Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda ka bi ka firgice."
Jamil ya ji kamar zuciyarsa zata fasa ƙirjinsa ta fito waje, a duk sa'ar da matarsa Rukayya ta zuba masa idanu, sai ya ji kamar kwayar idanunta zata iya hango ƙazamin sirrin dake boye a cikin zuciyarsa.
Jamil ya yi kaico, domin shi dama tun ranar da abin ya faru jikinsa ya bashi cewa, daga ranar sun yi hannun riga da kwanciyar hankali. Ya zargi kansa da wauta, domin sai da abin ya wuce sannan ya fara tunanin me yasa tun faruwar abin bai kira 'yansanda sun cafki dan iskan likitan nan ba? Me yiyuwa tsoron abin da mahaifinsa zai yi masa ne. To amma yanzu ya gwammace ya yi haka din, domin da tuni abin ya wuce, da tuni yana nan ciki farin ciki shi da matarsa Rukayya. A ƙalla dai ba shi ya kashe ta ba.
Sai dai kuma duk wannan tunanin ihu ne kawai bayan hari, domin shi ya san ya makara, dole ne idan har abin ya fito fili ya fuskanci hukunci mai tsanani.
"Jamil kai fa...nake tambaya, ina za ka? Ko ka taba fita ka bar ni ni kadai a irin wannan ranar?"
Jamil ya juya cikin karfin hali.
"Nan cikin lambu za ni, zo mu je tare."
Ga mamakinsa sai ya ga ta mike daga kan kujerar cikin hanzari ta matso kusa dashi ta rike hannunsa.
Suka tafi har zuwa cikin lambun kafada da kafada. Har sa'ar da suka nemi gindin wata bishiyar yazawa suka zauna babu wanda ya ce da wani ƙala. Ma'auratan biyu suka yi jugum suna duban juna na kusan mintuna biyar ba magana kamar kurame. Daga karshe Rukayya ta kawar da shirun.
"JAMIL...."
Ta kira sunansa a sanyaye gami da rike tafin hannunsa.
"RUKAYYA...."
Shima ya kira sunanta a sanyaye.
Tsawon dakiku suka sake yin shiru, sannan sai ta ce.
"Jamilu ka dubi girman Allah da Annabinsa ka fada min abin dake damunka, ko mene ne shi zan yi ma maganinsa....ka san bani da abin so da ya kai ka...idan ka ƙi fada min gaskiya Jamil, hakika zamanmu bashi da wani amfani, domin farin cikinmu ya gurɓata."
Ta yi shiru tana dubansa hawaye na zuba. Jamil ya dubeta sai ya ji zuciyarsa ta karaya.
"Rukayya ba za ki taba iya magance min abin dake damuna ba.
Rukayya ta zaro idanu sannan ta daɗa
matsawa jikinsa.
"Dan me yasa kace haka?" Jamil ya rufe idanu,
sannan sai ya cije fatar baki yace.
"Saboda ba zaki iya taba tashin
MATACCE DAGA CIKIN KABARI BA"
.
****** ******* ******
Ma'aikatan gidan ruwan dauke da digogin hakar kasa da shebura suka zagaye malam dogo cikin mamaki, idanunsa suka zazzaro kamar zasu Fado kasa saboda firgici kowannensu hancinsa a toshe. "Nafada muku....Wallahi wani abu aka binne a
gurinnan, gashi nan sara daya har ramin ya rufza ciki, agarin haka ramin ne suka huda mana fayif a banza"
"Amma kuwa duk wanda yayi wannan aiki baiyi
tunani ba.....dan me zai binne mushe a kusa da
babban fayif din ruwa...." Lurwanu ya ce ransa a bace Abashe yana duban inda ramin ya rubza.
"Haba malam ji fa yadda doyi yake tashi" Abashe yace hancinsa a toshe. Mutanen hudu suka zubawa katon ramin da ya rubza idanu, daga inda suke suna iya hangen wani dan Bangaren kadan daga inda fayif din ya huje yake fesar da ruwa.
"Ina tsammanin lokcin da aka sami fayif din bai
sami lahani sosai ba sai daga baya. Yau da
kullum ce tasa kofar ta kara girma" Malam dogo yace yana share gumi.
"Ina ganin mu fara haƙe mushen da aka binne
tukun mu gyara fayif din"
"A'a, kunji malam dogo da rigima ko, ina mu ina
wani mushe! Mu toshe fayif din kawai mu binne mu yi tafiyarmu" Rilwanu yace yana duban su Abashe malam dogo ne yafara nuna rashin Amincewarsa, "Kasan dai ba wani kayan kirki ne da muba, kaga kenan muna iyayin gyarannan ya ki yin kyau to idan muka bar mushen a gurin zaici gaba da gurbata ruwan gidan alhaji.....kunsan kuwa halinsa da mita amma idan kana ganin mu
barshi kada mu hake to shikenan, kaine oga sai
abinda kace, amma ina yima tuni da bacin ran
alhaji ana iya sallamarka aiki ma akansa. Fuskar lurwanu ta sauya launi nan da nan yaji jikinsa ya fara rawa tabbas maganar malam dogo gaskiyane. Dan haka sai rilwanu ya dubi sauran yan aikin yace
"To ya kuka gani" "yaya ka gani dai" suka amsa
masa gabadaya. Rilwanu ya hadiyi yawu da kyar yace to ku hake mushen, "yauwa ko kaifa ai gara mu hake muga ko menene yanzu hakama mushen tinkiya ce"
Ma'aikatan suka bushe da dariya dan jin abinda
malam dogo yace. Abashe ya dubeshi yana
dariya yace "Kai fa malam dogo ba ka rabuwa da surkulle in banda abinka kai tunda muka shigo anguwannan kaga inda ake kiwon tinkiya? Ina laifin ma idan kace mushen KARE !!"
Malam dogo ya ci gaba da hakar rami ba ji ba
gani in yayi yayi, sai ya fito da ga ramin su kuma
masu shebur su shiga su watso kasar da ya hako zuwa wajen ramin. Wajen yayi tsit anata aiki, to amma a gaskiyar al'amari mummunan ɗoyin da yake dada tashi ne a ko wani lokaci idan aka sari kasar shi ya addabesu, har abin ya hana musu hira ba tare da sun sani ba.
A dai-dai lokacin ne to malam dogo yaji digarsa ta sari wani abu CUS!
Sannan sa'ar da yayi kokarin cire digar sai yaji
tana kokarin masa tirjiya.
"Zo nan ka kamamin Abashe mu zare digar nan, cab ai ko dutse na sara ai sai haka" "mai yiwuwa haƙarƙarin tinkiyar ne ka sara" Abashe yace yana murmushin karfin hali domin doyin da ke tashi ya fara sa cikinsa juyawa. Suka kama digar da karfi suka fizgo sannan ne suka janyo Abinda yasasu tsalle gefe guda a tsorace.
.
"Ko da su rilwanu da ke tsaye a bakin ramin suna iya hango katon KAN da aka hako ko shakka babu katon KAN MUTUM ne.
"Malam dogo yace dan Amina Muhammadu....,..!! Na shiga uku ban lalace ba gawar mutum muka haƙo!" Ya rike numfashi "menene wancan"
Malam dogo ya nuna cikin ramin da hanunsa.
Ma'aikatan gidan ruwan suka yi duba izuwa inda yayi nuni meyiwuwa ko don da roba akayi shine, shiyasa bai rufe ba Allahu ya alamu malam dogo
ya kama fari....fari.....ja....jan kyallen da ya dingo
kai ta cikin ramin, yana ja sai kwarangwal din
hannu ya bullo waje a jikin kwarangwal din hannun harda awarwaro.
Abashe yaji gabansa ya fadi ras nan da nan yaji
kamar dawakai ne ke gudu a cikin kwakwalwarsa, shin shaidan ne ke yi masa huduba ko kuwa dai-dai tunaninsa yake. Abashe ya ture malam dogo
ya durkusa akan kwarangwal din ya kama fari-
farin kyallen ya dada fuzgoshi waje da karfi ya
kura masa idanu.KARSHE...
.
Malam dogo ya kama fari....fari.....ja....jan kyallen da ya dingo kai ta cikin ramin. Sauran ma'aikatan suka zagayeshi cikin mamaki.
.
"WAYYO....ALLAH....LARAI....na shiga uku...." ya kwalla ihu, sannan ya fadi cikin ramin sumamme. Mintuna biyar bayan haka farfajiyar gidan ta cika makil da yan sanda.
.
****** ****** *******
.
Malam Audu ya fito daga cikin dakin ransa a bace domin ya tambayai Abubakar inda matarsa Amina take yace bai sani ba.
"Abubakar" ya kwallawa yaron kira, da zummar ya turashi makwabta ya duba masa ko tana can, sai ya ji Amina tayi sallama.
"Daga ina kike?" Malam Audu ya tambayeta.
"Gidan shahararren boka naje..." Amina ta amsa masa kai tsaye akwai alamar farin ciki a fuskarta wanda Malam Audu ya rasa ko na menene. "Boka fa kika ce?" Amina ta gyada kai "kwarai kuwa boka, maganar Larai ce ta kaini gurinsa, da ban yi niyyar gayamaka ma ba." cikin mamaki malam Audu yace.
"To gashi kuma yanzu kin fada"
"Farin ciki ne ya sani malam....BOKAN nan ya ce da ni tabbas Larai tana nan da rai a duniya bata mutu ba kuma....." Karan tarhon da ya dauki ruri shi ya katseta. Malam Audu ya nufi dakin cikin sauri a rude da jin zantuttuka dake fita daga bakin matarsa Amina, an ya kuwa ba tunani ne ke son zautata ba?
"Wanene" ya tambaya sa'ar da ya dauki wayar tangarahon. Amina ta biyoshi cikin dakin
"Kwamishinan yan sanda ne jibo" aka amsa masa sannan ya fara yi masa bayani cikin gaggawa. Bayan minti biyu ya ajje kan tarhon din. Amina ta lura da sauyin yanayin da ke fuskarsa.
"Lafiya kuwa....?" malam Audu ya dubi matarsa fuskarsa a muruke ya ce.
"Kirawo Abubakar mu tafi"
"Ina zamu" "yanzunnan da kwamishina muka gama magana ya ce an gano Larai....sai dai kuma bokan ki
YA TABBATA BABBAN MAKARYACI.
.
****** ****** ******
.
Lokacin da suka iso tuni angama hako sauran abin da yarage na daga gawar Larai.
Yan sanda sai faman sunturi suke ana ta gwaje-gwaje da aune-aune.
Malam Audu yayi fakin da motar a gindin bishiyar turare. Matarsa Amina na bayan motar kusan ma a sume, domin hawayenta ya kare ba kuma ta motsi a zaune kurum domin kamar mutum-mutumi.
"Ku jirani anan ciki kada ku fito waje"
Malam Audu ya ce da su. Ita da ɗansu Abubakar ne zaune a bayan motar. Malam Audu ya nufi inda jami'an tsaron suke, tun daga nesa ya hango kwamishina jibo ya sulale daga cikin jami'an ya nufo inda yake. Suka kebe can nesa da jama'a.
"Kun tabbata ita ce din?" Abin da malam Audu ya fara tambaya kenan. Jibo ya shafi dogon sankonsa wanda yake ta zubar da gumi yace.
"Kwarai kuwa ita ce, ai saurayinta ma ya ganeta"
Malam Audu ya dubeshi cikin mamaki ya ce "Wa kenan?"
"Abashe mana, ai su suka tono ta suna aikin gyaran fasasshen fayif na ruwa.
"Duk da haka ai gara in je na ganta da kaina domin kara tabbatarwa" Kwamishina jibo ya girgiza kansa.
"Zaifi dacewa ka hakura, ka ringa tunawa da ita a zuciyarka kamar yadda take a da, domin ganinta a yanzu na iya sa ma mummunan tunanin da zaka yi shekaru da dama baka manta ba." ya danyi shiru yana maida numfashi sannan sai ya nuna ginin da ke farfajiyar gidan ya ce.
"ya na ciki suna tambayarsa" Malam Audu ya sake dubansa a rude "WA KENAN..."
Mai gidan mana, tuni har ya fara waken abinda ya faru sa'a muka yi kasan baya ma gari yayi tafiya dawowarsa kenan muka sa aka cafke shi....Allah ne ya toni asirinsa da yana nan bazai taba barin ma'aikatan ruwan su rabi gidan ba" Malam Audu ya share gumi sa'ar da Jibo yaci gaba da cewa.
"kaji ashe JAMILUN da muke nema shi ya kawo masa ita ya zubar mata da ciki.....ahaka aka sami matsala ta mutu"
"Duk yanzu ya fada muku wannan?" malam Audu ya tambaya wani busasshen murmushi ya bayyana a fatar bakin Jibo.
"Yaran mu ai sun iya Suburbuɗar mutum, zasu iya yiwa mutum dukan da zai iya tunawa ma da ranar haihuwarsa, bikin da irin abincin da aka dafa, ballantana kuma dan abinda ya faru shekara daya kawai"
Kukan jiniyar motar asibitin da ta shgo gidan ita ta katse jibo mutanen biyu suka juya baki daya.
"Abashe zasu dauka kasan ya fadi sumamme" ya danyi shiru sannan yace.
"Zo muje ku gana da likitan, nasan inda ace dacan ma kasanshi, to idan kagansa bazaka iya ganeshi ba a yanzu, kai Uwarsa ma bazata iya ganeshi ba a yanzu. Mu tafi" mutanen biyu suka nufi dakin, koda suka fara tafiya sai malam Audu yaji anyi kiransa a baya. Nan da nan ya juya. Ɗansa ne Abubakar ya biyo su dauke da wata guntuwar takarda a hannunsa.
.
"Baba kaga wannan wasikar, ɗazu na ganta a cikin littafina na (Biology) ina jin ita tasata a ciki. Malam Audu ya karbi wasikar, suka karanta shida kwamishina sannan sai malam audu ya juya yace.
"shikenan Abubakar koma cikin mota ku zauna da babarka" Bayan ya tafi, sai suka dubi juna, malam Audu ya juya takardar ya ce.
"Ina ma ace tun da wuri muka sami wannan shaidar" jibo ya shafi sanko.
"Koda ace ma tun da wuri muka sameta, banajin zata yi mana wani kwakkwaran taimakon, domin kuwa jamilu kawai aka rubuta a jiki, babu adreshi Jamilu kuwa da yawa a garinnan, wa zamu nema tunda dai ya bace kuma ba'a san inda yake ba" .....Malam Audu ya gyada kai cikin gamsuwa.
"Kwarai kuwa bata da wani amfani, domin in ban da Allah ya tonin asirin wannan Likitan da jamilu ya bace mana kenan.....amma yanzu ai dole ya nemo mana shi".
.
Jibo yayi murmushi.
"Tuni mun tura jami'an mu su cafko mana shi, na fa gaya ma Likitan nan ya daku, dan haka ya gama yin aman komai, zo dai......muje kaga dan banza".
Yan sandan biyar dake tsaye bakin kofar dakin suka kame gami da sarawa lokaci guda, sa'ar da tsohon kwamishina da mai ci a yanzu suka zo shiga gidan.
Koda suka wuce cikin gidan sai wani kurtun dan sanda ya dubi sajan din dake kusa da dashi yace cikin rada.
"kaga fusakarsa kuwa? Wallahi kamar bai damu ba da mutuwar yar tasa ba"
Sajan din ya dubi kurtum da fuskar katako yace da shi a fusace.
"Me kake tsammanin zai yi? FASHEWA DA KUKA ??"
Alhamdu lillah.
DARE DA RANA
Na Nazir Adam Salih
Ebook creator:- Shuraih Usman 99%
Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so

For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading
Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521

Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu
Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya
Hakkin mallaka (m) Nazir Adam Salih


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment