Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

' πŸ‡― πŸ‡¦ πŸ‡· πŸ‡­βœ: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’».........



πŸ’Ž *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*πŸ’Ž


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAIπŸ‘ŒπŸΌ WRITER ASSO........😜_*

*_page→7-8_*

......Umar kam tun aranar yaje yakar6i Babur d'in Adaidaita sahu, kuma aranar yafara aiki, ganin alkairin daya samu yasakashi farinciki sosai tareda samun kwarin guywa.
Bai sanarma kowa yafara aikiba agidansu saida inna tazo washe gari sukai magana dasu mama, badan mama tasoba ta amince, amma babu yanda zatayi Dan tanason inna binta sosai kodan k'aunar datake nunama 'yayanta, ta taka rawar gani sosai akan karatun Umar Dan d'an gidantane.
Tundaga ranar Umar yacigaba da hayar adaidaita sahunsa, dukda mama bata nuna farincikinta aikai hakan bai hanashi yimusu hidaimaba da d'an abinda yasamu, babu yabo babu fallasa suke kar6a, shikam Umar ko kad'an hakan baya damunsa harkokinsa kawai yakeyi.

Ana haka sai wani al'amari yafaru a wani daren Juma'a ranar alhamis kenan da daddare.
Bayan Umar yagama aikinsa misalin k'arfe 11 saiyayi harama tafiya gida.
Yana cikin tafiya saiyaga ana d'aga masa hannu tundaga nesa, lamarin yabashi tsoro Dan azatonsa 'yan fashine ko 6arayin Babur, haka yak'arasa wajen guywarsa asage yanata ambatar duk addu'ar datazo bakinsa.
Yataka birki agaban dattijo da wani matashi daketa k'ok'arin tsaidashi, matashin saurayinne yayma Umar magana.
Abokina Dan ALLAH kozaka kai alhaji gyad'i-gyad'i?.
Shiru Umar yayi na 'yan sakwanni zuwacan yasauke ajiyar zuciya tareda kallon agogon hannunsa, ya ce, "abokina darefa yayi duba kagani, gashi kasan akwai tazara daganan zuwa gyad'i-gyad'i.
Nasani abokina amma Dan ALLAH ka taimaka, wlhy daga airport na d'akko mai gidana saikuma mota tamana tsiya, tun d'azun muke tsumayen abin hawa amma bamu samuba.
Kafin Umar ya ce, " wani Abu dattijon Alhaji yalek'o yanafad'in yaro kadauro Dan ALLAH, wlhy nagaji sosai burina kawai nahuta.
Ajiyar zuciya Umar yasauke tareda gyad'a kai ya ce, "shikenan shigo mutafi baba.
Alhaji yaji dad'i sosai, Dan haka yashiga sakama Umar albarka, kayansa direban yakwaso zuwa adai-daitar sukaiyi sallama Umar yaja suka tafi.
Tunda suka tafi babu maima wani magana, Umar yana tuk'i yana tunanin rayuwa da yanda take tafiya, Alhaji kam yayi shiru abaya saboda gajiyar zaman jirgi dake nuk'urk'usarsa, saida suka isa gyad'i-gyad'i sannan Alhaji yanuma Umar layin dazasu shiga.
Ak'ofar wani katafaren gida suka tsaya, Umar yajinjina kai azuciyarsa yana fad'in wani kaya sai amale.....
Alhaji yakatse masa tunani da mik'a masa kud'i masu yawa Wanda shima baisan adadinsuba.
Umar ya yakalli kud'in ya kalli alhaji sannan ya ce, " baba 350 ne kud'inka aii.
Murmushi alhaji yayi ya ce, "d'ana karka damu kaidai kar6i.
A'a baba ngd kabani iya hak'k'ina kawai, girgiza kai Alhaji yayi dakuma ajiyema Umar kud'in akan cinyarsa, babu yanda Umar ya iya dole yakar6a yay godiya sannan yatafi gida da addu'ar ALLAH yakaisa lfy.
Inda yake kai adai-daitarsa yanufa, yasamu guri yay fakin, abinda yake lilli6eta yajawo zai rufe sai idanunsa suka sauka akan wani d'an k'aramin akwati, shiru yayi yana nazarin kowaye ya manta?.
Wata zuciya ta ce, " masa Alhajin Daka sauke yanzu.
Afili ya ce, "hakane kuma, ya kalli agogonsa saiyaga har 12:36, gsky yanzu yana tsoron sake hawa titin nan, kuma idanma ya iya komawa yanada tabbacin za'a barsa yashiga wannan gidan a irin wannan lokaci?, d'an tsaki yaja tareda d'aukar akwatin yana fad'in insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu da sassafe saina kai masa.
Da wannan shawarar yanufi gida, dama kullum shine k'arshen dawowa gida shiyyasa yake rik'eda key d'in gidan guda d'aya, bud'ewa yayi yashiga sannan yamaida yarufe tareda addu'ar rufe gida, d'akinsa yashiga yay wanka da shirin barci sannan yay nafilfilinsa kamar yanda yasaba ya kwanta.

_washe gari_
Tunda yatashi yay sallar asuba bai koma barciba dama shi haka yake bai iya barcin safeba kullum yana dawowa daga masallaci zai d'auki alkur'ani yahau karatu, saida gari yay sha sannan yay addu'oi yatashi, wanka yashiga.
Shigarsa babu dad'ewa mama ta shigo d'akin, idontane yasauka akan bak'uwar jakar mai k'yau, jikinta har rawa yakeyi tabud'e jakar, idanu tazaro amatuk'ar razane Dan ganin mak'udan kud'in dake cikeda d'an akwatin duk daloline sababbi k'ar.
Razanuwa da ganin kud'in yasa takasa aikata komai har Umar yafito daga wanka, shimadai bak'aramar razana yayi dagani kud'inba, Dan yauce rana ta farko daya fara ganin zunzurutun kud'i tsirara agabansa masu yawan haka.
Jikin mama amace ta ce, " Umaru INA kasamo wad'annan kud'in haka?.
Zama yayi abakin katifarsa, yajanyo jakar yana rufewa mama ba nawabeneba, wanine nad'auka jiya da daddare shine yamanta da jakar.
Mama ta washe baki tana fad'in Umaru aii yamzun sunzama naka tunda tsuntuwa kayi, lallai kagodema ALLAH da wannan arzik'i daya yimaka, dama masu iya magana necewa dare d'aya ALLAH kanyi bature.
Kallonta kawai yakeyi damamakin ganin rikicewar datayi Dan kawai taga kud'i, shi rabonma dayaga fara'ar mama agareshi harya manta wlhy, amma duba daga ganin kud'i dukta rikice, ya kauda Kansa saboda 6acin rai, amma kasancewarsa jarumin 6oye sirrin zuciya sai fuskarsa bata nunaba ko kad'an, cikeda ladabi ya ce, "mama zan maida MASA kud'insa ne, Dan zan gane gidan Dana saukesa insha ALLAHU.
6ata rai mama tayi, ta gallama Umar harara to Uban masana basaikaita maidawarba, idan banda ga6anci ALLAH yabaka irin wannan dukiyar har kayi tunanin maidama mai ita?, shi Kasan ta hanyar daya samu?, k'ilama 6arawon gwamnatine.
Kiyi hak'uri mama ALLAH ya huci zuciyarki, abinda zaki duba wannan kud'i ba hakkina bane, koma tayaya maisu yasamesu wannan shiyya d'aukarma Kansa kaya, inada damar maida masa kud'insa, to aii gara na maida domin ubangijinafa da barci ko gyangyad'i baya d'aukarsa yana kallona, kuma baya yafe hak'k'in wani akan wani face kanemi gafarar Wanda ka zalunta, tonikuwa mizaisani butulcema ni'imar da mahalliccina yay mini? na tsarkakakkiyar zuciya.
Mik'ewa mama tayi a fusace tafice tanata masifa.
Umar ya girgiza Kansa tareda sauke zazzafan huci, afili ya ce, " mama ALLAH ya shiryeki.

Niko bilyn Abdul sai na ce, "ameen ya UmarπŸ€·πŸ½β€β™€.

Koda Umar yagama shirinsa yanufi d'akin mama Dan mata sallama kamar yanda ya saba.
Da sallama yashiga falon, babu kowa sai Mufida da Rafi'a dake break fast kowanne sanye cikin kayan makaranta na gwamnati.
Gaisheshi sukayi, ya amsa yana tambayar ina mama?.
Mufida ta ce, "tafita makwafta yaya.
Makwafta kuma?, yanzu da sanyin safiyarnan?.
Shiru sukayi basuce komaiba, ya ce, " to kutashi mutafi idan kun gama?.
Rafi'a ta ce, "yaya bazakayi kari ba yau?.
A'a Rafi'a yau ina saurine, kudai kutashi muwuce, to suka fad'a suna mik'ewa, kowa yad'auki jakarsa ta makaranta suka fice.
Atsakar gida suka gamuda kawu, Umar yadurk'usa har k'asa yana gaida shi, Abba ina kwana.
Lfy lau Umaru anfito?, eh Abba mun fito, to wannan akwatinfa haka?, Abba wlhy wanine ya mantashi jiya dana d'akkoshi shine zanje na mayar masa, tofa yo kai Umaru banda abinka aii wannan tsintuwace, karik'e abinka kawai mana, nasandai bai wuce kaya bane aciki?, murmushi Umar yayi yanamai jinjina halin iyayen nasu aransa, ya ce, " karka damu abba nasan gidansa zankai masa dan takardune aciku, aikin 6ur inji tusa, a'a jeka kakaimasa abinsa, mizakayi dawasu tarkacen takardu dadai kud'ine ko kaya saika rik'e, nanma murmushi kawai Umar yayi harsu Mufida na tayashi.
Rafi'a da Mufida ma suka gaidashi, suma amsawa yayi cikeda fara'a.
Sallama sukai masa sannan suka fice, wajen adaidaitarsa sukaje, saida ya goge sannan suka shiga, makaranta yafara saukesu daganan yanufi gyad'i-gyad'i.
Da gyar ya iya gane layin, yatsaya adaidai inda yasauke dattijon Alhaji, gidan dayaga alhajin yashiga yake kallo, shi saima yanzu yaga gidan sosai, katafaren gidane na mai jida 'yan canji, komakaho yashafa katangar gidan yasan mai gidan ya shahara kuma yagama jik'ewa da data.
Yad'an dad'e atsaye yana tunanin yanda zai shiga gidan, baigama tunaniba yaga an wangale k'aton gate d'in gidan, wata dalleliyar motace tafito bak'a wulik sai d'aukar ido takeyi, k'arfin hali Umar yayi yamatsa kusada motar yana d'aga masa hannu.
Ahankali aka sauke bak'in Gila's d'in motar, wani matashin saurayi dabaifi sa'an Umarba ya bayyana.
Umar ya ce, "sorry Dan ALLAH inada tambayane?.
Inajinka saurayin yafad'a cikeda isa.
Umar ya ce, " jiya nakawo wani dattijo gidannan, to bayan mun rabu sainaga yayi mantuwa Dan haka nakawo masa abinda ya manta d'in.
Saurayi ya kashe motarsa sannan yacema Umar ya kamannin dattijon yake?, danshi ko kad'an baikawo dad d'insu bane.
Lissafa masa Umar yashigayi, cikeda mamaki Saurayin ya ce, "my dad, tomiya kaishi hawa adaidaita sahu?, bud'e motarsa yayi yafito, ya ce, " to muje cikidai.
Umar yad'auki d'an akwatin suka shiga cikin gidan, saurayi na baya Umar nabinsa abaya............








*_(((S)).....2017_*
*_Luv you all_*😻🀝.
[11/22/2017, 1:24 PM] ~πŸ‡© ' πŸ‡― πŸ‡¦ πŸ‡· πŸ‡­βœ: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’».........



πŸ’Ž *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*πŸ’Ž


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAIπŸ‘ŒπŸΌ WRITER ASSO........😜_*

*_page→9-10_*

.........Wata had'ad'diyar k'ofar Gila's suka nufa, saurayin ya danna wani abu k'ofar tabud'e da kanta, Umar dai yanadaga baya yana kallon ikon ALLAH.
Bayan k'ofar tabud'e suka shiga k'aton falon dayagama k'awatuwa da kayan alatu, gurin zama saurayin ya nunama Umar sannan yashiga cikin gidan domin Neman iso.
Umar na zaune yanata Rarraba idanu tsakanin falon da kayan dasuke ciki saurayin yadawo.
Bismillah yafad'a yana nunama Umar hanya, mik'ewa yayi yad'auki jakar suka tafi, gaba da gabanta Umar yafad'a aransa yayinda suka shiga falo na biyu, saiyagama falon farko Ashe bai had'uba, yayinda suka shiga na Uku sai kan Umar yakusa kwancewa Dan maganama ta gagaresa, benen dake tsakkiyar falon suka hau anankam Umar yakasa daurewa saida ya ce, "masha ALLAH, falone nafad'a aji Wanda koda saga binnin sin kazo dolene ka yaba, nanma gurin zama ya nunama Umar.
Umar yazauna kad'an akujerar tamkar bayaso, sai 'yan kalle-kalle yakeyi.
Woow!!...... Yaji wata zazzak'ar murya yafad'a.
d'ago fararen idanunsa yayi ya sauke akan k'yak'yk'yawar fuskar mamallakiyar muryar, ya sauke numfashi ahankali tareda kauda idonsa akanta Dan itama nata icon nakansa kam ko k'yaftawa batayi.
Batasamu damar yin maganaba dad da Safwan suka fito.
Umar yamike domin nuna girmamawa ga dattijon, dattijo yay dariya tareda fad'in a'a saurayi kaine?.
Nine Alhaji, Umar yafad'a cikeda girmamawa.
Bismillah zauna mana, zama Umar yayi ak'asa, Alhaji ya ce, " a'a tashi ka koma saman kijera mana, nanma yayi wlhy Alhaji ngd.
Daganan Umar ya gaida Alhaji, cikin fara'a ya amsa masa, Umar yad'ora da fad'in Alhaji dama mantuwar sannan kayi, to jiyan naso dawowa na maida maka saikuma naga dare yayi shiyyasa nabari sai yau.
Tunda Alhaji yay tozali da akwatin kud'insa sai mamaki da al'ajabi ya lullu6esa, damage akwai sauran mutane nagari aduniya irin Umar?, Alhaji yajawo akwatinsa gabansa yabud'e, kud'insa na nan yanda ya shiryasu, yad'ago yana kallon Umar cikeda mamaki, Safwan ma dai kallon Umar yakeyi, hakama budurwarnan tad'azun.
Ajiyar zuciya Alhaji yasauke tareda fad'in yaron kirki kenan, nunama rasa abin fad'a saboda lunbin mamaki daya cikani, yaro yaya sunankane?.
Umar Fharuk!.
Masha ALLAH Umar Fharuk mai gaskiya da rik'on amana, lallai kadace da k'yak'yk'yawar zuciya maicikeda alkairi, ALLAH yasa kad'ore haka har karshen rayuwarka, wlhy bammasan namanta jakarnan awajenka ba, amma saboda adalcinka ka kawomini, kila dasai natashi amfani dakud'in naita bulayin Neman, kaidai ALLAH yayi maka albarka.
Gaba d'aya suka amsa da ameen har mom da Suhaima dake fitowa yanzun, Safwan yamik'ama Umar hannu sukayi musabaha sannan ya ce, "d'an uwa munfa gode sosai, nizan wuce abujane lokaci NATA tafiya, To ALLAH yatsare Nina ngd sosai.
Safwan yayma iyayrnsa da k'annensa sallama harya kama k'arfen bene zai sauka budurwar d'azu ta ce, " ya Safwan Dan ALLAH karma manta da sak'ona wajen Fidoo.
Karki damu baby zan fad'a mata insha ALLAH.
hannu tad'aga masa tana murmushi harya sauna.
Umar ya ce, "zaitafi wajen aiki, harya mik'e Alhaji ya ce, " Hana Umar Fharuk koma ka zauna aii alkairi dank'one baya fad'uwa k'asa banza, baby kusa kuku yashirya mana break fast.
To dad, Budurwar d'azu wadda suke kira baby ta amsa.
Babu yanda zaiyi dole yahak'ura ya zauna har aka gama shirya had'ad'd'en break fast a dinning.
d'unguma sukayi gaba d'aya zuwa dinning, Umar dukaya takura, musamman akan kallon k'urullah da baby ketamasa tun d'azun, dasun had'a ido saita sakar masa k'ayataccen murmushi, adaddafedai yakammala break d'in yamik'e, Alhaji yakama hannunsa har falonsa dashima ya amsa sunansa dankuwa komai yaji tamkar baza'a mutuba, zaunar dashi Alhaji yayi akan luntsumemiyar kujerar ta alfarma sannan shima ya zauna, idonsa akan Umar ya ce, "Umar Faharuk kayi karatu?.
Eh Alhaji nayi.
Wane mataki ka taka?.
Nahad'a degree d'ina Alhaji harda bautar k'asa.
Masha ALLAHU, ammafa kabirgeni wlhy, awannan zamanin bokowane matashine kamarka zai kammala karatun Degree ba yadawo tuk'a adaidaita sahu, Dan aganinsu hakan zubar da girmane, kuma bahaka baneba.
Umar dai kansa na k'asa yana murmushin jin dad'i.
Alhaji ya ce, " to yanzu insha ALLAHU zan taimakeka domin nima ka taimakeni taimakon dabazan ta6a mantawa dakaiba atarihin rayuwata, idan kanason aiki kakawo takardunka zan nema maka, idan kuma kasuwanci kakeso wannan mai sauk'ine daga gobe ma zaka fara insha ALLAHU?.
Wani dad'ine yatsarga zuciyar Umar, yad'ago yana kallon Alhaji, zamowa yayi k'asa ya tsigunna yana masa godiya, Alhaji yakamashi yamaida saman kujera yana fad'in karma damu Umar kaima kazama d'ana aii, yanzu wanne kaza6a?.
Alhaji naza6i kasuwanci Dan dama shine burina, nayi karatune Dan kare mutuncin kaina amma badan aikiba.
To Alhamdllh naji fad'in za6inka nima sosai, Alhaji yamik'e yana fad'in jirani ina zuwa.
Babu dad'ewa yafito, yazauna kusada Umar tareda mik'a masa makullin mota, Umar ga wannan tukuycin alkairinka gareni.
Idanu Umar yazaro bakinsa na rawa ya ce, "baba motacrfa?.
Dariya Alhaji yayi ya ce, " nasani Umar motace tana nan aharabar gidannan, zansa direba yakaimaka har gida, idankuma zaka d'auka da kankane babu laifi.
Hawayen farinciki Umar yakeyi, ya ce, "baba dakabarsa, wlhy ban kawo maka jakarnan danka sakamin dawani abuba, namaido maka da itane saboda tsoron ALLAH da cin hak'in saba nawaba.
Alhaji yakamo hannun Umar yasaka masa key d'in Hana fad'in nasani Umar, nima namakane badan na biyakaba aii.
Godiya sosai Umar yayma alhaji sannan yafito.
Afalo yatarar da baby da Suhaima, suna ganinsa baby tamik'e tsaye cikin fara'a ta ce, "ya Umar kafito?.
d'an murmushi yamata tareda jinjina Kansas.
Takashe masa ido d'aya tana wani far da idanu, tobara namaka rakkiya ko.
Baice komaiba Dan tafara gundurarsa, kusan at are suka sauka, ganin haka yasaka Suhaima bin bayansu da sauri danson ganin abinda zai faru.
Har wajen gate suka rakoshi, yashiga a adaidaitarsa yatada, baki Suhaima ta ta6e afili tace kambu tak'ashinnan, yanzunan duk had'uwar bawan ALLAHn Nan a adaidaita sahu yazo?.
Hararta Baby tayi sannan tak'arasa kusada Umar dake k'ok'arin tafiya, ta ce, " ya Umar mungodefa sosai, inafata zaka cigaba da ziyartarmu Dan sada zuminci?.
Kallonta kawai yayi baice komaiba ya kauda kai.
Murmushi tayi azuciyarta ta ce, "ka cancanta my guy, afili kuma ta ce, " I Love you so much.πŸ’‹
Da sauri Umar yad'ago yakalleta amma tuni harta bar wajen ta isa inda Suhaima ke tsaye tana kallonsu.
Kasa tafiya yayi yatsaya binsu da kallo, harsaida suka isa gate sannan Baby tajuyo ta kanne masa ido d'aya tashige cikin.
Wata sassanyar ajiyar zuciya yasauke sannan yakuma tada baburd'in yafice daga anguwar cikeda farin ciki.
Tunanima yake wayakamata yafara fad'ama albishir d'innan, su mama ko inna ko Anty Sa'a?, baisan dawa zai faraba.
Daga k'arshedai ya yanke shawarar fara zuwa gidan inna, dankoba komai itace ta k'arfafa masa hayar adaidaita sahun, togashi tasilar hakan yayi gamon katar da tarin alkairi, kunga kuwa aii ita yafi cancanta tafara sani ko?.πŸ€·πŸ½β€β™€
Kai tsaye gidan inna yanufa kuwa........








*_(((S)))........2017_*
*_Luv you all_*
[11/23/2017, 4:57 PM] ~πŸ‡© ' πŸ‡― πŸ‡¦ πŸ‡· πŸ‡­βœ: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’».........



πŸ’Ž *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*πŸ’Ž


*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*


*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_


*_NIKA'DAIπŸ‘ŒπŸΌ WRITER ASSO......😜_*

*_page→11-12_*

........Tun'a k'ofar gida yaci karo da abinda yasaka farincikinsa rauni, wato ganin Asma'u da wani saurayin ranar, Asma'u na ganinsa ta 6ata fuska Dan gudun karya k'ara bata kunya kamar ranar, abisa tsautsayi suka had'a ido, yamaka mata wata uwar harara.
Kauda kanta tayi daga kallonsa, saurayin na gaisheshi amma ko kallon bai isheshiba yashige cikin gidan.
Asma'u tarakashi da harara.
Saurayin ya ce, "Asmy wanene wancan kuma?, nagafa sai hararmu yakeyi?.
Baki Asma'u ta ta6e ta ce, " yayanmune.
Kai Asmy shine baki fad'aminba na gaisheshi da k'yau?.
Uhmm kaga Zayyan share batunsa kawai, yanzu yaushene zaka dawo a tafiyar?.
Uhmm insha ALLAHU bazan wuce 2year's ba zan dawo.
Kai kana nufin bayan mun kammala s,s,c,e fa kenan?.
Eh hakane my Asmy, amma kiyi hak'uri nima Bahaka nasoba wlhy, kinsan karatunane yakawo haka, kuma umarnin Abba ne babu yanda na iya.
Shikenan ALLAH yatsaremin kai, yasa kaje a sa'a kadawo a sa'a.
To ameen my Asmy, shiyyasa nake k'ara sonki da k'yaunarki akowacce dak'ik'a ta rayuwata.
Murmushi Asma'u tayi, tareda fad'in nima ina sonka sosai zayyan, tayi maganar tana rufe fuskarta da hijjabi.
Dariya zayyan yayi yace Asmy sarkin kunya kenan......

A6angaren ya Umar kuwa ransa a6ace yashiga gidan, inna data fito daga d'akin baba mahaifinsu Asma'u ta ce, "a'a Umaru kaine agidan?.
Murya acinkushe ya ce, " nine Inna, sannu.
Yauwa Umaru, amma yanaga kamar Ranka a6ace yake?.
Da sauri ya saisaita nutsuwarsa, shikansa yana mamakin yanda baya iya 6oye Bacin ransa idan yaga Asma'u da saurayi, kuma aii hakan bata faruwa akan Mufida kosu fatee, wata zuciya ta ce, "aigara Mufida tayi girma tunda tana 100L a jami'a, amma Asma'u fa SS 1 take a secondary........
Innace ta ta6ashi, firgigit yadawo daga duniyar tunani, ta ce, " tunaninmi kuma kakeyi Umaru?.
Cikin inda-inda ya ce, "babu komai Inna wani albishir Nazo miki dashi, amma mi Asma'u yakeyi awaje da safennan?, mima yahanata zuwa makaranta.
Dariyace taso kufcema Inna saboda hango kishi k'uru-k'uru a idanun Umar, amma saita dake tace kasan suna Exam, toyau basuda ita shiyyasa, wancan kuma Zayyanne wai zaiyi tafiyane shine yazo suyi sallama.
Kansa kawai yagyad'a amma bai iya cewa komaiba yamik'e yana fad'in bara nagaida baba.
To kashiga yana ciki.
Ak'ofar d'aki yayi sallama, saida aka bashi izinin Shiga sannan yashiga.
Baba na zaune yana karin kumallo Umar yashiga, cikeda fara'a yataresa, Fharuku kaine agidan namu?.
Nine baba ina kwana?.
Lfy lau Umar ya hidimomin duniya?.
Alhmdllh baba.
To masha ALLAHU, kaga matso muci abinci ko?.
A'a wlhy baba nakarya nikam.
Kai Umaru karfa filako kakeyi?, a'a baba yazanyi filako agidanmu, nak'oshine kawai, to shikenan, yawajensu Maman taku?, lfy lau suke baba sunama gaisheku, a muna amsawa wlhy.
Umar yamik'e to baba bara naje mugaisa da Inna natafi wajen nema.
To Umaru ALLAH yabada sa'a kaji, ayitadai hak'uri da yanayin rayuwa, duk Wanda kaga yayi hak'uri baici ribaba to d'an kad'an yayi, duk abinda ALLAH ya albarkaci mutum dashi karya raina yace Alhmdllh, to insha ALLAHU ALLAH zaibasa mafiyinsa agaba kajiko?.
To baba ngd sosai, ALLAH yak'ara yawancin kwana.
Ameen Umaru ALLAH yayi albarka kuma.
Amen summa ameen baba, naira 500 ya ajiyema baba, baba ga wannan asha fura.
Kai a'a Umaru zoka d'auki kud'inka kaji, nikam bazan kar6aba, airik'e kankuma dakukeyi abin alfahirinmune basai kumbamu ko sisiba.
Hhh baba Dan ALLAH ka kar6a kasamusu albarka, nima banisu akayi.
To shikenan Umaru ALLAH yak'ara bud'i na alkairi ngd sosai.
Babu komai baba Umar yafad'a yana ficewa daga d'akin.
d'akin Inna yashiga, azaune yatadda ita tana jiransa, yasamu waje yazauna suka k'ara gaisawa da tambayar lfyar juna.
Alhmdllh Inna sai godiyar ALLAH.
To aii haka akesonji Umaru, wanekuma albishir aka kawo mini?.
Murmushi yayi tareda gyara zama yazayyane mata komai tundaga jiya har safiyar yau.
Farinciki sosai Inna ta Nuna harda kukan dad'i, tashi tayi tagad'oma baba shima yayi farinciki sosai, har d'akin inna yashigo yataya Umar murna da wanan k'yauta.
Suna cikin farincikinsu saiga Asma'u tadawo hannunta d'auke da Leda.
Itadai kallonsu kawai takeyi, data kasa jurewa saita ce inna wai miya farune kuketa murna haka?.
Inna ta zayyane mata komai, itama sosai tanuna farincikinta akai, ya Umar kam sai antaya mata haarar yakeyi, ko a jikinta wai antsikari kakkausa.
Bayan sun gama murnar yatashi yatafi akan zaidawo gobe yanuna musu motar.
To d'an Albarka, ALLAH yayi albarka kaji.
Ameen inna saina dawo.........

Daganan sai gidan Anty sa'a, ita kad'ai yatarrar agidan Dan yara suntafi makaranta, tamik'e da k'yar saboda tsohon cikin dake jikinta, oh ni Umar dama kana duniya?.
Dariya yayi ya ce, "Anty Sa'a ina zanje?, hidimomine kawai sukaimin yawa.
Haka kuka iya kullum kaida Abubakar da Harris bakwa rasa uzuri aii.
Tab Anty aii garani da wad'annan, kema kinsan ina k'ok'arin zuwa wajenki fiye dakowa agidanmu.
Eh to hakane kuma, amma aii kaima wani lokacin saika 6ace 6at.
'Yar dariya yayi ya ce, " hakadai kikace Anty sa'a.
Oh hakama zakace?, Anty sa'a tafad'a tana fita daga falon.
Babu dad'ewa tadawo d'aukeda tire shak'e da kayan ciye-ciye.
Da sauri Ya Umar yamik'e yatarota, kai Anty yakamata ki saukema kanji irin wad'annan aiyukan, ai kinyi nauyi dayawa.
Zama tayi da dabara, shima ya ajiye tiren sannan ya zauna.
Ta ce, "k'anina yazanyi, aii dole natashi nayima kaina, 'Yar mai aikin dake taimakamin kakarta tarasu taje gida tun shekaranjiya, jabeer da Laila kuma mizasu iyamin inbanda su 6ata.
To da wannan Dan wannan kuma, amma gsky mata kuna bani tausayi matuk'a, koda rainon cikinnan kad'ai akabarku aiba k'aramin k'ok'ari kukayiba, balle ga haihuwa, raino, tarbiyya dukfa suna kanku, kai ALLAH yasaka muku da aljannadai.
Amin d'an k'anina, Anty sa'a tafad'a tana dariya.
Shima dariyar yayi yana kai kofin zo6o bakinsa, saida yasha sosai saboda k'aunarsa da zo6o sanan ya ce, "big

Please Login or Register in order to submit comment