Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ALAKAKAI
Nazir Adam Salih
Made by Shuraih Usman
Daga http://fb.com/hausaebooks

ALAKAKAI-01
.
DAYA 1
Wata ranar lahadi aka tashi da gagarumin hadari wanda
yakan firgita birrai. Kodayake a safiyar ranar ba'a tashi da
alamun hadarin ba. Sararin samaniyar tarwai yake babu
alamar gajimare ko kankani wannan shi ya baiwa rana
lasisin ci gaba da dumama rufin gidaje da kayuwan bani
adama tun daga karfe goma na safiyar har zuwa karfe
daya na ranar. Abin bai zowa mutane a bazata ba
musamman ma wadanda suka sha miya da yawa domin
sun dade da yin amannar cewa duk sa'ar da zafi ya

tsananta alokacin damuna to hadari ne ke son haduwa.
Haka kuwa akayi babu zato ba tsammani sai hadarin ya
fara haduwa sahu sahu sannu ahankali har ya dakushe
hasken ranar ba'a dade ba sai iska gamida feshin
tsattsafar ruwa nan da nan jama'a suka fara tserere akan
tituna domin su sami gurin fakewa acikinsu harda Ni
wanda rabona da ofishina tun karfe tara na safe da wani
mutum yazo karbar bashinsa na gudu.
.
Wannan bashine karo na farko ba dana fara tserewa
masu bina bashi kusan watanni tara kenan da harkar fim
ta juya min baya tun fitowar fim dina na DAREN
MUTUWA shikenan sai mutane suka dau karan tsana suka
dora min.
Iskar hadarin ta fara tsananta dan haka sai nayi sallama
da mai shagon dinkin da nake boye aciki tun safe nace
dashi.
ISYAKU zan koma ofishina. Isyaku tela ya dubeni cikin
damuwa daman yasan irin matsanancin halin danake ciki
Gara ka tafi gida Hilal domin komawarka ofis ayanzu
ganganci ne... Na dubeshi gamida murmushin yake
kada ka damu isyaku leka waje ka gani hadari ne bakikirin
ga iska.. Nasan dai mutum yanzu in ba maye bane dole
ne ai yabar ofishin..... Kuma bugu da karawa ma dole ne
na koma ofishin domin na sallami sakatariyata LAURIYYA
dan nasan ko kudin mota bata dashi...... Abincin rana ma
bansan yadda zatayi ba.. Isyaku ya dubeni cikin mamaki.
Kana nufin haryanzu Lauriyya tana tare dakai? Na gyada
masa kai kwarai kuwa ai tattaraba ce uwar alkawari ita
kadai ta rage a yarana duk sun barni sai ita kadai... Isyaku
ya dan yi murmushi yana dubana.
Itama akwai dalili.. Na dube shi cikin mamaki
dalili... Kamar yaya ban fahimce ka ba isyaku yayi
atishawa sannan yace
Haba Hilal har sau nawa kake so in maimaita ma cewa
Lauriyya sonka take.
Nayi saurin girgiza kai
A'a bari bari isyaku kada kayi min mummunan fahimta
na yarda ni dan fim ne amma zakayi mamaki idan nace
dakai tunda nake ban taba soyayya ba da wata yar fim.
.
Kakkarfar iskar hadarin dake ta hankoron dauke rufin
dakunan masu rangwamen gata ta bugo kofar shagon
telan da karfin gaske
Isyaku yasa kafa ya tokareta.
Baka fahimce ni ba Hilal ko kuma ince kasan gaskiya ka ke
takewa ai ko makaho ya laluba yasan lauriyya tana
mutuwar sonka.
.
******* ********* ************
.
Lokacin dana baro shagon telolin saina tsallaka titi na nufi

ofishina cikin sauri da kyar nake ganin gabana saboda
kakkafar iskar ma'abociyar kara dake ta bulbule min
idanu.
Kura ta turnuke ko ina haka nan garin yayi jajur duhu ya
lullube ko ina kai kace karfe shida da rabi na yamma tayi
duk kuwa da cewa karfe daya ne na rana.
Cikin sauri na nufi ofishin inata waige waige domin
haryanzu jikina na bani cewa akwai sauran masu bina
bashi cikin ofishin suna jirana.
Tun kafin na karasa ofishin na fara hange hange da rabe
rabe sannu ahankali har na isa kofar ofishin wacce ke
rufe tana duban bakin titi.
Nayi tsaye a kofar ofishin kusan minti guda nayi kasake
kamar barawo ina saurare ko zan ji surutai ko hayaniya
shiru banji komai ba na dan dada matsawa kadan na kara
kunnuwana ajikin katuwar kofar nayi ajiyar zuciya
sannan sainayi shahada na daga hannuna zan tura kofar
kenan sai kawai naga an bude daga ciki.
Sannu da zuwa hilal yi maka ka shigo daga ciki yanzu
yanzun nan EMEKA yatafi tun sha daya yaketa jiranka
nace dashi katafi kaduna... Amma yaki yadda
Kirjina na dakan uku uku cikin sauri na shige ofishin.
Lauriyya ta mayar da kofar ofishin cikin gaggawa ta rufe
sannan saita jingina bayanta ajikin kofar ta kura min
idanu bata ko kiftawa.
Na nufi cikin ofishin ahankali hannayena cikin aljihunan
wandona zuciyata na kuna nayi kokarin nazarin ofishin
amma saboda duhun hadarin bana iya ganin komai cikin
ofishin.
Lauriyya ta fahimci haka cikin sauri ta nufi makunnar
lantarki ta kunna nan da nan dakin ya gauraye da haske.
Lauriyya tayi tsaye jikin makunnar lantarkin tana kallona
ina kallonta.
Akwai alamar tausayi karara a fuskarta banda wannan
kuma naso na hangi kwalla acikin kwayar idanunta. Cikin
sauri na dauke kaina gefe guda sannan nafara nazarin
ofishin..... Da a da dan wani lokaci can daya shude babu
wani ofishin darakta na fim daya kai koda rabinsa a
tsaruwa amma koda na tsaya ayanzu ina nazarin ofishin
sainaji kamar na fashe masa da kuka lallai ruwa ya daki
babban zakara.
Saidai hakuri Hilal haka duniya take rawar yan mata
lauriyya ce ke magana abayana cikin wata rarraunar
murya. Naji abinda ta fada to saidai kuma ban iya juyowa
na kalleta ba ballantana ma na tanka mata.
.
Zuciyata da tunanina suka koma baya kadan wani dan
shudaddan zamani.... Sa'ar danake tauraron jarumai na
wasan fina finan hausa.
Na rufe fuskata da tafukan hannuna sannan nafara
tunanin sa'ar dana shigo harkar fim da kafar dama cikin
watanni ukun farko da shigata harkar na fito cikin fina

finai sama da shirin wadanda duk nine jarumi acikinsu
sannu ahankali sai sunana yayi tambari duk inda ka
zagaya babu sunan wanda ake fade sai HILAL.
Duk inda na zagaya yara da manya basa barina na huta
sun yita bina kenan abaya kungiya-kungiya kamar uban
garke idan naje sayayya kasuwa ba'a karbar kudina haka
nan da zarar an kyalla ido na ganni saikaga anata rububin
ganina kowa na gayyata dana zo nayi siyayya ta a
rumfarsa duk kuwa da cewa ba kudina zasu karba ba.
Na mallaki abubuwa da dama a shekarata ta farko da
shiga harkar fim wanda adacan wani lokaci ban taba
mafarkin mallakarsa ba akwana kusa motoci uku na
hawa kayan sawa na kwalisa sama da kala dari uku da
goma sha takwas agogunan sarka ashirin na fata goma
takalma sittin safa kuwa da singileti duk wacce nasa sau
uku bana kara amfani da ita sai wata sabuwar.
Sannu ahankali samari suka fara kwaikwayon yadda nake
direshin duk abinda nayi koda sakarci ne sai ya burgesu
saikaga sun zamo masu kwaikwayona.
.
Ashekarar ne na bude katon ofishina wanda aka kawata
shi da kyale kyale gami da manya manyan kujeru masu
numfashi da taushi kamar ada da sau da yawa idan muka
sauki baki indai har zasu shafe mintuna goma suna zaune
sai an sami wanda ya bingire da barci saboda dadi.
Duniya ta dawo min sabuwa ina da yara dake aiki
akarkashina sama da mutum ashirin suna kuma jin
maganata fiye data iyayen da suka haifesu wasu suna
bina sau da kafa ne wai don kawai suna so na sa su
kokuma nayi musu hanya su shiga shirin fim yayinda
wasu kuma suke yi min biyayya don kawai kaunata da
sukeyi. Nazama kamar sarki acikin fadawa duk abinda
nake so shi za'ayi batareda bata lokaci ba. Da ace yarana
awannan lokacin suna da iko da fitsari da numfashi ma
su zasuyi min.
Muna nan ahaka har shekaru biyu suka shude
Kwatsam ran nan sai duniyar data dagani sama ina
shanawa tafara yin kasa kasa dani sannu ahankali ta
damfara ni da kasa.
Abin yafara ne a yammacin wata ranar lahadi sa'ar
danake karbar kudaden sabon fim dina RAGAS daya fito.
Shagon farko danaje sai akace dani wai fim din baya
tafiya nayi mamaki domin tunda kamfanina yake fim ba'a
taba samun wanda bai shiga ba.
Me ya faru da fim din? Na tambayai wani dillalin kasa
kasan fim din.
Eh to kasan dai mutane yadda suke ba'a iya musu inajin
dai gajiya sukayi dakai.... Kuma sunata korafi akan cewa
wa fina finanka na kwanan babu labari mai kyau.
Tun daga ranar ne al'amura suka dagule min abin kamar
sa hannu komai na taba sai ya lalace gashi dai nagama
kashewa fim din Ragas kudi... Na ranto kudin jama'a duk

na lafta saboda a tunanina zaiyi bala'in karbuwa saigashi
cikin ikon Ubangiji saidata kawo ko kashi daya bisa goma
na kudin fim din basu komo ba.
Rayuwata tsananta kaina ya dauki zafi rikici goma da
ashirin ga tarin bashi fal akaina gashi kuma ya
furodusoshin ma da suke daukana na fito musu a
matsayin jarumi duk sun gujeni ba'a dade ba duk yarana
suka watse suka barni daga ni sai yar amana LAURIYYA.
.
Koda na daga fuskata sa'ar danake tunanin na dubeta
saina tuno da kalamanta saa'ar da gari yayi mana zafi
bazan taba mantawa da ranar ba. Ranar wata laraba da
yamma bayan sama da mutane goma sun zo tambayata
bashin su.
Hilal.. Ina da shawara in zaka yarda. Lauriyya tace dani na
dago kai na dubeta.
Fadi shawararki lauriyya...indai mai amsuwace ai na
dauka.. Tunda dai ko banza dai ke kadai kika rafe atare
dani.. Wallahi lauriyya ayanzu kin wuce sakatariya
agurina saidai ko in Yar Uwa.
Lauriyya ta dan matso daf dani duk da yake duk ranmu
abace yake to amma na lura da alamun jin dadin abinda
nace karara a fuskarta na sani ba tun lokacin ba har zuwa
yanzu Lauriyya sona takeyi to amma ta rasa yadda zata
fito ta fada min.
Hilal... Ni ina ganin a shawara da ace kullum mutane
suyita binka suna tambayarka bashi... Suna muzanta ka
kamar barawo gara in kana ganin babu damuwa ka daga
dan kadarorin daka mallaka kasa su akasuwa in yaso
saika biya mutane bashin su... Ko banza dai ina ganin ai
tsira da mutunci yafi tsira da kudi. Hakan data fada saina
fahimci tabbas ta fadi gaskiya ba'afi sati daya da bada
shawarar ba na sayar da motocina guda uku gidana kai
da duk wani abu danake ganin zai iya kawo min wasu
dunkulallun kudi saida na sayar dasu.
Acikin makonne na biya jama'a da dama basussukansu ni
kuma nakoma gidan yayana inda daman tun farko acan
nake kafin na samu abin duniya
UNGULU TA KOMA GIDANTA NA TSAMIYA
.
To saidai kuma abin bakin ciki duk da kadarorina dana
sayar basu isa biyan bashin da ake bina ba.
Gashi kuma haryanzu babu wani labari daga gurin masu
shirya fina finai wadanda ada suke ta bina agindi agindi
suna rokona danazo na fito musu a fim yanzu da sun
hangoni sai su fara buya domin duk labari ya ishesu
acikin kankanin lokaci kamar wutar daji cewa wai
kasuwar fim ta daina yi dani......... Wannan duk wani
Abune daya shude Abaya.
.
ALAKAKAI 02

.
Wannan duk wani abune daya shude abaya
.
Hilal aka kira sunana abaya na juya firgigit Lauriyya ce
har yanzu tsaye ajikin makunnar lantarkin tana kallona
idanunta sunyi rau-rau kamar zata fashe da kuka.
Tunanin me kakeyi Hilal? Ta tambayeni bakinta na rawa
na juyo ahankali hannayenta harde da juna makale
abayanta.
Kikace Emaka yazo nemana? Lauriyya ta gyada min kai
bata yadda ta bude bakinta ba ina tsammanin da tayi
magana alokacin fashewa zatayi da kuka.
Sauran cikon kudin kwalin kaset din daya buga mana
yazo karba nace da ita batareda na iya hada ido da ita ba.
Ban da shima su shafi'i sunzo wai karbar kudin kayan
kwastum... Haladu da sabo da ma duk sunzo maganar
cikon kudinsu...
Tsahon lokaci babu wanda ya sake cewa kala nida ita can
bayan wasu yan dakiku sai lauriyya ta matso daf da inda
nake tsaye inata faman karatun wasikar jaki
ta dafa kafadata tace dani.
Juyo ka dubeni hilal... Ina da shawarar da nake
tsammanin me yiwuwa ta zama mafita agareka. Adaidai
lokacin aka saki wata katuwar aradu data girgiza ofishin
sannan wata walkiya mai tsananin haske ta harko cikin
ofishin duk kuwa da kwan lantar dake ci.
.
***** ******* ****** ****** ***
.
Na zurawa lauriyya idanu ina kallonta sannan kamar wani
sahorami domin bansan me zance da ita ba ganin bance
da ita komai ba sai ta dafa kafada na sannan ta sunkuyo
da kanta tace dani.
Ka gafarce ni hilal ba wani abu ne yasa nake tare dakai ba
haryanzu sai don...... Ta kasa karasawa tausayinta
yakamani haryanzu iska ake ta ketawa awaje saikuma
sautin yan kananan kwayoyin ruwan da iska ke ta alakoro
dasu akan rufin gidaje kafin isashshen ruwan ya karaso.
Cigaba lauriyya.... Ke nake sauraro nace da ita a sanyaye
lauriyya tayi dan jim na yan dakiku kana saitace cikin
karyayyyiyar murya.
Kau.....narka ce ta rike ni har zuwa wannan lokaci ina tare
dakai.... Duk abinda ya same ka kamar ni ya shafa ne
domin lokacin danazo garin nan kai ka karbeni ka
mutuntani ka maida ni mutum.
Banida cewa akan abinda tace dan haka sai nayi shiru ina
sauraron abinda zataci gaba da cewa.
Hilal.....abinda nake kokarin baka shawara akai shine me
zai hana muje kamfanin fina finan su ALHAJIJI me
yiwuwa...... Bata karasa ba sakamakon sauyin yanayin
data gani karara a fuskarta.
Haba lauriyya wace irin magana kikeyi ina ni ina wani

Alhajiji kuma? Lauriyya ta dada matsowa gareni kamar
zata kankameni.
Hilal ka saurari abinda nake son fada ma dan Allah nsan
dole bazakaji dadi ba domin zan saka yin abinda baka so
ba. Ta dan saurara.
Duk acikin yan shirin fim shi kadai ne nasan baya bakin
ciki dakai.... Shiyasa tun jiya nake tunanin me zai hana
muje mu gani ko zai samo ma wani fim din ajefaka aciki
koda a mataimakin jarumi ne saikaga kadan samu wani
abu ka rage bashin dake kanka. Tayi shiru tana dubana.
Nayi dim na yan dakiku ina jujjuya kalamanta acikin
zuciyata.
Lauriyya abinda nake so ki lura dashi shine mutumin nan
fa babu irin nacin da baiyi min ba sa'ar da nake kan
ganiyar tashe na akan nazo nayi masa jarumi a
finafinansa amma naki... Ke din nan da kanki sau nawa
yana bugo waya ina cewa kice dashi bana nan....?
Duk da haka dai hilal..... Haka nan zaka daure muje ai
durkusawa wada ba gajiyawa bane ni nasan ba zai
wulakanta ka ba tunda dai koda ada din ma ai ba fitowa
kayi kiri kiri kace dashi bazakayi masa fim din ba. Na
girgiza kai sa'ar danaji tayi shiru.
Lauriyya ban ki shawarar ki ba amma abinda kamar wuya
wai gurguwa da auren nesa ina ta faman nuna miki
Annabi kina runtse idanu abinda nake so ki gane shine
tuni labari ya watsu aduk fadin duniyar fina finan hausa
cewa kamfaninmu ya fadi bama wani tasiri akasuwar fim
shiyasa kikaga fa kowa ya gujeni an daina rububin sa ni a
fim domin ana ganin nazama asara.
To in dai kuwa hakane wacce irin hauka ce ta hau kan
alhajiji da kike tsammanin zai sani cikin fim dinsa in
janyo masa asara sa'ar danayi shiru saina lura tuni
hawaye ya fara sartu akan kumatun lauriyya.
.
Daina cewa zaka janyo masa asara Hilal....abin da nake so
ka gane shine ba kaine ka daina tashe ba kamfaninmu ne
ya karye ya daina tashe amma ni nasan ita duk duniyar
nan basu yarda ba ni nayi imani da cewa kana nan akan
HILAL dinka jarumin jarumai.
Kukanta yafara bayyana a fili.
Nayi sauri na rike hannayenta nace da ita a sanyaye.
Daina kuka lauriyya shikenan na yarda zamuje to amma
kuma wani hanzari ba gudu ba.
Lauriyya ta dago kai tana share hawaye cikin rashin
fahimta.
Yanzu idan mukaje bamu dace ba kinsan fa labari zai
watsu aduniyar fina finan hausa cewa tsohon jarumin
jarumai yafara tallan kansa..... Wacce illa kike tsammanin
hakan zata janyowa durkusashshen kamfaninmu?
Lauriyya ta bata fuska tace.
Hilal so dai kakeyi saika bata min rai ko? Da dai bana son
na fada amma yanzu ka takura ni saina fada? Na dubeta

cikin mamaki me zaki fada? Lauriyya ta harareni gamida
murmushin yake tace.
Alhajiji yana mutuwar kaunata nice dai ban bashi hadin
kai ba. Ni nasan ko yana so ko baya so dolene idan nayi
masa magana yasaka acikin sabon fim din zaiyi.
Tana gama fadin hakan saita kama hannuna ta fara jana
kamar wani karamin yaro.
Zo mu tafi dan Allah kada afara ruwa. Nabita abaya sumi
sumi kamar tunkiya muka shiga cikin iskar damina.
Jarumin jarumai Na kira kaina da kaina sannan sai na saki
daddadan murmushi. Lauriyya ta lura
Murmushin me kake? Na girgiza kaina nace babu
komai.... Kece kawai kika burgeni,
.
****** ********* *************
.
Sa'ar da muka isa kamfanin fina finai na alhajiji sainaga
toge abaya abjikin wani kantin kayan karau nace da
lauriyya
Jeki kuyi magana dashi ni bazan karasa ba... Lauriyya ta
dubeni zatace wani abu saikuma ta fasa me yiwuwa itama
ta lura da taron yan alabaku mu samun fim dake tare
birjik akofar kamfanin duk kuwa da uwar iskar da ake
ketawa. Lauriyya ta rike hannuna tace.
Toh shikenan hilal jirani anan naje na dawo ta lura da
fuskata haryanzu a murtuke take cikin damuwa.
Kada ka damu hilal komai zai zama daidai in Allah ya
yarda.
Kaidai ka jirani. Tana gama fadin hakan saita matsa
hannuna sannan ta jefeni da wani boyayyen murmushi
mai kunshe da dubban manufofi ta juya tana rausaya ta
nufi cikin kamfanin.
.
Na duba agogona bayana na jingine da itacen wayar
lantarki dake daf da kantin na cika da mamaki sa'ar
danaga tuni har mintuna goma sha uku sun shude da
shigar lauriyya cikin kamfanin. Adaidai lokacin da
damuwata ta fara tsananta saina hangi lauriyya ta fito
alhajiji kuma yana biye da ita cikin fara'a akwai alamun
farin ciki karara a fuskarsa me ywuwa na murnar zanyiwa
kamfaninsa fim ne. Sa'ar da kuma na tuna da cewa nifa
ayanzu ta kare min sai nafara tunanin to me yiwuwa
ganin lauriyya ta nemi alfarma agurinsa ne yasashi
murna.
Ina nan tsaye har suka iso gareni.
Yallabai! Yallabai!! Alhajiji yace dani cikin wata murya mai
sautin amon alburushi sannan ya cafki hannuna kamar
zai tsaga minsu saboda riko. Alhajiji kato ne baki mai
katon ciki da dogon gemu babu gashin baki fuskarsa
cikakkiya ce a mulmule kamar kwallon kafa duk sa'ar da
yayi dariya saikaga ya zama tamkar mutum mutumi
wannan ce tasa dayawa daga cikin shakiyan jaruman fina

finan hausa suke so suga yayi dariya dan kawai su sha
dariya. Wata shekara an taba fitowa dashi cikin wani
shirin fim na abin dariya amatsayin dan daudu.
.
Saika rabe kuma daga nan Hilal ai
SINAD PRODUCTION kamar gidan kace. Ya dubi lauriyya
cikin murmushi itama kuma ta dubeni da murmushin
yaudara ta kifta min idanu.
Mu shiga daga ciki Hilal.... Wallahi nayi farin ciki da
ganinka domin kaya ya tsinke agindin kaba daman
yanzun nan nake kokarin buga ma waya saiga Lauriyya
domin akwai wani babban fim dinmu na shekara da za'a
fita gobe kai nake so ka fito a jarumi sunansa.
MUTUWA DA FARINTA TAKE TAKE!
Sa'ar da na dubeshi na dubi Lauriyya sainaji kamar na
fashe da dariya domin ko shakka banayi nasan karya
yakeyi dayace wai ni yayi niyyar sawa amatsayin jarumin
tun farko kamata yayi a sanar dani tun satin daya gaba
tabbas Lauriyya ce ta yaudaro shi.
ALAKAKAI 03
.
BABI NA BIYU
Daga inda nake zaune ina iya jiyo sautin zubar ruwan
saman akan kwanukan gidajen jama'a.
.
Na muskuta ahankali sannan na mike tsaye na nufi tagar
dakin na dan janye gilashin tagar feshin ruwan saman
gami da sansanyar iskar ruwan suka bugi fuskata. Nayi
sauri na rufe tagar sannan nakoma na zauna akan kujerar
ina nazarin dakin. shin wai yaushe za'a dauke ruwan nan
ne. iskar dake cikin dakin ta fara karanci, hakan shiyasa
fankar dake juyawa ta kasa yin maganin zafin dake
addabata, gashi kuma idan nabude tagar dakin ruwa
yajikani.
Nasake mikewa tsaye naci gaba da safa da marwa hakika
indai har ba dauke ruwan nan akayiba to da kyar zan iya
barci. Gashi kuma tuni karfe dayan dare ta gota.
Dakin danake ciki matsakaicine kamar dai sauran gidajen
gwamnatin dake gurin. kujeru ukune kacal adakin kamar
aya gami da tsohon gadon katakon dake dakon katuwar
sabuwar katifar dana saya kwanaki biyu da suka wuce.
daga bangaren arewa na dakin akwai
talabijin mai kala da bidiyo asamanta. sannan kuma
asaman bidiyon fulawace ta roba acikin kofin tangaran
Amatsayina na
TAURARON JARUMAN WASANNIN FINA-FINAN HAUSA
dole ne naga nayi kokarin kawata dakin danake kwana
koh don taren bakin dake tafaman sintirin
kawomin ziyarce-ziyarce dare da rana. Yawan bakin da
suke kawomin ziyara ne yasa kawuna ya waremin
bangare guda agidan ya sanya

katanga tsakanina dashi domin nasamu damar ganawa
da bakina, tunda dai haryanzu banyi aure ba
Na koma bakin gadon na zauna sannan na cire rigata na
kwanta, inajin zazzafar iskar da fankar dakin ke busawa
akan fuskata sannan kuma lokaci guda ina mai adu'ar
Allah yasa a dauke ruwan saman koh na bude kofar dakin
nasha iska. Na rufe idanuna amma barci ya kasa daukata
gashi kuma gobe tashin asuba zanyi domin awashegarin
ne zamu fara sabon fim din kamfanin
SINAD PRODUCTION
mai suna MUTUWA DA MAFARINTA TAKE TAFE,
amatsayina na
jarumin fim din dole ne nasamu isashen bacci domin na
sami nutsuwar yin abin da daraktana yace nayi, toh sai
gashi kuma zafi na neman hanani barci. toh ashe abun
daban saniba shine bayan zafin dake addabata akwai
wani al'amari daban dazasu kawo wa shirin fim din nawa
matsala.
.
Ban san sa'ar da barci ya daukeniba acikin barcin ne nayi
mafarki wai ana ta bubbuga kofar dakin danake ciki nayi
firgigit na farka ina mutsutstsuka idanuna sannan ne to
naji ana buga kofar dakin danake kwance nayi shiru cikin
mamaki ganin mafarkin nawa ya zama gaskiya sannan
kuma nayi mamakin shin wanene ke buga min kofata
cikin wannan talatainin dare.
Nadubi agogon dake makale ajikin bangon dakin wanda
ke dauke da hoton yan wasan da muka shirya wasan fim
din
DAREN MUTUWA dasu karfe biyu da rabi na dare Tsoro
ya kamani domin kuwa banga wanda zai bugamin daki ba
cikin wannan daren sai koh BARAWO
Aka sake bubbuga kofar dakin Das Das kamar ana bugun
kwarya da sillan kara Nayi mamakin jin bugun kofar
dakin babu karfi domin kowane ne ke buga kofar dakin
hakika yana tausayamata aka sake bugawa raf raf raf har
sau uku. Gumi yafara kwararowa kan fuskata
hakika acikin mafiya yawan finafinan danake fitowa ni
jarumine mai zafi marar tsoro to amma fa azahiri tsoro
ne dani kamar farar kura dan karamin yaro ma yana iya
tsoratani da bindigar wasan yara saboda tsorona.
ALAKAKAI-04
.
Me yuwuwa kawuna ne nace da kaina to amma kuma
ban yadda da kalaman da zuciyata keyiba domin nasan
tun da kawuna ya ware min bangarena daban bai taba
koda lekowa ba idan kuwa shine to nasan tabbas ba lafiya
ba to
amma kuma idan shine ai kiran sunana zaiyi gami da
kwankwasa dakin, jikina ya sake daukar bari na juya a
hankali na dubi 'yan kayan dake dakin indai dan wannan
ne sai nabasu su tafi.

Acikin fina finan danayi nasha arangama da barayi da yan
fashi na daddakesu wasu kuma kamasu nake in daure to
amma wannan daban wasane, yanzu kuma shine zahiri
tunda gasu akofar dakina, Na zargi kaina saboda barin
kofar gidan danayi abude,ko da yake daman kuma
kullum ahaka take kwana saboda maziyarta da abokan
arziki dasuke yawan zuwa gurina da daddare to amma ba
karfe biyu da rabin dare
irin wannan ba...........
Raf Raf Raf aka ci gaba da kwankwasa kofar Na yunkura
hantar cikina na
rawa na nufi kofar dakin, ina ta salati da salalallami.
Wai.....wai wane ne? Nace muryata ashake ban iya shaida
muryar amatsayin tawa ba. Maimakon abani amsar sai
naji an sake kwankwasawa,
Wa......Nene? Na sake kuma tambayar shiru ba abani
amsa ba haushi ya kamani sannan sai na tuno da fim din
DAREN MUTUWA Muntaba wani sin
mai kamar wannan inda barayi suka zo suna kokarin
balla kofata nikuma na bari sai da suka gama jingina
ajikin kofar sannan na bude suka
zubo cikin dakin kamar an hankadosu nikuma nabisu na
daddakesu. To yau ma zan kwatanta.
Nace cikin zuciyata Saidai kuma wannan karon inhar
Allah yabani sa'a suka zubo cikin dakin to tsallakewa zanyi
na gudu.
.
Aka
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment