Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dada firgita ce, gashi dai yana son komawa gida, amma hanyar da ya biyo a baya da zai shigo dajin ta boye masa. Yana tsaye a tsakyar dajin, babu maboya, ga duhun bishiyun dai yana ji yana gani, kuma so yake yi ya shiga ciki ya buya, to amma akwai wani abu a cikin zuciyarsa dake yi masa gargadi.
"wannan hannu da yake taba maka kafada ba hannun wani shege ba ne ajinsin bil' Adama, kuma tabbas daga cikin duhuwar ake turo shi."
Aka yi tsawa mai rugugin gaske, amsa kuwwar tsawar da ta keta koramu da duwatsu dake a dajin, sannan sai wata walkiya mai hasken gaske ta haskake dajin kamar rana, a lokacin ne ya sake jin an taba shi a baya, ya juya a tsorace zai kwala ihu, a sannan ne ya yi ido biyu da ita. A tsaye a bayansa, kanta babu dankwali, gashin kanta a tsefe kamar shekar ungulu. Larai ce dauke da digar hakar kasa katuwa, ga kuma shebur a hannunta.
"Kai ka janyo min munafiki, kai ka sa aka kashe ni, aka binne ni a wulakance. To bari ka ji kaima yadda mutuwa take."
Larai na gama fadin haka sai ta daga digar ta kwada masa a kirji, nan da nan ya fadi yana ihu a firgice.
"Na shiga uku, ki yi min rai Larai."
Jamilu ya farka a firgice, yana farkawa sai yayi ido biyu da Rukayya matarsa. Tana a zaune akan gadon tana kallonsa a rude..
"Wacece Larai da ka ke mafarki da ita kullum?"
Rukayya ta tambaya a fusace.
.
**** **** ****
.
Jamil ya sake gyara zama akan gadon yana mutsttsike idanu, lokaci guda kuma ya share hawayen dake kwaranya akan fuskarsa kamar ruwa.
"Wa...wace...ce Larai...da har ta fi ni matsayi a wurinka, kullum sai kayi mafarki da ita?"
Rukayya ta sake maimaita tambayarta a gare shi, wannan karon bakinta na rawa.
Jamil ya kalleta a rude, domin shi kan sa bai san abin da zai ce da ita ba.
Me ki ka ce...ina cewa Larai ko me, wace ce kuma Larai?"
Ya ce shima bakinsa na rawa.
Kai ka santa, kai ka san inda za a same ta, tunda kullum dai a 'yan kwanakin nan sai kayi mafarkinta."
Jamil ya ji gabansa ya fadi, domin bai taba tsammanin a irin mafarke-mafarken da yake yi da larai sun fara fitowa fili ba. Ya yi kokarin ya hada ido da matarsa Rukayya amma abin ya gagara. Nan da nan sai ya ji wani zazzafan gumi yana barko masa, ya dago kai ba tare da ya yarda sun hada ido da matarsa ba, ya dubi agogon dake dakin ta farin watan da ya ratso cikin dakin ta taga, karfe goma sha biyu saura mintuna takwas na rana. Jamil ya dafa gadon da hannunsa, sa'anan ya matsa can kurya ya jingina bayansa da jikin bango, sannan sai ya ce cikin wata raunananniyar murya.
"Ni ban san abin da ki ke son fada ba....ni ban san wata Larai ba."
Ko shi da ya fadi maganar ya san karyar tasa a kasa ta fadi babu nauyi..
Matarsa Rukayya ta dube shi cikin kunan rai ta ce a sanyaye.
"Haba Jamil....tsakaninmu babu karya da cin amana, wannan fa ba a boye yake ba, kullum ta Allah, ko dare ko da rana in kana barci sai ka ambaci sunan LARAI. da farko ban dauki hakan a bakin komai ba, to amma daga baya sai naga abin naka yayi yawa, domin tun kana mafarki da ita da daddare, gashi abin ma har a barcin rana....."
Rukayya ta fara shasshekar kuka.
"ba sai ka yi min karya ba Jamil, idan ka san ka samu wata da ta fi ni ne kawai ka fada min shi kenan, ba sai ka tsaya wani noke-noke ba."
"Da ace haka ne ai da ta kwana gidan sauqi ma."
Jamil ya ce a cikin zuciyarsa.
.
Ko baka ji ni ba ne Jamilu?"
Rukayya ta ci gaba da cewa.
"So da kaunar juna ce ta hada mu tun asali Allah Ya kaddara aure a tsakaninmu, babu takurawa juna tunda dai har wacce ta fi ni a zuciyarka ta yi karfin da har zaka ke mafarki da ita
DARE DA RANA.
to mu hakurewa juna kawai!"
Ba abin da ta fada bane kawai ya sa Jamil kaduwa, akwai wani abu wanda ke akan fuskarta shi ne ya tabbatar masa da cewa, idan ya yi wasa tana iya gano sirrin dake a cikin zuciyarsa..
Wani zazzafan gumi ya ci gaba da keto masa ta ko'ina. Tun ranar da suka binne Larai ya yi imanin cewa shi da kwanciyar hankali sun yi sallama. Koda yake 'yan watannin da suka gabata sun zo wa Jamil a bazata...
'Yan watannin da suka biyo bayan aurensa da Rukayya sun zo masa a bazata, domin bai taba tsammanin zai sake yin farin ciki ba har iya tsawon rayuwarsa.
To amma sabanin tunaninsa, sai amaryarsa ta kasance mace ta gari, mai biyayya da kokarin ganin ta faranta masa a koda yaushe, ban da abubuwan al'ada da mace take yiwa mijinta, wani sa'in har dora kansa take yi akan cinyarta, kana ta fiƙe zazzakar muryarta tayi ta rerawa abin kaunarta Jamil waka, wannan abu ba karamin farantawa Jamil rai yake ba, tasirin hakan ne ma har yasa ya rage tunanin Larai, duk kuwa da cewa da zaran dare yayi ya kwanta barci babu abin da yake fara arba dashi sai Larai. Tun abin yana tsorata Jamilu, har dai ya fara sabawa, wani lokacin sai yayi mafarkin Larai tana yi masa murmushi tana cewa:
"Jamilu kaine masoyina, mijina, wani sa'in kuma sai ya ganta cikin fararen kaya, amma duk sun rine da jini.
To amma duk wadannan mafarke-mafarke da Jamil yake yi babu wanda yafi tsorata shi ya firgitashi, ya ruda shi, ya kuma sa shi fita daga hankalinsa irin na yau abu mafi muni ga al'amarin shi ne, surutun da yake yi a cikin mafarkin sun fara fitowa fili, gashi kuma a yanzu har matarsa Rukayya ta rike sunan Larai, wannan bakaramin tayar masa da hankali ya yi ba, domin in har akwai abu daya da ba zai iya fuskanta ba a duniya, to shi ne ya fuskanci matarsa Rukayya da gaskiyar labarin tsakaninsa da Larai, tun shekara guda da ta gabata.
Jamil ya dago kai a hankali, sai ya dubi Rukayya,
.
"Bani da wata mace a duniya da ta fi ki matsayi, sanin kanki ne cewa tun daga ranar da na aure ki ban taba yi maki zancen ko kuma ambaton wata 'ya mace ba a gabanki, to mene kuma na damun kan ki kan abin da nake fada a cikin mafarki?"
Jamil ya yi shiru yana nazarin fuskar matarsa Rukayya, abin da ya gani bai yi masa dadi ba, domin ko kusa ko alamu ya san zancensa bai samu wurin zama ba.
"Wace ce Larai?"
Rukayya tayi tambayar gami da dago kai, lokaci guda ya ji yawun bakinsa ya tsinke.
"Ban.... ban santa ba... mafarki ne kawai Rukayya.... kin san kuwa mafarki ba gaskiya ba ne...."
Yana gama fadin haka sai ya ga Rukayya ta sunkuya da kanta kasa, nan da nan hawaye ya fara zuba shar-shar kamar ruwa.
"Haba.... Jamil, yin karya ga matar da take biyayya a gareka bashi da alfanu, ka tuna fa Jamil tun farkon daren amarcinmu ka fara yi min karya.... shiru fa nayi kawai na kyale ka."
Jamil ya dubeta cikin mamaki.
"me ki ke nufi da nayi miki karya ran daren amarcinmu?"
Rukayya ta fashe da kuka.
.
"Da na tambayeka ko jinin mene ne a jikinka ka bani amsa?".
.
--------------------------------------------------------
KASHI NA SHIDA
Ko minti biyar bai yi da tafiya ba, sai ta mike ta nufi ban daki, ta wawwanke jirwayen hawayen dake a fuskarta, sannan ta dawo daki ta sauya sutturar dake a jikinta cikin sauri, ta dauki bakar jakarta ta rataya, ta fice daga cikin gidan ta nufi bakin titi.
Duk zancen da Malam Audu yake yi, matarsa Amina jinsa kawai take yi, domin ita a tunaninta babu wanda ya fita jin ciwon bacewar 'yarta Larai. Amma tayi imani da cewar, in har neman da 'yan sanda suke yiwa 'yarta na shekara guda basu gano inda Larai take ba, to kuwa ba zasu taba gano mata ita ba. Wannan shi yasa tun a daren jiya, bayan ta gama cin uban kuka, sai ta yanke shawarar tunkarar BOKA.
Domin sa'ar da suna 'yan mata ta taba jin wata kakarta mai suna Gwaggo Shatu, tana cewa wai bokaye na aiki da aljanu, wai wani sa'in har turasu suke yi su sato musu kudi, ko kuma duk wani nau'i na kayan masarufi da suke bukata. In har wannan batu da ake fada gaskiya ne, Amina ta jaddawa kanta, to babu abin da zai hana bokan da ta tunkara a yanzu ya tura aljanu su binciko mata duk inda 'yarta take a yanzu ba.
Ƙarfe goma sha biyu na rana daidai ta karaso bakin titin, tana tafiya tana waige-waige a alokaci guda kuma tana addu'ar Allah Ya sa kada wani abu ya dawo da mijinta Malam Audu baban Larai gida da wuri, domin kuwa bata sanar dashi cewar zata jarraba aikin bokaye ba.
Bata fi mintuna uku da tsayuwa ba, wata tsohuwat taksi ta nufo inda take. Rana tayi zafi, don haka motocin haya ke wahala, sa'ar da tsohuwar motar mai hanci kamar shantu ta tsaya bayan direban yayi gaggawar taka burki, babu mamaki shi kansa yana tunani idan har ba a irin wannan lokacin ya fito ba to babu wanda zai kula tsohuwar motarsa koda kuwa kyauta zai dauki jama'a.
"Ina zuwa ne Hajiya?"
Koda Amina tu dubi bakin direban sa'ar da yake murmushi, sai ta ga ashe hakoransa guda hudu na saman duk sun zube, sai wawukeken wawulo kamar kofar wambai.
"Shata nake son in dauke ka."
Ta ce cikin rawar baki, lokaci guda kuma tana waige-waige.
"zuwa ina?"
Direban ya sake tambaya, har yanzu wawulonsa a bude yake, shiru na dan lokaci yana dubanta kafin ta ceZuwa ina?" Direban ya sake tambayarta, har yanzu wawulonsa a bude yake. Shiru na dan lokaci yana dubanta kafin ta ce.
"Da dan nisa kadan, wani dan kauye ne zaka kai ni, zai kai kilomita talatin daga nan garin."
"To ai kamata ya yi ki fadi sunan kauyen Hajiya."
Direban ya ce.
"KWANAR MAKARAI zamu je."
Direban ya saki wata shaƙƙƙiyar dariya kamar ana sace taya,
"Naso in san labarin wani Boka a garin
BOKA MAKARAI ina jin can ki ke nufin Zuwa."
.
Amina ta ji gabanta ya fadi domin kuwa bata taba tsammanin wani direba mai tuki a nan garin zai iya sanin bokan ba.
"Nan...zamu je."
"Shigo Hajiya.....ai an gama har kofar gidansa zan kai ki."
Yana gama fadin haka sai ya bude mata kofar gidan ta baya, Amina ta shige motar cikin sauri, sa'anan ta rufe kofar.
Direban ya fizgi motar cikin gudu na mamaki, domin ko Amina dake zaune a bayan motar bata taba tsammanin motar zata yi gudu kamar haka ba.
Koda suka fara tafiya, sai Amina ta rika kalle-kalle ta tagar motar, tana hangen jerin gwanon mutane da suke ta kai kawo suna ta hada-hadarsu. A lokaci guda kuma tana mai fatan inama-inama.....
Har suka fice daga garin bata ga wata yarinya mai kama da Larai ba
.
***** ****** *******
.
Sha biyu da rabi dai-dai suka isa gidan Boka Makarai, gidan shi kadai ne a tsakiyar dokar dajin, ko da yake ba ace shi kadai ba, domin akwai kauye kimanin kilo mita biyu daga gidan Bokan.
Gidan a zagaye yake da dangan kararen dawa, haka nan akwai dakunan bukkoki har guda uku. Abu daya kawai ya baiwa Amina sha'awa a gidan, shi ne ganyen duma da korai da ya yi yado akan katangar gidan, kore shar dashi, ga shuke-shuken bishiyoyin lalle nan burjik a tsakar gidan, Malam buda mana littafi da kwaron lalle sai shawagi suke yi, kai ka ce ba zasu mutu ba. A can wata katuwar bishiyar tsamiya mai dauke da katon rarakakken kogo, wanda a ciki Boka mai makare ke sha'aninsa.
A kofar gidan Direban ya sauketa, don haka sai da Amina tayi tattaki har xuwa tsakar gidan. Tana jefa kafarta a cikin gidan sai ta ji duk an dauki sowa cikin wasu irin muryoyi marasa dadin ji.
"Sannun ki da zuwa! Baiwar Allah mu muke ganinki ba ke ki ke ganinmu ba. Maraba da gasasshe, kura ta ga bakin jaki! Ja ya fado ja ya dauka! Mu ci mutum danye mu sha jinin makiyinmu, masoyinmu kuwa ya ga biyan bukata."
Amina tayi sororo tana mai nadamar zuwanta wannan gida. Tunda take bata taba mu'amilla da bokaye ba, ko wannan ma wata kawarta ce Ta Madabo ta bata labari. A tunanin Amina zuwa wurin boka tamkar zuwa asibiti ne, ka bi layi ka sayi kati, sannan ka ga likita ya fada ma irin cutar dake damunka da kuma maganinta. Don haka a wannan sa'ar da Amina ta ji muryoyin sihiri masu sa firgici sun gauraye gidan, sai ta rikice ta fara yunkurin juyawa a guje.
"kada ki ji tsoro Amina, matso nan kusa da ni ki fadi bukatarki, tuni mun samu labarin zuwanki."
Amina ta dubi gindin bishiyar tsamiyar cikin mamaki da tsoro, domin daga nan ta ji ana kiran sunanta. Jiki na rawa ta matsa bakin kogon, jakar dake makale a kafaradarta kamar ta subuce ta fadi kasa.
Amina tayi ido biyu da wani jibgegen mutum mai kamar giwa, domin saboda girmansa ya cike duk kusan iya fadin kogon, yana sanye da hular gashi, kunnayensa dauke da wasu rafka-rafkan 'yan kunnaye masu kama da awarwaro, idanunsa jazur kamar garwashin wuta, yana sanye da rigar fata, kafafunsa a bude ya yi zaman karaga. Haka nan daga inda Amina ke tsaye tana iya jiyo warin dake tashi daga jikin bokan kamar mushe, gashi dai tana son ta rufe hancinta, amma tsoro ya hana ta.
.
"Me ke tafe da ke?"
Ya tambaye ta cikin wata irin murya mai kamar ana buso ta daga cikin bututu.
Amina ta gyara daurin zanen dake a kugunta, jikinta na rawa ta ce cikin rawar murya.
"'Yata ce ta bace....yau kusan shekara guda kenan, har yanzu babu labarinta boka."
Katon bokan mai kamar giwa ya fashe da dariya, ya ce.
"Tun tuni dama muka samu labarinki, tun bara war haka muna da labarin nacewarta. To amma yanzu me ki ke so ayi tukunna kafin na baki labarin bacewarta?"
Amina ta dada matsowa kusa jikinta yana bari saboda ɗoki..
"So nake in da hali a sa aljanu su dauko min ita a duk inda take a duniya...."
Sauran maganar ta makale a maqogwaronta. Boka makare ya sake kecewa da dariya.
"Saurara da kyau in baki labarin 'yarki. Da farko dai ina son ki sani cewa, a yanzu dai 'yarki tana cikin hadari, domin a ranar da ta bace 'DAN DAMASORO ya kawo min labarinta, ya ce dan Sarkin aljanun kasar sin sarki ZULZULAKUBKI ta takawa kai, shi ne fadawan sarkin suka kama ta suka tafi da ita can bayan bahar maliya, suka jefata a kurkukun aljanu. A yanzu haka tana can kullum sai an yi mata bulala, ko jiya ma da yamma sai da aka kawo min labarin cewa, ta sha duka a hannun shugaban kurkukun HANDADANA."
"na shiga uku, wayyo Larai!"
Amina ta fashe da kuka.
"Bari kuka tunda kin zo gare mu bakin cikinki zai yaye, zamu iya sawa ayi maki belinta daga hannun....wadannan mugayen aljanu."
Boka mai makare ya ce, sannan ya ci gaba da cewa.
"Idan har za ki iya sayen turmin atamfa biyar, wanda za a kaiwa matan Sarkin aljanu don kamun kafa, kwaryar zuma goma, a baiwa 'yar sarki don neman samun shiga, turmin farin alawayyo talatin wanda za a baiwa masu tsaren kurkukun, kaji ashirin, Zakaru goma wanda za a baiwa aljanu sa kaiwa mara lafiyar da 'yarki Larai ta takawa kai. To shi sarkin Aljanu koda raguna biyar aka yanka masa ya sha jinin ya isa ya huce fushinsa ya amince a sako Larai daga kurkukun. Idan kuwa ba haka aka yi ba, to sarkin aljanun dan banza ne, domin idan ya fara fushi baya hucewa sai bayan shekara saba'in da wata bakwai da kwana bakwai da yini daya."
Amina ta dafe kirji cikin takaici bakinta na rawa ta ce.
"Ala gafarta boka wadannan lissafe-lissafe da kiwo, ni duk ban gane su ba, sai dai ka lissafa min abin da za a kashe, in dai Larai zata dawo gare ni, to zan biya ko nawa ne."
Boka makarai ya ƙware jajayen idanunsa, sa'anan ya girgiza kai kamar ƙadangare, kusan minti biyu sa'anan ya dawo da kansa kasa ya dubi Amina.
"Sun ce da ni jimlar kayan da na lissafa maki gaba daya naira dubu saba'in ne."
Amina ta ji gabanta ya fadi, domin kuwa 'yan kudaden dake a cikin jakarta a yanzu basu fi dubu goma ba, suma kudin adashi ne da ta dauka shekaran jiya.
"Ala gafarta boka 'yan kudin dake hannuna a halin yanzu dubu goma ne kawai, amma in za a amince min alkalami, zuwa jibi duk inda zan kurdada in samo dubu sittin zan samo su in kawo maka."
Amina tayi shiru gabanta yana faduwa, domin babu mamaki ya ki amincewa da batun ta.
"Ajje su a nan."
Bokan ya ce da ita yana muzurai.
"Kada ki sake ki wuce jibi ba ki dawo da cikon kudinki ba, domin bana jin 'yarki zata iya jure bulalar aljanun nan ta kwana uku nan gaba....ina fargabar in har ki ka wuce jibi, to kima ajje kudinki, kada ki zo ki ɓata lokacin ki a nan, domin ko shakka bana yi zasu shanye jinin 'yarki Larai a cikin kwana ukun nan."
Amina ta girgiza kai cikin firgici.
"uhmn-uhmn, ba zan ma wuce ba wallahi, zan kawo ma mallam....boka."
Ta dan yi shiru na wani lokaci , sannan sai ta ce dashi cikin karyayyiyar murya.
"Don Allah boka idan aljanunka za su tafi can yau ka ce dasu su ce da Larai ina gaishe ta...."
Fadin hakan ke da wuya sai ta fashe da kuka. Ba kukan bakin ciki ba ne, na farin cikin jin cewar har yanzu Larai tana nan a raye ne bata mutu ba.
.
***** ***** *****
.
Tun daga babban ofishi na jiha wasu daga cikin jami'an tsaron da suka shaida shi suka fara bushewa suna sara mashi cikin girmamawa.
Da yawa daga cikin kuratan da Kofuran dake ta sara masa, suna yi ne kawai saboda sabo, wai gawa da yatsine, amma ba wai don sun ji dadin zama dashi ba.
Tsohon Kwamishinan 'yan sanda Audu ya yi fakin din tsohuwar motarsa ƙirar fijo 504 a daf da wata bakar motar 'yan sanda, sa'anan ya fito cikin sauri ya nufi ofishin kwamishina mai ci a yanzu . Jefi-jefin 'yan sandan da yake ta wucewa a hanya suka ci gaba da kamewa kamar itatuwa, shi ko bai ko kula ba, in har ma ya kula da abin da suke yi to bai wuce ya gyada masu kai kamar kadangare ba. Lokacin da ya je dakin tarba tuni sun samu labarin zuwansa, domin bai zo ba sai da ya bugawa kwamishinan ILYA SANDA JIBO ZAKIRAI waya kafin ya karaso.
"Kwamishina yana tsammanin zuwanka yallabai, kana iya wucewa kai tsaye."
Wani sajen ne mai molalliyar fuska kamar gwangawani yake bayanin game da sarawa tsohon Kwamishina Audu.
Kwamishinan llyan sanda Jibo Zakirai ya tari abokin sa kuma tsohon mai kujerar, wato AUDU S. BABALLO.
"Tun dazu nake sa rai da zuwanka."
Jibo Zakirai ya ce cikin fara'a. Malam Audu ya nemi kujera ya zauna a lokaci guda kuma yana nazarin tsohon ofishinsa, wanda babu wani kwakkwaran sauyi da aka samu a ciki, har yanzu dai fankadeden teburin nan ne wanda ke lullibe da gilashi, gami da manyan kujeru masu shudin karen muski dake dakin. To amma an samu sauyin tattausan kilishin dake shimfide a tsakar dakin, haka nan gurbin da hotonsa yake a da yanzu na Jibo ne, duk wannan ya lura dasu ne a kallo daya. Sa'anan sai ya dawo da kallonsa ga abokinsa Jibo.
.
Jibo Zakirai dogo ne fari kakkaura, yana da bille a fuskarsa, haka nan kansa dogo ne sai shan kwakwa, babu alamar gashi ko kwallo, kullum a haka yake yana ta sheki kamar kwalba, ga wadanda basu sani ba kullum suka ga Kwamishina Jibo babu hula, sai sun yabawa wanzamin dake iya jurar kankarar wannan dogon kai a wannan duniyar. Amma kuma wadanda suka san kwanan zancen su kan yi addu'a ne kan Allah Ya raba su da irin wannan sanƙon na Jibo Zakirai. To amma fa duk da haka a cikin wannan kan da sanko ya lulliɓe akwai tarin baiwar kwakwalwa ma'abociyar fasaha da hikima ta ban mamaki musamman a fannin bincike.
"maganar nan ce dai ta dawo da ni Kwamishina."
Mallam Audu ya ce bayan ya zauna"Maganar nan ce dai ta dawo da ni Kwamishina."
Malam Audu ya ce sa'ar da ya zauna.
.
Kwamishina Jibo ya shafi dogon sankonsa na dan lokaci, sannan ya ce.
"muna nan muna bakin kokarinmu."
Ya dan yi shiru. Sa'anan ya ci gaba.
"wato baka san wani abu ba Malam Audu, na dade ban ga kes mai rikitarwa ba irin wannan, domin kuwa ka ga duk kusan eriyar gidanka babu inda bamu tura yara sun bincika ba, amma kowa muka tambaya sai ya ce babu labari. Mun yi kokarin tattambayar mutanen dake garin, ko akwai wanda ya ganta a daren uku ga watan maris din bara, amma shiru. Ka san mutanenmu yadda suke, wani ko lissafin ranar da aka haifeshi baya iya rikewa ballantana ranar faruwar wani abu daban.
Jibo ya yi shiru yana duban Audu cikin damuwa, lokaci guda kuma yana wasa da wani jan biro dan siririn gaske.
"mun tura yara kowanne asibiti dake garin nan, ko ya Allah... In ma hadari ne ya faru da ita mun ji shiru babu labari, mun tura maƙwabtanmu sauran jahohi duk a banza. Kuma ka ga a yanzu haka kullum duniya sai mun aika yara biyu sun rika lura da eriyar gidanka ko Allah zai sa mu ga ko irin samarinta ne mu tambaye su, to amma abin mamaki shi ne, tun daga ranar bamu ga ko saurayi daya ba, sai wani dogon saurayi fari wanda shi kuma muka lura da cewa, duk sa'ar da ya je gidan yake shiga kai tsaye, kuma ya kan dade kafin ya fito. Don haka sai muka daukeshi kawai a matsayin dan uwanta ne, ko kuma dan uwan matarka, shi ya sa bamu sa yara sun latsa shi ba."
Jibo ya yi shiru sa'ar da yaga Malam Audu ya tsuke fuska cikin tunani.
"wanda ka ke fadi ka ce dogo ne?"
Audu ya tambaya a karo na farko. Jibo ya gyada kai.
"ƙwarai kuwa, a yadda rahotonmu ma ya bamu, har yana da dan tabo a gefen kuncinsa na dama, an ce tabon ya yi kama da ƙunan wuta."
"ABASHE kenan!"
Malam Audu ya ce.
"saurayin Larai ne, tun tana Ƙarama Yake son ta, duk da yake dai ba wani jituwa suke yi ba, amma dai har sa'ar da ta bata su kan dan zanta.".
"ban da shi kuma babu wani saurayi da take so daban?"
Malam Audu ya dan yi jim kadan.
"wato yanzu dai na fahimci bincikenku ya koma kan samarinta kenan!"
Jibo ya gyada kai.
"Tabbas, domin tun dadewa ma abin da ya kamata mu fara yi kenan. Don haka in zai yiwu zan hada ka da yaranmu cikin fararen kaya, domin a rahotanmu mun ji cewar duk sa'ar da ya je sai ya tura an yi kiran yaron ƙanin Larai, sannan suke shiga gidan tare. Ina ganin yaronka zai iya sanin samarinta. Ka san irin wannan sha'anin, da yawa kannen budurwa su kan san sirrin samarin yayarsu. Me yiwuwa mu samu bincike mai kyau a can.
Malam Audu ya gyada kai cikin gamsuwa, sannan sai ya ce dashi ba zato ba tsammani.
"Jibo....kai a tunaninka yarinyar nan tana da rai kuwa?"
Jibo ya dubi Audu cikin mamaki ya ce.
"Ba zan iya sani ba....Audu, amma kuma me yasa ka yi min wannan tambbayar?"
Malam Audu ya amsa kai tsaye.
"Saboda in har Larai bata da rai, to me yiwuwa uwarta ma mutuwa zata yi, domin a yanzu haka ko abinci bata iya ci."
.
---------------------------------------------------------
.
KASHI NA BAKWAI 7
Tun daga nesa abubakar ya fara tsalle sa'ar da ya hangi Abashe, ko shakka baya yi ya san yau kakarsa ta yanke saka, domin duk da ya san cewar wannan Jamilun mai zuwa da babbar mota yana kamshin turare ya fi Abashe kudi, to amma shi yaron ya san Abashe ya fiye masa alkhairi.
Lokuta da dama Abubakar yana tambayar kansa dalilin da yasa yayarsa Larai ta watsar da tsohon saurayin ta Abashe ta kama wannan Jamilun mai mota, shi kam a ido yafi son Abashe da wannan Jamilun nesa ba kusa ba, kuma ba wai dan Abashe yana yi masa alkairi bane, a'a kawai akwai wani abu da Abubakar ya tsana ne dake tattare da Jamilu, kuma ko banza ma ai Abashe ya dade yana ƙaunarta, kuma shi aka fi sani a gidansu tuntuni.
Amma wannan

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment