Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙarƙashin gado ta tuni ta fice ta yi hanyar zariya. Babban abin da ya fi ɗaga mata hankali shi ne zancen naɗe ƙafafuwansu da ta ji ance Fatalwa za ta yi mayar da su kamar alkaki. A duniya babu abin da ta fi so da ƙauna a jikinta kamar santala-santalan ƙafafuwanta, wannan ya samo asali ne sakamakon kirarin da marigayin mijinta yake yi mata akan Doguwa mai tsawon alheri tsawo rabin kyau ƴar fillo.Wannan kirari ba ƙaramin baƙanta zuciyar Lami kishiyar Lantan yake ba saboda ita gajeriya ce, kuma hatta bayan rasuwar mijinsu idan wani abu ya haɗo Lantan da Lami haka za ta yi ta hura hanci tana yi wa Lami habaici. To kuwa idan aka mayar da ƙafafuwanta kamar Alkaki ai ta shiga-uku don ta tabbata idan aka naɗe mata ƙafafuwa, ta san ko tsahon turmin gidansu ba za ta kai tsayi ba.

Lantan bata gama tunani ba ta riski maganar Dubu cikin kuka tana sake cewa, "Kuma har ce mini ya yi a cikin ƴan uwan sa zai aiko a tsotsewa wani ko wata roman da ke cikin Ƙwaƙwalwarsu. Saboda gonar Mahaifinsu da suka taɓa danne masa."

Lantan na jin haka ta ci gaba da karanto duk wata addu'a da ta san ta taɓa biyata a bakinta. Saboda ta san badaƙalar da suka shuka akan gonar Mahaifinsu. Hatta kalmar larabci indai Lantan ta santa a baki haka za ka ji tana maimaitata ya fi sau goma. Ta yi kiran sallah da tayar da iƙama ya fi sau biyar, idan ta biya addu'ar shiga banɗaki sai ka ji ta fara, "Labbaikallahumma Labaik" Idan ta dire sai ka ji ta sake cewa, "Hayya'alal salah" haka ta rinƙa yin addu'a don neman kariyar Ubangiji, amma addu'a har da ta shiga abin hawa haka ta rinƙa maimaitawa. Tana gamawa sai ka ji ta sake cewa, "Walaƙadkarramna bani adama..." Bata iya direwa sai ta ƙara kamo wata kalmar hatta sunayen Annabawa da Sahabai waɗanda ta san sunansu haka ta rinƙa biyawa.

Ana cikin haka suka jiyo muryar Baba Munkaila a bakin ƙofar Inna Furai yana cewa, "Lafiya kuwa mutanen gidan nan tun daga babban zaure nake sallama shiru ga ƙananan yara suna ta kuka." Ya ƙarasa maganar yana bubbuga ƙofar ɗakin, da ƙyar Yaya Idi ya ta so ya fara ƙoƙarin zare sakata.

A can ɗakin Yaya babba dirama ake yi da ita akan dole sai an barta ta fito wai sai dai Fatalwar ta ɗauketa ita da Dubu don ba za ta iya jure rashin Dubu ba. Hadiza da ke riƙe da kubar ɗakin ta ce, "Inno don Allah ki yi haƙuri ki zauna na san Dubu ba za ta zauna a waje ba, kuma ni fa gani nake sharrin shaiɗan ne amma babu wata fatalwa." Yaya Babba ta sake share ƙwalla ta ce, "Kaico rayuwa ban taɓa sanin haka zuciyarki ta ƙeƙashe ba Dije, wannan wacce irin falsafar rashin imani ce? Kowaccenku na riƙe da Ɗanta amma ni kun hanani nemo Marainiyar Allah. An ya kuwa Dije?" Hadiza babu yanda ba ta yi ba amma fir Yaya Babba ta kafe, don ban da ruwan hawaye babu abin da take yi. Hadiza na buɗe ƙofar Yaya babba ta fice da sauri tana ƙwalawa Dubu kira. Da sauri Dubu ta taho aikuwa caraf Baba Munkaila ya damƙi hannunta bayan ya gama jin labarin abin da aka bashi dangane da fatalwa. Yana fisgota ya zuba mata ranƙwashi a ka yana cewa, "Wallahi sam ban yarda da abin da wannan shaiɗaniyar yarinyar nan ta faɗa, ke a gidan uban wa kika ga fatalwa har ta baki saƙo?" Yaya babba na ganin haka ta ƙarasa wurin ƙafar Baba Munkaila ta yi zaman dirshen sai kawai ta fashe da kuka. Gabaɗaya ido ya dawo kanta, Baba Munkaila ya sassauta murya ya ce, "Inno lafiya kuwa?" Yaya Babba ta ɗago ya dubi Mukaila ta janyo hannunsa ta ce, "Ka dake ni kawai Munkaila na ce ka dakeni ka huce takaici. Kaga sai na tabbatar da falsafar rashin mutumcinka yanda ya kamata."

Baba Abubakar da shigowarsa kenan ya hango taron jama'a yana zuwa ya ga Mahaifiyarsa ce mutane ke zagaye da su. Har ƙasa ya russuna yana tambayar Mahaifiyarsa. Yaya Babba ta share hawaye ta ce, "Allah ya yi maka albarka Garba! Don Allah ka ga ya mini me na tsare wa Munkaila da Dije? Munkaila dai ya fi jin haushina. Garba ka gaya mini wacce tsiya suke tsinana mini, bayan Allah da ma'aiki waye gatana wa zai tsunduma ni a aljannah?" Baba Garba ya jinjina kai ya ce, "Inna wai me yake faruwa ne? Me suka yi miki?"

"Tsoronsu kake ji da zan yi magana ka amsa ƙasa-ƙasa. A cikinsu ka gaya mini akwai Malam ko kuma akwai ni. Ban da Allah da Manzonsa wa yake ƙaunata, ya hore mini lafiya da abin da lafiya za ta ci?" Yaya Babba ta yi maganar cikin ƙunan rai. Baba Abubakar ya ce, "Ayi haƙuri Inno"

Yaya Babba ta zuba hannuwa biyu tayi tagumi ta ce, "Garba ni wace ce a wurinku?" Baba Abubakar ya bata amsa, "Ke Mahaifiyarmu ce Inno"

"Idan na tsinewa su Munkaila wa billahi sai ta ka kama su ko ba haka ba?"

"Inno abar maganar tsinuwa don Allah." Baba Abubakar ya faɗa cikin sanyin murya. Yaya babba ta kuma rushewa da kuka sannan ta ci gaba da cewa, "Don Allah mecece tsinuwa da zan tsinewa ƴaƴan cikina. Idan na tsine musu na ɓalɓace duniya da lahira ko ina da wasu ƴaƴan bayan ku?" Baba Abubakar ya yi ƙasa da murya ya ce, "Inna don Allah ki yi haƙuri kin ga duk mutane kallonki ake yi."

Yaya Babba ta yi jim sannan ta ce, "Ka yi mini iyaka da Munkaila ko a hanya ya ganni kar ya nuna ya sanni, balle a lahira ya yi gabas na yi yamma. Haƙƙi ɗaya na san Munkaila yana bina, lokacin da aka yi masa shayi (kaciya) don Allah Garba ka biya shi cinyar kazar da na ci, ko ba za ka biya shi ba Garba?" Baba Abubakar ya rasa abin faɗa sai kawai ya girgiza mata kai. Yaya Babba ta ci gaba da cewa, "Me marainiyar Allah ta yi masa da zai ƙullace ta har ya sheganta mini ita? Don Allah Garba ka tambayar mini shi ta wurin da Dubu ta zama shegiya? Ka tambayi munkaila Ni Indo Kakarta ce shegiya ko matattun iyayenta?"

Baƙin ciki ne ya cika Baba Munkaila domin jikansa ya ba shi abin da Dubu ta faɗa ba gaskiya bane saboda ya san wacece ita, amma gani yake meye laifinsa don yana son hukunta Dubu domin ta faɗi gaskiyar magana. Gani yake idan ya yi haka shi zai kawo musu ƙarshen duk wannan guje-gujen da ake yi. Tun da tun farar safiya ya ji labarin abin da ya faru yake tantama akan Dubu don kowa ya san irin hatsabibancinta.

Wata uwar harara ya watsawa Dubu sannan ya kalli Mahaifiyarsa ya ce, "Yanzu Inno saboda na hukunta Dubu shi ne ya ɓata miki rai? Tun da haka ne na zame hannuna daga cikin sabgarta shi kenan?"

Yaya babba ta wara hannuwa alamun abin ya mata daɗi ta ce, "Sadaƙallahul azeem! Kana jin me ya ke faɗa ko Garba, dama me Munkaila yake yi wa Dubu? Ka gaya mini waye yake shiga lamuran Dubu bayan Allah da manzonsa idan ba ni ba?" Baba Abubakar ya sake ƙasa da murya ya ce, "To duk na ji wannan Inno amma don Allah ki taho mu tafi ɗaki."

Yaya Babba ta yi biris da Baba Abubakar tana cewa, "Don Allah ka yi mini iyaka da Dije saboda tsoro nake ku tafi ku bar ni da ita a ɗaki ɗaya, kar a wayi gari ta maƙure ni na mutu har lahira." Cewar Yaya Babba tana satar kallon Hadiza.

Rass gaban Hadiza ya faɗi da jin kalmar Mahaifiyarta, da sauri ta ce, "Inno ni kuma? Ni ce zan kashe ki?"

"Duk gidan nan babu wanda ya ƙullace ni yake jin haushi kamar Dije dubi irin kallon da take yi mini, haushina take ji saboda na ce ta buɗe mini ƙofa na je wurin Dubu. Don Allah Garba ka gaya mini me na yi mata ko zargina take akan mutuwar mahaifinku?" Sam wannan maganar bata yiwa duka ƴaƴan Yaya Babba daɗi da cikin yanayin rashin jin daɗin maganarta ya ce, "Haba Inno me kike yi haka ne kowa fa a wurin nan ke yake kallo saboda Allah me mutane za su ɗauka jiya-jiya Mahaifinmu ya rasu amma kina wannan abubuwan." Ya ƙarasa maganar yana dafa ƙafarta.

"Sakar mini ƙafata Garba." Yaya Babba ta faɗa a hassale. Ba musu ya sakar mata ƙafa. Sai kawai ta miƙawa Hadiza hannu ta ce, "Allah ya jiƙanki ba don kin mutu ba Dije don Allah taimaka min zan koma ɗaki, ko a baƙar zuciyar Munkaila kina ga zai kaini ɗaki?" Hadiza ta girgiza kai tana murmushi, Yaya babba ta ci gaba da cewa, "Don Allah ki ce Garba ya matsa daga gabana ko na fice na bashi wuri." Gefe Baba Abubakar ya matsa Dije ta samu ta lallaɓata suka shige da Yaya Babba ɗaki. Suna niyyar tafiya daga wurin suka ji ƙarar abu tim! Daga bayansu. Da sauri suka waiga sai gani suka yi Inna Furai ce da ƙaton buhunta tana ja Auwalu shima yana ja wai dole a barta ta fita ta yafewa zaman cikin gidan. Ita ma sai da suka sha fama da ita sosai sannan suka samu ta koma ɗaki. Baba Abubakar ya dubi Dubu yace,

"Dubu ince idan muka je da ke za ki iya nuna mana ta wurin da kika ga fatalwar?" Dubu ta gyaɗa kai suna haɗa ido da Baba Munkaila ya watsa mata harara. Shi kansa Baba Abubakar zuciyarsa raya masa take tabbas akwai wanda yake son tsoratar da mutanen cikin gidan tun da wanda ya mutu ya mutu kenan har abada baya ƙara tashi. Dubu suka tasa a gaba tana gaba suna biye da ita a baya, sai wani ɗari-ɗari take ita Allah dole tsoro take ji.

Zu-gar mutane ne suka yi dafifi don ganin ta wurin da Dubu ta ga Fatalwa da idonta. Ita kuwa hakimar kanta sai ƙara girma yake musamman yanda ta ga mutane kowa ambatarta yake ana jinjina mata bisa ga ƙoƙarinta na tunkarar wurin. Daga can hanyar banɗaki suka hango wasu fararan kaya, daga nan wasu suka fara cin burki, sai kuma hular Marigayi Mai carbi da iska take kaɗa ta sama-sama. Mamaki da ta'ajibi ne ya kama su hatta Baba Munkaila sai da ya zubawa kayan ido, ɗaya tsagin na zuciyarsa na son aminta da abin da Dubu ta faɗa sakamakon kayan da ya gani. Amma yana tuna wace ce Dubu zai ji ya ƙi aminta da komai.

Baba Abubakar ne ya yi bismillah ya ɗebo kayan yana ƙare musu kallo zuwa can ya kalli Dubu yana shirin yi mata magana, sai kuwa ta zabura tamkar wacce aka ɗanawa wuta. Can bayan Zulfa'u ta maƙale tana cewa, "Baba Habu wallahi tsoro nake ji." Baba Munkaila ya karɓi kayan yana jujjuyawa sannan ya ce, "Amma gaskiya ana raina wa mutane hankali." Baba Abubakar ya yi gaba yana cewa, "Dole mu san abin yi amma tabbas akwai wata a ƙasa. Da alama wani ne yake son kawo yamutsi amma kowa ya kwantar da hankalinsa komai ya zo ƙarshe." Baba Munkaila ya hau muzurai yana zare idanu ya ce, "Koma wane ne ni da hannuna zan ci ubansa don na san na gida ne yake aikata wannan abubuwan. Amma duk wanda yake da hannu cikin wannan tafiyar sai na kusa tsinka shi gida uku." Ya ƙarasa maganar yana yi wa Dubu kallon idan ma ke ce za mu gauraya da ke.

Kafin wani lokaci tuni maganar fatalwa ta fara zaga cikin garin Ɗangwauro, har da masu isar da labarin abin da bai faru ba. Kasancewar kowa da abin da yake ji shi yake idarwa.

************

"Dubu ki kwantar da hankalinki idan ma don wannan ne kamar an yi an gama a wurina. Ba dai ni na haifi Garba ba?" Yaya babba ta ƙarasa maganar tana kallon Dubu cikin sigar lallashi.

Dubu ta tura baki gaba tana cewa, "To ai ke sai an gama magana da ke lafiya ƙalau sai kawai daga baya ki sake shawara, gaskiya ni dai ko ki sa mu koma birni gidansa ko kuma ki ce su dawo garin nan wallahi sai mun fi cin daɗi tun da anan me muke ci kamar ba ke kika haifeshi ba." Yaya Babba ta yi jim sannan ta ce, "Ba zan koma birni ba domin Malam har wasiyya ya bari akan kar mu kuskura mu bar gidan nan to kin ga saɓawa miji haramin ne amma Garba ko ya ƙi ko ya so dole ya dawo gidan nan da zama."

Baba Munkaila ne ya kawo kai zai shiga ɗakin Mahaifiyarsu amma ya ga mutane sun yi carko-carko a ƙofar ɗaki ya tambaya ko lafiya.

Hadiza ta taɓe baki ta ce, "Inno ce suke shawara da Dubu shi ne ta koro mu waje." Haushi ne ya ƙara kamashi don ya san duk iskancin da Dubu take yi Mahaifiyarsu ce take ɗaure mata. Ɗaga labulen ɗakin ya yi suna haɗa ido da Yaya Babba ta ce, "Kai Munkaila ka tara mini ƴan uwanka yanzun nan ina son magana da ku!" Kallon Dubu ya yi ya ga ta yi ɗai-ɗai a cinyar Yaya Babba, gudun neman magana ya sa bai tanka ba ya amsa ya fice. Don baya raba ɗayan biyu Dubu ce ta kitsa mata wata maganar.

Ba a ɗauki lokaci ba Iyalan Yaya Babba suka cika a ɗakin kowa da abin da yake ƙissimamawa zuciyarsa. Dubu na ganin haka ta saci jiki ta tafi haɗa kayan aikinta domin da alama tana ganin wankin hula zai iya kaita dare, don ta ga mutanen gidan ba su da alamar tafiya.

"Na san za ku yi mamakin ganin wannan taron amma ba wata doguwar magana bace. Gabaɗayanku so nake idan an yi sadakar bakwai kar wanda ya sa ƙafarsa ya fita daga gidan nan akwai babban taron da za mu yi gabaɗaya gidan nan. Musamman kai Garba tun da kaine babba." Yaya Babba ta yi maganar tana ɓata fuska don kar wani ya nemi kawo mata wargi. Suma ganin haka ya sa babu wanda ya musa mata sai dai cikin ladabi ɗayan bayan ɗaya suka ta shi suka fita kowa yana wani lissafi daban a zuciyarsa.

Baba Munkaila yana lura da duk wani shige da ficen Dubu sai dai kamar yanda ya sa mata ido ita ma tana ankare da shi. Yi ta yi kamar babu wani shiri da take haɗawa don shi kansa a wannan lokaci ya fara rage zarginsa a kanta.

Tun da yamma ta kawo kai doshin magriba ƙafafuwa suka fara janyewa daga cikin gidan kowa daga alwalar magriba ya riƙe abarsa don kowa a tsorace yake. Wannan dalilin ya sa zaman cikin gidan ya gunduri Hajiya Nafisa Matar Baba Abubakar da iyalanta. Allah ya sani ita dama ba ma'abociyar son zaman ƙauye ba ce, don ta kusa shekara biyar ba ta kwana a garin ba sai dai taje ta dawo a ranar, haka ma daga ɓangaren ƴaƴanta shi ya sa basu cika wani sakin jiki da mutanen gidan ba.

Bayan Sallar Isha'i.

Daga cen bayan ɗakin Marigayi suka fara jin kiran sallah da muryar Marigayi mai carbi. Kasaƙe mutane gidan suka yi aka rasa mai zuwa kiran Mazan da ke ƙofar gida don sanar musu da abin da yake faruwa. Don kowa hantar ciki ta kaɗa saboda lokacin dare ma bai gama yi ba don ko tara na dare bata yi ba.

Tana gama kiran sallar ta fara wasa wuƙa ji kake , "Kuyat! Kuyat" Sai da ta ƙara matsowa hanyar cikin gidan ta fara wani irin kuka mai kamar haniniyar doki. Gidan tsit ya yi kamar an yi ruwa an ɗauke tun da Dubu ta ji haka cikin muryar marigayin Kakanta ta fara cewa, "Da alama yau za mu ɗebi mutanen gidan nan da yawa. Amma duk wanda ya cinye tuwon daren yau ya tsira ba za mu taɓa ko ta fatarsa ba."

Daga can ɗakunan mutanen ɗakin nɓa jin haka suka fara kantamar tuwon da ko minti ashirin ba a yi da kwasarsa ba. Da zafinsa suka rinƙa ci saboda tsira daga kaidin tawagar fatalwa. A ɗakin Inna Furai faɗa ne ya ɓarke tsakanin Lantan da Inna Furai akan suɗin kwano har Lantan ta ji haushi ta kwalawa Inna Furai silba a goshi.

Dubu na daga wurin da take laɓe tana jin hayaniyar mutane sai da ta kintaci lokaci, ta fara wani irin nishi mai ban tsoro tana cewa, "Duk wanda ban ji sautin tusarsa ba shima wallahi babu mai hanamu ɗaukansa a daren nan."
*DUBU JIKAR MAI CARBI*


©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*


FREE PAGE 4


Wannan karon gabaɗaya turus suka yi da jin abin da aka faɗa, kallon-kallo aka fara yi a tsakanin juna kowa da abin da yake nazari a zuciyarsa. Suna cikin haka suka sake jin an ce, "Bismillahir rahmanirrahim bari mu fara ɗauka daga kan ta bakin ƙofa." Ai Dubu bata rufe baki ba sai ji ta yi alamar guje-guje, Yahanasun Auwalu tun bayan sallar asuba da ta shiga ɗakin Inna Furai ba ta sake fitowa ba kuma ta ci alwashin ko da fitsari za ta ji sai dai ta matse abin ta, idan ta kama ma sai ta saki abin ta a wurin. To ashe tsugunne bata ƙare mata ba tun da har fatalwar za ta iya kawo musu farmakin dare har cikin ɗakuna, tun da ta ji an ce za a fara ɗauka daga na bakin ƙofa.

Nabila ƴar wurin Hajiya Nafisa, budurwa ce don ta yi sha tara a shekaru. Turo baki ta yi tana cewa, "Maganar gaskiya Mommy ni fa na gaji da wannan abubuwan kullin abu ɗaya wacce irin fatalwa ana zaune ƙalau bayan kowa ya san babu wata fatalwa a musulunci." Cike da ƙosawa Hajiya Nafisa ta ce, "Nabila ya za mu yi kin san dai ba mu da ta cewa tun da zuwan nan na dole ne ya kama mu haka Allah ya ƙaddara mana." Yaya Babba da ke gefe fuskarta ban da gumi da maiƙo babu abin da take yi, ta dubi Hajiya Nafisa da kallon sheƙeƙe ta ce, "Ke Nafi! Zuman ku a gidan na shi ne ƙaddara? Wallahi za ki ga ƙaddara kuwa ganin idonki. Wannan gidan da kike gani kin zo kenan zuwa sojan badaskare." Tana gama faɗa ta yi ƙwafa a zafafe. Dubu daga wurin da take ta jiyo hayaniya na tashi kaɗan-kaɗan ta sake shaƙe murya ta ce, "Ƴan sama jannati basa lamintar kuskure don haka za mu fara bi ta kan dabbobin gidan kafin mu fara taɓa mutanen ciki, ina tawagar Fatale ku fara dirowaaaa." A hankali ta lallaɓa da sauri ta buɗe ɗakin zabbin Baba Munkaila. Hannunta riƙe da muciya ta fara buga ƙyauren langa-langar da ke jikin ƙofar. Nan da nan zabi suka fitowa a tsorace suka fara tsalle da kuka "Ƙurƙet! Ƙurƙet!" Da yake da hasken wutar lantarki tuni zabbi suka fara bazama suna kuka, Dubu ta sa muciya ta riƙa make kawunansu ɗaya bayan ɗaya. Da ta bugawa zabo ɗaya sai ka ji ya yi ƙara ya faɗi ƙasa. Wannan kukan Zabbin ba ƙaramin ɗaga hankulan mutanen da ke cikin ɗakunan ya yi ba. Shiru suka yi suka zurawa sarautar Allah ido. Kowa da abin da yake ayyanawa zuciyarsa. Sai dai a wannan ƙadamin Lantan ta ci alwashin matuƙar tana da rabon ganin wayewar gari, babu wanda zai hanata tafiya don tun da ta zo duniya bata taɓa ganin masifa da tashin hankali irin wannan ba.

Zabbin nan gabaɗaya haka suka warwatsu suka shiga sauran sashen da ke cikin gidan. Muhsana ita ce ƴar autar Lantan, ta taho daga can sashen Baba Sule ba ta san abin da yake faruwa ba ta hangi Zabbin Baba Munkaila suna guje-guje wanda ya tabbatar mata da alama akwai abin da yake faruwa. Gabanta ne ya faɗi sakamakon ganin gawarwakin Zabbi kusan bakwai a ƙasa jini duk ya ɓata wurin. Sai dai har lokacin bata ga wanda yake aikata wannan abin ba, ɗaya zuciyarta ce take raya mata ko dai da gaske Fatalwar da ake faɗa ce ta fara aikinta, yayin da ta ƙara riƙe hannu Ɗanta Salihu don dama yaron ne ya fito da ita zai yi kashi. Ta bayan ɗakin Marigayi mai carbi ta je wucewa ba ta yi aune ba sai ji ta yi an fisgi hannun Salihu, aikuwa kusan tare suka ƙwalla ƙara daga ita har Salihun da ake ja, jan Salihu ta riƙa yi tana yi tana ihun neman agaji amma ba a daina jansa ba. Dubu na ganin Muhsana ta kusa fin ƙarfinta ta raɗa mata muciyar a baya tana cewa, "Ki taho mu yi rayuwar barzahu da ke. Ko ki bani Ɗanki Salihu na tafi da shi, ko kuma na ɗauke ku gabaɗaga." Muhsana bata gama jin ƙarashen maganar ba ta saki hannun Salihu ta yi cikin gida da gudu tana tafe tana sosa wurin da Dubu ta maka mata muciya. Shi kansa Salihu da ba a yi masa komai ba ya gama tsorata, dama jikinsa babu riga babu wando haka ya zuba a guje da tiƙeƙen cikinsa a daidai lokacin aka ɗauke wuta Salihu ya rasa wurin da zai bi haka ya riƙa gware da bango yana make sauran zabbin da suma ta kansu suke yi.

Ihun da Salihu yake yi ne ya tabbatar musu da lallai Fatalwa ta fara zuwa kan bil'adam, tun da; da farko sun ji kukan zabbi. A wannan lokacin Yaya Babba da ƙaramin tsorata ta yi ba don ko kaɗan Dubu bata faɗo mata a rai ba bare ta ambace ta. Lantan da ke ɗakin Inna Furai ta fara hawaye bibbiyu don saboda firgici ta tuɓe kayan jikinta ta sake saka su ya fi sau bakwai. Lokacin da ta riski muryar Muhsana na ihu, kuka ta riƙa yi wiwi don Mushana ita ce autarta. Da ta daina jin kukan Muhsana sai na Salihu wannan ne ya bata tabbacin tuni Tawagar Fatalen sun gama da Muhsana sun koma kan Salihu. Da ƙyar Salihu ya samu ya isa wurin ɗakuna ya fara lalubawa yana kuka, hannunsa ya ɗora akan ƙofar su Inna Furai yana bugawa yana faɗin, "Innaaaaa! Iyaaaa" Lantan na jin haka ta ɗare saman gadon Inna Furai hannunta riƙe da ɗan kanfen Badariyya tana ta tura kai duk a tunaninta rigarta ce za ta saka. Inna Furai wani farfari ta riƙa yi kamar wacce take kan hanyar suma, sai motsa baki take tana addu'a.

Zabbin da suka tarwatse wasu daga cikin su hanyar waje suka yi, suna kuka a firgice. Dubu tun da ta ga an ɗauke wuta ta haye katanga ta dira ta bayan gidan. Sai ga ta kamar mumina ta wuce shagon Lamarana ta siyo maganin sauro, da sauran wata hamsin ɗinta. Zuwanta ƙofar gidansu ya yi daidai tashin Baba Munkail kenan yana kaɗa Zabbin da ya ga suna tsalle suna fitowa ɗaya bayan ɗaya. Mutanen wurin ne suka fara taya shi, Dubu na zuwa ta zabga uwar sallama, ta yi haka ne saboda Baba Munkaila ya ganta don ta sake cire zarginta da yake daga kanta.

Cikin masifa ya fara yi mata magana, "Dallah sakarai matsa kina gani zabbina na fitowa sai wani ya ɓace a cikin duhu." Da sauri ta matsa gefe ta ce, "Baba Munkaila don Allah ara min fitila na kaiwa Inna Maganin sauronta tsoron soro nake." Ci kanki bai ce mata ba har suka samu suka kame zabbin, ban da masifa babu abin da Baba Munkaila yake yi, don a duniya idan kana son ganin ɓacin ransa cikin gaggauwa ka taɓa masa zabbinsa ko kuma wani laulawar keken hawansa. Yana

Please Login or Register in order to submit comment