Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cike da yashi. Hansatu ta nuna Bokitin tana faɗin, "Ɗan'iya ba wannan ba ne bakitin da ka fita da shi?" Nan take mamaki ya cika su. Hansatu ta suri bokitin ragadadar da ke cike da yashi, ko ta kan Balarabe bata bi ba ta wuce gidansu Dubu tana kumafar baki.

Lokacin da Yaya babba ta gama jin jawabinta, kallon sheƙeƙe ta yi wa Hansatu sannan ta ce, "Hansatu kura ko mayya kika mayar mini da Dubu da za ta iya cinye bokitin ragadada guda? Allah na tuba me ye ragadada abin da duk yaɗi da jijiya ne, me ye Dubu bata ci a gidan nan?" Takaici ya kama Hansatu ta yi ƙwafa sannan ta ce, "Dama ai sake ta samu shi ya sa take shuka tsiyar da take so, to wallahi daga kaina ba za ta sake yi wa wani haka ba." Tana gama masifar ta fice, Inna furai ta bita har soro tana mayar mata da martani.

"Aniyarki ta faɗa kanki, azzulama mai baƙin baki. Bayan zazzagar iya shegen da kika yi mata shi ne bai ishe ki ba za ki biyota har gida kenan." Sai da ta ga ficewar Hansatu ta juya ta samu Yaya tana faɗin, "Yaya an ya maganar yarinyar nan bata kan hanya, na san halin Dubu sarai za ta iya tare yaron nan ta karɓe bokitin ragadadar fa." Yaya babba ta yi ƙwafa cike da takaici ta ce, "Ai kuwa wallahi da na ɗebe mata falsafar albarka alƙur'an da babu ni babu ita."

Hansatu kai tsaye wurin mai unguwa ta wuce bayan ta kwashi gaisuwa ta zayyane masa abin da yake faruwa, ba shiri ya aika da kiran gaggawa gidan Marigayi mai carbi. Zuwan dogarawan ya yi daidai da zuwan Baba Abubakar shi da Aseem, wannan sammaci ba ƙaramin ɓata ran Baba Abubakar ya yi ba. Ya ci alwashin idan kuwa haka ta tabbata Dubu ce ta cinye ragadadar, tabbas ba ƙaramin hukunci zai ɗauka akanta ba don duk abin da Yaya babba za ta faɗa sai dai ya toshe kunnuwansa. Shi da Aseem suka wuce wurin mai unguwa ba tare da sun shiga cikin gidan ba. Suna zuwa aka aika kiran Dubu, tare da Dogarawan suka taho tana zuwa ta yi turus! Jiki a sanyaye ta zauna ta hangi Aseem na wurga mata harara sai Ɗan'iya da idanunsa suka yi wuri-wuri, saboda kukan da ya sha. Hansatu lokaci-lokaci take kallon Dubu tana ƙwafa cike da jin haushi.

Shiru wurin ya ɗauka Mai gari ya ƙurawa Dubu ido yana son gano gaskiyar lamari, don ya san sarai Dubu za ta yi abin da ya fi haka, bayan an gabatar da abin da ya tara su a wurin, Mai unguwa ya kalli Ɗan'iya ya ce, "Ɗan'iya ko za ka gaya mana yanda abin da ya kasance." Ɗan'iya ya fyace majina sannan ya zayyane duk abin da ya faru tsakaninsa da Dubu. Tun bai rufe baki ba Dubu ta yi caraf ta fara magana, "Alƙur'an ƙarya yake yi mini haka kawai zai yi mini sharri saboda ba ƙaunata ake..." Da sauri Baba Abubakar ya katse ta yana yi mata daƙuwa Hansatu ta tura ɗankwali gaba tana faɗin, "Allah ya taimakeka ka yi mini tsakani da Dubu wallahi muddin ta sake shiga gonata sai na yi ƙasa-ƙasa da ita. Ƙwaranƙwatsa kuma sai an biya ni kuɗin ragadadata." Mai unguwa zai yi magana Aseem ya zaro dubu biyar ya miƙawa Hansatu yana faɗin, "Shi kenan magana ta wuce." Dubu na gefe da ta ga maƙudan kuɗin da aka bawa Hansatu ta yi zaraf ta ce, "Wallahi ragadadarta bata kai da kuɗin nan bayan kafin na karɓi bokitin Ɗan'iya ya ce mini ta dubu ɗaya ce." Ta ƙarasa maganar za ta warci kuɗin da sauri Hansatu ta maƙe su tana cewa, "Ai irin wannan asara kullin ma Allah ya kawo ta." Baba Garba saboda ɓacin rai sallama ya yi wa Mai gari ya tafi ya tafi, shi kuwa Aseem hannun Dubu ya fisga suna tafe yana haɗa hannunsa da nashi yana murzawa. Ban da wash! Babu abin da take yi saboda yanda hannunta yake yi mata raɗaɗi.

Suna shiga cikin gidan suka wuce sashen su Yaya babba har lokacin hannun Aseem na riƙe da Dubu. Tun da Yaya babba ta hango su take sakin murmushi, don shi kansa Aseem har sai da ya saki murmushi saboda yanda ya ga kakar ta shi cikin farinciki. Tun kafin su zauna ta sake washe baki tana faɗin, "Allah ƙadiran alamanyasha'u. Ikon Allah! Allah mai sanin abin da yake cikin zuciya." Gabaɗaya ba su kawo komai a ransu ba sai ɗan murmushi da suka yi. Bayan sun gaisa cikin ɓacin rai Baba Abubakar ya fara yi wa Dubu faɗa, kasancewar mutum ne ba mai zafi ba ya sa bai cika faɗa ba, amma Dubu ba ƙaramin tsora ta yi ba. Saboda dama mai haƙuri bai iya faɗa ba. Yana gamawa Yaya babba ta dasa nata faɗan.

"Maganar gaskiya Dubu kin wulaƙanta ni ki rasa me za ki karɓarwa yaro sai ragadada?" Inna Furai ce ta shiga ɗakin tana girgiza kai ta ce, "Don Allah Garba ka ji wata muguwar ɗabi'a, ka gaya mana meye Dubu bata ci a gidan nan?" Yaya babba ta yi ƙwafa ta ce, "Gane mini hanya Furaira neman maganar fa. Garba ka rabani da Dubu tun takaicinta bai kashe ni ba, ba zan iya ba gaskiya ba za ta ƙara kwanar mini a ɗaki ba. Ina dalili ta kashe ni ta cuci iyalaina, ko da dai kun girama shi fa Maraici ba daɗi gare shi. Don Allah Garba idan babu ni ba kun zama marayu gaba da baya ba? Na gaji gaskiya, ka sa Dubu a gaba ka tafi da ita na bar maka ita halak malak."

Baba Abubakar ba ƙaramin daɗi ya ji ba, don dama ya jima yana san ɗaukan Dubu Yaya babba ce take hanawa. Ya gyara zama ya ce, "Dama Inno na daɗe ina yi miki maganar amma yanzu tun da kin amince zan tafi da ita." Madadin Yaya babba ta yi magana sai ta yi jim sannan ta ce, "Ni fa Garba ba raba ni da Dubu ne bana so ka yi ba, gaskiya a riƙa zalintar marainiyar Allah ne bana so. Wannan matar taka ba ƙaunar Dubu take ba, sai ta zo ta yi ta gallazawa marainiyar Allah, ina nan ban san halin da ake ciki ba. Kai kuma mutuwar sonta kake ballantana ka tsawatar mata. Gidan Ado kuma Fauziyya sai jaraba mace sai masifa ko ƴaƴan cikinta ba ƙaunarsu take ba bare kuma Dubu, raba ni da bawa Ado Dubu ana zaune ƙalau. Ita kuma waccan mai tausayin ƙasar komai nata ba kuzari ina dalili inkai Dubu ta riƙa barinta da yunwa? Ni inbawa Rahama Dubu ta kashe ta da yunwa Allah ya tsare ni. Don Allah Garba wacce riba suke ci wai Rahama basa karyawa sai goman safe, mu da anan ƙarfe goma an fara haramar na rana. A'a gara Dubu ta yi zamanta a nan ina ganinta ina jin daɗi." Baba Abubakar ya girgiza kai don dama sai da ya ayyana haka amma ya ci alwashin ko da dabara sai ya karɓi Dubu muddin ya dawo gidan da zama, don barinta a haka har girmanta akwai gagarumar matsala.

Yaya Babba ta kalli Inna Furai ta ce, "Furaira ki gaya masa mana ai kyayi mini kara dai ko?" Inna Furai ta washe baki ta ce, "Garba wani abin alkhairi muka hango kuma mun san da kai da kaya duk mallakar wuya ne. Mun yanke shawara ni da Yaya ya kamata a ci gaba da yaɗa zumunci." Gaban Baba Abubakar sai da ya faɗi don ya san wataƙila wani abin za su ɓallo masa.

Inna Furai ta karɓe zan cen da cewa, "Ka san dai bikin su Salisu da su Zulfa bayan babbar sallar nan ne kuma dududu bikin saura wata guda ina jin." Baba Abubakar ya gyaɗa kai ya ce, "Ai ina jin lokacinma mun dawo nan." Inna Furai ta yi dariya ta ce, "Ai za ku sha hidima tun da auren ƴaƴa shida ba wasa ba." Baba Abubakar ya yi murmushi don shi kansa idan ya tuna bikin har daɗi yake ji ace cikin gidansu za su aurar da ƴaƴa shida maza da mata kuma duk auren gida abin akwai farinciki.

Yaya babba ta katse masa tunani da cewar, "Ka ga da Zulfa da Bintu duka Dubu fa ta girme musu." Baba Abubakar ya gyaɗa kai ya ce, "Ai suma Yaya don kun matsa ne amma duka nawa yaran suke?"

Nan take Yaya babba ta ɓata fuska ta ce, "Yara dai Allah ya kawo musu mijin aure kar ka yi musu buƙulu, kai da ɗan'uwanka ba kun ɗorawa kanku bokon jaraba ba. To gaskiya bana son hassada Garba kuma na yanke shawarar haɗa Dubu da Soja don gaskiya ba za a zo ana yi mata gori ba tun da ƙawayenta kusan duka sun yi aure wasu ma sun haihu."
*DUBU JIKAR MAI CARBI*


©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*


FREE PAGE 10
https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels

Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.


Baba Abubakar da Aseem lokaci guda suka ɗago suna kallon Yaya babba, da ta ci gaba da zayyano zance ko a jikinta. Dubu na maƙure a gefe sai raba idanu take don ita kanta ba ta san da wannan shawarar da Yaya babba ita da Inna Furai suka yanke ba. A madadin fushi sai ma wani murmushi da Aseem ya ke yi, wanda kana gani za ka tabbatar da murmushin mamaki ne da tsantsar baƙin ciki. Yaya babba da bata kawo komai a ranta ba ta ci gaba da cewa, "Allah ya sani dama wannan ne dalilin da ya sa na aika kiranka kai da Soja, don kune maganar ta shafa ba su Munkaila ba. Waye ya haifa maka Soja bayan kai da uwarsa Nafisa?" Yaya babba ta tambayi Baba Abubakar. Shiru ya yi yana murmushinsu na manya, sannan ya ɗago da kai ya ce,

"Inno na ji daɗin wannan maganar ta ki, kuma ni zan fi kowa farinciki da wannan haɗin domin abin da ya yi Dubu shi ya yi Aseem. Amma wani hanzari ba gudu ba..." Da sauri Yaya babba ta katse zancensa da cewar:

"Don Allah Garba ka faɗi alheri ko ka yi shiru. Wannan fa abin farinciki ne, kuma me ye aibun Dubu yarinya san kowa ƙin wanda ya rasa. Ƙwaranƙwatsa dubu babu abin da Soja zai nunawa Dubu, kyau ya fita ko tsafta? Yarinyar da sai ta yi wanka sau uku a rana ko ba haka ba Furaira?" Inna Furai ta taɓe baki ta ce, "Ina dalili tun ba a ji ta bakin yara ba Garba za ka kawo mana hanzari, wannan kamar zazzage albarkar da ke cikin auren za ka yi. Gaskiya karka ɓata auren yara tun ba a je ko'ina ba, yoo Allah na tuba wane hanzari gare ka da ya wuce ka sa albarka?"

Baba Abubakar ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "Inna ni fa baku fahimce ni ba. Ina nufin su yaran a fara ji ta bakinsu don kar ayi abu ba da son ransu ba. Amma idan kuna faɗin haka sai in ga kamar kuna nuna Dubu da Aseem ba ɗaya ba ne a wurina." Yaya babba ta washe baki ta ce, "Shi dai Soja na san ai ba zai ƙi ƴar uwarsa ba, ita kuwa Dubu kar ku ji ta, na san ta yanda zan shawo kanta." Aseem saboda takaici miƙewa ya yi ya fice daga ɗakin, Yaya babba na ganin haka ta saki dariyar farinciki tana faɗin,

"Ai na gaya muku wannan shiru-shirun da yake yi wallahi aure yake so, ja'iri ga shi nan kunya ta kama shi ya fita yana sunne kai, yoo waye zai samu Dubu bai yi farinciki na? Alƙur'an ana auren ku basu wata tara sai dai ku ji haihuwa, Soja wai mu zai yi wa hikima bai san na daɗe da gano lagwansa ba." Baba Abubakar ya yi shiru yana nazari domin ya san ba ƙaramin ruwa Yaya babba ta kunto masa ba, saboda ko makaho ya shafa fuskar Aseem ya san yana cikin yanayi marar daɗi. Saɓanin Dubu da ba za ka tantance ainihin halin da take ciki ba, na farinciki ne ko baƙinciki ba.

Yaya babba cikin murmushi ta kalli Baba Abubakar ta ce, "Yanzu dai Garba ka je ka shaidawa Nafisa halin da ake ciki don a fita haƙƙinta na mahaifiya, kar ta ji magana daga sama don ma bata da fushi ba kamar Fauziya Matar Ado ba, kai gaskiya Garba duk cikin ƴan uwanka akwai wanda ya yi dacen mace irinka kuwa? Allah ya sani Nafisa macen arziƙi ce idan na zageta sai dai na yi mata ƙazafi. Suma ƴan uwanka zan shaida musu abin da yake faruwa don kar su ji maganar aure bagatatan, na san Sule da baƙar zuciya sai ya ɗau fushi da ni ba gaira babu dalili. Yo ko auren na yi musu ban sanar musu ka ga laifina Garba? Kai ne dai uban soja halak malak, wani ne ya haifa mini kai? Ni ina na iya gaba halin ƴan wuta, ina masoyiyar Annabi (S.A.W) me zai haɗa ni da wuta ana zaune ƙalau? A'a rabani da wannan falsafar zan sanar da su da kaina, kar shaiɗan ya ɗebe ni idan suka ɗau gaba da ni na biye musu, ana zaune ƙalau na tsine musu su ɓalɓace." Baba Abubakar ya zaro kuɗi a aljihu ya dire musu a gabansu ya yunƙura jiki ba ƙwari ya ce, "To shi kenan Inno Ni bari na wuce." Cikin haɗin baki Yaya babba da Inna Furai suka fara faɗin, "Ka gaida gida Allah ya yi albarka."

Yana fita Dubu ta ɓata fuska ta ce, "Wai ke Inno ce miki na yi ina son shi bayan mugu ne, baki ga irin wuyar da ya bani ba rannan." Yaya Babba ta rungumo Dubu cikin lallashi ta ce, "Ke yi shirunki, kin san me ya sa na yi wannan haɗin?" Dubu zuciyarta ɗaya ta girgiza, Yaya babba ta ci gaba da cewa: "Allah ya sani Dubu idan ba mutuwa ba zan iya rabuwa da ke ba. Idan kika auri Soja a cikin gidan nan za ku zauna, ga wuri nan a gyara masa ku yi zamanku. Amma idan bare kika aura kin san dole ki fice daga gidan nan. Na san irin rayuwar da za ki yi a can gidan? Sam! Ba zan laminta ba a rabani da Marainiyar Allah ina ji ina gani." Daɗi ne ya kama Dubu lokaci ɗaya ta washe baki cikin farinciki. Lokaci ɗaya kuma sai ta ɓata fuska ta ce,

"Inno idan ya harbe ni da bindiga fa? Wallahi ba shi da tausayi tsaf kashe ni zai yi." Inna Furai ta hau jinjina kai sannan ta ce, "Wallahi har kotun ƙoli sai mun je a kan shari'ar nan. Ke bar zancen bindiga tsaf za ki saye zuciyar shi, tun da da me na birnin za su fiki?" Dubu ta ci gaba da washe baki tana jin nishaɗi ita a dole za ta auri Soja kuma ɗan gayu.

A ranar Yaya babba da Inna furai suka gama isar wa da Mutanen gidan, hukuncin da suka yanke har suke ɗorawa da cewar, yara tuni sun haɗa kawunansu don Aseem tsabar kunya tun da ya fito bai dawo ba. Ita kuma Dubu ban da murmushi babu abin da take yi, nan fa ƙananan maganganu suka fara tashi a cikin gidan kowa da abin da yake tsakura yana isarwa.

Lokacin da Baba Abubakar ya fita a cikin mota ya samu Aseem, yana zaune ya haɗa kai da sitiyari. Har Mahaifinsa ya shiga bai sani ba ya zurfafa cikin tunani. Da kallon tausayi ya dubi ɗan nasa ya ce,

"Aseem!" Jiki a sanyaye idanu jawuri ya ɗago ya kalli Mahaifinsa, murya a shaƙe ya ce, "Na'am Daddy."

"Dukda ban shiga zuciyarka ba amma san wannan hukuncin ba lallai ya yi maka daɗi ba." Kamar mai jira ya shagwaɓe murya yana faɗin, "Yanzu shi kenan Daddy duk abin da su Inno suka faɗa, komai ta ce sai dai ku hau ku zauna? Gaskiya ni kam babu yanda za a yi na auri waccen yarinyar. Yarinyar da kowa ya san bata da nutsuwa, don Allah Daddy ya za a yi ma na auri wata Dubu? Never wallahi." Ya ƙarasa maganar a shagwaɓe kamar zai yi kuka. Baba Abubakar ya yi murmushinsu na manya ya ce, "Rashin nutsuwarta ba komai ba ne idan har kana sonta, kai namiji ne za ka iya nusar da ita akan abin da ya dace." Cikin hanzari ya furta, "Ni ba na ma sonta, Allah ya sani ta nemi wani ta haɗa ta shi amma ba ni ba."

A karo na biyu Baba Abubakar ya sake kiran sunansa, "Aseem." A marairaice ya ɗago ya amsa sannan Mahaifinsa ya ci gaba da cewa, "Inno fa mahaifiyata ce kana ganin zan iya kaucewa umarninta, idan har ina neman albarka duniya da lahira? Su fa iyaye biyayya ake musu akan duk abin da suka buƙata matsawar bai saɓawa mahallici ba, ko da kuwa baka ƙaunar abin sai ka ga wata rana abin ya zame maka alkairi." Murya a raunane Aseem ya ce, "Daddy nima ban taɓa saɓa umarninka ba, amma maganar gaskiya idan aka tilasta ni na auri Dubu sai dai na barta a gidan nan, na yi tafiya ta."

"Da ka wulaƙanta ƴar ɗan'uwa bayan ka aureta; ai gara ka ce mini ban isa na saka ko na hanaka ba. Zan yi ƙoƙarin ganin na shawo kan Inno idan ta amince shi kenan, idan bata amince ba, ka yi haƙuri ka amshi ƙadaddararka hannu bibbiyu, ka san kowanne bawa baya kaucewa ƙaddararsa, ta yiwu alkairin na gaba kai da kanka za ka ji daɗin haka. Saboda sautari muna ƙin abin da shi ne alkairi a tattare da mu sai daga baya mu fahimci haka." Shiru ne ya ratsa Aseem ya kasa furta komai, zuciyarsa ban da zafi babu abin da take yi masa. Jiki a sanyaye ya tuƙa mota suka wuce gida, kowa na saka da warwara a cikin zuciyarsa.

Tun shigar su cikin gidan Hajiya Nafisa ta fahimci gabaɗaya babu mai cikakkiyar walwala a tattare da su, har ta fi damuwa da damuwar Aseem saboda Baba Abubakar ba wani zaman daɗi suke yi ba, duk akan maganar komawarsu Ɗangwauro. Aseem na shiga ɗaki ta bi bayansa, a ɗaki ta same shi yana kaiwa da kawowa haɗe da kaiwa bango naushi. A ɗan tsorace ta fara watsa masa tambayoyi:

"Lafiya Asem? Wani abin ne ya faru da ku daga kai har Daddynku na ga baku da walwala?" Murya a can ƙasa ya ce, "Mommy babu komai, kawai wurin aiki ne suka kira ni akan wani issue ɗin." Kallon tsaf ta yi masa tana son gano gaskiyar abin da ya faɗa sannan ta ce, "An ya ba wani abin ne yake faruwa a Ɗangwaro ba?"

Da sauri ya kalle ta sai kuma ya ɗauke kai gefe saboda ambatar sunan garin, ba ƙaramin dawo masa da ɓacin rai ya yi ba, ya zauna a gefen katifarsa ya dafe kansa da hannu bibbiyu ya ce, "A'a Mommy." Taɓe baki ta yi ta ce, "Idan ma wani abin kuke ɓoyewa indai Hajiya babba ta kafe kai da fata na san ko ba daɗe ko ba jima zai fito fili." Tana gama maganar ta fice daga ɗakin.

Aseem ya ƙi sanar da Mahaifiyarsa ne saboda ya san Daddynsu ba zai taɓa sanar mata a wannan ranar ba, duba da yanayin zaman da suke a wannan lokacin. Uwa-uba kuma ya san idan ya gaya mata kamar ya ƙara hura wutar tashin hankali a tsakanin iyayen nasu ne. Lokaci ɗaya tsanar Dubu ta mamaye zuciyarsa don duk ita ce silar komai, dukda hali irin na mahaifiyarsa tun da ya taso bai taɓa jin suna sa'insa ita da Mahaifinsa ba. Amma lokaci ɗaya ta tarwatsa farincikinsu ga auren iyayensu, da yake tangal-tangal tun da har lokacin Hajiya Nafisa na kan bakarta da ta koma ƙauyen nan, gara ya sallameta ta kwashi ƴaƴanta, ta riƙe a wurinta ko sa samu irin mijin da take buri da fatan su samu. Kamar yanda ta gama yi wa Aseem tanadin ƴar ƙawarta, saboda komai ta fi so su yi cikin bajinta da harkar girma.

A daren ranar ya haɗa kayansa tsaf a cikin jaka, washegari da sassafe ya wuce Lagos da yake acen yake aikinsa. Wannan ya ƙara tabbatarwa da Hajiya Nafisa tabbas akwai wata a ƙasa, amma zafin zuciya irin nata ya sa ba za ta iya tambayar mahaifinsa don jin abin da yake faruwa ba. Kuma ta lura shi kansa har lokacin baya cikin walwala, ga yawan waya da ta ga yana yi da ƴan'uwansa. Ga shi ba wata kyakkyawar alaƙa gare ta da facalolinta ba, bare ta kira ɗaya daga ciki don ta ji halin da ake ciki ba.

BAYAN SATI BIYU

Duk wani daɗin baki da dabara irin ta tsofaffi Yaya babba ta yi wa Dubu, kuma tuni ta ji ta aminta da Aseem a matsayin mijin aure. Don ba ƙaramin ƙawatawa Yaya babba ta riƙa yi mata ba, tana nuna mata irin rayuwar jin daɗin da za ta yi matuƙar da auri Aseem, hatta wanki ta daina sai dai ya ɗauko mai yi mata. Kan Dubu ba ƙaramin girma ya ƙara ba don ji ta yi duk faɗin garinsu babu wacce ta yi dacen mijin aure sama da ita.

Tuni maganar auren Aseem da Dubu ta karaɗe cikin ƙauyen Ɗangwauro, mutane da yawa mamakin wannan haɗin suke yi ganin Aseem cikakken ɗan gayu amma ya ƙare a auren Dubu. Cikin dangi sai tsegungumi ake da wannan maganar, lokacin da labarin auren Aseem da Dubu ya isa kunnen Hafsa ƴar wurin Hajiya Fauziyya, zama ta yi dirshen tana kuka don duk duniya babu wanda take so da ƙauna sama da Aseem, amma rana tsaka a ce wai Dubu ita ce za ta aure shi. Tun daga ranar ta bar walwala bata da aiki sai zaman ɗaki, ga shi an yi tambayar duniya ta ƙi faɗa, sai dai ta ce bata jin daɗi.

A wannan lokacin saura kwana uku tariyarsu a Ɗangwaro, sun gyara sashensu da sauran ɓangarorin gidan, gidan ya fito kamar a birni. Har fasalin ƙofar gida suka sauya suka rushe gaban gidan, suka saka ƙaton gate wanda mota za ta iya shiga har harabar wurin da suka zagaye da ya zama wurin parking space. Haka bikin su Dubu a lokacin saura sati biyu cif, su Yaya babba har an fara gyaran Amare. Aseem da Dubu a gefen sashen su Yaya babba aka gyara musu, gini ne mai ɗaki uku sai kitchen da banɗaki. Sai Salisu da Zulfa suna maƙota da su Dubu, Bilalu da Murja suna maƙotaka da Baba Auwalu sai kuma Bashari da Maryama a suke maƙotaka da su Baba Adamu. Duk gyaran da ake wa amaren Yaya babba da Inna Furai sune jigo da ragamar komai.

Sai dai duk wannan budurin da ake yi mai gayya mai aiki, Mahaifiyar Aseem bata san wainar da ake toyawa ba har sai ana gobe tariyarsu, a lokacin da suke tsaka da hatsaniya ita da mijinta. Suma ganin Manyan akwatuna ta yi a ɗakinsa kishi ya rufe mata ido don a tsammaninta idan sun koma Ɗangwaro aure zai ƙara. Bayan ya gama sauraronta ya saki murmushin ƙeta don ya san muddin ya sanar da ita abin da yake faruwa ba lallai ta samu damar runtsawa a ranar ba. Saboda yana da tabbacin Aseem bai sanar mata da abin da yake faruwa ba, saboda har lokacin shi ma ɗaukan maganar yake kamar almara. Kafin lokacin akwai lokacin da Baba Abubakar ya kira a kan maganar kayan lefe, amma babu wata tsayayyiyar amsa da Aseem ya bashi. Hakan ne ya sa ya bugi ƙirji ya yi masa komai, saboda idan ya biye ta tashi ya san babu abin da Aseem zai yi.

Shi kuwa Aseem har kullin sai ya yi yunƙurun sanar wa mahaifiyarsa halin da ake

Please Login or Register in order to submit comment