Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iska mai dauke da kamshin ya'yan itatuwa da furanni ta buso cikin falon. Kalima ta hangi cikin lambun baki bude.
Ina fatan kinji dadin zuwa. Salim yace sa'ar daya zauna kusa da ita. Adaidai lokacin ne to wata kofa ta bude sannan wani dogon saurayi fari dan gaya mai tarin suma duguzunzum kamar kayar bushiya ya shigo falon dauke da farantin kayan shaye shaye da tande tande ya ajiye akan dogon teburin mai shan kwai dake gabansu.
SALO dan Allah duk wanda yazo nemana bana nan. Salim yace da saurayin mai suna Salo wanda ya kasance shineSalim yace da saurayin mai suna Salo wanda ya kasance shine babban yaronsa wata sa'ar ma tare suka tafiya duk inda zashi.
An gama oga. Salo yace gami da dan rankwafawa kaikace ba sa'ansa bane. Salim ya dauki wayarsa ta tafi da gidanka ya mikawa salo yace. Ga wannan ma duk wanda ya kirani kace bana kusa. Salo ya karbi wayar ya fakaici kallon kyakkyawar fuskar Kalima. Yayi fito sannan ya fice daga falon yana tafiya yana dan tsalle kamar gurgu.
.
Bayan ficewar salo ne sai matasan biyu sukaci suka sha batareda sunyi wata kwakkarar magana ba.
Kina sha'awar yin harkar fim kuwa kalima?
Salim ya tambaya bayan sun gama cin abincin.
Kalima ta sunkuyar da kai kasa tace meyasa kayi min wannan tambayar.
Saboda ina ganin zakiyi bala'in dacewa da shirin fim.... Dole ne ma kyakkyawa kamar ta dace. Kalima tayi murmushi kanta a sunkuye
kaidai ka cika zuga. Salim ya girgiza kai ba zuga bace Kalima Allah fuskarki abar gani ce akan kyamara. Kalima ta sunkuyar dakai na tsawon lokaci can saita dago kai ta dubeshi tace.
Jiya munyi maganar da yayata kuma ta amince fuskar salim ta washe azuciyarsa yana addu'ar Allah yasa ta amince har ta aure shi nan gaba. Kin amince kenan? Kalima ta gyada kai da murmushi.
.
Wannan shine farkon faruwar komai. Tun daga wannan ranar salim yazama bawanta baya jin maganar kowa sai ta Kalima su Samira da sauran yan matan dake karkashin kamfanin fim dinsa duk Kalima tasa ya kore su. Ance a shekarar ne kalima tafara fitowa acikin fim din gaibu fim din dayayi tashen da ba'a taba samun wani fim dayayi koda rabinsa ba. Hakan nan ance salim shine cin kalima shine shanta shine cin yan gidansu jita jita na cewa hatta rubabben gidansu yayar kalima ma saida ya ruguje shi aka sake musu sabo aka dora musu bene. Asaman benen ne kalima ta tare salim ya hada mata kayan alatun duniya adakin sannan ya saya mata kayan sawa sama da kala dari da ashirin ance wai idan akullum kwanan duniya kalima zatasa kaya kala uku iri daban daban saita shekara hudu bata maimaita sa wasu kayan ba. Wannan shiyasa ta zama uwar jarumai mata yan shirin fim. Kulluma suna tare agindinta idan tasa kaya sau daya bata kara sawa saita zabi wata daga cikin yan matan dake karkashinta ta bata har layi yan matan keyi na karbar kayan.
Ranar Tara ga watan satumba shekarar milidiyya ta dubi biyu da hudu salim yayiwa jaruma kalima kyautar sabuwar mota kirar marsandi mai budadden sama. Wannan kyauta dayayi mata gaisuwa ce da rokon iri domin a iya tsawon zaman da sukayi da kalima ya tuntube ta da maganar aure sau arba'in da bakwai amma sai kalima ta shiritar da zancen. Wannan al'amari yafara damun zuciyar salim domin akullum kwanan duniya idan ya kalli kalima saiyaga kamar kara kyau takeyi gashi kuma aduk cikin kowane minti daya sunanta sai kara yaduwa yakeyi aduniyar yan kallon fina finan hausa. Farin jininta na dada karuwa. Salim na fargabar idan yayi wasa yanaji yana gani kwado zaiyi masa kafa ya koma ruwa don tabbas ko ba dade ko bajima wani mai karfin aljihun zai sako kai ya aure kalima yanaji yana gani. Wannan shiyasa salim tunani duk da irin kyautattukan hauka dayakeyi mata saiyaga kamar sunyi kadan dan haka awannan rana ta tara ga wata sai ya sayo mata wannan mota kirar marsandi sannan awashe garin ranar ne yake tambayarta maganar aurensu sai gashi bayan duk wahalhalun dayayi mata abaya ya yada sunanta aduniya ya mayar da ita mutum amma kalima harta sami ikon daga ido ta dube shi tace wai ba aurene agabanta ba.
Kai wannan rashin godiya dayawa yake.... Ai ko alkunya tayi min. Salim yace da kansa sa'ar daya dawo daga dogon tunanin.
Sannu ahankali saiya goge hawayen dake idanunsa awayance sannan ya dauke mutum mutumin karen ruwan ya ajiye agefe guda sannan ya dubi kalima wacce ke can inda yabaro zaune tana taunar cakuleti abinta.
Ni... Zan fiya... Yace da ita muryarsa na rawa zuciyarsa na kuna.
Gida zan mayar dake kokuwa anan zan barki harna dawo. Kalima ta kada masa idanu kafin tace.
Wankin kafa nake son ka kaini. Salim ya danyi shiru.
Kinsan dai sauri nakeyi kuma jirana akeyi... Ba ga motar ki nan ba ki tafi mana ke kadai. Kalima ta zunkuda kafada ta turo baki gaba tace.
Ni naki kai nake son ka kaini. Abinda salim baisani ba shine duk da irin jan ran da kalima keyi masa tana alfaharin duk inda zata aganta tareda fitaccen jarumi salim.... Kuma wani abin ban haushi tana masifar kishinsa kamar bala'i don ko nan da can bata son su rabu don kada ma wata ta sami shiga zuciyarsa.
Haba kalima ga motarki nan tafi aciki mana ki barni ni in tafi gurin shooting din nan.
Kalima ta hada rai ta dubeshi a fusace.
Kaga in bazaka kaini ba shikenan yar motar daka bani jiya har ka fara sa mata ido? To ni banyi niyyar fara fita yawo acikinta ba ta mike tsaye a fusace ta nufi kan kujerar da salim yake ta warci mutum mutumin karen ruwanta afusace ta juya zata fice daga dakin sai wayar salim tayi wani sassanyar sauti. Kalima ta tsaya cak atsakar dakin kamar an soka mata kibiya ta riga tasan me sautin wayar ke nufi alamu ne da ke nuni da cewa sabon sakon wasika yazo awayar. Idan hara akwai abinda kalima ta tsana shine yan matan da a kullum sai sunyi masa sakon wasikar gaisuwa kokuma soyayya ta cikin waya.
Wace tsinanniyar ce kuma? Kalima ta tambaya a fusace lokaci guda kuma ta juyo zuwa inda salim yake zaune ta rankwafa akusa dashi. Suka fara karanta sakon dake kan fuskar wayar kamar haka:
..... NASAN BAKA SANNI BA AMMA NI NA DADE DA SANINKA DOMIN KAINE KESA ZUCIYATA FARI KAINE FITILAR IDANUNA ADA INA NESA DAKAI AMMA AYANZU INA DAF DA KAI ME YIWUWA MA KANA IYA JIN NUMFASHINA AKAN KYAKYKYAWAR FUSKARKA. NAN BADA DADEWA BA ZAKA ZAMA SARKI IN ZAMA SARAUNIYAR KA.... I CARE.
Nice FALMATA.
.
Shegiya tsinanniya kalima tace a fusace bakinta na rawa sannan saita warce wayar daga hannun salim cikin sauri ta daddana madannan wayar ta goge sakon wasikar sannan ta mika masa wayar tace tana huci tashi mu tafi. Salim ya dubeta cikin mamaki yace ina zamu? Kalima ta rike hannunsa ta kankame tace Inda zaka. Cikin mamaki salim ya sake dubanta yace.
Kikace kuma wankin kafa zaki. Kalima ta girgiza kai ta dada kankame hannunsa a tausashe.
Nafasa zuwa dakai zamu tafi inda zaka. Salim ya mayar da wayarsa aljihu sannan ya wuce gaba kalima tabishi abaya. Azuciyarsa yace YAU NA HADU DA JARABA.
.
HUDU 4
.
'Yaya kayi shiru? Cigaba mana baba sidi. Naji ka ambaci sunan mutumiyata falmata kana nufin kace har ta sauka a kano? Baba sidi ya yi murmushi sannan ya mike wuyansa kamar zakara yace.
Samo min ruwan sha Nas. Wannan tubanin duk ya mimmike min awuya cikin sauri na mike tsaye na zagaya bayan gidan sidi mai jaka na shiga wani shagon sayar da kaya dake daf da kasuwa na sayo jakar ruwa biyar cikin sauri na dawo na ajiye ledojin ruwan agabansa azuciyata ina ta tunanin zuwan falmata kano.
Sidi mai jaka ya dauki jakar ruwan daya yasa tsofaffin hakoransa ya huda ledar sannan yasa abaki Ja daya ya zuke ruwan ya jefar da ledar kana ya sake daukar ledar ruwa ta biyu ya zuke sannu ahankali ya zuke guda hudu sannan ya dubeni yace.
Wani lokacin tubani ba ruwa hadarine bakaji yadda suka tokare min kirji ba kamar na hadiyi tabare. Na bushe da dariya nace.
Ai kana kokari ma baba sidi dan ni da tubani saidai daga nesa nesa sidi mai jaka ya girgiza kai.
Kaga kuwa ba karamar asara kakeyi ba rashin cin tubanin nan don baka san dadin da nakeji bane shiyasa kullum nayima tayi bakasan ci.
Wata rana zanyi kokari na gwada cin kwaya daya nace dashi duk kuwa da cewa nasan abu ne mai wuya. Sidi mai jaka yayi kamar ya dauki ragowar jakar ledar ruwan sanyi data rage ya shanye can dai saiwata zuciyar tace ya bari tukunna sai anjima. Maimakon haka sai ya dauki tubani guda ya jefa abaki ya dubeni.
Nas gashi dai har Allah ya kawo mu karshen zarurrukan labarinmu guda uku kuma yanzun nan zan kulluma su guri guda. Ya danyi shiru.
Ina fatan kana biye dani. Na gyada kai.
Sidi mai jaka ya gyara zama yace bari to mu fara kulla zararrukan labarin guri guda. Sannan sai yaci gaba.
.
Acikin wani kayataccen madaidaicin daki a Ni'ima hotel dake nan kanon dabo falmata ce kwance akan gado wayar ta tafi da gidanka ahannunta tana danne danne cikin murmushi daga inda take kwance takan jiyo sautukan jaruman fim din dakee daukar shirin fim acikin otal din. Tun sa'ar data sauka a otal din kwanaki biyar da suka shude ta sami labarin cewa jaruman zasu zo otal din daukar shirin fim acikinsu harda jaruminta SALIM.
Ranar lahadin data baro garin borno ta shigo kano karfe uku na dare dauke da katuwar jakarta. Dan kabu kabun daya dauketa ne ya kaita ni'ima otal sakamakon tambayarsa da tayi na ya kaita wata kebantacciyar otal mai kyau.
Lokacin da kan kabu kabun ya sauketa saita zaro naira dari biyar ta mika masa dan kabu kabun yayi kokarin yabata canji saita girgiza kai ta haske shi da murmushin alkawarinta tace.
Kabar shi kawai... Na gode ta juya ahankali tana rausaya kamar bishiyar turare lokacin iskar damina ta nufi wajen karbar baki.
Dan kabu kabun yabita da kallo har saidata bace sannan ya girgiza kai sannan ya tuka babur dinsa cikin farin ciki ya tafi abinsa murmushin datayi masa yafi kudin data bashi faranta ransa azuciyarsa yace. Matar wani bata wani ba.
Washegarin ranar da safe falmata ta dauke shatar mota tace da direban ya kaita inda ake cankin kudin kasashen waje direban bai tsaya da ita ako ina ba sai a wafa fagge falmata ta canza kudi na akalla naira dubu dari uku sannan direban tasi din ya daukota akan hanyarsu ta dawowa falmata ta sayi jaridu akalla kala bakwai bayan data dawo dakinta ta kwanta saita fara bin jaridun daya bayan daya tana karantawa har ta gama bataga wani labari daya keda alakar mutuwar mijinta ba. Kuma har wannan rana ta juma'a da take kwance akan gadon wayarta ahannu tana kokarin turawa abin kaunarta salim sako na biyu babu wata jarida data buga labarin mutuwar mijinta.
Falmata ta sauko daga kan gadon sa'ar daFalmata ta sauko daga kan gadon sa'ar da ta tabbatar da cewa sakonta na biyu ya tafi izuwa wayar Salim sannan saita nufi tagar dakin ta leka. Daga inda take tsaye yana iya hangen salim tsaye akusa da wasu jerin kyawawan fulawowi gajeru wata budurwa gwanar iya sa hoda da jan baki akusa dashi.
Shegiya nacacciya. Falmata tace tana murmushi. Kusan mintuna talatin kenan falmata na lekensu ta tagar dakin kuma ta lura a iya tsawon mintuna talatin din nan duk inda salim zai motsa wannan budurwa na biye dashi kamar inuwa. Da farko falmata bata gane budurwar ba sai daga baya data yi nazarin fuskar da kyau sai falmta ta fahimci budurwar amatsayin Kalima. Jarumar data sha ganinsu tare da salim acikin finafinan hausa da dama.
Falmata na nan gindin tagar dakin tana lekensu zuciyarta na tafasa da wutar kishi. Ayanzu kam duk duniya babu wacce ta tsana kamar kalima da zata mutu ma alokacin to da haka tafi so. Jaruman biyu na nan tsaye can sai falmata taga kalima ta dora hannunta a kafadar salim. Falmata ta zabura ajikin tagar dakin sa'ar dataji wani abu mai kamar kibiya ya soki zuciyarta.
Kadan ya rage ta fada waje ta cikin tagar dakin.
Bi ahankali yarinya falmata kada ki kashe kanki a banza abinda ko saninki ma baiyi ba. Wata zuciyar ce ke cewa da falmata haka.
Falmat tayi ajiyar zuciya sannan ta dubi fuskar wayar tafi da gidanka tayi tsaki wannan shegen sakon ma haryanzu yaki zuwa gare shi. Mintuna goma suka shude falmata na nan tsaye tana lekensu can saitaga wani farin saurayi mai gashi duguzunzum yazo ya tsaya agabansu salim. Sukayi dan kus kus da saurayin sannan sai taga salim ya kama hannun kalima sun nufi wani bangaren kayataccen gini dake fuskantar ginin da take ciki. Falmata ta lumshe idanunta ta daina ganinsu ji takeyi kama zuciyarta zata fasa kirjinta ta fito saboda masifar kishi.
Bayan wasu yan dakiku saita bude idanunta. Gurin babu kowa sai wani dan siririn lebura mai dan karamin kai kamar kwakwa ke sintiri agurin dauke da wani shudin bokiti na roba. Falmata ta kurawa inda ta tabbatar da cewa nan su salim suka shiga idanu. Kana sai ta juyo zuwa tsakar dakin ta nufi akwatin kayanta na musamman data tanada dan wannan muhimmiyar rana datake fatan yin ido da ido da babban masoyin zuciyarta Salim.
Sa'ar da falmata tagama sa kayan saita nufi madubi ta zauna sannan tafara dube dube da goge goge duk kuwa da cewa dazu saida tayi sama da sa'a guda tana kwalliya.
Falmata ta sake kallon kanta ajikin madubin ta juya hagu ta juya dama saitayi wa kanta murmushi domin tasan duk duniya babu namijin da zai ganta yawun bakinsa bai kafe ba. Cikin sanda tana tafiya kamar hawainiya saita bude dakin sannan ta wuce zuwa falo daga nan kuma tabi ta tsakanin jerin shuke shuken da ke kofar dakinta na musamman ta nufi inda su salim suka tsaya dazun. Sa'ar data isa gurin saita jingina bayanta adaidai da inda salim ya jingina bayansa lokacin daya tsaya agurin.
Adaidai lokacin to leburan nan mai sintiri ya dawo zai wuce ta gurin dauke da bokitin robarsa ahannu nan take sukayi ido biyu da falmata mutumin yaji numfashinsa ya tsaya cak. Domin ya dauka aljana ce ta bude masa idanu.
Shekarunsa ashirin yana aiki a otal daban daban amma tun dayake bai taba ganin mutum da kyawun aljanar dake gabansa ba.
Mu...tum.. Ko aljan? Ya tambayi falmata a tsorace. Falmata ta dubeshi a fusace tace.
Shashashan banza ka taba ganin aljan ba kofato? Bace min da gani bakinka ya isheni da wari. Dan siririn mutumin ya zuga aguje har sa'ar daya isa wajen karbar baki bai yarda cewa ba aljana yagani ba.
.
**** ***** ***** ***** ********
.
Salim ya share gumi daga kan kyakkyawar fuskarsa adaidai lokacin da dan gajeren daraktan mai kai kamar masaki ya dakatar da daukar shirin fim din. Kusan mintuna arba'in kenan suna daukar bangarorin fim din babu ko kakkautawa. Mutum takwas ne acikin dakin daga cikinsy akwai darakta, mai daukar hoton kyamara, sai me yiwa jarumai kwalliya dakuma mai kula da sa kayan jarumai sauran mutum hudu din duk jarumai ne. Duk wanda ka kalla acikin mutum takwas din sai gumi yake yana naso kamar waina saboda zafi sakamakon na'urar sanyaya dakin da aka kashe da gudun kada sautinta ya shiga cikin abin daukar maganar magana sannan kuma bugu da kari ga hasken fitilar mai mugun haske da feso zafi wacce take amfani wajen haskaka dakin da kuma fuskokin jaruma domin asami hoto mai inganci da haske ba duhu.
Kai nifa zafin nan ya ishe ni zanyi waje na dan sha iska. Salim yace yana goge zufa daga goshinsa.
Kana iya zuwa kasha iska kafin adan jima na tura akirawo ka. Dan gajeren daraktan ne ke magana batareda ya dubi salim ba idanunsa akan takardar dake dauke da labarin dim din da sukeyi.
Yawwa dan dagizge. Salim yace da dan gajeren cikin murmushi sannan ya nufi kofa aguje domin yasan inda ya tsaya jifansa zaiyi da duk abinda yafara zuwa hannunsa.
Zaka dawo ne ka sameni... Dan banza da tsayi kamar hanya. Daraktan yace adaidai lokacin ne Kalima ta mike tsaye zumbur zatabi bayan salim
Ina kuma zaki? MAKALEMATA. Dan gajeren daraktan yace da ita yana kallonta da murmushi. Kalima ta harareshi sannan tayi tsaki.
Wayace ma shi zan bi uban sa ido? Dan gajeren daraktan ya fashe da dariya yace.
Kya karata can da munafurcinki kina so kina kawai kasuwa....
Allah kiyaye... Ai kasan Wallahi salim ba saurayina bane ubangidana ne.
To indai gaskiya ne ba kya son sa me zai hana mu sasanta kinga sai in kara ta biyu da ke. Kalima ta harare shi tace cikin tsiwa.
Allah sawwaka ahaka din zan aureka?... Kamar akife da kwando.
Adaidai lokacin da dan gajeren daraktan ke cacar baki da kalima salim ya isa farfajiyar otal din wasu yan mata guda biyu sukazo wucewa ta kusa dashi sai sukayi turus domin sun gane shi don sun sha ganinsa a fina finai.
Sannu... ABBAS. Dayar datace dashi. Abbas shine sunan daya fito dashi acikin fim din Gaibu. Salim ya juyo fuskarsa ahade ya dubesu yace.
Yawwa sannunku dai sannan ya dauke kansa gefe guda. Ganin basu sami shimfidar fuska agurinsa ba sai yan matan biyu sukayi gaba kafa ba kwari amma duk da haka dai sunyi farin ciki da ganinsa azahiri.
Salim na nan tsaye adaf da wata bishiya mai kamar dabino saiyaji wayarsa ta dauki sauti cikin damuwa salim ya bude wayarsa domin yaga sakon da aka aiko.
Salim ya dubi fuskar wayar sannan yafara karanta sakon kamar haka...
.
.......TUN DAZU NAKE JIRA KO ZAKA BANI AMSAR SAKONA NA FARKO, BAKA AIKO BA SAIGASHI CIKIN IKON ALLAH KA SAKE MATSOWA KUSA DANI AYANZU HAKA MA INA IYA GANIN KYAKYKYAWAR FUSKARKA. SHIN KANA SON GANIN TAWA FUSKAR? MATSOWA GABA KAWAI ZAKAYI SAIKA SHA KWANA ANAN ZAKA SAMI FALMATA.
.
Salim ya rufe wayar ahankali cikin tsananin mamaki sannan ya dubi gabansa adaidai da inda tace yasha kwana zai ganta agurin.
Yau kuma da wa Allah ya hadani? Salim ya tambayi kansa cikin mamaki yana girgiza wayar dake hannunsa tsahon lokaci yana gurin tsaye zuciyarsa nata wasi wasi. Shin ya leka ya ganine ko kuwa kada yaje. Meyiwuwa ma wata shakiyiyarce take son yin wasa da hankalina.
Salim ya fadawa kansa. Ba'a dade ba sai yaji wayarsa ta dauki sauti mai kara cikin sauri ya daga wayar zai amsa saiyaji ta daina yin sautin.
Koda ya duba lambar wayar da aka buo saiyaga lambar falmatan dake damunsa ce dai. Hannunsa na rawa cikin mamaki ya bude wayarsa sannan saiya buga lambar ya kara a kunne ba'afi ko dakika biyar ba sai yaji acan daya bangaren ance.
Hellooo. Salim yaji gabansa yafadi tun dayake bai taba jin muryarsa mai dadin wannan ba. Wacece ke maga....na salim ya tambaya muryarsa na rawa.
Zagayo nan ka ga mai maganar mana. Aka ce dashi sannan lokaci guda ta katse wayar daga can bangaren. Salim ya dubi gawar kan wayar da ke hannunsa ya sake kallon saitin kan kwanar akaro na biyu sannan saiya nufi gurin ahankali yana tafe hannunsa na wasa da fulawowin da sukayi jerin sahu har zuwa karshen ginin inda za'a sha kwanar sa'ar da salim yaje daidai da karshen ginin saiya dan tsaya ya karkata kunne ahankali yana saurare ko zaiji motsi tsahon dakiku baiji sautin komai ba sai sautin katon injin bada wutar lantarkin dake can bayan ginannukun otal din. Sannan ne salim yaji wani irin turare mai taushin kamshi ya bugi hancinsa zuciyarsa ta harba. Duk dayake bai taba jin kamshin irin wannan turaren ba amma kamshinsa yayi kama da irin kamshin turaren mata. Salim ya jingina kafarsa jikin ginin gamida ajiyar zuciya kana yayiwa kansa murmushi yace.
Haba jarumin jarumai ya kake abu haka kamar wani farin shiga. Da wannan kalamin sai salim yasa hannayensa biyu cikin aljihu ya karya kwanar yana takama. Koda yasha kwanar sai kuma ya tsaya cak cikin mamaki domin babu kowa agurin. Salim ya dan sake matsawa gaba ahankali yana takawa daidai kamar namijin agwagwa har dai yakawo daf da wasu rukunin shuke shuken baiga wani mahaluki ba sai wasu mutane biyu magidanta daga can nesa suna busa sigari. Salim ya girgiza kai cikin mamaki gamida murmsuhi oh duniya dai baka rabata da masu son wasa da hankulan mutane. Yace da kansa sannan saiya mika hannunsa zai tsinko wani jan fure dake tsakiyar rukunin shuke shuken katsam sai yaji wani tattausan hannu ya dafa kafadarsa ta baya salim yayi mutuwar tsohuwa hannunsa makale a sararin samaniya bai iya kaiwa ga tsinkar furen ba domin ko shakka bayayi hannun mace ne ya dafa shi. Salim ya juyo ahankali tattausan kamshin turaren na bugun hancinsa yana juyowa sai yayi ido biyu da cikakkiyar halittar.
.
Kayi hakuri naga kamar na tsorata ka. Sannan saita haske shi da murmushin alkawarinta.
SUNANA FALMATA. Kai ko ba ka ma sunanka ba domin na dade da saninka falmata tayi shiru kana ta sunkuyar da kai kasa cikin murmushi hannunta na hagun akan kafadarta ta dama yayinda hannunta na dama ke dauke da wayar tafi da gidanka tana latse-latsen lambobi. Tsawon lokaci salim na tsaye yana kallon tsabagen kyau idanunsa suka dauko hoton santa santalan hannayenta suka zarce zuwa dogon wuyanta madaidaicin bakinta ma'abocin MURMUSHIN ALKAWARI.
Sannan da girar idanunta baki sidik tana sheki gashin kanta.Bakinta ma'abocin MURMUSHIN ALKAWARI sannan da girar idanunta baki sidik tana sheki gashin kanta a kwance a bayan dogon wuyanta.
Falmata ta dago fuskanta Gazar Gazar din gashin idanunta suka daga sama kamar zasu taba kan girar idanunta kana ta tausasa murya tace da salim.
Yaya kayi shiru? Salim yayi ajiyar zuciya yace A'a.
To me kike son nace dake malama falmata?
Abubuwan masu dadi.... Mana... Shin baka san ni bakuwar ka bace... Saboda kafa nazo garin nan dan ma baka zo nan ba da ni zan neme ka. Ta danyi Shiru tana duban abun data dade tana muradin Son gani a zahiri.
Sannan ki to da zuwa falmata barka da zuwa Kanon Dabo. Ko Dame kika zo anfiki jin haka sai falmata ta fashe da dariya salim yaji kamar busa masa sarewa take acikin kunne.
Koda me nazo an fini fa kace salim? Salim ya gyada kai gamida murmushi domin kyakkyawar ta fara burge shi.
Kwarai kuwa. Falmata ta girgiza kai tace badai komai ba... Salim ta haske ta da MURMUSHIN sa irin na kwararren jarumi.
Ai ko da me kika zo falmata an fiki yace duk kuwa da cewa a zuciyar sa yana tunanin zai dade yana zagaye kafin ya samu mai kyawun ta.
Toh shikenan ai zamu gani falmata tace kanta a sunkuye kyawawan biyu sukayi shiru na dan lokaci suna kallon juna can sai falmata tace zanso kuwa na ziyarce ka in ba damuwa salim yaji zuciyar sa ta harba abu na farko daya fara zuwa zuciyar sa shine kalima dan ya riga yasan mugun bakin kishin ta. Amma acan wani Bangare na zuciyar sa sai kururuwa take yi masa tana cewa dashi.
Kai shashasha! Allah ne yakawo ma sauyin kalima ba tana tunanin ita kyakkyawa bace to gashi Allah ya jeho ma da wata daga sama ai kawai bata adireshin ka jarumin jarumai. Salim yaji zazzafan gumin daya Koro shi waje yafara dawowa zuwa goshin sa.
In kuma kana ganin akwai takura kabar shi kawai wannan ganin ma danayi ma na... Gode tace dashi cikin wata rarraunar murya ta yaudara. Da salim ya kura da ita a lokacin daya ga farare idanunta akan fuskar sa suke suna nazarin sa cikin tsanaki domin falmata ta fahimci cewa duk da kwarewar sa ta shirin fim dakuna tarin kyawawan matan dayake mu'amala dasu ganin ta ya gama rudashi. Ita kanta abin yabata mamaki domin bata dauka zata iya ruda shi haka sa wurwuri ba. Ashe dai abin duk bogine akan allon talabijin. Falmata tace cikin zuciyarta.
.
Kada ki damu. Salim yace da ita tausashe in banda abunki waye zai gujewa bakon sa... Ya danyi shiru sannan sai ya lalubi aljihun sa ya dauko wata farar takarda da alkalami yayi rubutu ajiki sannan ya mika mata yace.
Ga adireshina nan amma anfi samu na da safe kamar tara zuwa sha daya jikinta na rawa falmata ta karɓa.
Kai amma fa nagode Wallahi gobe in Allah ya yarda zaka ganni... Zan ma kira ka a waya kafin nazo. Salim ya mayar da alkalaminsa aljihu hannunsa na rawa amma kadan kadan domin yafara girgijewa daga kaduwar ganin ta na farko.
Wani Sabon fim din

Please Login or Register in order to submit comment