Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwana biyu.

_Humm kai jama'a wanan wace irin uwace? kamata yayi tayi bak'inciki dayima ya Umar fad'a akan miyasa ya sayar, amma kuduba murna takeyi akan zasu sami kud'i, bata kallon halin dayake ciki da Wanda zaishiga nan gaba, a'a ita burinta kud'i, gashi tanata bin matakan dazata raba zumincin 'ya'yanta, yau ta nuna tafison wanan, gobe kuma tafison wancan, kaiconmu da masu hali irinna mama, wlhy iyaye kugyara, shikenan da 'ya'yanka sunfara girma saika d'auki duk nauyinka ka maida akansu, wlhy hakan yana kawo raini tsakanin 'ya'ya da iyaye. Indai d'a yakasance nakwarai kuma d'an halak bazai manta da halaccin iyayeba, bazai manta da gwagwarmaya irinna iyayeba musamnamma uwa, kahanata barci tun kana acikinta, kahanata cin abinda take so tun kana acikinta, kahanata sukuni tun kana acikinta, ta haifeka cikin magagin wahala, ta raineka, idan bakada lafiya kana kuka tanayi, idan kaji yunwa tabaka kaci koda ita bataciba, tagoyaka, ta wanke kashinka, idan anta6aka ranta ya6aci, konawa tasamu zata kashesu akanka dankayi farinciki, katuna gwagwarmayar da mahaifinka yakeyi wajen nema muku abinda zakuci da kud'in makarantarku Dana asibiti._
_Amma dan rashin tunani harka iya kasa k'yautata musu sai sun rok'eka, kai wlhy kaicon wad'annan 'ya'ya. Iyaye mugyara, 'ya'ya mugyara Dan ALLAH._

Koda ya Umar yafita saiya samu adaidaita yashiga zuwa gida. Zuciyarsa namasa ciwo da tunanin hali irin na mahaifiyarsu, amma kokad'an abinda take masa bai gutsiri ko kwayar zarrah daga k'aunar dayake mataba irinta d'a da uwa, yanason mahaifiyarsu, akullum kuma yana mata addu'ar neman shiriya wajen ubangiji.
Har suka iso baimasan sunzoba, saida mai Babur yata6ashi sannan yakawo nimfashi, kud'insa yabasa yay masa gidiya.
Shago yafara Shiga suka gaisa dasu Harris sannan yak'arasa cikin gida.
Idonsa nakan Asma'u dake a kwance a tsakar gida bisa tabarma, agogon hannunsa ya kalla 5:13pm. Ya girgiza kansa, afili ya ce, "yarinyarnan bazaki daina wanan barcin la'asar d'inba dakika koya ko?. Narasa mike damunkine haka?.
Yana maganar yana tafiyane gareta, harya k'araso yazauna Kusada ita. takalmin k'afarsa yafara k'ok'arin cirewa yana fad'in Husna! Ke Husna! Tashi mana.
Asma'u batada nauyin barci sosai tabud'e ido ahankali, ganin ya Umar zaune Kusada ita yasata yunk'urawa ta tashi da k'yar. yad'an juyo ya kalleta ya kakka6e safar daya cire. Waini barcinnan dad'i yakemikine dakika kasa dainawa? Magana tanawa nayi miki akan barcin la'asar?.
Hamma Asma'u tayi tanad'anyin mik'a, kayi hak'uri Yaya wlhy nima bansan sanda barcin ya sacenibamafa, zaune nake ina kallo awaya.
Takalmansa yagyarama zama, yad'ora safar akansu sannan yamatsa baya sosai ya zauna tareda jingina da bango.
Jawo Asma'u yayi kusadashi. Husna kodai akwai abinda ke damunki? Wanana barcin naki yafara yawa, yanzufa mawuyacine nashigo gida ban tarar dake kina barciba. Kalli yanda tsakar gidanan yay datti amma kinkasa sharewa, kuma aii da bahaka kikeyiba, kalli wancan wanke-wanken tunda zan fita naganshi acan gurin, haba Husna sokike kikoyi k'azantane?.
Kanta ak'asa ta ce, "a'a!."
Tomike damunkine?.
Wlhy Yaya nima ban saniba, haka kawai barci baya isata yanzu, koda zanyini inayinsa.
Shiru yayi yana kallonta, itama shitake kallo, ajiyar zuciya yasauke yana fad'in to ALLAH ya k'yauta. nibara narage kayan jikina.
To tafad'a tana binsa da kallo.
Silifas d'inta yasaka, yad'auki takalmansa yanufi cikin falon.
Yana shigewa Asma'u takoma ta kwanta abinta.
Bayan kamar minti 16 ya Umar yafito, kallon Asma'u kawai yayi ya girgiza kai. Shibaima San yazai mataba wlhy, amma zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu dolene yakaita wajen Dr Al-ameen, k'ilama shawarace ke damunta, dama gata makwad'aiciya.
Tsintsiya ya d'auka yafara k'ok'arin share tsakar gidan. Tas kuwa yashareshi, dama bashida wani girma, yajawo ruwa a rijiyar dake gidan ya ciccika bambun waje dana toilet d'insu duka sannan yafara wanke-wanken.
Duk abinda yadace saida yagyarashi sanan. Aikodai yaji jiki, jiyakema bayansa ya rik'e. Mik'a yayi yana mammotsa ga6o6insa. Kai mata mafa suna aiki, kana ganin aikin cikin gida kamar k'aramin Abu ammafa ba k'arami baneba, wlhy bayana harya k'age, aidole nayi wanka da ruwa mai zafi.
Shikad'ai yaketa surutanta yayinda yake kwashe kayan wanke-wanken yana kaiwa kichin.
Yana gamawa ana kiran sallar magriba, alwala yayi kawai. matsowa yayi Kusada Asma'u yana tada'ita, k kasa sarkin barci tashi lokacin sallah yayi.
Da k'yar ta iya tashi, Dan jin jikinta take dukyayi nauyi, saidama ya taimaka mata sanan tamik'e tsaye. Zaki iya kona rakaki kiyi alwalar?.
Asma'u daketa faman lumshe ido ta ce, "a'a zan iya."
To ni saina dawo.
Bai wani tsaya jirantaba yafice masallaci.
Itakam sororo tatsaya tanabin ko'ina nagidan da kallo, abin mamaki wai yau ya Umar dakansa yay aikin gidan? K'arasawa tayi wajen banbunan ruwa, ko ina cike yake da ruwa, talek'a kichin nanma tsaf, dukda dai yasaka kayan wanke-wanken duk ba daidaiba. Murmushi tayi ta ce, "ina sonka dayawa yayana, ALLAH yabarmu tare.
Itama sallar taje tayi.
Tana idarwa tafito da zummar nema musu abinda zasuci, leda ta hanga saman tabarmar data kwanta, tak'arasa tad'auki ledar tabud'e, tofa wayabama Yaya dambun nama haka?.
Mamace tace nakawo miki.
Da sauri tad'ago danbataji shigowarsaba. Tayi murmushi kai amma nagode, tana nan lafiya itada Abba dasu Rafi'a?.
Lafiyarsu k'alau, bamma tadda kowaba agidan, Abba yana wajen aiki, su mufida kuma suna islamiyya.
Ayya.
Robar tamaida ta k'ulle tana fad'in bara nashiga kichin yaya..
Kichin kuma? Mizakiyi akichin?.
Yaya abinci mana, da ranafa banyi komaiba Dan naga bakanan.
La'ila misu Harris sukaci to?.
Anty Saddiqa takawo musu abinci.
To kekumafa?.
Ni kawai nasha garin kwaki.
Garin kwaki kuma?.
Eh wlhy Yaya shinake sha'awar sha.
K'arasowa yayi daf da ita, Yakama hannunta suka zauna atabarmar, sai binjikinta yakeyi da kallo kamar mai Neman wani abun. Husna anya kuwa kinada lfy?.
Yaya lafiyata k'alau wlhy.
Kin tabbata babu abinda yake damunkine?.
Kanta tad'aga masa alamar eh.
Shiru yayi yana nazarinta, zuwa can ya ce, "kinga shirya muje wajen Dr Al-ameen.
Asma'u tazaro ido waje, Yaya wlhy lafiyata k'alau, kuma awanan daren zamuje wajen Dr Al-ameen? Aii yanzuma yatashi aiki.
Shiru yayi yana nazarin maganarta, zuwa can kuma ya sauke ajiyar zuciya to ALLAH yakaimu safiya.
To Ameen, saidaifa nidai lafiyata k'alau.
Inafa kikaga lafiya my Husna? Wai kinga yanda kike ramewa kuwa?.
Hannu tasaka tana shafa wuyanta, azuciyarta ta ce, "rama kam aii fitinarkace takawota, amma afili saitace yanayine kawai Yaya.
Baice komaiba, yadai jawota jikinsa ya matse.


*_washe gari_*
Tunda wuri ya Umar yasaka Asma'u tashirya badan tasoba, shima shirinsa yayi cikin d'anyar shadda green mai duhu, yayi k'yau ainun.
Yafito sai zabga k'amshi yakeyi, itama haka Asma'u tana k'amshi mai sanyi bawai irin nasaba.
Kai my Husna ALLAH kuwa jikina ciwo yakemin har yanzun.
Dariya Asma'u tayi, kai Yaya dagayin d'an aiki duk ka cikamu da raki tun jiya. Sharafa da wanke-wankene sai d'ibar ruwa, amma jiya saida namaka tausa, kayi wanka da ruwa mai zafi kuma.
Kibari kawai har yanzu ban dawo garauba gsky, inagama sai Dr Al-ameen yabani maganin ciwon jiki.
Dariya sosai Asma'u take masa.
Shikuma yatsuke fuska wai yaji haushi.................πŸ˜„







*_(((S)))........2017_*.
*_I love you all_*
[12/22/2017, 9:00 PM] ~πŸ‡© ' πŸ‡― πŸ‡¦ πŸ‡· πŸ‡­βœ: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’».........



πŸ’Ž *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* πŸ’Ž


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAIπŸ‘ŒπŸΌ WRITER ASSO.....😜_*


_ina kike my k'anwa Marak'isiyya?, wanan shafin nakine, gaisuwa agareki da fatan alkairi, ALLAH ya tabbatar da farinciki agareki my sweet lil d'inaπŸ’‹_*
*_page→53-54_*


..........Lokaci k'an k'ani suka isa Asibitin, ko kad'an ya Umar baya buk'atar had'uwa da Dr Jafar, Dan haka yasa sukabi tabaya shida Asma'u.
Saidai kumar abin fad'a suna karya kwana saiga Dr jafar shida wasu Norses.
Ya Umar Harya d'auke kansa saikuma yaga rashin dacewar hakan, gyara tafiyarsa yayi yadawo kan hanya sosai, sa6anin da daya koma gefe.
Shima kansa Dr jafar baiyi niyyar gaisawa da ya Umar ba, amma ganin ya Umar yanufoshi ga wani kwarjini daya masa saiya dake shima.
Sallama ya Umar yamasa, da k'yar Dr jafar ya amsa, ya Umar yayi murmushi yana mik'a masa hannu, haj Jafar talaka baya ganinku?.
Wata dariyar k'eta Dr jafar yayi tareda fad'in mu mun Isa? Aikune manya-manya maganin k'ana-k'ana.
Dariya sosai ya Umar yayi wadda har zuciyarsa yayita, yazame hannunsa daga na Dr jafar yana fad'in to mungode, ya aikin?.
Alhmdllh Dr jafar yafad'a cikin 'yar kunya.
Asma'u kam tana gefe ko kallo baima ishetaba, Dan yana jerin manyan wad'anda tatsana wlhy. Koda yad'ago suka had'a ido, yawashe baki zai gaisheta saita daka masa wata uwar harara.
Ruf yarufe bakinsa yakasa magana.
Abin nasu yaso bama ya Umar dariya, amma saiya gimtse yayima Dr jafar sallama yabi bayan Asma'u dahar takusa shan kwana.
Harara Dr jafar yaraka bayan ya Umar da ita.


Nikam bilynku na ce, "ohodai ihu bayan hari kenan."πŸ€·πŸ½β€β™€πŸ˜œ


Da k'yar ya Umar yacimma Asma'u suka k'arasa office d'in Dr Al'ameen batareda suma juna maganaba.
Cikeda fara'a Dr Al-ameen yakar6esu Dan dama yasan da zuwansu, cikin barkwanci aka gaisa sannan yafara tambayar waye bashida lafiyane?.
Ya Umar yanuna Asma'u, wlhy doctor my wify ce babu lafiya, kullum sai yawan barci datakeyi, so gashi sai ramewa takeyi babu gaira babu sabar.
Dr Al-ameen ya maida kallonsa kan Asma'u yana fad'in madam abinda oga yafad'a gskyane?.
Fuska tad'an marairaice, Dr nifa nagaya masa k'alau nake amma yak'i yarda, babu inda yakemin ciwo saidai yawan barcin kawai.
Murmushi Dr Al-ameen yayi batareda ya ce, ''komaiba.
Rubutu yayi atakarda kafin yad'ago yana mata 'yan tambayoyi.
Duk tana basa amsa yanda yakamata. Bayan yagama tambayarta ya ce, "ga bayinan tashiga tayo masa fitsari a wata 'yar kwalba daya mik'a mata.
Kar6a yayi jiki a sanyaye Dan itama tafara zargin Kodai batada lafyarne da gsk?.
Mintuna kad'an tadawo, Dr Al-ameen ya kar6a sanan yay kiran Norse Hafsat. Saida ta gaisheahi sanan yamik'a mata kwalbar, sister plz ina buk'atar result dangane da fitsarinan yanzu.
Rissinawa tayi takar6a tana fad'in okey sir.
Sunanan zaune a office d'in, marasa lafiya suka cigaba da shigowa Dr Al'Ameen yana dubasu.
Bayan kamar minti talatin saiga sister Hafsat da takarda ahannunta.
Rissinawa tayi tabama Dr Al-ameen sanan tafice.
Kallon farko da Dr Al-ameen yayma takardar fuskarsa ta Nuna alamar farinci. Yad'ago yana kallon ya Umar da Asma'u.
Alhaji Umar congratulations, madam tana d'aukeda babbar k'yautane.
Doctor kana nufin matata tanada ciki kenan?.
Hakane Alhaji Umar, ALLAH ya inganta.
Ya Umar yad'aga hannu sama yana muk'a godiyarsa ga ubangijin talikai. Asma'u kam mamakine yakamata, dama haka akeyin cikin salin alin? Itafa wlhy ko ciwonkai bataji, babu wani wuri dake mata ciwo, saidai kawai kasala da barcin datakeyi yanzu babuji babu gaini........
Ya Umarne ya rungumeta yana fad'in Alhamdllh, wanan yasaka Asma'u dawowa hayyacinta.
Har k'yautar agogo mai masifar k'yau na azurfa ya Umar yayma Doctor, agogo ahannunsa yake amma yacire yabashi.
Ya Umar ya ce, "amma Doctor kofa laulayinnan namasu ciki batayi, saidai barcin kawai, da rama?."
'Yar dariya Dr Al-ameen yayi, karka damu wanan bawata matsala bane, kowacce mace akwai salon cikinta. Wasu zakaga sun farane da amai, wasu kwad'ayi, wasu ciwon ciki, wasu zazza6i, wasu basason abinci, yanayin kala-kala yake zomisu, wasukuwa kamar na madam d'inkane babu ciwo komai, watama saitaje watan haihuwa ko irin ciki yakai wata biyar d'inan sanan take fara laulayi.
Jin jina kai ya Umar yayi Alamar gamsuwa, magunguna yarubuta musu da Asma'un yakamata tad'an fara amfani dasu Dan inganta lafiyarta da jaririn cikinta.
sukai masa godiya sanan suka tafi. Daka kalli fuskar ya Umar Kasan yanacikin farinciki, yanason yara amma aka rabashi da nasa, ALLAH gafurun rahimun gashinan ya azurtashi da samun wani.
Itadai Asma'u tayi shiru, dukda tana cikin matuk'ar farinciki itama zata zama uwa, amma tana fargabar ranar haihuwa Dan ance akwai wahala....
Ganin sun tsaya k'ofar gidansu tad'ago da sauri tana kallon ya Umar. gira yad'aga mata yana biyan mai adaidaita kud'insa.
Hannunta yakama suka nufi cikin gidan, itama fuskarta d'aukeda farincikin ganin innarta da abbanta.
Kwace hannunta tayi zata shek'a da gudu, da Sauri ya Umar yarik'eta, k" tsaya karkimin ganganci mana, tsayawa tayi saboda rik'e hannunta dayayi, ya harareta kinmanta da abinda ke jikinkine?.
Bakinta tad'an turo gaba amma batace komaiba. Jan hannunta yayi suka k'ara cikin gidan.
Afalo suka tadda fatee da Hasiya suna yankan d'inki, sunajin sallamar Su Asma'u suka tashi suna ihun murna, rungume juna sukayi, ya Umar yazauna yana murmushi.
Ihunsune yafito da inna daga d'akinta, tana fad'i kai lafiyarku kuwa kuke mana ihu haka?.
Asma'u tana ganin inna tasaki su fatee tanufi inna ta rungume.
Wai! Asma'u zaki karyani aii.
A'a innata, INA murnar ganinkine.
Itama saita rungumeta tana fad'in sannunku da zuwa to.
Ya Umar ya ce, "inna barka da fitowa."
Barka kadai Umaru, wannan rigimammar tahanani zama.
Dariya yayi shima, inna ai tana murnar ganinkune, kwana nawa bata gankuba?.
Da sauri Asma'u ta ce, "wata bakwai kenan rabona da gidannan, tundafa nayi aure saud'aya nata6a zuwa saikuma yau." β€˜tak'are maganar tamkar zatayi kuka.’
Hasiya da fatee kam dariya suke mata, inna ma saida ta dara, ta ce, "umaru kana fama wlhy."
Murmushi yayi, yana sunkiyar dakai k'asa.
Asma'u da fatee da Asiya kam tuni sun shige d'aki, kira inna ta kwalama fatee tafito, inna gani.
O yau Dan kunga Asma'u shine ko ruwama bazaku kawoma yayankuba.
La'ila wlhy inna na mantane, da sauri tafita saigata da ruwa harma da zo6o da abinci.
Ya Umar yafad'ama inna abin farincikin daya samesu. Yana maganarne kansa ak'asa.
Dariya inna tayi Dan ganin yanda ya Umar yamaida ita surukarsa yau. To Umaru ALLAH ya inganta.
Ameen yafad'a a la66ansa.
Hirarsu suka cigaba dayi shida inna, dukda dai yaud'in akwai 'Yar kunya tsakani.
Itama Asma'u tanacan itada k'annenta.
Sunkai wajen awa hud'u agidan sanan suka tafi, Asma'u nata zum6ura baki ita bayanzu zata tafiba.
Ya Umar bai kulataba suka tafi, daga nan sai gidan mama.
Tarba sosai mama tamusu wadda tayi matuk'ar bama ya Umar mamaki, amma saiya danne mamakinsa yasaki jiki da ita sosai kodan Asma'u.
Itama yafad'a mata Asma'u nada ciki. Rungumeta mama tayi tana saka mata albarka, duk mugun halin mama nason kud'i tana k'yaunar jikokinta, sosai ta nuna farincikinta, suma Rafi'a da Mufida sunyi matuk'ar farincikin ganinta, nanko sukaita shan hirarsu.
Anan Umar yabarta sai bayan isha'i yadawo suka koma gida.



____________________
Bayan wasu satittika.
Abubuwa nata tafiya yanda yakamata, Asma'u tanata rainon cikin dabatajin kamar akwaishi, har yanzu tana nan da barcin tsiyarta. Ya Umar ma yana bata kulawa ta musamman, jiyake da ita aynun, komai takeso shine daidai.
Ana haka matar Muktar ta haihu, sosai akasha hidima, ya Umar yataka rawar gani, hakama su Asma'u sune amarori.
Taro yatashi lafiya, Asma'u tacigaba da rainon cikinta.
Wata ranar laraba da safe Anty Sa'a tazo dakanta takawoma Asma'u alk'awarinta.
Bayani tamata sosai yanda zata fahimta, amma ta ce, "kada tasha sai nan gaba cikinta yayi kwari.
Godiya sosai Asma'u tamata.
Anan takusan yini, sai gabda azuhur tatafi gida.

Angama komai danganeda mall d'in ya Umar, kuma kayan dasukayi oda sun iso, komai anzuba awajen, yakoma tamkar yanda yake ada, dukda dai kayan basu cikaba tamkar da d'in.
Amma kokad'an ya Umar baya zuwa wajen da rana ballema wani yagansa, muktar da Harris da Sadam ne ke kula da wajen, shikuma Yakoma zaman shago kamar da.
Harris ma bai fad'ama kowa ya Umar ya bud'e mall nasaba, yadai Sanar da iyayen nasa yasamu aiki a tsohon gurin ya Umar, wad'anda suka sayi wajenne suka d'aukeshi aiki.
Bikin Mufida nata matsowa, kullum mama tana zuba idanu taga ya Umar yakawo mata kud'i, amma saitaji shiru wai malam yaci shirwa.
Tunda tana kawaicin jira har ranar ta tambayesa maganar kud'in.
Murmushi yayi kamar yanda yasaba, muryarsa a tausashe ya ce, "mama har yanzu basu baniba, amma kitayani da addu'a ALLAH ya kwato min......"
Da sauri tad'aga masa hannu, cikin masifa ta ce, " kai sauraramin! Nizaka madai sakarai Umaru!? Shin wane shegene zai sayi Abu ya hanaka kud'inka?.
Nafa lura yanzu kaima ka canja, harma gara Abubakar d'in dakai.
Kud'i karik'e karka bada, ALLAH bazai hanamu yanda zamuyiba, nitashi kabani guri shashasha kawai.
Anutse ya Umar yatashi yafita batareda yace da ita komaiba.
Yana fita wayarsa tafara wringing............



_kuyi hak'uri da wanan._







*_(((S))).......2017_*
*_Love you all_*
[12/27/2017, 3:16 PM] ~πŸ‡© ' πŸ‡― πŸ‡¦ πŸ‡· πŸ‡­βœ: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’».........



πŸ’Ž *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* πŸ’Ž


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAIπŸ‘ŒπŸΌ WRITER ASSO.....😜_*

*_Mutuwa! mutuwa!! Mutuwa!!!. Mutuwa maiban tsoro, batabarin kod'an yaro, ko jinjiri saita d'auka, takaishi koda bayaso mak'abarta. Sarki ALLAH jallah, Jallah nidai natuba ALLAH, rabban kayafemu albarkacin manzo nawa d'an gata._*
_wannan wak'a gsky Ce, kuma tana ta6amin zuciya aduk lokacin Dana tunata wlhy._
😭😭😭

*_page→55-56_*


..........A kasalance yad'aga, dan wringing d'in wayar bak'aramin fad'uwar gaba yasashiba. Komiye dalili oho.
Asslamu alaikum, yayi maganar cikin sanyi.
Daga can yazeed ya amsa masa shima muryarsa a raunane, yad'ora da fad'in abokina kakalli labarai kuwa?.
Yanzuma a sanyaye ya Umar ya amsa masa da a'a abokina, amma miya faru?.
Jimmm yazeed yayi, zuwa can kuma ya sauke ajiyar zuciya, Umar sirikinkane sukayi had'arin jirgi yanzunan babu dad'ewa.
Da Sauri ya Umar ya dafe k'irji, cikin matuk'ar razana ya ce, "kana nufin dady mahaifin lubna!!!?.
Eh Umar, idan kana kusada TV ka kalla gashinan suna nunawa........
Bai bari yazeed yagama fad'aba yajuya cikin gidansu arazane.
Mama tana zaune har yanzu tana mita da zagin ya Umar saitaga yashigo aburkice, baibi takantaba yanufi TV ya kunna, NTA yakamo, ilai kuwa abinda suke nunawa kenan, had'arin yafarune a hanyarsu ta zuwa legos daga nan kano.
Mama ma sai jikinta yayi sanyi tatsaya sagare tana kallo.
Bak'aramar tarwatsewa jirgin yayiba, ga mutanenan kwance, wasuma Kansu yacire, wasu k'afa, wasu hannu, wasuma babu ta yanda za'a shaidasu dan duk sun canja kamanni. d'aya bayan d'aya akebi ana nunasu dan ana kwashe gawawwakinne da duba masu rai, dukda babu alamun akwai wani mahaluki dake numfashi acikinsu. gawar mahaifinsu lubna aka nuno, cikin amincin ALLAH shikam kamanninsa na nan, saidai jini dukya 6atashi, sannan hannunsa d'aya yafita.
Ya Umar yaruntse idonsa hawaye na kwarara, mama kanta kuka takeyi, (bak'aramin abune yake raunana jarumtar gwarzo namiji irin ya Umar ba) zuciyarsa da kwakwalwarsa suka Shiga tuno masa waye dady?, mutumin kirki maison talaka da son k'yautata masa, ya tuno ranar daya fara ganinsa shida direbansa, alkairin daya masa ya d'aga darajarsa fiyema da 'ya'yan cikinsa, wasu zafafan hawaye suka k'arayo ambaliya akumatunsa.
Mamace tayi k'arfin halin kama hannunsa ta zaunar akujera, a hankali take shafa kansa tana lallashinsa, ita kanta tasan miye matsayin dady azuciyar ya Umar, kosu sukace sun manta da halaccinsa akan d'ansu sunyi butulci ba k'aramiba.
Lallashin ya Umar takeyi sosai Wanda yake kuka harda shashshrka, kansa yana saman cinyar mama.....Umaru yanzu ba kuka yake buk'ataba, yana buk'atar addu'a ne daga garemu, babu abinda zamu sakanka masa dashi aduniyarnan inba addu'aba, Wanda ya haliccesa shine ya kar6i abinsa, muma nan duk irin wannan ranar muke jira Umaru...... Da ire-iren wad'annan maganganun ta kwantar masa da hankali.
Ahankali yafara sassauta kuka nasa saidai ajiyar zuciya, haka su Rafi'a suka dawo daga gidan inna suka samesu.
Suma sungani agidan inna dan haka basa buk'atar k'arin bayani, saidai ya Umar yabasu tausayi ainun.
Baibar gidanba saida aka kira sallar magriba.


Atsakar gida yatarar da Asma'u zaune saman kujera 'Yar tsugunno. Ta rabga tagumi.
Ko motsin shigowarsa batajiba barema sallamarsa, shima bashida k'arfin mata magana, saikawai yajingina da bango yazuba mata idanu tamkar mai nazarin wani abu.
Sunkai minti20 ahaka sanan ALLAH yabama Asma'u ikon d'agowa danjin kamar alamar mutum tsaye akanta.
Tarazana sosai, dan haka tayi shirin takewa da gudu, muryarsa a sanyaye ya ce, "Asma'u ninefa."
Gabantane yay azabar fad'uwa danjin muryar ya Umar dakuma sunan daya kirata dashi, Wanda zata iya rantsewa bata ta6ajin sunan abakinsaba sai yau.
Ya Fharuk lfy kuwa?.
Ajiyar zuciya ya sauke wadda yayita sau babu adadi, muryarsa hard'an rawa takeyi ya ce, "dadai sauk'i Husna."
Shiru tayi tana nazarinsa, saikuma yabata tausayi, gashi sunyi azumi, takama hannunsa suka shiga ciki.
A babban falo ta zaunar dashi bisa tabarmar data shirya kayan shanruwan.
Baice mata komaiba, tazuba zo6o mai sanyi tamik'a masa, kai ya girgiza mata alamar a'a ya k'oshi. Tuni idanunta suncika tab da kwalla, ganin haka sai kawai ya kar6a ya shaya kusan rabi, daganan yajingina da bango yay shiru.
Itama Asma'u shiru tayi, tasan

Please Login or Register in order to submit comment