Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya farfado sai ya tsinci kansa a cikin
jirgin ruwa ga marwatu da dakarunsa sun kewaye
shi,yana daga kansa sama ya dubi gabas sai ya hango
kurkukun Darul maut a nesa da su kadan,jirgin Na
tafiya acikin teku,al'amarin da ya jefa Imhal acikin
bakin ciki kenan have acikin zuciyarsa Yanzu mene ne
amfanin wannan yunkurin guduwar da nayi?wai shin
menene dalilin da yasa baki kashe kansa ba ya huta
da wannan bakin ciki?yana cikin wannan tunanin zuci
ne jirgin nasu ya I so kofar kurkukun Darul maut,nan
take aka tsaida jirgi ya tsaya cak! sannan dakaru suka
kama Imhal suka tashe shi tsaye aka fitar dashi daga
cikin jirgin ,shi kuwa marwatu baki fits daga cikin
jirgin ruwan ba sai ya dubi dakarun da suke rike da
Imhal have dasu Kada Ku kaishi bangaren dakin
fursunoni Ku kaishi dakin RIJIYA GABA DUBU Ku
daure shi a jikin bango da sarkoki Ku barshi a
haka,kuma kada a bashi ruwa ko abinci had sai Na
dawo,
.RIJIYA GABA DUBU
Littafi na biyu 2
Na Abdulaziz sani m gini
Typing:- Ibrahim S combatant
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 2D
Na tafi gidan Sarki domin inyi masa albishir bisa
nasarar kamo Imhal da mukayi,koda gama fadin haka
sai marwatu ya juya ya umarci masu tukin jirgin da
su juya akalar jirgin su nufi cikin gari,ba tare da
gardamar komai ba kuwa suka bi umarninsa suka
juya jirgin suka kama hanya akan ruwa.
Su kuwa dakaru sai suka shigar da jarumi Imhal cikin
kurkukun,suna shigewa aka mai da kofar Gidan aka
rufe,tayi kara mai karfi tamkar an kulle kofar birnin
gaba daya,yayin da aka zo wucewa da jarumi Imhal ta
bangaren dakunan fursunoni suka kyalla I do suka
hango shi sai suka kama ihu da shewa suna yi masa
tafi da jinjina sabo da kasancewarshi fursuna Na
farko da ya taba samun nasarar guduwa kuma ya
tsira da rayuwarsa.Koda fursunoni suka ga an nufi
dakin RIJIYA GABA DUBU da Imhal sai gaba dayan su
jikin su yayi sanyi suka kamu da tsananin
tausayinsa,ba komaine ya haddasa hakan ba face
sanin cewar duk mutumin da aka shigar dashi cikin
(ayya frnds ayimin afuwa wlh fefar littafin ta tsakiya
banganta ba)
.
Koda Imhal yazo nan a zancensa sa aljani Sautil
makatur ya bushe da dariyar mugunta a karo Na biyu
yace, Sai kayi kokari ka fita daga nan din cikin
hayyacinka yadda zaka iya bude idanunka ka kalli
maharbi Imzanu. Koda gama fadin haka sai aljani
Sautil makatur ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa
ba acikin dakin,nan fa Imhal yaci gaba da jin tsananin
zogi da radadin Harbin da kunamun nan suke masa
har ya dinga jin kamar ya yanke duk wadan nan
kurajen na jikinsa wadan da suka duri ruwa, gashi
kuma a wannan lokacin yunwa da kishirwa sun
addabe shi sai birgima yake yi a kasa yana mutsu-
mutsu,kai komai rashin tausayin mutum idan yaga
Imhal acikin wannan hali dole ya tausaya masa, haka
dai Imhal ya kasance acikin wannan hali har sai da
dare ya raba sannan aka bude kofar dakin RIJIYA
GABA DUBU aka shigo aka baiwa Imhal wani irin
ruwa mai tururin zafi acikin kwarya,Hakika masu iya
magana sunyi gaskiya da suka ce, Wanda yake cikin
ruwa ko takobi aka mika masa kamawa zai yi, domin
ana mikawa Imhal wannan ruwa a lokacin da yake
fama da kishi sai kawai ya karbi kwaryar ya kafa a
bakinsa ya fara kwankada duk da cewar ruwan yana
kona masa harshe kuma yana mugun wari sannan
bashi da dadin dandano,shi dai kawai burinsa ya jika
makogwaronsa ya kawar da kishirwar da ta addabe
shi. Hakika rashin Sani yafi dare duhu! Inda Imhal
yasan abinda sai biyo baya da bazai sha wannan
ruwan ba,gwara ya gwammace kishirwa ta zama
ajalinsa domin yana gama shan ruwan da kamar
dakika daya sai cikinsa ya murde matuka ya kama
ciwo yaji kamar ana daddatsa hanjin cikinsa,bai San
sanda yaci gaba da birgima ba a kasa yana rusa
ihu,idanunsa kuwa suka kumburo sukayi bulu-bulu
kamar zasu fado kasa.
Kurajen dake jikinsa kuwa sai suka cigaba da
tsananin zogi suna kara kumbura, Daga can kuma sai
Kurajen suka dinga fashewa da Kansu suna zubar da
jini gami da wani irin mugunyar ruwa mai doyi, nan
take kurajen Na gama fashewa gaba daya sai ya
sume, bai sake farfadowa ba sai da sanyin asuba ya
buga.A sannan ne aka sake bude kofar dakin aka
kawo masa abinci loma daya da ruwa mukurwa uku
acikin wani Dan karamin kofin kasa, Haka dai aka
cigaba da ganawa Imhal azaba kullum, daga cikin
azabobin da aka tanada na cikin RIJIYA GABA DUBU,
har tsawon kwana goma sha hudu ya zamana cewa
ya rame matuka ya lalace kuma ko ina a jikinsa duk
ciwuka ne babu kyan gani,hatta fuskarsa ma sai da
tayi muni amma duk wannan tsananin azaba da
yunwar da ake yi masa horo da su bash sa ya mutu
ba.
A Ranar kwana na goma sha hudu ne da sassafe aka
bude dakin RIJIYA GABA DUBU aka fito da jarumi
Imhal a cikin matukar galabaice tamkar an dauko
tsumma domin ko kadan babu kuzari a jikinsa da
kyar ma yake iya taka sawayensa, da yawa daga cikin
fursunonin Gidan ma da aka zo za a wuce dashi ta
gabansu kasa shaida shi suka yi saboda yadda
kamanninsa suka sauya da kuma yadda ya rame
matuka, Koda fursunoni suka shaida shi sai suka
kamu da tsananin tausayinsa harma wasu suka zubar
masa da hawaye, nan dai aka fitar da Imhal daga
cikin kurkukun gaba daya aka saka shi acikin jirgin
ruwa a daddaure cikin sarkoki, kai kace wani katon
goggon biri aka kamo, kuma suma dakaru DUBU ne
suka kewaye shi acikin jirgin ruwan don kada yayi
wani yunkuri na guduwa, nan take aka nufi Gidan
sarautar birnin kisra da wannan jirgin ruwan,Wannan
shine abinda ya faru da jarumi Imhal bayan ya gudu
daga kurkukun Darul maut an kamo shi ansake dawo
da shi.
Al'amarin shugaban dakarun kurkukun Darul maut
kuwa, wato sadauki Marwatu, lokacin da yaga sun
dawo da jarumi Imhal kurkukun cikin nasara sai ya
tafi izuwa gidan Sarki Gurzalu yana mai tsananin farin
ciki.
Da Isar sa gidan sarautar kuwa aka yi masa iso a
wajen Sarki, take Sarki yayi masa izini ya shiga har
cikin turakarsa inda ya iske shi tare da matarsa
Muzaina a zaune acikin farin ciki da nishadi suna
ciye-ciye da shaye-shaye, da isowar Marwatu kusa da
kujerar da su Sarki suke zaune sai ya zube kasa
kamar zai yi masa sujada ya kwashi gaisuwa sannan
ya dago kai da nufin yayi bayani amma sai Sarki
Gurzalu ya daga masa hannu yana mai yi masa muni
da yayi shiru,Sarki Gurzalu ya mike tsaye ya tako har
gaban Marwatu ya kama kafadun sa ya tashe shi
tsaye sannan ya dube shi fuskarsa cike da annuri
yace, ya kai Marwatu kayi sani cewa a iya tsawon
aikin da kake yi mini a kurkukun Darul maut baka
taba yi mini aiki mai kyau ba kamar wannan na kamo
jarumi Imhal, domin inda ya samu nasarar tserewa
da ya karya alkadarinmu gaba daya,kuma da ya rusa
tarihin da mahaifina ya kafa akan kurkukun Darul
maut, tabbas sakamakon da zai biyo bayanka shine
mutuwa, to amma yanzu da ka samu nasarar kamo
shi na baka kyautar dinare dubu dari biyar gami da
Bayi mata da maza guda dubu, sannan kuma na baka
gidan gona ta na birnin Saihur, Koda Marwatu yaji
wannan bushara sai ya dimauce ya sake zubewa kasa
yana sumbatar kafar Sarki yana mai yin godiya, Sarki
Gurzalu ya bushe da dariyar murna yace, Tashi ka tafi
abinka ya kai Marwatu, domin ka kamo min zakin da
idan ya balle daga daji zai iya hallakani ya kawar da
dukkan zuri'ata ta yanzu, Nan take Marwatu yayi
sallama da Sarki ya mike tsaye da nufin ya juya ya
fita,sai matar Sarki Gurzalu ta kirawo sunansa ya
waigo sannan ta dube shi tace, Ya kai Marwatu kayi
sani cewa nayi maka matukar farin ciki matuka da
kasa aka kai wannan babban makiyi namu dakin
RIJIYA GABA DUBU na kurkukun Darul maut, lallai
acigaba da yi masa azabobin cikin RIJIYA GABA DUBU
har tsawon kwanaki goma sha hudun nan kafin as tafi
da shi birnin misra inda Sarki zai kashe shi a gaban
miliyoyin jama'a a lokacin GASAR JARUMTA, Koda
Muzaina tazo nan a zancen ta sai Marwatu ya risina
yace,Angama ya shugabata sannan ya juya ya fice
daga cikin turakar.
.RIJIYA GABA DUBU
Littafi na biyu 2
Na Abdulaziz sani m gini
Typing:- Ibrahim S combatant
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 2E
Faruwar hakan ke da wuya sai ga wata tsaleliyar
budurwa ta kunno kai cikin turakar, Hakika wannan
budurwa ta cika dari a fagen kyau domin sau tari idan
ta fito cikin gari bata wucewa tabar mutane lafiya
dole sai kaga hadari na faruwa, domin Wanda ke kan
jaki ko doki zai bangaje masu tafiya a kasa bai sani
ba,wadanda ke dauke da kaya a Kansu zasu saki
kayan su zube bash sani ba,Kai bama maza ba hatta
'yan uwanta mata idan suka yi arba da ita sai kaga
sun Wangame baki suna dalalar da yawu basu sani
ba,sabo da tsabar kyawunta da burgesu da take yi,Ba
wata bace wannan budurwa face Gimbiya LAMIRAT
'ya guda daya JAL! a wajen Sarki Gurzalu, A duniya
babu abinda Sarki Gurzalu yake so sama da Gimbiya
LAMIRAT, ba don komai yake tsananin sonta ba sai
saboda halayenta sun zo iri daya da NASA,wato ko
kadan lamirat bata son talakawa kuma sannan bata
da imani da tausayi ko kadan,Laifi kankani bawa ko
baiwa za su yi mata tasa a gaba musu azaba mai
tsanani ko kuma tasa a sare musu hannaye, idan ma
ranta ya baci sosai da kanta zata zare takobi ta sare
musu kai,Gimbiya lamirat ta gado mahaifinta Sarki
Gurzalu a tsananin Magunta da iya yaki sannan tana taba
samun tsananta gaba akan makiyi, domin idan tasa
shi a gaba sai taga bayansa, Bisa wannan dalili ne
take yiwa 'ya'yan sarakai da 'ya'yan attajirai na birnin
matukar kwarjini suke tsoron tunkararta da batun
soyayya ko aure, Ita da Kanta Gimbiya lamirat ta
dauke alkawarin baza ta auri wani namiji ba face
Wanda ya fita bata,karfin damtse kuma ya cinye gasar
jarumtaka ta nahiyar akan mahaifinta tunda
mahaifinta shine ke rike da kambun gasar sama da
shekaru ashirin ankasa samun Wanda zai karbe daga
hannunsa.
Lokacin da Gimbiya LAMIRAT ta shigo cikin turakar
Sarki Gurzalu ta iske shi tare da mahaifiyarta
Muzainat a zaune cikin farin ciki bayan fitar
sadauki Marwatu sai ta karasa garesu cikin tsananin
murna ta fada kan kirjin Sarki Gurzalu ta rungume shi
tana mai cewa, Ya kai Abbana ina mai tayaka murna
da aka samu nasarar kamo wannan babban makiyin
namu bayan ya gudu daga kurkukun Darul maut kayi
sani cewa naso ace ka bani dama naje har Darul
maut na kashe wannan makiyi namu da hannu na
domin ko sunan sa bana so naji an ambata bare
kuma na ganshi da idanu na".
bushe da
dariya yana mai janye jikinsa daga cikin na LAMIRAT
sannan ya tsuke bakinsa ga barin yin dariyar ya
dubeta cikin nutsuwa yace,yake 'yata rabin jikina ki
kara hakuri daga nan zuwa ranar da zamu hadu da
wannan babban makiyi namu a filin gasar JARUMTA
ta misra, zaki ga yadda zanyi masa kisan gillah ta
hanyar yi masa mugayen sare-sare da takobi na,lallai
sai na daddatsa shi kamar yadda ake daddatsa nama
a mahauta, yanzu zan sanar daku wani babban sirri
Wanda baku sani ba ke da mahaifiyarki, Ku sani cewa
wannan jarumi Imhal Wanda nake so nayi gasar
KAMBUN JARUMTA dashi ba wani bane face Dan
marigayi Sarki Imhal na kasar nan Wanda na kashe
shi na hau karagar mulkin da karfin tsiya,idan ban
kashe wannan yaro yanzu ba nan gaba sai ya kashe ni
ya karbi karagar mulkin sa,duk naga wannan al'amari
ne a cikin madubin tsafi na bisa bincike da nayi a jiya
da daddare. Koda Sarki Gurzalu yazo nan a zancen sa
sai hankalin Gimbiya lamirat da mahaifiyarta ya
dugunzuma ainun suka rasa abinda yake musu
dadi,cikin alamun tsananin damuwa lamirat tace,Ai
kuwa tunda haka ne yanzun nan zan he kurkukun
Darul maut na kashe jarumi Imhal da hannu na in ba
haka ba ina cikin zulumi da fargaba tunda ance Ka
kashe makashinka karfin ya samu damar kashe
ka,Koda gama fadin haka sai Gimbiya lamirat ta mike
tsaye da nufin ta fice daga cikin turakar amma sai
Sarki Gurzalu yayi wuf ya ruko hannun ta yana
murmushi ya dubeta yace,Haba yake 'yata ai kin sani
cewa duk irin kiyayyarki da Imhal bata kai tawa ba
amma sai gashi nayi hakuri ina jiran lokaci ya cika
Wanda ya dace da zan kashe wannan yaro, kin sani
cewa dake zanyi wannan tafiya izuwa birnin misra a
gabanki zan kashe wannan yaro, abinda nake so dake
shine, lallai ki danne kiyayyarki ga Imhal a yayin
wannan tafiya tamu, kada ki kuskura ki sanar dashi
cewa nine na kashe mahaifinsa da dukkan zuri'arsa
domin idan ya gano hakan burina na kashe shi a filin
gasar JARUMTA ba zai cika ba,Koda Sarki Gurzalu
yazo nan a zancen sa sai zuciyar Gimbiya lamirat tayi
Dan sanyi ta dube shi tace ,shikenan ya kai Abbana
zan cigaba da hakuri har izuwa wannan rana amma
fa ka sani cewa ba zan iya danne zuciya ta ba akan
nunawa Imhal kiyayya gami da cin zarafin sa da
azabtar dashi kafin mu isa birnin misra, Sarki Gurzalu
yace A a bana son ki taba lafiyarsa domin ina so ya
murmure kafin mu isa can din ramar dake jikin sa ta
bace kuma ya samu isasshiyar lafiya don kada
mutane suga cewar da nakasasshe zanyi wannan
gasa, Koda jin wannan batu sai Gimbiya lamirat ta
ciza yatsanta cikin tsananin takaici domin ba haka
taso ba,tabbas taci buri ta kara azabtar da Imhal
ainun bayan da ma ya Sha azabar RIJIYA GABA DUBU.
wannan shine abinda ya faru a gidan Sarki Gurzalu
kafin cikar kwanaki goma Sha hudun da za a fito da
Imhal daga cikin kurkukun Darul maut.
Al'amarin Jarumi Imhal kuwa bayan Angama yi masa
wannan azaba ta kwanaki goma Sha hudu da kayan
masifun dake cikin RIJIYA GABA DUBU an fito dashi
an kai shi gidan sarautar sarki Gurzalu a matukar
galabaice kuma a daddaure cikin sarka sai aka watsar
da shi a cikin rana yayi ta gasuwa a cikin harabar
gidan sarautar har tsawon kimanin sa'a guda sannan
sarki Gurzalu tare da 'yarsa Gimbiya LAMIRAT suka
fito Daga cikin gidan sarautar a cikin gagarumar
shigar yaki gami da kimtsawar tafiya, tun daga nesa
Gimbiya LAMIRAT ta kurawa Jarumi Imhal idanu
Wanda ke kwance a kasa magashiyan ya jike sharkaf
da gumi yana faman nishi kamar Wanda ransa zai
fita. duka da cewar Imhal ya rame matuka amma
surar jikinsa irin ta manyan sadaukai tana nan kuma
babu abinda ya taba lafiyar kyakkyawar fuskarsa,
koda tayi arba dashi a karon farko sai taji zuciyar ta
ta buga da karfin gaske kuma ta kasa sanin dalilin
haka, Yayin da sarki Gurzalu da Gimbiya lamirat suka
iso akan jarumi Imhal suka tsaya sai sarki gurzalu ya
sa kafarsa ya dunguri wani ciwo dake hakarkarin
Imhal,Imhal yayi Dan ihu sakamakon mugun zafin da
ya ji, shi kuma sarki gurzalu sai ya dube shi ya bushe
da dariya yace Ya kai yaro, ka sani masu iya magana
suna cewa, Rana bata karya sai dai uwar diya taji
kunya,Yau gashi ranar yin gasar mu ta JARUMTA ta
so kamar yadda na shaida maka, ko da gama fadin
haka sai sarki ya kirawo wadansu hadimansa yace, Ku
dauki wannan fursunan kuje kuyi masa wanka kuma
a kirawo likita na yayi masa magani sannan a bashi
kayan yaki yasa azo dashi bakin kafar gari inda za
muyi wannan tafiya tare dashi, Koda gama fadin haka
sai wadannan hadimai suka ciccibi Imhal suka tafi
dashi dakaru kimanin guda dubu na kewaye da su
don tabbatar da tsaro, saboda kar Imhal yayi
yunkurin guduwa duk da cewar yana daure cikin
sarkoki, Bayan an tafi da jarumi Imhal ne sarki
gurzalu ya juyo ya dubi Gimbiya Lamirat yace, amma
fa kin bani mamaki, wai shin duk ina zafin zuciyar taki
ya tafi ne alhalin ga babban makiyin namu a gabanki
amma ko dukan sa ba kiyi ba bare kiyi masa azaba ko
wulakancin da kike furucin za kiyi masa, koda jin
wannan batu sai lamirat tayi dan guntun murmushi
tace,ya kai Abbana kasani cewa bana cin zalin
ramamme ko nakasasshe, na fison na zalunci
lafiyayyen mutum Wanda ko yaya na taba shi zai ji
mugun ciwo amma ba ragowar mutuwa ba,Koda jin
haka sai sarki gurzalu ya bushe da dariyar farin ciki
yace Dakyau 'yata hakika barewa bata gudu danta
yayi rarrafe, lallai yanzu na gamsu cewar kin gaje ni
kuma ko a bayan raina nasan zaki iya tafiyar da mulki
kamar yadda nake tafiyar da shi.
.
.
RIJIYA GABA DUBU
Littafi na biyu 2
Na Abdulaziz sani m gini
Typing:- Ibrahim S combatant
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 2F
.
Koda gama fadin hakan sai sarki ya kama hannun
Gimbiya lamirat ya na ta suka tafi izuwa can kofar
gidan sarautar inda aka ajiye keken dokin da za su
hau don tafiya birnin Misra kuma ga dakaru masu
yawan gaske sun kewaye keken dokin gaba da baya,
kuibi-kuibi, wadanda zasu yi musu rakiya, kamar
yadda sarki gurzalu ya bayar da umarni haka akayi,
wato sai da aka yiwa Imhal wanka aka sa masa
magani a jikin raunikansa sannan aka kawo abinci
mai rai da lafiya aka bashi yaci yasha ya koshi,daga
nan kuma aka sanya masa kayan yaki a jikinsa, amma
maimakon a dama masa makami sai aka sake zuba
masa sarkoki aka daure shi aka kawo shi cikin
tawagar sarki da zata tafi birnin misra, nan take aka
sanya Imhal acikin wani akurki Wanda dawakai ke
Jansa aka kulleshi a ciki, sannan aka dunguma gaba
daya aka fice daga cikin birnin gaba daya.
Tsakanin birnin kisra da misra tafiya ce ta sa'a bakwai
don haka fun safe aka fara wannan tafiya ba a iso
birnin kisra ba sai da rana ta take, kai tsaye tawagar
sarki gurzalu ta nufi gidan sarautar sarki Taiyara don
haka sai ya shirya ya fito ya tare su cikin tsananin
murna, nan take aka shigar da Gimbiya lamirat da
mahaifiyarta izuwa inda iyalan sarki Taiyara suke, shi
kuwa jarumi Imhal sai aka kai shi cikin wani daki mai
kama da kurkuku aka kulleshi, Sarki gurzalu da sarki
Taiyara kuwa sai suka shige izuwa turakar sarki
Taiyara inda suka zauna aka kawo musu abinci da abin
Sha har da giya suka ci suka Sha suka yi tatul suna ta
kyalkyala dariya, daga can sai sarki Taiyara ya
numfasa ya dubi sarki gurzalu yace, Ya kai tsohon
abokina jarumin jarumai na wannan nahiyar, wai
shin bana da wanne guzuri kazo mana da shi ne?ka
sani cewa duk shekara Kaine kake lashe gasar nan
don haka babu sabon wani al'amari Wanda zai sa mu
samu kudade masu yawa tunda kowa ya San cewa
kaine zakaran gasar, yayin da sarki taryan yazo nan a
zancen sa sai sarki gurzalu ya bushe da dariya
sannan yace, Kwantar da hankalin ka ya kai abokina
kayi sani cewar nazo mana da wani gwarzon jarumi
wanda zai burge yan kallo kuma nine kadai zan iya
gamawa da shi, kafin na kara dashi zan bashi dama
yayi wasa kamar sau shida, ina mai tabbatar maka da
cewar a ranar da yayi wasan farko labarinsa zai bazu
a ko ina, kuma kashegarin da zai sake wasa sai filin
gasar ya cika ya batse da yan kallo don haka kafin
ranar da zamu kafsa ni da shi ba kananan kudin shiga
zamu samu ba.
Wannan karon har dukkanin sarakunan da ke nahiyar
nan sai sun zo sun kalli wasan karshe, domin suga
yadda zata kaya, Yau baza ayi wasa ko guda daya ba
sai gobe saboda ina son jarumin nawa ya huta sosai
ya samu karfin jikinsa, Koda sarki gurzalu yazo nan a
zancen sa sai sarki taryan ya bushe da dariya sannan
yace, Ya kai abokina nifa duk wannan labarin da na
bani naji sane kamar tatsuniya, duk da cewar banga
wannan jarumi ba da kazo dashi nasan nawa jarumina
sadauki Darwaz ya fishi komai da komai, don haka a
goben da safe ina son Darwaz da jarumin naka su
kara.Koda jin wannan batu sai sarki gurzalu ya sake
bushewa da dariya yace Ai shikenan, dama masu
salon magana sun ce sai an gwada akan San na
kwarai.
Sarki Taryan yana da 'ya' guda daya wata kyakkyawar
budurwa ta kwatance mai suna Shumaira, Shumaira
da Lamirat sun kasance kawayen juna tun suna yara
kanana saboda abotar dake tsananin iyayensu, don
haka suma sun shaku ainun, Wani abin mamaki
shine, ko kadan ra'ayinsu baizo daya ba,domin ita
Gimbiya Shumaira tana da tsananin tausayi, sabanin
lamirat wadda ta kasance Mara imani ga zalunci,
hakan bata sa sun kasa shakuwa da kaunar juna
ba,amma suna yawan samun sabani domin ako
yaushe Shumaira tana matsawa lamirat akan ta daina
zaluntar talakawa da masu rauni, wani lokacin ma
idan suka samu sabani, sai su kwana uku basa
magana da juna,kuma su daina kwana a waje daya da
con abinci tare.
Gimbiya Shumaira na zaune a cikin turakar ta sai ga
Gimbiya lamirat ta shigo, Koda ta dago kai suka yi
arba da juna sai Shumaira ta Mike zumbur! ta ruga
gareta cikin tsananin farin ciki suka rungume
juna,Shumaira ta janye jikinta daga cikin nata suka
fuskanci juna sannan tace,Ai tun jiya nake zuba ido
naga kun iso amma sai naji shiru tunda dai shekara
ta zagayo, Lamirat tayi murmushi tace Ai mun kara
kwana daya ne akan lokacin da muka saba tasowa,
saboda wannan karon mun taho da wani gagarumin
jarumi, wanda za a samu kudade da yawa a dalilin
sa,Koda jin wannan batu sai mamaki ya Kama
Gimbiya Shumaira tace, Haba ya ke kawata yanzu
Ashe har za a iya samun wani jarumi wanda zai
burge mutane a wannan nahiyar tamu sama da
mahaifina ki?Lamirat tayi murmushi tace,Ai bana
nufin yafi mahaifina JARUMTA, amma dai zai taka
muhimmiyar rawa a wannan gasa da za ayi ta
bana,kuma ina tabbatar miki da cewar inba mahaifin
nawa ba babu wanda zai iya kaishi kasa a wannan
gasa, Shumaira ta girgiza kai tace Yake kawata kin
sani cewa ban taba zuwa kallon wannan gasa ba
saboda ko kadan bana son naga jini yana zuba, bana
son naga ana kashe mutane a aikin banza, amma
wannan karon naji zuciyata tana son taga wannan
bakon jarumi wanda kika zo mini da labarin sa don
haka indai zai yi wasa gobe zan fita filin gasar na kalle
shi don kawai naga iyakar jarumtakar tasa da kike
kodawa, Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube
Gimbiya lamirat saboda ta dade tana son ta dinga Jan
Shumaira suna fita kallon wannan gasa tare amma
taki tsawon shekara da shekaru, Tabbas lamirat tayi
mamaki da taji Yau dare daya Shumaira ta amince
zata fita kallon wannan gasa.
.
.
RIJIYA GABA DUBU
Littafi na biyu 2
Na Abdulaziz sani m gini
Typing:- Ibrahim S combatant
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 2G
.
A daren wannan rana kuwa aka yi ta shela birni da
kauye cewar sarki gurzalu yazo da wani sabon
gwarzon jarumi kuma ansa cacar kudi akan sa cewar
duk jarumin da ya kai shi kasa za a bashi dinare
miliyan daya,kuma sannan zai yi wasan farko a gobe
da safe tare da sadauki Darwaz na birnin misra, Koda
wannan labari ya bazu sai gari ya rude da kace nace
ana mamaki, attajirai kuwa suka yi ta shirya cacar
kudi a tsakanin su kowa na zabar gwaninsa a
tsananin jarumi Imhal da sadauki Darwaz, Jama'ar
gari kuwa mata da maza yara da manya kowa ya
dinga dokin gari ya waye yaje ya biya kudin shiga filin
gasa domin ya ga irin gumurzun da za ayi tsakanin
wadannan manyan jarumai.
Kai! tun kafin ma gari ya waye filin gasar ya cika makil
ya zamana cewar har akan katanga mutane ne a
zaune, duk inda mutum ya duba baya ganin komai sai
kawunan bil'adama, babu wani guri da yayi saura sai
na sarakuna da manyan attajirai, sune kadai basu iso
ba,sai kuma jaruman da za suyi gasar, wato jarumi
Imhal da sadauki Darwaz.
Sadauki Darwaz wani narkeken katon mutum ne mai
girman gaske wato mai kirar mutanen farko, Darwaz
ya kasance shahararren gwarzon mayaki mai
tarwatsa maza a filin daga,A ranar da suka fara yin
gasar kambun JARUMTA shi da sarki gurzalu, dakyar
shi sarki gurzalu ya samu nasarar kaishi kasa,don har
sai da ya yanki sarki gurzalu sau biyu bayan sun shafe
sa a daya da rabi suna bakin yamutsi, daga wannan
lokaci basu sake haduwa ba kawo I yanzu, kuma har
gobe ta ciki na ciki, domin kowannensu yayi matukar
bakin ciki bisa yadda gumurzun nasu ya kasance
saboda sun Sha bakar wuya sun zubar da jini,
wannan karon da sadauki Darwaz yaji cewar jarumin
da zai kafsa dashi, sarki gurzalu ne yazo dashi sai yaci
mugun burin daukar fansa a kansa ya kudurce a
ransa cewar a gaban sarki gurzalu zai yiwa jarumin
kisan gillah.
Sai da gari yayi haske sosai sannan jama'a suka ji
anfara buga tambura ana busa algaita da sarewa
alamar cewa sarakuna zasu fito daga cikin gidan
sarautar, nan take gaba daya jama'ar dake filin gasar
suka mimmike tsaye don girmamawa, Fadawan sarki
taryan da manyan attajiran kasar suka fara shigowa
cikin filin gasar, sannan sai ga sarki taryan, sarki
gurzalu, Gimbiya lamirat da gimbiya Shumaira sun
shigo,dakaru da kuyangi na take musu baya har suka
iso wajen da aka tanadar musu mai dauke da kujeru
na alfarma,Koda jama'ar gari suka ga Gimbiya
Shumaira ta fito kallon wannan gasa sai suka cika da
matukar mamaki, nan dai su sarki taryan da su
Shumaira suka isa mazauninsu suka zazzauna.
Al'amarin jarumi Imhal kuwa, tun a jiya bayan anyi
masa wanka, ansa masa magani ajikin raunikan
jikinsa, kuma an bashi abinci na alfarma ya cika cikin
sa sai ya nutsu sosai ya dawo cikin hayyacinsa inda
ya fada cikin kogin tunanin abubuwan da suka faru a
baya.
Babu abinda ya fara fado masa a rai face irin
tsananin azabar da aka gana masa a dakin RIJIYA
GABA DUBU ta tsawon kwana goma Sha hudu, A
tsawon kwanakin azabar gobe tafi ta jiya, haka akai ta
azabtar dashi babu sassauci, azabar farko itace
wadda kunamun nan suka fito suka yi ta cizon
sa,kashegari kuwa macizai ne suka fito suka yi ta
saran sa,haka abin ya cigaba da wakana, wata ran ya
ga dodanni suyi ta dukansa suna tamola dashi. Koda
jarumi Imhal ya gama tuno wannan masifaffiyar
wahala da ya Sha acikin RIJIYA GABA DUBU wacce ke
cikin kurkukun darul maut, sai ya takarkare ya
kwarara uban ihu,Ihun nasa ya cika gidan sarautar
gaba daya, har sai da dakaru masu yawa suka rugo
izuwa kofar dakin da yake,Koda suka leka suka gan
shi a kwance a kasa kuma a daure ga kofar dakin a
kulle sai hankalin su ya kwanta, sabo da dama can an
gargade su matuka

4 Comments On RIJIYA GABA DUBU
avatar
mlm

1 year ago

Reply

Next please

avatar
khadija-1-4

1 year ago

Reply

??????

avatar
muhammad-musa

1 year ago

Reply

Good book

avatar
ismail-9-8

10 months ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment