Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Shima kansa Harris d'in yalura da kallon da yayan nasa kemasa, Dan haka yay k'asa da Kansa alamun jin kunya.
Inna duk tana kallonsu. Ya Umar yaje kusada inna ya durk'usa cikeda ladabi ya gaidata.
Cikin fara'a ta amsa masa da tambayar lafiyar iyali?. Ya ce, komai Alhamdulillah. Asma'u ma na gaishesu.
Muna amsawa.
Kallonsa yamaida ga Anty Saratu, ya ce, "sarkin yawo kenan, kekam kina iya sati d'aya bakizo gidannanba?..
Kanta ak'asa ta ce, " ya Umar wlhy har sati uku inayifa."
Harara ya balla mata, a'a har shekara kinayi, inna ba kwana hud'u dasuka wuce Nazo gidannan natarar da yarinyarnan ba agidannan?.
Dariya inna tayi, wlhy hakane Umar, nima yanzu babu jimawa nagama mata fad'an yawo, dan ba abune mai k'yauba.
Ya Umar yakuma harararta, mijin nakine sakarai dayake barinki, ke ko saboda yara yawon baya damunki?. To daga yau karna sake ganinki agidannan sainan da wata uku. Idan bahakaba kuma ranki zai 6aci matuk'a.
Gyad'a kai tayi dukda hukuncin NASA bawai yamata dad'i baneba, Dan Anty Saratu akwai d'ambazan yawo kamar taci k'afar kare. (Shima mijin NATA bayaso, amma saboda yana matuk'ar sonta saiyake barinta)..
Daga nan hira akad'an ta6a, wadda ya Umar bawani saka musu baki yakeyiba sosai, garama idan inna tayi magana.
Zuwa can ya ce, "inna Nazo wajenkine."
To yaron arzik'i, nima kuwa dama ina nemanka.
Saratu da Hasiya, fatee kufita. Amma Harris yatsaya.
d'agowa ya Umar yayi ya kalli Harris d'in da yay k'asa da Kansa, Dan bak'aramar kunyar ya Umar yakejiba.
Bayan fitarsu Inna ta kalli ya Umar. Umaru! Inaso kabani Aron hankalinka nan, mufara maganar da Harris yazo da ita, dukda nasan bakazomin da sakaren maganaba kaima, amma na Harris ma yanada matuk'ar muhimmanci.
To inna ina saurarenku.
Inna ta kalli Harris daya marairaice fuska tamkar zaiyi kuka. Harisu taso kazo nan.
Jiki a sanyaye Harris yataso, yazo kusada ya Umar yazauna. Inna ta nuna masa ya Umar da ido.
Zamansa ya gyara muryarsa na rawa ya ce, "yaya Dan Girman ALLAH kayi hak'uri, ka yafemin duk abinda namaka. Wlhy na tabbata duk gidammu babu mai mana Abu tsakani da ALLAH kamarkai. Abunda yafaru abayama sharrin shaid'anne. Ka gafarceni, insha ALLAH bazan sakeba. Wlhy yanzu ina tareda kai 100%.......
Ya Umar yakatseshi da fad'in wai Harris miya farune? Nifa bakamin komaiba wlhy.
A'a yaya namaka wlhy, Dan ALLAH karkace ban maka komaiba, idan kace haka zan d'auka bazaka yafeminba.
Hummm shikenan Harris nayafe maka, harma sauran, damani banrik'e kowa acikinkuba, saidai inason kuringa fahimtar miye rayuwa akowane yanayi tazo gareku.
Wlhy ya Umar nagane kam yanzu. Jiya naje wajen ya Abubakar akan yabani naira dubu goma na kar6o result d'ina. Amma shine ya hauni da masifa wai bashidashi, shima somuke mu karyashi kamar yanda muka karyaka *_KARAYAR ARZEEK'I_* tasameka. Yanzufa nauyin kayan d'akin Mufida yana kansa. Shi wlhy bazai iya da fitinarmuba mudasu mama........
Ya Umar Yakuma katseshi da Sauri, Harris ban ganeba, ansakama mufida ranar aurene? Da har aka fara maganar kayan d'akinta?.
Inna da Harris suka kalli juna cikin mamaki.... Har had'a baki sukeyi wajen fad'in kana nufin baka saniba?.
Ahankali ya Umar yakad'a kansa tamkar k'aramin yaro.
Sallallami inna tafara tana tafa hannu, oni binta wannan wace irin rayuwace haka?. su yaya Kabiru suka d'auki duniyane?.
Ammafa ranar da'aka kawo kud'in danaje ban gankaba saida na tambayi Maman taku, shine ta ce, "anfad'a maka amma kace aiki yamaka yawa Abubakar ya wakilceku tunda shine babba.
Shekaran jiya kuma daza'a saka ranama saida nayi magana, naga babukai babu iyalinka, nanma tace anfad'a maka harma kazo, anasaka rana wai katafi saboda Asma'u batajin fad'in jikinta.
Wani huci mai zafi ya Umar yashiga furzowa daga bakinsa, idanunsa sun kad'a sunyi jajur, yay ka d'a kansa yana ambatar *_" innalillahi wa'inna ilaihirraji'u."_*
Ganin haka mama takwalama Hasiya kira. Ta ce, "takawo ruwa mai sanyi.
Saida ya Umar yasha sosai sannan hawaye suka fara gangarowa akumatunsa masu zafi kuwa.
Babu Wanda yahanashi, Dan hawayen zasu saka zuciyarsa yin sanyi tarage nauyin datayi.
Harris ma hawayen yakeyi, danshima yafara fuskantar matsala irinta ya Umar awajen mama da Abba. Kullum saita masa gori baita6a yimusu komaiba itada abba.
Inna ta ce, " ya isa haka, kuyi hak'uri, kucigaba dama iyayenku addu'a kunji. Komai zaizama labari.
Ya Umar yasauke ajiyar zuciya yana fad'in babu komai mama, yawuce, amma yanzu wane wata aka saka bikin Hamidan?.
Nanda wata biyarne Umaru kaji.
Murmushi yayi ya ce, "ALLAH yakaimu inna. Kuma insha ALLAH bazan nuna musu nasan komaiba, kaima Harris karka nunama kowa ka sanarmin.
Harris ya jinjina masa kai kawai.
Daga nan mama tamusu nasiha da nuna musu muhimmancin zuminci da kula dajuna, had'inkai suzama tsintsiya mad'aurinki d'aya.
Suduka nasihar tashigesu dak'yau.
Sukaitama mama godiya.
Ya Umar kuma yafad'a musu shima alkairin daya samu ayaud'in daduk abinda yafaru. Farin ciki sosai suka shigayi, Harris harda rungume ya Umar, shima yarungume d'an uwansa suna farinciki. Bayan sun nutsu ya Umar yace to Dan ALLAH su binne maganar anan kar kowa yaji.
Inna ta ce, " hakan yayi Umaru!, koni ban goyi bayan wani yaji zancennanba. Harrisu kakula kaji.
Insha ALLAH inna babu maiji wlhy. Amma yaya tunda zaka fara aiki zandawo tsare shagon, basai Asma'u tazaunaba.
Murmushi ya Umar yayi, dama bayason zaman Asma'u ashagon Dan yanada tsananin kishi sosai. Godiya sosai da farinciki ya Umar yanuna akan abinda Harris yamasa. Daga nan hira mai dad'i suka cigaba dayi har zuwa wani lokaci sukaima inna sallama suka tafi.
Daga nan gidansu suka nufa.
Duk afalo suka iskesu har ya Abubakar da matarsa, anbaje alawa da biskit anata rabo.
Ya Umar yagaida mama cikeda fara'a, ko kad'an bai nuna musu komaiba, ya Abubakar ma suka gaisa, suma hamida da Rafi'a suka gaisheshi. Matar ya Abubakar sai wani cika da batsewa takeyi ita adole matar mai kud'i. Kota kanta baibiba yamuk'e yamusu sallama.
Kowa yayi mamakin da yau bai zauna hiraba, tunda yaga duk suna nan, (kuma kowa yasan ya Umar dason ahad'u gaba d'aya ayi hira) amma yau sai sukaga sa6anin haka. Gashi ko alawa da biskit d'in gabansu bai tambayi kona miyeba, kuma fuskarsa asake babu wani alamar 6acin rai agareshi.
Sallama yamusu yafice. Mamadai tasha jinin jikinta, hakama ya Abubakar, dama shine yazuga mama wai kar agayama ya Umar, idanma angaya masa mizai musu? Mutumin da bashida ko sisi. Kayan dake shagon nasa basu wuce na dubu 60 ba gabad'ayansu. Da ire-iren wannan musalan yabige hankalin mama da Abba, ya ce, ''kuma shine zaima Hamida kayan d'aki.
Su su Rafi'a basusan ya Umar baisaniba, amma sunsha mamaki dabasuga Asma'u ba awajen saka rana.

Daga nan gidansa yanufa hankali kwance. Yana tsaye abakin titi zai tare adaidaita sahu, harma ya tsayar dawata suna ciniki saiga wata ash d'in mota ta giftasu. Har mai motar yad'an wuce saikuma yadawo baya.
Horn yayma ya Umar, ya Umar bai d'agoba, dan kokad'an baid'auka dashima akeba.
Mai motar nan yasake yin Horn harsau uku.
Ganin haka mai adaidaita yayma ya Umar dake k'ok'arin Shiga magana. Malam dakaifa mai motarcan yake.
Dani kuma? Ya Umar yay maganar yana lek'o kansa Dan tabbatarwa.
Hannu kuwa yaga and'ago masa. Tofa bara naga wanene ina zuwa.
Babu damuwa mai adaidaita yafad'a.
Ya Umar yafito zuwa motar.
Maimota yabud'e yafito yana fad'in *_Umar bin Usman!_* dama rai kanga rai?.
Soasai ya Umar yazaro ido waje, Yazeed! Dama Kaine?.
Cikin farinciki suka rungume juna.
Yazeed ya ce, "Umar ina kashige haka? Nayi nema harna gaji. Natambaya amajillisa su alkasim sunce min suma basusan inda kakeba yanzu, wai tunda mall naka yak'one ka gujesu gaba d'aya.
Murmushi ya Umar yayi kawai, ya ce, " Yazeed wannan bamaganar titi bace, kabari next time Idan mun had'u zamuyita. Amma yaushe kadawo k'asarnan?.
Wlhy tun sati biyu daya wucefa. Tunda nadawo kaina fara nema awashe gari, naje gidanka akace aii katashi, natambayi abokai sukace basu saniba. Naje gidansu Lubna natarar suna biki. Cikin ikon ALLAH yanzu har zan wuce saina hangoka.
ALLAH Sarki Yazeed, yanzu dai ina zamu had'u mai Babur yana jirana.
Wai inama motarka naganka zaka hau adaidaita?.
Murmushi kawai ya Umar yayi ya ce, "Yazeed kaidai babu abin fad'a abakina sai Alhamdulillah.
Yazeed ya jinjina kai, shikenan sallami mai adaidaitar kazo muwuce.
A'a kaje uzurinka, baikamata na katse makaba.
No. Babu Inda zanje wlhy, nakai Zuhrah gidane suna wani taro a family d'insu.
Yazeed yaje dakansa yabama mai adaidaita d'ari biyar sannan ya sallamesa.
Mai adaidaita sai zabga godiya yakeyi yatafi.
Ya Umar kam yashiga motar Yazeed suka tafi suma..............









*_(((S)))........2017_*
*_Luv you all_*
[12/15/2017, 7:37 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻.........



💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_*

_sak'onki ya iso gareni *Ummu sadeeq* alkairin ALLAH yakai gareki aduk inda kike._
Luv you zam zam😻 .
*_page→43-44_*


*........Wanene yazeed?.*
Yazeed Mudansir kura. shine cikakken sunansa. d'ane ga Alhaji mudansir kura shahararren d'an siyasa kuma d'an kasuwa. Mutumne shi mai gaskya da tsayawa agidansa, wannan shine yabama 'ya'yansa damar tsayawa sukayi karatu, dakuma samun ingattacciyar tarbiyya.
Yazeed sun had'une da ya Umar awajen bautar k'asa. Sosai suka shak'u awannan lokacin, dan abotace maicikeda k'auna da gskya acikinta. Bayan kammalawarsu kowa yakoma gida. Akuma wannan lokacinne rashin lafiya takama Alhaji mudansir, aka kaishi k'asar London domin yin jiyya. Yazeed ne yake zaune awajensa.
Tundaga lokacinnan ya Umar yadaina samunsa awaya. Har ALLAH ya azurtashi alokacin. Kusan shekara biyu basu sake had'uwaba har akayi bikinsa da Lubna sannan su Yazeed suka dawo. Dawowarsu babu dad'ewa mahaifinnasu yarasu Alhaji Mudansir kura. Tunda ya Umar yaji Rasuwa hankalinsa yatashi, dayake lokacin Yakama k'asa yanada kud'i babu laifi shine yaja abokansa su Dr jafar, Alkasim etc....... Dadai sauransu sukaje gaisuwa.
Murna sosai yazeed yayi daganinsu, yabama Ya Umar hak'urin rashin nemansa, sannan suna arikice ko wayar da Number sa ke aciki bai d'aukaba.
Ya Umar ya ce, "babu komai yamasa uzuri.
Tundaga nan yazeed yazama d'an cikinsu shima, idan yanada lokaci haka zai shiryo yazo majalissar matasan masu kud'in asha hira. Daga nan aka saba sosai.
Gafda za'ayi aurensa da Asma'u yazeed yatafi k'asar Indonesia wani course, wanan yasa basu sake had'uwa da ya Umar sai yau..

Wannan kenan



*mundawo labari.*
Suna tafiya ya Umar yana bama Yazeed labarin abubuwan dasuka faru abaya.
Idon Yazeed yayi jajur saboda azabar 6acin rai, yanason ya Umar sosai.
Muryarsa cikeda damuwa ya ce, " amma miyasa bana samun no d'inka kusan shekara d'aya kenan?.
Hum kabari kawai yazeed, wlhy cire sim cart d'in nayi gabad'ayama na ajiye, nabar na family na kawai, amma na kasuwa bana buk'atar kowa taredani, saboda abubuwan da mutane suka aikatamin.
Hakane Umar, d'an Adam sai abarsa da halinsa, kaga yanzu yakamata kagane bakowane ke k'aunarka Dan ALLAH ba saidan kud'inka. Wlhy Umar haka rayuwar take tafiya ga kowa, idan kanadashi saikaga anata sonka, amma dasun k'are sai kowa yafara gudunka. Dan Adam kenan mai manta alkairi. Amma gsky Lubna da family d'inta da Dr Jafar sunfi kowa bani mamaki. Babu komai kayi hak'uri Umar, ALLAH yanason mutane masu hak'uri.
Wlhy komai ya wuce yazeed. Yanzu kam bana tareda kowacce irin damuwa.
Dariya sosai yazeed yayi, ainasan bazaka damuba tunda kana tareda amarya kanashan amarci.
Harararsa ya Umar yayi, yana fad'in aikai dama matsalarka kenan bakada kirki kokad'an. Duk hanyar tsokanar magana kasani.
Hhhhhhhh abokina aikaine kanada abubuwan mamaki Dana dariya. Ankawo maka yarinya kanata wani mata mazurai. Kuma babu kunya saika lalla6a daga baya hhhhhhhh.
Kai waya gaya maka na lalla6a? Masheranci.
Hhh nasanka Umar wlhy sosai. Inaga daga Family d'inka babu Wanda yaymaka irin sanin dana maka.
Kaji dashidai masheranci. Saika tsaya munzo gidan.
Yazeed yataka burki amatsakaicin k'ofar gidan na ya Umar, jiyayi tausayin ya Umar yakuma shigarsa. Dabadan karyayi kuka akirashi maceba da wlhy saiyayima ya Umar.
Lokacin anak'ok'arin shiga sallar La'asar. Ya Umar ya ce, "sufara yin sallah sannan.

Suna idar da sallah cikin gidan suka nufa. tun atsakar gida wani farinciki yaratsa zuciyar ya Umar. Dama Yasan Asma'u tuni mai tsaftace. Shiyyasa baita6a fargabar zuwa dawani gidansaba akowane yanayi.
Tunda suka shigo yazeed ketabin ko'ina nagidan da kallo. Tabbas rayuwa nada abin tsoro. Idan yatuna yanda Umar yasamu kud'i abaya, ko'a mafarki wani baxaiyi tunanin ganinsa a irin wannan gidanba. Amma abin birgewa kokad'an babu wata k'asurgumar damuwa tartare da Umar d'in. Tab aii da wanine dayanzu yabi daji ciwon hauka yakamashi. Kai gsky Umar jarumin namijine abin kwatance awannan zamanin.
Ya Umar yakamo hannun Yazeed Dan ganin yana tafiya ahankali. Ajiyar zuciya yazeed yayi tareda dawowa cikin hankalinsa. Ya Umar baice dashi komaiba sukai sallama ak'ofar falon.
Asma'u ta amsa cikin nutsuwa. Jin kamar muryar ya Umar yasakata fitowa daga bedroom. Adaidai nan kuma su ya Umar suka shigo falon. Komawa tayi ciki da saurinta Dan d'aukar hijjab.
Carpet d'in dake falon ya Umar ya nunama yazeed. Saida yaga ya zauna sannan yabi Asma'u.
Abakin k'ofa sukayi karo tasako hijjab. rungumeta yayi, daddad'an k'amshinta na kuma sakashi a shauk'in k'aunarta.
Kanta ak'asa ta ce, ''sannu dazuwa."
Yauwa Sarauniyata, ykk? Ya jikin?.
Lfy lau, kuma ni lfyta k'alaufa. Murmushi yayi yana kallon yanda take cuno baki. Ya sunkuyo kad'an yabata kisses guda uku, abakinta da goshinta. Kunyace takuma kama Asma'u, Dan haka tayi k'ok'arin kwace kanta ta gudu amma saiya ruk'ota da k'yau.
Humm guduwa kikeson yine? To aiia tare Muke da babban bak'o.
Da sauri tad'ago ta kallesa, yaya bak'ofa?.
Kansa yad'aga mata, har yanzu idonsa akanta.
To amma miyasa Baka kirani kafad'aminba? Da saina masa binci na Musamman, tunda kace abban bak'one.
Hakane my Asmy yazeed babban bak'one agaremu. Amma kiyi hak'uri Nima a ahanya na tsintoshi.
Ayya to babu damuwa. Amma yanacin garau-garau?.
Gira yad'aga mata, tareda k'ara rungumeta ajikinsa ya ce, "aibakinkine garau-garau d'in. mizai hana yaci sarauniyata."
Dad'ine yake ratsa zuciyar Asma'u aduk lokacin dataji ya Umar yasauya mata wani suna daban, musamman sarauniyata dayake cemata.
Jin tayi luf ajikinsa yasakashi d'agota. Yadai Husanata? Ko kina buk'atar d'umin mijinkine?.
Da Sauri ta d'an tureshi tafice daga d'akin.
Shima bayanta yabi yana dariya k'asa-k'asa.
Afalo ya isketa suna gaisawa da yazeed. Sosai yazeed yaba da tarbiyyar Asma'u.
Ya Umar na fitowa Asma'u tana mik'ewa tafita. Akusadashi ya Umar ya zauna. Yazeed ya kalleshi daikuma ya bushe da dariya.
Harararsa ya Umar yayi. Mikuma yabaka dariya kaikuma?.
Yazeed bai iya maganaba sai dariya, daya kalli ya Umar saiya sake tuntsurewa da dariya. Ganin haka ya Umar Yakuma harararsa. Kai malam yafa isheka, wai miye matsalarkane?.
Cikin dariya yazeed yakunna waya yayma ya Umar hoto.
Da Sauri ya Umar ya warce wayar danson ganin miya faru?.
Idanu yazaro waje, shima saiya fara dariyar. Bakinsa yagani duk jambaki. Da Alama kiss d'in dayayma Asma'u ne yakwaso jambakin.
Sunacikin dariya Asma'u tashigo. Itama suna had'a ido da ya Umar tayi murmushi ta ajiye tiren hannunta. Tun d'azun tana ganin jambakin amma tak'i Sanar masa.
Saving d'insu tayi. Had'd'd'iyar jallop d'in shinkaface wadda taji kayan lambu, dukda babu nama aciki bare kifi sai zabga k'amshi takeyi. Tunkan sufaraci yawunsu ya tsinke suduka. Ta tsiyaya zo6onta dayaji kayan k'amshi a kofuna guda biyu sannan tamik'e. Bismillanku, tafad'a tana mik'ewa.
Tunda suka faracin abinci babu mai iya yima d'an uwansa magana. Ta kurma kawai akeyi, babu Baka sai kunne. Sosai sukaci abincinnan, Dan abincin yayima yazeed dad'i. Shi matsalar dayake fuskanta kenan agidansa, matarsa bata iya girkiba. Ko indome tadafa masa saidai yaci kawai da hak'uri. Amma badan dad'iba kam.
Bayan sunci sunyi dam, suka kora da sassanyan zo6on. Ayanzu kam yazeed yakasa daurewa saida yayi magana.
Kai abokina kana kwasar gara wlhy. Yoni Ina samun haka mizai dameni.

Kallonsa ya Umar yayi yana murmushi jin dad'in an yabama Asma'unsa. Haba abokina Kanada matafa? Yakake fad'ar irin wannan maganar.
Hummm abokina kenan aii kasan ko'a Matan wata tafi wata.
Hakane. ALLAH yasa mudace.
Ameen yazeed yafad'a yana k'ara tsiyaya zo6on akofi.

Bayan sun kammala Asma'u tafito ta kwashe komai. Jok d'in zo6on kawai tabar musu. Daga nan suka cigaba da hira har zuwa magriba.
Sun tattauna abubuwa da dama, ciki harda kud'i da yazeed yabama ya Umar har na 10millions yayi gyaran shagonsa.
A take anan kuma yay masa transfer a Account d'insa.
Yanda kasan gumaka haka ya Umar da Asma'u suka koma awajen. Ya Umar yarungume yazeed yana masa godiya.
A'a Umar babu godiya a tsakaninmu, kayana nakane. Hakama kayanka nawane. ALLAH ne yahad'amu, to dan haka saimu gode masa.
Hakane abokina amma kaid'in nadabanne acikin al'umma. ALLAH ya saukar da farinciki da alkairi arayuwarka da zuriyarka. Yanda ka k'yautata mana kaima ALLAH ya k'autata maka damafiyin haka.
Ameen Umar ngd sosai da addu'arka.
Yanzu abinda yakamata gobe idan ALLAH yakaimu kashirya zamuje wani waje akan kayanka da custom suka rik'e.
Ajiyar zuciya ya Umar ya sauke. Yazeed wlhy dama mun hak'ura kawai. Duk hanyar danake tunanin kayannan zasu fita nabi, amma kowa saiyace babu yanda zaiyi.
Murmushi yazeed yayi, yadafa kafad'ar ya Umar, karka damu Umar, awannan karon insha ALLAH zasu fito. Aii komai na k'asarmu hanyace. Kaidai karka fidda rai da rahamar ALLAH.
Shikenan yazeed ALLAH yakaimu goben. Ngd ngd ngd.........
Katseshi yazeed yayi da sauri..... Nifa banason godiyarnan. Idan kanayi sainaga tamkar baka d'aukeni d'an uwaba.
Tom kayi hak'uri na daina.
Daganan yazeed yamik'e, rafar 'yan d'ari biyar yabama Asma'u wai tukuycin ciyar dashi daddad'an girki datayi.
Girgiza kanta tayi, idanunta ak'asa, a'a ya yazeed ngd basai kabani tukuyciba. Banmmasan zakuzo tareba da anmaka na musamman aii.
Kai aii wlhy wanna danacima na musamman ne. Ke dai kawai ALLAH yak'ara dank'on k'auna keda abokina. Ngd sosai..
Asaman kafet d'in ya ajiye suka fita..
Godiya sosai tamasa, da sak'on gaisuwa ga iyalinsa sannan takoma ciki, tana mamakin yazeed. Dama akwai irin wad'annan mutanen har yanzu adoron k'asa?.

A can kuwa ya Umar yarakashi har mota yana k'ara masa godiya da k'yak'yk'yawar addu'a shida zuriyar sa. Saida yaga yabar Layin sannan yashigo cikin gida.







*_(((S))........2017_*
*_Luv you all_*
[12/18/2017, 4:29 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻.........



💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_*

_gaisuwar da shafin duk nakine dear Zarah Bukar. barkakanki da dawo online, Alkairin ALLAH ya iso gareki aduk inda kike._
Luv you sosai-sosai😻

*_page→45-46_*


............A falo ya iske Asma'u tsaye tanata k'ara mamakin halin kirki irinna Yazeed.
Sallamar dayayi ta amsa. Yad'ora dafad'in Husna uana ganki atsaye, lafiya kuwa?.
Lafiya lau yaya, kawai ina mamakin halin kirki da dattako irin na ya yazeed ne. dama har yanzu duniya tanada mutane irinsu acikinta?. Yaya 10millions fa 1 time, batareda tunanin komaiba.
Murmushi ya Umar yayi, my Husna hakane, yazeed ya cancanci yabo ainun, tunda k'addarar nan ta sameni babu Wanda yata6a taimakamin dako sisi dagake sai innata, saiko Anty sa'a. Abokaina, wasu daga cikin 'yan uwana duksun gujeni saboda banidashi yanzu. Atunaninsu zan zame musu nauyi, naringa binsu inacewa subani. Humm lallai naga rayuwa, ALLAH ya shirya zukatanmu.
Shikam yazeed aibammasan mizance akansaba, saidai kawai naita masa k'yak'yk'awar addu'a shida zuri'arsa daganan har k'arshen numfashina.
Gsky ne yayana, Nima zan tayaka insha ALLAHU.
ammafa gsky su ya Yazeed sunada kud'i.
Sunada kud'i sosai Husna, mahaifinsu yatara musu, kuma yakoyama kowa yanda zai nemi nasa, kina ganin yazeed nan bak'aramin d'an kasuwa baneba.
To ALLAH yasakanya masa da mafiyin abinda yabamu. ga wad'annan suma.
Ameen ya rabbi husna, amma wad'annan nakine, kije ki ajiye abinki. Nida akabama 10millions niyakamata nak'ara mini aii ko?.
A'a yaya, Dan ALLAH karik'e, ni babu abinda zanyi dasu, aii komai nawa nakane.
Murmushi yayi yana d'aga mata gira, hakane kuma sarauniyata. To yanzu ki ajiyemin su zan kar6a kinji.
Kanta ta jinjina a sanyaye.
Ya Umar yakamo hannunta yana fad'in yauwa wana kama?. d'azu wakikema dariya?.
Dariyarce takuma zuwama Asma'u alokacin da tatuno jambaki a la66an ya Umar. Takuma shek'ewa da dariya harda rik'e ciki.
Ya Umar tsayawa yayi kawai yana kallonta. Saida tayi mai isarta

Please Login or Register in order to submit comment