Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai sameni tun ina karama sosai fa nake bi ta wannan hanyar da daddare ma mun sha tahowa daga rigarmu zuwa cikin gari idan ana biki. Ta danyi shiru sannan sai ta dan dago kai a wayance ta dubeshi ga mamakinta saitaga ashe idanu ya kura mata yana murmushi.
Kasani agaba sai dariya kakeyi ba nonon zaka saya ba?
Nono zan saya mana shi yasa ai na kirawo ki.
.
Wanne to kake so daga ciki kaga sauri nakeyi zan sami yan uwana acikin gari tun dazu suka tafi.
Salim yayi shiru yana sauraron daddadar muryarta ji yakeyi kamar tana busa masa sarewa.
Nawa babbar kwaryar can ta kasa? Salim ya tambyeta. Lari ta dauke korukan biyu dake saman babbar ta ajiye agefe guda sannan ta bude kakkauran kindirmon nonon.
Kawo dari da hamsin tace dashi a kunyace duk kuwa da cewa nonon ya kai na dari biyu da hamsin. Salim ya rike numfashi cikin kaduwa domin yasan idan a birni ne nonon dake cikin katuwar kwaryar yafi naira dari shida.
Wadannan fa nawa zaki sayar min dasu. Ya nuna sauran korukan da dan yatsansa.
Wannan ta kasan ka kawo naira saba'in wannan karamar kuma ta sama ko ashirin ma ka bani shikenan.
Naira dashi biyu da arba'in fa kenan duka? Lari ta gyada kai a kunyace tace.
Eh amma fa don kaine. Salim yaji wani dadi ya lullube zuciyarsa sa'ar dayaji ta fadi haka. Wannan itace irin macen dayake so macen da bata san menene buri ba. Macen da batada wannan wayewar ta shaidanci da mugun son kai da ake cewa wai wayewar zamani koda ya kura mata idanu saiyaji zuciyarsa duk tafi masa tarin wayayyun matan nan masu shegiyar iya kwalliyar sa hoda da jan baki wadanda yayi imanin cewa daga ranar da akace tauraruwarsa ta dakushe watsewa zasuyi su bar shi.
Meyasa kikace dan nine? Daman kin sanne ne? Lari ta girgiza kai cikin murmushi tace.
Ni nataba ganin ka ma in ban da yau?
To ai yadda kikayi maganar ne sai naji kamar kin sanni salim yace yana duban bakin gashin kanta daya zubo ta cikin dankwalin dake kanta. Lari ta sunkuyar da kai batace komai ba.
Juye min duk nono a ledodi... Ko bakida ledar?
Ina da ita mana. Lari tace lokaci guda kuma ta zaro bakaken ledodi da dama dake makale agefen zanenta. Cikin dan kankanin lokaci ta juye duka nonon dake cikin korukan guda uku acikin ledodi biyar. Adaidai lokacin ne balarabe ya bude kofar motar ya zo gare shi.
Bari insa cikin mota tunda ka saya. Abinda ka iya kenan. Salim yace cikin dariya. Malam ina kwana? Lari tace da labarabe akuunyace
.
Lafiya lau yan mata balarabe ya amsa sannan ya dauki ledodin biyu ya shiga dasu cikin mota bayan dan lokaci ya kwashe ledojin masu nonon sannan ya dube su yace da Salim.
Idan kun gama ni ina daga ciki. Dahaka sai ya koma cikin motar.
Tsawon lokaci matasan biyu suna durkushe daya bafulatana mai karancin wayewa wacce ke zaune acikin yar karamar duniyarsu ta bayan gari yayinda dayan ya kasance fitaccen jarumi dan kwalisa wayayye dan birni gaya.
Yanzu daga nan ina zaki? Salim ya tambayeta.
Gida zan koma tunda ka saye nonon lari ta amsa. Salim ya mike tsaye ya lalubi aljihun wandonsa na baya ya dauko jakar kudi wacce ke kunshe da jajayen takardun kudi daga ciki ya zaro yan dari biyar biyar guda biyu ya mikawa lari.
Ga kudin nononki lari tadubi kudin cikin mamaki.
Wannan duk na menene? Ai kudin sunyi yawa ai dari biyar din ma saina baka canji salim ya dubeta da murmushi yace.
Sauran canjin kyauta ce nayi miki... Lari ta girgiza kai tace.
A'a ka barshi Wallahi.. Wannan kudin ai sunyi yawa.
Kada kiyi min haka kyautace fa na baki da can da baki sanni ba na taba baki? Lari ta karbi kudin akunyace tace.
Nagode Allah saka... Salim yayi yar dariya.
Gashi har zan tafi ko sunanki ban sani ba.
Lari ta dubeshi sannan ta sunkuyar dakai tace Sunana Lari.
Lari? Salim ya maimaita sunan.
Amma sunan naki da dadi... Ban taba jin irinsa ba.... Ni sunana Salim ina fatan watarana idan nazo wucewa zamu sake haduwa.
Me zai hana indai muna raye dakaje bakin kasuwar yola inka tambaya duk an sanni agurin. Salim ya ciro tabaron dake fuskarsa yafara goge shi da farin kyalle. Lari ta zubawa tabaran idanu.
Tabaran nan naka ya burge ni Wallahi.
Ko kina so? Salim ya dubeta cikin murmushi. Lari ta danyi shiru ta riga tasan babu wani amfani da tabaran zaiyi mata to amma maganadisun dake jikin dogon saurayin ya firzge zuciyarta ya shuka mata sha'awar duk wani abu dake tattare da saurarin.
Idan nace inaso bani zakayi? Lari ta tambaya tana dubansa cikin rashin tabbas. Ga mamakinta sai ya cire tabaran ya mika mata.
Kinfi karfin abinda yafi ma wannan agurina. Lari ta dubeshi cikin shakka batareda ta miko hannu dan ta karbi tabaran ba. Duk kuwa da cewa tana matukar son ta ajiye abinda zai ke tuna mata shi. Domin tasan me yiwuwa har abada bazasu kara haduwa ba.
Wai da gaske kake yi? Salim ya gyada kai yace. Wallahi da gaske nakeyi idan kina so ga shi.
To kai kuma ka sa me? Lari ta tambaya salim yayi mata murmushi.
Ina da irinsu agida sunfi kala goma wannan abinda yace da lari irinsa yafadawa babbar jaruma Kalima acikin fim dinsu na MAGANADISU cikin shakka sai lari ta dan miko hannu tana dariya tace.
Bani to in da gaske kakeyi... Ni nasan da wasa ka... Kfin ta rufe bakinta salim ya mika mata tabaran. Lari ta karbi tabaran cikin tsananin mamaki tafara jujjuya shi nan da nan taji kamshi ya fara bugun hancinta bayan wasu yan dakiku sai lari ta dago kai tace da salim.
Nasan ma da wahala na sake ganinka. Salima ya girgiza kai sannan ya shafi kyakkyawar fuskarsa yace da ita a tausashe.
Me zai hana in Allah ya yarda duk ranar da nasake dawowa nan.... Sai na neme ki Lari.
.
Wannan duk wani shudadden labari ne daya faru tun shekaru biyu kuma daga wannan lokaci har zuwa yanzu da lari ke zaune abakin tafkin tana juya tabaran da salim ya bata ahannunsa bata kara ganin salim ba sai bayan shekara guda. Shima din ba'a zahiri ta ganshi ba akwatin talabijin ta ganshi adakin matar wani Alhaji da lari take kai masa nono har gida.
Shekara daya data biyo bayan haduwar salim da lari don kullum acikin tunanin dogon saurayi mai tabarau take. Tabaran daya bata ya kasance tamkar wata layar sa'a agurinta domin duk inda zata bata rabuwa da tabaran dashi take kwana akusa da ita haka nan duk inda zata yana tare da ita amakale agefen zaninta kuma lari ta riga ta camfa tabaran da cewa duk ranar dataje dashi tallar nonon anfi sayewa da wuri kuma wai nonon yafi yin kudi masu dan kauri. Akullum kwanan duniya idan lari ta kama hanya zuwa garin yola tallar nono saita tsaya adaidai inda suka hadu da salim ta danyi jim na yan dakiku tana bijiro da daddadan kalamansa cikin zuciyarta sannan tayi gaba abinda. Yan uwanta da suka kai nono tare sun taba tambayarta abinda yasa kullum take tsayawa daidai gurin sai lari ta kada baki tace.
Farin cikin rayuwata nake tunawa. Da yawa daga cikin yan uwanta sun fara tunanin me yiwuwa gamo tayi da aljani. To amma abinda ke sa su shakkar hasashensu shine in ka dauke tsayuwar da take adaidai gurin babu wani abu da lari takeyi na mu'amalarta wanda yayi kama da bacewar hankali.
Sannu ahankali kwanaki na shudewa lari nata tsammanin zasu sake haduwa da salim har dai ta fitar da rai. Wata sa'ar idan tunaninsa da shaukin ganinsa suka dami zuciyarta saita koma can bayan garken shanunsu tasa tabaransa agaba tayi ta kuka tana wake Salim da wata murya kasa kasa mai kamar rada cikin harshen fillanci.
Rannan da rana ranar datayi daidai daRan nan da rana ranar datayi daidai da shekara daya da haduwarsu da salim sai wani Alhaji daya saba sayen nono agurin lari ya aiketa gidansa dake nan daf da kasuwar domin takai wa iyalansa nonon daya saya. Lokacin da lari ta isa gidan saita tarar da matansa biyu zaune awani dakin shakatawa suna kallon fim din GAIBU.
Lari ta basu nonon ta kuma gaishe su saitaga yakamata yau daya dai ta tsaya ta kashe kwarkwatar idanunta tunda dai nononta ya kare da wuri.
Lari ta zauna akan kilishin dake mamaye da dakin shakatawar taci gaba da kallo abinta ita da matan mutumin.
Fara kallonta keda wuya sai aka nuno wata kyakkyawar budurwa mai iya kwalliya zaune acikin wani lambu ma'abocin furanni sannan a zaune akusan da kyakkyawar budurwar sanye da riga da wando kwat da bakin takalmi sau ciki yana sheki kamar mudubi dogon saurayine salim mai tabarau ko shakka batayi shine. Lari taji zuciyarta ta harba tsakanin hakarkarinta yawun bakinta ya kafe nan da nan taji wani tsananin kishi ya soki zuciyarta musamman ma sa'ar da kyakkyawar budurwar ta matsa daf da salim da faffadan murmushi tace.
Shin kana jin zaka iya aurena kuwa?
Lari ta mike tsaye jikinta na rawa adaidai sa'ar da matan da suke zaune tare suka dauki sowa da tafi.
Lari taji kamar ita sukewa dariya don haka cikin sauri saita fice daga dakin shakatawar batareda sun lura ba domin kallon fim din suke abinsu kuma yana burgesu.
.
Sa'ar da lari ta dawo gida ayammacin ranar bata iya kurbar koda makwarawar ruwa ba ballantana wani abu wai shi abinci. Har garin Allah ya waye tana kuka rungume da tabaran da salim yabata a kirjinta,
washegarin ranar da abin yafaru ko tallar nono bataje cikin gari ba.
Maimakon hakan saita koma karkashin wata katuwar bishiyar maina dake bayan garken shanunsu tayi tagumi azuciyarta tna tunanin hanyar da zatabi ta sake ganin wannan kyakkyawan saurayi dogo mai tabarau.
Gaban lari yafadi sa'ar data tuna da bala'in dake boye da ita shekara da shekaru na farko dai ta riga tasan koda ta sake haduwa ma da wannan saurayi salim to abanza domin tasan babu makawa ko mutuwa zatayi sai an aura mata JA'E.
Don tun tana yar kankanuwa shekara biyar kacal aduniya aka bata wannan dan dukurkushin saurayi mai tarin suma cako cako atsaitsaye kamar kayar bushiya saurayin da lari ta tsana kamar yadda ta tsani mutuwarta. Haka nan lari nada masaniyar cewa tuni samari biyu sun sheka kiyama duk saboda ita. Wannan shiyasa sa'ar da suka hadu da salim ta nuna masa in zai sake nemanta yaje bakin kasuwa maimakon tace ya nemeta a rigarsu.
.
Don haka ayanzu da lari take zaune a bakin koramar kafafunta acikin ruwan zuciyarta cikin zullumi da fargabar halin da kaddara ta jefata aciki ta riga tasan duk wani mafarki data ke na mallakar dogon saurayi mai tabarau shirme ne domin ayanzu zaman da take sati guda kawai ya rage a daura mata aure da Ja'e. Saurayin da akayi masa alkawarinta tun kusan shekaru goma da suka shude.
Ba'a banza lari take kin ja'e ba.
Na farko dai tun lokacin da lari ta kawo munzalin mace ta fahimci cewa wannan saurayi ja'e mummuna ne na gaske dan dugurgushi baki wuluk fuskarsa kamar an shafa masa shuni yana da tarin sumar sama da shekara biyar ba aski akan katon kansa. Wannan ita tasa idan ka hango shi daga nesa saika tsammaci bakin rawani ja'e yayi saboda girman kansa yana da katon hanci tababbe kamar an daki fura da tafin hannu. Shekaru uku da suka wuce aka buge hancin da sanda agurin farauta ja'e bai damu da wanka ba gashi bakin jahili don ko yar makarantar yaki da jahilcin da akeyi a rigar bai taba lekawa ba bugu da kari kuma ance ja'e bai damu da wanke baki ba. Kullum bakinsa na wari kudaje na shawagi kamar bakin kura. To saidai kuma fa duk wannan nafila ne ga halayyar ja'e domin mafi munin al'amarinsa shine ja'e maketaci ne marar imani na gaske domin jita jita na cewa sau uku yana kashe mutane. To saidai kuma har zuwa wannan lokaci da lari ke zaune abakin wannan koramar tana tunanin hanyar da zatabi ta rabu dashi babu wata kwakkwarar shaida data tabbatar da hakan. Lokacin da lari take yar shekara goma wani bafulatani saurayi waishi HAKIMI yataba nuna sha'awarsa agareta mutane da yawa sun tseguntawa hakimi cewa anriga an baiwa Ja'e lari sun kuma gargadi hakimi akan ya rabu da ita. Hakimi baiji ba don haka rannan sai aka tsinci gawarsa acikin wannan koramar da lari take zaune ayanzu an fafe masa ciki da wuka shekaru biyu da faruwar wannan al'amari wani saurayi waishi MUDI bahaushe ne yake shigowa tun daga cikin gari zuwa rigar yana kokarin zantawa da lari abakin wata garkar rogo.
.
Ka rabu dani.... Dan Allah indai kana son kanka da lafiya. Lari tace da mudi watarana da yamma sa'ar dayasha gabanta daidai gonar rogon.
Bazan iya rabuwa dake ba lari domin na riga na mace akan kaunarki. Baifi sati guda da wannan kalamin ba aka tsinci gawarsa atsakiyar garkan rogon an fafe masa ciki da wuka.
Mutanen dake kusa da wannan yanki sun yi imanin cewa duk Ja'e ne ke aikata wannan tabargazar
To amma babu wata cikakkiyar shaida.
Lari ma tasan da haka wannan ita tasa abubuwan duniya suka taru suka cakude mata zaman gida yayi mata zafi don haka sai ta taho bakin koramar domin ta sami damar tunanin hanyar tsira.
Daidai da dakika guda lari bata taba jin cewa zata iya auren mutum kamar ja'e ba koda adacan to ballantana kuma sa'ar data dora idanunta akan salim saurayi mai fara'a da iya dadin zance.
Lari ta lumshe idanunta hawaye yafara sartu akan kyakkyawan kumatunta har yanzu tabaran na hannunta tana jujjuya shi lokaci lokaci takan kara tabaran a fuskarta ta lumshe idanunta.
Sati daya ya rage kawai! Sati guda a daura aurenta da maketaci ja'e. Lari tace cikin zuciyarta dole ne na sami mafita.... Wallahi ba zan iya aurensa ba bazan iya ba! Ta sake fashewa da kuka. Adaidai lokacin ne taji kamar motsi abayanta. Bata damu data juya ba domin ta riga tasan ko wanene domin yasha samunta abakin koramar alokutan baya.
La...ri. Wata rarrunar murya tayi kiran sunanta abaya cikin sauri ta juya domin taji ashe ba muryar ja'e bace. Koda ta juya saitaga NAFI'U atsaye dogare da santa akansa a sunkuye.
Koda lari ta dubi nafiu saitaji gabanta yafadi domin tasan rayuwar na cikin hadari.
Tunda jimawa lari take tattare da masaniyar cewa nafiu fa yana kaunarta amma a boye sau da yawa yakan gaishe wata sa'ar har kyautar fanke mai nama yakeyi mata dayake shi wayayye ne dan kusan kullum acikin garin yola yake wuni inda yake halartar makarantar gaba da sakandire. Akwai sa'ar ma da yake kawo mata kayan ado irin na mata yakuma tabayi mata kyautar farin gyale mai dishi dishin dutse launin gwal to amma fa duk wannan kyauta sai aboye yakeyi mata don ya tabbata idonsa idon ja'e yashiga uku ya lalace. Wannan shiyasa ita kanta lari mamaki ya kamata sa'ar data juya ta ganshi abayanta dogare da sanda littafinsa na karatu a makale a hammatarsa.
Na....fiu me yakawo nan? Lari tace tana dubansa a tsorace muryarta na rawa. Nafiu ya tsugunna agabanta kana ya dubeta yace.
Zuwa nayi in da damar taimako na taimaka miki... Na lura kamar kina cikin tashin hankali.
Lari ta sunkuyar dakai na tsawon lokaci sannan saita dago kai ta dube shi tace.
Nafiu ka kyautata min alokutan baya shiyasa kake burgeni kuma inason nace ma nagode kuma don Allah ina son ka taimakeni ka tashi daga nan ka kyale ni domin bana son wani tsautsayin ya fada ma ka riga kasan halin danake ciki.
Nafiu ya gyada kai.
Na fahimce ki amma kina son ki sani cewa indai akanki ne bana tsoron komai yafaru a kaina nasan ba dole bane ki so ni amma ki sani cewa ni ina kaunarki azuciyata kuma ina son idan har akwai wani taimako da zan iya miki ki fada min shi ko menene zan yi miki domin na nuna miki cewa ni mai kaunarki ne. Koda bazaki iya sona ba ni ban damu ba ba abin kawai da nake so shine nayi abinda zai saki farin ciki.
Lari ta zuba masa idanu cikin tsananin mamaki domin bata taba tsammanin kaunarsa agareta yakai haka ba.
Nafiu... Ka rabu dani bana son ja'e ya cuce ka.
Kada ki damu larin indai har zan iya tsameki daga bakin cikin da kike ciki babu wani abu daya isa ya tsoratani koda kuwa mutuwa ce.
Lari ta tsame kafafunta daga cikin ruwan ta dada fuskantarsa sosai.
Kana jin idan nafada abinda ke damuna zaka iya taimaka min? Cikin doki nafiu ya matso kusa da ita yace.
Fade shi ko menene indai zan iya nayi miki alkawarin yinsa. Lari ta dubi ruwan koramar na tsayin lokaci sannan saita rufe fuskarta kirjinta na harbawa tace.
Nafiu akwai wani saurayi da nake SO sama da shekara biyu kuma bansan inda zan same shi ba.... Sunansa SALIM. Nafiu yaji kishi ya soki zuciyarsa arance yace. Ina ma ni take so haka.
Salim a ina kika hadu dashi? Lari ta dada rufe fuskarta.
Akan hanya zamu kai nono cikin gari... Dan birni ne.
Nafiu ya dubeta a rude yace.
To ai lari da kinsan garin ma dayake da dasauki. Amma yanzu tayaya zamu iya ganoshi?
Hawaye ya subuce daga idanunta ta dubi Nafiu.
Wallahi... Nima abinda ke damuna kenan ban tambaye shi garinsu ba..
Nafiu yayi shiru na dan lokaci cikin rudani lokaci guda kuma ya caccaka gindin sandan dake hannunsa akasa cikin damuwa.
Kuma baki sake ganinsa ba tun daga lokacin?
Lari ta gyada kai ban sake ganinsa ba sai a talabijin acikin irin wasan kwaikwayon da akeyi nafiu yaji zuciyarsa ta harba.
Kin ganshi a wasan kwaikwayo? Kina nufin kice da Salim jarumin fina finan hausa kuka hadu? Nafiu ya tambayeta cikin kaduwa domin yasha ganin salim a finafinan hausa a sinimar cikin gari. Bashi da wani jarumi daya wuce salim ayanzu haka ajikin bangon littafin dake makale a hannunsa akwai sitikar hoton salim a manne ajiki.
Kasan shine? Lari ta tambaya cikin doki tana duban fuskarsa domin ta lura da sauyin yanayi a fuskarsa. Nafiu ya danyi shiru sannan ya ajiye sandarsa agefe guda ya dauko littafin dake makale ahannunsa ya bude bangon littafin ya dubeta yace.
Matso kusa ki gani wannan shine?
Jikin lari na rawa ta matsa kusa da nafiu ta leka cikin littafin.
Zuciyarta ta harba sa'ar datayi ido biyu da saurayin maiZuciyarta ta harba sa'ar datayi ido biyu da saurayi mai tabarau koda ta sake kallon hoton da kyau sai taga ai da irin tabaran daya bata ma ya dauki hoton.
.
Shine... Wallahi... A ina ka sami hotonsa?
Lari ta tambaye shi hawaye na kokarin sake kubuce mata nafiu ya dubeta yace.
Wanene baisan salim ba? Ai sai in mutum baya kallon finafinan hausa. Lari ta zabura ta mike tsaye jikinta na rawa tace.
Dan Allah ina zan sake ganinsa a... Ina yake. Nafiu ya dauki sandarsa sannan shima ya mike ya dubeta cikin damuwa yace.
Gara ma ke kinyi sa'a Allah ya nuna miki shi a zahiri ni in ba'a talabijin ba ko a hoto sai ko a mafarki amma ban taba ganinsa azahiri ba.
Kana nufin kenan ba ka taba ganinsa ba? Lari ta tambaya cikin karyayyiyar murya Nafiu ya girgiza kai.
Mutumin KANO ne. Ya danyi shiru yana duban lari cikin damuwa.
Amma inayi miki fargabar cewa kin dauko dala ba gammo domin salim ba karamin mutum bane kuma tun da nake arayuwata ban taba ganin mutum da farin jinin salim ba idan baki sani ba to yau ki sani duk kusan yan matan garin nan dake kallon finafinan hausa kaunarsa sukeyi. Sau da yawa zakiji suna zaginsa saboda hassada amma ina tabbatar miki da cewa azuciyarsu basuda wani abin kauna kamarsa ance dayawa daga cikin matan masu karancin tunani da hankali sun sha rabuwa da mazajensu saaboda shi.
Wannan shi yasa nace kin dauko dala babu gammo tunda yan matan birni ma wayayyu yaya suka kare dashi ballantana ke... Bayan kuma naji suna cewa wai yanada shegen girman kai kamar ibilishi. Lari taji kafarta ta fara rawa.
Indai a kano yake sai na nemo shi koda zan zagaye fadin garin ina tambaya. Inason kuma ka sani cewa ni sa'ar dana hadu dashi bai nuna min wani girman kai ba ko kankane domin shi ya kirawoni ya saye nonona muka dade muna hira dashi yayi min kyautar naira dari bakwai sannan daga karshe dana fasa masa sunana yace wai sunan na da dadi. Nafiu yayi tsaye yana kallonta sororo baki bude domin duk abinda take fada ta bayan kunnensa yake bi. Yasha jin a birni ana zancen girman kan salim in kuwa abunda ake fadi gaskiya ne yasan babu abinda zai hada salim da lari to amma kuma me zaisa tace sun hadu da salim in basu hadu din ba?
Wai Allah lari da gaske kike kin ganshi da idonki? Nafiu ya tambaya akan shakka lari ta dauko tabaran dake gurinta ta mikawa nafiu tace.
Kaga wannan tabaran ma shi ya bani in kuma baka yarda ba sake duba hoton zakaga da shima ya dauki hoton. Nafiu ya karbi tabaran cikin mamaki sannan ya bude bangon littafin ya sake kallon tabaran dake fuskar saurayin sannan ya dubi na hannunsa. Ko shakka babu irinsa daya. Tsahon lokaci yana kallon hoton sannan saiya dago kai ahankali ya dubeta.
Yanzu wane irin taimako kikeso agareni?
Ya tambayeta yanzu kam ya tabbata duk abinda ta fada gaskiyane.
Babu abinda nake so kayi min saika rufa min asiri sannan yau da daddare ka rakani nabar garin nan zuwa kano. Nafiu ya girgiza kai yace.
Ke lari baki taba zuwa kano ba tunda kike bazaiyu ba yau tashi daya ki shiga garin cikin dare lari ta dada matsawa kusa dashi ta tausasa murya.
Da'a aura min ja'e maketaci dana bar garin nan cikin dare wanne kafi so? Nafiu ya danyi jim cikin rudani ya riga yasan cewa ja'e macuci ne babba azzalumi. Ba lari dayake kauna ba ko akuyar dayake kiwo bazai so ta auri Ja'e ba don haka saiya dubi lari yace muryarsa na rawa..
Gara.... Ki Gudu... Da Ki Auri JA'E.
.
**** **** **** ***** **** *****
.
SIDI mai jaka yayi shiru sa'ar dayazo nan sannan ya dubeni yace Nas ina fatan kana biye dani akan wannan dogon zaren labari. Na gyada kai nace.
Kwarai kuwa baba amma ni nakasa gane irin wannan wauta ta yan mazan zamani yaya baki taba zuwa gari ba bakisan kowa agarin ba zaki tafi neman wanda shime yiwuwa ma tu agurin da kuka hadu ya manta dak? Sidi mai jaka ya canko wasu dankwala dankwalan tubanai guda biyu ya jefa abaki. Idanunsa suka fara diga kamar kuturu saboda yaji amma duk da haka dattijon bai nemi ruwa ba. Azuciya nace lallai idan naci gaba da kawo tubanin nan watarana sai nayi kisan kai.
Ai Nas kayi mamakin al'amarin na irin wadannan mata domin yadda suke kaunar jaruman shirin fim abin ya wuce tunanin mutum amma banga laifinsu ba domin irin yadda matasan jaruman ke kwaikwayon abu ashirin fim saika rantse da Allah da gaske ne wannan shike rudar wadannan mata amma fa nas kada kayi kuskuren fahimtar zaren labarin nan kaga Lari kaunar salim takeyi tsakani da Allah badon jarumtakarsa ta shirin Fim ba.
Hakane nace dashi.
Yawwa Nas. Bari to nayi sauri na karasa maka wannan zaren labarin kafin na dauki na karshe wanda daga shine zan hada maka zararrukan guda uku guri guda na kullesu.
Ina sauraron ka baba sidi. Nace dashi sannan na gyara zama.
Yawwa nas to adaren wannan rana saia aka yi rashin sa'a domin tun da magariba aka kece da ruwa kamar da bakin kwarya. Wannan ita tasa nafiu bai sami damar zuwa gidansu Lari da karfe takwas ba kamar yadda sukayi alkawari sai karfe tara saura. Nafiu ya jinkirta zuwansa tun farko ne domin
A tsammaninsa za'a tsagaita ruwan to amma ganin ruwan sai karuwa yakeyi shiyasa shi biyowa cikin duhun daren ruwa na dukansa ya shiga rigarsu Lari.
Sa'ar da nafiu yakawo rigar saiya dabarbarce ya rasa abinda ya kamata yafari domin ayadda suka shirya a yammacin ranar sun yanke cewa zai sami lari ne agindin wata katuwar bishiyar mangwaro dake arewa da garken shanunsu to amma ruwan saman da ake ketawa ayanzu kamar da bakin kwarya shiyasa shi cikin wasi wasi domin yasan abune mai wuya lari ta iya jiransa cikin wannan uban ruwan da ake shekawa.
Nafiu yayi tsaye cikin duhun jikakken daren ruwan na dukansa babu ko kakkautawa lokaci lokaci yakan sa hannunsa ya share ruwan dake zuba akan fuskarsa daga inda yake tsaye yana iya hangen duhu duhun bukkokin dake rigar sannan lokaci lokaci yakanji bololon kukan shanu jifa jifa. Nafiu yaji

Please Login or Register in order to submit comment