You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
auren zumunci aka yi musu sakamakon Mahaifiyar Mai carbi ta nuna itama dole ya auri ƴar ƙaninta tun da ya auro ƴar ƙanwar Mahaifinsa. Wannan dalilin ya sa aka sake yi masa aure bayan yin aurensa da shekara biyu a lokacin Yaya Babba tana goyon Baba Abubakar.
Ƴaƴan Yaya babba Shida Maza biyar Mace ɗaya. Akwai: Baba Abubakar, Baba Munkaila, Baba Sule, Baba Shehu, Baba Aminu, Baba Adamu sai Hadiza. Inna Furai tana da ƴaƴa biyar akwai: Larai, Baba Sabi'u, Baba Musa, Baba Sha'aibu sai Baba Auwalu.
Gabaɗaya waɗannan ƴaƴayen kowanne yana da tashi zuri'ar, daga cikin waɗanda ba sa cikin gidan gandun, akwai Baba Abubakar Mazaunin unguwar Na'ibawa, kuma lakcara (Lectural) ne kwalejin Sa'adatu rimi. Sai Baba Adamu.
Baba Abubakar yana da mace ɗaya Hajiya Nafisa da yara Huɗu: Aseem, Nabila, Husna da Humaira. Aseem da Humaira sunan Mai carbi da Yaya babba suka ci amma ana kiran Humaira da Ummi. Baba Adamu yana zaune a unguwar Gyaɗi-gyaɗi likitane yana aiki a asibitin Aminu Kano. Yana da mata biyu Hajiya Rahama ita ce Uwar gida tana da ƴaƴa biyu Fahad da Fatima sai Hajiya Fauziyya mai ƴaƴa uku Halifa mai sunan Marigayi Mai carbi, Zainab sai Hafsa. Sai Hadiza da Larai da suke aure a wasu gidajen.
Tsayawa zayyano wannan ahalin Marugayi mai carbi ba ƙaramin ɓata lokacin mai karatu bane.
Dawowa Labari.
Kimanin sha biyun rana da ƴan mintuna, zaune yake a cikin motarsa yana ƴan danne-dannensa. Ya kai kimanin mintuna ashirin da faka motar amma yana ciki bai fito ba. Ɗaiɗaikun yara ne suka fara zagaye motar suna kallo wasu daga cikinsu har da masu shafawa. Tsirarin ƴan mata sa'annin Dubu har da masu kallon fuskarsu a jikin mudubin motar, ganin suna niyyar yi masa ɓarna ya sa ya zuge galashin motar. Wani sihirtaccen ƙamshi ne ya fito daga cikin motar nai sanyin ƙamshi. Ƙamshinsa ne ya ankarar da su akwai mutumin da ke cikin motar. Kallon su ya fara yi kowa ya shiga taitayinsa sakamakon ganin fuskarsa ko ɗigon murmushi babu. Mugun kallon da ya wurga musu ne ya sa kowacce daga cikinsu ta kama kanta, sum sum sum suka wuce. Gajiya ya fara yi da zaman motar sannu a hankali ya zuro ƙafarsa waje tare da fitowa ya jingina da jikin motar yana ƴan danne-danne a wayarsa. Kakin sojan ba ƙaramin ƙarɓarsa ya yi ba, ya yi kyau matuƙa ga wani kwarjini da yake da shi.
Kasancear mutanen ƙofar gidan sun watse sakamakon ruɗanin da yake faruwa wasu daga ciki kuma sun tafi asibiti wurin Inna Furai.
Lambar mahaifiyarsa ya kira sai da ta kusa katsewa sannan ta ɗauka. Kamar zai yi kuka ya fara yi mata magana: "Momma don Allah ki zo ki shigo da ni banga su Daddy ba kuma na san gidan cike yake da mutane..." Bai ƙarasa magana ba Baba Munkaila ya ƙarasa wurinsa yana washe baki ya ce, "Wa nake gani kamar Soja? Soja mazan fama saukar yaushe." Zame wayar ya yi yana sosa kai ya ce, "Yanzu na ƙaraso Baba."
"Bismillah mu je ciki mana" Baba Munkaila ya nuna masa hanya. Sai da ya kulle motar sannan suka ƙarasa cikin gida.
Dubu tun a hanya su Kaltume suka tare ta da zancen baƙon da suka yi. Hura hanci ta yi kanta na ƙara girma sannan ta ce, "Wani dogo mai mota baƙa? Yau ma da kayan sojoji yazo ko?" Har rige-rigen bata amsa suke sannan ta tallaɓi ƙwaryar tsakin da ta karɓo ta fara buɗa kafaɗa tana cewa, "Ai shi ya sa nake gaya muku duk shegen da ya kawo raini wallahi haɗa shi da Yaya Aseem zan yi ya ci ubansa. " Tana gama maganar ta yi gaba. Su kuwa kowa ya yi zuru-zuru don basa manta ranar da suka taɓa ganinsa da bindiga.
Dubu cike da ɗoki ta shiga gidan don ko ba komai so take ta riƙa ƙare masa kallo tana ayyana wai shi ma ɗan uwanta ne a matsayinsa na soja. Ita ba shi yake birgeta ba illa kakinsa na soja da sautari idan zai zo garin da su yake zuwa.
Kamar wacce aka wurga tana shiga gidan ta yi ciki da Nabila ai kuwa suka fara faɗa, juyawar da Dubu za ta yi a zafafe ta sheƙawa Aseem garin tsakin da ta karɓo daga injin niƙa. Sai ga Aseem da ke cikin unifom ɗin sojoji har da hankicin ɗin goge-goge ya fito furu-furu kamar wanda ya yi wanka da toka. Gashin kansa har wani tsinin farin garin masara ya yi.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[7/1, 5:59 PM] My Data sim number: *DUBU JIKAR MAI CARBI*
©AMEERA ADAM
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
FREE PAGE 6
https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels
Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.
Duk wannan abin da ya faru sam Dubu bata lura ba, masifa na cin ta bata san da ta sheƙa wa Aseem garin masara a jiki ba, sai ma uban tsalle da ta buga ta cukumi wuyan Nabila tana kai duka tana cewa: "Wallahi ba za ki daki banza, kwarankwasa dubu sai na koya miki hankali, hegiya tsigi-tsila da ƙafa kamar ta tsinken tsintsiya" Ganin ɗankwalin da ke kanta na niyyar kawo mata cikas ya sa ta fisge shi wurga shi ta baya sai kuwa ya sauka a kan fuskar Aseem, ban da tsami da bashi babu abin da yake tashi a cikinsa. Sai ga kitson kanta ya fito duk ya tuje hatta da tsagar kitson ta haɗe sai furu-furun amosani a saman kan.
Warin ɗankwalin ne ya doki fuskar Aseem har ya shaƙa da ƙofofin hancinsa ya sa shi farkowa daga suman tsayen da ya yi na wucin gadi. Aseem tun da ya zo duniya ba a taɓa yi masa abin da ya fusata shi lokaci ɗaya kamar abin da Dubu ta yi masa, dom shi abin daga haushi ma sai ya koma ba shi mamaki. Bakinciki da ganin yadda mutane suka zura masa ido ne ya ɓata masa rai har ya gagara sanin abin da zai aiwatar don ya wanke masa zuciya. Amma tabbas sai ya koya mata hankali don ya lura har lokacin Yaya babba ba ta ɗora ta a hanyar arziƙi ba.
Duk yanda Dubu ta so nunawa Nabila ƙarshen iyawarta abin ya ci tura don a girme Nabila ta girme ta da kusan shekara huɗu. Gudun kar a kunyatata cikin jama'a ya sa Dubu ta tattara ƙarfinta ta fara wani fisge-fisge kamar mai aljanu tana kai duka ta ko'ina, ai kuwa ta ɗaga ƙafa bisa taautsayi ta harbawa Aseem da ke saƙa da warwara akan irin abin da ya dace ya yi mata. A hassale ya ƙarasa wurinta cikin zafin nama ya fisgi hannunta. Cikin tsiwa da rashin sanin wa ya riƙe ta Dubu ta ce, "Wallahi duk wanda ya riƙe ni sai na yi masa jini da majina dalla ku sake ni wallahi ba za ta daki banza ba." Ai kuwa ya sauke mata mari a fuska, kafin wancen marin ya gama ratsa fuskarta ya sake kifa mata wani marin har sa da ta ga wasu irin taurari na gilma mata. A gigice Dubu ta buga tsalle cikin fitar hayyaci ta ce, "Innalillahi wayyo Baba Munkaila zai kashe ni wayyo! Inno fuskata."
Sauke hannun Aseem ya yi daidai da fitowar Yaya Babba za ta zagaya banɗaki. Da sauri ta saki butar hannunta ta fashe da kuka ta ƙarasa wurinsu, tana shirin riƙe hannun Dubu; Aseem ya sake fisgar Dubu ya nufi hanyar fita da ita. Duk irin kiran da Yaya Babba take yi masa ko waiwayenta bai yi ba bare ta saka ran zai tanka mata.
Duk yanda zuciyar Dubu take a bushe wannan karon sai da hanjin cikin ya kaɗa, tsoro ya mamaye ta musamman ta lura da irin ɓarin makauniyar da ta yi masa da garin masara. Suna zuwa soron ƙarshe ta yi ta maza ta fara ƙoƙarin fisge hannunta tana faɗin:
"Wai ina za ka kaini? Ka sakar mini hannu malam." Idanunsa sun kaɗa jawur saboda ɓacin rai don haka tambayar Dubu ba ƙaramin baƙanta masa rai ta ƙara yi ba. Bai tanka mata ba ya sake fusgarta da ƙarfin tsiya ya buɗe mota ya wurga ta sannan ya buɗe mazaunin direba ya zauna.
Ganin ya tuƙa mota da ya fice da gudun tsiya ya ƙara hargitsa hanjin ciki Dubu, don wannan karon har ta fara bubbuga gilashin motar tana ihu. Can gefen titi ya gangar ya faka motar sai dai uffan bai ce ba. Sai da ya share minti biyar a haka yana jin kukan da Dubu take yi da ɗan ƙarfinta, ya zaro ƴar ƙaramar bindiga ya juya yana ce mata.
"Idan baki rufe mini baki ba zan harbe ki na wurgar da banza a wurin nan." Wata ajiyar zuciya da Dubu ta sauke idan ka ji za ka yi tsammanin numfashinta na ƙarshe ne zai fita. Bata san lokacin da ta haɗiye kukanta ba, ban da raba idanu babu abin da take yi, haɗe da jin wata irin da-na-sanin zuwanta duniya. Saboda ta san da ba'a haifo ta ba babu wata ƙaddara da za ta haɗo ta shi har ya nemi kashe ta da bindiga murus ya wurgar a gefen hanya. Don tun da take bata taɓa ganin bindiga ido da ido ba sai dai ko idan tana daga moto ta hangota a hannun Sojoji ko ƴan sanda. Amma yau har ita ake yi wa iƙirarin harbewa da ita da rana tsaka. Tana son tambayarsa inda zai kaita amma tsoro ya hanata, tana cikin tunani ta ji ya sake fisgar motar da wani irin matsanancin gudu, ai kuwa ta ƙwalla uwar ƙara tare ta ƙanƙame jikin kujera.
A wannan yanayin suka ƙarasa gidan Mahaifinsa da ke unguwar Na'ibawa. Yana zuwa ya ciro mukulli ya buɗe gate ɗin gidan ya shiga da motar sannan ya buɗe murfin motar ya fisgi hannun Dubu, ai kuwa tana ganin zai shiga gidan da ita ta riƙe ƙofar gate ɗin gidan da sauri tana cewa.
"Wallahi ni ba ƴar iska ba ce da za ka kawo ni gidan nan." Maganarta ba ƙaramin dariya ta so bashi amma ya sake tamke fuska ya ce, "Ni ko ɗan iska ne an gaya miki zan yi iskanci da kucaka irinki?" Yana gama maganar ya sake fisgar hannunta aikuwa ta rungume wani ƙarfe tana cewa, "Kwarankwatsa dubu ba zan shiga ba, dama Inna ta ce ƴan iska ne suke bin maza." Tsugunnawa ya yi cikin ɓacin rai zai yi mata magana, ita kuwa Dubu tuni ta shagala da ƙarewa fuskarsa kallo don tun bayan fitowarsu ta lura da abin da yake jikinsa. Ai sai tsoro ya sake kamata saboda bata taɓa zaton haka garin masarar ya yi masara furfurar da bai shirya ba. Ta maza ya yi ya tsugunna a gabanta don wani tsami ne yake bugar hancinsa, saboda tun da aka yi rasuwa Dubu bata ƙara saka ruwa a jikinta ba. Dama wankanma sai Yaya babba ta yi da gaske take yi to rurumar jama'a ya sa ta basar ta ci gaba da harkokinta. Zaro bindigar aljihunsa ya yi ya ɗora mata akan goshinta nan take kuwa ƙirjin Dubu ya fara bugawa da ƙarfi, da hannu ya nuna mata ƙofa alamar ta shiga Dubu ta soma hawaye tana cewa, "Don Allah ka yi haƙuri idan saboda na zuba maka garin masara ne. Wallahi ban kana kusa ba."
Idan ka ji yanda Dubu take magana a ladabce za ka rantse da Allah mutuniyar kirki ce. Iya nadama Dubu ta shige ta don ta gama tsorata gabaɗaya, amma duk da haka bata jin za ta bi Aseem cikin gidan saboda ba za ta taɓa manta Baraka da ta yi ciki ba aka riƙa tsangwamarta ƙarshe sai sayar da gidansu Mahaifinta ya yi suka bar garin. Ita kuwa idan ta yi ciki ai ta san ko sama da ƙasa za ta haɗe babu wanda zai yarda a sayar da gidan Mai carbi.
"Idan kika bari na ƙirga uku ba ki tashi ba zan baki mamaki." Maganar Aseem ta farkar da ita daga dogon tunanin da ta tafi. Cikin hawaye Dubu ta ce, "Don Allah me za ka yi mini a ciki."
Banza ya yi mata yana buga bakin bindigar a ƙasa a hankali cikin sigar, idan baki tashi ba kin san sauran. Dubu bata yi ƙasa a gwiwa ba ta sake tambayarsa. Bai ɗago ya kalle ta ba ya ce, "Idan kin shiga kya gani."
"Wallahi ko me ka ce zan yi amma ni ba ƴar iska bace." Dubu ta faɗa lokacin da gumi da hawaye ya gama mamaye ilahirin fuskarta zuwa wuyanta.
"Ni ɗan iska ne." Ya bata amsa yana miƙewa a fusace ya fisgi hannun Dubu tana ihu tana fisge-fisge ya wuce da ita ciki. Yana shiga ya datse ƙofar ya wurgar da ita gefe sannan ya faɗa wani ɗaki da ke ɓarin hagu. Dukda gidan ba baƙon Dubu ba ne amma a wannan ranar gabaɗaya bata da nutsuwa. Bai jima da shiga ba ta ga ya fito da wani abu a hannunsa na dama, ɗayan hannun hagun kuma wata ƴar ƙaramar wuƙa ce, ai kuwa ta zabura kamar wacce aka ɗanawa wuta za ta gudu. Fuska a murtuke ya fisgi hannunta ya wuce da ita cikin banɗaki. A wannan karon Dubu duka ta fara kai masa tana cewa.
"Jama'a ku taimaka min zai yanka ni. Kuma ka rabu da ni na ce maka ni ba ƴar iska bace. Wallah idan ka kashe ni na rataya a wuyanka duk zunuban su Inna Furai dana ɗauka kai za a ɗorawa." Suna shiga ya sa hannu ya bige bakinta har sai da ya fashe ai kuwa Dubu ta fashe da wani marayan kuka bai bi ta kanta ba ya sa kilifar aski ya ɗora mata akan gaban goshinta. A zabure ta matsa baya ta ce, "Aski za ka yi..." Idanun da ya zuba mata ne ya sa ta haɗiye maganar ba tare da ta ƙarasa faɗa ba. Ta ci gaba da hawayen baƙinciki da nadama.
"Idan kika sake yi mini magana sai na yanke harshenki da wuƙar nan." Dubu na ji na gani haka Aseem ya sauke mata sumar kanta ban da hawaye babu abin da take yi. Kafin wani lokaci sai ga kan Dubu ya fito ral da shi babu gashi. yana gamawa ya nuna ta wuƙa hannunsa ya ce:
"Wannan da kika gani somin taɓi ne amma matuƙar kika sake shiga hannuna sai na yi miki zanen gobirawa da wuƙar nan a fuskarki." Ganin wuƙar na sheƙi ba ƙaramin razana Dubu ta yi ba, kuma a yanda ta ga babu ɗigon tausayi a fuskarsa ta san zai iya aikatawa don haka ta hau gyaɗa kai hawaye na zuba. Hannunta ya fisga zuwa falo ya sata tuƙin mashin. Dubu tun tana ganin kamar da wasa yake har ta tabbatar da yau sai ya kusa halakata a cikin gidan. Tana ganin ya ciro belt ta shiga taitayinta. Kuka take wiwi saboda yanda ƙafafuwanta suka ƙage, gashi ko nan da cen Aseem ya ƙi matsawa bare ta samu ta zauna ta huta. Tana zama kuma yake lafta mata belt ba shiri za ta sake miƙewa ta tashi tana soshe-soshe.
Sai da ya ga Dubu ta yi lugub sannan ya miƙe ya faɗa banɗaki ya yi wanka.
A wurin Dubu ta zube tana sauke numfashi da ƙyar, ta jera masa Allah ya isa ya fi a ƙirga. Kamshin da ya game hancinta ne ya ankarar da ita dawowar da Aseem ya yi. Ya yi kyau sosai cikin ƙananan kaya, haushinsa ne ya sake mamaye zuciyar Dubu don bata taɓa yadda da faɗar da ake yi akan sojoji mugaye ba ne sai a wannan lokacin. Kan kujera ya zauna sannan ya kirata, da sauri ta ƙarasa wurin ƙafarsa ta zauna. Danne-danne ya fara yi har sai da Dubu ta gaji da zaman sanna ya kalle ta ya ce, "Har yanzu kina nan da rashin kunyarki ko? Inno ta ɓata ki kina shuka tsiyar da kika ga dama. Wallahi daga yau na sake ji ko ganin kin aikata wani abin na rashin ɗa'a gaba hannu da ƙafafuwanki zan yanyanke miki, wannan bakin naki sai na datse shi na ga ta ƙaryar iskanci." Kamar ƙosashen ƙadangare haka Dubu ta riƙa gyaɗa kai tana hawaye. Yana gama maganar ya fisgi hannunta suka fice daga cikin gidan.
Yaya babba na ganin irin marin da Aseem ya yi wa Duba ta zuba salati haɗe da dafa ƙirji, don har jin saukar marin sai da ta ji wani iri a jikinta. Tana ganin fitarsa ai kuwa ta zauna daɓar a wurin ta fashe da wani irin kuka. Hajiya Nafisa ci kanki ba ta ce mata ba, sai ma jin zuciyarta da ta yi ta mata fes saboda ta san tun da ta tabo Aseem ba za ta ji da daɗi ba. Saboda ko su Nabila baya musu ta daɗi bare Dubu da kowa ya shaida fitinarta. Yaya Babba wayarta ta zaro ta miƙawa Hadiza tana faɗin.
"Maza kira mini Garba idan shi ya ɗaure wa wannan fitsararren yaron yake shuka rashin matumci, har ina kiransa yana ji na sai ya mini bayani. Wallahi ba Soja ba yau ko Barek ɗin ce da kansa sai an yi mini iyaka da shi." Hadiza jiki a sanyaye kamar kazar da aka tsamo daga ruwa ta karɓi wayar ta fara lalubo lambar, amma a ƙasan zuciyarta tana ayyanawa irin rikicikin da za a kwasa a cikin gidan.
Baba Abubakar suna hanyar dawowa gida daga asibitin da Inna Furai take kwance har an bata sallama, da yake dama likitocin sun ce damuwa da fargaba ne ya jefa ta a halin da take ciki. Bai yi aune ba ya ji kiran waya. Hadiza na jin an ɗauki wayar ta miƙawa Yaya babba, shi kansa Baba Abubakar tun da ya ga kiran mahaifiyarsu ya ayyana dole akwai abin da yake faruwa. Ɗaukan wayar ya yi da sallama jiki babu ƙwari, Yaya babba ko amsa sallamar sa ba tayi ba ta ce, "Garba! Garba!! Garba!!!" Gabansa na faɗuwa ya amsa sannan Yaya Babba ta ci gaba da cewa, "Sau nawa na kira ka?" Ya amsa mata.
"Sau uku Inno"
"Wallahi tun ban kwashe wa ɗanka falsafar albarka ba ka zo gidan nan yanzu-yanzu" Kansa ɗaurewa ya yi don shi ya manta ma da sun yi magana da Aseem akan zai zo gaisuwa saboda haka ya cewa Yaya babba.
"Inno wa kenan?"
Yaya Babba ta fashe da kuka tana cewa, "Karka zo ka bari idan ya kashe mini jika shi kenan."tana gama maganar ta katse kiran. Da sauri Baba Abubakar ya danna wayar Aseem sai dai ya ji ta akashe don lokacin tuni ya kashe ta saboda ya san dama tabbas za a neme shi.
Wayar Hajiya Nafisa ya kira tana ɗauka ya shiga jero mata tambayoyi, tana jin haka ta saci kallon Yaya babba da ta cika fam sannan ta bashi amsa da, "Ka san dai yarinyar nan Dubu ba kunya gare ta ba, daga zuwan Aseem ta sheƙa masa garin masara. Dama kuma ta cikumi Nabila tun da ta rainata kamar takalmin ƙafarta. Sauran maganar dai sai ka zo." Yana tafe a mota amma gani yake kamar tafiyar bata sauri don ya san lamari ya gama kwaɓewa gabaɗaya amma gyarawa sai Allah.
Yana zuwa ya samu Yaya babba a zaune ban da hawaye babu abin da take yi, a gefenta ya tsugunna ya ce, "Ga ni Inno."
"Garba ka raba ni da wancen mai busasshiyar zuciyar. Wallahi ni an cuce ni da aka tura mini jika aikin soja, dama tun tuni na ce bana son wannan aikin saboda cire musu imani ake yi amma aka ƙi yanzu ga irinta nan. Yaro ya koma kamar basamude haka ya riƙa kifawa yarinyar mari babu tausayi barr imani. Wallahi idan ya kashe mini jika ba zan yarda ba shari'a sai ta kaimu har kotun ƙoli." Sai ta kuma rushe wa da kuka tana ci gaba da cewa, "Saboda Allah me Dubu ta tsare masa da zai riƙa zabga mata mari kamar Allah ya aiko shi. Kana ganin wannan shirgegiyar matar ta min tsaye a ka, ko ta tsawatar masa wa ya sani ba ko ita ta saka shi don na lura ba ƙaunar Dubulliyata take ba. Kaico yanzu yarinyar ko a wane hali take oho." Yaya Babba ta sake rushewa da kukan da ya fi na farko taɓa zuciya.Nan take aka yi wa Baba Abubakar bayanin abin da ya faru, ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba. Da ƙyar ya samu ya lallaɓi Yaya babba ta rage faɗan sai dai bakinta ya kasa yin shiru.
Bayan wani lokaci suna nan zaune Aseem da Dubu suka shiga cikin gidan, fuskar Dubu duk ta yi zurur-zuru tana tafe tana gwale ƙafafuwa. Gabaɗaya mutanen wurin binta suka yi da kallo, Baba Abubakar rai a matuƙar ɓace ya tari Aseem da kyakkywan mari. Dubu kuwa na ganin haka ta sake ɗangalewa ta rushe da kuka ta faɗa kan Yaya Babba.
Da sauri Yaya babba ta matsa baya tana zaro ido ta ce, "Dubu me nake gani kamar aski akanki." Dubu ta rushe da kuka ta ce, "Inno wallahi aski ya mini kuma wallahi ɗan iska ne." Cak Yaya Babba ta tana ƙarewa Dubu kallo sannan ta ce, "Dubu je ki can mu gani." Dubu ta tashi tana ƙobare ƙafafuwa saboda irin gwale-gwalen da ta sha.
Ba su yi aune ba sai ga ni suka yi Yaya babba ta faɗa ɗaki ta rushe da kuka. Da sauri suka bi bayanta saboda kusan kowa bai ji daɗin abin da Aseem ya yi ba musamman Mahaifinsa, faɗa yake yi masa sosai sannan suka shiga ɗakin. Yaya babba kallonsu ta yi fuska a murtuke ta ce, "Garba ka tara mini ƴan uwanka saboda wannan ba maganar tsaye ba ce. Kuma idan har Aseem ya farke mini Dubu na rantse da Allah ba ita kaɗai ya yi wa illa ba, ya fi kowa shiga uku domin babu makarin maganin ƴan shafi mu lerar da za a bashi. Kai ni wallahi ban lamince ba ke Nafisa ke ce uwarsa wuce ki je ji bincike shi tas, don wallahi Idi ɗan wanzan ya mutu babu wani magani da zai karya laƙanin aikin, saboda aikin har da haɗin ƴan shafi mu lera." Tana gama maganar ta fisgo Dubu tana shafa mata suɗaɗɗen kanta ta ci gaba da cewa, "Ka ga yanda Kan Dubu ya sulle kamar bayan sulba. To kwarankatsa dubu idan har ka farketa kaima haka wurin zai shafe kamar bayan silba."
Kallon-kallon aka fara yi da juna, jikin Hajiya Nafisa ya yi sanyi dukda ta san a tarbiyyar da suka bawa Aseem ba zai taɓa yi wa Dubu fyaɗe ba. Amma shaidar ɗan yau bata da tabbas, domin ɗa ne ka haifshe baka haifi halinsa ba. Babban abin da ya fi ɗaga hankalinta da ta ji an ce Aseem ɗin ta ya koma kamar bayan silba. Ita da take yi masa tanadin Yusra ƴar aminiyarta ya aura.
Baba Abubkar ya kalli Aseem da kallon tuhuma rai a ɓace, Aseem ya sunkuyar da kai ƙasa saboda ba ƙaramin takaici kakar tashi ta bashi ba. Da wata irin murya Baba Abubakar ya ce, "Abin da Inno ta faɗa haka ne?"
Aseem ya furzar da iska mai huci ya ce, "Daddy don Allah ka bar biyewa maganar tsohuwar nan ka san dai wasu maganganun nata ba su..." Bai ƙarasa ba Baba Munkaila ya buga masa tsawa ya ce, "Ka iya bakinka Aseem duk yanda Mahaifiyarmu take furta lafazi Mahaifiyarmu ce."
Yaya Babba ta wara hannuwa ta ce, "Kuma na fi wannan gajeriyar uwar tashi mai kama da gajeren turmi, na gama maka komai tun da na haifo uban da ya haifeka. Atoh gara ka yi bayani wallahi babu inda zani in wahalar da kaina wurin neman maganin gargajiya. Alƙur'an dama sai da Idi wanzan ya gaya mini ɓat haka za a nemi komai a rasa. Wa ya sani ma ko aljanunsa ne za su ɗauke su cinye su barka a shafe.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[7/1, 5:59 PM] My Data sim number: *DUBU JIKAR MAI CARBI*