Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuke yi mana ne? Falmata ta tambaya. Salim ya gyada kai da murmushi.
Ko zamuje ne ki ga yadda akeyi? Tabbas falmata Nason zuwa taga yadda ake daukar fim domin kullum burinta kenan amma jin shi yafara yi mata tayi sai ta girgiza kai ta dube shi a kunyace tace.
A'a... In kun gama dai ma gani a kaset.
Jin amsar ta yasa salim jin haushin kansa da kansa. Bi a hankali dan samari kada ka yi gaggawa ka bata rawar ka da tsalle. Ya fadawa kansa.
Wane irin kaya yakamata nasa gobe idan Zanzo. Salim ya dubeta ya fashe da tattausar dariya.
Haba malama saikace mai zuwa gidan biki.. Ina ni ina zabawa bakona kayan da zaisa falmata ta tsuke baki ta Kalle shi ido da ido sannan ta kashe murya tace.
Salim yau shekara biyar kenan ina burin nasaka a idanuna sai yau nayi dace cikar burina wannan shiyasa Nake fargabar kada na saka kayan da bazasu faranta maka ba. Salim yaji gabansa ya fadi. Wato har ta fara yin tayin kanta a gareni. Yace cikin zuciyar sa sannan sai yace da ita a fili.
Kyakkyawa kamar ki bata bukatar zaben kayan da zata sa na tabbata ko algarara kika yafa ajikin ki sai kinyi kyau domin irin kune ke sa kaya yayi kyau. Ba kaya ne ke saku yi kyau ba.
Wannan bayani na salim ya dada narkar da zuciyar falmata nan da nan ta ji kaunar sa ta dada kunna kai cikin zuciyarta.
Kai salim zugarka.... Bata sami karasa kalamin ta ba sakamakon motsin da suke ji a bayan su.
Idan kun gama surutun banzan saika dawo ciki ana jiran ka wata murya tace dasu daga baya salim yaji gabansa ya fadi ras. Cikin sauri ya juyo kalima ta Harare shi idanunta a zazzare kamar zata haushi da duka.
Falmata ta dubi kalima. Kalima ta dubi falmata basa bukatar sake hada idanu akaro na biyu domin sun san sun har abada bazasu sake kaunar juna ba.
Ni zan tafi salim nagode sosai... (Take Care) falmata tace dashi gamida haskake shi da murmushin alkawarinta saita sha kwana ta nufi dakinta.
Salim yabita da kallo har saida ta kule sannan a hankali sai ya juyo ya dubi kalima.
Munafuki tsayar me kuke da ita? Daman wannan shine shan iskar? Salim yayi tsaye bai ce da ita uffan ba idanunsa akan fuskar ta akaro na farko tun sa'ar daya fara ganin ta sai salim ya fara tambayar kansa da kansa wai shin dan Allah me yagani ne tun farko a fuska da jikin kalima da har yake ta gama binta yana rokon ta aure shi tana ja masa rai. Koda salim ya sake kallon fuskar kalima alokacin sai yayi kokarin kwatanta ta da falmata data bar gabansa yanzun nan ga tsananin mamakin sa sai yaga tamkar hadin fitilar kwaine da haske rana. Dan haka a yanzu da ya kurawa kalima idanu sai yaga duk tayi masa TSUFA.
Sai kuma alokacin ne ma ya lura da cewa fuskar ta har ta fara alamun tauye daga tsakanin hancin ta zuwa bakinta rufin asirin hoda ne kawai ke lullube da fuskar.
.
In har ban cancanci ki girmama ni a matsayina na ubangidan ki ba to ina ganin kuwa bai kamata ki kirani fa kalmar munafuki ba salim yace da ita fuskarsa a hade sannan saiya rabe ta kusa da ita ya nufi dakin da suke daukar fim din cikin sauri.
Haka zakace dani salim? Kalima tace a fusace salim baiko juyo ba balle ya Kalle ta abin dake xuciyarsa a yanzu shine kyakkyawar fuskar nan ma'abocin MURMUSHIN ALKAWARI.
.
****** ******* ******* ******** ****************
.
Washegari da safe misalin karfe tara na safe salim yafito daga rantsatstsen dakin kwanan sa zuwa cikin dakin shakatawar sanye da sabuwar riga shat baka akirjin ta an rubuta KANYWOOD wandon dake jikinsa launin toka tokane mai fatsi fatsin fari daga nesa saika dauka kashin tattabaru ne ajikin wandon amma sa'ar da salim ya dubi kansa ajikin madubi kafin ya fito sai yaga rabon dayasa kayan da suka kwanta masa arai kamar wannan har ya manta. Duk kuwa da haka zuciyar sa bata daina wasi wasi ba domin har yanzu gani yake yi kayan basu dace ya tari wannan kyakkyawar dasu ba.
A bandaki sa'ar da ya shiga wanka saida ya shafe sama da sa'a daya da rabi ajikin mudubin yana taje gashinsa gamida sa masa sinadaran mai domin yana daukar idanu aduk lokacin da haske ya sauka a Doron kansa. Wannan shafe shafe da goge goge saida ya baiwa salim dariya. Oh saikace wani dan daudu... Ka fita kawai ahaka tunda dai ko me zakayi baka isa ka dakushe kyawun ta ba. Salim ya fadawa kansa sa'ar da ya gama gyaran gashin.
Dan haka a yanzu da ya shigo falon sai ya dada kara hancin sa akusa da kirjinsa kamshin turare sama da kala takwas daya farfesa kadan kadan ya bugi hancin sa duk tsiya dai bata isa ta gane kamshin turaren dake jikina ba salim ya dada fadawa kansa sannan saiya dubi rantsatstsen agogon dake hannunsa kana ya nufi teburin dayasa aka shirya da kayan ciye ciye da Shaye Shaye na musamman duk dan saboda zuwan falmata tsawon mintuna biyar salim yana tsaye akan teburin yana nazarin kayan kwalam da makwalashen
Ta Saman tabaron dake tsaye tsaf asaman Doron hancinsa daga karshe saiya gyada kai cikin gamsuwa gamida yabawa Yaron sa Salo. Wajen wannan babban aiki.
Sannan saiya nufi kan kujerar dake fuskantar kofar shigowa falon ya zauna ya dora kafara ta hagu akan ta dama sannan ya dauki mujallar fim yafara karantawa bai ji motsi an shigo dakin shakatawar ba. Salim na dago kai daga kan mujallar sai sukayi ido biyu da KALIMA.
.
Gabansa ya fadi sa'ar daya ga kamanninta domin ko shakka bayayi yasan yau sai sun debo tsakiyar miyagu da ita.
KALIMA ta shigo cikin falon tana takawa a hankali sanye da doguwar riga baka har kasa ta rufe kanta da wani dan sirrin Gyale mai kamar rawani kafarta sanye cikin bakin takalmi mai tsinin dunduniya hakanan a rataye a kafadarta kamar zabira wata farar jakace mai shan kwallon kafa a gefen ta daga hannun hagu an rubuta da siraran haruffa kamar tafiyar tsutsa kamar haka TOWN GIRL.
Kalima ta nufi daya daga cikin rukunin kujerun dake bangaren kudu ta ajiye jakar ta ta zauna a hankali ta harde kafafu sannan saita dubi katon teburin mai dauke da kayan makwalashen na dan lokaci sai kuma ta dubi salim daga karshe.
Duk abin da take salim baice da ita kala ba.
Domin irin abin da take kai kace a fagen daukar fim suke. Haka nan salim ya lura da idanunta duk sun yi jajur har ma sun dan kukkumbura kamar wacce ta kwana tana KUKA.
.
Tsawon lokaci kalima na zaune akan kujerar tana karkada kafafu fuskar ta murtuke kamar Kamu tana kallon salim can sai tayi ajiyar zuciya sannan saita sunkuyar da kai kasa.
ITA KAKE JIRA?
Kalima ta jehowa salim tambayar ba zato ba tsammani salim yaji gabansa ya fadi yasan wa take nufi yakuma san boye mata wani abu a halin yanzu bazai kashe gobarar dake kokarin tashi ba Sai ma ko dai ya dada kunnata.
Don haka sai salim ya ajiye mujallar a gefen sa kana ya dubeta ya gyada kai kamar Kadangare batareda yace wani abu ba. Nan da nan sai yar hodar dake kan fuskar kalima ta fara narkewa a hankali tana haduwa da zazzafan gumin daya fara tsatsawo a fuskar.
Salim ya lura da Hakan kuma yasan Hakan na nufin yanzun nan zasu fara bala'i kenan.
Amma ga mamakin salim sai yaga kalima ta dago kai a hankali tace dashi a tausashe.
Son ta kake yi ne? Salim yaji kansa yayi wani gingirim domin tambayar tayi masa tsauri dan haka sai ya girgiza kai yace bakinsa na rawa.
Ziyara ce kawai tsakanina da ita... Sanin kanki ne ba yau mata masoyan Finafinaina ba suka saba kawo min ziyara.
Kalima ta dube shi sa'ar daya gama bayanin sannan saita yi masa wani faffadan murmushi tace.
Su ziyara manya amma ni tunda nake ban taba ganin bakuwar da kayiwa irin wannan karramawar ba. Ta Nuna teburin kayan makwalashen da hannunta.
Naga wasu maziyartan naka ma awaje kake samun su ko shigowa dasu ba'a yi ita wannan bakuwar ta musamman ce? Salim ya sunkuyar dakai sa'ar da yaji gumi yafara rufe shi haka nan jikinsa ya bashi cewa idanun kalima akansa suke. Shiru shiru na tsawon lokaci salim bai ce da ita kala ba jin haka sai kalima tace a tausashe.
Wallahi salim kabani mamaki domin ban taba tsammanin bayan duk dadewar da mukayi dakai ba dakuma shakuwar Da mukayi dakai daga karshe zakaci amana ta kafara fifita wata 'ya mace akaina. Salim ya dago kai sa'ar da yaji tafadi haka.
Idan kikace haka bakiyi min adalci ba kalima kiji fa abunda kika ce na fifita wata ya mace a kanki! Na dauka jiya war haka Ina Nan Ina rokon ki akan ki aure ni... Ki aure ni shin ashe yanzu a duniya har akwai wata fifitawa da tafi wannan? Kalima ta sunkuyar dakai nan da nan sai hawaye yafara sartu akan fuskar ta.
.
Kayi hakuri..... Salim Wallahi bansan abin da ya sami kaina ba Wallahi bansan ina kaunar ka ba sai jiya danaga inajin ina gani za'a rabani dakai..... Dubi fa jiya har muka tashi daga wajen fim din nan bakayi min magana ba.... Daga haduwa da ita har ka fara guje min.. Kalima ta fashe da kuka baki daya salim ya Mike tsaye ya nufi kan teburin nan ya tsiyayi ruwa mai sanyi ya kora a makwogoronsa domin duk ya bushe kana sai ya dawo ya zauna a inda yake cikin damuwa domin kukan da kalima take ya fara sosa masa zuciya.
Salim.... Kalima ta kira sunansa bakinta na rawa.
Haryanzu kana son ka aure ni? Ta tambaye shi da karyayyiyar murya.
Koda salim ya dago kai ya dubi jikakkiyar fuskar ta idanunta fari fat dan kwallin da tasa ma duk hawaye ya wanke shi sai ya kwatanta kalima da falmata cikin zuciyar sa sai salim yafara tunanin a yanzu fa ko a kafa aka daura masa kalima jefar da ita zaiyi. Domin kyawun ta ya riga ya gushe a gareshi.
Iye! Salima. Kai Nake tambaya kalima tace cikin kuka sa'ar da taga salim ya sunkuyar da kai. Abin da bata sani ba Shine da salim yafada mata hakikanin abin da ke zuciyar sa gara ma yayi shiru.
.
SALAMU..... ALAIKUM....
Wata kakkaurar murya tace dasu gaba dayan su suka juya firgigit suka dubi babban Yaron salim salo sa'ar daya shigo falon cikin sauri yazo ya tsaya agaban salim ya dubi kalima na yan dakiku sannan saiya dauke kai gefe guda yace da salim.
Kayi bakuwa... Tana waje wai so take ta ganka. Salo yace hannayensa biyu a harde a bayan sa salim yaji xuciyarsa ta harba da karfi dan ya riga yasan FALMATA TA BAYYANA.
Ga mamakin sa sai yaji ya dokanta daya sake ganin kyakkyawa MURMUSHIN nan nata. Tuni har yafara ganin wushiryar ta a fili cikin zuciyar sa
To me yasa baka shigo da ita ba? Na dauka tun jiya Nace ma ina sa rai da zuwan bakuwa?
Salim yace yana duban salo saurayin mai tarin suma kamar kayar bushiya ya dubi salim da wani munafukin murmushi yace.
KA gane Oga. Bawa bebi din bata hadu vane amma ni sai Naga kamar..... Irin ka gane beb din yar kauye ce shiyasa ban shigo da ita ba.... Amma fa ta hadu Zita. Ashe a kauyen ma akwai kyawawa haka. A daidai lokacin ne kalima tayi zumbur ta mike tsaye tana share hawaye.
Ina zaki? Salim ya tambaye ta.
Daki zan shiga idan ka gama da ita na dawo kafin salim ya sami damar cewa wani abu tuni kalima ta wuce zuwa dakin kwanan sa ta shige sannan ta mako kofar da karfi salim yayi ajiyar zuciya ya dubi salo a rude yace.
Yar kauye fa kace salo? Salo ya gyada kai yace
Kwarai kuwa Amma fa kyau sai ka zagaye duk duniyar fim baka sami mai kyaun ta ba... Saidai kawai rashin diresin dayayi mata yawa.
Kaidai shashasha ne salo yaya zaka dubi wannan kace mata yar kauye kai kaga irin diresin din dake jikinta kuwa jiya da muka hadu da ita? Salo ya gyara tsayuwar sa yace
Haba Oga Wallahi wannan beb din yar kauye ce amma kyau Kam kamar ita tayi kanta wau.
Salim ya sunkuyar dakai na dan lokaci cikin mamaki ya riga yasan shakiyancin salo domin akwai lokacin da yake son yi masa wasa da hankali tunanin haka shiyasa ya dago kai yace.
Jeka shigo da yar kauyen.
Salo ya juya cikin sauri salim ya zurawa kofar idanu barka da zuwa falmata salim yace cikin zuciyar sa ba a dade ba sai salo yashigo yarinyar na biye dashi Abaya suna zuwa sai salo yayi gefe guda sannan je to salim yayi ido biyu da ita. Budurwar tayi tsaye agabansa sanye da wata yaloluwar riga doguwa ta yage daga gefen hannunta na dama yalolon gashin kanta ya sauka akafadar ta kafarta sanye cikin takalmin roba danyen kyau na zuba daga doguwar fuskantar mai sheki.
Budurwar ta dago kai ta dube shi da manya manyan idanunta farare sannan saita jefa masa wani abu akan cinyar sa jikinsa na rawa salim ya dauki abin koda ya duba sai yaga ashe TABARAU ne.
Ko har yanzun ma baka Gane ni ba? Budurwar ta tambaye shi cikin tattausar murya mai sa shauki.
.
Hannunsa na rawa ya dago kai ya dubeta yace.
NA GANE KI... TAYAYA ZAN MANTA DAKE LARINa gane ki..... Tayaya zan manta dake LARI.
.
BIYAR 5
Sidi mai jaka yayi wata doguwar hamma kamar zai yaga baki lokaci guda kuma ya dubi kwanon tubanin cikin takaici domin duk yawan tubanin nan ya hadiddiye shi bai fi dunkule biyar ba acikin kwanon.
Kai... Wallahi nafara Jin barci Nas. Sidi Mai Jaka yace lokaci guda kuma ya dada dame baki kamar kada ya dada yin wata hammar akaro na biyu.
Amma dai ko barci kake ji zaka karasa min ko baba Sidi? Na tambaye shi cikin kaduwa domin ba karamin aikin Sidi mai jaka bane ya ajiye labarin anan sai kuma mun sake haduwa idan kuwa yayi haka ba karamar gamawa dani yayi ba domin yanzu ne ma labarin ya faro dadi.
Kada ka damu Nas. Baba Sidi yace dani yana duban agogo
Sai yanzu ma sha biyu tayi bari nayi sauri mu gani ko na karasa maka kafin lokacin Sallar azuhur.
Yawwa baba Sidi nagode. Nace dashi. Sidi mai jaka ya dube ni kana ya tura busassun yan yatsun sa cikin farin gashin sa yace.
Kaga Nas sannu a hankali na hade maka zararrukan labarin nan guri guda ko? Na gyada kai bance komai ba.
Yawwa to bari kuma mu shafawa zararrukan labarin kala mu ga abin da zasu bamu. Ya danyi shiru kana saiya dubeni yace.
.
A daidai lokacin da duk wannan ke faruwa a gidan jarumi salim. Falmata na can dakinta kwance cikin zullumi domin ta fahimci cewa ita da sake fita waje da hasken rana sai baba ta gani dole ne ta fara halin Mujiya.
Al'amarin daya jefata cikin zullumi yafara ne tun adaren jiya bayan ta fito daga wanka zuciyar ta fari fat domin ga dukkan alamu mafarkin data dade ta nayi shekara da shekaru ya kusa zama gaskiya.
A tunanin falmata sa'ar data fara kokarin gabatar da kanta ga salim ta cikin waya ta dauka saita dade tana tarairayar sa kafin ma ya yasami damar kula ta. Amma ga mamakin ta sai taga ashe ma salim din arahar gani ne dashi kamar rana koda yake sa'ar data dawo dakin bayan sun rabu da salim ta sake duban kanta ajikin madubin saita yiwa kanta murmushi tace da kanta.
Banyi mamaki ba don na ruda shi.... Domin ni kaina idan na dubi kaina rudewa nake.
Falmata ta riga tasan tagama kame zuciyar salim abin kawai take bukata shine sake haduwa gobe ko shakka batayi rabuwar salim da wannan nacacciyar mai fuska kamar robar yazo karshe.
Da wannan kwarin gwiwar falmata ta fito daga wanka daure da tawul a kirjinta kamar yadda ta saba ga al'ada kafin ta nufi kan gado sai taga yadace ta saurari wakokin Fina finan salim.
Ko ta dada samun kwanciyar hankali tana rausaya ta nufi inda yar redion ta yake wacce ta zo da ita cikin akwatin kayan ta tare da kasa kasan wakokin fim din salim sa'ar data dauko rediyon ne wata zuciya ta ce da ita tun fa da kika zo garin nan baki saurari gidan rediyon su ba.
Wannan tunani shiyasa falmata kunna rediyon kunnawar ta keda wuya sai ta ji wakar wani fim din salim data taba gani na tashi a rediyon cikin sauri falmata ta dauki rediyon ta karo sauti sannan ta kwanta rigingine akan gadon rediyon a ruwan cikin ta idanunta a lumshe ta ci gaba da jin daddadan sautin da a zuciyar take tsammanin muryar babban masoyin ta salim ce tana nan cikin wannan hali kwatsam sai aka dakatar da wakar sannan ne to zazzakar muryar mai labaran ta bayyana inda ya kira shirin da sunan INDA RANKA.
Falmata tayi tsaki zata kashe rediyon sai ta ji mai labaran yafara karanto kanun labaran kamar haka.....
....... WATA MATA MARAR IMANI TA SOKE CIKIN MIJINTA DA WUKA YA SHEKA BARZAHU A YANZU HAKA JAMI'AN TSARO NA NAN SUNA NEMAN TA RUWA A JALLO DOMIN SUYI MATA TAMBAYOYI.... WAKILIN MU DA KE BARNO ZAI ZO MUKU DA CIKAKKEN LABARIN......
.
Falmata tayi jifa da rediyon zuwa tsakar dakin rediyon ta rabe biyu. Falmata ta lumshe idanu jikinta yafara yawa kamar mazari. Har garin Allah ya waye batayi barci ba.
Washe gari tun da sassafe ta aika a sayo mata jaridu. Ba karamar kaduwa tayi ba sa'ar da taga uku daga cikin jaridun shidan da aka kawo mata dauke suke da manya manyan hotunan ta a gefen hoton jaridar farko an rubuta kamar haka
...... SHIN KO KUN GA WANNAN?
IDAN KUN GANTA KUNA IYA SANAR DA OFISHIN JAMI'AN TSARO MAFI KUSA DAKU DOMIN ANA BUKATAR YI MATA TAMBAYOYI DA SUKE DA ALAKA DA KASHE MIJINTA CIKIN RASHIN IMANI.
A cikin sauran labarin ne falmata ta karanta hirar da yan sanda suka yi da mijinta saifullahi asibiti ashe ma saida ya kwana biyu a asibiti kafin ya mutu.
Wannan shi ya rusa duk wani mafarki na falmata yanzu kam tana riga tasan ko acikin otal din bata isa tayi yawo da rana ba domin hoton ta ya gama gari.
Dan haka a yanzu da falmata ke kwance akan gadon hawaye na zuba daga idanunta tasan cewa haduwa da salim a yanzu Abune Mai wahala domin bazata iya fita da rana ba ana farautar ta kamar mujiya. Don haka saita yanke shawarar ta buga masa waya ta sanar dashi cewa bazata sami damar zuwa ba saida magariba hannun ta na rawa ta daddanna lambobin salim sannan ta kara a kunne tana jiran salim ya dauki wayar sannan ne to ta tambayi kanta da kanta tambaya mai tsada. SHIN KWANA NAWA ZA'A DAUKA KAFIN SU KAMANI?
Ta riga tasan ko ba dade ko ba jima kudin dake jikinta zasu kare kuma jami'an tsaro zasu cimmata falmata ta fashe da kuka jikinta na rawa kamar mai zazzabi ba kamun ne yasa ta kuka ba tunanin rabuwa da salim ne ke damunta.
.
******** ********* ******** ******** ****** *****
.
Salim yayi kokarin Mikewa tsaye sai yaji kamar idan ya tashi faduwa zaiyi sakamakon jirin dake daukarsa don haka sai ya dubi salo yace.
Kana.... Iya tafiya idan falmata Tazo ka wuce da ita wajen saukar baki zan same ku acan.
Salo ya rankwafa kadan sannan ya sake kallon lari wacce haryanzu take tsaye ya fice daga dakin.
Zauna Lari. Salim yace muryar sa na rawa lari ta zabi guri guda a tsorace daga baki bakin kujerar.
Saki jikin ki kizauna sosai lari ta dube shi a kunyace tace.
HAKA ma ya isa nagode. Salim yayi shiru yana jujjuya tabaran data bashi na tsawon lokaci kwakwalwarsa ta kasa tunanin komai domin hankalin sa ya rabu gida uku can cikin dakin kwanan sa KALIMA ce yakuma tabbata duka abunda akeyi afalon tana saurare haka nan yasan kowane lokaci daga yanzu falmata na iya zuwa kuma ga lari yar Fulani zaune agabansa.
Naga kamar bakaji dadin zuwa na ba.
Tattausar muryar lari ta ratsa shirun dake falon salim ya dago kai ya dube ta yace da ita a tausashe.
Bahaka bane lari Wallahi samuna kikayi acikin tarin matsaloli amma ina ganin zuwan ki tamkar wani sauki ne daga Allah salim yayi shiru sannan batareda ya dubeta sai ya nufi teburin kayan makulashen ya janyo shi zuwa inda lari take zaune sannan saiya zauna akusa da ita ya dauki kofi ya tsiyaya mata tataccen ruwan kayan marmari mai sanyi ya mika mata.
Sha wannan lari. Lari ta dube shi a kunyace kana ta girgiza kai gamida jifansa da wani dan marayan murmushi.
Nasha ruwa zan taho salim ya dan hade fuska sannan ya dada mika mata kofin yace.
Wannan ba bakin ruwa bane sha ki ji lari ta karbi kofin bata dube shi ba ta rike a hannun ta amma bata kai bakinta ba.
Sha mana.... Lari kada fa ki bata min rai jin haka keda wuya sai lari ta kai kofin bakinta tasha ruwan lemon sannu a hankali salim ya dauko wancan yabata ta dan ci ya dauko wannan yabata har dai lari ta dan ci kayan dadi da dan dama bayan sun gama ne salim ya dubeta yace.
Waya kawo ki gurina nan? Lari ta sunkuyar da kai.
Ni kadai Nazo...... Ta danyi shiru
Daman kina da yan uwa agarin nan ne?
Lari ta girgiza kai.
Bani da kowa SAI KAI kuma saboda kai nazo garin nan. Ta danyi shiru sannan sai tace
Yanzun ma auren dole za'a yi min da wani saurayi shiyasa na gudo gurin ka.
Ki ka gudo gurina? Salim ya maimaita abin da tace cikin Kaduwa. Lari ta gyara tsahon Gyalen ta rubabbe mai kamar algarara kana ta ci gaba da cewa.
Bazan boye maka komai ba salim... Domin banida wanda zuciyata ta amince dashi sai kai.... Banajin zan iya auren wani mutum a duniya idan ba kai ba.......... To amma nasan a so ba'a dole mutum kamar ka ba'a rabashi da tarin mata masu kaunarsa. ta sake yin shiru kanta a sunkuye.
NIDAI gani gare ka tun ranar da Allah ya hadani dakai kace zaka dawo baka dawo ba na shiga halin kunci bana ganin komai a zuciyata sai kai.
Salim yaji duk al'amarin kamar a Mafarki.
Ya daga hannayen sa guda biyu ya rufe fuskar sa dasu yana tunanin shin meke faruwa a gareni ne?
YA tambayi kansa sannan sai yafara dauko hoton kalima cikin zuciyar sa ya dauko na falmata sannan sai lari ta dora hotunan da kuma halayen sa akan Doron sikelin xuciyarsa ya auna.
Salim ya riga yasan tun sa'ar daya fara ganin lari yaji kaunarta ta mamaye xuciyarsa domin tayi daidai da irin matan dayake so ya zauna dasu masu karancin wayewar rudadden zamani irin wannan.
Hakanan salim yasan yana kaunar kalima saboda sun dade kuma sun saba da ita sannan kuma zuciyar sa Nason falmata don tsabar kyawunta badon komai ba toh amma duk a cikin su babu wacce zai kebe da ita ya sami nutsuwa sai lari. Kalima dai da man akullum cikin rikici suke yana yi mata bauta ita ko tana rainawa falmata kuwa kwana guda kawai yayi da saninta bai ma san daga inda take ba duk da yake dai kyakkyawa ce amma ya lura da cewa wayewar ta yayi yawa domin in bahaka ba me zaisa ta sauka a hotel maimakon ta nemi gida?..... Koda yake ai tace bata san kowa ba.
Wannan al'amari su suka taru suka cunkushe kwakwalwar salim ya kasa tunanin abunda zaice da LARI.Wannan al'amari su suka taru suka cunkushe kwakwalwar Salim ya kasa tunanin abunda zaice da LARI.
.
Nasan da man da wahala ka auri yar kauye kamata kuma.... Tayi shiru sa'ar da muryarta ta fara rawa kamar zatayi kuka. Salim ya Mike tsaye ya nufi inda take ya tsaya akanta yace a tausashe.
Bari kuka... Lari Inason Ki kwantar da hankalin ki domin ina kaunar ki amma don Allah a yanzu Ina cikin wasu manyan matsaloli da suka sha gabana abunda Nake so dake shine dan Allah dan Annabi kibar kuka.... Ki kuma bani zuwa gobe dan inada bukatar tunani.
Salim ya danyi shiru sannan yaci gaba
A ina kika sauka ne? Lari ta dago kai ta dube shi tace
A yankaba nake.... Yau kusan kwanana biyar kenan da zuwa wata yar arziki ce ta tafi dani gidan ta domin lokacin da aka sauke mu a tashar yankaba karfe uku na dare... Shine da gari ya waye muka hadu da matar tana

Please Login or Register in order to submit comment