Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai a kunyace ta ce.
"sannunku dai bayin Allah."
Shiru na dan wani lokaci Sani ya sake cewa.
"in ba zaki damu ba abokina ne ke son tayaki za6en lemo."
Budurwar tayi murmushi tana duban Jamilu a kunyace.
"Ai na gama zaben, kuma ma ba wani abin kirki zan saya ba, madara ce kawai guda biyu."
.
Hakan kawai da ta ce, sai Jamilu ya ji yarinyar ta burge shi. Nan da nan ya matso kusa ya fara abin da aka saba.
"kada ki yi gaggawar cewa kin gama zabe, ai tunda nazo, to zabe ma yanzu kika fara. Zabi duk abin da kike so."
Budurwar ta dube shi a rude ta ce.
"Ni babu abin..."
Jamilu ya katseta ta hanyar daga hannunsa.
"Kada ki yi min haka 'yanmata, ai babu kyau maida hannun kyauta baya, ke dai bari ki gani in zaba miki."
Kafin ƙiftawa da Bisimillah sun cika mata jakar leda biyu da kayan ciye-ciye da lashe-lashe.
Wannan shi ne farkon ƙaddarar.
.
Suka dauketa a motar Jamilu har gida, tun daga ranar kusan duk kwana hudu ko uku sai Jamilu ya je gidansu Larai
Ba zai taba mantawa da kalamanta ba a ranar da suka fara haduwa da ita bayan su ajiyeta a ƙofar gida.
"Gashi kuma zamu rabu, amma ko sunanki ban sani ba."
Jamilu ya ce da ita yana murmushi. Budurwar ta dubeshi ido da ido sannan ta ce dashi.
"SUNANA LARAI..."
Ta dan yi dariya a ciki.
"ina fatan dai idan na dawo zaki yi farin ciki da hakan?"
Larai ta dubeshi a hankali na dan lokaci sa'anan ta dan yi ƙasa-ƙasa da murya ta ce.
"fiye da komai kuwa a duniyar nan. Ko yanzu ma da na fara ganinka a yau ina farin ciki, to ina kuma ga idan ka dawo?"
.
Soyayya suka yi tayi tsabtatacciya mara algus. Har ga Allah Larai Ƙaunar Jamil take yi kamar ta hadiyeshi, domin shi ne Ɗa namijin da ta fara qauna a duniya. To amma ga Jamil, abin hannun rigane da ra'ayin Larai, domin har kullum Sani Aliyu ya kan ce dashi.
"kada fa ka yi mana sanya, kayi qoqari ka sami rabonka kafin bikinka ya qaraso, kaga kullum lokaci ƙaratowa yake yi, to amma kai naga kodayaushe sai shukar banza kake tayi babu kyakkyawar yabanya."
"Ba haka bane."
Jamil ya ce dashi.
"ka san irinsu sai a hankali, tunda dai ta kamu da sona, ai aiki kamar ma an yi ne."
Sani ya girgiza kai.
"nifa har yanzu ina ganin sakacinka, yanzu ace kamarka kyakkyawa, ga ilimi, ga iya tsari, ga kudi amma ace har yanzu baka qwarance da harkar sabbin hannu ba.
"lokaci dai Sani...lokaci dai."
Abin kawai da Jamil ya ce dashi kenan.
Don haka a wani yammaci, misalin qarfe takwas na dare, bayan Jamil ya baro wurin abar qaunarsa Rukayya, sai ya tafi wurin Larai hira kamar yadda ya saba.
Ga al'ada idan Larai ta fito abin da zata fara yi shi ne, ta bude gidan gaba na motar ta shige abinta, sa'anan su fara hira da abin qaunarta Jamil, to a wannan yammacin tana shiga sai Jamil ya dubi Larai, ya ce.
"ya kamata yau daya mu tafi ki ga gidana, domin baki taba zuwa ba."
Buqatar tasa taxo mata a bazata, don haka sai da ta yi minti biyu bata bashi amsa ba, tayi kurum.
"ko baki son zuwa ne?"
Jamil ya tambaya, nan da nan Larai ta girgiza kai cikin hanzari, domin ko kadan bata son abin da zai batawa Jamilu rai.
"A haba Jamil, ai kafi qarfin komai a wajena, abin da yasa dama kaga nayi maka dan dum, saboda ban fada a gida ba ne, kuma ba a son ina dadewa a waje. Amma tunda ai ba dadewa zamu yi ba, muje kawai Jamil."
Larai ta ce a cikin murmushi, domin a zatonta ko dan dum din data yi ya ɓata masa rai.
"Ba dadewa zamu yi ba, nan da awa daya zamu dawo."
Sa'ar da suka isa gidan Larai tayi matuqar kaduwa, domin duk da yake dai Larai ta san Jamil dan masu akwai ne, don kuwa babu abin da zata kalla bai saya mata ba. To amma sa'ar da suka iso gidan sai da numfashinta ya dauke, ga shuke-shuke a ko'ina, fitilun alfarma birjik suna ci kamar rana, dakin shaqatawa kamar ba a Najeriya ba. Larai ta gama tsinkewa da al'amarin Jamilu.
Bayan da suka gama ciye-ciye da shaye-shaye ne to, Jamilu ya nemi da ta rakashi ya nuna mata bangarorin gidan. Ta dakin girke-girke suka fara, sannan suka zazzaga duk dakunan shaqatawar gidan, sa'anan daga qarshe suka isa dakin kwana.
"Anan zaki tare idan Allah Yayi aurenmu."
Jamil ya ce da ita cikin murmushi sa'ar da ya lura da cewa, duk hankalin Larai ya tafi ga kallon fankadeden gadon dake a katafaren dakin.
"Dan zauna mana ki ji."
Larai ta fashe da dariya tana cewa.
"kai fa Jamil wallahi abinka kenan, mutum da wayewarsa sai kana nema ka mai da shi dan ƙauye."
Jamil yayi dariya,
"ba haka bane wallahi, nima wannan gadon da kika ganshi ban taɓa kwana akai ba. Domin ko sati bai yi ba da kawowa, dakin kwanana yana baya, dazu ai na nuna maki shi, wannan kuwa sai na aureki."
Suka fashe da dariya. Ba zato ba tsammani sai Larai ta ji hannun Jamil a bayanta, abin ya bata mamaki, to amma kawai sai ta dauka ko tsantsar nishadi ne ya daukeshi, domin ai da bai taba yi mata haka ba.
"zauna mana, kin tsaya sai kallona kike yi."
Jamil ya ce a cikin murmushi. Larai ta zauna tana dan murmushi, amma yanayin fuskarta ya sauya, domin har yanzu hannayensa na rataye a kafadarta. Haka nan tsigar jikinta sai yar-yar take.
"Idan na aureki Larai."
Jamil ya ci gaba da cewa.
"ban san irin farin cikin da zan yi ba."
Larai ta dubeshi gami da lumshe idanu cikin farin ciki, hakan da ya ce shi ne..Larai ta dubeshi gami da lumshe idanu cikin farin ciki. Hakan da ya ce shi ne fatanta a kullum duniya.
"na auri Jamil....na kyautata masa...nayi masa abin da yake so...na haifa masa 'ya'ya...mata biyu maza biyu...a'a mata biyu dai namiji daya...wadannan sune abubuwan dake a cikin zuciyar Larai DARE DA RANA.
.
Larai bata yi aune ba sai ta ji hannun Jamil ya janyota ƙirjinsa, nan da nan ta ji jikinta ya dauki rawa, tunda take bata taba kwanciya a jikin namiji ba.
"Oh! Jamil don Allah bari."
Larai ta ce dashi muryarta na rawa. Duk da haka dai akwai murmushin yaƙe a fuskarta, domin tana gudun kada ta sosa masa rai. Jamil ya dada kwantar da ita gaba daya akan kujerar, bayanta akan cinyarsa, shi kuma yana kallonta ta sama, hannayensa akan kirjinta. Jikinta ya fara ɓari.
"me Jamil yake nufi?"
Larai ta tambayi kanta. Can sai ta ji hannunsa akan cinyoyinta. Nan da nan tayi caraf ta rike hannunsa muryarta na rawa.
Ta ce.
"Rufa min asiri...dan Allah Jamil...haba Jamil, kada kayi min haka mana."
Jamil bai kula ba sai ya fara qoqarin ɓalle maɓallan rigarta dake daf da ƙirjinta yana cewa
"Larai ai fuk son ne ya kawo haka, kin san..."
Bai karasa ba Larai ta buge hannunsa a fusace, ta mike a fusace.
"Jamil menene haka? Haba Jamil kai da zaka aureni mene haka kuma? Maganarta ta makale sa'ar da ta ga Jamil ya mike a fusace.
"To ya isa, tashi in mai da ke gida."
Larai ta dubeshi cikin ƙunan rai.
"kayi haquri don Allah Jamil...wallahi ban taɓa yi ba...kuma kaga babu kyau...amma in ba haka ba ai ka san kafi ƙarfin komai a wurina, tunda..."
Tashi dai nace mu tafi, ni ba wa'azi na nema ba."
Larai ta ji ƙirjinta kamar zai fashe, babu abin da take masifar so a duniya kamar Jamil. Tana tsammanin idan ta rasa shi me yiwuwa mutuwa zata yi.
"Jamil."
Larai ta kira sunansa tana duban murtukakkiyar fuskarshi.
"Jamil. Ka gafarceni, kada ka yi fushi da ni....jamil duk duniya bani da abin da ya fika. Ɓacin ranka nawa ne...da ace na rasaka gwamma in rasa komai... Jamil in dai ni ce kake so, ni mai baka abin da kake so ce. Ina so ka sani, ni a zuciyata wallahi bana so....amma idan har hakan shi ne zai faranta ma, to kazo ka yi, ka daina kallona kamar wacce tayi ma kisan kai..."
Jamil yayi sororo kamar ruwa ya cinyeshi, da farko har Larai ta fara tunanin kamar ko ta karya zuciyarsa, to amma ga mamakinta sai ta ga babu kunya babu tsoro ya nufota, ya janyota jikinsa. Larai ta rufe idanunta ta fara kukan zuciya, kuka marar amfani, domin ta manta da fushin Ubangiji saboda tana tsoron fushin masoyi. Har sa'ar da ya kwantar da ita akan gadon Larai bata san inda kanta yake ba.
.
Kwanakin da suka biyo bayan haka sun fi komai baki a wurin Larai, domin tun daga ranar da Jamil ya santa 'ya mace bai sake zuwa wurinta ba, sannu-sannu har wata guda ya shude...wata biyu..babu Jamil babu labarinsa. Abin da ya fi tayar mata da hankali fiye da komai shi ne rashin al'adarta. Ba sai ta tambaya ba ita kanta ta san abin da hakan ke nufi, don haka wata safiya da sassafe ta shirya sai gidan Jamil.
Jamil ya dubeta sheƙeƙe sa'ar da ta bude masa dakin shaƙatawar ta shiga.
"mene ne kuma?"
Larai ta dube shi cikin bakin ciki, saboda na farko dai da ganin fuskarsa ta san bai yi na'am da zuwanta ba, haka nan kuma ko neman afuwar rashin zuwansa ma bai kula ba. Larai ta fashe da kuka.
"ka..cuce...ni Jamil, ka cuce ni....wato ka gama cin moriyar ganga kenan ka jefar da ƙwaure...to sai ka farka domin ban ga AL'ADATA ba."
Jamil ya ji gabansa ya fadi ras! Kamar an doka guduma. Ya sha harka da mata a baya babu adadi, to amma bai taɓa yiwa wata ciki ba.
"ban gane abin da kike nufi ba Larai."
Larai ta ji kamar zata fadi a gurin sumammiya, saboda bakin ciki. Larai ta sake dubanshi ido da ido, ta ji ta tsaneshi, bata ƙaunar ganin wani abu mai kama dashi a wannan lokacin.. Zuciyarta tayi bakikirin.
"Abin da nake nufi shi ne, KAYI MIN CIKI....sai ka san yadda zaka yi da ni, in kuma ba haka ba Wallahi in tafi gidan iyayenka in haife musu shi a can."
Cikin Jamil ya duri ruwa, wannan ita ce kalma mafi tayar da hankali da ya ji a shekarar, domin da ta je gidan iyayensa da sunan yayi mata ciki, gara ko nawa zai kashe ya kashr a Zubar da cikin. Tab! Ciki a gidansu. Tunani da fargabar mahaifinsa suka mamaye zuciyarsa, nan da nan gumi ya fara sartu akan goshinsa. Ya san mahaifinsa da zuciya kamar kuturu. Tsohon Janar din soja ne. Idan ya samu labarin wannan aika-aikar babu makawa harbeshi zai yi. Domin akan dan ƙankanin abu ma bara, in banda kakarsa tana gidan da tuni mahaifin nasa ya aika dashi barzahu, to amma da taimakon Allah da taimakon kakarsa, sai ta sha gabansa ta ce sai dai in ita zai harba. Hakan ne ya taƙaita abin.
"Larai, wannan ba wani abin tashin hankali ba ne, bari a samo Likita ya tabbatar..."
Jamil ya ce bakinsa na rawa. Ran Larai ya ƙara baci, domin ta san ba kaunar da yake mata ce ta sa shi wannan rawar bakin ba, sai barazanar da tayi masa.
Bai taba yiwa mace ciki ba tunda yake, to amma ya san ƙwararren Likitan dake zubar da cikin 'yan matan abokansa 'yan bariki, Jamil ya nufi kan talfo ya danna wasu lambobi.
Mintuna goma sha biyar kacal likita yayi yana 'yan aune-aunensa ya gama.
.
"Sai ki tafi gida, zan aiko maki da sakon duk yadda za'ayi. Kada ki damu don Allah Larai, komai zai wuce.
Jamil ya ce da ita cikin kalaman munafurci. Larai ta fice daga gidan tana kuka.
Washe garin ranar shi yayi daidai da sha biyar ga wata Junairu 1990. Da safe misalin qarfe takwas da rabi, wani kaninta Abubakar ya shigo dakinta rike da wasika ya mika mata.
Larai ta dube shi.
"wa ya baka wannan?"
Abubakar ya ce.
"wannan Jamil din ne mai zuwa gurinki a mota, ya bani ya ce na kawo maki, naje sayen sabulun wanka muka hadu dashi yazo kofar gida."
Larai ta ji gaban ta ya fadi ras!
"yana nan bai tafi ba?"
Abubakar ya girgiza kai.
"Yana bani ya tafi."
Larai ta lumshe idanu cikin takaici.
Ganin haka sai Abubakar ya fice yana mai mamakin abin da yasa yayarsa kuka, domin kuwa yaga idanunta sun kukkumbura sun yi ja.
A daidai lokacin da Larai ta bude wasikar ne zata fara karantawa, sai ta ji ana sanarwa a 'yar karamar rediyon dake kan teburinta mai magana yana cewa.
.
"A madadin Sani Aliyu (Rubzan & sons company) suna farin cikin taya Jamil Ishak murnar baikon aurensa da Rukayya."
Larai ta jeho rediyon daga kan teburin cikin kaduwa...Jamil....Sani Aliyu abokinsa...Jamil zai yi aure....Na shiga uku. Ta lumshe idanunta, domin ji take kamar zata sume.
Tsawon mintuna biyar tana nan zaune kamar gunki, sannan sai tayi ta 'yan maza ta bude wasikar ta fara kallon rubutun tafiyar tsutsa wanda duka-duka bai wuce layi hudu ba kamar haka:
.
15-1-1990
Larai.
Likita ya tabbatar min da cewa ciki ne dake dan wata daya da 'yan kwanaki, amma ya ce zai iya cire maki shi. Don haka duk lokacin da kika shirya, sai kizo mu tafi gidansa a cire cikin.
JAMILU
.
Tana gama karantawa sai ta mike a fusace cikin fushi wasikar na hannunta, har zata fice da wasikar sai wata zuciyar ta ce da ita.
"kuma idan wani ya ganta a hannunki ya karanta fa?"
Ta fara dube-duben inda zata ajje wasikar, sai ta hangi katon littafin janinta Abubakar a jikinsa an rubuta (MODERN BIOLOGY), cikin sauri ta bude littafin ta ajiye wasikar a ciki, sannan ta nufi tsakar gida tana mai addu'ar Allah sa mahaifinta ya fita wajen aiki.
"ina zaki naga kina sauri Larai?"
Mahaifiyarta ta tambayeta.
"Dakin Baba zan share."
Ta wuce kai tsaye. Tana shiga sai ta jawo kofar ta kulle, sannan ta janyo kan talfon din mahaifinta ta fara dannan lambobin wayar Jamilu.
.
Har zuwa yanzu nan da Jamil ke tuƙa motar Larai na zaune a kusa dashi, yana iya tuna kalaman Larai sa'ar da ya dauki wayar
"Na gode da abin da ka yi min Jamil, ina son kuma ka sani cewar...zubar da cikin ba yanzu ba, sai nayi niyya na bugo maka waya na sanar da kai."
"kada ki yi min haka Larai....ki fito kawai in anjima da dad..."
Larai ta katse shi.
"ban yi niyya ba Jamilu...idan kuma ka takura min wallahi sai in tafi gidanku da cikin...kada ka manta kuma idan an zubar da cikin sai ayi mana baiko...ina tsammanin dai yanzu kayi girman da zaka iya rike mata biyu?"
.
Jamil yayi ajiyar zuciya sa'ar da ya rage gudu, sa'annan ya lanqwasa kan motar suka nufi dan karamin gidan dake boye a bayan 'yan shuke-shuken kayan marmari. Gidan a cikin duhu yake dundum alamu ba wuta. Jamil ya raba a hankali ta jikin wata tsohuwar mota wacce ke zaune abinta akan duwatsu hudu babu tayoyi, ya cusa hancin motarsa cikin farfajiyar gidan mai kamar makabarta saboda duhu ga kuma shuke-shuke da suka qarawa gidan duhu.
Jamil ya juyo a hankali ya dubi Larai sa'ar da ya kashe motar, sa'anan ya ce.
"jira ni anan in je in same shi, kin san bai san da zuwanmu ba."
Larai ta share hawaye ilahirin jikinta ya dau rawa
Ganin haka sai Jamil ya bude kofar motar zai fita. Ga mamakinsa sai ya ji Larai tayi caraf ta riƙe hannunsa sannan ta ce a sanyaye.
"jamil don Allah kada ka barni, wallahi tsoro nake ji."
Jamil ya ce cikin mamaki.
"tsoron me, duhu ko me?"
Larai ta girgiza kai sannan ta ce.
"ka gafarceni Jamil, wallahi ji nake kamar idan na shiga gidan nan ba zan fito ba."
**** ***** ****
KASHI NA UKU 3
.
Idanun LIKITA SURAJO suka zazzaro waje kamar zasu fado sa'ar da ya.Idanun Likita Surajo suka zazzaro waje kamar zasu fado kasa sa'ar da yaga Jamil tsaye a kofar dakinsa hannunsa kan kararrawa.
"Dan Amina Muhammadu! Jamil lafiya na ganka haka a cikin wannan daren...na dauka yau ne amaryarka take tarewa?"
Jamil ya dubi dan siririn Likitan mai dogon wuya kamar an sheka ruwan shayi, ya ce muryarsa na rawa.
"Amarya kam ta riga ta tare, yanzu ma da amarya ta biyu muke tare zata tare a nan."
Likita Surajo ya shafi 'yar karamar fuskarsa mai kamar kashin zogale ya yi murmushin yaƙe.
"Yarinyar nan da aka auna kwanakin baya mai ciki wata daya, ita ce yanzu ta taso ni daga dakin amaryata da wannan dare...wai sai yanzu take son a cire cikin...."
Likita Surajo ya girgiza kai, akwai alamar takaici a fuskarsa.
"A'a ha, haba Jamil sai ka ce ba dan birni ba, yanzu don wannan ne ma har ka bari wata 'yar iska ta fito da kai daga dakin amaryarka ran darenka na farko....kai kuma don me zaka biye mata?"
Jamil ya hadiyi yawu.
"saboda idan naƙi amincewa da tayinta gidanmu zata je da cikin, ina fatan kuwa ka san abin da hakan ke nufi, ko da yake wani abu makamancin haka bai taba shiga tsakaninmu da kai ba, na san abokaina kwastomominka ba za su gaza baka labarin mahaifina ba.".
Likita Surajo ya gyada kai ya ce.
"ƙwarai kuwa."
"to tunda ka fahimci yanayin bari in koma mu taho tare da ita, tare muke, cewa nayi bari in leko in gani ko kana nan."
"to amma fa ka san aikin..."
Jamil ya katse shi.
"kada ka ji komai, indai maganar kudi ce, ka cire mata cikin nan kawai mu rabu lafiya....wallahi Likita akan maganar cikin babyn nan ko barci bana iya yi, domin na san tana zuwa gurin Dad dina to ni na san tawa ta baje min kenan."
"je to ka taho da ita, bari ni in shiga in fara shirya kayan aikin...idan kun zo sai ku jira ni a falo."
Larai ta dago kai ta dubi Jamil a tsorace sa'ar da ya leƙo ta tagar motar ya ce da ita a sanyaye.
"fito mu shiga yana ciki, ke yake jira."
Larai ta zura kafafunta waje, jikinta a sanyaye kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.
A karo na biyu tausayinta ya sake mamayar zuciyarsa.
"Ki...yi hakuri Larai...in Allah Ya so komai zai zama Ok."
Har zuciyarsa a lokacin abin da yake nufi kenan. Yana gaba tana bin sa a baya har suka isa dan madaidaicin dakin shaƙatawar. Matasan biyu mace da namiji suka dubi juna cikin nadamar abin da suka aikata, daya a tsorace iya tsoro, yayin da daya ke cikin damuwa iya damuwa.
Larai ta ji wani wari-wari yana bugun hancinta, ita kanta bata san ko warin mene ne ba, to amma kuma wata zuciyar ta ce da ita warin magunguna take ji. Idanun Larai suka fara nazarin falon a tsorace, babu wani abin kuzo ku gani a ciki, daga kujeru hudu masu kama da na motar yaki, sai wata tsohuwar kanta irin ta turawan mulkin mallaka daga can ƙuryar falon dauke da kwalaben magunguna...haka nan a maƙale a jikin kowanne bango na dakin, hotuna ne na ɓangarorin jikin mutane abin babu kyawun gani.....larai ta ji zuciyarta na tashi kamar zata yi amai.
"Zauna mana."
Jamil ya ce da ita, sa'ar da ya lura da sauyin yanayin dake fuskarta. A dai dai lokacin ne to likitan ya fito sanye da doguwar riga fara irin ta likitoci, hannayensa sanye cikin safar roba.
.
"Sannunki Madam."
Likita Suraj ya ce da Larai yana murmushi.
San..nunka dai."
Larai ta ce dashi numfashinta sama-sama. Shiru na dan lokaci sa'anan Likitan ya ce.
"idan kin shirya sai ki shigo daga ciki, yanzun nan zamu gama."
Ganin gumin fargabar dake tsattsafowa daga goshinta shi yasa likitan ya kara jifanta da murmushin ƙarfafa gwiwa.
"kada ki ji fargabar komai 'yanmata, ba wani zafi za ki ji ba. Allura za a yi maki, da zarar an yi za ki yi barci, baki ma san lokacin da za a gama ba."
Hakan da ya fada maimakon ya kwantar da hankalinta, sai ma ya dada ruɗata. Larai ta juyo a hankali ta dubi Jamil, ganin hakan sai Likitan ya juya yana cewa.
"idan kun gama, ki same ni cikin wancan dakin mai farar kofa."
Sa'anan ya dubi Jamilu ya ce.
"Ina jin fa sai kayi jiran kusan awa uku kafin mu gama, domin fitar da cikin zai daukemu kusan awa biyu, za kuma ta huta na awa daya kafin ku tafi."
Jamil ya ji gabansa ya fadi, amaryarsa Ruqayya da babbar ƙawarta Badura na can suna jiransa.
"Babu yadda za'ayi da gaggaw..."
"Ba zai yiwu ba."
Likitan ya katse shi yana ɗaɗɗaga girar idanu kamar biri.
"Domin ba aikin gaggawa ba ne."
Jamil yayi sauri ya gyada kai, saboda kallon da yaga Larai ta fara yi masa. Likitan ya sake duban Larai gami da sake yi mata murmushin tabbacin nasara a aikinsa, sannan ya juya ya shige cikin daki mai farar kofa.
.
Hannayenta a harde akan ƙirjinta gumi na kwaranya akan kyakkyawar fuskarta, Larai ta zubawa Jamil idanu na tsawon lokaci kamar zata hadiye shi. Ga mamakinsa sai Larai ta matsa daf da shi, sannan ta dora hannayenta akan kafadarsa, ta ce cikin muryar da har abada Jamil ba zai taba mantawa da ita ba.
"Abin da ya faru, ya riga ya faru Jamilu...ka gafarce ni Jamil, ƙauna dai ba zan daina ƙaunarka ba...domin Allah ya gama halittar soyayyarka a cikin zuciyata ka ga..."
Shassheqar kuka ta katse kalamanta.
Jamil ya rasa abin da yake yi masa dadi a zuciyarsa....a cikin dan takin lokaci sai ya ji wani dan ɓurɓushi na kaunarta ya darsu a zuciyarsa, nan da nan tausayinta ya lullubeshi. Hakika ba laifinta bane....duk abin da ya faru shi ne ya haddasa....kaunar da take yi masa ce ta sa yayi tasiri akanta har ta yarda suka aikata wannan masha'a.
"kada ki yi kuka Larai....ki yi hakuri don Allah...wallahi Larai a yau na tsani kaina, ina ƙyama da kunyar kaina da kaina akan abin da nayi maki...."
Jamil yayi shiru. Can kuma a zuciyarshi abin na bashi mamaki, saboda yadda yaji gwuwoyinsa sun yi sanyi ga kuma hawaye da suka fara sartu kan kumatunshi.
Larai ta dubeshi taga yadda kwalla ke kwaranya akan kumatunsa...rabonta da farin ciki tun ranar da abin ya faru, sai gashi a daidai lokacin da take cikin tsakiyar bakin cikin rayuwa ganin kwallarsa a dalilinta ya sake faranta mata rai.
A daidai lokacin ne suka jiyo Likita Surajo yana kwankwasa kofar dakin, alama ce dake nuni da cewa ita fa yake jira.
.
Larai ta yiwa Jamilu dogon kallo, ga mamakinsa kuma sai ta saki murmushi, kana ta mika hannunta ta kamo tafin hannunsa ta ce.
"Jamil idan ka je gida, ka gayar min da ƙawata MATAR KA RUKAYYA."
Da haka ta juya da sauri ta nufi daki mai farar kofa. Tana zuwa bakin kofar sai ta sake juyowa tayi masa murmushi, sannan fatar bakinta ta motsa a hankali....
.
Da wannan ta bude dakin ta turo kofar a bayanta bayan ta shige ciki.
Jamil ya yi tsaye sororo idanunsa cike taf da ƙwalla, bai ji abin da ta ce ba sa'ar da ta motsa leɓen bakin nata, to amma zuciyarsa."KA GAFARCE NI JAMIL...
YAU ANYI ƁATACCIYA...
Tunda nake haka bata taba faruwa ba akaina...." yadan yi shiru yana maida numfashi. "Jamil....yarin
yar nan ta zubar da jini dayawa.." jamil ya katse shi ta hanyar daga hannayensa a fusace. "Ka ga malam fadamin abinda yafaru kai tsaye mana...idan ta zubar da jini dayawa ba sai mutafi asibiti ba" Likitan yayi kamar ya fashe da kuka sa'ar da yaji abin da jamil yace . "Abin ya wuce da haka jamil...
Yau Kam nashiga uku... 'yaya biyu yan tagwaye ne acikin duk kuma na ciresu...amma ina mai fargabar sanar dakai cewa itama ta RIGA MU GIDAN GASKIYA"
"LARAI ta mutu!! " jamil ya maimaita cikin kaɗuwa, ya dafe kirji domin ji yake kamar hanjin cikin sa zasu fito waje ta baki.
.
Arude jamil ya banke dan siririn likitan gefe guda ya wuce cikin dakin mai farar kofa...tun kafin ya hange ta yafashe da kuka.
Larai nakwance akan wani dan karamin gado mai tayoyi, jikinta lullube da wani shudin yadi. Jamil ya rankwafa hannayensa dafe da bakin gadon ya kura mata idanu yana cewa cikin kuka arude. "Haba....larai....yanzu daman kinsan mutuwa zakiyi ....kika barni kikasa muka zo....larai na shiga uku duk ni na janyo miki larai...dan Allah ki gafarceni..." jamil ya yishiru lokaci guda yana sheshekar kuka domin sai yanzu ya ankara cewa ashe fa da gawa yake magana. A haka idan kadubeta saika rantse da Allah bacci takeyi. Ko da Jamil ya sake duban fuskar Larai sai ya ga kamar ta ɗaɗa kyau nan da nan ya sake fashewa da kuka a rude sannan ya shafi fuskar ta yanacewa. "Larai... Larai.... Kiyi hakuri....duk dan iskan da ya kasheki saina rama miki..."
.
Yana fadin haka sai yayi wajeda gudu a rude. Likitan mai suna sirajo ya dube shi a tsorace sa'ar da ya ga jamilu ya fito da gudu ya nufo kansa, kafin ya farga sai jinsa ya yi a sama yana reto... Jamil ya bugashi da

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment