Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta nufi sashen Baba Abubakar fuuuu tana tafe tana surfa faɗa kamar za ta ari baki. Ko sallama bata yi ba ta doka ƙofar ɗakin tana faɗin, "Daddyn yara wai yaushe ka zama haka ban sani ba? Waye ya haifamin su Nabila da za ka kwashe mini su ka kaisu gidan su Fauziyya, na lura zaman lafiya ne baka so amma wallahi a wannan karon zan nuna maka ɓacin raina." Sai da ta kammala ya juya ya kalle ta ya ce: "Na ji kin ce ba za ki koma Ɗangwauro ba shi ya sa na kwashe yarana na kaisu gidan ɗan'uwana, domin da kai da kaya duk mallakar wuya ne." Taku biyu ya yi ya buɗe durowar kayansa ya zaro wata doguwar takarda ya ɗora mata akan gado yana faɗin, "Don haka na yanke wannan hukunci ina ganin zai fi zama masalaha, ki tattare kayanki wuri ɗaya saboda gobe zan turo a ƙarasa kwashe kayan gidan nan." Yana gama maganar ya fara ɗaura agogon hannunsa, ya ci gaba da harkar gabansa kamar ma bai san da mutum a wurin ba.

Tuni jikin Hajiya Nafisa ya yi sanyi idanunta suka ciko da ƙwalla ta kasa ɗaga ido ta kalle shi ta ce, "Daddyn yara sakina ka yi saboda abin da bai taka kara ya karya ba?" Turare ya fesa a jiki sannan ya ɗauki wayoyinsa zai fita ta sha gabansa ta ci gaba da cewa, "Wallahi indai akan maganar auren Aseem ne bana ɗar ko dana-sanin hukuncin da ka yanke, tabbas na yadda Namiji ƙudan zuma ne (Littafin Maman Islam ne, ku neme shi don jin yanda labarinta yake mai tafe da ɗaukan darasi.) Na yarda duk yadda mace ta kai da shekaru a gidan aure, dole akwai shafin da namiji zai iya buɗe mata ba tare da inkiya ba. Na gode sosai da wannan son zuciya da kuka nuna min." Hawaye ne ya ci ƙarfinta ta kasa ƙarasa maganar bakinta.

Murmushi ya yi da jin kalamanta saboda ya san dama muddin ta yi tozali da takardar da ya ajiye mata abin da za ta kawo kenan, shi kuwa gani yake wane laifi za ta aikata masa wanda zai saka mata da hukuncin saki? Matar da ta aure shi tun yana malamin makarantar firamare har Allah ya ɗaga dajarasa ya zama babban malami a makaran jami'a. Yana tsaka da tunani ya ji ta ci gaba da cewa:

"Kai namiji ne ba lallai ka fahimci ɗacin abin da nake ji na mahaifiya ba, ace ina matsayin mahaifiyar Aseem a yi masa mata ba tare da sanina ba har sai bikin ya rage ƴan kwanaki. An ce za mu koma ƙauye rayuwar ƴaƴana za ta nakasta, duk wannan bai isa ba har sai da ka raba ni da ƴaƴana me ya sa ahalinku suka fiye san kansu ne?" Maganganunta sun taɓa shi sosai kuma tabbas kowacce mahaifiya ba za ta so abin da aka yi mata ba, amma hakan shi ne mafita tun da shima yana yi ne domin biyayya ga mahaifiyarsa. Tana shirin sake magana ya ɗaga mata hannu tare da cewa, "Maganar auren Aseem fatan alheri za ki yi masa, domin bakinki kamar yankan wuƙa yake idan kika aibanta auren ba Dubu kawai kika yi wa ba, bakinki zai iya faɗawa har kan zuri'ar da za su haifa." Yana gama maganar ya fice daga ɗakin. Sai da ta zauna ta ci kuka ta godewa Allah sannan ta ɗauki takarda ta wuce ɗakinta, ta fara haɗa kaya sannan ta wuce unguwar Ɗorayi gidan mahaifiyarta.

Duk abin da ka ga bai zo ba sai dai idan ba a ƙayyade masa lokaci ba, ranar juma'a iyalan Yaya babba suka tarkato gabaɗaya suka koma sabon muhallinsu da ke cikin gidan Marigayi mai carbi. Hajiya Fauziyya ban da cika da batse babu abin da take yi, duk yanda ta kai ga biye-biyen malamanta akan komensu gidan abin ya faskara, sai dai ta ci alwashin sai ta gasawa Yaya babba aya a hannu cikin kisan mummuƙe ta yanda babu wanda zai gano ta. Hajiya Rahama dama macece mai sauƙin kai, tuni suka shirya da mijinta ta fauwalawa Allah lamuranta tare da neman alkairin komawar tasu. Sauran surukan cikin gidan murna a wurin abin baya musaltuwa saɓanin ƴaƴan Baba Abubakar da Baba Adamu da suke jin su kamar waɗanda suka koma rayuwar ƙunci. Yaya babba bakinta har kunne har wani annushuwa take ji da farinciki ganin kan zuri'ar Mai carbi ta haɗu wuri ɗaya.

Wannan kenan!

Aseem ya shiga cikin matsananciyar damuwa, har wata ƴar rama ya yi sai dogon wuya, fuskarsa ta yi fayau. Kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci rashin kwanciyar hankali ya samu matsuguni a jikinsa. Ko sati ba a rufa ba aka yi masa canjin aiki shi da Nasir, Nasir aka kai shi Kaduna shi kuma Aseem a ka kai shi garin Kano. Abin da ya daɗe yana so ne ya samu amma kuma wannan canjin aiki ya zo masa lokacin da baya buƙatar zamansa a kusa da gida. Amma babu yanda ya iya haka suka haɗa kayansa kowa ya koma wurin da aka yi posting ɗinsa.

Hajiya Nafisa tun da ta koma gida ta sanarwa da Mahaifiyarta abin da yake faruwa, da farko mahaifiyarta ta ji zafin Baba Abubakar amma daga baya ta riƙa nunawa ƴarta kuskurenta amma da yake idonta ya rufe, sai dai ta bi da Mahaifiyarta ta yanda take yi mata faɗa. Ƙanin mahaifiyarta Malam Mudam ne ya je gidan ake sanar masa da abin da ya faru, shi kansa ya ji haushin abin da ya faru don haka ya dubi Hajiya Nafisa ya ce, "Ke Nafisa saki nawa ya yi miki? Idan da kome zan nemi Abubakar ɗin mu yi magana. Ita rayuwa ai ƴar haƙuri ce, tun da ƙuruciya ba a yi wannan shashancin ba sai yanzu da girma ya zo." Hajiya Nafisa ta ɓata fuska ta ce, "Kawu ka barshi kawai ai sai ya ga kamar gajiya na yi da zaman nan ɗin." Daƙuwa ya yi mata da hannu ya ce, "Wannan sakarcin banza ne ai, duk abinki ke da Abubakar kun zama ɗaya." Hajiya Nafisa ta ce, "Ai ni tun da na sa takardar da ya bani a jaka ban ƙara bi ta kanta ba, tun da haka ya ga ya fi ai shi kenan." Ba don ta so ba haka ƙanin mahaifiyar tata ya tilas mata ɗauko takardar, tana buɗewa kunyar duniya ta isheta. Babbar takarda ce sai kuma ƙanana guda biyu da basu kai ta farkon girma ba, sai kuma cheque ɗin kuɗi a tsakiya. Takardar farko rubutu ya yi mata kamar haka:

"A kodayaushe ina gaya miki girma ya riga da ya kama mu, tsayawa kace-nace bai da amfani. A lokuta da dama abin da muke ƙi shi ne mafi alheri a gare mu, don haka Manzon Allah (S.A.W) ya ce, "Kada a tsananta soyayya kuma kada a tsananta ƙiyayya." Bakin uwa na da matuƙar tasiri akan ƴaƴanta don haka ki yi wa Aseem fatan alheri, shi ne abin da ya fi alheri. Ni Abubakar ina ƙaunarki fiye da tunanin mai tunani, don haka idan na sake jin kalmar rabuwa a bakinki sai na hukuntaki da hukunci mai tsanani." Takarda ta biyu kuma gabaɗaya kalaman soyayya ne dattijon mijin nata ya cika mata da su, sai cheque ɗin kuɗi masu yawa da ya bata ya ce ta riƙe saboda sha'anin biki.

Lokacin da ta karanta wata irin soyayyar mijinta ta ji na ratsata, nan take ta sanarwa da Kawunta abin da yake faruwa. A take a wurin ya ɗaga waya ya kira Baba Abubakar ya sanar masa da abin da Hajiya Nafisa ta yi tare da sheda masa ya zo ya ɗauki matarsa a ranar nan take.

Bayan tariyarsu da kwana biyu Yaya Babba ta nemi ganin iyalan gidan gabaɗaya a sashenta ita da Inna Furai, kusan gabaɗaya iyalan gidan sun hallara, sai ƴan tsirarun da suke aiki a nesa da gida irinsu Aseem, da waɗanda suke fita fatauci garuruwa. A ƙalla iyalan da suke zaune a tsakar gudan sun haurewa mutum tamanin, kowanne yana zaune da matansa da ƴaƴansa sai Yaya babba da Inna furai da suke zaune akan wani dogon benci. Sanye suke da tamfarsu iri ɗaya tare da hijabinsu ruwan toka iri ɗaya kamar yanda suka suba tun farkon rayuwarsu a gidan marigayi.

Bayan buɗe taro da addu'a Inna furai ta fara da cewa, "Da farko za mu ce Allah ya jiƙan malam ya haskaka kabarinsa." Yaya babba ta saci kallonta a ɗan ƙufule don bata so ta yi mata katsalandam ba, gabaɗaya mutanen wurin suka amsa da, "Amin ya rabbi." Inna Furai da bata lura da irin kallon da Yaya babba take yi mata ba ta ci gaba da cewa, "Mun tara ku ne domin mu ƙara jan kunnenku domin gabaɗayanku babu yara a ciki, don haka babu wanda zai kawo mana zazzagar rashin ɗa'a a wurin nan."

Dubu da ke gefe ta yi karaf ta ce, "Inna yanzu Ma'azu da ake yi wa shayi shi ma ba yaro bane? Kin ga su Iro fa." Ta ƙarasa maganar tana nuna Iro da yake kan cinyar mahaifiyarsa yana shan mama. Ai kuwa kamar mai jira Hajiya Nafisa ta ce, "To zaƙin zaƙafere... Ke kaɗai ce mai bakin magana manya na magana za ki sa baki saboda rashin ɗa'a." Baba Abubakar ya ɗago ya kalli Hajiya Nafisa amma sai ta kalli wani wurin daban don ta san haka za ta iya faruwa. Dubu ta watsawa Hajiya Nafisa harara tana mata fari haɗe da murguɗa baki, Hajiya Nafisa ta cije baki cike da takaici. Dama a ƙule take saboda kiran da Yaya babba ta yi mata ba don san ranta ta je shi ba saboda ko kaɗan ba ta san haɗa inuwa da sauran facalolinta don gani take ba ƙaramin zubewar mutumci ba ne a wurinta. Matan Baba Abubakar ma don ta san babu abin da nata mijin ya fi na su shi ya sa bata cika kawo musu wargi ba.

Baba Abubakar ne ya yi magana hayaniyar da ke tashi ƙasa-ƙasa a wurin ta lafa, amma kallon yanda Hajiya Nafisa take duban Dubu za ka tabbatar da babu ɗigon ƙaunar sirukar tata a zuciyarta.

Inna Furai cike da ƙwarin gwiwa ta ci gaba da cewa, "Fatan mu dai ku zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya. Allah ya sani bama son tashin hankali da gutsiri-tsoma, gabaɗaya tushe ɗaya kuke sai a ɗorar da zazzagar zaman lafiya. Amma duk wacce ta kawo mana wargi alƙur'an mai hana mu zazzage albarkar da ke kanta sai Allah ko ba haka ba Yaya." Yaya babba murya can cikin ƙasan maƙoshi ta ce, "Wacce falsafa za ki tambaye ni Furaira? Meye nawa a ciki kuma bayan tun farko baki bani girma da darajata ba. Ƙwarakwatsa dubu ba don kar na baki kunya a gaban su Auwalu da Ado ba, babu abin da zai hana watsa miki falsafar rashin ɗa'a." Yaya babba muryarta ta fara rawa alamar za ta yi kuka, ta dubi Inna Furai ta ci gaba da cewa, "Alƙur'an ban taɓa sanin za ki yi ɗiban karen mahaukaciya da wasiyyar Malam ba. kaico! Rayuwar duniya." Inna Furai ta fara zuwa wuya don haka a ɗan hassale ta ce:

"Yanzu me ye ma ba ki yi mini ba, wacce irin albarka ce baki zazzage mini a tsakar ka ba." Sai kuma ta juya musu baya tana faɗin, "Allah ya sani Yaya kin zazzage mini kwandon ɗiban albarka." Yaya babba ta taɓe baki ta ce, "Ai kinsan dai ni ce babba a gidan, tun zuwanki gidan nan ni nake fara komai, amma ƙasa ta rufe idon Malam har kina neman kwara mini falsafar rashin mutumci." Inna Furai ta kusa kaiwa bango, a fusace ta miƙe za ta bar wurin tuni su Baba Munkaila suka fara sa baki ta zauna.

Inna Furai ta harari gefen Yaya babba ta ce, "Dama duk daɗinka da kishiya sai ta yi maka zazzagar rashin mutumci. To ni dai nan gani nan bari, kujera ce dola a zauna a kaina."

Wannan maganar ba ƙaramin ɓata ran Yaya babba ya yi, ai kuwa nan take ta fashe da kuka. Wurin shiru ya ɗauka ban da sautin kukan Yaya babba babu abin da yake tashi, Inna fura ta ɗauke kai gefe alamun ita ko a jikinta. Sai da Yaya babba ta yi mai isarta sannan ta fara leƙe-leƙe, daga can gefe ta hango Salisu, da ɗan yatsa ta nuna shi tana faɗin, "Salisu zo nan don girman Allah." Salisu na jin haka ya fara noƙewa don fatansa bai wuce, Yaya babba karta kunyata shi a gaban iyaye da sirikansa ba. Jin ya yi shiru ya sa Baba Sule ya yi masa magana jiki ba ƙwari ya fita ya je gefen Yaya babba ya russuna ya ce,

"Gani Inno."

Yaya babba ta ruƙo hannuna Salisu tana goge hawaye idonta, ta ce, "Allah shaida kaine shaidata Salisu, daga yau babu ni babu Furaira ko a lahira idan ta nuna ta sanni ban yafe ba." Tana rufe baki mutane wurin kamar haɗin baki suka ɗauki salati lokaci ɗaya. Yaya babba ta hango Sha'aban Jikan Inna Furai na huɗu shi ma ta ƙwala masa kira, yana zuwa ta riƙe hannunsa ta ci gaba da cewa, "Sha'aban na fasa wakilta Salisu saboda sam bai da ɗa'a bashi da kunya, Kaine shaida ko a gaban Ubangiji ka za ka shede ni." Salisu zuciyarsa fes har zai bar wurin Yaya babba ta fisgo ƙugunsa ta tana faɗin, "Dawo munafuki babu in da za ka dama da biyu na shirya zaman nan, saboda kai da yarinyar nan Zulfa. Amma dai Allah ya yi wa Soja albarka, yaron nan shi kaɗai yake da kawaici." Yaya babba ta mayar da kallonta wurin mutanen da ke zaune kowa ya zuba idanu suna jiran abin da za ta faɗa.

"Munkaila!" Ta ambaci sunan Baba Munkaila a hankali ya amsa don yana gudun kar a kwatanta ta kwanaki. Yaya babba ta ci gaba da cewa, "Kwarankwatsa dubu ka shawarta da ƴan uwa wallahi auren nan janyo shi za a yi; ku rufa mini asiri ku aurar da yaran nan na daina jin miyagun maganganun da kunnena suke ji, wai ma saura kwana nawa?" Baba Munkaila ya haɗiyi yawo cike da fargaba don har zuwa lokacin bai gama haɗa kuɗin kayan gadon Zulfa ba, shi kuma baya jin zai iya taɓa kiwonsa ko kaza ce ya sayar. A hankali ya ce, "Yau saura kwana goma sha takwas."

"To a rage kwanakin nan gaskiya, don na gaji da jin falsafar rashin ɗa'a a kunnena. Ina dalili ina zaune ƙalau a janyo mana fushin mala'iku har cikin gida. A'a don Allah ka rabani da faɗawa halaka, me ye haɗina da Jahannama ana zaune ƙalau? A'a wallahi ina daga sahun farkon masoyiya Manzon Allah (S.A.W)" Kowa dai ya yi shiru cikin zuƙutansu da irin wasiƙar da suke karantawa.

Yaya Babba bata damu ba ta ci gaba da cewa, "Ku gane mini shi don Allah wa zai ce Salisu halin yahudu gare shi? Maganganun da ya faɗa rannan a ɗakina alƙur'an da ƙyar bacci ya ɗauke ni." Baƙin cikin duniya ya cika Salisu, ban da harare-harare babu abin da yake yi.

"Wai har da I musu yu, don Allah ku ji kalmar arnanci kamar me kiran muzuru, ni Soja nake yi wa kallon ɓatacce mai halin Yahudawa ashe ina tare da shi a kusa ban sani ba" Hajiya Nafisa ta cika fam wannan kalmar na ƙona ranta idan ta ji Yaya babba na danganta jininta da yahudawa.

Cike da takaici Inna Furai ta juyo ta ce, "Yaya raba kanki da aibanta mini jika idan ba haka ba alƙur'an babu mai hanani zazzage miki albarka a ka." Yaya baba ta sakar mata harar mai ɗauke da manufar, ai ba ke kika haifar mini mahaifinsa ba. Sannan ta ɗora da cewa, "Furai wa ya haifar mini Uban Salisu a gidan nan?"

Inna Furai ta taɓe baki ta ce, "Yoo don kin haifi ubansa ni da Malam ya yi mini kyautar ubansa tun yana tsammafa." Yaya babba ta saki dariyar ta ce, "Yoo wa yake bin wasiyyar matacce, Malam dai ya mutu Allah ya jiƙansa amma ba wanda ya isa ya yi mini iko da jinina."

Inna Furai ta ɓata fuska har da huccinta, ta kalli Auwalu ta ce, "Auwalu Allah idan baka rakani ofishin human rai (Human right) ba kwarankwatsa mai hanani zazzagewa gidan nan albarka sai Allah. Allah ko ka rakani a bi mini haƙƙina ko ku neme ni ku rasa daga nan nida Indo shari'a har ƙashen duniya." A tsorace Yaya babba ta dafe ƙirji ta ce, "Furai yau ni kike ambata da Indo gatsal? Wallahi magana dai na yi kai Sha'aban ga ƙarin wata shaidar, kwarankwatsa dubu ko a lahira ka shaida abin da Furai ta yu mini, yoo ƙarya na yi masa ba da kunnena na ji watsewar kalaman yahudawa ba wai I musu yu (I miss you), abin da ko a mafarki ban taɓa ji Soja na faɗa ba dukda shi ma ina kokwanto akan tauhidinsa, yo me ake da aikin Soja na aikin kafirai masu busasshiyar zuciya. Allah ya sani Garba ka cuceni da ka sa mini Jika a harkar ɓata don..."

Sallamar Aseem ce ta katse Yaya babba daga jawabin da take yi.

Zuwansa kenan daga garin Lagos, ya shiga cikin gidan ya ga duk babu kowa don haka ya yanke shawara zuwa sashen su Yaya babba. Yaya babbb na ganinsa ta fashe da dariya tana faɗin, "Kun ga Ɗan'halak. Soja zo nan." Da mamaki ya fara bin mutanen wurin, yana mamakin abin da ya kawo su suka tattaru wuri ɗaya. Bai ankara ba ya ji muryar Yaya babba raɗau a kunnensa tana ci gaba da cewa.

"Soja ka dubi Allah da Annabi, ka san dai Sule bashi da wuta da aljanna bare idan ya ji ka faɗi gaskiya a kan Ɗansa Salisu ya babbakeka. Ka gaya mini meye I musu yu? Don wallahi ba zan juri zama cikin fushin Ubangiji ba?"


Shafi na biyun ƙarshe🤸🏻‍♀️💃🏼 daga shafin gobe an gama free pages ku yi hanzari ku fara biya kar a yi babu ku💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
*DUBU JIKAR MAI CARBI*


©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV

LAST FREE PAGES 13

Guntun tsaki Aseem ya ja ba tare da kowa ya fahimce shi ba, yana daga wurin da yake ya ce, "Inno lafiya kuwa na ga mutanen gidan sun taru?" Ya yi maganar fuska a tamke don ba ya son ta sake jefa masa wata maganar, saboda gabaɗaya ransa a dagule yake. Bai rufe baki ba idanun mutanen wurin suka sauka a kansa, yadda ka san sun ga sabuwar hallita haka suka zura masa idanu. Dubu kuwa sai kallonsa take tana yashe baki, musamman da ta tuna irin huɗubar da Yaya babba ta yi mata akan kissa da kisisina, wai murmushi ma yana daga cikin abin da yake sace zuciyar namiji. Don haka Dubu ta zage ta riƙa yashe haƙora tana kallon saitin wurin da Aseem yake, har sake miƙa wuya gaba take don ya fi hangota a kan sauran mutanen wurin.

Yaya Babba na jin kalaman Aseem ta ɗan ɓata fuska ta ce, "Tsiya ta da kai kenan Soja. Don Allah ka ƙaraso ka taya ni jin wannan lamarin ko so kake na ji ni kaɗai?" A hankali ya fara takawa yana saƙale da jakar goyonsa wacce kayan aikinsa suke ciki, sai kuma trollybag wacce ke ɗauke da sauran kayansa suke ciki. Ƙirjin Hafsa ban da lugude babu abin da yake yi, tana jin zuciyarta na wani iri kamar za ta faso ƙirjinta. Soyayyar Aseem na ci gaba da mamaye zuciyarta, a fakaice ta sunkuyar da kai ƙasa ta sharce hawaye ba tare da ta bari wani ya lura ba.

Aseem na ƙarasawa shi ma Yaya babba riƙo hannunsa tana faɗin, "Soja wai saura kwana nawa aurenku don Allah?" Nan take fuskar Aseem ta sake haɗewa ya ɗauke kai gefe ya ce, "Na manta." Ta yashe baki tana kallon mutanen wurin ta ce, "Kun ji abin da nake faɗa, alƙur'an Soja da ba kallon da bana yi maka don Allah ka gafarceni. Allah ya sani ko Garba ba zai nuna maka kunya ba, don shi ma da kake ganinsa a lokacin samartaka ƴanmatan da ya yi Allah ne kaɗai masani. Allah mai sarauta irin soyayya da Garba ya yi da Kandala da gidan nan na magana da ya shede ni, bana buƙatar shedar Furaira don ko a lahira na yanke zumunci da ita."

Aseem bakinsa sai motsi yake yana san ya yi magana amma yana gudun ta fito mara daɗi, yana shirin cire hannunsa daga jikin nata ya ji Inna Furai ta ce,

"Me ye naki na ambatar sunana kuma? Wallahi ko a aljannah sai na zazzage miki albarka a tsakar ka." Yaya babba bata bi ta kan Inna Furai ba ta ci gaba da cewa, "Amma dai har Garba ya auri uwarka wallahi ban taɓa jin kalmar Allah wadai a bakinsa ba, gaskiya ba da ni ba wannan falsafar dole a dakatar da ita, maganar gaskiya Shehu auren nan ranar juma'a mai zuwa za a ɗaura shi. A kai yaran nan ko ma huta; ina dalili laifinsu ya shafe mu, mu riƙa sallah ba a karɓa Mala'iku su yi fushi da mu." Ta ƙarasa maganar tana kallon wurin Baba Shehu.

Baba Shehu ya kwantar da murya ya fara cewa, "Inno da za a taimaka a bari lokacin nan ya zo, mun riga da mun buga katin gayyata duk mun aikawa mutane idan wani abin yaran nan suka yi bayan taro ya watse sai mu zauna a tattauna." Yaya Babba ta ƙura masa ido har ya gama sannan ta ce, "Dole ka nuna mini iyakata Shehu, ba sai ka faɗa ba dama ai ba ni na haifa muku su ba." Yaya babba ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka.

Wurin shiru ya ɗauka aka rasa mai bakin magana, Baba Aminu ya ɗago ya dubi mutanen wurin ya sallame su. Ɗaya bayan ɗaya haka suka fara wucewa suna barin wurin, dama Aseem da Salisu kamar a kan ƙaya suke tun Baba Aminu bai rufe baki ba suka wuce gaba.

Shiru wurin ya yi daga Yaya babba sai Inna Furai da sauran iyaye maza kowa yanayinsa ba daɗi. Baba Abubakar ya ƙarasa wurin Yaya babba ya ciro hankicif ɗinsa ya miƙa mata ya ce,

"Inno share hawayenki."

Yaya babba bata ɗago ta kalle shi ba ta ce, "Ka barni ya yi ta zuba idan ya ƙare na mutu kun huta ai." Murmushi suka yi don ta so basu dariya, ya juya wurin Inna Furai ya ce, "Inna don Allah ki sa baki ta tsaya mu yi magana." Inna Furai ta ɗauke gefe tana wurga masa harara ta ce,

"Wacce zazzagar kuke so na yi? Maganar gaskiya abin da Yaya ta faɗa yana hanya, wai me ye a ciki lamarin nan fa na gida ne kuma auren nan ko yau aka ɗaura shi akwai wanda zai ce don me?" Baba Abubakar ya yi shiru don ya lura gabaɗaya a rikice suke, Inna Furai ta ci gaba da cewa, "Ba zan hana Yaya ba saboda Allah ina dalili ana nuna muku Annabi kuna runtse ido." Yaya babba na jin haka ta sake rushewa da kuka. Sai da ta yi mai isarta ta miƙe za ta bar wurin, da sauri suka dakatar da ita sai da ƙyar suka shawo kan Yaya babba ta zauna. Amma duk yadda suka so a bar biki a lokacin da yake fir ita da Inna Furai suka ƙi amincewa. Babu yadda suka iya haka suka amince akan ɗaurin auren ranar juma'a mai zuwa wanda a lokacin gabaɗaya saura kwanan huɗu.

Tun a ranar su Baba Abubakar suka riƙa kiran mutane suna sanar da su janyo lokacin bikin, haka a cikin garin Ɗangwauro kafin wani lokaci tuni labarin ya karɗe ko'ina. Baƙin ciki a wurin Hajiya Nafisa har ya ƙi musaltuwa don ranar kwana suka yi suna yin babu daɗi ita da Maigidanta. Haka daga wurin Aseem ranar kusan kwana ya yi cikin

Please Login or Register in order to submit comment