Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwanta, shikuma yad'auke idonsa daga kanta yamaida hankalinsa akan maganar doctor.
Okey doctor babu damuwa ngd sosai, saida safe.
ALLAH yakaimu Alhaji, agaidamin da madam.
Okey zataji, agaida iyali.
Koda ya Umar ya kammala wayan baikalli Asma'u ba yatashi yafice, itako tak'ara k'udundune kanta a bargo, tamkar wadda ake shirin sacewa.

Waje yaje wajen Muktar, saida sukad'anyi magana ta mintuna sannan yadawo gidan.
Kaitsaye d'akinsa yanufa, yay wanka tareda shirin barci tsaf sannan yakoma d'akin Asma'u.
Harma tafara barci ita.
Yad'an dad'e akanta yana k'are mata kallo cikeda tunani kala-kala tamkar bayason abinda yay niyyar yi agareta na bata taimakon da doctor yabashi shawarar.
Tsawon mintuna sannan yazauna abakin katifar tareda d'aga bargon yashiga ahankali.
Jawota yayi ya manna da jikinsa, wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke tareda rinmtse idanunsa. Itakam sai kawai tagyara kwanciyarta danjinta cikin wani lallausan jiki, gawani d'umin mai dad'i da k'amshi. Barcin yaci k'arfinta shiyyasa ko farkawama batayiba.
Amma ga mutumin naku ba haka baneba, jinsa yakeyi tamkar bashiba, tuni yasan shi mutumne mai yawan buk'ata shiyyasa yake tausayin fara kusantar Asma'u, amma yazaiyi? Zuciyarsa takasa daurewa, akwana biyunnan hak'uri kawai yakeyi. Yanason kasancewa da matarsa amma yana gudun karkuma ta rainashi. Yakuma k'ank'ame ta sosai tamkar za'a kwaceta daga gareshi, jin anrik'eta tamau yasakata motsawa, shima saiya sassauta mata.
Addu'a yamusu ta barci, tanata barcinta amma shi yagagara yin nasa saboda kwad'ayin kasancewa da ita................




*_"ngd duknaga sak'on gaisuwarku, harma damasu kirana, harma wad'anda basu sami damaba, dukna gode ALLAH yabar zuminci, nama warke, ammafa ina jiran kazarπŸ˜‹πŸ˜‹πŸ€·πŸ½β€β™€πŸ˜„"_*.
Luv you allπŸ’‹πŸ’―







*_Luv you all_*
*_(((S))).......2017_*
[12/9/2017, 8:40 PM] ~πŸ‡© ' πŸ‡― πŸ‡¦ πŸ‡· πŸ‡­βœ: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’».........



πŸ’Ž *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*πŸ’Ž


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAIπŸ‘ŒπŸΌ WRITER ASSO........😜_*

*_page→33-34_*

.......Haka yakasance yana gadinta har asubahi baisamu wani barcin kirkiba, itakam bamatasan yanayiba, barcinta tasha sosai, musamman datajita cikin wani ni'imtaccen jiki mai yalwataccen k'amshi, ga d'umi na musamman dayafi bargon data wuni aciki.
Kiran sallar asubahine yasakata farkawa, akuma lokacin wani barci mai dad'i ya d'auki ya Umar kasancewar baisamu yiba farkon dare, ahankali ta bud'e idanunta tanamai ambatar addu'ar farkawa daga barci, saukar numfashin datakeji ahankali visa gadon bayanta yasakata juyawa ta sauke idanunta akan fuskar ya Umar daketa barcinsa. Sosai tawaro idanu waje, azuciyarta ta ce, "la'ila. miya kawo ya Fharuk nan? Kardai tare muka kwana? Nabani wannan abin kunya har ina. Tana k'ok'arin zame jikinta ya Umar yafarka. K'ara rik'eta yayi danjin zata bar jikinsa, kokad'an baiyima zaton asuba tayiba.
Jin haka Asma'u ta ce, " ya Fharuk asuba yayifa." 'Muryarta narawa tayi maganar.'
Bud'e idanunsa yayi shima, ahankali cikin muryar barci ya ce, "Asmah da gsk asubahi tayi?."
Kanta ta iya d'aga masa kawai, amma takasa magana.
Yunk'urawa yay yatashi zaune shima yana binta da kallo, kauda idonta tayi daga kansa tashige bayi. Shima saiya tashi yafita zuwa d'akinsa.

Yana dawowa daga masallaci yalok'o d'akinta, tana zaune akan sallaya tana karatun alkur'ani, saida takai k'arshen surar sanan tatsaya, dama takusa kammalawa. Kanta ak'asa ta ce, "ina kwana."
Ya ce, "Lfy lau, yajikin naki?.
Alhmdllh. Nama warke.
Masha ALLAH, har sanyin kindainaji kenan?.
K'asa takumayi da kanta Dan kunya, haka kawai yau taji tana matsanancin jin kunyarsa, kokad'an bataso su had'a ido, musamman idan ta tuna cewa aguri d'aya suka kwana, manne da juna kuma..........
Katse mata tunani yayi dafad'in, kinyi shiru, ko har yanzundai kinajin sanyinne? Idan kinaji kuma to sainak'ara baki d'umin jikina.
Tusa kanta tayi cikin cinyoyi, kai ya Fharuk kabari plss.
Hummyim toni minayi kuma?.
Shiru tayi tana k'ara k'ank'ame kanta acikin cinyoyin nata.
Ganin haka ya Umar yamik'e abinsa, shikenan bara naje shago kinsan 'yan makaranta da saurin fita.
Kanta ta jinjina amma bata d'agoba ta ce, ''ALLAH yabada sa'a.
Ameen yafad'a yana fita...........




____________________
Akwana ukunnan sosai ya Umar ke kulada Asma'u, wanan karonkam sunci gari, Dan har mama saida tazo dubata, hakan yayima ya Umar dad'i sosai, dazata tafi yahad'a mata abubuwa sosai.
Dukda batawani d'auki shagon da muhimmanciba tamasa godiya tawuce.

Bayan tafiyar mama saiya shigo gidan, Asma'u nazaune akan katifarta tana canja zanin gado, canjama filo riga takeyi.
Yay sallama. d'ago k'yawawan idanunta tayi tasauke akansa, gira yad'aga mata tareda sakin wani sassanyan murmushi.
Itama murshin tamasa sannan tajanye idanunta tacigaba da abinda takeyi.
Harta wuce?.
Uhm tawuce, yafad'a yana zama bakin katifa. Ya ce, " lallai kekam 'yar gatan mamace, yau har tana zuwa dubaki?.
Ya Fharuk kenan, dama can ni 'yargatan mamace koka mantane?.
Ban mantaba my Asmah Husna!.
Murmushi Asma'u tayi danjin wani salon suna daga yayan nata.
Kwanto da kansa yayi saman filon data d'ora akan cinyarta bayan tagama saka rigar, ya hard'e hannayensa a k'irji tareda lumshe idanu.
Itadai Asma'u tana kallon ikon ALLAH, Tunda tayi zazza6in nan take ganin sabon salo wa yayan nata, ta tsurama k'yak'yk'yawar fuskarsa ido, sosai ya Umar ya had'u, gashi bak'i sosai, kuma bak'insa mai k'yaune, kwanakin baya yarame amma yanzu saitaga yamata k'iba, kodan hankalinsa yafara kwanciyane?.
Hannu takai ahankali zata ta6a girarsa dake matuk'ar burgeta sosai, girarsa tanada yawa, tayi kamar zata had'e dajuna, kasancewarsa bak'i kuma bai hana bayyanartaba.
Bud'e idanu yayai ahankali danjin motsin hannu akan idonsa. Da sauri Asma'u tasa hannu tarufe fuskar tata. Yayi murmushi mai sauti. My Asmah miyafaru?.
Babu komai fa.
Hummm k'arya babu k'yau.
'Yar dariya tayi, batareda ta ce, "komaiba". β€˜zuwa can kuma ta ce, " Yaya bazakaje shagobane?.’
Bud'e idonsa yayi sosai tareda d'age gira d'aya yana wani murmushin gefen bak'i, ya ce, "kingaji daganinane?."
Lah a'a bafa haka nake nufiba.
To mikike nufi?.
Uhm damafa dankar mutane suyita jirankane, jibafa har 9:48.
Juyawa yayi yana kallon agogon shima, saikuma yadawo da dubansa kanta, karki damu akwai mutum a shagon.
Akwai mutum?. β€˜Asma'u ta tambaya cikin mamaki.
Tashi yayi zaune sosai, yad'auke filon daga cinyarta yagyara asaman katifar sosai ya kwanta. Itadai binsa kawai takeyi da kallon mamaki. Bata ankaraba taji yajawota, ta fad'o jikinsa. Kafin tayi wani yunk'uri ya rungumeta tsam tamkar za'a kwaceta.
Tuni jikin Asma'u yafara rawa, tamarasa mizatayi ta kwaci kanta. Gogan naku kuwa abubuwa yake mata masu nuna tsananin k'yauna da bege agareta. Tun tana iya yunk'urin hanashi harta Gaza komai sai kuka ahankali damasa magiyar yayi hak'uri bafatada lfy. Kokad'an bai saurari furicin nataba, sosai cukirkud'ata ya cigaba dayi yanda yakeso.
Saida yayi mai isarsa sanan yasaketa yana maida numfashi. Itakam kuka takeyi sosai, ganin yasaketa tatashi da hanzari tabar masa d'akin. Binta kawai yakeyi da kallo yana zuba murmushi tamkar wanda yasamu abinda yakeso..



_____________________
Tsawon kwanaki hud'u kenan tsakanin Asma'u da ya Umar ana 'yar wasan 6uya, ko kad'an bata yarda su had'u dan harga ALLAH tsoronsa takeji, shago kam ko lek'e bata lek'ashi.
Yauma suna zaune atsakar gida itada maman faisal tana mata kitso (dan Asma'u ta iya kitso sosai), hirarsu suketa zubawa irinta mata, maman faisal tana tambayarta kozatasha wani magani takawo mata?.
Anty magani kuma? Maganin miyene?.
Dariya maman Faisal tayi sannan ta ce, "magani dai na mata.
Asma'u bata fahimci zancen na Maman Faisal ba ko kad'an, dan haka tayi dariya, kai anty saddiqa mu mata har wani magani ke garemu daban?.
Maman Faisal tajuyo tana kallon Asma'u da k'yau danson gaskata maganarta. Banganeba Asma'u! Kina nufin bakisan miye maganin mataba? Kina matar aure.
Asma'u dake kallon maman Faisal tad'an yatsine fuska, wlhy Anty saddiqa kiyarda dani bansaniba.
Jinjina kai kawai Anty saddiqa takeyi cikeda mamakin furucin na Asma'u. Dama har yanzu akwai matan dabasusan ire-iren wad'annan abubuwanba arayuwa kenan?. Idan akayi la'akari da yanda mata suka lalata kansu dashan magunguna yanzu, wasuma cutar dasu sukeyi amma sun gaza ganewa, dolene duk wadda tanuna bata saniba ayi mamaki.
Asma'u dai tacigaba dayima maman faisal kitsonta, sauraren k'arin bayani kawai takeyi daga gareta. Jin tayi shiru ta ce, " anty Saddiaqa kigayamin dan ALLAH, miye maganin mata?.
Bak'aramar dariya tambayar tabama Maman Faisal ba, dan haka tadara, saidatayi dariya sosai sannan ta ce, "Asma'u nabaki dama kitambayi Umar nasan zai fad'a miki miye maganin mata.
Shiru Asma'u tayi tana tunani azuciyarta, mizaisa anty saddiqa ta ce, " ta tambayi ya Fharuk? Shimiye had'insa da wanan maganar? tunda maganin mata akace.
Badai takuma cema Anty Saddiqa komaiba, amma ta k'udiri aniyar tambayar ya Fharuk d'in kamar yanda anty Saddiqa tafad'a mata.
Maman Faisal kam tayima Asma'u gatsene dantaga shin rainamata hankali tayi (tasan maganin Matan) kokuwa batama San miye ma'anar shan maganin matanba. Amma amamakinta saitaji Asma'un tayi shiru batace komaiba.
Itama daganan wata hirar takawo mata, ta watsar dawaccan maganar gefe kawai.
Bayan sun kammala k'itson sukad'anyi hira har yara suka dawo daga islamiyya, sunsan babu Inda mamansu take zuwa sai gidan Anty Asma'u, Dan haka suka shigo Nanal.
Oyayo 'yan islamiyya antaso?.
Eh Anty INA yini.
Lafiya lau yarana, ya makaranta?.
Lafiya lau.
Daga nan suka gaida mamansu ma.
Maman Faisal ta ce, "kunga kuje gida acanja kaya, Faisal kacanjama kowa kajiko, karfa Ku hargitsa kayan.
To mama, Faisal yaja k'annansa suka fita.
Asma'u da Maman Faisal kuma sunata hirarasu.
Suna nan zaune saiga ya Umar yashigo, da alama dai akwai abinda yazoyi cikin gida. Da Sauri Maman Faisal taja hijjabi tasaka.
Shi koma Inda take bai wani kallaba, yadai amsa gaisuwarta sannan yakalli Asma'u da ak'alla yad'au tsawon kwana Biyar bai gantaba, tun randa abinnan yafaru basu sake had'uwaba.
Itama kallo d'aya tamasa ta d'auke kanta daga gareshi.
Yana shigewa Maman Faisal ta zunguri Asma'u.
Asma'u kitashi gafa mijinki yashigo.
Yatsine fuska Asma'u tayi, yo Anty nimizan masa? K'ilama wani abun yazo d'auka.
Idanu Maman Faisal tazaro waje, Asma'u bangane mizaki masaba? Mijinkine fa? Yashigo gida amma bazakije kiji matsalarsaba?. Anya kinada wayau kuwa? Kamar yanda nake tsammani?.
Hummm Anty kenan inada wayau mana.
Inafa kikaga wayau tunda bakisan yazaki kula da mijinkiba. Bara kigani natashi idan Dan ganina zai hanaki bama mijinki kulawa.
Da Sauri taruk'o hannunta, lah wlhy Anty Bahaka bane, yihak'uri kizauna Dan ALLAH, kinad'an d'ebemin kewa kuma kice zaki gudu? Nidai yanzu fad'amin mikikeso nayi to?.
Maman Faisal ta sauke ajiyar zuciya, tana mamakin wai dama haka Asma'u take? batada wayo, ta girgiza kai tareda fad'in yanzu kije kikaimasa ruwansha, sannan kiji miye matsalarsa.
Shike nan Anty zanje, amma kimin alk'awari bazaki tafiba?.
ALLAH babu Inda zanje, jeki kidawo.
Da azama Asma'u tamik'e, kicin tashiga tad'iba ruwa a jok sannan tanufi cikin falonsu.
Ganin babu kowa anan tashiga d'akinsa da sallama k'irjinta na dukan tara-tara.
Gabantane yafad'i yayinda tayi tozali da Ya Umar tsaye yana goge jiki da Alama wanka yayi.
Taisaurin kauda kanta daga gareshi, zuciyarta na faman tambayarta wankan mi ya Umar yayi yanzu da yamma haka? d'azunfa babu dad'ewa yayi wanka?.
Ganin mutum agabanta yasaka rawar jikinta k'aruwa, jok d'in ruwan haryana girgiza.
Ya Umar ya jinjina Kansa kawai yana kallonta, ruwan hannunta ya kar6a kafin ta zube masashi akan katifa, Dan yakula arikice take sosai.
Tana bashi takama hanyar fita. Dasauri ya ce, "wai saurin mikikeyine haka?.
In INA tafara namarasa gsky, u...u....um....dama zanjene Anty Saddiqa tana jirana awaje.
Hum Kodai kinason guduwa saboda kina tareda dodo? Miyasa kike tsorona yanzun Husna? Konamiki kama da abin tsorone?.
Azuciyarta ta ce, " sosaima wlhy". β€˜amma afili sai ta girgiza MASA kai.’
Ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kai, kokad'an babu walwala afuskarsa, ya ce, "jeki kawai.....
Aibama tabari ya k'arasaba tafice da Sauri har tanayin tuntu6e zata fad'i. Tayi saurin tare Bango sannan tafice.
Ya Uamar yacije le6ensa da k'arfi yana naushin iska, yamatse hannayensa da k'arfi yana magana afili kamar wani sabon kamu.
Gashinan Umar dama abinda naketa gudan maka kenan, gashinan tanajin tsoronka, guduna takeyi, dama abinda Yasa ban nemi komai daga garetaba Kennan.
Jiba wai d'an abinda naimatannan yasa har tafara guduna. Wayyo nikam miye fafita!!.............?







*_Luv you all_*.
*_((((S)))).........2017_*
[12/11/2017, 8:57 PM] ~πŸ‡© ' πŸ‡― πŸ‡¦ πŸ‡· πŸ‡­βœ: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’».........



πŸ’Ž *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*πŸ’Ž


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAIπŸ‘ŒπŸΌ WRITER ASSO........😜_*

*_page→35-36_*

.......Haka yayta zagaye d'akin yana surutai, saida yagaji Dan kansa sanan yashirya cikin wankan k'ananun kaya yafito sai baza k'amshi yakeyi. Idan kaga ya Umar saika d'auka irin matashin saurayinnan ne dabai wuce 26 ba, yanada tsafta Da son k'amshi sosai.
Atsakar gidan Yakuma tarar da su Asma'u, wadda tun d'azun tadawo wajen Maman Faisal.
Saina dawo yafad'a yana k'ok'arin ficewa.
Adawo lafiya sukafad'a suduka, shikuma yafice.
Yana fita Maman Faisal tashiga yima Asma'u fad'a (Dan ta girmeta gsky, zata iya zama sa'ar Anty saratu ma). Haba Asma'u yanzunan mijinki zai fita bazaki masa rakkiyaba? Idanfa kika saka wasa wata zatazo ta kwace miki miji. Nakula kinada sakaci sosai. Hakamafa d'azun abirkice kika fito, kamar wadda taje wajen dodo. Kodai akwai matsalane?.
Girgiza kai Asma'u tayi, Dan aganinta baikamata tabama Anty Saddiqa labarin abinda yafaru itada ya Umar ba.
Maman Faisal tacigaba da fad'in to gsky ki gyara kinjiko. maza sunason ana kula dasu tamkar kwai a cokali. Indai kinama namiji haka to tabbas zai koma miki tamkar jinjiri wlhy.
Hakane anty amma wlhy ya Umar daban yake, yacika tauri dayawa. Wani lokacinma dolene kiji matuk'ar tsoronsa.
Hummm Asma'u kenan, duk taurin namiji mace saita sakashi laushi. Shawarar dazan baki ki fara karatun Hausa Novels, insha ALLAH zaki k'aru matuk'a da ilimin zama da miji. (Musamman idan kin had'u da buk d'in marubutan dasuka san Kansu) akwai wasu buks dana karanta na bilyn Abdul, na tabbata zaki k'aru acikinsu.
To a ina zan samu?.
Bak'yayin charting?.
Inayi da, amma yanzu banayi.
Tom Indai ba mijinki ya hanakiba kikoma yi zan baki no. d'inta.
To Anty ngd sosai.
Maman Faisal tamik'e dak'yar saboda tsohon ciki datakedashi, haihuwa yau ko gobe, bara naje gida, nasan sunacan sunamin 6arna tunda sukak'i dawowa.
To Anty ngd.....



..................................
Su Lubna anata hidimar biki, shiri sukeyi na garari Dan bikin namasu akwaine babu k'arya.
Komai awadace yake tafiya, party kam aii anshirya yafi kala 10, su Lubna sune amarori k'irjin biki.
Yau kamu Dan haka sukaci uwar kwalliya nawani sky blue d'in less itada Suhaima, sai walk'iya sukeyi, idan kagansu kai kace sune amaren, bakowa zaiga Lubna ya ce, "ta ta6a aureba bareba harda yara biyu.
Harabar gidan suka fito inda abokan Ameer suke birjik, duk sunci wankan bak'in wando da yellow d'in Riga, wanan shine kwalliyar kamu na maza.
Matankuwa yellow d'in wando da bak'ar riga. Sudai su Lubna basu sakaba.
Wani abokin Ameer ya ce, " kai yarinyar canfa tawuce dani wlhy, wai k'anwar Amee CE?.
Inaganin k'anwarsace, ammafa in k'aramar tafimin k'yau, kasanni ko aure zanyi banason yar 20+ gsky. Nafison daga 16 zuwa k'asa.
Dariya abokin yayi, ya ce, "humm aikai mugunta kakeji.......
Wucewarsu Luban tagabansu tahanasu cigaba da hirar. Sukam basusan sunayiba, sun wuce sun barsu da k'amshinsu.
Mota suka shiga, Lubna tajasu suka bar gidan.
Kaitsaye hall d'in daza'ayi kamu suka nufa. Dangin amarya Suma sunyi shirinsu sosai, amarya tad'auki k'yau, naira tayi kuka agidannan. Su Lubna sai nan nan akeyi dasu, sukuma suna fankama da Nuna isa, su adole dangin miji.
Babu dad'ewa su Ameer suka iso. Ba awani tsaya 6ata lokaciba aka fara gudanar da kamu Wanda yak'ayatar.
Sai wajen 9pm aka tashi, ansha casu kam babu k'arya. Idan kuga yanda Lubna tadage tana rawa saikusha mamaki......



____________________
Tunda Anty Saddiqa tafad'a mata idan tana sakaci wata zata kwace mata miji tashiga damuwa, tana matuk'ar son mijinta, tanajin ya Umar yafi sauran maza awajenta, idan akace wata zata iya kwaceshi agareta takanji tamkar an soki zuciyarta da mashi.
Wasu zafafan hawaye suka gangaro bisa kumarunta. Bata sharesuba, saima cigaba da matso wasu datayi.
Duvanta takai ga agogon d'akin, karfe 9:23pm amma har yanzu ya Umar bai dawo gidanba, tun fitar d'azu da yamma. Tana mamakin ina yajene har zuwa wannan time d'in?.
(Zuciyarta ta ce, ''yaje tad'i.") Rushewa tayi dawani kuka mara dalili....

Ni dariyama tabani araduπŸ˜‚.

Tana nan tana kukanta saitaji motsin bud'e k'ofa, da sauri tad'ago tana kallonsa. Ya Umar ne sanye cikin kayan barci, da'alama ma yadad'e da dawowa gidan.
Shima kallonta kawai yakeyi amma fuskarsa ko kad'an babu walwala. Cikin d'akin yak'araso, yaja tum-tum yazauna har yanzu idanunsa akanta. Itadai nata na k'asa, ga hawaye sha6e- sha6e a fuskarta.
Ahankali ya firzo huci daga bakinsa yana mai kauda kansa daga gareta. Ko kad'an bayaso yaga mace na kuka. Shi mutumne mai tausayi sosai musamman akan mata.
Yakuma dawo da kallonsa gareta, kukan mikikeyine? Ko har yanzu bakida lafiyar?.
Shiru tamasa, bata d'agoba, bakumata tanka masaba. Dan zuciyarta wani irin zafi takeji, gani takeyi kamar da gsk daga tad'in yake.
Cikin d'an fad'a-fad'a ya ce, "wai bakijinane!!?.
Da sauri tad'ago takalleshi, ganin yanda yakuma tur6une fuska sai tsoronsa yakuma kamata. Bakinta na rawa ta ce, "bakaine kaje tad'iba."
Tad'i!?. β€˜ya Umar yafad'a cikin sigar tambaya da mamaki.’
Itama kanta tad'a tana wani kumbura baki.
Siririn tsaki yayi, amma batajiba. Ya ce, "kewaye yagaya miki naje tad'i?.
Gabantane yafad'i, dan kuwa dai zuciyartace ta sak'a mata, bawanine yafad'a mataba.
Shima ganin haka sai kawai ya girgiza kai. Yakuma yin k'aramin tsaki tareda fad'in kinga ni bar wannan banzan shirmen naki gefe, magana nazo muyi. Tashi kije ki wanke fuskarki kidawo.
Ahankali tamik'e kamar wadda kwai yafashema aciki tashiga bayi. Fes tawanke fuskarta sanan tadawo gareshi.
Saida sukaja wasu 'yan mintuna sannan yay gyaran murya:- inaso kibani hankalinki nan muyi magana. Kanta ta jinjina masa alamar to.
_d'azu fitar danayi naje office d'in su muktar ne, dama tun kwana hud'u daya wuce munyi magana, ya ce, " nabada takarduna zai kaima ogansu yanemamin aiki. Dafarko ban aminceba Dan narigada na fidda raina ga aikin. Amma saiya nace sosai da magiya da kawomin hujjoji akan fa'idar Neman aikin harna amince.
Jiya yakai takardun, yaukuma ogan nasu saiya buk'aci ganina. Shine Muktar yakirani ina shago yasanarmin. Wanna dalilin yasa nashirya naje.
Tom saidai kuma abinda yagirgizani shine ogan su muktar abokine ga dad (mahaifin Lubna) akwai dangantaka mai k'arfi a tsakaninsu ta kasuwanci gsky, Dan sanda ina k'arkashinsa yasha aikena awajensa.
Abu na biyu kuma shine Alhaji Ahmad mai kano yad'aukeni aiki ak'ark'ashin kamfanin nasa, ya ce, "kuma yana buk'atar bayani daga gareni akan abinda yasa muka rabu da mahaifin Lubna.
Yabani dama daga nan zuwa gobe, idan nafad'a masa yace zuwa Monday zan fara aiki.
Yakika gani nafad'a masa gsky?, kokuwa na hak'ura da aikin kawai?. Ban fad'ama kowa maganarnanba saike, koshi Muktar baisan yanda mukayiba.
Asma'u tasauke ajiyar zuciya sanan ta gyara zama. Yaya nidai abinda nake gani kafad'a masa kawai, Dan ALLAH yagani bacin amana ko cutarwace taravaku da mahaifin anty Lubnar ba, yanzu kuma aiki za'a d'aukeka idan kayi kuma za'a biyaka, kaga kuwa guminka zakaci bawai a k'ark'ashin wani zaka zaunaba.
Kuma ina ganin koda kafara aiki tom nikuma saina cigaba da lura da shagon harmuga abinda ALLAH zaiyi.
Sosai ya Umar yagamsu da bayaninta Dan haka ya jinjina mata kai alamar gamsuwa, gawata k'aunarta na ratsashi, wani lokacin idan tayi Abu tamkar wata babba. Idan shirmen yamotsa kuma sai an sauke masa cikin tirelaπŸ˜‚.
Asma'u tayi murmushi mai kwantar da zuciya, ya Fharuk natayaka Murna, ALLAH yabada nasara da sa'a.
Ameen Husna ngd.
Filo yajawo ya kwanta.
Gaban Asma'u ne yafad'i, karfa asake irin ta ranar.
Kamar yasan tunanun datakeyi saiya mik'e zaune yana fad'in yau baza'a bani abinci bane?.
Da sauri Asma'u tamik'e, Dan danan tacika gabansa da kulolin abinci, tashi yayi zaune tazuba masa komai.
Yanzukam babu laifi yad'an saki fuskarsa, Dan yanacin abinci yana satar kallonta. Sukan had'a ido lokaci-likaci, ganin haka ya Umar yad'auke idonsa gaba d'aya daga kanta yamaida ahankali kan cin abincinsa.
Kamar daga sama yaji Asma'u ta ce, "ya Fharuk inada tambaya?."
Idanunsa masu haske yad'ago yana kallonta, saida ya had'iye abincin bakinsa sannan ya ce, ''ina saurarenki?."
Shiru nawani lokaci tanata juya maganar a zuciyarta, kamar tayi kamar kartayi, can wata zuciyarta na angizata akan ta tambayesa da ace tazauna cikin duhu.
Jin tayi shiru yace yadai? Kokin fasane?.
A'a. Dama inason tambayarka minene maganin mata?.
Sosai ya ware idanunsa akanta. Aransa yace mike damun kan yarinyarnan?. (Inhar bai mantaba Lubna ta ta6a fad'a masa kayan k'arin ni'ima sune ake kira Maganin mata. Dan yata6a rutsata tana sha saiya tambayeta maganin minene wannan?. Dayake Lubna macece da batada kunyar Abu kai tsaye, musamman ga mijinta, sai takecemasa maganin k'arin ni'imane)..........
Ganin yayi shiru yadaina cin abincin, kuma

Please Login or Register in order to submit comment