Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gida don Allah maganar gaggawa ce ina son ganinki." Hajiya Ikilima ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Gani nan zuwa yanzu kuwa amma ince dai mijinki baya nan ko? Don kinsan gani yake kamar ni nake zuga ki shi ya sa ma bana son zuwa idan yana nan." A ƙagauce Hajiya Nafisa ta ce, "Ba fa ya nan ya can ƙauyensu ni dai sai kin ƙaraso." Daga haka suka yi sallama, Hajiya Nafisa ta fara sintiri a cikin ɗaki.

Tana nan tsaye ta ji sallamar Aseem, tun bai tufe baki ba ta fita falon idanu a ƙanƙance ta fara magana: "Aseem yanzu saboda Allah wannan tsohuwar ta yi mana adalci kenan? Saboda Allah a ce duk abin da waccen ƴar iskar yarinyar, mai zubin sheɗanun ta gaya mata da shi za ta yi amfani. Wacce rayuwar za mu tsinta a zaman ƙauye? Tun da ba ta ce mu koma ba sai da ta ga yaranmu sun zama ƴanmata wato yanda waccen za ta zauna a ƙauye tana baƙincikin su Nabila su sami miji a birni. Da sake wallahi, Allah sai dai Mahaifinka ya zama ko zaman ƙauyen ko kuma mu raba gari."

Dama ya san za a rina don haka ya shiga sashen mahaifiyar tashi don ya samu ya taushe ta. Amma maganarta ta ƙarshe ta fi firgita hanjin cikinsa, saboda tun da yake bai taɓa jin makamanciyar wannan maganar daga bakin Mahaifiyarsa ba. Shi kansa sheda ne duk irin ɗabi'un Mahaifiyarsa na rashin haƙuri amma mace ce mai kyawawan ɗabi'u. Matsalarta ɗaya rashin haƙuri da kawar da kai sai kuma son kanta da saurin ɗaukar zuga, amma bayan wanna baya jin tana da wasu halaye marasa kyau.

Cikin sigar lallashi ya kalli mahaifiyarsa ya ce, "Don Allah mommy zauna mu yi magana." Bata musa ba ta zauna a kan kujera tana kallonsa. Aseem ya ci gaba da cewa, "Mommy don Allah ki kwantar da hankalinki wannan fa ba abin tashin hankali bane. Kamata ya yi a ajiye maganar nan agefe har zuwan bayan sadakar bakwai, amma Mommy kun taho gida ke da su Nabila da Aunty kina ganin Daddy zai ji daɗi?"

"Dama ban aikata haka don jin daɗinsa ba, Aseem idan kana da wata maganar bayan wannan ka yi amma magana ɗaya za a gaya mini na saurara cewar mun fasa komawa ƙauye. Ina nan wallahi mahaifinku zai dawo ya same ni." Tashin hankali wanda ba a sa masa rana. Miƙewa Aseem ya yi ya ce, "Allah ya huci zuciyarki Mommy amma hakan sam bai dace ba yanzu idan Iya ce (Mahaifiyar Hajiya Nafisa) ta ɓata miki rai na san ba za ki yi haka ba, kin ga Daddy shi ma gani zai yi don ba mahaifiyarki ba..."

"Fita ka bani wuri" Hajiya Nafisa ta faɗa tana nunawa Aseem ƙofa azafafe. Sum sum sum ya miƙe zai fita ta ci gaba da faɗa, "Ai wallahi dama na sani wannan zaman daɓaron da tsohuwar nan take zuwa duk lokacin dana haihu ba banza ba, ta gama asirce mini ƴaƴa fa magane-maganen da take basu tun jarirantaka. Ban da lalacewa kai ba me shigar mana ba ne sai inda ƙarfinka ya ƙare, a'a kai gudun ɓacin ran mahaifinka kake yi." Aseem ya fice daga falon ya bar Mhaifiyarsa tana da sababi.


Gidan Baba Adamu.

Hajiya Rahama ita kaɗai ta ƙule a ɗaki tana nazari, lokaci ɗaya ta ji kamar ba su kyauta da abin da suka yi ba domin suma idan mahaifansu ne dole su yi musu biyayya. Tashi ta yi jiki a sanyaye ta nufi sashen Kishiyarta Hajiya Fauziya, a falo ta same ta tana waya, tana ganin Hajiya Rahama ta ce, "Ok, ba damuwa za mu yi waya an jima." Hajiya Rahama ta kalli Hajiya Fauziya ta ce, "Mamin yara na zo mu yi magan." Kujera ta nuna mata fuska ba walwala ta ce, "Zauna ina jin ki."

"Gani nake kamar ba mu kyatawa Alhaji ba, saboda Mahaifiyarsa tamkar mahaifiyarmu ce idan ta mu mahaifiyar ce muma babu yanda muka iya dole mu yi mata biyayya. Kina gani ko sadakar uku ba a yi mun taho gani nake gaskiya akwai..." Tun bata ƙarasa ba Hajiya Fauziyya ta katse ta da cewar,

"Don Allah idan wannan ne ya kawo ki kwashi tsummokaran ƙafafuwanki ki ƙara gaba, bana son kutungwila da shegen iyayi kamar ta macen kyankyaso. Kin san da haka kika ɗebo ƙafa kika taho ai sai ki tashi ki koma ba sai kin zo min ba." Hajiya Rahama ta miƙe tana cewa, "Ni na kawo kaina duk abin da kika faɗa, nina ja wa kaina."

"Oho fice ki bani wuri tun da ban gayyatoki ba, kinibabbiya kawai." Hajiya Fauziyya ta faɗa tana huci kamar wacce ta yi tseren gudu."

Hajiya Rahama na komawa sashenta ta samu ana kiran wayarta, tana dubawa ta ga lambar maigidansu har sai da hanjin cikinta ya kaɗa, da ƙyar ta yi ta maza ta ɗauki wayar da sallam. Bai amsa mata ya fara da cewa, "Rahama ina yi miki kallon mai hankali ashe ba haka ba ne. Kun nuna mini Mahaifiyata bata isa da ku ba, kun kama hanya kun taho ba tare da izinina ba. Na gode kun nuna min ni kaina ba wata tsiya bace a wurinku." Jiki a sanyaye Hajiya Rahama ta ce, "Don Allah ka yi haƙuri Alhaji wallahi nima na yi nadama amma yanzu zan taho insha..."

"Duk wacce ta sake ta fito daga gidan nan wallahi-wallahi a bakin aurenta. Tun da kun riga da kun yanke hukunci shi kenan, rasuwa dai Mahaifina ne ya rasu bana buƙatarku kuma komawa Ɗangwauro kamar mun koma mun gama, duk wacce ta ga za ta koma bismilla wacce ta ga ba za ta iya ba za ta iya komawa gidansu. Ita ma waccen zan kira na shaida mata." Yana gama maganar ya katse bai jira cewarta ba. Lokaci ɗaya ta ji duniya ta yi mata zafi don ita kanta ta san abin da suka yi ba su kyauta ba.

Gidan Baba Abubakar.

Hajiya Ikilima ce zaune cikin mamaki ta dubi Hajiya Nafisa ta ce, "Wai wannan maganar da kike gaya mini da gaske ne ko kuma zolayata kike yi?" Haushi ya fara kamata da jin kalaman aminiyar tata ta ce, "Ƙawas kin san bama irin wannan wasan da ke. Serious ki bani shawara Allah dana koma Ɗangwauro gara aure ɗna ya mutu da bawan Allahn nan." Cikin zuciyar Hajiya Ikilima ƙyal saboda farinciki don ta jima tana hangen kanta a gidan wannan baƙin bafulantin mai cike da kwarjini, amma ina ƙawarta ta yi mata shamaki. Ta dube ta da fuskar tausayi ta ce, "Gaskiya dole ki ɗau mataki kika koma ƙauye wallahi kin faɗo, yanzu abin yi ki shirya na raka ki Ƙauyen tudun-wada akwai wani Malami yana taimako wallahi, zai taimaka miki sosai ke ko kashe tsohuwar nan kike son yi murus za a gama da ita." Hajiya Nafisa ta zaro ido waje tana faɗin, "Kin san fa ni bana haɗa hanya da ƴan tsibbu shawarwarin da kika saba bani dai su za ki bani. A kashe ta, ta rataya a wuyana. Ba za a yi haka ba kedai..." Bata ƙarasa maganar ba Aseem ya shiga falon don sarai ya ji abin da suke tattaunawa, sai ya wuce kan daininga da kofin shayi a hannu yana danne-dannen waya. Hajiya Ikilima ta saci kallonsa cikin ƙasa da murya ta ce, "Ko dai ya ji mu?" Hajiya Nafisa ita ma kallonsa ta yi sai ta ƙanƙance murya ta ce, "An ya kuwa amma bari ki ga." Hajiya Nafisa ta kalli Aseem ta ce, "Aseem jeka ɗakina ka ɗauko kuɗi akan mudubi ka tsallaka titi ka siyowa mamanka fura." Babu yanda ya iya haka ya tashi ya tafi kamar zai yi kuka don ya so jin ƙarashen hirar tasu. Dama ya jima yana zargin wannan matar da zuga mahaifiyarsu ashe kuwa ita ɗin ce take zuga ta.

Yana fita Hajiya Ikilima ta ci gaba da ɗora Hajiya Nafisa akan shawarar banza. Sai dai abin da kullin yake ɓata mata rai duk yanda take son ɗora Aminiyar tata akan biye-biyen malamai taƙi bada kai bori ya hau, kuma da haka take son cimma ƙudurinta akanta amma bahaushe ya ce a juri zuwa rafi watan tulu zai fashe.

Bayan Sadakar Bakwai.

Dubu ce tafe za ta tafi makarantar Islamiyyar Malam Jafaru, tana tafe da ƴar maƙalaliyar jakarta ta buhu tana rera waƙar Bureka (Breaker) ta Jaruma, idan ka ji yanda take rairawa sai ka rantse ita ta biyawa mawaƙin waƙar. Ɗan'iya da ke tafe da Mahaifiyarsa ya ƙwala mata kira. "Dubu!"

Dubu ta juya hagu da dama sai a can daga nesa ta hango Ɗan'iya ai kuwa ta yashe baki, tana ɗaga masa hannu. Ɗan'iya sai da ya ga sun ɗan yi nisa da Dubu sannan ya ce, "Dubu mai kan Silba mun san komai ashe ƙwaryar molo aka yi miki." Lawandi da taron abokansa da ke bakin bishiyar dalbejiya me za su yi idan ba dariya ba. Ma'azu har da tuntsirawa kamar zai faɗi ƙasa. Wannan abu ba ƙaramin ɓata ran Dubu ya yi ba, ta tattakura ta ɗaga murya da cewa, "Eh na ji ɗin Ɗan gidan Balaraɓe kwarton dare" Da sauri su Lawandi suka riƙe baki kasancewar dama ana ta raɗe-raɗin wannan zargin da ake wa Balarabe ashe har kunnen yara ya fara bazuwa.

Hansatu mahaifiyar Ɗan'iya ta nufo wurin Dubu a fusace tana zuwa ta ce, "Iskancin na ki yau akan mijina ya sauka? Dan uwarki za ki ƙara cewa mijina kwarto?" Bata rufe baki ba sai da ta zabgawa Dubu mari sannan ta ɗora da cewa, "Wallahi ba Balarabe ba ko Bala na sake ji a bakinki sai na yi ƙasa-ƙasa da ke. Na lura iskancinki ƙara yawa yake saboda baki da mafaɗi..." Dubu ta fisge hijabinta tana cewa, "Allah ya isa kuma wallahi bashi kika ɗauka. Na faɗa waye bai san Balaraɓe kwarto bane har ɗakin Baba Auwalu sai da ya taɓa leƙawa lokacin da Yahanasu tana amarya. Banza kina gida kina tare da ɗan iska..." Kukan kura Hansatu ta yi ta fisgo Dubu ta fara jibga kamar Allah ya aikota. Jin Hansatu na niyyar hallakata ya sa ta fara kiciniyar ramawa, ai kuwa Hansatu ta cukwikwiye Dubu a cikin hijabi ta riƙa dukanta ta ko'ina sai da ƙyar su Lawandi suka ƙwaci Dubu. Suna fisgarta sai ga hijabinta a hannun Hansatu nan fa kan Dubu ya fito ral da shi yana ƙyalli don ranar Yaya Babba ta sharɓane mata shi da man kaɗanya. Nan Ɗan'iya ya fara tafi yana cewa, "Yeeh Dubu mai kan Silba (Silver)" Ai kuwa kafin wani lokaci tuni yara suka taru ana kallo, dukda tsoron da suke yi wa Dubu amma ruruma ta ɗauke hankalinsu suka fara sowa da tafi suna cewa, "Yeeh Dubu mai kan silba."

Idanun Dubu ne suka kaɗa jawur saboda baƙin ciki, sai dai har lokacin idanun Dubu a bushe suke babu ko ɗison hawaye don gudun kar a ga hawayenta yara su rainata. Cikin takaici ta kalli Hansatu ta ce, "Kwarankwatsa dubu bashi kika ɗauka kuma da ni kike zan cen." Ta juya ta kalli sauran yaran da suke tsokanarta ta ce, "Ku kuma za mu gauraya da ku kowanne shege sai na sa an harbe Uwarsa." Tana gama maganar ta suri jakarta da ke cen gefe ta fisgi hijabinta ta ɗora aka ta yi tafiyarta. Sai dai kusan rabin yaran jikinsu ya yi sanyi don suna tuno Yayan Dubu soja ne hantar cikinsu ta kaɗa har da masu bin ta suna bata haƙura amma babu wanda ta waiga, bare ya sa ran za ta amsa masa.

Dubu tun daga soron gidansu ta fara barke baki tana ihun kuka, amma ci kanki babu wanda ya tanka mata saboda sanin hali irin nata. Matan kawunan nata suna gani ta wuce cikin gida. Tana zuwa sashen su Yaya babba Inna Furai ta tare ta da tambaya, "To ƴar nema wa kika tsokano wanda ya fi ƙarfinki?" Dubu ta goge majina da hijabin hannunta sannan ta kuma yage baki tana ihu har sai da Yaya babba ta fito tana tambayarta.

"Inno wallahi daga yau ba zan ƙara fita waje ba. Ki dubi irin cin mutumcin da Hansatu ta yi mini ita da Ɗan'iya yau kashe ni ne kawai ba ta yi ba. Yara suka taru suna ce mini mai kan silba. Ni dai wallahi Allah ya isa da askin nan da azzalumin nan ya yi mini." Dubu ta faɗa tana sake fashewa da kukan baƙinciki, don abin ba ƙaramin ciwo ya yi mata ba. Yaya Babba ta karɓe zan cen da cewar:

"Wallahi faɗi ki ƙara Dubu Allah ya iskan ki, don Allah me kika tsarewa Soja da zai sauke miki gashi ana zaune ƙalau? Hassada dai ka rasa wa za ka yi wa sai jininka. Na rantse da Allah ko uwarsa Nafisa ba za ta gwada miki gashi ba. Kanta da har gobe kamar hamtar ɗan isa ga uban sanƙo da almajiran ƙeya. Wallahi ni bansan abin da Garba ya gani a jikin gajeriyar matar nan ba ya aura, mace sai faɗin ran tsiya tana baje hanci kamar tattasai ya ji sanyi wuri." Dubu ban da tuntsira dariya babu abin da take yi har da hawaye saboda ƙeta don tuni ta goge hawayen idonta saboda ko ba komai Yaya babba ta biya ta, da ba'ar da ta yi wa mahaifiyar Aseem.

Inna Furai da ke gefe ta sa dariya ta ce, "Yaya ai ba za ki ga baje hanci ba sai ta shiga gaban mota yanda kika san funkaso." Sai kuwa suka sake kwashewa da dariya. Yaya Babba ta ce, "Furaira wai dama ranar da muka fita da Garba tana gaba kina ankare da ita?" Inna Furai ta ce, "Ina gani mana wai har ca take ka saya mana wani abin mana a danja wai ita mai miji." Ai kuwa dubu me za ta yi idan ba dariya.

Yaya babba ta saki dariya ta ce, "Furaira alƙur'an ni kuma fuskar Nafisa ta ƙi ɓace mini lokacin da muka karɓi haihuwarta ta wannan yaron soja kin tuna lokacin har cewa take wai Inno zo na goyaki. Na ce mata ke Nafisa rabani da zancen goyon nan, rabona da goyo tun shekaru tsububu sai yau da kike nakuɗa za ki goya ni, na turmushe ki Garba ya ɗau gaba da ni." Inna Furai dariya har da hawaye sannan ta ce, "Yoo kafin ki zo har cewa take Inna karɓi cikin, na ce Nafisa lamari ya lalace ina Uwar Garba na karɓi cikin Garba ai ba kanta sai cewa ta yi har Garban na bar miki gabaɗaya." Dubu ta kife a wurin ban da dariya babu abin da take yi.
*DUBU JIKAR MAI CARBI*


©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*


FREE PAGE 9
https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels

Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.

Sallamar Baba Munkaila ne ya dawo da Dubu cikin hayyacinta, ba shiri ta shiga nutsuwarta ta fara kumbure-kumbure don ta san babu makawa zai samu labarin abin da ya faru tsakaninta da Hansatu. A daidai kan Dubu ya tsaya fuska babu walwala ya ce, "Ke!" Kamar bata ji shi ba ta yi biris, sai da ya sake buga mata tsawa sannan ta amsa. Cikin faɗa ya ci gaba da cewa, "Dubu ki kiyaye ni fa, kullin iskancinki da iya shegenki ƙara gaba yake ko? Ƴar ƙanƙanuwarki da ke har kin isa tarar matar aure ki ce za ki yi dambe da ita. Wallahi a hir ɗinki idan kika shiga hannuna na lahira sai ya fiki jin daɗi." Dubu dama kamar me jira yana dire zancensa ta fashe da kuka tana faɗin, "Dama na san komai ni za a ɗorawa alhalin ita ce bata da gaskiya." Rankwashi ya sakar mata a tsakiyar ka aikuwa ba ƙaramin shigarta ya yi ba, a zabure ta yi gefe ai kuwa Yaya babba dama ta fara cika ta dubi Baba Munkaila cikin faɗa ta ce, "Munkaila nakasa marainiyar Allah za ka yi? Ka duba irin ƙusar da ka sakar mata a tsakiyar ka sai ka huda mata kai, ka cuceni ka cuci Ado. Ko da ya kasance likita ba sai an sayi magunguna da alluran da za a yi mata aiki ba. Gaskiya bana so ka fita rayuwar yarinyar nan shi ya sa ga tana kamar ruwan aski kullin bata kumari." Baba Munkaila bai tankawa Yaya Babba ya dubi Dubu ya ce, "Tashi ki ɗau hijabinki ki wuce makaranta. " Tun bai rufe baki ba Dubu ta suri kayanta ta fita waje tana kurma uban ihu.

Inna Furai ta ja tsaki ta dubi Baba Munkaila ta ce, "Munkaila wai me ya sa ko yaushe burinka ka zazzagewa yarinyar nan albarkar da ke kanta? Yanzu da ka kaɗa ta waje idan ta shiga gari wa ya shiga uku idan ba mu ba." Yaya babba ta cafe zancen da cewa, "Wallahi idan na rasa Dubu hukuma ce za ta raba ni da Munkaila dama na daɗe ina zargin ba ƙaunarta kake ba." Baba Munkaila ya yi murmushi sannan ya ce, "Inno yanzu so kuke a zurawa Dubu ido ta taso babu nutsuwa da rashin ilimi? Kuna ganin Fatima yarinyar nan kowa sha'awarta yake, saboda ilimin addininta. Mu kuwa wa yake sha'awar Dubu? Ku shaida ne a rana sai a kawo muku ƙara ta yi sau goma. Amma Inna furai ai bai kamata mu zura mata ido haka har girmanta ba."

Yaya babba ta yi shiru tana nazari sannan ta ce, "Munkaila ka yi tunani, kuma wallahi ina jin hannu aka sawa Dubu dole na sake nema mata maganin baki don wallahi baki ba ɗan'uwa ba ne." Baba Munkaila na ganin ya yi wa Tsofaffin iyayen nasa dabara ya tashi ya fice daga gidan.

Dubu na fita ta goge hawayenta ta maƙale jakarta ta ɗauki hanyar islamiyya, sai dai tana saƙa da warwarar abin da za ta yi wa Hansatu don ta fanshewa abin da ta yi mata. Kamar daga sama tana shan kwanar hanyar da za ta sadata da makarantarsu sai ga Ɗan'iya ya fito da tallar wake da shinkafa a kansa, hannunsa na riƙe da bokitin ragadada. Yana ganinta ya yi baya da sauri a tsorace don ya san mai ƙwatarsa a hannun Dubu sai Allah, don haka bai yi wata-wata ba tun Dubu bata tanka masa ba ya fara cewa, "Dubu don Allah ki yi haƙuri wallahi ba zan ƙara ba." Kamar wani abu bai haɗasu ba, haka Dubu ta basar da Ɗan'iya ta ce, "Da aka yi me?"

Ɗan'iya ya washe baki ya ce, "Faɗanki da Innarmu mana." Dubu ta zurawa bokitin ragadadar hannunsa ido, take ta ji yawunta ya tsinke, ta kai hannu za ta taɓa ya janye da sauri. Dubu ta riƙe ƙugu tana jinjina kai sannan ta ce, "Ɗan'iya wallahi ko ka bani bokitin nan ko kuma in haɗa gabaɗaya da Shinkafa da waken da shi bokitin ragadadar in kifar da su don wallahi wannan rigimar mun fara ta kenan ni da ku."

Tun ba ta rufe baki ba Ɗan'iya ya soma hawaye ya ce, "Don Allah ki mun rai wallahi Innarmu duka za ta yi min." Dubu ta yi dariyar mugunta ta ce, "Idan ka koma gida in ta tambayeka ka ce ta zo gudanmu ta karɓi kuɗinta." Ɗan'iya ya fara ja da baya Dubu na tsaye ta ce, "Tsaya-tsaya Ɗan'iya gaya mini duka kayan naka na nawa-nawa ne?" Ɗan'iya a tunaninsa rangwame Dubu za ta yi masa idan ta ji tsadar abinci ya taƙarƙare da ƙarfinsa ya ce, "Shinkafa da wake na Dubu biyu ne Ragadadar dubu ɗaya ce." Dubu ta yamutsa fuska ta ce, "To Allah ya yi belinka saboda wallahi da babu kayan nan sai na jiƙa maka jikinka, amma yanzu dole za ka bani bokitin ragadadar nan wallahi, ko in haɗa da kai da su duka na damalmale ku a cikin ƙasa." Ɗan'iya ya yi shiru yana nazari don ya san ciniki ko hamsin ne babu a ciki, Innarsu cin ubansa take bare bokitin Ragadada gabaɗaya. Ragadadar da sai sun yi da gaske suke samu Mahaifiyarsu ta ke basu yanka ɗaiɗai yau ita ce zai ɗauka ɗungurungun ya bada bokitinta.

Dubu na ganin haka ta buga tsalle tana ƙoƙarin janyo robar shinkafar, Ɗan'iya na ganin haka ya miƙa mata da sauri don kar ya yi biyu babu. Wani wawan kuka ya saki lokaci ɗaya ya juya zai koma gida Dubu ta sha gabansa ta ce, "Maza wuce wallahi ba za ka koma gida yanzu ba sai ka sayar da abincin nan salan ka min mugunta tun ban gama cinyewa ba ka sa azo gidanmu. Munafiki yana zare idanu kamar shege a rabon gado." Ta ƙarasa maganar tana ɗake masa ƙeya. Babu yanda ya iya haka ya nufi titi yana share hawayen fargaba da tashin hankali.

Dubu sai da ta saita Ɗan'iya ya bi titi sannan ta bi wani layi bata tsaya ko'ina ba sai cikin wani sabon gini da ba a ƙarasa ba. Zama ta yi dirshan ta kwashi ragadada tana ci tana siɗar romo, kafin wani lokaci tuni ta cinye shi tas, saboda ba ƙaramin daɗi ya yi ba, ya ji farin magi zaƙwai ga ɗan yaji-yaji. Tana gama ci ta sa gefen hijabinta ta goge baki. Ta ɗauki bokitin ta cika shi da yaji ta ɓoye a cikin hijabi ta fice daga cikin kangon.

Dubu bata tsaya ko'ina ba sai ƙofar gidan Hansatu, Hansatu na tsaye a kan ƴarta Mairo da take ta zuba ragadada a ƙananan robobi, ta hango Dubu tsaye a ƙofar gida. Suna haɗa ido Dubu ta ƙarasa ciki kamar mutuniyar kirki ta ce, "A bani ragadada." Tana maganar tana sakin wani irin murmushi. Hansatu ta hangame baki tana yi wa Dubu kallon mamakin wato rashin kunyar Dubu ta bunƙasa haka. Balabare da ke bakin bishiya yana sharɓar ragadada ya yi zaraf ya ce, "Dubulliya ta nawa za a baki?" A fusace Hansatu ta ce, "Ta nawa za ki siya?" Ba musu Dubu ta miƙa naira ashirin nan fa Balarabe ya fara leƙenta yana kashe mata ido ɗaya. Dubu ta ɗauke kai kamar bata gan shi ba. A fakaice Dubu ta sunkuya tana gyara takalminta ta cikin hijabi ta dire mata bokitin ragadada, ta bayan ƙatuwar tukunyar ragadadar. Ta matsa can gefen bishiyar da Balarabe yake zaune. Hansatu mace ce mai matuƙar son kuɗi don duk abin da zai haɗa ku da ita muddin ka zo siyan abu wurinta bata zuciya. Tana da tsumulmula saboda ko ita bata iya zagewa ta ci ragadada idan ba mijinta Balabare da Allah ya jarrabeta da mutuwar sansa ba. Duk abin da Balarabe ya tambaya ba ta iya hana shi. Don haka a ƙa'ida kullin ta sauke tukunyar ragadada kwanonsa daban yake, kuma ko kara ya ajiye ba za ta iya tsallakawa ba.

Hansatu na ɗauko leda ta shiga wurgawa Dubu harara sanna ta fara zuba mata, za ta ƙulle ledar Balarabe ya ce, "Ke Hansatu ƙara mata ta hamsin." Ai kuwa kamar ya watsa mata ruwan zafi ta ɗago a zafafe ta ce, "A kan wane dalili za ka siya mata bayan ɗazun nan yarinyar nan ta gama ci mini mutumci..." Nan fa Hansatu ta zayyanewa Balarabe yanda suka yi, kamar ta rufe bakinsa shiru kake ji sai dai sam ba haka ya so ba, Dubu na karɓar ragadadarta ta nufi hanya za ta fita sai ga Ɗan'iya ya shiga gidan yana kwala ihu.

Da kallon mamaki ya bi Dubu har ta fice, Hansatu don sauri zaninta har faɗuwa yake. Ta fara jefo masa tambaya a hargitse, "Ɗan'iya ina bokitin ragadadar?" Tun bata rufe baki ba ya hau nuna ƙofa ya ce, "Dubu ce ta karɓe mini." Ai kuwa kamar wanda ya ɗanawa wuta haka Hansatu ta zabura tana cewa, "Buhun uban can, kai buɗe baki ka yi mini magana yanda zan fahimta." Dubu na jin haka ta fara zuba sauri bata tsaya ko'ina ba sai islamiyya.

Ɗan'iya ya zayyanewa Mahaifiyarsa abin da ya faru. Hansatu na jin ƙarashen labarin ta shuri takalma garin ɗaukan takalmi ƙafarta, ta shuri bokitin Ɗan'iya da ke

Please Login or Register in order to submit comment