Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sayar da abinci ita taji tausayi na ta tafi dani gidan ta domin ban boye mata Matsalar danake ciki ba... Yanzu ma yar ta ce ta rakoni nan gidan... Tana waje tana jirana. Salim ya dubeta cikin mamaki yace..
Yaya to kika barta awaje baku shigo tare ba? Lari ta sunkuyar dakai tace.
Cewa tayi wai bazata shigo ba wai sun taba zuwa da wata kawar ta ka wulakanta su akace dasu wai baka nan bayan kuma sun hange ka a bayan wata mota a zaune. Salim ya dubeta da murmushin yake yace.
Muje wajen ta na bata hakuri inyaso sai mu wuce Naga gidan da kika sauka din.
.
Lari ta Mike tsaye sannan akaro na farko ta fara nazarin kayan alatun dake cikin dakin shakatawar hakika tsarin dakin ba karamin sa hantar cikinta kadawa tayi ba tun da take a duniya bata taba ganin kayataccen falo kamar wannan ba a zahiri saiko a cikin Fina finan su Salim.
Lari ta wuce gaba Salim ya bita Abaya yana kallon hikimar ubangiji gwanin halittar kyawawa. Gata dai acikin tsumma take amma kyawun ta a bayyane yake kai kace rigar lu'ulu'u ce a jikinta tabbas shekaru biyun dayayi bai ganta ba sun sa ta dada yi masa kwarjini wannan larin dake gabansa a yanzu cikakkiyar macece sabanin waccen larin daya sani shekaru biyu da suka wuce a daidai lokacin da suka kai kofar fita daga dakin shakatawar ne Salim yaji dan motsi a bayan sa cikin sauri yace da lari.
Jeki jirani a farfajiya gani nan tahowa yanzun nan.. Dan Allah kiyi hakuri fa wani abu zan dauko acan cikin daki.
Lari ta dube shi a kunyace cikin murmushi tace
Babu komai. Bi a hankali ma zanyi jiranka batareda ta sake juyowa ba saita fice daga dakin da Ace lari ta juyo baya da kyau data hangi Kalima tsaye acan cikin falon tana kallon su muguwar tsana karara a kan fuskar ta.
Salim yayi ajiyar zuciya sa'ar da lari tafice daga dakin sannan saiya dawo da baya zuwa cikin falon ya fuskanci kalima
Ina kuma ka samo wannan yar bolar? Uban kwashe kwashe kalima tace dashi tana ciccije baki.
Salim yaji ransa ya dan sosu don me zata Kirata da yar bola? Ya tambayi kansa.
Ba yar bola bace mutum ce kamar ke Salim ya mayar mata da martani a fusace.
YA kuma kamata ki iya bakin ki kalima domin kalaman ki sun fara tsauri dayawa.
Kalima ta rufe baki ta Kalle shi cikin kaduwa bazata iya imani da wannan sauyin fuska na bazata ba Yan sa'o'i kadan da suka wuce yana nan gabanta yana rokon ta amsa cewa zata aure shi sai gashi yanzu har dasu tsawa.
.
Ni kake yiwa tsawa Salim?
Abin Dayafi tsawa ma zan iya miki yanzun nan domin kin fara isata. Salim yace sannan sai ya juya kamar zai fice daga dakin sai kuma ya dan tsaya ya juyo kadan yace.
YA kamata kisan inda dare yayi miki domin ni fita zanyi. Jikinta na rawa hawaye na zuba kalima ta taho a hankali har saida Tazo daf da Salim kamar zata bangaje shi sannan ta tsaya ta fesa masa hucinta a fuska tace.
Yanzu kam kabani amsar cewa bazaka aure ni ba. Nagode da abin da kayi min Amma Inason ka sani cewa in yau Kaine da nasara to gobe bakai bane keda ita.
Tana gama fadin haka saita juya cikin sauri ta nufi kofar dakin bata juyo ba har sa'ar data fice daga cikin dakin.
Salim yayi ajiyar zuciya sannan sai ya yiwa kansa MURMUSHIN yake yace.
SHEGIYA MASIFA. NA RABU DA ƘAYA.
.
******** ******** ******** ************
.
Karfe shida saura kwata daidai na yammacin wannan rana wasu yan yansanda biyu na tsaye a farfajiyar ofishin jami'an tsaro na unguwar GWAGWARWA wata budurwa ta keto ta cikin farfajiyar aguje dauke da jarida ahannunta yan sandan biyu suka juya aguje sukabi bayanta domin basusan da wacce tazo ba. Adaidai lokacin da budurwar ta kai daf da kofar shiga ofishin ne yansandan biyu suka tare gabanta.
Ke malama ina kike tsammani zaki? Wani kato mai kwarjini da murdadden gashin baki kamar igiya ne ya buga mata tsawa nan da nan sauran jifa jifan yan sandan dake ofishin suka zagayeta cikin mmaki. Budurwar ta dago kai ta dube su tana haki kamar ranta zaifita na tsawon lokaci bayan data dan dawo da numfashinta ne ta nuna musu hoton dake jikin jaridar tace.
Na.....san inda wannan take ance kuna nemanta ko.. Wallahi jiya naganta. Yansandan suka dubi budurwar cikin mamaki domin suna tsammanin ko tabuwa tayi. Wani dogo mai kyawun fuska daga cikin jami'an tsaron ya karbe jaridar daga hannunta nan da nan yan sandan suka zagaye jaridar. Sannan ne to suka dawo hankalinsu domin duk suna da labarin wannan mata da ake nema.
.
Biyoni muje ciki ki amsa tambayoyi. Dogon dansandan yace da ita budurwar ta bishi har zuwa cikin dan madaidaicin ofishin mai dauke da kujeru hudu na katako da katon teburi.
Zaiuna mana. Dan sandan ya umarceta budurwar ta zauna shima ya zauna akan kujerar dake bayan teburin sannan wasu jami'an tsaro biyu suka zauna agefe guda suka zura mata idanu zuruu. Kamar zasu hadiyeta.
Yaya sunanki?
Sunana KALIMA.
A ina kike da zama?
Anan cikin GAMA nake.
Dansandan ya danyi wasu rubuce rubuce akan takarda sannan saiyaci gaba da tambayoyinsa.
Yanzu kin zo ne ki tamake mu mu kama ita wannan mai laifin? Kalima ta gyada kai.
A ina to kika ga ita wannan mai laifin?
Jiya da safe a ni'ima otal sun ma dade da wani ubangidana da muke shirin fim tare da shi.
Kin tabbata itace kika gani? Kalima ta gyada gyada kai.
Bazan taba mantawa da fuskar ba yallabai... Kaga dai ni macece kamarta amma bazan boye ba wannan kyakykyawa ce da ba'a fiye samun irinsu a ko ina ba.
A ina kika sami wannan mujallar?
A bakin BATA... Dazu da rana naje sayen littafin da zan karanta ya kwantar da zuciya saboda wani abu dake damuna alokacin ne to na hango hoton ajikin jarida mutane sun zagaye shi wasu na saya wasu ko na ta tsine mata albarka domin ashe wai tun jiya ma aka bayar da labarin a filin INDA RANKA na gidan rediyo freedom.
Yanzu a ina kike tunanin zamu sameta?
Kalima ta dube shi da murmushi sannan tace. Yanzu ma idan zaka hadani da yansa zan iya kaika inda nake kyautata zaton zamu sameta... Idan bata nan sai mu wuce ni'ima otal. Dansandan ya sake rubuce rubuce sannan ya dubeta ido da ido.
Ba fa ma son wasa kinsan dai matar nan laifin kisan kai ake zarginta dashi.... Kin tabbata zaki kaimu gareta?
Kalima ta dube shi da wani faffadan murmushi tace.
Yanzu ma ku tashi mu tafi... Me yiwuwa ba zaka yarda ba yallabai amma ina tabbatar maka da cewa nafika son akamata.
.
*** *** ***
Salim yayi sallama daga sallar sannan ya dauki tasbaha yafara ja yana tasbihi ga Ubangiji mai iko akan komai bayan wasu yan mintuna ya daga hannu sama yace.
Ya Ubangiji kaine mai iko akan komai Allah kayi min maganin matsalar da nake ciki Allah ka zaba min mafi alkhairi daga cikin matan nan guda uku da suka zagayeni. Allah kaine kafi karfin komai Allah kafi karfin duk abinda yafi karfina salim ya shafa sannan ya mike tsaye ya dubi agogonsa karfe bakwai saura minti uku.
Me yahana falmata zuwa ne haryanzu?
Salim ya tambayi kansa cikin mamaki domin dazu suna cikin motarsa dasu Lari da rana falmata tayi masa waya. Hannun salim na dan rawa ya amsa wayar amma babu doki domin tun sa'ar da lari ta bayyana kanta gareshi ta mantar dashi dukkan kyawun wata halitta dake cikin zuciyarsa.
Falmata kina inane?
Ina nan... Bazan sami damar zuwa ba sai kusan magariba domin banajin dadi kaina ne ke yi min ciwo.
Ayya... Allah sauwake salim yace sannan kafin ya sake cewa wani abu saiyaji ta kashe wayar. Salim ya dubi lari wacce ke zaune akusa dashi saiyaga kamar murmushi takeyi da gefen bakinta.
.
Dariyar me kikeyi? Lari ta girgiza kai gamida sake yar dariya tace.
Salim kenan... Me yan mata. Hakan datace ya faranta masa rai domin bata nuna alamar wani bacin rai ba. Salim yayi mamakin abinda zai faru inda ace kalima ce zaune akusa dashi.
Sa'ar da suka isa gidan da lari ta sauka a yankaba saida salim ya kusan zubar da hawaye domin gidan rubabbene katangarsa ma ta ruguje azagaye yake da kwano ga wata katuwar kwata data gifta ta kofar gidan lari da yar gidan matar data sauketa suka shiga cikin gidan bayan yan dakiku suka dawo su da matar domin su gaisa da ita. Tuni har yara zun zagaye motar salim suna tsalle suna cewa.
GA ABBAS GA ABBAS ashe sun gane shi wannan shi yasa sai agurguje suka gaisa da matar salim yayi mata godiya sannan yayi mata kyautar naira dubu biyar. Matar ta fashe da kuka domin ko a zamanin da take budurwaSee Photos

Go to Home
Daga Marubutanmu
MURMUSHIN ALKAWARI-15
.
KARSHE
Domin ko zamanin da take budurwa ba'a tabayi mata kyautar dubu biyu ba. Ballantana biyar.
Bayan matar ta shige gida sai salim da lari suka koma gefe.
Salim ya dubeta yace.
Shiga motar ki rakani unguwa yanzu zamu dawo. Lari babu musu ta shiga cikin motar sannan suka tafi.
Mintunansu talatin da biyar acikin katin WELCARE salim yana kashe mata masu gidan rana bayan da suka dawo ne sai salim ya mika mata jakankunan kayan kyale kyalen da ya saya mata yace.
To lari barka da zuwa kano gashi nan kije ki gyara kanki sosai daga yau bana son na kara ganinki cikin tsumma.
.
Karfe hudu saura kwata salim yadawo gida zuciyarsa cike da farin cikin abida yayiwa lari don haka sa'ar dayazo yin sallar la'asar saiya daga hannu yayi irin addu'ar dayayi adazu. Abinda ke damunsa awannan lokacin shine da wacce kuma falmata zata zo.
Salim ya mike tsaye ya sake kallon agogonsa akaro na biyu sannan sai ya fara safa da marwa acikin dakin shakatawar domin ya matsu falmata tazo su gama abinda zasuyi don yayiwa lari alkawarin zai koma gurinta awannan daren. Adaidai lokacin da salim ke safa da marwa ne salo ya shigo cikin dakin sauri kusan duk a firgice.
Yaya ta karao ne? Salo ya girgiza kai yace.
Haryanzu dai bata zo ba. Ya danyi shiru sannan yace.
Wai oga lafiya kuwa naga motocin yan sanda har guda biyu tsaye akofar gidan nan?
Salim ya dubeshi a rude.
Motocin yan sanda fa ka ce. Salo ya gyada kai.
Kwarai kuwa su biyu duk acike da yan sanda salim ya danyi jim cikin mamaki sannan sai yace.
Muje mu gani.. Me yiwuwa ko wani abune yafaru a makwabtanmu mu bansani ba.
Salim na gaba salo nabinsa abaya har suka kawo izuwa tsakiyar farfajiyar gidan. Adaidai lokacin ne to wata tasi ta shigo cikin salim da salo suka dubi motar cikin mamaki domin bau taba ganin wani bakonsu yazo gidan cikin tasi ba in ma a tasi din yazo saidai ya sauka waje ya karaso a kasa.
Kofar gidan gaba na tasi din ta bude kamshin turarenta yafara biyo gaba sannan sai kyakkyawar kafarta kana kuma saita bayyana sanye take da doguwar riga baka har kasa tsayin rigar shiyasa salim ya kurawa kasa idanu sannan ne ya hangi farin takalminta mai tudu ya dan dingo ta karkashin rigar kanta lullube shima yake acikin bakin gyale sannan sai idanunta aboye cikin bakin tabarau.
Yi hakuri salim ka dade kana jirana ko? Falmata tace sannan ta haskakeshi da murmushi salo na tsaye abayan salim ya kura mata idanu a cikin hasken kwayeyen lantarkin da suke haska farfajiyar gidan.
Ka jirani anan tare zamu koma falmata tace da direban akaro na farko sai salim ya dubeta yace.
Ki sallame shi kawai zansa amayar dake...
.
Idan ta sallame shi mu ma muna son magana da ita wata busashshiyar murya tace dasu daga baya su duka uku suka juya a firgice domin basuji motsin zuwan mai katuwar muryar ba saijin sa kawai sukayi abayansu. Juyawarsu keda wuya sai sukayi ido biyu da dankara-dankaran yansandan guda biyar sannan ba'a dade ba sai sauran yansandan dake waje suka kawo dauki dauke da bindigogi kamar yaki nan da nan aka zagaye su salim.
Koda salim ya dubi tsakanin ansandan sai ya nemi yawun bakinsa ya rasa. Kalima a tsaye a tsakiyar yansandan ta dube shi da faffadan murmushi sannan saita dubi shugaban jami'an tsaron tace.
GATA NAN KO BA ITA BACE?
Falmata taji gabanta ya fadi sannan saitaji zuciyarta ta harzuka bawai kamun da akayi mata bane ke bata tsoro ba rabuwa da salim yafi komai tashin hankali agareta falmata ta cire gilashin dake fuskarta sannan saita dubi tarin jami'an tsaron ta haskake su da MURMUSHIN ALKAWARI Tace.
Ku bani minti guda muyi sallama dashi yan samari.
Falmata ta juyo ta dubi salim wanda ke tsaye kusa da babban yaronsa Salo cikin kaduwa ta dubi salim a tausashe tace.
Salim... Kaga abinda ya kasance agareni. Nasan koda baka sani ba nan gaba zaka sami labarin laifin dana aikata inason ka sani cewa duk mugun abinda na aikata banida da wani abin so aduniya sai kai salim... Kuma inason ka manta da laifin danayi acikin zuciyarka ka daukeni kawai amatsayina na mai kaunarka kaji salim zuciyarta ta karye hawaye yafara kwaranya akan kumatunta amma abin mamaki murmushin alkawarinta na nan bai gushe ba falmata ta dan matso kusa da salim yayinda yan sandan dake zagaye dasu suka dada zagayesu sosai. Suna kallon ikon Allah falmata ta kurawa salim idanu na tsahon lokaci sannan saita ciro wani kyakkyawan zobe daga dan yatsanta ta kama hannun salim ta sa masa zoben sannan ta rike hannunsa tsakanin tafukan hannayenta biyu tace a tausashe.
Ga zobena nan nabaka kyauta... Dan Allah idan ka sami waccce zaka aura yar mutunci ba irina ba.. Ka bata wannan zobe kace da ita wata babbar masoyiyarka ce ta baka. Falmata ta dada matsowa hawaye na zuba daga idanunta.
Ce ne dani wani abu mana salim ko naji dan dadi kafin su tafi dani? Salim ya dubi kyakkyawar fuskartasaiyaji tausayinta ya kamashi dan haka saiya dubeta a tausashe yace.
Nagode da kyautarki falmata kuma inason ki sani cewa duk laifin laifin da kika aikata kinfi waccan agurina. Salim ya nuna kalima da baki.
Falmata najin haka saita juya ta dubi Kalima tace.
Shashasha! Haryanzu ni ce ke da nasara akanki. Kafin ta rufe bakinta tuni har jami'an tsaron sun tisa kyeyarta sun nufi inda motocin su suke akofar dankareren gidan jarumin jarumai salim. Koda jami'an tsaron suka sa falmata a tsakiya sai Kalima ta juyo ta dubi Salim da murmushin yake tace.
Shikenan ko! Kanwa ta kar tsami kwarnafi ya kwanta. Sai kuma ka nemi wacce zaka aura ko? Kalima ta fashe da dariya ta buga kafa a kasa tace.
Biyu babu kenan salo ya taba kadafar salim a fusace yace.
Kyaleni na kaddamarwa marar kunyar yar tsakuwar nan.
Salim ya dubi salo da murmushi ya girgiza kai sannan saiya kama hannunsa suka juya ahankali suka nufi cikin gidan suka bar Kalima tsaye tana tsuma.
.
Adaidai lokacin da suka kai daf da kofar shiga ginin ne salim ya dubi salo yace.
Ai shirun danayi mata yafi kona rai abinda kai baka lura ba shine yanzu ne Kalima tafara kaunata ni ko na riga nagama zamaninta dan haka kyaleta da abinda ma ke damunta salo ya juya ahankali ya dubi bayansa saiyaga ashe haryanzu Kalima na nan tsaye tana kallonsu.
Kaga marar kunyar nan haryan tana tsaye. Salo yace da salim.
Rabu da ita salo na fada ma na gama yayinta. Dahaka suka shige cikin gidan adaidai lokacin da salim ke kokarin rufe kofar ne yajiyo muryar Kalima ta fashe da kuka. Salim ya dubi Salo cikin murmushi yace.
Kaga abinda nake fada maka ko?
.
Sidi mai jaka yayi mika sannan yafara kokarin mikewa tsaye. Yazaka tashi baka karasa labarin ba?
.
Na tambayi sidi mai jaka cikin kaduwa.
Haba Nas me kake son kuma kaji? Ai iya labarin kenan YA KARE.
.
Gaskiya baba sidi kai kullum baka son ka karasa labarinka. Sidi mai jaka ya fashe da wata bushashshiyar dariya.
Me kake son ji Nas?
.
So nake naji yadda ta kasance tsakanin salim da lari shin ya aureta ne? Sidi mai jaka ya dawo ahankali ya zauna akan kujerar sannan ya dubi tsohon agogonsa mai kamar ankwa yace.
Toh bari nayi maka KURUNKUS acikin yan mintuna biyar din da suka rage kafin lokacin.
Kaidai Nas na fahimci kafi son labari sai anyi maka KURUNKUS. Na dube shi cikin murmushi nace.
To ai ni bana son kabar ni ne acikin duhu.... Kasan yaran zamani ba kasafai muka cika son takura kwakwalwar mu ba.
Hakane Nas Allah ya kyauta Sidi mai jaka yace sannan sai yace.
.
Bayan an kama falmata da kwana uku salim da lari suka nufi Yola da sassafe kafin su tafi saida aka sha cacar baki tsakanin lari da salim inda lari take nuna masa cewa indai har fa yana kaunarta to kada ya sake ya mayar da ita kauyensu domin za'a aura mata azzalumin nan JA'E.
Kada ki damu lari na riga nayi istahara na kuma fuskanci cewa aure tsakanina dake akwai alheri acikinsa mai tarin yawa inason ki kwantar da hankalinki ni zanje na sami iyayenki da kaina babu me rabani dake sai Allah.
Don haka kafin su tafi saida salim yakai lari gidan mahainsa ya nunata yace dasu shifa ya samu matar aure.
Ko kaifa amma kanata yawo agari anata zaginka ana cewa bakuda aiki sai iskanci kun ki are sai fim kaga yanzu ai kafi mutunci idan kayi aure. Mahaifiyar salim HAJIYA HASIYA ce ke maganar. Salim ba karamin farin ciki yayi ba lokacin dayaga irin karbar d aiyayensa sukayiwa lari. Ga kuma kyauta mai tarin yawa da mahaifansa da yan uwansa sukayiwa Lari.
Lokacin da suka fito da safe zasu kama hanya sai salim yace da babban yaronsa Salo.
Ko kalima tazo kada ka ka kyaleta ta shiga gidan nan. Salo ya bushe da dariya yace.
Haba... Oga ai indai gidan nan ba gidan ubanta bane dole ta barshi. Ko baka fada min ba Wallahi bazan barta ta shiga ba.
Dahaka suka kama hanyar yola karfe biyar na yamma suka isa rigar su Lari tun daga nesa suka hangi wasu samarin fulani su uku gindin wata bishiya sunyi cakare cakare suna kallon motar cikin mamaki domin basu taba ganin mota mai kyan wannan ta shiga rugar ba.
Salim yayi fakin da motar agindin wata katuwar bishiyar mangwaro tun kafin su fito dangin lari suka fara fitowa daga cikin bukkokinsu suna kallon motar.
Kaga mahaifiyata can lari tace da salim lokaci guda kuma ta nuna masa wata yar siririyar bafulatana kamar ta karye saboda siranta amma fa kyakkyawa ce ta gaske lari ce tafara fita daga motar sannan sai salim. Fitar lari keda wuya sai mutanen rigar suka dauki sowa suna tsalle da murnar dawowarta. Mahaifiyar lari wacce rabonta da tasa wani abin kirki abakinta tun kafin batan lari ta fadi sumammiya.
Saida aka shafe sama da mintuna goma kafin asako kan mahaifiyar Lari.
Ana cikin wannan rudani ne mahaifin lari yadawo. Tun kafin yakararo Lari ta sanar da salim cikin sauri salim ya tare shi sannan ya durkusa har kasa ya gaishe shi. Bayan da aka nutsu sai mahaifin lari ya dubeta yace.
.
Ke kuwa Lari ina kika tafi duk wannan tsahon lokaci. Lari ta sunkuyar da kai tana tunanin abinda zata fada zuciyarta na harbawa duk kuwa da cewa salim yace da ita Allah na tare dasu.
.
Ke nake jira kinyi shiru. Mahaifinta ya maimaita tambayar lari ta dubi mahaifiyarta a rude tana neman taimako domin tasan ita kanta bata goyon bayan aurenta da Ja'e daman ubanta ne ya jajirce akan al'amarin.
Fada min Gaskiya lari ina kikaje... Inason ki kwantar da hankalinki in don maganar aurenki da ja'e ne wannan magana ta ruguje domin jale yanzu haka ma yana hannun hukuma ana zarginsa da laifin kisan kai. Jin haka keda wuya sai lari ta nufi mahaifiyarta aguje ta rungumeta tana kukan farin ciki.
Duk wannan abinda akeyi salim na gefe ya harde hannu yana kallo yayinda sauran jama'ar rigar suka taru suna kallonsa da motarsa.
Lari ta dago fuska tace da mahaifiyarta.
Ina NAFI'U kuwa... Ban ganshi ba ko yana rugarsu. Mahaifiyarta tayi shiru na dan lokaci tana duban mahaifin lari sannan saita dauke kai gefe guda sannan ta ce "Ja'e ya kasheshi, yanzu haka yana hannun 'yan sanda."
.
Salim ya dubi Lari ya ce, "wane ne kuma Nafi'u?" Lari ta kauda kai ta ce, "Shi ne tsohon saurayina."
Salim ya cire zobe da me hannunsa ya ce da Lari kawo hannunki in sanya miki. Cikin kunya Lari ta ce, "Wace ce ta baka zoben?" Salim ya yi kamar ya 6oye mata amma sai ya tuna Lari tafada masa gaskiya don haka sai salim ya tausasa murya yace.
Wata mai kauntace ta bani zoben nan ta kuma ce dani idan na sami matar da nake son aura ina iya bata shiyasa na baki shi yanzu. Salim ya danyi shiru yana dubanta.
Ina fatan fadin hakan bai zama laifi ba?
Lari ta dago kai cikin sauri tace.
Don dai laifi babu wuya. Ga mamakin salim saiyaga lari ta saki wani tattausan murmushi kana ta lumshe idanu tace cikin murya kasa kasa.
DUK MAI KAUNAR KA AI MAI KAUNATA NE SALIM.
.
SIDI Mai jaka ya mike tsaye zumbur sa'ar da yakawo nan ya dubeni da bushashshen murmushi yace.
To Nas KURUNKUS nan shine karshen wannan labari saikatashi muyi alkawa kaga lokacin sallah yayi cikin sauri na mike tsaye nace.
To yanzu baba sidi sai yaushe kenan zan sake dawowa? Sidi mai jaka ya fashe da dariya yace.
Ko ka dawo ma nan gaba bazan sake baka wani labari ba saika biya ni labaran uku dana baka. Jin haka keda wuya saina fara lalubar aljihuna zan dauko kudi.
Sidi mai jaka ya girgiza kai yace.
Haba Nas na sha fada ma abaya kudi basuda wani amfani mai yawa ga tsoho kamata don haka idan ka dawo da labari nake son ka biyani... Ina fatan ka fahimce ni? Na gyada kai a tsorace ina tunanin sake haduwa dashi. Yanzu kamar ni data karewa labaraina suka kare wane labari zan iya baiwa baba tsoho ??
.
KARSHE.
.
NAZIR ADAM SALIH (NAS)
MURMUSHIN ALKAWARI complet
Na Nazir Adam Salih
Ebook creator:- Shuraih Usman 99%
Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so

For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading
Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521

Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu
Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya
Hakkin mallaka (m) nazir adam Salih


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload

Please Login or Register in order to submit comment