Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


BAR RAINA ALLURA, KARFE CE
Na BENAXIR OMAR
Misalin karfe takwas daidai yayi parking
motarsa kirar benz E450 amazauninta, yafito
a hankali sanye yake da kananun kaya, farar
tshirt anrubuta,Love is life , sai kuma
jeans,dakuma shade dinsa dayacire ya ajiye
a motar kafin yafito, tafiya yake yana juya
agogon rolex din dake hannunsa don yaga
karfe nawa, har ya isa kofar yadanna
kararawar, watace sanye da uniform fari
wanda zai tabbatar ma dacewa mai aikice,
tabude tare da rusunawa tanacewa welcome
sir!, bai kulata ba balle ya amsa mata kai
tsaye yashige falon zama yayi dirsham a kan
kujeran yana maida numfashi adaidai lokacin
yaji saukowa, yasan wacece donhaka yakara
langwamewa tareda jiranta, tana saukowa
fuskanta cire da annuri, dattijuwa ce,
maabocin faraa da kamala, ga hasken fuska
da kammani da dan nata wanda batare daka
tambaya ba zakasan ita tahaifeshi komi nata
tsak a fuskanshi, takaraso tareda cewa
babana ka isone? Cikin shagwaba yace
mumy wlh nagaji yunwa nakeji, tace yanzu
zaakawomaka abincin ka tsaya kadan
dafatan kayi sallah? Yace saidanayi a
masallaci nakaraso, wasu ne sanye da
uniform kamar wacce ta bude masa kofan da
farko suka shigo rike da tire a hannunsu,
kulolin abinci ne da plates, haka suka jera
komi akan table din sannan suka juya,suka
fice, mikewa yayi hajiyar tasa tana biye
dashi har suka isa dinning din, budewa
yafarayi daddaya, ferfesun kaza ne, sai
kunun gyada, dakuma coconut fried
spaggetti, duk kamshi yacika dakin,
2 BAR RAINA ALLURA KARFE CE
Na Benaxir Omar
Ya dauki serving spoon yafara zubawa ,
sannan yafaraci , yace hajiya ina rahma da
ramlat? Tace yau sunada lectures har 6
inaga sai magrib kagansu, yadan yi shiru
sannan yace ni wlh hajiya, dakin barsu
sunzauna a hostel wannan to nd fro dasuke
tayi, tace a a kam, inasu ina hostel? Kafini
sanin halin kannen naka, baruwana donhaka
ka hanzarta kaci kaje ka watsa ruwa, tafice
tabarshi agun, wayarshi yadauka yakunna
data dinsa, sannan yadale instagram, yanajin
dadin abun ko bakomi yana ganin fuskokin
mutane, hotunan abubuwa dakuma yadda
duniya take ciki, yayi liking abunda yaga zai
iya, sannan yasauka yakoma whatsapp,
kwata kwata abincin baifi cokali uku yayi ba,
anma duk hankalinsa nakan iphone6 golden
colour, dayagama akalla yakai awa daya
ahaka yamike yahaura sama dakinsa yanufa,
dakin tsaf tsaf, daganan mutum zaigane
cewa irin maza masu tsafta ne, don dakin
kamshin turare take, ga sanyin ac. Na buga
dakin, bandaki yashiga ya watsa ruwa, yafito
ya shirya tsaf bayan turaruka daya fesa
masu uban tsada ya kwashi wayoyinsa,
guda biyu sannan yafito kasa yasauka yaje
daidai gun keys set, yafara duba makullan
motan, yana tunanin wanne zai hau,
FE CE
NA BENAXIR OMAR
can dai yaga ta lexus yadauko sannan
yakara hawa sama dakin mumy yanufa
yabude dakin nata, kamshine yabugi
hancinsa as normal kullum don shi yana
ganin gadon mahaifiyarsa yayi, tanada son
tsafta da kamshi, yace mumy barinje
nadaukosu rahma , ta ce yoo gani kake
kaman bazasu dawo bako? Kaikam kaida
yarannan,ya sosa keya tareda cewa nikam
dai mumy sainadawo, ficewa yayi yatafi
garage yabude lexus din yashiga fara ce sol,
gashi yasha wasu kananun kaya fari dakuma
bakin wando, yana shiga yakunna a c din
motan sannan yafito horn yayi wa maigadin
suka bude masa kofan sannan yafice, atbu
yanufa yana isa gate din makarantan yadau
wayansa yakira rahma, cikin karamin
muryarta tace yayah ina wuni? Yace kuna
ina? Tace muna slt. Yace ganinan zuwa
batareda ya sauraresu ba yakashe wayan, slt
yanufa sannan yaja yayi parking, bai daga
waya yakira yace ya isoba, baikuma kashe
motanba, rahma da ramlat dake zaune suna
jiran lecturern ance bazaizo ba, ramlat tace
kitashi muje waje kinsan yanzu mayb yayah
yazoshi kuma kinsan akidanshi bazai taba
kiranki yace ya isoba, kuma bazai taba tafiya
ba, anma ke kinsan abunda zaiyi as result is
beta tun farko mufita ko zamu ganshi, suka
mike tsum tsum suka fito aikuwa suka
ganshi rahma ce tabude gaban motan
tashiga ramlat kuma tashige baya, rahma
tadanyi yakee sannan tace yayah yaushe ka
iso? Yace dazu , tayi shiru. Tohfa rayuwan
kenan, kullum yanaso yaga suna gefensa
anma dazaran sunzo saikuma zaman
kurame, zaman kudaje sukeyi,
Nasan zaku damu kusan wayeshi wannan
guy din, inata bada labari anma bakuma san
sunanshi ba ko? Toh sunanshi HAIDAR
AMINU HAIDAR,*Kubiyoni donjin labari
wanene shi? Sannan suwaye wannan
yanmatan?

FE CE NA
BENAXIR OMAR
Haidar aminu haidar Da ne danfari agurin
alh.aminu haidar dakuma haj.hauwa wacce
aka fi sani da hajiya fulani, shikadai ne
namiji sai kannensa biyu mata ramla yar
shekara 22 tana karanta chemical
engineering a atbu ajinta biyar, yayinda
rahma yar shekara 19 tana aji biyu tana
karantan architrcture. Rahma da haidar suna
balain shiri halinsu daya, sunkuma shaku,
saidai gaba daya suna tsoron yayan nasu
don mutum ne wanda baaganin faraarsa da
garaje. Idan anga yayi murmushi toh hajiya
fulani ce agefensa donko a gaban mahaifinsa
baya murmushi. Kullum fuskansa ba yabo ba
fallasa,suna zaune ne a kaftareren gydan da
alh.aminu ya gina musu a g.r.a gydan sama
ne. Babban gyda wanda yakamata a ajiye
mata hudu, saidai inaa alh.aminu bayada
burin auren mata biyu, donhaka haj.fulani
itakadai take zaune a gydan ba kishiya,
yaran suntaso cikin tarbiya. Da kudi da
shagbwa, saidai akwai ladabi wana gaba
dakuma hankali da nutsuwa , alh.aminu
bayada son jamaa hakan yasa hatta
matarsa bata kawo masa mutane. Balle azo
kan yaran dama asali shi haidar bayada
wata wacce yake kulawa
5 BAR RAINA KARFE ALLURA CE NA
BENAXIR OMAR
Kannenshi biyu sunzame mishi hasken
idaniya, domin inhar zasu fita toh rahma ce
agaba, gasu farare tas irin shuwa arab
dinnan, kana ganinahi da rahama kamar yayi
kaki ya ajiyeta, ramla kuma dibin ta
dabanne, saidai itama akwai kyau
tubarkallah , ga gashi da tsayi wanda
shikanshi farin ciki yakeji imhar yafita dasu,
donma Allah yasa bamai tara tarkacen
abokai bane, abokinsa daya sadiq , sadiq
yakada yaraya akan haidar yahadashi da
kanwarsa daya anma inaa, haidar yaki,
bakuma don wani hali na sadiq dinbane,
shikawai yasan bayaso abata wa kanwarsa
rai, idan aka bata toh tabbas kowaye
zaasamu matsala dashi shiyasa tun farko
baya so hakan tashafi abokantakarsu.
Inmuka gangaro kanshi haidar wani irin
namiji ne mai farin jinin yanmata, indai zai
wulga ko yashiga taro sai ansamu wacce
zata biyoshi, mata masu ji dakansu kuma,
yayan masu kudi da yaran sarakuna, idonshi
kadai ya isa yatafi da imanin kowacce mace,
don cikin kwayan idonsa blue ne wanda
hakan na wuyan samu agun mutane,
saikuma manyan ido, yana da dimple ga
gashun saje yasauko yarufo gefen fuskanshi,
dogo ne yanada faffadan kirji, wanda hakan
zai tabbatar ma dacewa baiyi wasa da
lafiyar sa ba, bayason rana ko kadan. Hakan
yasa yakanyi wuya aganshi da rana, sannan
duk maitan shi da abu indai aranane yakan
hakura. Duk da nafada bari dai nakara
maimaitawa tsafta ni benaxira irin wannan
tsaftanshi tana ban mamaki. Namiji mai
uban kyankyami, ga son kamshi, bayason
kazanta, acikin garin bauchin akwai
anguwoyin dabaya zuwa, ko hanya bayabi
saboda yanayin anguwan. Balle kuma yaga
mace kazama akan hanya jiyakeyi kaman
yayi amai, abunda bai taka kara yakarya ba,
sai aji haidar yatoshe hanshi. Yanada raina
tsaftar mace. Duk tsaftarki kankanim wari
yana bugan hancinsa zai juya bakuma zaki
gara ganinsa ba. Social ntwkn nayau da
gobe yasa yasamu kawaye dayawa anma
bakowacce yake kulawa ba, duk dacewa
saidai a chatn anma banda haduwam fuska,
baicika zama ba akasar balle ma atakurashi,
wannan shine HAIDAR AMINU HAIDAR
CE NA
BENAXIR OMAR
Ahankali yake tukasu harya isa gyda, horn
dayayi ne yasa masu gadin suka bude a
hanzarce. Yaduru cikin gydan daidai inda
yadauki motan yaje ya ajiye sannan suka
tsaya yabude kofansa sannan suka bude,
don aladansa ne, idan har zai kaiki guri idan
kun isa dole kijira yafara bude kofa duk
saurinki kina budewa zaice kim rainashi
yazaayi yakaiki guri kuma kifice kibarshi ko
bazai fita ba, zai bude kofansa saike kibude
naki kafin yamayar danashi yarufe, ganin
yabude nashi yasa suma suka bude nasu,
suka fito ramla Allah Allah take taganta
adakinta don wlh tagaji ga yunwa gakuma
ana so afara kiran sallan magrib, masallaci
yafice yayinda sukuma suka shige ciki. Sama
suka haura kowacce da dakinta acikinsu,
rahma colourn dakinta komi pink yayinda
ramla purple dakinsu tsaf wanda zaace
budurwa nai tashe daji dakanta tasamu,
komi a kimtse, watsa ruwa sukayi, yayinda
masu abinci suka fara zarya zarya don
shirya musu abinda zasuci, dama a
maakaitan gydan tsabar tsince tsince irnna
haidar da kyankyami yace shi bazaici abincin
masu aiki ba, zuwa akayi akanemo
musulmai wanda sukayi cathering skul
subiyu, akayi training dinsu kan yadda zasu
tsaftace komi kafin ya yadda yafara cin
abincinsu, komi nashi dabanne
BENAXIR OMAR
Rahma ce tafara saukowa kafin ramlat kan
dinning suka nufa, abincin suka bubbude
suka fara diba, ganda ramla tadiba taja gefe,
yayinda rahma tadauko fruit salad tafarasha,
rahma tace ni nace sudena samin pineapple
banaso sunki. Ramla tace yooh toh inbanda
abunki yazaamiki fruit salad ba pineapple ai
dadin bazai cika ba, nan dai rahma taringa
surutai, dama ita shes too picky akan abinci,
kamar yadda haidar yake shima, shigowa
yayi tare da sallama yanufi kan kujera
yazauna sannan yakunna tv, ball yafara
kalla, arayuwansa shi dan arsenal ne. Yana
balain son arsenal, komi nasu ya mallaka,
agogo, tshirt, dawasu car statue, da akafita
break yamike yadau waya tareda cewa sadiq
kana ina? Sadiq din yace ina hanya barin
karaso, dama a kaida tare suke kallon ball,
baadawo daga break dinbama sadiq yashigo
suka zauna ayayinda masu hidiman abinci
suka fara zarya zarya don serving dinsu
dinner, suna tadi sunaci har aka gama kallon
ball suka mike, ficeewa sukayi sukabar
gydan, haidar ne mai tuki, ahankali yake tuki
harya sukayi hanyan aroma, dama normally
gurin akwai yan good evening, yanmata
karuwai wanda sukecin kwalliya su tsaya
abakin titi duk namijin dake raayi sai yazo
ya tsaya ya kwashesu, sunsaba wucewa
kullum shidai haidar Allah wadai yake dasu,
gashi kyankyami suke bashi, kuma kaman
dole kullum sai yazo yawuce inhar zai sauke
sadiq,yauma sundanno har zasu wace sai
sukaga kaman fada akeyi ma, yanmatan su
ukune sunsa kananun kaya, toh biyu saisuka
sa daya agaba da duka
BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA
BENAXIR OMAR
Sadiq dake ta gefen yaja glass dinsa yana
kallonsu, harsuka wuce, yace nikam toh
aneman kudinsunma akanme zasuyi fada?
Haidar ko kulashi baiyiba donshi haushi suka
bashi kaman yamusu duka, sunwuce har sun
isa gate, sai sadiq yafara salati namanta
wayana wlh dan Allah kazo muce in dauka,
haidar yace kaifa matsalana dakai kenan
kacika mantuwa wlh, nikam oya zoka ja
motan, sadiq yafara lankwasa murya a a don
Allah kayi hakuri muje aboki na,haidar ce ai
baka isaba, fita yayi yazaga yaja yabude
yace oya fito kaje kaja nagaji, donhaka sadiq
yayi murmushin tareda futowa yashiga yaja
motan fuuu suka fice, haka suka kara wuce
gurin yanmatannan anma kaman abun
tsananta yayi domin wannan karon sunyaga
mata riga taja gefe tana kuka, shidai sadiq
duk shiyake lura yayinda gogan naku
shikuma ko ajikinsa, suka je yashiga
yadauko wayan sannan yafito, suka kara
dawowa ahanyan dawowa ne yafara rage
gudu, haidar yace mekuma kamanta? Sadiq
yace ba mantuwa bane inaso naga
yarinyannan ne kaman tana cikin wani hali,
haidar yaja tsaki akwai mutanen dayakamata
kataimakawa dayawa ba karuwa ba okay?
Shidai sadiq bai saurareshi ba, ya tsaya da
motan tasa daidai inda ta tsuguna, ta
sunkuyar dakanta akasa, tajanye inda aka
yage domin tarufe tsiraicinta, hasken wutan
yarage tareda horn anma bata dago ba,
hakan yasa ya dalleta da haske, shidau
haidar naganin ikon Allah, ahankali tadago
fuskanta, duk da bata ganin suwaye tamike
tareda ja baya don taga sun tsaya, a
tsammaninta kar kuma su zata zata tafi ne
itama
A
BENAXIR OMAR
Wadannan yanmatan dasuka mata dukan ne
sukazo dagudu suna tsaye tareda buga glass
din alamun gasu sun iso, sadiq yasauke
glass din sannan yace kumin magana da
wancan,dayar wata baka wanda tunda
haidar yadaga ido yaganta yajuya bai kara
juyawa ba, asali toshe hancinsa yayi don
wani wari yakeji da babu kanta, tadan
yamutsa fuska sannam tace ai ita wancan
ba aikim take ba, mune kadai muka rage,
sadiq yace ae ki kirata, tadanja gefe tajeta,
bayan mintuna kadan sai ga wancan din
tazota ahankali, duk jikinta bari yake, sadiq
din yabude kofan motan, alokacin haidar ji
yayi kaman yafita yarikoshi yafara masa
duka, anma yasan sadiq da laushin zuciya
da son taimako, yana fita tana gefen
windown haidar din aloacin ko kallonta
baiyiba, atunaninsa zaiga irin wancan fuskan,
saidai wannan baiji wariba, haryake cewa
toh ko ita bata wari ne, sadiq ne yace meya
sameki naga suketa daka kaman sunsami
sakwara,? Abun yaso yabawa haidar dariya
anma dai yadanne, batace komi ba,
yakaracewa ko zaa kaiki gyda ne? Tadan
gyada masa kai. Yace toh oya shiga muje
nakaiki, yabude mata gydan baya, haidar ji
yayi kaman yasa hannu akai ya tsala ihu,
anma bayaso ya disga abokin nasa don
motanshi ne, sai yashare kawai, yayi
nadaman bashi tukin aidashine da ba wanda
ya isa yasashi tsayawa sadiq ya zago yafara
tukawa yace wani anguwa kike? Cikin rawar
murya tace agydan yayata nake zaune a
gwallaga saidai kar ka kaini, ka kaini ko
wunti ne na kwana, yace meyasa? Cikin
sheshkan kuka tace saboda zatamin duka
tace miyasa bansamo kudi ba,, haidar saiyaji
jikinsa yayi sanyi, daga ganinta saan rahma
ce karamar yarinya ce. Saiya yi shiru sadiq
yace muje nakaiki, sai nabaki kudin nawane?
Tace arana dai kwana daya dubu biyu ne ko
dubu uku, haidar wani tsaki yaja, wai ace
karamar yarinya har zataje tabada kanta don
kawai tasamu dubu biyu? Ashe sadiq shima
abun yatabasa donhaka saiyace, yanzu kina
nufin kullum kina zuwa nam don abaki dubu
biyu, tazaro ido tareda girgiza kai cikin kuka
tace wallahy bantaba kwana da kowaba,
akwai wata kawata datayi aure idan antyna
tace nasamo kudin sai kawartawa tace
mijinta yabani, toh jiya mijin ne yace
yanasona sai muka bata da kawar tawa,
sanadin haka yau nafara zuwa nan, shiyasa
danazo wadannan suka rinka cewa ban
iyasa kayaba, sukeso suciremin don nadawo
irinsu danaki shine suka hauni da duka, Allah
ne yataimaken harkuka iso, sadiq shiru yayi
barinma haidar da tunda tashiga motan bai
tanka ba, kuma bai nuna alamun zai tankan
ba, ita kanta rashin maganan nasa yasa ta
tsargu hartake jin ko yanajin haushinta ne,
sadiq ne yatsaya adaidai kasuwan. laushi
fita yayi ya je yasiyo kayayaki yazo yabude
kofan yaje shagon matan, tareda rokon
subata guri domin tasamu. Tacanja, yadawo
motan yazauna yana jiranta, yacewa haidar
kayi hakuri abokina wlh yarinyan tayi karama
ne sosai for all this stuff shiyasa kaga
nadage, kuma daga gani kasan shes a
novice, haidar yace bakomi. Hakan ya
mugun bawa sadiq mamaki, anma dai yayi
shiru tunda ansamu saa abokin nasa bai yi
complain din dayake expecting ba, bude
motan sukaji tashigo alokacin sadiq yajuya
tareda cewa muje nakaiki? Ta gyda kai ae
uncle, dariya ce ta kufcewa haidar wanda
baiyi niyyan yiba, tare dacewa wato ma
sadiq yadawo uncle, yadda yayi maganan
har cikin ranta taji maganan, wato yasan
yanada dadin murya daz y yake makalewa
saboda kar anaji
1 0 BAR RAINA ALLURA KARFE CE NA
BENAXIR OMAR
Sadiq yadan hade rai tareda cewa haidar
kaikuma watz funny? Haidar ya girgiza kai
baice komiba, itakuma bata kara cewa komi
ba, sadiq ne yace sunana abubakar sadiq,
zaki iya kirana sadiq, tace toh yaya sadiq,
yauwa gwara hakan injishi da fada domin
shikanshi yaji wani iri datace masa uncle,
gwallaga suka isa, tana nuna musu hanya
dakyar suka ringa duruwa, tunda haidar yake
baitaba zuwa gunba duk ginin gun yamasa
wani iri, har yake jinjinawa aransa lalle toh
tundaga wannan kusurmin lungun take
takawa bakin titi? Babu abinda yabashi
mamaki saijin datayi cewa mu tsaya anan ,
mota baya shiga ta lungun, sadiq yayi
parking yace zaki iya karasawa da kanki? Ta
gyada kai tare dacewa ae, yaciro bandir din
dari biyar yabata, ungo wannan kiboye,
kullum kina cire dubu biyu kinabata,
shikenan zata barki ko? Ta gyada kai tareda
cewa anma idan ta bincikeni tagansu
dayawa zata iya korana naje nanemo irinsu.
Ya karba yaware dubu uku yabata, yace
ungo wannan kibata, gobe zanxo saiki fito
nabaki haka zamunayi har Allah yakawo
hanya ko, karki kuskura ki saida mutuncinki
kina ya mace
[5/24, 9:56 PM] Adda bena: BAR RAINA
ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR
Ta gyada kai tareda cewa nagode, nagode.
Allah saka da alheri, Allah kara budi, yajikan
iyaye.bashiba hatta haidar yaji dadin
adduan, duk da Allah Allah yake tafita don
so yake tafice yanaso yayi magana, tana fita
ya danka wa sadiq harara tareda cewa
bangane kanaso ka makalewa yar mutane
ba, daga ganin yarinya bakasan halinta ba
zakafara biyeta?,you are so cheap, who
knws ko yarinyan tazauna ta sheka maka
karyane?, shidai sadiq gyra mota yayi yafice
baice uffanba, gydansu ya tsaya tareda cewa
abokina i believe bacci kakeji tuka kakoma,
haidar tsaki yaja cike da takaicin yadda
sadiq yabata masa lokaci yafita a motan
yakoma gurin mazaunin mai tuki sannan
yaja motan, ayadda yaja yatabbatarwa sadiq
lalle ran abokinsan yabaci. Haka yashige
gyda duk tunanin yarinyan yakeyi gashi ko
sunanta baisaniba,
Haidar nashiga gyda yabada mukullin wa
maigadin tareda cewa gobe ka tabbata gobe
anwanke motan nan don Allah, yace toh
oga!, yana shiga toilet yawuce yasake wa
kansa shower, saidai yadda yarinyan take
magana yakeji akansa, haushinta duk yabi
yacikasa, shikam jiyake kaman yahadata da
ita da sadiq yayiwa duka, haka dai yakwanta
ranan
Washegari sadiq tuni yashirya domin yatuna
alkawarin dayamata nacewa zaina zuwa don
yabata kudi, yana xuwa daidai inda motan ta
tsaya jiya yajirata, yakai minti ashirin kafin
yaga tafito sanye da hijabi har kasa, zata
wuce Allah yataimakeshi wutan gefen gydan
dayayi prking ne ta haska dabazai ganetaba
harta wuce, tuni yamata horn anma taki
juyowa ita a tunaninta zataga motan jiya,
fitowa yayi yasha gabanta ta mugun tsorata.
Don dogo ne a zube yake, tsayinsu daya da
haidar, zata yi magana yace muje kishiga
kafin su ganki, nan ta tsuguna ina wuni ya
sadiq, bai kalleta ba yawuce motan yabude
mata tashige sannan shima yazaga yashiga
tagefensa, yana shiga yaciro kudin yabata.
Sannan yakaramata dubu daya gashi ko zaki
bukata. Kinada waya? Tace bandashi, yace
zansiya miki, ta zaro ido antyna zata kwace
kabarshi kawai, yace toh shikenan, gobe in
zaki zo ki tsaya anan innazo zaki ganni,
harzata fita tace dawannan motan ko? Kar
wasu dabanne, yace motata ba daya bace
kowani mota zaki iya gani, kedai inkinzo
kitsaya in nine zanfito, tace toh, harta fita
taleko tareda cewa ina dayan yayan? Yau
baizoba, yayi dariya yace waye haidar?
Wannan halane ki kara ganinshi, baya shiga
maganan mata, tajuya tareda cewa sai
anjima, harta shiga lungun ta tuna har
lokacin bai tambayeta sunanta bafa! Lalle
mutumin nan wani iri ne?
[5/24, 10:12 PM] Adda bena: BAR
RAINA ALLURA KARFE CE NA BENAXIR
OMAR
Sadiq kuwa jan motanshi yayi yafice,
tundaga ranan kullum zaixo yabata kudi
hardana kashewa baitaba tambayanta
sunanta ba, sannan kullum inzata fito toh da
hijabine, inzai wuce gydansu haidar saiyazo
yabata kafin yatafi, ahaka har sati biyu,
kuma kullum in haidar zaice daga ina? Toh
zaice daga gun baiwar Allah, wataran kam
ma, saiyace inagunta yanzu zandawo, ranan
saida haidar yatikeshi tareda cewa banga
maikagani ajikin yarinyannanba, kabi kanace.
Yanmata nawane masu asali a garin bauchi
ka gagara dubawa? Shidai sadiq baice uffan
ba , daga bayane ma yace bazaka gane
ladan danake samu bane, sunsha samun
matsala akanta anma sadiq haka yake
shanyewa tunda yake baiga yadda haidar ya
tsani mace kamantaba, kiri kiri yake nunawa,
watarana urgent meeting takama sadiq yabi
flight sai abuja magrib nayi yatuna cewa
lallai ashe yau ashe zai bawa baiwar Allah
kudi, yarasa yazaiyi gashi tunda yake
baitaba zuwa da kowa ba, balle yace aje
akai, mutum dayane haidar kuma yasan ko
sama da kasa zata hade bazai je ba , yarasa
yazaiyi saiya fara tausayin yar baiwar Allah,
yarasa yazaiyi da ransa, wayansa yadauka
duk dayasan bamai yiwuwa bane yakira
haidar. Haidar na dauka bayan sungaysa
cikin tausayi yace abokina kataimakeni,
haidar yace menene? Yace nasan bazakayiba
anma badon halina ba don Allah nace maka,
yacr inajinka, wannan baiwar Allahn ne
nabarta, yau yakamata nakai mata kudinnan
kuma kasan daddy yaturon urgent meeting
abj, inbatakai kudin gydaba antynta zata iya
sata awani hali, don Allah kacece tarbiyan
ya mace, harya gama haidar baice uffan ba,
saidaya gama sosai, sannan haidar yace
kanemi wani, kafin yakashe wayan sadiq
yace wlh tlh babu wanda yasan gun saikai,
haidar yace nidin angayama zanganene?,
sadiq yace kai zakafi ganewa da kwatance
don Allah abokina, don darajan manzo SAW
ba don halinaba, ganin yadda yaketa rokonsa
yasa yace oya karka kashe wayanka harna
isa, tsalle sadiq yayi don baizata haidar zai
yadda ba. Da kwatance yakaishi har gurin
inda yake parking sannan yace yajira zatazo
yanzu, suna magana saigata da jibgegen
hijab, saidai datazo ta tsaya agefe kamar
yadda sukeyi sai ta tsaya idan sadiq yaga ta
tsaya sai yabude motan yamata magana, toh
kaikuma gogan haidar ashe ya shaka har
ransa! Yazaayi ita dazaa taimakawa tazo ta
tsaya kaman soja yacewa sadiq wlh zantafi
inbanda iskanci tazo ta tsaya agaban motan
nizan fita na sameta? Ko ba ita bane? Sadiq
yace itane kabude kofan kamata magana,
haidar yaja tsaki lalle kuwa ashe bazata
taba karban kudin nanba, saidai na juya
natafi, har ya kunna motan yayi horn dakarfi
bashiri tazo tagun, yaciro kudin yamika
mata, ta saba tashigo sugaysa donhaka
shigowa da zatayi anma ganin yamika kudin
ba magana yasa ta sha jinin jikinta tasa
hannu takarba ganin ba sadiq bane, anma
haidar ne for the second time takare masa
kallo lallai guy din yahadu, tace cikin zakin
muryanta ina wuni yaa haidar. Haushi yaji
kaman yamata duka aina tasan sunansa?
Tana karban kudin ya ja motarsa fuuuuuuii
yafice yabarta a tsaye agun!
[5/25, 3:49 PM] Adda bena: BAR RAINA
ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR
Mamaki yacikata wannan wani irin mutum
ne? Komawa tayi gyda, shikuwa gogan naku
ya na tafiya haushinta duk yabi yacikesa,
yama zaayine yakai mata abu sannan ta
tsaya tana jira yafita yamata magana. Yana
isa gyda yatarar da rahma na kallo a falo,
zama yayi yana hushi daganan tasan lalle
ranshi abace ne. Donhaka tamike taje ta
yanko fruits. Takawo masa, kallonta yayi yaji
sanyi aransa. Yanason kanwar tashi tana
ganinshi cikin damuwa zata nemo hanyan.
Sashi dariya, dama kowacce mace hakane
anma yadda yakai kankanan bakinshi daya
tuna da yadda baiwar Allahn sadiq tamishi
saiyaji duk yakoshi, yarasa wani irin tsana
yake mata, shi a matanma tsananta
dabanne, ya tsani yaga namiji yana lallabin
mace ko rarrashinta, mikewa yayi yanufi daki
sannan. Yashiga wanka yamike yafara danne
danne awayansa kamar yadda yasaba,
Sadiq kuwa sai yayi regreting meyasa tun
farko bai saya mata wayaba, duk da yataba
so yabata taki amincewa, yau ga amfanin
wayan, gashi bai samu daman dazaice
haidar yabashi ita suyi magana ba, yasan
haidar sarai yanzu zai iya gasa masa
magana zaice akan me zaiba wa wata can
wayarsa tarike? Inkuwa baaci saa ba, zai iya
hakura dawayan akan tarike, donhaka sai
kawai yashare yafara maidakai saboda
yasamu yakammala washegari yakoma,
kodan yasan haidar bazai kara masa alfarma
ba. Washegari kuma sai baisamu yadawon
ba tunda yamma yafara kiran haidar yana
lallabi anma haidar yanuna baisan maganan
ba asalima kashe wayansa yayi abunsa,
balle yadameshi, can dai sadiq baida choice
rahma yakira yasan itakadai ce zata iya
lallabin haidar yaje. Donhaka yamata bayanin
komi daga farko har karshe ta tausaya sosai
takuma ce masa yamata kwatancen gun
anma ya gwada mata bazata saniba, ta
gwada masa ai tasan anguwan yamata
dallah dallah zataje tun kafin dare yarufa,
yace toh zai namata harta isa. Tamike tsaf
tashirya cikin abayanta, wacce musamman
daga dubai mumy tasiyo matasu, sunsha
tsada dakyau ga daukan ido, ta kira dahiru
direba takarbi mukullin matrix tashige, ahaka
suna waya da sadiq harta isa kasancewar ta
mai saurin fahimta, yace adaidai gun zaki
tsaya inkinje dare dare, zata fito, sai rahman
tace toh y not nashiga yanzu kawai? Yace ai
matsalan nikaina agun nake tsayawa bansan
gydansu yanata inabane
[5/25, 4:03 PM] Adda bena: BAR RAINA
ALLURA KARFE CE NA BENAXIR OMAR
Tace toh bakomi zankoma, zandawo
anjiman, takoma gyda har lokacin. Haidar
bayanan, tana idar da sallahn isha ta shirya
tsaf, tayiwa mumy bayani dalla dalla mumy
tace toh suje tare da ramlat , tunda tasan
haidar sarai bazuwa zaiyiba, suka shiga
motan harsunzo first gate saiga motanshi ta
danno kai, suka yi wining glass din , yace
ina zuwa? Rahma tace aika yanzu zamu
dawo, yace zuwa ina adaren nan bazaku
jiran nazo nakaiku ba?; tace saboda bazaka
yadda bane ai , aikan yah sadiq ne. Yayi gim
yace wani aika kuma? Tana fada mishi yana
hada rai. Wato sadiq saidana. Cemasa karya
fara anma yakijina ko? Kukoma gyda!,tace
haba yaya nagayawa mumy fa. Ba dadi wlh,
parking motanshi yayi yace koma baya,
takoma baya yakarbi tukin baikara kulasu ba
harya isa cikin gari

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment