Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasa "Dan ubanka wayace ka kashe min ita" Likita sirajo yasa ihu cikin kaduwa Jamilu ya sake naushin bakinsa, jini yayi tsartuwa akan tsohon kilishin da ke shinfide atsakar dakin, jamil na ganin haka ya daga likitan wanda ke zubar da jini ta baki da hanci ya nufi can kuryar dakin inda wani tsohon kan tarho yake sa'annan jamil ya juyo yana duban likitan dake kwance akan kilishin yana murkususu yace dashi.
"Dan uban ka yau sai na ɓatar dakai...Wallahi yan sanda zan bugawa waya su zo su nademin kai, daga yau ka sake kashe wani...." Likitan yayi sauri ya tashi zaune jikinsa na ɓari. Yasan cewa
Idan har ya bari Jamil ya bugawa 'yansanda waya to kashinsa ya bushe...me yiwuwa ma ƙarshen rayuwarsa yazo kenan.
"Don Allah kayi min rai."
Likitan ya roke shi a firgice.
"Idan 'yan sanda sunzo sai kayi masu bayani."
Jamil ya ce cikin shasshekar kuka. A daidai lokacin ne to wata basira ta bijirowa Likitan, nan da nan ya fesar da jinin dake zuba a bakinsa ya ce muryarsa na rawa, domin maganar da yake son zai fada ita ce sarauniyar cankarsa a cacar da ake, in dai har wannan ba ta ci ba, to ya riga ya sallama, shi kam daga yau ya san kashinsa ya bushe, tafiya tazo masa karshe.
"Kada ka buga wayar nan Jamilu."
Likita Surajo ya ce dashi da muryar gargadi. Jamil yayi zaune sororo da kan tarho din a hannunsa, akwai wani abu da ya ji a muryar dan siririn likitan a matsayin gargadi ga barin hakan.
"wannan al'amarin mu kadai muka sani, daga ni sai kai, to amma yanzu idan ka kira 'yansanda wanne bayani zaka yi musu su gamsu a matsayinka na wanda ya yiwa yarinyar ciki? Kuma bugu da kari idan maganar ta fito fili ya zaka ce da sabuwar amaryarka? Yaya kuma zaka yi da mahaifinka?"
Likitan yayi shiru yana mayar da numfashi, lokaci guda kuma yana nazarin fuskar Jamil. Nan da nan yaga launin fuskar ya sauya, kan tangarhon ya kwace daga hannun Jamil ya fado a tsakar dakin.
Ganin hakan ne ya baiwa Likitan ƙwarin gwiwar mikewa tsaye yana goge jinin dake zuba ta baki ta hancinsa, domin ya san yayi nasara.
"(Cool down) Jamil."
Likitan ya ci gaba da cewa cikin sauri.
"ka kwantar da hankalinka, ina da mafita, domin wannan abu da ya faru ba yau aka fara ba...wannan ita ce mace ta biyar da ta mutu a hannuna."
.
Jamil ya dubeshi cikin kaduwa.
"kai shaidan ne!!" Jamil ya ce a fusace.
"ka kwantar da Hankalinka Jamil ai shaidan ba'a daya, amma abin da nake so yanzu shi ne, ka amsa min tambaya daya, in dai har an dace to babu wanda zai san wata budurwa ta mutu a hannun mu."
Jamil ya runtse idanunsa cikin kunan rai, domin ji yake kamar dawakai ne suke sukuwa a cikin kwakwalwarsa. Dan lokaci ya bude idanunsa a daidai lokacin da likitan ya ci gaba da cewa.
"Lokacin da kuka taho nan, akwai wanda ya san cewar nan kuka taho? Ma'ana akwai wanda ya ganku tare?"
Cikin takaici Jamil ya girgiza kansa.
"ka tabbata?"
Jamil ya sake gyada kai kamar ƙadangare. Domin bai gasgata muryarsa ba balle ya ce ƙala.
"Da kyau, magana ma ai ta wuce, kwantar da hankalinka kawai, jira ni ina zuwa."
Likitan ya fice daga cikin falon gaba daya. Jamil ya bi shi da kallo, bai san inda za shi ba, to amma yana tsammanin can baya ya zagaya.
.
"....Jamil Allah Ya halicci soyayyarka a cikin zuciyata.... Jamil meye haka, kai da zaka aure ni kuma... ka hajura don Allah Jamil wallahi ban taɓa yi ba, bana so...to shi kenan in dai dole ne sai kayi, to zo gani kayi abin da kake so..."
.
Kalaman Larai suka yi ta kai kawo a cikin zuciyarsa. Yana nan zaune yana zubar da hawaye, har Likitan ya dawo. Ba ƙaramin kaduwa yayi ba sa'ar da yaga abin da Likitan ya shigo dasu riƙe a hannunsa. A riƙe a hannun likitan wata ƙatuwar diga ce ta hakar Ƙasa, da kuma shebur.
"me..me kuma zamu yi da wannan.?"
Jamil ya tambaya a rude.
"Binne gawar zamu yi a bayan gidana."
Likitan ya ce kai tsaye, kai ka ce wani mushen akuya ne za a binne.
"Kai...kai dai....shaidan ne!"
Jamil ya ce dashi cikin ƙaraji.
"kada ka haifarwa kanka hauhawar jini Jamilu, ba ita kadai za'a fara binnewa ba a gurin, kafin ita ma akwai wasu gawawwakin mata guda hudu."
.
**** **** **** *****
.
Sa'ar da suka zagaya bayan gida, abin da Jamil ya fara zazzare idanu yana kokarin gani shi ne guraban ƙabarurruka guda hudu. Amma maimakon haka bai ga wata alama ta tudun tsohon kabari ba.
Suna zuwa wurin sai likitan ya saki digar da kuma sheburin suka zube ƙasa tum! Amsa kuwwar zubewarsu ya doki kunnen Jamil da wani irin sauti mai tayar da tsigar jiki.
Inda suka tsaya farfajiyar bayan gidan, wani katon lambu ne mai fadin gaske mai kama da dan karamin daji, domin ganyayen bishiyar dabino da turare sun fi yawa a ciki, sai kuma daga can ɓangaren gidan daga arewa, jerin bishiyoyin ayaba ne da yazawa sun yi sahu-sahu, gami da karawa gurin duhu da gizo, saboda tsabar duhun dake wurin da kuma tsananin kaduwar dake tattare da Jamil, a duk lokacin da ya daga kansa sama ya dubi sahu-sahun bishiyoyin sai yaga kamar kawunan mutane ne a maƙale.
Da yawa daga bangarorin lambun cinkushe suke da ciyayi. To amma kuma sashin da suke tsaye duk yashi ne sabanin sauran sassan gidan dake zagaye da kasa mai tauri.
Likitan ya dubi Jamil gami da shafar dan sirrin wuyansa, sa'anan ya ce.
"bari in fara, idan na gaji da hakar sai ka karbe ni na dan huta."
Jamil yayi saurin girgiza kansa yace
"BANAJIN ZAN IYA TAIMAKON KA DAJamil yayi sauri ya girgiza kansa.
"Bana jin zan iya taimakonka da wani haka rami yanzu."
Cewar Jamil muryarsa a sarƙake.
"A'a ai kuwa ka san ba zata saɓu ba, ka kalle ka, ka kalle ni, ka fi ni kirar karfi, in kuma kana ganin lallai ba zaka yi hakar ba, to zan haƙa, kai sai ka dauko gawar ka binneta."
Jamil ya ce cikin fargaba kamar mai jin sanyi.
"Allah Ya tsare ni."
Likita Surajo ya dube shi yana zazzare ido.
.
"To in baka son binne gawa sai ka shirya saran kasa.
Yana gama fadin haka sai ya juya ya nufi wani yanki dake nan gabansu kadan. Likitan ya zaro cocila daga aljihunsa, 'yar siririya ce mai kamar karas, amma lokacin da ya haskata sai duk ta haske wajen. A cikin hasken cocilar ne to ya hangi katuwar kofar ta karfe kwance akan kasar ma'abociyar yashi.
Shin sauran ƙabarurrukan ma duk a nan suke ko kuwa a ciyayin can? Jamil ya fara tambayar kansa. Wata sassanyar iska ta buso cikin lambun, nan da nan lambun ya rude da sautin ganyaye da rassan bishiyun suna gogayya da juna.
Dukkan abubuwan da suke faruwa a lokacin tamkar mummunan mafarki ne ga Jamil. Babu abin da yafi tayar masa da hankali irin idan ya tuna cewa a nan inda yake akwai gawawwakin 'yanmata a binne.
"Me yiwuwa ma nan inda kake tsaye akan wani kabarin kake."
Jamil yayi tsalle gefe guda a tsorace, bayan yayi zancen zucin.
.
"Kar ka fadi ka ji rauni a banza."
Siririn likitan ya ce dashi.
"kama min nan mu dauke kofar nan, a gurbinta zamu haka ramin da zamu binne ta."
Koda Jamil ya kama masa zasu kama kofar su matsar, sai ya ji kamar ana fuzgar rigarsa ta baya. Ji yake yi kamar wani hannu ne ta cikin duhun daren ke kokarin dauke shi.
.
**** **** **** ****
.
Jamil ya jefar da digar dake a hannunsa ya mike tsaye yana duban ramin, gumi nata sartu ko ina a jikinsa kamar ruwa.
"Na...na gaji...da wannan aikin."
Ya ce yana huci kamar maciji, lokaci guda kuma yana ta murza tafin hannayensa da juna.
Likita Surajo ya dubi saurayin shekeke, ya tausaya masa kwarai da gaske, domin ko ba komai dai sabuwar amaryarsa na can tana jiransa., haka nan kuma shi kansa ya san cewar wannan saurayin bai taba yin aiki mai wahala irin wannan ba tunda yake a rayuwarsa ta duniya. Don kuwa mahaifinsa miloniya ne, sai dai kuma yayi Hakan ne domin ya cika ƙa'idarsa. Ya dade da yin alwashi duk wanda ya dokeshi sai ya rama, koda bata hanyar duka ba. Haƙa ramin da yasa saurayin yayi ne don ya rama dukan da yayi masa.
"Ai kayi kokari ma, ina ganin kuma zurfin ramin ma ya isa haka."
Likitan ya ce, yana duban Jamil a fakaice kamar ya fashe da dariya. Jamil ya matsa can baya nesa da ramin yana sharar gumi.
"Sa'a ma aka yi ai gurin akwai yashi, amma da ace tsandauri ne to da ba karamar wahala za'a sha ba."
Jamil ya dubi katuwar kofar da suka matsar gefe guda. Sannan a karo na farko tun sa'ar da ya shigo gidan, sai yayi amfani da 'yar siriyar cocilar likitan ya duba agogon hannunsa. Ƙarfe biyu daidai na dare.
".....Rukayya amarya da kawarta Badura....na can suna jiran dawowarsa."
.
"Sai mu shiga mu dauko gawar ko..? Gara muyi sauri ko ka koma gida, na san yanzu amaryarka na can gida tana zaman jiranka."
Jamil ya ji zazzafan gumi ya fara kwaranyo masa, domin babu mummunan abu da tashin hankali ayanzu irin ace da sa hannunsa wai za a binne Larai a cikin wannan uban ramin. Ya kawo yarinyar da ranta....sun kashe ta, gashi kuma zasu binne ta! Kai wannan bala'in har ina?
"Bahaka muka yi da kai ba."
Jamil ya ce bakinsa na rawa. Likitan ya dubi Jamil, ya san abin da yake tunani.
"nima ai ban ce da kai zamu binne ta ba, amma dole ne mu tafi ka rike min kofar da zan bude ta bayan falo na, domin ta nan nake son na turo gadon da take kai."
.
Mintuna goman da suka shafe suna kokarin mirgino gadon da gawar take kai zuwa bakin ramin, sune mintuna mafiya muni da tashin hankali da Jamil ya taba gani a rayuwarsa, wani lokaci da ya wuce, wata kakarshi ta taba mutuwa a asibiti, da ƙyar da maƙyarƙyata ya sa hannu aka cicciɓo gawar tata daga kan gadon asibitin sa'ar da za a kawota gida. A lokacin Jamil ya dauka wannan shi ne lokaci mafi tayar da hankali da zai gani a rayuwarshi, don kuwa sai da yayi kwana uku baya iya barci. Da ya runtse idanunsa sai ya ganshi yana cicciɓar gawa. To sai gashi kuma yau wai har dashi za'a binne gawar da yayi sanadiyyar mutuwarta.
Mutanen biyu suka yi cirko-ciko a gaban ramin suna mayar da numfashi. Jamil bai iya sa idanunsa ya kalli kan gadon da Larai ke kwance ba. Waye zai ce wai wannan Larai ce, wacce 'yan sa'o'i kadan da suka wuce take zaune a cikin motarsa kusa dashi tana numfashi? Tana motsi da numfashi tana murmushi.
"Wajen kan zaka kama min, ko kuwa wajen kafar?, zaɓi inda kake son kamawa mu sanyata a cikin ramin, in yaso sai ka tafi bayan bishiyar can ka jira ni na karasa binnewa."
"Ai bamu yi haka da kai ba..."
Jamil ya ce cikin kaduwa.
"Ni..ba zan iya..taba ta ba.."
"Haba Jamil yaya kake tsammanin ni kadai zan iya kinkimar wannan gawar?"
Jamil yayi sororo baki bude, cikin tsananin rudewa. Gumin dake zuba a jikinsa ya kusan karewa, don haka sai kadan-kadan yake tsattsafowa a goshinsa.
"kama mana Jamil, ko mayi mu gama, ni fa na fara gajiya da zama da gawa."
Jamil ya kintaci inda yake tsammanin a daidai nan kafar Larai take ya kama, shi kuma likitan ya kama wajen kan, suka ciccibi gawar a hankali suka saka ta a cikin ramin. Hannun Jamil sai karkarwa yake yi kamar wanda ya taba wutar lantarki. Cikinshi sai juyawa yake yi kamar zai yi amai.
"tafi bayan bishiyar can ka jira ni kafin in gama rufe ramin, in kuma kana iyawa karbi fitilar ka rika haska min ramin kona iya gamawa da wuri."
Da farko Jamil yaso yayi na'am da tayin da aka yi masa na komawa gefe guda, to amma sa'ar da ya tuna cewar, akwai sauran kabarurruka har guda hudu a ɓoɓɓoye a cikin lambun, sai tunanin hakan ya fice daga zuciyarsa, domin bai san a inda tsofaffin kabarirrikan suke ba. Me yiwuwa ma inda likitan ya nuna masa ya je ana kabarirrikan suke. Gara in yi zamana a nan. Jamil ya ce a zuciyarsa, a kalla dai zama da kabari daya ya fi zama da hudu.
"A'a au tsayawar zaka yi kenan?"
Likitan ya ce cikin mamaki sa'ar da Jamilu ya mika masa hannu domin ya bashi siririyar cocilar da zai haska masa ramin.
Mintuna goma ya share kafin ya gama rufe ramin, tsawon mintuna goman tamkar tsayin shekara ne a wajen Jamil, sa'ar da Likitan ya fara kwasar qasar yana watsawa a cikin ramin, Jamil ji yake tamkar a jikinsa Likitan ke watsawa, don haka sa'ar da likitan yayi ajiyar zuciya ya jefar da sheburin gefe guda, sai Jamil ya ce dashi cikin maƙaƙƙiyar murya.
"Shi ke...nan...?"
Likitan ya dube shi cikin duhun dare ya ce.
"aiki daya kawai ya rage."
Fuskar Jamil ta yamutse a cikin fargaba da tashin hankali.
"kada ka tashi hankalinka, ba tono gawar zamu yi ba, wannan katuwar qofar zaka kama min mu mayar da ita gurinta."
Jamil ya kama masa kofar suka mayar da ita, sai gashi ta rufe iya gurin binnannen ramin. Duk da Jamil a rude yake sa'ar da yaga haka sai da ya yaba da tunanin siririn Likitan, domin kofar ta batar da duk wata alama ta kabarin, babu wanda zai ga wurin yayi zaton an binne koda kaza ce ballantana mutum.
"Shi kenan, kamar ma ba ayi ba, sai iyayenta su nemi inda take. Likitan ya ce yana goge hannayensa a jikin wandonsa.
"sai ka koma ga amaryarka..."
Kafin ma ya gama maganar tuni har Jamil ya juya a sanyaye zai fice daga lambun.
.
"Jamil!"
Likitan ya kira sunansa da wata irin busasshiyar murya. Jamil ya juyo cikin mamaki.
"Yaya maganar kudin aikina kuma?"
Jamil ya ji kamar Likitan ya watsa masa wuta a zuciya, saboda bakin cikin jin maganar. Jamil ya zura hannunsa a aljihu ya nufo inda likitan yake, sai da yazo daf dashi ya tsaya a gabansa yana kallonsa.
"nawa ne kudinka?"
Jamil ya tambayeshi, idanun likitan suka zazzaro waje kamar zasu fado kasa saboda tsabar hadama.
"Dubu biyar zaka bayar, tunda aikin bai yi kyau ba"Dubu biyar zaka bayar, tunda ba a samu sa'ar aikin ba."
Jamil ya dunkule yatsunsa biyar, ya dubi 'yar karamar fuskar Likitan mai kamar kashin zogale ya kirba masa naushi tim! Iya karfinsa, har sai da ƙwanjjinsa ya girgiza.
.
"Ah!!...."
Likitan ya fadi kasa wanwar jni na tsartuwa ta baki ta hanci, feshin farko na jini daga bakinsa ya feso da haqoransa guda uku.
"In kuma wannan dubu biyar din basu ishe ka ba in karama."
Jamil ya ce a fusace, sannan sai ya juya cikin sauri kafafunsa na ta rawa ya nufi inda motarsa take, ya bar likitan kwance kusa da kabarin yana murkususu.
.
**** **** ****
.
Ƙarfe uku dai-dai ya isa babban falon gidansa, Jamil ya lura da kalllon da mai gadinsa yayi masa sa'ar da ya bude masa qofa, kallon damuwa ne, don tunda yake bai taba ganin yazo gida a makare haka ba. Duk da yake dai yana kaiwa dare, to amma mafi yawan dadewarsa shi ne ya kai karfe daya na dare. Jamil bai damu da kallon Maigadin ba, abin da yafi damunsa shi ne halin da zai samu sabuwar amaryarsa da kawarta Badura.
Ya kwankwasa kofar cikin natsuwa, sa'anan Jamil ya shiga dakin. Bai yi mamaki ba sa'ar da yaga duk tsawon lokacin nan 'yan matan biyu basu yi barci ba, amaryarsa Rukayya da kawarta Badura na nan zaune sun hada kai da gwiwa. Badura na ganinsa sai ta mike tsaye zumbur gami da ajiyar zuciya.
"Ja..mil...ka barmu cikin damuwa....ya ya jikin na Mama?"
Jamil ya dauke kansa gefe guda, domin ba zai iya hada idanu dasu a lokacin da zai shirga masu karya ba.
"Jikin da sauqi...dogon suma tayi, shi yasa na dade.... naso na bugo waya ma, to amma duk rashin lafiyar ta Mama ta rudani...."
Jamil yayi shiru yana duban amaryarsa Rukayya wacce ke zaune cikin ado tana sheki, sai dai kuma akwai alamar gajiya da barci a idanunta. Rukayya ta dubi Jamil ta jefe shi da murmushi cikin damuwa.
"Yaya mai jikin?"
Ta ce dashi a kunyace. Jamil ya dubeta cikin jin dadi, duk kuwa da cewar har yanzu ji yake yi kamar an tono shi daga kabari.
"Darling... na barki ko...ki yi hakuri...wal... wal..."
"Haba Jamil, ai rashin lafiyar uwa yafi karfin wasa."
Rukayya ta katse shi ta na murmushi.
Ina ganin ni zan tafi."
Badura ta katse su ta ce ita ma cikin murmushi.
"Ki tafi ina?"
Jamil ya tambayeta cikin mamaki.
"Gida mana, dan makullin motarka zaka bani gobe na dawo maka da ita da safe."
Jamil ya girgiza kai.
"Ƙarfe ukun dare zan barki ki tafi gida? Ba zai yiwu ba, zo dai mu tafi in kai ki dakin da zaki kwana, akwai duk abin da ki ke bukata."
Badura tayi ajiyar zuciya. Ta ce.
"To shi kenan."
Lokacin da Jamil ya dawo falon, amaryarsa Rukayya ta tashi daga kan kilishin tsakar dakin, ta koma kan daya daga cikin kujerun dake dakin.
"Amarsu... ta ango."
Jamil ya ce. Rukayya tayi murmushi tana kada masa idanu.
"barci ki ke ji Rukayya, zo mu tafi daki."
.
Dakin amarya ya gama shan ado da ƙyale ƙyale na zaman duniya, ga qamshi sai tashi yake yi iri daban-daban, shi kansa Jamil bai taba jin irin qamshin turaren da aka fesa a dakin amaryar ba. To amma fa duk da wannan kamshin, tunanin al'amuran da suka faru a daren ya shuka wani irin bala'i da tashin hankali a zuciyarsa, domin daga yanzu har zuwa mutuwarsa in har an kira mai suna Larai, sai gabansa ya fadi. Kai ko sunan mace ne mai kama da Larai, Jamil ya san cewar ko barci yake yi ba zai daina tunani da ganin siffar gawar Larai ba.
.
Suka zauna akan fankadeden gadon dake a dakin, Rukayya ta dubi Jamil cikin kunya ta ce.
"Jamil... kayi hakuri... wannan daren amarcin namu yazo ba a dai-dai ba."
Jamil ya dubi amaryarsa, lokaci guda kuma ya dubi jerin kananun fitilun alfarmar da aka yiwa bangon dakin ado dasu, suka haske dakin kamar rana..
Jamil ya tallabi kan amaryarsa ya matso da ita kirjinsa, yana kokarin mantawa da al'amarin da ya shafi mutuwar Larai. Lokaci guda kuma yana mai addu'ar Allah Ya sa lokacin da ya dauki Larai babu wanda ya ganshi. Haka nan kuma Allah Ya sa katon ramin dake a bayan gidan Likita Surajo yayi ta zamansa a rufe har abada.."
A da-dai lokacin da ya sake matsowa da amaryarsa kusa da kirjinsa domin fara wasan amarci, sai ya ji jikinta ya sandare, numfashinta ya dauke a lokaci daya cikin firgici.
"Ah! meye wannan?"
Jamil yayi sauri ya dan dubi jikinta yana duban fuskarta cikin mamaki, akwai alamar tsoro karara a fuskarta.
"Me...mene...ne?"
Rukayya ta daga kyakkyawa siririn yatsanta ta nuna fankacecen kirjinsa dashi.
Sannan ta ce da angonta Jamilu muryarta na rawa. "WANNAN JININ MENENE A JIKIN RIGAR KA..?"
.
RANA
25-2-1991
KASHI NA BIYAR 5
.
Amina ta tasa abinci a gabanta tayi zuru kamar mutum-mutumi. Wani sa'in in har ba kula kayi da kwayar idanu da girar idonta ba, sai ka rantse da Allah akan ko motsi bata yi.
Wannan mata ta dade tana wannan al'ada ta zama, sai ta shigo daki ita kadai tayi fakare tana tunani. A duk sa'ar da tunanin yayi tsanani sai ka ga hawaye yana kwaranya akan fuskarta kamar ruwa. Matar ta motse ta rame babu alamar walwala a tare da ita, domin rabonta da ace ta samu ta ci abinci tun kafin ɓacewar 'yarta LARAI.
Malam Audu ya shigo dakin a hankali dauke da baƙar jaka ta fata a hannunsa, wacce a duk lokacin da zai fita wurin aiki da ita yake fita.
Malam Audu dogo ne baki kakkaura mai faffadar fuska da gemu, ance wai idan ransa ya baci bakinsa har kumfa yake yi kamar ya ci sabulu, idanunsa su kada suyi jazur kamar gauta. Idan yana fada babu wanda ke bashi baki ya hakura sai matarsa Amina.
Malam Audu tsohon kwamishinan 'yansanda ne, wanda yayi ritaya tun kusan shekaru biyar da suka wuce saboda girma ya fara kama shi. A halin da ake ciki a yanzu ma'aikaci ne a wani kamfanin Inshora, domin sa'ar da yayi ritaya yaso ya zauna ya huta, to amma sai yaga ba zai iya jure zaman gida ba, kullum a zaune, ka ci kayi kashi kamar fara, babu amfanin komi, wannan shi yasa ya nemi aiki a kamfanin Inshora. Mai bincike ne na musamman akan al'amuran shiga da fita na kudi da kan je su komo a kamfanin.
Matarsa Amina ta dago kai ta dube shi sa'ar da yake shigowa cikin dakin. Har yanzu hawaye ke kwaranya akan fuskarta.
"Haba Amina, don me zaki ƙuntatawa rayuwarki akan abin da Allah Ya riga Ya kaddara?"
Lokaci guda kuma sai ya dubi abincin dake gabanta, yadda ya barshi dazu, yanzu ma haka yake ko taba shi bata yi ba.
"Amina ai ko abincin ma ba ki ci ba."
Malam Audu ya ce cikin kaduwa yana duban ramammiyar fuskarta.
"Ba ki kyauta ba wallahi...yanzu ace mutum musulmi bai iya sallamawa Ubangiji duk abin da ya same shi? Sai ki zauna ki ƙi ci ki ƙi sha ki yi ta kuka har tsawon shekara guda?"
Yayi shiru yana mai da numfashi da ƙyar.
Amina ta dube shi hawaye na zuba ta ce.
"Wallahi na kasa...jurewa ne....tun bayan batan Larai hankalina ya fita jiki na, yanzu duba ka gani, yaran nan dama can su biyu muke dasu a duniya... kuma sai a dauke min Larai.... a dole in yi kuka! Dole nayi kuka!!"
Ta sake fashewa da kuka.
"Amina ai duk irin son da ki ke yi mata sai ki dauki ƙaddara tunda dai kin san kukanki ba zai dawo mana da Larai ba, kin ga dai Larai diya ta ce, babu wani jami'in tsaro mai fada a ji a garin nan da bai san batan Larai ba, suna nan suna iya kokarin su. Hatta Kwamishinan 'yan sanda Gagarabadau ma da ya hau kujerata ya san labarin, kuma suna iya kokari... kin ga kuwa in dai haka ne ai sai kawai mu ci gaba da addu'a."
Amina ta share hawaye da gefen mayafin dake kanta. Ganin haka sai mai gidanta Audu ya durkusa a gabanta, sannan ya dubi jerin sahu-sahun kujerun da suke dakin ya ce da ita a tausashe.
"Tashi ki koma kan kujera ki samu ki dan sa wannan a cikinki....dubi duk yadda ki ka rame Amina ta. Daure ki kwantar da hankalinki don Allah.. kada bacin ran ya zame min biyu, ga naki ga kuma na batan diyata Larai."
Ya yi shiru yana duban fuskar Amina. Ga mamakinsa sai ta mike tsaye ta koma kan kujerar ta zauna, sannan ta ce cikin karyayyiyar murya.
"don Allah baban Larai ka takurawa...mutanen nan naku...ko sa samo min Larai dita. Yau shekara guda fa kenan, babu Larai babu labarinta."
Ta yi shiru lokaci guda tana shirin fara ci gaba da kuka.
Malam Audu ya gyara rikon bakar jakar dake rike har yanzu a hannunsa, sa'anan ya matsa daf da matarsa Amina ya ce.
"kwantar da hankalinki....babu wanda ya isa ya batar da diyar tsohon kwamishinan 'yan sanda ya kwana lafiya! In dai tana raye sai mun gano Larai."
.
**** **** **** ****
.
"Wayyo Allah! Na shiga uku."
Jamilu ya sa ihu a tsorace sa'ar da ya ji kamar an taba shi ta baya. Shi kadai ne a cikin dokar daji, ga dajin bakikirin kamar kabari, babu alamar hasken farin wata ballantana taurari, domin hadarin firgita birni ya turniƙe sararin samaniyar ruf.!
Duk inda ya juya sai ya ji kamar ana biye dashi ne, amma da ya juya sai ya ga babu kowa babu alamar mutum, da farko ya dauka abin wasa ne, to amma sa'ar da ya kara yin gaba kadan cikin bakin dajin, sai ya ji an sake taba shi a baya, a wannan karon abin da gaske ne, domin ya ji hannun da ya dafa bayanshi har da dan danshi-danshi. Wannan abin shi yasa Jamilu kara ihu a firgice, ya juyo a firgice, amma maimakon yayi ido biyu da mutum sai ya yi ido biyu da manya-manyan..Da farko ya dauka abin wasa ne, to amma sa'ar da ya sake yin gaba kadan a cikin bakin dajin, sai ya ji an sake taba shi a baya, a wannan karon kuma har da dan damshi-damshi, wannan dalilin shi ya sa Jamilu ya kwalla ihu a firgice, ya juyo a firgice, amma maimakon yaga mutum sai ya yi ido biyu da manya-manyan bishiyoyin dake tsaye sun yi sahu-sahu a cikin dajin, kamar jerin sojoji a ranar bikin faretin murnar samun 'yanci.
Wannan abu shi ya

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment