Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aunty dawani daddad'an albishirfa nazo miki.
Tofa k'anina ko ansami matar aurene?.
d'an tsaki yayi ya ce, " Anty wane matar aurefa, aii aurena banan kusaba kuma dainamin zancensa.
Umar kanka d'aya kuwa?, wai sokake saika tsofe agidane?, shekararka fa 28 yanzu, amma ace babu aure agabanka?.
Hummm Anty sa'a kenan, Ku kawai auren kuke ambata, amma bakwa tunanin inda mutum zai ajiye matar, abinda zataci, Wanda zai mata sittira dakuma matsalolin yauda kullum musamman na rashin lafiya dakanzo tamkar ha6o.
Hakane Umar amma aii duk ALLAH ne mai komai da kowa ko?.
Hakane Anty ALLAH yasa mudace to, dama albishird'in nawa shine..................tas ya zayyane mata komai.
Saboda farinciki jitake kamar tatashi taita tsalle, ta ce, "ALLAH sarki Umar kaga ribar hak'uri ko?, lallai yau nayi farinciki sosai, ALLAH yasa iyakar wahalar kenan.
Amen Anty sa'a ngd.
Sund'an dad'e suna hira sanan yatashi yaymata sallama yatafi.
Daga nan aikinsa yatafi, yau cikin d'unbin farinciki yakeyin komansa har zuwa dare daya koma gida.
Yaukam dawuri yakoma gidan Dan ana isha'i yakoma.
Afalo ya iske mutanen gidan suduka, har yaya Abubakar yazo, suka gaisa Harris da su mufidama suka gaisheshi, mamadai ta had'e masa gabas da gamma, amma wanan bai hanashi gaishetaba.
Kamar yafad'a musu saikuma yayi shiru da bakinsa, and'anyi hira ya Abubakar yatashi yatafi, shima Umar mik'ewa yayi yamusu sallama yatafi d'akinsa, ganin haka Harris ma yamik'e akabar mama da 'yan matanta..........







*_(((S)))........2017_*
*_luv you all_*🀝😻.
[11/23/2017, 4:57 PM] ~πŸ‡© ' πŸ‡― πŸ‡¦ πŸ‡· πŸ‡­βœ: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’».........



πŸ’Ž *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*πŸ’Ž


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAIπŸ‘ŒπŸΌ WRITER ASSO........😜_*


*_Gaisuwa da fatan alkairi agareku, Action baby & Maman Khaleed, alkairin ALLAH yakai muku aduk Inda kuke, ALLAH yabar zuminci, INA alfahari dakuπŸ˜»πŸ˜β€πŸ‘ŒπŸΌ._*
*_page→13-14_*

........washe gari Umar yay shirinsa, kamar yanda yasaba yalek'a ya gaida mama, dukda bata wani amsa masa yanda yakamataba amma hakan bai damesaba yamik'e yashiga d'akin Abba shima ya gaisheshi, baisake bin takan kowaba yafice abinsa sai gidan Alhaji.
Yau har ciki mai gadi yabarsa yashiga da Babur d'insa, yananan tsaye saiga baby tafito yaudai tayi kwalliyarta sa6anin jiya dayasameta cikin kayan barci.
Cikeda rangwad'a tak'araso garesa, Umar yajanye idonsa daga kallonta, Hii my guy, tafad'a tana dafa adaidaita sahun.
d'aure fuska Umar yayi, ko kallonta baiyiba barema tasamu amsa.
Abin ya6ata mata rai, amma saita dake, ta ce, "sorry Assalamu alaika.
Sai yanzu Umar yajuyo fuskarsa babu yabo babu fallasa ya ce, " wa'alaikissalam.
Murmuahi tamasa tareda fad'in dama haka kake babu sauk'i?.
No bahaka bane, yadace duk inda d'iyan musulmi yashiga farko yafara sallama kafin yasamu damar aiwatar da Abu nagaba, ina fata daga yau zaki gane kuskurenki ki gyara.
Tayi far da idanunta, cikin sanyin murya ta ce, "kayi hak'uri zan gyara insha ALLAH.
Wani murmushin daya kasheta yamata, talumshe idanunta domin jin wani dad'i ya ratsa zuciyarta, bata dawo daga magagin shauk'in so ba muryarsa tadaki kunnenta.........
Wai miye cikakken sunankine?, nasandai baby ba suna baneba......
Da sauri taware idanunta akansa, cikeda salo ta ce, "sunan Lubna."
Shima maimaita sunan yayi a la66ansa, ya ce, "lubna!, nice name.
Cikeda jin dad'i ta ce, "da gsk?.
Kansa ya jinjina mata yana murmushi.
Wani uban tsalle tayi Wanda yasakashi tsayawa kallonta, ngd ya Umar I love you wlhy.
Umar kam yadaskare atsaye, mamakinta yakeyifa, tun jiya take ambatar kalmarnan akansa, amma yagaza gane inata dosa......... Muryar alhajice takatse masa tunaninsa, Umar kayi hak'urifa baby tacikaka da magana.
Murmushi Umar yayi ya ce, "babu komai Alhaji aii muna gaisawane.
Duk'awa yayi yana gaida Alhajin, Alhaji ya amsa yanamai kamasa ya tadashi tsaye, Lubna tazo saitin kunnen Dad d'inta tagaya masa wani Abu danima banjiba.
Dariya dad ya ce, " baby da gsk koda wasa?.
Dad serious wlhy, tarufe idonta.
Masha ALLAH babyna ALLAH yatabbatar mana da alkairi, kisa aranki kinsameshi kinji, kanta tagyad'a tanamai farinciki, shidai Umar dabaisan miye zancen nasuba kallonsu kawai yakeyi.

Tundaga Ranar Alhaji yad'ora Umar akan dukiyarsa, Umar ya ajiye daidaita sahu, yafara hawa motar da Alhaji yabasa, lokacin dayakaima su mama wannan zance mama tamkar zata goyashi Dan farinciki, tundaga ranar yazama d'an lelenta, komai Umar, duk wani motsinta Umar, abinci saiya za6a, idan yadawo daga kasuwa tayita nannan dashi tamkar wani jariri.
Shi Umar ma wani Abu dariya take bashi damamaki.
A6angaren kasuwa kuwa komai yaaa tafiya masa daidai saboda kasancewarsa mai ilimi, kullum cikin dabarar kasuwanci yakeyi Dan haka dukiyar Alhaji tak'ara bink'asa, ga Umar mutumne mai gsky da rik'on amana Dan haka Alhaji yake matuk'ar son Umar Fharuk.
Umar yazama d'an gida sosai, bashida wani shamaki agidan Alhaji, ko ina shiga yakeyi, ahaka kuma soyayaya mai k'arfi tak'ullu tsakaninsa da Lubna, soyayya mai tsafta suke nunama juna.
Umar kam komai yacanja masa yanzu, yafara zama babban mutum, ga d'inkuna na alfarma Alhaji namasa, duk motar dayaso hawa yake agidan Alhaji, gashi kowa sonsa yakeyi agidan.
Ganin yanda abubuwa suke tafiya daidai Alhaji yabama Umar jarin kansa ya ce, "shima yajuya, amma duk da haka yana kula masa datasa dukiyar.
Ubangiji mai hikima cikin k'ank'anin lokaci Umar yabunk'asa yazama babban d'ankasuwa abin kwatance, ga abokai masu kud'i daji da Kansu, kowa sonshi yakeyi, agidansu kam yazama shine babba, sai abinda yace, yamaida k'annensa makarantar kud'i, yagyara gidan tsaf tamkar bashiba, hakama inna binta bai mantataba, dakansa yacanjama Asma'u wata makaranta tafara zuwa, suma su Hasiya ya canja musu makaranta, dangi kowa yanacin amfanin Umar, mamako sai d'agawa da Nuna isa itama d'anta yazama wani Abu, zannuwa take sakawa masu tsadar gsk, harta canja k'awaye, komaidai zamzam.
Ana cikin haka Alhaji yabashi damar turo iyayensa domin Neman auren Lubna.
Sosai Umar yay murna da wanan batu Dan yana tsananin k'yaunar Lubna sosai, babu Wanda bai Santaba a family nasa, taje gidansu sau babu adadi domin gaida mama, har inna da Anty sa'a saida aka kaita ta gaida.
Manya sun shiga ansaka ranar auren Ya Umar da Lubna watanni kusa.


\\\\\\\\\\\\\\\\\\\\\\
Asma'u takalli 'yan uwannanta dasuka baje kayan alawa da biskit sunata rabo, baki ta ta6e tareda kauda kanta daga Kansu tacigaba dacin abincinta.
Antu Saratu ta harareta, kekuma miye kike wani ta6ema mutane bakine?.
Nifa yaya Saratu bance komaiba.
Fatee dake 6are cingam ta ce, "yaya Asma'u kodai kina kishine?, Dan sainaga kamar kinason ya Umar.
Kutttt, Asma'u tafad'a tareda jifan fatee da murfin kwano.
Kaucewa fatee tayi tana dariya, suma 'yan d'akin dariya sukeyi duka, Asma'u tayo kan Fatee tana masifa, da gudu Fatee tafito Asma'u ta biyota.
Gaf tayi karo da Abu, baya taja da sauri tareda dafe goshinta tana fad'in wash ALLAHna, abisa tsautsayi ta taka 6awon ayaba, aiko tazame suuuuu zata fad'i.
Da sauri yaruk'o hannunta ta fad'o jikinsa, daddad'an kamshin turarensa ta shak'a ta lumshe idonta, saikuma tabud'e da sauri danjin antureta gefe.
Ya harareta kewai bakida Kaine?.
Idanunta ta kwalalo waje, saikuma tahau kakka6e jikinta tana wani had'e fuska, yakatseta da fad'in ina hankalinki yatafi?.
Saida tad'an murgud'a bakinta amma bai ganiba sannan ta ce, " yana jikin......
Bata k'arasa fad'aba ta hango fatee, dagudu tawucesa tabi Fateen suka afka d'akin inna.
Girgiza kai Ya Umar yayi shima yanufi d'akin.
Afalon yatarar dasu suna zagaye kujeru, hasiya da Anty Saratu sunata tuntsura dariya, cikin dariya Anty Saratu ta ce, "wlhy Ma'u kifad'i gsky, Dan nima nadad'e ina zargin soyayya kukeyi da ya Umar, kumafa wlhy kun dace, kardai ki cuci kanki, kifad'a sai'a had'a masa biyu kawai.
Dan ALLAH Anty Saratu kibari, ALLAH zakusa nakuma TSA.......
Bata k'arasaba ta hangi ya Umar tsaye abakin k'ofa, mak'alewa maganarta tayi amak'oshi.
Suma duk kallonsu Yakoma kansa, yak'araso d'akin shima, guri yasamu ya zauna suka gaisa, ya ce, " innafa?.
Inna tana gidanku aii tunda safe.
Ayya aiban saniba, dayake badaga gidan nakeba.
Ruwa Hasiya takawo masa da zo6o, zo6on yasha Dan yanaso sosai, domin shima Inna takeyin zo6o ta ajiye .
Asma'u kam d'aki tashige, tana shiga hawaye suka fara bin kumatunta, tabbas son Yaya Umar na neman illata mata zuciya, tadad'e da d'umbin sonsa azuciyarta tun tana karama, haka taketa dakonsa, saboda alkunya irinta 'ya'ya mata Hausa Fulani dakuma tsoronsa Dan tuni ta lura ya Umar kam haushintama yakeji, wannan yasa take dannewa da k'ok'arin ciresa aranta, amma hakan na Neman gagara.
Ashe duk k'ok'arin danne zuciyarta da takeyi akan ya Umar 'yan uwanta harsun fara fahimtarta?, ya ALLAH ka kawomin agaji akan wannan lamari, idan ya Umar mijinane ALLAH ya karkato da hankalinsa kaina, idan kuma ba mijina bane ya ALLAH kaciremin sonsa azuciyata na hak'ura da zayyan d'ina, daya dawo muyi aurenmu.....
Share hawayen fuskarta tayi da sauri danjin muryar ya Umar na kwala mata kira.
"Husna!."
"Husna!!."
Lumshe idanunta tayi sannan ta amsa, shikad'aine yake kiranta da Husna, shiyyasa takanji sunan daban kamar ba nataba.
Asanyaye tafito, yana tsaye a bakin k'ofa da alama fitama zaiyi, kallo d'aya tamasa ta kauda kanta, tad'anje nesa dashi tashaya kamshin turarensa na bugun hancinta, shima idonsa akanta yamik'a mata kud'i yana fad'in da safe kije gidan matar Yousif kikaimata ta ajiye masa, saura kuma idan kinje ki kai dare.
Saida ta tura baki gaba sannan ta kar6a, yamik'a mata d'ari biyar na mashin, nanma kar6a tayi, baijira cewartaba yafice.
Da harara tarakashi, tajuyo cikin falon tana k'unk'uni.
Anty Saratu dasu Fatee suka shek'e da dariya harda tafawa suna fad'in soyayya ruwan Zuma.
Asma'u bata kulasuba tashige d'akin inna domin ajiye kud'in............







*_(((S))).......2017_*
*_Luv you all😻🀝 ._*
[11/25/2017, 5:37 PM] ~πŸ‡© ' πŸ‡― πŸ‡¦ πŸ‡· πŸ‡­βœ: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’».........



πŸ’Ž *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*πŸ’Ž


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAIπŸ‘ŒπŸΌ WRITER ASSO........😜_*

*_masha ALLAH, ALLAH yasauki k'awata Ayusher Muh'd lfy, ya azurtata da samun haihuwar baby gal, Ubangiji ALLAH yaraya mana ita akan turbar musulinci, ALLAH yasa Bad'i mudawo sunan twin's kuma_*😻😜



*_page→15-16_*

............Shirye shiryen biki ya kankama sosai, ya Umar yagama gyaran gidansa tsaf, gidane na garari Wanda za'a iya kira namai kud'i, kowa yagani dolene ya yaba Dan gidan yaginu babu k'arya.
Agidansu amaryama shirin biki akeyi na 'Yar gata Dan wannan shine karo na farko dazasu aurar, komai na 'yan gata aka shirya, damma mahaifiyarta batason auren, Dan taso ace lubna ta auri d'an shahararren mai kud'i irinsu amma ba Umar ba, to amma babu yanda zatayi tunda takafe shitake so.
Mama kam wannan aure yamata dad'i d'anta zai auri d'iyar masu kud'i, sai d'agawa da fariyya takema 'yan anguwa.
Asma'u tunda aka fara shagalin bikinnan tashiga matsanan ciyar damuwa, amma haka tadage da addu'oi harda azumi tana addu'ar ALLAH ya danne zuciyarta tazama mai hak'uri, inna tana kula da duk halin da Asma'u tashiga amma babu yanda zatayi saidai ta taya d'iyar tata da addu'a tunda haka ALLAH yatsara lamarinsa.

*_biki buduri_*
Ansha biki na nunawa a duniya Dan taron d'aurin aurene daya halarci manya-manyan masu fad'a aji ak'asarnan, sarakuna, 'yan siyasa, 'yan kasuwa, harda shugaban k'asa, lamarin bak'aramin girgiza Ya Umar yayiba, Dan baita6a zaton ko kansilan anguwarsu zaizo d'aurin aurensaba bare shugaban k'asa gaba d'aya.
Biki kam saidai Sam barka Dan nera tayi kuka sosai.

Bayan biki amarya da ango ansha amarci babu k'arya, sosai suke zuba soyayya kamar babu gobe, saida ya Umar yay sati biyu baya fita kasuwa, koda yaushe yana gida manne da lubna, abinci saidai suje su sayo.
Tsawon wata d'aya ana kashe kan amarci, amarya babu abinda takeyi dagaci sai barci, komai saidai 'yan aiki, wani lokacinma ya Umar keyimata wankan, abinda yafara 6ata masa rai da ita shine son jiki, komai saidai ayi mata tana a kwance, daidai da ruwan dazaisha saidai tasaka 'yan aiki sukai masa, gyaran d'akinsama haka, wani abin k'arin haushinma shine duk sanda zaidawo gidan saidai ya Tatar da ita shame-shame kwance 'yan aiki namata tausa, wannan lamari na 6ata masa rai matuk'a.
Daya kasa daurewa yafad'ama mama saitace yacika k'orafi shikam, ya yarinya tatashi cikin Hutu yanzu zai k'ok'arin tsinke mata, itafa bata yarda ko fad'a yaringa yima Lubna ba, abin ya6ata masa rai, yarasa wane irin haline da mahaifiyarsu?, haka yabar gidan ransa a6ace.



////////////////+////////////
A6angaren Asma'u kuwa abubuwa sun mata sauk'i, tanata k'ok'arin cire ya Umar azuciyarta, tamaida hankalinta sosai akan karatu babu wasa, burinta bai wuce Zayyan d'inta yadawo suyi aureba.

Ana haka Lubna ta fara laulayin ciki, zazza6i da yawan amai sun addabeta Dan haka ya Umar yakaita asibiti, gwaji farko akace cikine.
Cikin tashin hankali lubna ta ce, "doctor jafar cikifa kace?".
Dariya Doctor jafar yayi, ya ce, " hakane lubna kina d'aukeda babynmu.
Afusace takalli ya Umar da farinciki yacika zuciyarsa shima zai zama baba, ta ce, "Umar kanajindai abinda doctor yafad'a aii?. Murmushi ya Umar yayi yarungumota zuwa jikinsa yana fad'in naji sweet d'ina, kuma inacikin farinciki......
Bai k'arasaba ta fisge jikinta daga nasa, ta6d'i jan Umar wlhy bazata sa6uba, yaza'ayo kamarni 24year's ace inad'aukeda ciki, lallai akwai lale awannan batun.
Cikin mamaki ya Umar ya ce, " Lubna akwai lale kamar yaya?, wannan ba abin farinciki bane?.
Abin farincikine agareka Umar, ammani abin kunyane da bak'inciki agareni, ace kamarni beby wata hud'u da aurena aganni da ciki, haba saikace dai wata akuya, asaima k'awayena sumin dariya wlhy.
Daga ya Umar har doctor jafar kallonta sukeyi cikeda mamaki, ya Umar ya kwantar da murya cikin Nuna damuwa ya ce, "haba Lubna miye abin kunya ga samun k'yautar ALLAH?, kitunafa akwai dubunmu dasuke nema amma ALLAHA bai basuba muyabamu, bakuma dan munfisu agurinsa bane, a'a ikonsane yasa yabamu sukuma baibasuba, amm.......
Hannu tad'aga MASA cikin masifa ta ce, " kaga Umar Dan ALLAH sauraramin da wannan wa'azin naka mana, nifa nace banason ciki yanzu, danhaka saikasan yanda zakayi dani, ban shirya rainon cikiba ayanzu kuma babu mai tursasani nayi.
Ran ya Umar yafara 6aci, Dan haka afusace shima ya ce, "to wlhy Lubna babu mai zubarmin da ciki, dukma abinda zakiyi saidai kiyi, yamik'ama doctor jafar hannu sukayi musabaha, abokina ngd, yadaka mata tsawa dallah malama tashi muwuce.
Mik'ewa Lubna tayi Dan tsawar Umar d'in ta razanata sosai
Tundaga wannan ranar zamansu yafara rawa, kullum cikin fad'a da tashin hankali, abin kamar wasa har yakaisu ga zuwa wajen iyaye, mahaifiyar Lubna ta goyi bayan lubna ta zubda ciki, amma mahaifinta ya hana, sosai lamarin ya6ata ran Lubna, tundaga wannan lokacin komai ya canja musu, shidai yana nuna mata kulawa sosai da tattali, duk abinda ta ce, "tanaso zai saya matashi, ga cikin NATA da saka shagwa6a, tattalin dayake nuna mata yasakata sakin jiki itama ta manta da komai suka koma zuba soyayyarsu, mama bata had'a sati d'aya batazo gidanba ganin Lubna.
Ahaka cikin lubna yashiga watan haihuwa, kuma Yakama lokacin hutunsu Asma'u suna gida.
Ya Umar yaje ga inna tabashi Asma'u danta taya Lubna zama tunda tace bataso akawo mata kowa, dayace to yad'akko Asma'u?, saitace ta amince zata zauna da Asma'u Dan mutuniyarta ce.



%-%-%-%-%-%
Tunda Asma'u tazo saita raina tsaftar matar gidan Dan bawani zuwa sukeyi sosaiba, batayi k'asa agwiwa ba tace duk 'yan aikin su huta tazage sosai tagyara gidan har d'akin ya Umar ko INA yad'au k'amshi, takuma shiga kichin tamusu abinci mairai da lafiya.
Lubna dakebin Asma'u da kallo ta ce, "lallai sunnunki da k'ok'ari, wai bak'yajin ciwon jikine?.
Dariya Asma'u tayi tareda fad'in wlhy aunty Lubna banajin komai, aiini ban d'auki aikin gidannan aikiba, idan dawani bayan wannan tom zanyi kuma natashi garau.
Baki luban ta ta6e tace lallai wahala da rai.
Asma'u batace komaiba saidai dariya.
Da ya Umar yadawo tun a harabar gidan yaga canji, yashigo falon shima cikeda mamaki yakebin ko ina da kallo, Asma'u dake zaune tana kallo tamik'e tana fad'in sannu da zuwa ya Fharuk.
Kallonta yayi ya ce, " yauwa Husna sannunki, Lubna kam ko kallo bai ishetaba tana zaune turus ak'asa, ya Umar yak'arasa gareta yana murmushi, rungumota yayi had'eda manna mata kiss akumatunta, Uwar biyu ykk?. Fuska ta yatsine masa tana wani kumbura Baki, kacefa yanake tunda kahad'ani da aiki, murmushi yayi acikin kunnenta ya ce, "aitare mukayi bani kad'aiba ko?, bare amin d'agwaiy, dukan wasa tamasa ak'irji, yatashi yana dariya, daidainan Asma'u tafito daga kichin d'aukeda k'aramin tire tad'ora ruwa da lemo da cup, ganin yamik'e ta ce, ''ya Fharuk ga ruwa.
Kallonta yayi acikin wani yanayi, tunda yay aure ba'a ta6a akawo masa ruwaba ayayin daya dawo gida, wani lokacinma saizaici abinci za'a bashi kokuma ya rok'a, kansa ya jinjina mata yakoma ya zauna, Asma'u ta tsiyaya ruwa ta mik'a masa, kar6a yayi tareda bismillah yasha, Lubna ta ce, " Asma'u kedai bakya gajiya, yanzunan k'ato dashi saikin kawo masa ruwansha?.
Kallonta kawai Asma'u tayi amma bata iya furta komaiba, shimadai ya Umar zuciyarsa ta sosu da maganar ta Lubna amma saiya share yamik'e bayan yagama sha, d'akinsa yashiga danya rage gajiya, Kallon ko ina yakeyi cikeda sha'awa, yasan wannan aikin Asma'u ne Dan matarsadai bata iya komaiba sai addabama 'yan aiki, dawad'annan tunane-tunanen yay wanka yashirya sannan yadawo falon, inda yabar Luban nan yasameta da wahalallun 'yan aikinta suna faman mata tausa, harya zauna Asma'u ta ce, "ya Fharuk ga abincifa.
Kallonta yayi saikuma ya kauda idonsa, ya ce, " yaushe kika iya abinci?, idanu Asma'u ta kwalalo danjin rainin hankalin mutuminnan, saikace yau yafara cin abincinta, tad'an murgud'a baki sannan ta ce, "aibani nayiba Anty Lubna CE.
Da sauri ya kalleta, saita kauda idonta, ya jinjina kansa Dan yagane bak'ar magana tamasa, itako Lubna saita washe baki tana fad'in a'a kedai kikayi abinki, ni inani ina aikin wahalarnan, my Honey kaje kaci wlhy akwai dad'i sosai dantafi kuku iyawa, nidama zata dawo nan gidan danaso haka..
Kallonta kawai yakeyi cikeda al'ajabi amma yagaza furta mata komai, saida ya mula Dan kansa harma Asma'u tayi fushi sannan yasakko k'asa Dan bayacin abinci a dinning, Asma'u tajere masa komai tazuba masa, aii mutuminku dayayi cokali d'aya saida ya lumshe idanu, sosai yakejin dad'in abincin, wannan yana d'aya daga cikin abinda yasa ya d'akko Asma'u ta zauna dasu.

Tundaga ranar komai Asma'u takeyi agidan, tazama tamkar itace matar gidan, kwananta takwas dazuwa Lubna ta haihu 'yan biyu duk mata, wayyo zokaga murna wajen ya Umar da sauran dangi harma da family d'in Lubna, ranar suna yara sunci sunan mama da momyn Lubna, wato Maryam da Haleematu, za'a ring a kiransu Amrah da Afrah.
Bayan suna dakamar sati biyu su Asma'u suka koma makaranta, Dan haka ta tattara ta koma gidan d'aukeda shatara ta arzik'i daga Lubna da Ya Umar...............








*_(((S))).....2017_*
*_Luv you all_*
[11/26/2017, 4:48 PM] ~πŸ‡© ' πŸ‡― πŸ‡¦ πŸ‡· πŸ‡­βœ: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’».........



πŸ’Ž *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*πŸ’Ž


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAIπŸ‘ŒπŸΌ WRITER ASSO........😜_*


_masu karatu karfa Ku rikice, har yanzu muna cikin tunanin Asma'u ne_.
*_page→17-18_*

.........Shekaru sun shud'a sosai Dan su Asma'u harsun kammala s,s,c,e d'insu, amma haryau Zayyan bai dawoba, abin yana damunta, hakama iyayenta, gashi bata kula kowa Dama saishi, iyayenta sunso Sumata aure tunda ta kammala secondary amma hakan ya gagara, suna zaman jiran dawowar Zayyan, a haka Asma'u takusan cinye shekara agida.
Ranar ya Umar saiyazoma Inna da shawarar mizai hana Asma'u takoma makaranta da wannan zaman?, idan saurayin nata yadawo koda tana karatunne sai ayi auren tacigaba agidan mijinta.
Da farko inna da baba sunk'i, amma ya Umar yadage da nuna musu fa'idar karatun sai suka amince.
Babu 6ata lokaci yafara nema mata makaranta, dandanan kuwa aka samu Dan yanzu su Yaya Umar sunzama manya, komai shine yayi mata, tafara zuwa makaranta nan FCE kano.


___________________
Agidan ya Umar kam abubuwa na tafiya daidai, yaranshi sunyi girma ko ina zuwa sukeyi, ga surutun tsiya abakinsu, soyayakam shida matarsa sai abinda yay gaba, hakama danginsa kowa sonsa yakeyi tamkar ya goyasa musamman mama da kawu kabiru, ga abokaimadai hakane, abokai gareshi tamkar tsiya, shikansa yana mamakin wasuma a ina ya sansu?, 6angaren kasuwarsa saidai godiyar ALLAH, kullum k'ara cigaba yakeyi, yabud'e babban super market akasuwa, komai kashiga zaka samu awajen, tundaga suturu akwai 6angarensu, kayan kwalliya, kayan mak'ulashe, kayan abinci, kayan d'inki, kayan wuta, kai harsu wayoyi dukzaka samu, ya bunk'asa sosai, gashi yabuga musu wani k'aton gida na garari mai 6angare buyu, tuni Lubna tarud'e da tambayar d'ayan 6angaren nawaye?.
Ya ce, "mata na yarane, idan sunyi girma can zasu koma, hankalinta yad'an kwanta amma ba sosaiba Dan bata yarda dashiba ko kad'an.


Rayuwadai ta shud'a sosai, hargasu Asma'u sun kammala karatu na tsawon shekara uku, tafito da result mai k'yau, masha ALLAHU Asma'u tazama cikakkiyar budurwa mai kimanin shekaru 22 Aduniya, har yanzu bata kula kowa wai tana jiran Zayyan, amma k'ark'ashin ranta tana mak'ale da son ya Umar har yanzu dan dai babu yanda zatayine, ayanzuma ganin take yamata nisa fintin kau danya zama babban mai kud'i matashin maiji da kansa, tako ina ya Umar yagama had'ewa gashi da d'abi'u irin na manya wad'anda suke matuk'ar k'ara masa kwarjini a idon jama'a.
Ayanzukam bak'aramin bud'ema Asma'u wuta su inna sukayiba akan ta fidda miji, hankalinta yakai k'ololuwar tashi, idan tana kuka saidai su Fatee suyita lallashinta da bata baki.
Ana cikin haka saiga Zayyan tamkar an jehoshi, Asma'u tayi farinciki mai yawa, amma daga baya tayi kuka harya kaita ga kwanciya asibiti saka makon maganar da Zayyan yazo mata dashi mai ratsa zuciya.

Lokacin da Zayyan yazo Asma'u tafito bayan ya aika kiranta, batayi zaton shibane Dan haka tafito cikin fushi, yayinda tayi tozali da Zayyan yaci wani uban wanka yana jingine da motarsa saita rikice Dan farinciki, cikeda zumud'i tak'araso garesa tana fad'in zayyan da gsk Kaine?, kokuwa mafarkin Dana saba yine?.
Zayyan yad'ago yana kallonta babu yabo babu fallasa, tun anan jikin Asma'u yayi sanyi Dan ganin halin ko in kula da Zayyan ya nuna agareta, jiki a sanyaye tace sannu da zuwa, bai amsaba amma yamik'a mata IV.
Cikeda mamaki ta amsa tanamai Kallonsa, tayi k'arfin halin fad'in zayyan wannanfa?.
Yatsine fuska yayi ya ce, "IV

Please Login or Register in order to submit comment