gurun
tsafin zagaye a kugun MUZAIRA, MUZAIRA ta saki
rigar ta rufe gurun sannan ta cigaba da cewa,
Albarkacin wannan guru ne na samu damar shigowa
gidan nan ba tare da kowa ya ganni ba,kuma abinda
sarki gurzalu bai sani ba shine, tun kafin su shigo
cikin garin nan na sace gurun a wani lokaci da suka
ya da zango a cikin daji ya fita daga cikin tantinsa yaje
yayi wanka a wani rafi.RIJIYA GABA DUBU
Littafi na uku 3
Na Abdulaziz sani m gini
Typing:- Ibrahim S combatant
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 3D
.
Dama ina biye dasu tun daga can birnin kisra a cikin
siffar wata tsuntsuwa basu sani ba,A lokacin na shiga
cikin tantin nasa,kuma nayi sa'a na iske akwatinsa a
bude, ya manta bai kulle ta ba bayan ya dauki
mayafin da zai tsane ruwan jikinsa bayan yayi
wankan, Bai taba mancewa da kulle wannan akwati
ba sai a wannan lokaci, don haka bayan na sace
gurun tsafin sai na datse kwadon akwatin ,shi kuwa
dan mabudin kwadon akwatin dama ko da yaushe
yana jikin mazagin wandonsa.
Lokacin da ya dawo cikin tantin nasa ya iske
akwatinsa a rufe bai iya tunawa cewa a bude ya barta
ba,Bayan na mallaki gurun tsafin ne jiya na shiga har
cikin turakarsa na bude akwatin da karfin sihiri, kuma
na barta a bude domin nasa shi zargi cewa a nan ne
aka sace Gurun.
Yanzu zan baki labarin abinda yasa na sace wannan
Guru.
Nan take Zumaira ta bawa labarin duk yanda akayi
aka yanka mahaifiyar Imhal aka kaita daji aka yar ana
zaton ta mutu har tsoho imzanu ya ganta ya ceci
rayuwar ta kuma ta cigaba da rayuwa a cikin hauka
har izuwa sanda ta haifi jarumi Imhal, a karshe ta
mutu ta barshi a hannun tsoho imzanu ya cigaba da
rainonsa har ya girma, kawo izuwa sanda sarki
Gurzalu ya tura a kashe tsoho imzanu a kamo Imhal
har izuwa cikin gari inda suka fada cikin gidan ta ta
taimake su.
Koda MUZAIRA tazo dai-dai nan a labarin ta,sai taga
hawaye na zuba a idanun Shumaira sakamakon
tsananin tausayi da ta ji bisa jin tarihin rayuwar
Imhal da yadda aka yiwa iyayensa kisan gillah, Nan
take Shumaira taji ta tsani sarki gurzalu don jin
mugun zaluncinsa, kuma ta kudurce a ranta cewar
lallai sai ta raba alakar dake tsakaninsa da mahaifinta
sarki taryan, Koda Zumaira taga Shumaira na kuka,sai
itama zuciyar ta ta karaya ta fashe da kukan aka rasa
wanda zai rarrashi wani har izuwa tsawon 'yan dakiku
sai daga can Shumaira ta nutsu ta daina kuka ta dago
kai ta dubeta tace,Yanzu wane irin taimako kike so
nayi miki? Koda jin wannan tambaya sai Zumaira ta
nutsu tace,Ba wani taimako nake so kiyi mini ba face
ki ajiye duk abinda na fada miki sirri a cikin zuciyar ki
har izuwa ranar gasar Imhal ta karshe, wato ranar da
zai fafata da sarki gurzalu domin idan kika gayawa
Imhal cewar sarki gurzalu ne ya kashe iyayensa ya
hau karagar mulkin a yanzu duk shirin mu ya watse
baza mu iya daukar fansa ba akan sarki gurzalu,
domin Imhal zai hau kace ne yace yanzu-yanzu zai
dauki fansa,kinga kuwa ba zai iya ba,tunda sarkin
yawa yafi sarkin karfi,karfi.
Inda dai ace nasan sirrin yadda ake amfani da
wannan gurun sihirin ne na sarki gurzalu da nayi
amfani dashi wajen hallaka shi, abinda zan iya yi
yanzu kawai shine, nacigaba da boye wannan gurun
tsafi a waje na har izuwa ranar da zasu fafata shi da
Imhal ya zamana cewa ta kowane hali bai bar
hannuna ba,domin indai gurzalu baya tare da gurun
tsafin, bazai iya samun nasara ba akan Imhal,sirri
daya na sani na amfani da wannan gurun, wato sirrin
bata,duk wanda yake tare da wannan gurun da
wanda ke tare dashi ba a ganinsu, kuma ba a jin
muryarsu Koda kuwa za suyi ta tsandara ihu, su
kwana suna yi,yanzu sai ki tashi kiyi mini jagora izuwa
inda aka tsare Imhal domin na ganshi ko ma samu
'yar nutsuwa, amma baza muyi masa magana ba ,don
ko munyi ma bazai ji ba ,ba tare da gardamar komai
ba Shumaira ta mike tsaye ta kama Zumaira ta ka ta
suka fice daga cikin gidan sarautar suna ta ratsawa ta
cikin lunguna da sakuna, suna tafe suna hira abin
su,kuma gashi duk inda suka ratsa akwai dakaru a
tsaitsaye suna rangadi amma babu mai ikon ganinsu
ko jin muryarsu, duk inda suka je kuma suka iske
kofa a rufe basa bukatar su bude sai dai kaga sun
ratsa ta cikin karfen kofar sun wuce, tamkar yadda
danshi ke tsatstsafowa daga cikin kasa,Albarkacin
wannan gurun tsafin dake daure a kugun MUZAIRA
hakan ke faruwa, A haka dai suka iso kofar dakin da
aka sa jarumi Imhal a ciki. da yake kofar dakin anyi
tane da sandunan karfe sai suka ganshi kwance a
kasan dakin ko shimfida babu yana ta faman shara
baccin wuya, Koda suka ga halin da yake ciki ,kuma
suka ga katon raunin dake kan kirjin sa sai suka fashe
da kuka, Tabbas duk wanda ya dubi Imhal a wannan
yanayin da yake dole ne ya tausaya masa domin
numfashinsa ma yana fita ne da sauri-sauri kamar ba
zai rayu ba,sai da suka dade a tsugune a wajen suna
kallon sa sannan MUZAIRA ta zura Kanta ta cikin
sandunan kofar da hannun ta guda ta shafa kan
Imhal, a lokacin da hawayen idanun ta ya zubo akan
kumatunsa, shafa kan nasa ke da wuya ya farka daga
bacci, Koda ya ji danshi a kumatunsa sai ya shafo shi
ya duba, Koda ya fahimci cewar ba ruwa
bane,hawaye ne,sai ya mike tsaye zumbur! ya kama
waige-waige amma bai ga kowa ba,A lokacin ne
Shumaira tayi sauri ta kama hannun MUZAIRA ta
janye ta suka bar wajen.
Nan take Imhal yaji a jikin sa cewar lallai wata ce tazo
wajen sa har tayi kuka hawayen ta ya zuba akan
kumatunsa, Amma abin tambayar shine,Shin Wacece
wannan mai zubar da hawaye saboda tausayinsa?
Amsar da ya kasa baiwa kansa kenan, shi dai a sanin
sa bashi da kowa a wannan duniya wacce zata zubar
da hawayen ta saboda tausayinsa, nan dai jarumi
Imhal ya fada kogin tunani inda ya tuno da abokin sa
MARIGAYI ZAUWADU kuma ya tuno da wasiyyar da
ya bar masa sanda ya bashi wata sarka yace dashi,
lallai komai dadewa yaje unguwar sharkas a cikin
birnin kisra ya nemi masoyiyarsa SUHAILA ya bata
wannan sarka, kuma ya bata labarin rayuwar su a
cikin kurkuku har izuwa lokacin da ajali ya riske
shi,Koda yazo nan a tunaninsa sai hawaye ya zubo
masa yaji yana fatan ya rayu ya sake kubuta Daga
sharrin sarki gurzalu domin yaje ya sauke wannan
alkawari da ya daukarwa abokinsa Zauwadu.
Wannan shine abinda ya faru tsakanin Gimbiya
Shumaira da Zumaira kanwar mahaifiyar jarumi
Imhal wacce itama take da burin daukar fansa akan
sarki gurzalu.
Al'amarin sarki gurzalu kuwa, lokacin da su Gimbiya
LAMIRAT suka sake shafe wuni guda suna neman
barawon sa a cikin birni da kauye suka dawo babu
nasara, sai sarki gurzalu ya zama kamar mahaukaci
ya dinga buge-buge da iface-iface, da kyar!LAMIRAT
ta shawo kansa ya dawo hayyacinsa, sannan ta dube
shi tace,Ya kai Abbana yanzu mene ne dalilin da ya
hana ka tashi na garzaya izuwa can birnin kisra
domin kar shiga dakin halwar tsafin ka ka binciko
wanda ya sace maka gurun nan?Koda jin wannan
tambaya sai sarki gurzalu yayi aniyar zuciya yace,
Abinda yasa naki komawa birnin kisra shine tunda
nake zuwa wannan gasa tsawon shekaru talatin baya
ban taba komawa gida ba a lokacin da aka gasar
ba,idan na koma mutane za su iya cewa na tsorata ne
da abokin gwamina ko kuma na karaya na koma gida
don nayi sabon shiri, kinga kenan yanzu duk zabi
biyun da nake dasu akan matakin da ya kamata na
dauka duk sun rushe, muna ji muna gani kenan
makiyanmu za su iya samun nasara akan mu.
Koda jin haka sai lamirat ta gyada kai tace, Haba ya
kai Abbana, hanyar kashe makahon kare yawa gareta,
ina da wata dabarar, cikin mamaki da zumudi sarki
gurzalu ya dubi lamirat yace, Ya ke'Yata wace irin
dabara kike tunani? lamirat ta numfasa tace,Ni ina
ganin cewa ka saka sarki taryan ya kirawo maka gaba
daya bokayen kasar nan su dukufa akan binciken
gano barawon ka,indai bokayen kasar nan suka hada
karfi da karfe, lallai zasu iya gano barawon ka a cikin
kwanaki kadan kafin Imhal ya sami lafiyar da zai iya
cigaba da wannan gasa har haduwarka dashi tazo,
Koda jin wannan shawara sai farin ciki ya lullube
sarki gurzalu yace, ina alfahari dake 'yata tabbas kinyi
dogon tunani mai kyau, to amma fa dole ne muyi
la'akari da irin raunin dake jikin Imhal mu kiyasce iya
tsawon lokacin da muke ganin zai warke, idan kuma
yazo dai-dai da sanda Bokayen za su samu nasarar
gano barawon shikenan bamu da sauran
damuwa,amma idan har Imhal ya samu lafiya kafin
su gano barawon akwai matsala babban,Lamirat tace,
kada ka damu ya Abbana, duk zan kula da hakan,
kuma a Yau dinnan za a gama komai, Koda gama
fadin haka sai Gimbiya lamirat ta mike tsaye ta fice
daga cikin dakin,bata zame ko ina ba sai turakar sarki
taryan, bayan anyi mata iso ta shiga inda yake sai ta
risina ta gaishe shi sannan tace, ya shugabana,
Abbana ne yace nazo na nemi alfarmar zuwa ganin
jarumi Imhal, Koda jin haka sai sarki taryan ya girgiza
kai yace,Ai bazan iya baki wannan dama ba domin
yana daga cikin dokar wannan gasa ba a barin abokin
gasa yaje ya gana da dan'uwansa,idan har kika je kika
gana da Imhal kamar sarki gurzalu ne yaje tunda kin
kasance 'yarsa,Lamirat tace,na yarda ka hadani da
amintattun Hadimanka su rakani gareshi, idan ana
zargin ko zanje na cutar dashi ne,,Koda jin haka sai
sarki taryan yayi shiru yana tunani, daga can kuma
sai yayi aniyar zuciya yace,shikenan na amince, Take
lamirat tayi godiya, ba tare da bata lokaci ba aka
hadata da wadansu amintattun Hadimai su hudu
gami da dakaru dari suka tafi izuwa dakin da aka kulle
jarumi Imhal.
Da isarsu suka iske jarumi Imhal a kishingide a jikin
bango yana con abinci dakyar kamar zai yi amai ko
Riga babu a jikinsa sakamakon katon raunin da ke
kirjin sa.
Tun daga nesa jarumi Imhal ya hango Gimbiya
lamirat tare da dakaru sai ya kura mata idanu yana
mai yi mata murmushi.
.
.RIJIYA GABA DUBU
Littafi na uku 3
Na Abdulaziz sani m gini
Typing:- Ibrahim S combatant
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 3E
.
Ita kuwa Koda taga yana yi mata murmushi sai ta
murtuke fuskarta tamkar taga bakin kumurci(Bakin
maciji mai masifa da mugunta) kuma sai ta dinga
satar kallon raunin da ke kan kirjinsa, tana nazari da
tunanin adadin kwanakin da take ganin cewar ciwon
zai iya warkewa har ya iya cigaba da yin wannan gasa.
Lokacin da Gimbiya lamirat suka iso daf da kofar
dakin sai suka tsaya cak! Akayi tsit! ana kallon-kallo
tsakaninta da jarumi Imhal, kawai sai Imhal ya
dubeta fuskarsa cike da annuri yace,"Mene ne ya
kawoki wajena,ko kuwa kinzo ne ki karasani saboda
kina tsaron karona da mahaifinki? "
Koda jin wannan tambaya sai murmushi ya
subucewa Gimbiya lamirat bata sani ba,ta dubeshi
cikin gadara tace, "Ai matsoraci baya kusantar abokin
gaba,nazo ne domin naga lafiyar abokin gaba, domin
idan ka mutu yanzu sai nafi kowa bakin ciki, saboda
bani da burin da yafi na sare kanka da hannun nan
nawa".
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama jarumi
Imhal yace," Wai shin menene dalilin da yasa keda
mahaifinki kuka tsananta kiyayya a kaina,alhalin babu
wani mugun sabani da ya taba shiga tsakanina da Ku?
shin ta yaya Zaki samu damar sare kaina da hannunki
alhalin bakya cikin wannan gasa ta KAMBUN
JARUMTA? Koda ma kina cikin wannan gasa ni bazan
iya kashe ki da hannu na ba,domin a cikin fadin
duniya kaf a yanzu babu abinda nake kauna sama
dake".
Koda jin wannan batu sai lamirat da gaba daya
dakaru da hadiman dake bayan ta suka cika da
tsananin mamaki, lamirat ta fusata ainun, ta dakawa
Imhal tsawa tace,"Kai talaka, makaskanci! ka sani
cewa wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa,kuma RUWA
da WUTA basa haduwa, batun soyayya a tsakani na
dakai babu har abada sai kiyayya! Nayi maka
alkawarin cewar wannan karon baka isa ka kubuce ba
daga sharrin mu face munga karshenka!!"
Koda jin wannan batu sai jarumi Imhal ya bushe da
dariya, lokaci guda kuma ya hade fuska yace,"Ni kuwa
nayi miki alkawari sai kin nemi gafarata da murya
mai taushi, kuma kin rokeni na So kind......!!!"
Kafin jarumi Imhal ya rufe bakinsa tuni lamirat ta tofa
masa yawu a fuska tace,"Da dai na SO ka har na furta
maka kalmar SO gwara na rasa rayuwata, kuma ka
saurari ranar da za kayi gasa ta uku, nice abokiyar
gwaminka ".
Tana gama fadin haka sai tayi sauri ta juya cikin fushi
zuciyar ta na tafasa tamkar zata kone, cikin hanzari
hadimai da Dakaru suka bita a baya.
Shi kuwa jarumi Imhal sai yasa hannun sa ya lakuto
yawun da lamirat ta tofa masa a fuska ya shanye shi
yana murmushi yace, " Ba a soyayya da karya... kuma
ba a kiyayya da karya, na kamu da tsananin sonki
Gimbiya lamirat, kuma bazan daina sonki ba Koda
Zaki zamo sanadin ajalina!
Yana gama fadin haka sai ya koma ya kwanta a kasa,
kansa yana kallon Rufin dakin yana murmushi gami
da mamakin yadda akayi radadin SO ya sa shi ya
bayyana soyayyarsa a fili a Yau ba wadda ta tsane shi
kamar yadda ta tsani ajalinta, kuma ya cigaba da
wasu-wasi a cikin zuciyarsa akan cewar; "Wai shin da
gaske ne Lamirat ce abokiyar gwaminsa ta uku a cikin
wannan Gasar Jarumtaka?"
Abinda baiwa sani ba shine, shi kansa sarki gurzalun
baiwa San cewa Gimbiya lamirat ta shiga cikin
wannan gasa ba,don tun kafin su iso birnin ta aiko da
wasika mai dauke da hatiminta da sa hannunta ba
sarki taryan tace lallai a sata a matsayin jarumar da
zata fafata a karo na uku da bakon jarumin da za su
zo dashi ".
Koda sarki taryan yaga wannan wasika sai ya cika da
dimbin mamaki, amma da yaga hatimi da sa hannun
ta sai yasa aka rubuta sunanta a cikin jaruman gasar.
Wani iko na Allh kuma sai ya manta ya tambayi sarki
gurzalu dalilin da yasa ya bar Gimbiya lamirat ta
shiga cikin wannan gasa.
Bayan lamirat ta baro wajen Imhal sai ta koma izuwa
turakar sarki gurzalu ta gaya masa cewa," Dole ne
Bokayen da za su kira suyi musu wannan bincike su
kammala a cikin kwanakin da basu wuce bakwai
ba,saboda na tabbatar da cewar kafin Imhal ya warke
har yaji karfin da zai iya fitowa filin gasa sai ankai
kwana bakwai ".
Sanda sarki gurzalu yaji wannan batu sai fuskar sa ta
fadada da murmushi, yace," Ai faduwa tazo dai-dai
da zama, domin tuni na gana da shugaban bokayen
kasar nan a Yau bayan na rabu da ke, kuma har ya
tabbatar mini da cewar nan da cikar kwanaki bakwai
dai-dai za su gano mini Barawon,tabbas aikin ki yayi
kyau.
Da jin haka sai farin ciki ya lullube Gimbiya lamirat
tayi godiya kuma sai fuskarta ta sauya yanayi izuwa
matukar damuwa ta sunkui da Kanta kasa tana mai
yin shiru,Al'amarin da ya tayar da hankalin sarki
gurzalu kenan ya dubeta shima cikin damuwa yace,
"Ya ke 'yata me ya faru,kuma naga fuskarki ta sauya
yanayi daga farin ciki zuwa kishiyarsa?" Sanda ta ji
wannan tambaya sai ta dago kai a lokacin da idanun
ta suka kada suka yi jawur kamar hawaye zai zubo
mata tace,"Ya kai Abbana a iya sanina a cikin tarayya
ta dakai ban taba yi maka karya ba kuma ban taba yi
maka laifi ba,ko ba haka bane?"
Cikin mamaki sarki gurzalu ya gyada kai yace,"Tabbas
tun daga kuruciyarki kawo izuwa girmanki baki taba yi
min wadannan abubuwan biyu ba".
Lamirat tace,wannan karon nayi maka wani laifi tun
kafin mu baro gida, kayi hakuri bazan iya gaya maka
wannan laifi ba sai bayan an kammala wannan gasa
ta khango JARUMTA, amma ina rokonka da ka yafe
min wannan laifi tun kafin ka San shi"
Koda Gimbiya lamirat tazo nan a zancen ta sai sarki
gurzalu ya sake kamuwa da tsananin mamaki, yayi
shiru yana tunani da nazari har izuwa tsawon dakiku,
daga can sai ya dubeta cikin murmushi yace, "Na yafe
miki wannan laifi'Yar Lele,kuma ko bayan na San
laifin na rantse da girman abin bautarmu bazan yi
fushi da ke ba"
Koda jin haka sai farin ciki ya kama lamirat ta
rungume sarki tana mai yi masa godiya, nan dai
lamirat tayiwa sarki gurzalu sallama ta tafi izuwa
masaukin ta,wato dakin Gimbiya Shumaira.
Tana shiga dakin sai ta hango Shumaira zaune tana
sarrafa hannayen ta alamar cewar tana yin magana
ne da wani.
Amma da lamirat ta karaso cikin falon sai taga Ashe
babu kowa a cikin falon, Shumaira ce kadai a zaune.
Al'amarin da yayi matukar bata mamaki kenan, ta
dubi Shumaira tace,Shin akwai wani aljani da yake
zuwa wajen ki kuyi hira?
Cikin mamaki Shumaira ta dubi lamirat tace,Ai babu
wani aljani da ya isa ya shigo cikin gidan sarautar nan
domin iyaye da kakanni sun gama shirya gidan da
tsari na musamman.
LAMIRAT tace,"Wannan gaskiya ne,domin mahaifina
ya tabbatar min da haka, amma yanzu da na tunkaro
wannan falon naki naga kina sarrafa hannayenki
alamar cewa kina yin magana ne da wani "
Koda jin haka sai Shumaira tayi murmushi tace,A'a
babu wanda nake hira da shi ,kawai dai ina tunani ne
gami da zancen zuci ,
Cikin sanyin jiki Lamirat ta zauna a gefen Shumaira
suka yi shiru tsawon'yan dakiku kadan.
Duk wannan abu dake faruwa MUZAIRA na zaune a
gefe daya tana hararar lamirat, kuma jikinta na
tsuma, ji take kamar ta mike zumbur! ta je ta shake
Gimbiya lamirat har sai ta kasheta saboda kiyayya.
Ita kuwa lamirat gashi dai tana fuskantar kujerar da
MUZAIRA take zaune a kai amma ba ta iya
ganinka,Shumaira kadai take iya gani a cikin falon.
Daga can sai lamirat ta katse shirun da suke ciki ta
dubi Shumaira tace,Ya ke kawata ina son zan baki
wata shawara guda daya, shawarar kuwa ita ce,Kada
ki so saurayin da ba shine ya fara nuna soyayyarsa ba
a gareki, domin watakila kiyi SON MASO WANI.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Gimbiya
Shumaira tace, Ke kuwa mene ne dalilin da yasa kika
fada mini wannan magana alhalin ban taba gaya miki
cewar ina son wani saurayi ba?
Koda jin haka sai lamirat tayi murmushi tace, Tun da
dai nayi miki hannun ji mai sanda baki gane ba bari
na fito fili nayi miki baro-baro watakila za ki fi
fuskantar inda nasa gaba.
Idan za ki iya tunawa, a ranar da aka fara gasar
kambun JARUMTA tsakanin jarumi Imhal da sadauki
Darwaz sai da kowa ya gane cewar kin kamu dason
jarumi Imhal sakamakon nuna matukar tashin
hankali bisa ganin zai hallaka da kuma yadda kika
nuna farin ciki lokacin da ya samu nasara, to ina mai
tabbatar miki da cewa jarumi Imhal yana da tsananin
so da bege a cikin zuciyar sa,kuma har ya fito fili ya
bayyana mata sirrin zuciyar sa,sai dai kashe! Anyi
rashin sa'a,domin wacce yake so din ta tsane shi
kamar yadda ta tsani mutuwarta, bisa wannan dalili
ne na gaya miki cewa ki taka a hankali, kada kiyi SON
MASO WANI wanda hausawa suke cewa KOSHIN
WAHALA.
Na baki wannan shawara ne a matsayinki na
tsohuwar kawata da muke tare tun kuruciya,sannan
idan kunne ya ji jiki ya tsira,shawara kuma ta rage ga
mai shiga RIJIYA.
Koda gama fadin hakan sai Gimbiya lamirat ta mike
tsaye ta shige cikin dakin bacci ta kwanta domin ta
huce gajiyar da tasha a ranar SAKAMAKON yawon da
suka Sha na farautar barawon mahaifin ta.
Ita kuwa Gimbiya Shumaira sai taji zuciyarta ta buga
da karfi, tunani da wasu-wasi suka cika mata ranta
bisa kokarin gano ko Wacece budurwar da jarumi
Imhal ya kamu da tsananin sonta haka?
Koda MUZAIRA taga hankalin Shumaira ya
dugunzuma ainun sai ta mike tsam! Daga kan kujerar
da take zaune ta koma wajen ta ta dafa kafadunta ta
dubeta tace,"Kwantar da hankalin ki ranki ya dade,a
matsayina na uwa a gun jarumi Imhal in dai ina
numfashi a doron kasa sai na siyo miki soyayyars
Imhal,domin kece kika dace dashi fiye da kowace
budurwa a wannan duniya, domin soyayyarki a
gareshi, soyayya ce ta gaskiya, wacce babu algus! a
cikin ta".
Koda jin wannan batu sai hankalin Shumaira ya
kwanta ta rungume MUZAIRA tana mai yi mata
godiya gami da fatan samun nasara akan makiyansu.
.
.
RIJIYA GABA DUBU
Littafi na uku 3
Na Abdulaziz sani m gini
Typing:- Ibrahim S combatant
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 3F
.
Kwana Uku cur!da Faruwar wannan al'amari ne sarki
gurzalu na tsalle-tsalle gami da yin wasa da takobi a
wani babban fili dake cikin harabar gidan sarki taryan
don baiwa kansa horon yaki, sai ga 'yarsa Gimbiya
LAMIRAT ta durfafoshi sanye cikin shigar yaki kuma
rike da takobi,
Al'amarin da ya bashi mamaki kenan, ya tsaya cak! ga
barin baiwa

4 Comments On RIJIYA GABA DUBU
avatar
mlm

1 year ago

Reply

Next please

avatar
khadija-1-4

1 year ago

Reply

??????

avatar
muhammad-musa

1 year ago

Reply

Good book

avatar
ismail-9-8

10 months ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment