Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki tana nuna ghana must gon tace minal ai wannan zubar da mutuncine kina nufin da ghana must go zamu tafi, kisa sukara rainamu kenan


Murmushi minal tayi tace to meye aciki wasuma nema suke sun rasa
Aziza ta shigo rike da kwalayan takalma guda uku ta jefa akan gado ta kalli minal tace kekuma meye haka,haba ai wannan kauyancine ya zaki tafar mana da ghana must go,dallah cire mana kayanmu akazamin ghana must go dinnan


Rike baki minal tayi tace haba yan uwa bai kamata kukai kanku inda Allah bai kaimuba,don munje da ghana must go meye aciki


Tsaki aziza tayi tace dallah matsa chan saikace bakiyi makarantaba,ummi jeki gidanku ki dakko mana akwatinnan

Tashi ummi tayi tana dariyar keta,yayinda minal ta daka mata harara tayi zamanta akan gado,tana karewa tafkeken hoton safwan kallo,ko yana ina oho,ko yana raye oho

Hawaye taji yana malala a idanuwanta,saurin gogesu tayi

Aziza dake kallonta tace dama kinsan kinason safuwan kika bari ya tafi baki nunamai ba?kinga yanzu bakisan inda yake ba kuma kin kamu da kauna.

Jijjiga kai minal tayi tana hawaye tace yar uwa ba haka bane,ina tuna ranar da safwan zai dawo ya ganni nayi aure ina tare da annur mahaukacin masoyina



Aziza tace haba yar uwa yakamata ace kin daure ki jira safwan


Minal tace a a da son mahaukacin masoyina na rayu dasonsa zan dauwama,shinake buri in aura duk danasan yanada larura haka nake sonsa


Aziza tace hmmmm bazaki taba fahimta bane,namiji badan goyo bane,kinsan mahaukaci baya da hankali zai iya miki illlah



Minal tayi murmushi tace hmmmm zanso haka,indai wanda nakeso ne yamin illah ko ya nakasani ba damuwa


By
Maryam yarmama
[11/03 11:44 am] salmah💍💍: *_(P.W.F)_*
*🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*-7
By
Maryam yarmama
Dedicated to my fans



*TUSHEN SU MINAL*


Alhaji imran.a.maigari dane ga maigarin adammawa,a rugar fulani,su biyu iyayensu suka haifa shida abubakar (abba) saboda kasancewarsu yaya tilo maigari yadasu a makarantar boko da arabic, maigari yana kaunar imran saboda yakasance mai hangen nesa da taya mahaifiyarsa acikin gida saboda batta da mace,abba yanajin haushin son da akewa imran,shine ya dauki tsanar duniya ya doramai,basa jituwa,abba baya kaunar karatu kokadan,yafi kauri a lalata yayan mutane ya sato kudin maigari ya bawa yarinya yayi lalata da ita,yan mata basa kinsa domin ba baya bane wajen kyau,shiyasa mata suke rubibinsa suke sallamamai komai,rashin lafiya yakama maigari,imran yafi kowa shiga tashin hankali,duk ya fice a hankalinsa,shiko abba ba abinda ya damesa Allah Allah yake mai gari ya mutu yaci gado don ya hango garken shanu da gonaki,ana cikin haka mai gari ya amsa kiran mahallacinsa,imran ya firgice sosai,mahaifiyarsu halima tanajin maigari ya mutu zuciyarta ya buga itama ta fadi ta mutu,imran yafi kowa shiga tashIn hankali

Haka aka musu rabon gado sauran aka bawa dangi,imran ya tafi birni ya fara sana,ar siyar da dankunne yari,yazo yafara kaurin suna haryana fita dubai dakko kaya,gwala gwalai,dasu atampopi,bawanda baisan imran da taimakon al,ummaba,haka ya gina tafkeken gida,yana zuwa kasar saudiyya sukaci karo da hindy nan suka kulla soyayya,amma dakyar aka dauramai aure da hindy kyakyawar mace,dayake ta fito daga gidan talakawa,akayi biki ,suka dawo gida nigeri,a da zama.




Imran ya tafi kauye yaga duk abba ya addabi gari da lalata yan mata har yawa wata yarinya ladi ciki,iyayenta suka kekeshe saiya aureta


Agaban imran aka daura auren ya biya komai suka tahi birni,tunda ladi ta bude ido taga,hindy ta dauki karar tsana ta dora mata,haka imran ya siya musu gida maidan kyau flat,abba ya dau aniya azuciyarsa indai yana raye sai ya raba imran da dukiyarsa



Ladi ta zubar da cikin,abba bai mata maganaba


Cikin hindy yashiga wata tara ta haifo danta santallele,imran kamar ya mutu don dadi,ya gayyaci yan uwan hindy yan saudiyya ya biya musu kudin jirgi


Tunda babbar yayansu hindy taga dan ta kwallafa rai,dayake tayi aure bata taba haihuwaba,ran suna ya zagayo dangin imran sunzo,sa,biyu aka yanka ansha shagalin suna da yaci sunansa,shamsudeen


Da yan saudiya zasu tafi, babban yayarsu ta dinga ihu da kukan abata shamsi zata kula dashi


Imran yaki yarda amma daga baya ya bata shi badan yasoba,saboda bayason ran hindy ya bace


Haka da murna suka bar gidan suka hau jirgi suka tafi kasar saudiyya amma a hanyar zuwa sukayi hatsari,bawanda ya rayu acikinsu,hindy tayi sumar tagaji,haka sukaje saudiyya suka ginawa iyayenta gida?imran yabawa iyayenta jari



Ba,afi shekaraba hindy ta kara samun ciki, bayan wata tara ta haifi mace kyakyawa fara kamarta,ranar suna aka samata hadiza amma anace mata aziza,ana cikin hidimar suna ladi tahaifi yarta ya mace lubabatu,amma ana ce mata luba



Haka rayuwa yaci da tafiya ,aziza tana wata biyar umma ta karasamun cikin minal ta haifo minal a kyawu aziza bazata kami minal ba saida ta nunamata fari kawai


Itama ladi minal nada wata daya ta haifo hasiya,fara kyal da ita





Arzikin imran sai kara habaka ykk,haka yadauki su aziza da minal dasu,lubaba yasasu a makaranta mai shegrn tsada,a makaranta kullum cikin fada suke,saboda dukansu aji daya akasasu,minal da aziza sunfi kowa hazaka da kokari,lubaba kuwa kullum sai an jibgeta


Abotar ummi da minal tasamo asaline amakaranta sun shaku,har agida ansan abotarsu ummi da minal da aziza


Ko antashi wataran agidansu ummi suke zama,har sukaje ss1
Inda minal take da burin zama likita,yayinda aziza take burin zama bussiness woman,ita kuma ummi *yar jarida*


Nan mahaifinsu minal ya fara ciwo mai tsanani ciwon suger,duk dukiyarsa abba ya mallake,ko ance ya kawo kudin magani sai yace ai yasamu karayar arziki,sai abba ya tabawa mahaifinsu minal,abincin da likitoci suka hana abasa,su minal nada shekara goma sha uku a duniya Allah yawa mahaifinsu rasuwa sun shiga tashin hankali bakadan ba,

Karantunsu ya tsaya,ga umma ta laulayi,haka abba ya musu korar kare ya mallake gidan tunda wai bata da yara maza,maman ummice hajiya ta bawa su minal karamin fillin ta wanda yake fuskantar gidanta ,
Umma sukayi ginin gidansu daidai gwargwado,da taimakon hajiyar ummi,akayi komai,


Umma duk ta rasa kadarorinta,duka,hajiya tana taimaka musu sosai,har aka haifi auta,(jawahir)itama hajiya bawani karfine da itaba,yayanta uku Allah yawa mijinta rasuwa,daga yayansu ummi nasir da ke karatu a kasar waje,sai yayar ummi dake auren d.p o a abujah,sai ummi data kusa ta kammala karatunta a yanzu,
Su minal sun ga kuncin rayuwa da wahala,haka wataran suke hakura basacin komai

Har auta data mutu kwanaki da suka wuce,wannan shine takaitaccen labarinsu minal

Ayanzu ahaka minal tanada shekara goma sha bakwai a duniya,takasance doguwa wankan tarwada ga dara daran idanuwa,ga hanci har baka,tanada diri;gason kwalya da faran faran da jama,a ahakuri minal ta dakko halin umma,yayinda aziza take fara kal harta zarce minala diri,tana da dan jiki kadan,ita burin aziza ta auri maikudi,duk saurayin dayazo wajenta bata kulasa,saidai tamai bala,i ta koresa,batta da hakuri samsam ,aziza tana shekara goma sha takwas,
Itama ummi fara ce kyal saidai batta da hanci sosai but amma akwai kyau da iya ado,yanzu ummi haka tanada mijin dazata aura lawyer,sainanda shekara daya akasa ranar


*wannan kenan*

*DAWOWA LABARI*


BY
MARYAM YARMAMA
[11/03 11:44 am] salmah💍💍: *_(P.W.F)_*
*🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*-8

By
Maryam yarmama
Dedicated to all my fans


;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;,;;;,,,;;;;;;;;;;,,,;;,,,;;;;;;;;;;;;

Haka su minal suka shirya,sukayi sallama da umma,ankon dogon riguna sukasha,na kanti,sunyi matukar kyau,duk inda suka dara kowa saiya kallesu

Gaban minal ne yafadi dataga sansanyar iska yafara kadawa,wannan ya nuna alamun mahaukacin masoyinta zai bayyana


Waige waige tafara, ido hudu sukayi da mahaukacin masoyinta,duk kayansa ya yayyaga,rike yake da taya ya nufota yana kwalla mata kira aunty aunty


Murmushu minal tasaki,ta gyara tsayuwa

Ummi tace wayeshi,kafin minal ta bata amsa aziza tace wai shine wanda take da burin aura


Ummi ta dake kirji munshiga uku minal kuwa bata samu tabin hankaliba kuwa,mahaukaci kike da burin aure


Harara minal ta dankara mata tace ai mahaukacin mutumnr Allah ne yayisa


Annur ne ya nufo wurin aguje haryana neman hankade aziza yace aunty kizo in rage muku hanya


Cikin bacin rai aziza ta dakamai tsawa tace kai kaga munyi kallar yan uwanka,yar uwata ba sa,ar auranka bace,kaje ka auri mahaukaci ya kamar ka


Ran minal ya bace tace aziza!

Daga mata hannu aziza tayi tace dakata,in banda abinki wannan wawan zaki aura maiya sani arayuwar aure,iye sannan ta kalli annur ta dakamai tsawa tace barnan sauna ba amfani


Idon annur yayi jaa,hawaye ya fara malala a idonsa ,ya juya da niyyar tafiya,minal tasha gabansa tace annur ni inasonka,lafiyanka kalau karya suke kai ba mahaukaci bane.

Hankade minal yayi,yayi tafiyarsa yana share hawaye


Aziza ta kalli minal tace Allah ya kara ,ai indai wannan dutsen. Kikayi rantsuwa zaki aura yanzu kika fara gani
Aziza zatayi magana taji an zura mata bulala a bayanta zuwet,saboda zafin bulalan tayi ihu wayyo mamana,suna juyawa suka gano,annur ne rike da katuwar dorina sharbebiyya,aguje suka fanna


Yayinda minal tatashi ta ruko bulalar annur tace a a annur masoyina hasken idaniyata kayi hakuri ,ka kyalesu


Girgiza kai annur yayi yajuya yayi tafiyarsa
Minal ta kyallesa tana zuzuta kyan halitarsa,


Acan nesa ta gasu aziza sai maida numfashisuke,minal ta matse dariyarta ta nufi wajen aziza sai faman harararta take


Minal ta kyalkyale da dariya tace,a a kike hararana bani naja mukuba bakinkune ya jawo miki



Ummi tace munji muguwa kuzo mukarasa gidan bikin


Abbane zaune da abokansa sunfi ishirin anaci anasha,sai raha ake

Ga gefe An daure shanaye biyu awaje

Yana hango su minal ya hade rai,amma yana. Hango wasu bare,ya saki. Murmushi harda gaishe gaishe,karasowa wajen sukayi minal ta durkusa har kasa ta gaisheshi amma aziza,tana tsaye ta kwashi gaisuwa


Abba ya kalleta yace ke wace yar iskan yarinyace ,kin tsaya akaina ko haka kike zatonzan baki. Sadakar. Ne? Banza. Sakarai


Tabe. Baki aziza. Tayi,ta. Kallesa shekeke tace nidai ba yar iskabace,kuma inma ka bamu Sadakan. Ai da kudin mahaifina kake bushasha.



Abba dayaga aziza zata Bashi kunya,yayi shiru ya basar Yaci gaba da gaishe-gaishensa



Azixa ta gama yadamai bakaken magagganu,tashige ciki




Bin bayanta sukayi ,suna shiga asiya ta taresu damurna,abin ya basu mamaki ko din zatayi aure tayi hankali



AZiza ta hade rai yayinda hasiya ta dafa minal suna tafiya harta kaisu masaukin yan mata



Yan matane a dakin birjik. Sai kwalyan. Kamu ake.


Lubaba. Sai yarfa mata fulawa ake tana. Ganinsu aziza ta fara harare harare ta daga murna tace to jama,a kowa yayi hankali da jakarsa akwai masu. Halin bera anan


Amshe zancen aziza tayi tace to Allah ya rabamu. Da masu halin jaba ma



Yan mata suka. Amsa amin




Lubaba. Ta dinga yada habaici iri iri,har sukaso suyi. Dambe. Da ummi



Hasiyace tashigo tace aziza wai kuzo inji mama zaku gaisa da su dangi dasukazo daga kauye


Tsaki aziza tayi tace wlh ba inda zani waya taba zuwa ya dubamu ba wanda yasan darajarmu. Don haka ba wanda zanje in gaisher



Minal hawaye na. Zuba a idanunta tace aa yar uwa in mukaki zuwa umma taji labari,bazaji. Dadiba,ko bakomai danginmune



Lubaba ta rangada buda tace wama zaije wajenku abinda bakuda abin hannu ai kudi su suke magana yanzu

Ummi tace ai arziki nufin. Allah ne bawanda aka haifa da kudi ko mulki



Lubaba ta fusata,tace to karere yar kallan dangi muna maganar mu na dangi meye zakisa mana baki iye?



Minal ta jawosu ummi da aziza suka nufi dakin mama,minalne taga yan uwan mahaifinta,kwasar gaisuwa sukayi

Nan yan uwa aka dauki kukan,mutuwar alhaji imran akafara jimami



Minal Ma tarushe da kuka

Aziza ta tsaya yana musu kallon munafukai

Mama ta kalli Aziza tace ke me zuciyr fir,auna ke ko kwalla bazakiyi ba ,waya. Saniko ke Kika. Kashe. Mahaifinki, daga ganin idonki da Alama ke yar ruwace


Aziza tace Kece Babbar fir,auna. Wallahi ma aka bincika akwai sunanki ajerin yan wuta,ai wanda ya danne hakkin marayu shida rahamar Allah. Har abada,da kike cewa mahaifiyata karuwace,ai. Indai karuwa ake nema aka samu kamarki an gama


Mama. Ta fashe da kukan munafurci tana ni dama yarinyar nan ta tsaneni tun tana karama



Dangin. Mahaifinsu suka tunzura suka dinga zagin aziza suna tsine mata albarka,

Minal ta. Rushe da kuka yayinda. Aziza ko ajikinta ta kalli yan uba tace dallah chan ba wanda yakaiku mugunta ai da mahaifinmu yananan ba yar. Iskar data isa ta mana kallon raini,tunda ya mutu me kukayi mana


Daya. Tsohuwatace aziza nice mune. Yan iska?


Aziza tayi dariyar keta tace and so what ai. A duniya bawanda na tsana kamarku. Ayanzu




By
Maryam yarmama
[11/03 11:44 am] salmah💍💍: *(P.W.F)*
*🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*_9


mama ta tashi ta fashe aziza da mari


Har aziza zata rama,minal tayi saurin rike hannunta ,suda ummi suka jata waje,suna bata baki,dakyar aziza ta huce ba kukan data tsana ta gani irin kukan yar uwarta minal,washe gari aka shirya tafiya dinner,minal tayi matukar kyau da tsari sunsa ankon kawaye,sun daura blue din rosis da takalmi blue komaima blue,dama ankon swiss less ne pink,aziza sai mita take tana danasan anko kawaye mukayi da banyiba

Abokan angone suka fara zuwa kwasar yan biki,minal suda aziza da ummi sun tsaya,wani hadden mota ya faka a nesa da su,yace minal tazo,a sannu a hankali take tafiya ta nufi wajen hadadden gayen maijini ajiki

Cikin yanga gayen yace sunana yusif shehu abukakar,ni dane ga shugaban custom,nagankine kuma kinyimin sosai in ba damuwa inasonki da aure

Minal tayi yar murmushi tace ai saidai kayi hakuri anmin miji ,indai kana kaunata ga yar uwata chan aziza sai ku daidaita

Yusif yace amma banji dadyba,amma inason yar uwarki tunda naga kuna kama sosai farine ya rabaku dadan jikinta,minal tace to bari inkirata,nufar wajen tayi tawa aziza magana,aziza ansamu abinda takeso ,ta nufi wajen suka gabatar da kansu ga juna,ya kwashesu;dukansu taje ya siya musu dankareriyyar waya ya basu kudin niki,aziza ana gaban mota anata zuba soyayya.


Minal suda ummi sai dariya suke abayan mota,dama haka aziza ta iya soyayya take wulakanta samari,


Taro yayi taro,ashe ma mijin hasiyan tsohone sa,an abbane ma

Aziza tace lalle kuwa auren kudi su mama sukawa hasiya,minal tace Allah yasa ta zauna


M.c taji yana cewa to jama,a yan mata da samari saidai kuyi hakuri prince annur adams saraki bazai samu hallataba amma yabada gudunmuwar miliyan daya


Gaban minal ya fadi tace waye mai irin sunan masoyina kuma,prince annur adam saraki? Inason ganinsa


Wasu mata tagani suka fashe da kuka wata tace wlh saboda prince annur nazonan ,na aro kaya naci ado amma baizoba,meye wannan abin dan Allah,wlh sonsa zai kasheni,
Minal zuciyarta ya fara bugawa da sauri tana tausaya musu lalle daga ganin prince dinnan ya hadu,tunda gashi rabin yan matan wajen basuji dadiba



Aziza ta kyalkyale da dariya ta kalli minal tace wa ummi kinga minal yanda ta kame kamar kunki inaga ta tuno da masoyintane

Ummi tace shareta indai akan wannan mahaukacinne wanda bashida kyan gani zatayi zata gaji,duk fuskarsa yayi baki kamar anshafa baki tsabar rashin wanka


Minal kota kansu batabi ba

Haka akayi taro aka watse yusif ya maidasu gidan biki


Washe gari aka daura aure,aka chashe su umma da hajiya sukazo suka tafi,aka kai amarya ring road,


Wanke wanke tuli awaje


Mama tashigo dakin taga su minal nata hada kaya,mama ta rike kugu tace me kuke nufi tafiya zakuyi bakuyi wanke wankeba eye?


Harara aziza ta dankarawa minal dataga tatashi tayi hanyar waje da nufin taje tayi wanke wanken,bashiri minal ta koma ta cigaba da hada kayan


Mama tace au bazakuyiba,to wallahi baku isa kubar,gudannanba dole kuyi


Aziza suka gama hada kayansu aziza tace wlh bawanda ya isa yasamu wanke wanke,a tsakiyar daren nan,


Bangajeta sukayi sukayi wucewarsu suna zage zage ummi da aziza


Mama ta ce wallahi zamu hadu daku yayan mace kawai.


Yusif ne ya daukesu ya saukesu a kofar gida,minal da ummi suka fita motar suka shiga cikin gida suka,umma suka tadda batanan,gidansu ummi suka shiga suna tambayar hajiya umma tashigone,hajiya tace ai muna dawowa daga gidan biki muka rabu kuje ku duba bayan gidamana


Minal tace to inaga tafita muje dai mukara dubawa umman da bata yawa daganan gidan sainan gidan


Shiga cikin gidan sukayi,wata farar takarda suka gani ga takalmin umma a yashe a wajen,
Minal ta fara karanta takardar kamar haka
*dafatan kuna lfy yayan umma*


_mu barayine masuyin asiri da garkuwa da mutane,mun dauke ummanku kuda ganinta sai a lahira_
*daga boyayyen mutane*



Ihu minal ta saki ummmmma ta zube a wajen sumammiya

Yayinda ummi ma tasaki kara ta nufi waje da gudu aziza na zance da yusif,suka fara tambayar lafiya?


Kuka ummi tasako tace ansace umma


Aziza tace dagaske banson wasa


Ummi ta rusa kuka tace wlh dagaskene minal ma ta suma



Ihu aziza tasa ta shga gidan aguje,tana minal umma namu ya kare,itama ta zube awajen ba numfashi😭😭😭



By
Maryam yarmama
[11/03 11:45 am] salmah💍💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*-10

By
Maryam yarmam
*dedicated to*
*all my lovely fans*

😭😭masoya kunji shiru kwana biyu ko,wlh karatu nake,ku dinga mana adu,a masoyana ,adinga hakuri damu


_wannan shafin nakine kawata rabin jiki,ba abinda zai ce miki saidai ince nagode sosai *my salmati Ali wadah*nagode sosai Allah yabar zumunci_





Kuka ummi ta rusa yayinda yusif yaje motarsa da sauri hankalinsa a tashe ya dakko faro bottle water,ya shigo cikin gidan ya rasa takan wazai fara jikinsa sai rawa yake ya kwarawa ,minal,sannan ya kwarawa aziza,ajiyar zuciya minal tayi,itama aziza ba,a jimaba ta farfado,kuka suka dinga rusawa



Hajiya ce tashigo gidan tana lfy lfy nakejin ihu da kukanku ummance har yanzu bata dawoba ko



Yusif ya gaishe da hajiya yace eh yanzu nake tunanin muje police station,muyi reporting don abin nan bana zama bane ace an sace umma


Dafe kirji hajiya tayi tace dagaske sace umma akayi tayaya haka ta faru,duniya ina zaki kaimu


Minal tace dan Allah mu tafi police station har gidan radio a yada ta kara rushewa da kuka



Yusif yace haka za,agi ku taso mu tafi





Anyi cigiya an sa jami,an tsaro abu yaci shirya shiru kakeji,saboda basu da karfi donma yusif yananan,gashi saura sati biyu ya tafi course

Aziza ta damu matuka shikenan basu da gata yanzu,minal tayi hakuri ta dangana kullum acikin adu,ar take Allah ya bayyana umma




Minal na zaune a tsakar gida tayi tagumi gidan ya mata fadi,ba umma,kallon aziza, minal ta fara da taga hawaye na zuba a kwaryan idanuwanta



Minal zuciyarta yayi rauni ta fashe da kuka ,ba tsammani sukaga baffa ya shigo da wasu mutane guda biyu sun sha malin malin


Cike da tsoro minal bakinta na kakkarwa tace abba ina wuni,

Abba ya nunata ya murtuke fuska yace ni ba abbanku bane abbanku yana kasa,inaso kafin sati biyu ko wacce shegiya ta fito da mijn aure in mata aure kokuma kubi uwarku wanda ta fantsama duniya yawan karuwanci,donni siyar da gidan zanyi


Kuka minal ta fashe dashi tace wayyo umma ina kikene abba ka tuna mu marayune bamu da komai gidannan ne ya rage mana, ina zamu nufa


Abba ya kyalleta yace to marainiya nima ai marayannan ne,kuma ai ubanku ni ya barwa dukiyarsa kafin ya mutu


Aziza ta mike tsaye tace to azzalumi kasani komai mai karewane,inka siyar da gidan sai me?kuma kace babanmu yana kasa karka manta kulli nafsin za,ikatul maut,kaima kana tunanin bazaka shiga kasar bane,kokuma kana tunanin da gida da mota da gwagwalai za,a binneka

Kafin aziza ta karashe kalamanta,taji an tsinka mata mari,dagowar da zatayi taga daya daga cikin alhazawanne wani kato dashi baki kirin,yace ke bakki da kunya kike zagin tsohonnan


Aziza ta dafe kunci tace nika mara to wallahi ka tsinkawa uwarka mari,banza azzalumi bakin mugu,da gudu aziza ta shige dakinsu tasa sakata tana zage zage


Abba ya durkusa yana bawa mutanen hakuri harda daukan alwashin dukanta


Minal tana kuka tace abba nidai inada tsayayya zance ya turo magabatansa ayi auren


Cikin sauri abba yace dan waye,a garinnan,bafa zaki auri maikudiba fa

Murmishin takaici minal tayi tace abba badan kowa bane mahaukacine mai bin bola,yana neman abnci kuma bansan asalinsaba


Abba yaji kamar ammai albishir da gidan aljanna yace maxa maza kice ya turo da magabatansa ai dama yar karuwa sai mahaukaci,ku da kuka gama zubar da mutuncinku a kwararo wani dan arxikin ne zai tsaya ya aureki saidai mahaukacin


Kuka minal tasaki,yayinda aziza dake daki ta ce aikune mahaukatan da kukecin hakkin al,umma



Ran abba ya bace ya karbi makulli a hannun dayan alhajin,ya karkame kofan dakin da aziza take aciki,yana kya dandana kudarki yau




*masoya captain shayeeda amin afuwa gobe zan cigaba*

Daga taku mai debe muku kewa
Maryam yarmama
[11/03 11:45 am] salmah💍💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁* -11
By
Maryam yarmama
Dedicated to
*All my fans*



Aziza dake garkame da kwado bata sadudaba tace ai zanso ka kasheni inka isa sunanka abba,



Minal ta durkusa tace dan Allah abba ka budemin yar uwata ,karta mutu ita kadai ta ragemin ka taimaka ka budeta wallahi tana da asma kuma chronic ne


Abba yace mai ruwana da asmarta tsabar karya waya bata asma ai inyana dashi zamu sani,kinga tafiyata dakey din


Har kofar gida minal tabisu abba tana kuka da basu hakuri,daga bisani ma abba ya hankadeta ta fadi kasa wanwar har bakinta yadan fashe ,minal kuka tasa dataga sun shiga mota sunja sunyi tafiyarsu



Taimakon wa xasu nema,bayan su hajiya sun tafi abujah hutu,kuka ta kara fashewa dashi,ji tayi an wullo mata abu ya fadi kasa makulli tagani da dan karamin takarda ansa
_daga boyayyen masoyinki banson kina kuka ki share hawayenki_


Dafe kirji minal tayi tace waye kuma wannan inaga ma wucewa yazo yi kokuma ma makullin karyane,jefar da makullin minal tayi tana neman mafita ga aziza tana ta faman sheka uban tari.


Ba shiri minal ta dauki makullin tana adu,ar Allah yasa ya budu,kafin kace me kofa ya bude,da gudu minal ta fada dakin tana aziza,

Aziza dake faman sheka tari tace minal dakko min drug dina in shaka yi sauri,da gudu minal ta fita daga dakin ta nufi dakin umma inda umma take aje magunguna ,abin mamaki tana daga robar maganun ya kare,ihu ta kwalla tace ya Allah ka kawomin agaji kar in rasa yar uwata


Minal ta fito daga daki cin karo tayi da maganin irinshi,ba tantama ta dauka ta kaiwa aziza,aziza tana shaka tana fesawa abakinta tayi ajiyar zuciya cikin nishi sama sama tace wlh sai naci uwar abba dan bantan ubansa


Cikin damuwa minal tace yanzu aziza kina nufin baki sadudaba kenan,


Aziza ta gyara kwanciyarta tace ai wlh sainaga bayansa ta sanadinsa muka rasa babanmu ta sanadinsa karatunmu ya tsaya muna ss2 gashi har ummi ta kusa zama nurse amma mu sai zaman gida,ta sanadinsa muka daina jin dadi da walwala muka rasa auta muka rasa umma,tayaya zan saduda in Allah ya yarda sai yayi mutuwar wulakanci,bazan taba yafe masaba.


Minal tace haba aziza ki dinga godewa Allah ai Allah ma yana yafewa mutum balle mu yan adam ajizi,ni yanzu na tsani auran maikudi da in auri maikudi gwanda na zauna ba aure har abadan abada


Zaro ido aziza tayi tace ke wace irin sokuwace ke ana neman inda za,a huta ai munfi kala da matan manya,nidai in bamai kudiba wlh bazan auri kowaba


Subhanalllah minal take fadi tace anya kinada hankali kuwa meyasa kike da hangen dala,


Tunzura aziza tayi ta wanke minal da mari tace ai gwandani ban tare a gindin mahaukaciba dan uwarki


Kuka minal tasa tace yar uwa nikika mara kika zaga,ko wanine ya zageni saikin dau mataki,ko kin manta amanata yana hannunki a yanzu,kece uwata kece ubana kece gatana,ke yakamata ki nunamin madaidaiciyar hanya amma tunda bakya sona gidannan bari in kwashe kayana in tafi in barmiki gidan,minal ta tashi da niyyar fita aziza ta ruko hannunta tana hawaye tace a a yar uwata ba inda zaki,kiyi hakuri ki yafemin




By
Maryam yarmama
[11/03 11:45 am] salmah💍💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*-12

By
Maryam yarmama

Dedicated to all my fans





Kuka minal tasa ta rungumi aziza suna kuka mai tsuma zuciya




Bayan kwana biyu minal zaune da kyakyawan mahaukacin masoyinta a tsakar gida ,sai gabzar lomar abinci yake yana santi kai aunty haka kika iya abinci dama

Kallonsa minal take komansa burgeta yake

Dago ido annur yayi,dara daran idonsa suka hadu dana minal nan minal ta kara dumaucewa duk kwarjininsa ya cika mata ido sunkuyar da kanta tayi,
Annur ya kyalkyale da dariya,yace kai aunty ke matsoraciyace idona kike tsoro iyeh kika sunkuyar da kai kamar munafuka


Minal batasan lokacin da dariya ya subuce mata aziza ma dake waya a kuryar daki saida ta dinga dariyar data dade batayiba


Minal tace kaga nidai abinda nakeso kaje gida ka gayawa umma da abba,su kawo lefe a daura mana aure


Ihu annur yayi ya rufe fuska yayi waje da gudu,dariya minal ta fashe dashi aziza dake waya a daki hawaye ya zubo mata shikenan yar uwarta mahaukaci zata aura,oh yanzu yar uwarta zata shiga sabon rayuwa,



;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;


Washe gari minal tana sharar tsakar gida,taji sallama,amsawa tayi baki uku tagani tsofaffi uku mace daya, duk kayansu yasha ruwa gasu rike da karamin akwati daya tal

Minal ta gaishesu cikin ladabi da biyayya ta shimfida musu taburma ,aziza dake bacci ta farka fitowa tayi ta gaishesu, ta zauna a gefensu


Wata farar tsohuwar tace mudai mune iyayen annur wanda yake yawan bamu,labarin minal wacece amaryar tamu


Sunkuyar da kai mainal tayi

Tsohuwar taci gaba da cewa shine yazo mana da magana gadan gadan wai kince ya kawo kayan auransa,muka karyatashi yana da larura wazai auresa,kuka ya dinga mana harda zazzabi gashi muba haline damuba,annur marayane iyayensa sun mutu.mu muka rainesa tun yana karami yake tare da laruran nan,shine muka hado akwati daidai karfinmu ku kira ummanku da abbanku

Aziza jikinta yayi sanyi tace ai mu ma marayunne


Jinjina kai dattijan sukayi ,sukace Allah yaji jansu to waye zai wakilci

Please Login or Register in order to submit comment