Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Jamilun kullum daga mota sai mota bai son fitowa daga ciki kamar mujiya.
"sannu da zuwa Abashe,"
Abubakar ya tarbeshi cikin fara'a da gaisuwa ta girmamawa."
"Yauwa Abubakar....baba tana ciki ne?"
Abashe ya ce muryarsa a sanyaye. Abubakar ya dube shi cikin damuwa, 'yan kwanakin nan duk Abashe ya canza, baya walwala da fara'a kamar da, tun daga ranar da Larai ta bace bai ƙara ganin hakoran Abashe da sunan dariya ba.
"Ta tafi unguwa dazu, amma ba ta dade sosai ba."
Abashe ya duba agogo sha biyu da kusan mintuna talatin da uku.
"mu shiga daga ciki ka dan jira ta, me yiyuwa ba dadewa zata yi ba, ina jin makwabta ta shiga."
Abubakar ya ce da Abashe yana dubansa, lokaci guda kuma yana dan bubbuga kofar gidan da hannunsa.
"bari to mu shiga na jirata koda minti goma ne, domin aiki ne damu a wani gida....."
Maganar dake bakinsa ta katse sa'ar da ya hangi wata budurwa sanye da farar riga doguwa lullibe da farin mayafi za ta shiga wani gida, nan da nan ya ji zuciyarsa ta fara harbawa, wani zazzafan gumi ya fara sartu a kan fuskarsa kamar ruwa.
Abashe ya dade yana kaunar Larai tun tana karama, sai dai kuma yayi rashin sa'a babba, don kuwa Larai bata damu da shi ba ko kadan. Mafi yawan lokuta idan yazo hira shi kadai zai yi ta kidansa yana rawarsa ba tare da kulawarta ba.
.
"Ka yi hakuri Abashe, yarinya ce karama idan ta girma tayi hankali zata daina ne."
Amina mahaifiyar Larai ce ke cewa dashi haka a wata rana da yazo hira Larai bata kula shi ba.
'Yan shekarun da suka biyo baya sun zo da sabon canji, amma kadan ne ba mai yawa ba, domin lokacin da Larai ta fara isa munzalin mace, sai ta daina yawan muzanta shi, musamman ma abin da ya shafi bakaken maganganu da sauransu. To amma duk da haka in ma ta fito sai dai ta tsaya nesa dashi, ta harde hannayenta a kirjinta ta sunkuyar da kai, bata kara cewa dashi uffan, sai dai idan ya takura mata da yawan tambaya ta gyada kai ko ta girgiza kai, kamar kadangaruwa.
Wannan al'amarin na halin ko in kula da Larai ke yiwa Abashe, duk bai shalle shi ba. Gashi dai karamin ma'aikaci ne a gidan ruwa REKA, ba wani albashin kirki ne dashi ba, domin su ke yin ayyukan wahalar kamar hake-haken kasa da kuma daddaura fayif din ruwa da binnewa, amma duk wannan bata hana Abashe ya kashewa Larai sama da albashinsa ba.
Wani lokacin idan ya kawo mata abin alkairi ko godiya bata yi sai da kyar da jibin goshi mahaifiyarta Amina ke sa Larai ta gode masa.
Ana cikin wannan badakala kuma katsam sai Jamilu ya sawo kai, wannan ba karamin tayarwa da Abashe hankali ya yi ba, domin lokacin guda ya lura da cewa, Jamilu ya saye imanin Larai da abin duniya.
Abashe ya hada kansa da matsayinsa a zuciya tsakaninsa da Jamil, sai ya ga tamkar banbancin ruwa ne da kalanzir, Jamilu ya fi shi arziki, ya fi shi ilimi, ya fi shi wayewa. Duk da haka sai Abashe ya ci gaba da jajircewa, domin a cewarsa wai mari bashi sa gaban jaki ya fadi.
Duk sa'ar da Abashe ya so hira, sai ya koma gefe ya takure yana hangen Larai ita da Jamilu a cikin mota suna ta hira. Haka zai yi ta zama a cikin bakin ciki da kunan zuciya, har iya tsawon lokacin da hirar zata zo karshe, sai idan Larai ta zo wucewa zata shiga gida ne sannan Jamil zai mike tsaye a gajiye ya tari gabanta.
Ya ce.
"Tun dazu nake nan ina jiranki Larai."
Ita kuwa sai dai ta tabe baki ta dube shi a yatsine ta ce.
"Ba ka gaji da wahala ba ne, kaga Abashe gara fa tun wuri ka nemi wurin fakewa, domin wannan inuwar tafi karfinka. GA MIJINA CAN."
Sai ta nuna masa Jamilu da hannunta, sannan ta shige gida tana rangwada.
.
A washe garin wata rana, bayan Larai ta sake yiwa Abashe irin wannan wulakancin , sai ya fara tunanin me yiwuwa fa hidimar da yake yi mata ne ta fara yi mata kadan. Don haka a ranar bayan ya dauki albashinsa naira dubu biyar ne cif! sai ya wuce kasuwa ya yi cinikin wani leshi dan ubansu da mata ke yayi, akan kudi naira dubu hudu da dari takwas, Abashe ya cake kudi ya biya, sannan ya dawo gida ya kwanta yana jiran magriba tayi ya tafi gidan su Larai ya kai mata.
Kafin lokacin ya yi sai da Abashe ya bude farin leshin nan sau kusan talatin yana kallonsa, yana fasalta yadda zai dace da abar kaunarsa Larai.
Lokacin da Larai ta gama hira da Jamilu, sai Abashe ya tare ta tana qoqarin shiga gidaLokacin da Larai ta gama hira da Jamilu sai Abashe ya tare ta tana kokarin shiga gida.
"Ba ka ji abin da na fada maka ba kenan ko Abashe?"
Larai ta tambaye shi cikin tsiwa.
"ki yi min afuwa Larai, don Ubangijin da ya halicceki, wallahi ba zan daina iya sonki ba ne, da zan iya da tuntuni na daina."
Ya dan yi shiru yana jujjuya bakar ledar dake a hannunsa jikinsa na rawa, idanunsa akan fuskar Larai, kullum gani yake kamar tana kara kyau.
"wata alfarma nake roko a gare ki Larai, ina fatan za ki yi min don Annabin talikai ba dan ni ba."
Larai ta yi kamar ta shige gida kawai abinta ta bar tsohon maye a gurin, to amma magiyar da ya yi ita ta karya mata gwiwa, haka nan akwai wani yanayi akan fuskarsa da ke nuni da cewa in har bata saurare shi ba, to fashewa zai yi da kuka. Hakan shi ya sa Larai ta tsaya, rabi tana fuskantarsa, rabi kuma tana duban kofar gida.
"mene ne?"
Ta tambaye shi cikin kaguwa.
"Larai wata kyauta nake so in in yi maki, na san me yiyuwa ki ce ba za ki karba ba, shine to nake rokon alfarma. So dai na san ba dole ba ne ki so ni, to amma ni kaunarki ban iya barin ta, shi ya sa nake rokon alfarma da ki karbi wannan kyauta da zan yi maki, ina fatan kuma za ki ɗinka ki sata a jikinki ko da sau daya ne."
Yana gama fadin haka sai ya mika mata leshin dake a cikin jakar da take hannunshi. Larai ta dubi jakar na dan lokaci , kana ta dubi Abashe, sai tausayinsa ya kamata. A hankali ta mika hannu ta karba, sa'anan ta ce.
"Na gode, sai da safe."
Da haka ta shige gida. Tunda Abashe yake bai taba jin kalma mai dadi irin wannan ba. A ranar bai yi barci ba saboda farin ciki.
Tun daga ranar kullum sai Abashe ya yiwo zagaye, ko zai ga Larai sanye da leshin, amma a banza. katsam ranar uku ga watan maris, Abashe ya shigo layin bayan magriba, yana shigowa sai ya hangi Larai sanye da kayan da ya saya mata, amma sauri take yi ta nufi bakin titi. Farin ciki ya lulliɓeshi, nan da nan ya nemi guri ya zauna, ya jingina bayansa da bango, me yiyuwa aikenta aka yi. Ya ce a cikin zuciyarsa. Babu mamaki kuma unguwa zata je, kuma ya riga ya san ko ya tare ta ba tsayawa zata yi ba, don haka sai ya zabi ya nemi wuri ya jirata, koda kuwa zuwa tsakiyar dare ne.
Yana nan zaune sama da awa uku har barci ya fara mamayarsa, ya fara gyangyadi, nan da nan ya mike tsaye a rude, ya dubi agogo ya ga ashe ya shafe sama da awa uku a kofar gidan. Ya fara waige-waige bai ga kowa ba, domin jama'a tuni sun kauracewa layin, sun shiga makwancinsu, wannan shi ya sa ya gamsu cewar tabbas yana barci Larai tazo ta shige cikin gidan ba tare da ta tashe shi ba.
A washe garin ranar ne kuma aka tashi da mummunan labarin bacewar Larai. Wasa-wasa ana ta cigiya kamar zata dawo, gashi yau har shekara guda ba labarinta
wannan al'amarin kullum Abashe ya tuna dashi sai ya zubar da hawaye, domin ko shakka baya yi wannan ganin da ya yiwa Larai ta nufi bakin titi daga shi ne bata dawo ba, ya san shi ne ganin karshe da ya yi mata, kuma ganin bakin ciki, domin daga nan ne abar kaunarsa Larai ta bace sanye da fararen kaya sababbi da ya saya mata da dan guntun albashinsa na karamin ma'aikaci a gidan ruwa.
Wannan ita ta sa yanzu da ya hangi budurwar sanye da fararen kaya zata shiga wani gida sai ya ji zuciyarsa kamar zata rabe biyu. Domin ganin karshe da ya yiwa Larai sanye take da fararen kaya.
"Shi kenan ma ga Baba nan ya dawo!"
Abubakar ya ce cikin doki a dai-dai lokacin da suke daf da shiga gidan.
Abashe ya juyo a kunyace, domin shi a kullum cikin jin kunyar mahaifin Larai yake.
Motar ta ja ta tsaya a kofar gidan, lokaci guda kofofin baya suka bude, wasu mutane masu busassun fuskoki suka fito su biyu. Daya a cikinsu ya yi sauri ya bude gidan gaba. Malam Audu ya bude ya fito su ka bar direban a ciki.
.
"Barka da zuwa Ba..ba...."
Abashe ya durkusa a kunyace bakinsa na rawa ya gaida mahaifin Larai.
"Lafiya lau Abashe."
Malam Audu ya ce, gami da yin shiru na wasu 'yan sakanni, sannan sai ya dubi Abashe.
"Na ji dadin ganinka Abashe, dama yanzun nan nake son in tura a nemo min kai."
Ya dubi jami'an tsaron biyu dake a kusa dashi cikin fararen kaya ya ce.
"SHI NE WANNAN."
Sannan sai ya dubi Abashe.
"wadannan sune mutanen suna son magana da kai."
Yana gama fadin haka sai ya tura Ƙyeyar dansa Abubakar suka shige gida.
Koda Abashe ya dubi fuskar mutanen biyu, sai ya ga kamar an aiko musu da mala'ikan mutuwa, ko tantama baya yi ya san ko su wane ne.
.
***** ***** *****
.
Abashe ya yi wuri-wuri cikin firgici a bayan motar jami'an tsaron biyu wadanda suka sa shi a tsakiya.
"wasu tambayoyi muke so ka amsa mana, da fatan zaka saki ranka ka daina rawar jiki, domin ba karshen duniya bane yazo. Wadannan amsoshin da zaka bamu suna da muhimmancin gaske, domin yau kusan shekara guda kenan da bacewar masoyiyarka Larai."
Jami'in tsaron ya dan yi shiru, sannan sai ya dubi dan'uwansa dake zaune a can barin hannunsa na hagu. Nan da nan jami'in tsaron ya zaro wani dan karamin littafi daga aljihunsa gami da alkalami.
"Yaya sunan ka?"
"Suna na Abashe."
"Mene ne alakarka da Larai?"
Abashe ya ji fatar bakinsa ta bushe, don haka sai ya turo harshensa ya jika fatar bakin sa. Sannan ya ce muryarsa na rawa.
"tsaka....ni na da Larai babu wata alaka da ta wuce soyayya, tun tana karama nake son ta...."
"kun taba fita da ita wani wuri, ma'ana kamar unguwa ko wani guri daban?"
Abashe ya girgiza kai.
"bamu taba ba, in har ma nayi sa'a ta saurareni to iyakarmu kenan, kuma ni kadai nake hirata bata amsa min."
Jami'in tsaron ya dubi Abashe cikin mamaki.
"me ka ke nufi da cewa kai kadai ka ke hirarka?"
Abashe ya hadiyi yawu.
"Domin ba wani sona take yi ba sosai."
"me yiyuwa kun taba fada kenan, tunda bata sonka sosai".
"bana fatan Allah Ya nuna min ranar da zan yi fada da Larai, ai Larai abar kaunata ce, ba abokiyar fada ba, duk abin da tayi min ina sonta."
Jami'an tsaron biyu suka dubi juna, domin sun fahimci cewar har yanzu tambayoyinsu basu samu bullewa ba. Suka kurawa Abashe ido na dan lokaci , to amma basu ga wata alamar rashin gaskiya a fuskarshi ba.
"kana sane da ranar da Larai ta bata?"
Abashe ya gyada kai.
"Ƙwarai kuwa, ba zan taba mantawa da wannan ranar ba, uku ne ga watan maris."
Jami'in tsaron ya gyada kai cikin gamsuwa.
"shin to ko zaka fada mana ayyukanka a ranar? ma'ana a inda kake da kuma al'amuran da kayi daga safiya har zuwa daren rana."
Abashe ya gyada kai a lokaci guda kuma gyara zama, domin jami'an tsaron sun yi matukar matse shi a tsakaninsu.
.
"Tun daga karfe takwas na safe har zuwa sha daya ina gida a kwance, domin a ranar na tashi cikina a ruɗe bana jin dadi. Bani na sami fita aiki ba sai kusan sha biyu da rabi, karfe biyar da rabi na dawo, na zauna na ci abinci a gida, na huta a kofar a gida har zuwa magriba. Ina nan ma aka yi sallar Isha'i, daga nan nayi wanka na taho gun LARAI."
Jami'an tsaron suka dubi juna a dokance.
"ka ganta...ma'ana kun zanta da Larai din?"
Akwai alamar dokin jin wannan amsar a muryoyinsu.
"Eh...to zan iya..."
Jami'in tsaron ya katse shi.
"Yi mana bayanin abubuwan da suka wakana tsakaninka da Larai a lokacin da ka shigo layin."
.
"Ina shigowa layin na hangi Larai sanye da fararen laya, tana sauri ta nufi bakin titi."
"Ya aka yi ka gane ita ce?"
Abashe ya ji haushin tambayar, domin ya tabbata yadda yake kaunar Larai ko inuwarta ya gani sai ya gane ta.
"Fararen kayan da ta sanya a ranar ni na saya mata su a matsayin kyauta, kuma ko ba haka ba ina iya gane Larai a duk..Abashe ya girgiza kai.
"Ganina na karshe kenan da Larai, domin ina nan zaune har har na fara gyangyadi bata dawo ba, na tafi gida wajen sha biyu, a tsammani na dai wucewa gida tayi lokacin da nake gyangyadin. Ashe ta....fiyar kenan Larai..."
Ya fara zubar da hawaye.
.
"Bi a hankali Malam, sa'ar da ta nufi bakin titi baka ga alamar kamar wani yana bin ta a baya ba, ko kuma in ce baka ga inda ta nufa ba a bakin titin?"
Abashe ya girgiza kai..
"Guri na share na zauna jiran dawowarta, ni ban bi ta a baya ba."
"kai kadai ne saurayinta ko kuwa ka taba zuwa ka same ta da wani?"
Abashe ya ce.
"Eh to, a gaskiya akwai wani sabon saurayi da ya fara zuwa wurinta sunansa JAMILU, shima a wurin kaninta Abubakar na ji sunanshi, amma in ban da shi ban san wani ba."
"A ina Jamil din yake?"
Abashe ya girgiza kai.
"Nima ban sani ba. Ban san daga inda yake zuwa ba."
"Mene ne sana'arka?"
"Ni ma'aikacin gidan ruwa ne lebura, yanzun nan ma gyaran wani fayif zamu je na ruwa da ya fashe, na san tuni abokan aikina suna can."
"To malam Abashe mun gode, in kuma akwai wani abu zamu sake nemanka.".
Mintuna uku da gama yiwa Abashe tambayoyin, Malam Audu ya dawo wajen jami'an tsaron.
"Ya aka yi?"
Daya daga cikin jami'an tsaron ya ce
"wannan dai kam tsaf yake, amma muna da bukatar haduwa da wancan Jamil din."
Malam Audu ya ce.
"Abin kuwa da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, domin na tambayi Abubakar ya ce ya san shi, amma bai taba sanin daga inda yake ba."
Tsahon lokaci jami'an tsaron suka dauka suna duban tsohon Kwamishinan nasu.
"Yanzu mene ne to abin yi?"
Malam Audu ya tambaya.
"Dole ne mu gano inda Jamilun nan yake."
Malam Audu ya dubi jami'an nan rai a bace ya ce.
"ta yaya zaku gano shi bayan ya bace sama ko kasa ya bace ba a san daga inda yake ba, wa ya sani ma ko shi aljani ne ya dauke ta?"
.
BABI NA TAKWAS.
.
KADAN ya rage dan kabu-kabu ya zarce da Abashe sakamakon wutar da yake ta faman kugawa dashi kamar zai shallake zuwa sararin samaniya.
"Malam anan zan sau...ka kada ka wuce da ni."
Abashe ya ce lokacin da muryarsa ke sassarkewa, saboda hawayen da idanunsa ke tsiyayarwa kamar kuturu sakamakon iskar da tayi ta fesowa zuwa cikin idanunsa.
Dan kabu-kabun ya yi fakin dashi a kofar wani gida, wanda babu kowa a kofar gidan in ka dauke wani motsattsen buzu mai gadi yana zaune shi da wani kare mai yawan gashi da shudayen idanu yana lasar baki.
Koda Abashe yazo sauka daga kan mashin din, sai wani karfe ya cafi rigarsa ta baya. Nan da nan ya ji rigarsa ta fara kuka 'Qyaaa' Abashe ya yi sauri ya fusge rigarsa a fusace, wata asarar ta afku, don kuwa ya baro wani sashi na rigar a jikin mashin din.
Abashe ya dubi rigar cikin kunan rai, sa'anan ya ciro kudi ya biya dan kabu-kabun. Tun kafin su gama shiga hannunsa ya sa giya ya warci mashin din a guje ya bar Abashe nan yana duban asarar da ya tafka a rigarsa.
Tuni dama Abashe ya yi nadamar hawa mashin din, domin babu abin da yake tsoro a rayuwarsa irin hawa acaba, in ban da cewar irin wannan wurin da zasu yi aiki a yau mota bata zuwa, to da babu abin da zai hada shi da mashin. Yaso ya yi sammako yau ya samu riskar ma'aikatansu a wurin aiki, domin da ya same su to da a cikin motar ma'aikata za a kawo su. To amma da yake ya zamar da zuwa gidansu Larai farilla haka nan ya biyo acabar.
Tun kafin ya karasa ya fara jiyo hayaniyar Malam Dogo, domin kullum a cikin musu yake, bai taba iya yin shiru da bakinsa ba.
Inda ma'aikatan gidan ruwan suke aiki bayan wani makadaicin gida ne wanda ke tsakiyar wata farfajiya ma'abociyar lambu mai dauke da shuke-shuken bishiyoyin dabino da na turare. Mafiyawan gidajen dake a wannan yakin duk hakan suke yin gininsu dan tsurut a cikin tafkeken fili, sai ka yi kimanin minti biyar a zaune ba tare da kaga giftawar wani mahaluki ba, in ma zaka gani to sai dai kaga wucewar mota aguje fuu! Babu ruwan kowa da kowa, ba zaman jana'iza bare na daurin aure, idan ka shiga wani lungun sai ayi maka dukan tsiya ba tare da mai ceto yazo ba.
Abashe ya nufi wajen da abokan aikinsa suke wadanda ke tsaye a jikin motar ma'aikatar tasu a bayan gidan, kowanne sanye da shudiyar rigar aiki, sanye da takalma bakake iya kwauri na shiga ruwa.
Abashe ya ji kamar ya bushe da dariya sa'ar da ya hango Malam dogo sanye da hular kwano ga kuma diga ta sarar kasa a hannunsa.
Sunan Malam Dogo na gaskiya Haruna, to amma Malam Dogo duk ta rufe sunan. Dan gajeren wada ne, yana da katon kai kamar masaki, wanda hakan ya sa duk da girman hular kwanon sai ta makale a saman kan tsurut kamar an dora gammo a bayan kwarya. Sai dai kuma duk da wannan gajarta ta Malam Dogo, an yi ittifakin cewar duk cikin leburorin dake aiki a gidan ruwan babu gwanin iya saran kasa da diga kamar sa, ance yana iya yin aikin sa'a biyar ba tare da ya kurbi koda kofin ruwa daya ba ballantana ya huta. To amma fa duk da haka yana aikin ne yana fesa labari, bakinsa baya rufuwa, kamar cakwaikwaiwa.
"Aha!...kun gani ba, ga mutumin nan uban makara, kun ganshi nan sai yanzu."
Malam Dogo ya ce sa'ar da ya hango Abashe cikin sauri ya karaso gurin. Sauran mutane biyar din suka juyo suka dubi Abashe.
"Sannunku da aiki, ku kadai nake yiwa sannu, banda aku kuturu."
Sauran ma'aikatan suka bushe da dariya, domin sun san tsamar dake tsakanin Malam Dogo da Abashe ba tun yau ba.
"Malam kada ka wani wayance, tun dazu muke neman inda matsalar take bamu gano ba har yanzu , amma kai kana can kana shiririta, mu muna nan muna ta faman bincike."
"don Allah malam rufe mana baki mu ci gaba da abin da ya kawo mu."
Wani dan tsololo ne mai kamar lauje ke fadin hakan, shi ne kuma shugaban tawagar aikin, bashi da karfi ko na sisin kwabo don haka duk sa'ar da aka fito bakin aiki bashi da wani aiki da ya wuce ya koma gefe daya ya tsugunna ya yi ta korafi, har sai sun gama haka ramin sannan shi ya shiga ya yi hadin mahadar fayif din ruwa a saukake.
"Ya kamata mu hanzarta muyi abin da ya kawo mu."
Tsololon ya ci gaba da cewa.
"Abashe kai ne kazo a makare, wato abin da yake faruwa shi ne, ruwan gidan ALHAJI SHU'AIBU KWANGILA. ne baya zuwa sosai, wani sa'in ma idan yazo sai kaga ruwan sam ba tsafta. A yadda mai gadinsa ma ya bada rahoto jiya, cewa ya yi shekaranjiya da hantsi yana baiwa fulawoyi ruwa, ya ji wai ruwan har doyi yake yi kamar ruwan mushe."
"Doyi kuma?"
Abashe ya tambaya cikin mamaki. Lokaci guda kuma ya zaro kayan aikinsa daga cikin wata bakar jakar leda dake gaban motar ya fara sawa.
"Haka dai ya ce, wai ruwan yana wari, ka san yadda masu gadin attajiran nan suke da shegen feleke, tunda in ban da neman magana ma ruwan da ba shi suke sha ba fulawa fa kawai ake baiwa ruwan.
Mai yiyuwa kuma tsoro suke kada furen fulawar ya rika warin mushe maimakon ya bada kamshi."
Malam Dogo ya ce.
Sauran kuwa suka fashe da dariya.
"A ina to matsalar take?"
Abashe ya tambaya. Lurwanu ya dubi katon gidan dake a gabansu wanda duk farfajiyarsa a zagaye take da waya da kuma manya-manyan bishiyun dabino. Ya ce.
"A wannan gidan ne matsalar take."
Lurwanu ya nuna masa gidan da hannu. Koda Abashe ya lura da kyau, sai ya ga ta karkashin wayar da ta zagaye gidan, ruwa ne ke ta kwaranya ta cikin ciyayi, tuni ma ruwan har ya fara cinye kasan motarsu.
"wannan duk daga ciki ruwan ke fitowa?"
Lurwanu ya gyada kai.
"daga ciki ne mana, abin da ya dame mu yanzu dama shi ne, mun tambaya ko mai gidan yana nan domin mu tambayi izinin shiga, sai aka ce damu wai baya nan ya yi tafiya, ina jin hutu ya samu."
"me yiyuwa kuma ba zai rasa iyali ba."
Abashe ya ce.
"A'a, an ce mana wai shi kadai ne a gidan, an ce KUMA LIKITA NE.""An ce mana wai shi kadai ne a gidan, kuma wai Likita ne."
"Ai fa, lallai sai Likitan."
Abashe ya ce yana dan murmushi.
"domin naji an ce sune basu son yawan surutu shi yasa suke yin gida a irin wadannan wuraren."
Abashe ya dan yi shiru yana kokarin sa takalmin aikinsa.
"to yanzu mene ne abin yi, ma shigar masa gida kuwa ba izini.?"
Lurwanu ya girgiza kai.
"Mun yiwa uwar gidan Alhajin waya, ta ce da mu mu shiga kawai babu komai, idan ya dawo daga tafiyar tasa Alhajin ya yi masa bayanin aikin da aka yi. Ni dai ina jin matsalar daga cikin farfajiyar gidan take."
"Ta ina to zamu shiga?"
"kai Abashe ka cika tambaya, ga inda waya can ta yage ba sai mu shiga ta can ba, in banda fa mun hango ka da yanzu muna ciki."
Mutanen shida suka kurdada ta inda wayar ta barke suka shiga gidan, Malam dogo na gaba suna binsa a baya, sannu a hankali suna bin hanyar da ruwan yake ta kwararowa ta cikin ciyayin dake a kasan lambun.
"GA INDA RUWAN KE FITOWA
Malam Dogo ya ce cikin doki. Gaba daya mutane biyar suka Karasa inda Malam dogo yake a tsaye yana nuna musu.
Ruwan ta karkashin wata KATUWAR KOFA ce dake kwance a wurin yake bullowa.
"A kasan kofar ina jin waccan tsohuwar mahadar fayif din ta ke."
Lurwanu ya ce. Sannan sai ya kara da cewa.
"ku dauke kofar ko ma ga hakikanin daga inda ruwan ya ke fitowa."
Nan da nan Malam Dogo ya kama bangare guda Abashe ma ya kama suka daga kofar da ƙyar. Koda suka dauke kofar, sai suka ga ashe wurin har ya rufta ciki ya yi rami, ruwa na ta ɓulɓulowa daga ciki har yana tsiri sama, haka nan gefe wurin kamar kasar a tsattsage take.
"me nake gani haka kamar ruwa na fitowa daga ramin tururuwa ?"
Malam Dogo ya tambaya.
"kaifa baka rabuwa da shirita, tururuwa ta rasa a inda zata yi rami sai a kasan mahadar fayif din ruwa?"
Lurwanu ya ce.
"To in ma dai ba ramin turuwa ba ne tabbas akwai ramin wani abin a wurin nan, baka ganin yadda duk ya zagaye wurin ya fara tsattsagewa, gashi nan ma har ya rufta kamar tshohuwar kushewa?"
.
****** ****** ******
.
Ƙarfe daya saura 'yan mintuna Jamilu ya fito daga wanka, har yanzu jikinsa rawa yake yi, haka nan akwai wasu alamu a fuskarsa dake nuni da cewa lallai yana cikin garari.
'Yan mintuna kadan ya dauka kafin ya gama shiryer-shiryensa. Ya fito cikin babban falo sanye da shudin wando (Jeans) da bakar (Shirt) wacce a gabanta aka rubuta
I DON'T CARE
Matarsa Ruqayya na zaune akan kujera ta yi tagumi, sa'ar da ta ji motsin shigowarsa sai ta dago kai ta ce cikin sassanyar murya.
"Jamilu....ina kuma za ka?"
Jamilu ya dube ta a rude, domin har yanzu hawaye zuba yake yi kamar ruwa a kumatunta.
"Nan...nake so in je."
Ya ce yana nuna kofar fita daga falon.
"Jamil ina zaka, Jamil me ke damun ka ne.... da na tambayeka sai ka rika yi min karya, ni wallahi yanzu idan na dubeka gabana har faduwa yake yi, dubi fa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment