Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ai baka ma ji komai ba awannan labarin me akayi da maza inji karya? Abin ma da yanzu muka fara ai labari saima tubanina ya karaso tukunna. Ya danyi shiru sannan sai yace.
.
Nas sa'ar da falmata ta shigo dakin shakatawar jikinta na rawa saita wuce kai tsaye zuwa bandakin datayi wanka dazu aciki tana zuwa saita kalli mudubi. Tsoro da fargaba suka damki zuciyarta sa'ar data ga duk kammninta sun sauya kwalliyarta ta baci fuskarta tayi fari fat. Kamar taga fatalwa. Cikin sauri ta dauke kanta daga kan madubin sannan ta nufi inda komin wanka na tangaran yake jikinta na rawa ta cire kyawawan kayan dake jikinta ta watsar gefe guda domin amfaninsu agareta ya wuce. Jikinta na rawa tsirara saita shiga cikin komin wankan sannan ta kunna shawa.
Sassanyan ruwan ya fara wanke kanta sannan sai gangar jikin.
Wannan shi yafara dakushe kaduwar dake jikinta domin kaduwa ce kawai amma ko kusa ko alama bata nadamar abinda tayiwa mijin nata domin maci amana ne... Maci amana wanda yaci amanata duk kuwa da aurensa danayi alhali bana kaunarsa falmata.
Koda sassanyar ruwan shawar yaci gaba da kwaranya atsakiyar
Koda sassanyar ruwan shawar yaci gaba da kwaranya atsakiyar kanta da bayanta sai zuciyarta ta tafi dofon tunanin wani shudadden lokaci shekara kusan guda kenan kafin ta auri Saifulahi.
.
Tun sa'ar da wannan kyakkyawar mata tafara kaiwa munzalin 'ya mace nas sai Allah ya jarabce ta da kaunar wani saurayi wanda bata taba ganinsa azahiri ba sai acikin akwatin talabijin.
Wannan saurayi shi Falmata ta fara kauna aduniya kuma akanta ta kare kauna haka nan har zuwa lokacin data soke mijinta Saifullahi da wuka babu wanda wutar begensa ke ruruwa akullum kwanan duniya sai wannan saurayi.
Anan sidi mai jaka ya dakata da labarin ya dubeni.
Ina fatan dai kasan saurayin da falmata take kauna? Na dube shi na girgiza kai. In banda abinda baba sidi yaya zan sanshi mutumin dake can borno nikuwa anan kano? Sidi mai jaka ya girgiza kai yace ai saurayin da falmata ke kauna kafita saninsa ma domin kai ka sha ganinsa azahiri ita ko sai ko akwatin talabijin. Na dubeshi cikin mamaki
wa kenan kake nufi? Sidi mai jaka ya gyara zama.
Jarumin jaruman fina finan hausa
SALIM nake nufi duk garin nan wanene bai san shi ba?
Kana nufin kace wai salim take so? Sidi mai jaka ya gyada kai.
Idan har akwai abinda tafi so ma to Falmata nayiwa salim domin alokacin da kafira ce ma sai ince shi take bautawa don tsabar kauna kaga nas ko barci batayi saita kalli hotonsa. Tun sa'ar data fara kallon fim dinsa na GAIBU saitaji duk duniya batada abin so kamar sa. Ko kunshin turare akayi mata sai an rubuta mata sunan salim atafin hannunta kai abindai ya wuce hankali sai ko hauka domin ko wanka falmata zata shiga da yar karamar rediyo take shiga bandaki tasa kaset din wakar fim din salim na gaibu tana wanka tana sauraron wakar azuciyarta kuma tana ayyana cewa itace Jaruma KALIMA wacce ta fito ajarumar fim din DAREN MUTUWA.
Wadannan jarumai guda biyu wato salim da kalima suna da matukar muhimmanci arayuwar falmata domin salim dai shi take kauna fiyeda duk wani abu me rai dake motsi abayan kasa yayinda kalima kuma ta kasance macen da falmata tafi tsana fiyeda mutuwarta domin duk da yake a fim ne kalima ke soyayya da jarumi salim amma falmata na matukar kishi da hakan akwai lokacin da take fatan inama tayi ido biyu da wannan tsinanniyar mai dogon wuya kamar jimina da babu abinda zai hanata kasheta. Kowa ma ya huta falmata nada yakinin cewa duk jarumai mata dake shirin fim akano babu wacce takama kafarta akyawun sura wannan shike dada kara mata kwarin gwiwar cewa duk ranar da sukayi ido biyu da salim saita raba shi da duk wata diya mace dake kusa dashi.... Koda tsiya koda arziki.
Tun tsahon shekaru uku da suka gabata falmata ta dauki alkawarin aduniya indai tana numfashi saita auri salim duk dayake dai ta riga tasan cewa salim baisan da zamanta ba amma tayi imani da cewa duk sa'ar data bayyana kanta agareshi bai isa ya juyawa kyakkyawar surarta baya ba.
Falmata nakan wannan babban kuduri nata tana ta tunanin hanyar da zata bi tazo KANO domin takai kanta ga abin kaunarta salim kwatsam ran nan da yamma sai mahaifinta ya kirawota yace da ita wai an samo mata miji falmata taji kamar an soka mata wuka a kahon zuci lokaci guda ta turo baki gaba kamar tsuntsuwa tace da mahaifinta.
Nifa ina da wan nake son aura.
Mahaifin nata wanda yafi kowa sanin tsiwarta ya dubeta cikin mamaki domin tunda yake bai taba ganin ta tsaya da wani saurayi na sama da mintuna biyar ba.
Wanene kike so? Falmata ta sunkuyar da kai tace.
Wani...ne.... Wanine a kano. Mahaifinta ya girgiza kai yace.
Kinga falmata kada kuruciya ta debeki zuwa ga aikata aikin dana sani. Domin na tabbata wanda kike son nan baikai koda rabin wannan da muka samar miki arziki ba... Kinga wannan babban mutum ne kamfaninsa biyu agarin nan ga tarin nera kamar bola. Jin haka keda wuya sai falmata ta zabura zata mike tsaye cikin fushi mahaifinta ya tsammaci haka tun farko cikin zafin nama ya fizgota sannan ya sharara mata mari har sau uku. Falmata ta kwalla ihu agigice.
Saurareni da kyau dan iyayenki ba amincewarki muke bukata ba mun riga mun bada ke... Gobe mijinki zaizo ku gana idan kuma kika sake naji kinyi masa wani abu ba daidai ba Wallahi yanka ki zanyi dan ubanki.
.
Adaren wannan rana yadda taga rana haka taga dare kwana tayi tana kuka hoton jarumi salim data saya naira ashirin rungume a kirjinta ahaka ta wayi gari cikin zulumin ganin irin mutumin da za'a kawo mata amatsayin miji.
Washegari da azuhur saiga mutumin shi da direbansa sunzo gidansu falmata. Ba karamar kaduwa falmata tayi ba sa'ar dataga mutumin mummuna ne kamar zane. Kuma ya girmeta nesa ba kusa ba.
Dan Allah... Dan annabi malam ka rufa min asiri ka rabu dani domin Wallahi bana kaunarka...inada wanda nake so. Falmata tace da saifullahi tana kuka domin tsoro takeyi kada ta wulakanta shi dan ta riga tasan halin mahaifinta ayadda yace idan ta munanawa mutumin saiya yankata ko da bai yankata din ba sai yayi mata dukan da zai nakasata idan kuwa har akwai abinda falmata ke tsoro fiyeda komai aduniya shine ataba kyakkyawar surarta domin da dan karamin kwaro ya ciji kan kyakkyawar fuskarta mai santsi gara tayi asarar makudan kudade
.
Kiyi hakuri yan mata bakin alkalami ya riga ya bushe.... Dama kwantar da hankalinki kikayi dan in dan ke bakya kaunta ni ina kaunarki in kuma dan mummunan fuskata ne kike ki na to ina son ki sani cewa kyan da namiji shine NAIRA. Duk kyawunsa in ba kudi shi mummuna ne agun mutanen duniya dan haka ina son ki sani cewa auren ki babu fashi dama kin bar bata hawayenki dan gidan nan naku ma rushe shi zansa ayi na sake muku sabo.... Na tabbata idan ke bakya sona mahaifinki bazai yarda yayi wasa da babbar dama irin wannan ba. Falmata ta fashe da kuka sa'ar dataji abinda yace.
Sati guda da faruwar wannan al'amari aka daura musu aure. Ranar daren amarcinsu na farko saisullahi yayi matukar mamaki sa'ar dayaga falmata ta tare shi hannu bibbiyu. Atsammaninsa sai sun debo tsamiyar miyagu kafin su sami jituwa sa'ar da ya shigo dakinta adaren amarcin ita da kanta ta cire masa babbar riga tace a tausashe har da dan murmushi.
Sannu da uwa....! Cikin mamaki saifullahi ya dubeta yace.
Kin bani mamaki... Kina nufin kice kin hakura zaman aure zakiyi? Falmata ta sunkuyar da kai da murmushi.
Yaya na iya da raina?
Saifullahi ya lumshe idanu gamida sakin murmushin samun nasara. Abinda bai sani ba shine murmushin falmata shine bacin rai da hadarinta. Tun daga wannan lokacin ne tunaninta kashe shi yafara darsuwa acikin zuciyarta.
To amma wannan tunani bai sami wani kwakkwaran goyon baya ba sai bayan kusan shekara guda da auren.
Awani yammaci wata babbar aminiyarta mai suna INYAMI ta kawo mata ziyara duk da yake dai inyami bata kaita kyawu ba amma ta fita iya kissa da tarairaya nesa ba kusa ba tun sa'ar da inyami ta shigo gidan falmata ta fuskanci jajayen idanun saifullahi na kan babbar aminiyar tata. Da farko ta dauki abin amatsayin dace ne kawai akayi amma sa'ar da inyami ta mike tace zata koma gida sai saifullahi ya mike gamida linke jaridar dake hannunsa ya dubi matarsa da aminiyarta falmata yace.
Ni ma fita anyi ina ganin in kawar taki tafiya zatayi basai na rage mata hanya ba. Cikin matsanancin kishi falmata ta dubi aminiyar tata tace.
Ai saku tafi ya rage miki hanya ko?
Tun daga wannan rana ce saifullahi ya kwallafa ransa akan inyami duk dayake yayi imani da cewa inyami batayi ko rabin falmata ba wajen kyawun sura amma irin iya kissarta da tarairayarta su ke narkar da zuciyarsa sannu ahankali yafara bin inyami har gida suna tattaunawa.
Ana cikin wannan hali ne rannan da yamma sai inyami ta kawowa babbar kawarta falmata ziyara lokacin datazo gidan saita iska babu kowa sai saifullahi cikin farin ciki ya tareta.
Rabo na Minallahi wai tsuntsu daga sama gasasshe kinzo kuma yau gidan babu kowa saini kada. Saifullahi yace lokaci guda kuma ya matso daf da ita jikinsa na rawa rabon daya zauna koda hira ne da matarsa falmata anfi wata hudu.
Ina ta tafi? Inyami ta tambaya tana waige waige. Saifullahi ya lumshe idanu yawun bakinsa yafara kafewa.
Bikin wata yar uwarsu akeyi bazata dawo ba sai dare ya danyi shiru yana duban kofar dakin kwanansa dake fuskantar falon.
Mu shiga daga ciki mana Inyami ta girgiza kai cikin sauri tace.
A'a rufa min asiri badai anan ba... Kayi hakuri ma hadu gobe a inda muka saba haduwa saifullahi ya dada matsowa kusa ya dafa kafadarta yace.
Kin cika tsoro... Bazata dawo ba sai karfe takwas na dare.
.
Basu fi sa'a daya da shiga dakin ba sai sukaji kamar motsi acikin falon dayake basu da gaskiya agurguje suka fito tare zuwa cikin falon sannan sai sukayi turus cikin tsananin kaduwa a zaune akan kujera tana kallonsu. Falmata ce da kofin ruwan sanyi a hannunta. Falmata ta dubi firgitattun fuskokinsu ta shafi kyakkyawan gashin kanta sannan saita jefe su da murmsuhi tace.
Kuyi hakuri kun dade kuna zaman jirana ban karaso ba ko?
.
Wannan duk tsohon labari ne daya faru yakuma wuce da falmata ke karkashin sassanyar ruwan na kwarara ajikinsa sai tayiwa kanta murmushi sa'ar data kawo karshen dogon tunanin sannan saitace a tausashe.
Shege mummuna nayi maganinsa gobe ma ya kara cin amanar wata... Saidai ko gawa irinsa. tana gama fadin haka sai ta kashe shawar cikin sauri ta dauki wani shudin kyalle dake makale akan wani karfe launin gwal mai kamar tsani ta daure shi akirjinta sannan ta nufi cikin dakinta da sauri.
Tsahon mintuna ashirin ta fito dauke da wata katuwar jaka mai taya ta ajiyeta akan kujera sannan ta murza wasu lambobi ta bude akwatin kana tayi nazarin kayan dake cikin akwatin na tsahon lokaci sannan saita gyada kai cikin gamsuwa kana ta nufi wata katuwar loka dake jikin bango ta bude lokar daga cikinta ta zaro dami dami na dalar amurka har dami biyar ta bude wani boyayyen aljihu acikin jakar ta watsa kudin aciki sannan ta mike tsaye ta rufe akwatin da karfi lokaci guda kuma ta daga kasan doguwar rigarta domin ta tabbatar da zaman hoton salim dake boye aTa daga saman doguwar rigarta domin ta tabbatar da zaman hoton salim dake boye akasan mararta. Sannan jikinta na rawa saita nufi dakin kwanansu inda tabar saifullahi aciki.
Ta shige dakin ahankali ta matsa kusa da inda saifullahi yake kwance baki sannu sannu ahankali saita janyo wani katon mayafi mai gashi ta lullube shi da mayafin sannan tace.
Sai watarana Saifuna. Yau bazan kwana a ko ina ba sai kano garin babban masoyina SALIM.
.
Da haka ta fice daga dakin zuwa falo ta dauki jakarta mai taya ta fice daga falon zuwa farfajiyar gidan tana tafe tana rera wakokin fina finan salim.
Sa'ar da maigadin gidan ya hango kyakkyawar uwargijiyarsa tana janye da katuwar jaka sai abin yabashi mamaki domin baitaba ganinta akasa ba acikin mota. Hakan shiyasa shi rugowa aguje yazo ya durkusa agabanta yace bakinsa na rawa.
Hajiya.... Lafiya kike tafe ke kadai? Ina zaki haka ga magariba ta kawo kai? Falmata ta dubi maigadin wanda yayi sa'an ubanta tace.
Inda ka aikeni zani ta wuce shi bata ko dube shi ba magadin yabita da kallo cikin kaduwa.
Shaidani. Yace cikin zuciyar a boye.
.
BABI NA BIYU 2
.
ADAMAWA-YOLA
.
RANAR LITININ 6 GA WATAN SATUMBA 2004
.
Sidi mai jaka yayi shiru sa'ar da kanina yayi sallama sannan ya ajiye kwanon tubanin agabanmu. Sidi mai jaka ya dubi kanina da faffadan murmushi yace.
Allah yayi maka albarka kaji dana.
Sannan batareda bata lokaci ba sai ya dauki kwanon tubanin ya dora abisa cinya sannan ya fara juya tubanin da busasssun yan yatsunsa masu kamar katako yanayi yana hadiyar yawu kamar wani tsohon maye sa'ar daya tabbatar tunabin ya gaurayu da yajin saiya dauki wani kato ya jefa abaki sannan ya dubeni cikin farin ciki yace.
Wannan daddadan tubanin yazo min adaidai domin nan shine karshen wannan dogon zaren labari kuma yanzu bada dadewa ba zan fara sakoma zaren labari na biyu. Amma kafin naci gaba yaya ka gani shin labarin yayi ma ko kuwa mu sake sabo? Cikin suri na girgiza kai a kagauce nace.
Haba baba sidi ai ni wannan zaren labarin ma da ka ajiye banso yakre ba yanzu yanzu ko anya wannan na biyun zaikai wancan na farkon dadi?
Baba sidi ya sake tsamo tubani ya jefa baki yana zazzaro idanu kamar mujiya.
Wato dai nas na fahimci cewa haryanzu baka yarda da al'amarin labaraina ba ko? Cikin sauri na girgiza kai nace
Haba baba ni na isa. Wane mutum inji mutuwa ai ni har kullum nkan girmama mutane masu baiwa irin ku.... Na danyis hiru sannan naci gaba.
Wallahi labarin ne daka faro na falmata mai murmushin alkawari yafara burgeni. Domin idan kace tayi murmushi sai inji kamar ni takeyiwa. Baba sidi ya fashe da dariya har rabin tubanin dake bakinsa ya kwace yafado akasa.
Nas kenan wato saikaji kamar kai takeyiwa murmushin? Na gyada kai.
Babu mamaki tunda kai haryanzu da sauran kuruciyarka ni agurin dunkulen tubani uku masu yaji sunfi min falmata da duk kyawun nan nata... Amma kaga kai ta burgeka dayake yar zamani ce irinku. Ya dan saurara yana nazarin kwanon tubanin.
Ai ba ya ma fara burgeka ba sai nafara kulla ma zararrukan labarin guda. Na dubi baba sidi na girgiza kai ahankali nace.
Ai ni kuma sa'ar dakace ta soke mijinta da wuka sainaji duk ta sane min kyawunta ya zame min kyawun dan maciji. Sidi mai jaka ya jefa tubani abaki batareda ya dubeni ba yace.
To ma ji ma gani saidai yadda labarin ya kare meyiwuwa kuma nan gaba ka dawo kace falmata mai murmushin alkawari ke burgeka. Na fashe da karamar dariya.
Ni murmushin alkawarin ma yafi burgeni fiyeda ita. Sidi mai jaka ya gyada kai gamida murmushi yace.
Kama fadi gaskiya dan samari abinda nasan ku yaran zamani mace ko aljana ce indai tana da dogon gashi ta burgeku to balle kuma mutum. Sidi mai jaka ya danyi shiru yana lasar fatar baki. Sannan sai ya dubeni.
Nas. Inason ka dauke tunanin zaren labarin falmata cancak daga cikin zuciyar sannan ka biyoni mu mayar da hankalinmu bakin wata korama inda Fulani suke shayar da dabbobinsu wani dan kauye dake daf da birnin Yola. Cikin girmamawa ga baiwar da Allah yayi masa na dubi dan tsoho mai jakar labarai nace Ina sauraronka Baba.
.
Yawwa Nas yanzu ga wata kyakkyawar budur nan bafulatana yar shekara goma sha shida kacal zaune abakin wata korama wacce ta kasance mashayar dabbobinsu ta jefa fararen kafafunta ababen sha'awa cikin koramar tana ta karkada kafafun nata acikin ruwan hannunta dauke da wani kyakkyawan tabarau fari. Lokaci guda kuma kamar tana kallon shanun mahaifinta dake gefen koramar suna kiwo. To amma fa azahiri wannan budurwa ba shanu take kallo ba hakanan inda zata ka tambaye cewa sa'o'inta nawa zaune gurin bazata iya fada ma ba donin hankalinta da tunanin sun taru atsakiyar zuciyata suna ta neman hanyar da zata sake ganin kyakkyawan saurayin nan ma'abocin iya sa tabarau.
.
Wannan budurwa Nas kyakkyawa ce amma kyawunta yasha bamban da kyawu irin na falmata domin ita kyawunta irin na fulani ne danyen kyau irin kyawun nan da akan mayar da fuskarsu doluwa amma daka dubesu saikaji suna burge ka harma kana son ka sake ganinsu kyakkyawar budurwar sunanta LARI.
Doguwace
.
Kyakkyawar budurwar sunanta LARI. Doguwa ce fara siririya mai fadin kuturi da yalwar kirjin da kansa zuciyar mazaje harbawa tana da yawan gashi masu santsi har gadon bayanta tana da yawan gashin gira gazar gazar baki sidik suna sheki hakanan wani abu dakan burge mazaje agameda halittar lari shine aduk sa'ar datayi murmushi saikaga kuncinta na hagu ya lotsa ciki wani kyakkyawan rami mai sheki ya bayyana wannan budurwa nada wani sinadari a halittarta wanda ke jan hankalin mazaje kamar yadda mayen karfe ke jan hankalin karafa. Duk mutumin daya kalleta sau daya sai ya sake kallonta sau biyu sannan ya sake na uku awayance wasu ko ma'abota wayewar zamani da karancin kunya har kiranta sukeyi suce wai kyawunta yana burgesu wannan shiyasa aduk sa'in da suka kai tallar nono zuwa babbar kasuwar Yola nata ne ke karewa da farko kafin a sayi na sauran.
Nas kada kace na zuga wannan budurwar da yawa domin inason ka san cewa saboda tsabar kyawunta wani darakta na bangaren tallace tallace na kamfanin wata sabuwar madara ta ruwa dake ikko ya taba hangenta akasuwar yola har ma ya nemi da ta amince suyi amfani da hotonta ajikin sabuwar madarar tasu mahaifinta ne yaki amincewa domin yan uwansa masu karancin wayewa sunce dashi idan ya sake aka tafi da hoton lari wai tsafeta za'ayi amayar da ita kudi. Wannan yafaru ne tun tana da shekara goma kacal aduniya.
.
Lari taci gaba da karkada kafafunta acikin koramar tana jujjuya farin tabaran ahannunta akanta asama tana kokarin yabawa gajimaren dake tafiya a fuskar rana wanda hakan shi ya dakushe haskenta garin ya sami damar yin sanyi ga kuma iskar dake tura gajimaren sai fifita siraran gashin kanta sukeyi wata sa'ar har rufe mata fuska gashin yakeyi.
Wannan saurayi dake narkar da zuciyar lari yakuma sa gabobinta sanyi aduk lokacin data tuna shi sau daya tak lari ta taba ganinsa kaddace ta hadasu. Wata ranar juma'a da safe shekaru biyu kenan da suka gabata amma har yanzu fatalwar murmushinsa da dadadan kalamansa agareta na nan garai garai acikin zuciyarta kamar a faifan majigi.
Ranar wata juma'a ne da safe misalin karfe goma da yan mintuna wannan saurayi shida abokinsa suka kamo hanya daga wani gari dake gaban yola niyyarsu itace su isa kano tun da sauran hasken rana.
Wannan saurayi nas ba wani bakonka bane SALIM dinmu ne dai shida abokinsa BALARABE suke tafe cikin motar salim cikin farin ciki da shirin fim din da suka gama dauka awani dan gari dake gaba da yola. Tun karfe uku na daren ranar suka gama daukar fim din don haka gari na wayewa sai salim da abokinsa kuma daraktansa suka kamo hanya domin dawowa kano don halartar wani sabon fim din da za'a fara a yammacin wannan rana. Don haka sa'ar da suka baro garin sun bar sama da mutum ashirin acan jarumai da kuma ma'aikata da hadiman shirin fim.
Adaidai lokacin da suka kawo dab da garin Yola ne suka hangi wani katon garken shanu yana tsallakawa ta kan kwaltar da suke bi salim yayi sauri ya taka birki ya tsaya domin ya jira shanun su wuce sannan lokaci guda kuma yafara dannawa shannun hon cikin damuwa.
Da ma ka daina bata lokacinka wadannan shanun hon bayayi musu. Balarabe yace yana kallon tika tikan shanun salim ya dubi rantsatstsen agogon dake hannunsa sannan ya gyara farin tabaran dake saman karan hancinsa yace.
Banason hudu tayi mana ahanya Wallahi amma na fuskanci dole ne ma sai mun makara Balarabe ya zunkuda kafada cikin nuna halin ko in kula yace.
To yaya za'ayi kai kadai da ranka ai dole ne ajiraka tun da dai idan babu kai babu fim din.
Salim ya shafi fuskarsar cikin damuwa sannan yayi ajiyar zuciya.
Kasan halin mutanenmu ko yaya kayi wani abu da zaisabawa abinda suka so sai su fara tayar da jijiyawar wuya suce ka fiya son wulakanci su ba sa kula da irin tarin uzururrukan da suke kan jaruman shirin fim. Balarabe ya dada zunkuda kafada yace.
Haka ne daman haka harkar ai ta gada kowa rashin hakuri kowa cikin gaggawa kowa a uzurce shiyasa kaga sau dayawa ayyukanmu suke baci musamman idan.... Yayi shiru bai karasa ba domin ya lura da tuni salim ya daina sauraronsa hankalinsa ya koma kan wata yar filani dake wucewa ta can daya bangaren titin dauke da korukan nono akanta.
Me kake kallo? Balarabe ya tambayeshi ko nono zaka saya mana? Salim ya girgiza kai batareda ya dauke kansa daga kallon budurwar ba.
Budurwar nake kallo balarabe... Wallahi kyakkyawa ce kaga yadda kirar jikinta yake kuwa.... Dubi fa yadda take tafiya saikace tarwada... Kai ni ban taba ganin kyau irin wannan ba. Balarabe ya fashe da dariya yace.
Yanzu haka fa azuciyarka har ka fara tunanin sata ashirin fim ko? Salim ya girgiza kai yace kokusa wannan baizo zuciyata ba Balarabe kawai dai ji nayi kamar tana burgeni balarabe ya dubeshi cikin mamaki.
Haba salim ina kai ina wata bafulatanar kauye... Ai daukakar ka aduniya fim tafi karfin haka duk irin kyawawan matan dake zagaye dakai suna kawo ma hari?
Salim baiko dubeshi ba sai ya tuka motar gaba kadan sa'ar dayaga shanun sun gama wucewa sannan ya sauka gefen titi da motarSaiya tuka motar gaba kadan sa'ar dayaga shanun sun gama wucewa sannan ya sauka gefen titi da motar.
Ikon Allah balarabe yace cikin mamaki mekuma zakayi mata? Salim ya juyo akaro na farko ya dubi balarabe da murmushi.
Kada ka damu darakta balarabe nono zan saya mana.
Karya kakeyi dan banza. Labarace yace. Suka fashe da dariya salim ya bude kofar motar yafita lokaci guda kuma ya dada turo da tabaransa kan doron hancinsa ya zura hannayensa biyu acikin aljifan bakin jeans dinsa sannan sai ya shake muryarsa irin na kwararren jarumi yace.
Me nono na sayarwa ne?
.
Sidi mai jaka yayi shiru sa'ar daya kawo nan sannan ya dubeni kana ya dubi kwanon tubaninsa cikin farin ciki ya dauko daya ya jefa abaki sannan yace dani. Ina fatan fatan kana biye dani Nas. Na gyada kai cikin gaggawa.
Toh Nas indai kana lura zaka fahimci cewa wannan zaren labarin duk a gutsutsture yake domin da farko akan zaren labarin Lari muke tafiya daga baya saina sauka na koma kan zaren labarin su salim to yanzu kuma zan sake sauka daga kan wannan zaren labari nasu salim na koma kan na Lari saina hada su guri guda na kulla ma su.
Na gane nace gamida gyada kai duk kuwa da cewa ba ganewar nayi ba na gyada kaine kawai don yaci gaba da labarin.
Yauwa Nas sa'ar da lari taji wannan kwararriyar murya sassanya tana tambayarta idan nonon ta na sayarwa ne sai lari ta dago kai ta dubi inda saurayin yake tsaye jikin motar adaidai wannan lokacin ne KADDARARTA ta faru. Domin tana kallonsa saitaji gabanta ya fadi ras. Da farko ta dauka ma tsoronsa takeji daga baya kuma saita sami kanta tana mai dada dago fuska ta dube shi wannan shi ya tabbatar mata da cewa ba tsoronsa takeji ba kwarjininsa ne yasa gabanta faduwa... Kuma hakan ya burgeta.
Na.... Sayarwa ne mana. Lari ta amsa bakinta na yar rawa lokaci guda kuma ta nufi inda motar salim take ta hanyar tsallaka titin tana zuwa saita ajiye korukan nonon guda uku agabansa. Duk wannan abin dake faruwa balarabe na kallonsu ta cikin gilashin motar.
Ashe dai kinada karfi salim yace da bafulatanar lokaci guda kuma ya durkusa agabansa yana satar kallon fuskarta mai kyawu na mamaki. Ma'abociyar gashin gira mai sheki acikin hasken hantsin wannan safiya.
Da ka dauka bazan iya saukewa ba dan ka ganni siririya? Lari yace cikin murmushi amma a kunyance batareda ta iya kallon fuskarsa ba.
Gani nayi ai korukan kamar da nauyi. Salim yace da dan murmushi.
Eh da nauyi mana amma ai na saba.
Yanzu kullum saikin bi wannan hanyar ke kadai bakya tsoro? Lari ta rude idanunta akunyace ta saki wata yar siriryar dariya tace.
Tsoro kuma? Me

Please Login or Register in order to submit comment