Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

auranne


Minal ta musu kwatancen gidansu abba,aziza takaici ya kusa ta kasheta dataga an bude dan karamin akwatin sarka dan saba,in guda uku,dan kunne dan goma goma dozin biyu,turare dan dari biyu da hamsin guda biyu,takalmi dan dari uku guda daya tak,bacilin da gyalle daddaya,sai turmin atampa biyu.


Aziza kamar ta rusa ihu takeji,ai wannan gwanda basu kawoba ko sadaka albarka minal taja musu zagi agari shikenan sun zamo abin nuni agari


::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::;::::::::

Abba yaji dadin wannan auren minal da dan talaka atake ya yanke aure kwana uku masu zuwa


Minal kullum bata rabo da mutane,yan tsokana mata da maza,suna mata gorin auren mahaukaci,

Minal ko ajikinta,hajiyace suka dawo daga abuja taji labarin minal zata auri mahaukaci,ummi kamar tayi hauka tsabar takaici dama ashe minal bata sadudaba


Hajiya ta kasawa minal magana data ganta cikin farin ciki da annashuwa kawai ta mata adu,ar Allah ya kawo Zuriya masu albarka,sannan ta siya mata katifa da kayan kitchen da taburma makeke


Kuka aziza da minal suka dingahi suna godiya,hajiya tazama uwa agaresu


By
Maryam yarmama
[11/03 11:45 am] salmah💍💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*13


By
Maryam yarmama
Dedicated to my fans



Aziza suka yanke shawarar daukar gwal din dasuka taba boyewa da umma,da nufin siyarwa amma suka nemesa suka rasa abin ya basu mamaki,

Jikinsu yayi sanyi kodai barayin dasuka sace umma sun tafi dashi

Kuka minal tafara tace wai sai yaushe zamu daina kuka da bakin cikine rana tayi zafi inuwa kuna babu sanyi

Aziza tace muyi hakuri mu dangana,muje amana kunshi da fulawa kawai kinsan gobe daurin aurenki ke da masoyinki annur


Murmushi minal tayi yayinda taji takun takalma lubabace tsaye suda mama ,mama ta rangada buda tace ahayye kaikayi ya koma ga mashekiya andaiji kunya anrasa mijin aure an fake da auran mahaukaci ,wanda baisan gaibuba


Lubaba ta anshe zancen ai saura ke aziza in Allah ya yarda dan maye zaki aura yata lakada miki duka


Aziza tayi tsaki duk jikinta yayi sanyi,aziza dana sani da rashin kunya da raina mutane bata kyalewa taja bakinta tayi shiru hawaye na malala a idanunta tace duk mai kukamana duniyace ta ishi kowa riga da wando


Lubaba suka rangada buda suka tafa da mama sai kace kawaye mama tace su kanwar fir,auna baki ya mutu kenan ai kadan ma kuka gani banzaye jakuna


Ba wanda ya tanka musu har suka gama sambada rashin mutuncinsu sukayi tafiyarsu ba wanda yace kala acikinsu minal




Rana bata karya saidai uwar diya taji kunya,yau mutane shida suka shaida auran minal da annur akan sadaki naira dubu biyu,wanda suka hallaci daurin auren daga abba sai abokinsa sai,baban annur da liman,ana watsewa abba yasa dubu biyun a aljihunsa yayi gaba abinsa


A gida minal dasu ummine a zaune sunhi dan girki,yusif ya kawo wa minal gudunmuwar kayan abinci su shinkafa lemo faro,katon din taliya biyu,turmukan atamfa sabulu dadai sauransu


Yusif ya sanarwa da aziza zai tafi course zuwa port harcour zai yi wata biyu in yadawo zasuyi maganar aurensu


Aziza jikinta yayi sanyi gani take kamar karshen haduwarsu yazo ,anya yusif ba guduwa zaiyiba ,wata zuciyar tace a a bazaimin hakaba



Da daddare akasa dan kayan minal a kura su katifa dasu abubuwan da take bukata,a kafa su ummi suka kaita kwarbabben gida kuma na jar kasa


Kuka aziza ta fashe dashi suka jera gadon minal aciki da yan kayanta


Minal kuwa sai farin ciki da annashuwa suke saida aziza sukazo tafiya ta fashe da kukan rabuwa,dakyar suka banbare jikinsu daga jikin juna suna kuka


Ba,a jimaba aka kawo nepa haske ya gauraye dakin, ya gauraye da haske,dakin yadanyi kyau,dauro alwala minal tayi tayi sallah ta,cire riga daga ita sao dan singlet saboda zafin da ake tafkawa,kwanciya ringingin tayi.


Annur ne ya taho da bataliyan yara,yana kuzo kuga mata ta yara,minal ta kokarin saka hijjabi suka danno kai dakin

Rufe ido annur yayi sakamakon ganin rabin dukiyar fulanin minal awaje yace laaaa dama aunty ke yar iskace?



By
Maryam yarmama
[11/03 11:45 am] salmah💍💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*-15
_BY MARYAM YARMAMA_


_MASOYAN LITTAFINA_
Ina muku dimbin godiya ba abinda zance muku saidai godiya

_this page is dedicated to adorable *my ummie jafar,awesome salma ali wadah,my sweet and beautiful hauwa mamee*_
_thank you for ur special love and care you guys you are in ma heart_





♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥

Annur yace anty,nizanyi wanke wanke karki damu jeki kwanta na iya


Murmushi minal tayi batason ,ta musamai ta nufi,daki tana gyarawa,annur yasamu bayan tukunya ya lakuta ya dauki wani kofi fari kal yace kai kofinnan yayi fari diyawa yakamata ace, nachanjamai kala zuwa baki


Duk fararan kwanukan minal annur ya lanbata baki akai suka dawobaki , ya dauki dish da nufin wankewa ,yaran jiya sukashigo,tashi tsaye annur yayi ya saki dish din ya fadi ya tarwatse,yana murnar ganin abokansa


K'aran ne ya jawo hankalin minal dake faman gyara dakin,a guje ta fito hartana tuntube tace dear mezan gani haka iyeh,haba dear wannan ne iyakacin dish mukuma .


Annur ya zaro ido kai anty,yanzu akandan wannan abun ranki ya bace to yahakuri bansaniba bazan karaba,anty bakiga na maida kwanukan da kofinnanba sun dawo baki abin sha,awa



Minal ta zaro ido tace mezan gani,nashiga uku ni minal



Annur ya ,hankade minal suka shige daki suda abokansa sunata tsalle tsalle da ihu akan gado


Minal cikinta ya duri ruwa,tace nadakko ruwan dafa kaina

Ihun annur minal taji yana fadin anty nayanke kizo wayyo zan mutu

Aguje minal ta fada dakin kukatasa,ta zauna a kan gado ta rike dan yatsan daya yanke wanda jini keta zuba,tausayinsa ya kama minal itama tafashe da kuka ta rungume annur ,duka dakin yadauki kukan abokan annur da minal dashi annur din kansa,



Sai rusa uban kuka suke,minal harda shessheka,azizace tayi sallama ta fado dakin tana waye ya mutu?

😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂



By
Maryam yarmama
[11/03 11:45 am] salmah💍💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*-14

_by_
_maryam yarmama_

_wannan shafin nakune masoyana saboda kaunar da kuke nunawa littafina ,masu bugomin waya masu yimin text da fadin sunanku kuna diyawa,naga sakonku kuyi hakuri next page zan fado sunanku kuna diyawa i love you too😍😍_



Dafe kirji minal tayi yayinda tayi saurinsa hijab,tayi yake dataga dandozon yaran sunata lalata mata risho,


Minal cikin sanyin murya tace ku bari mana annur ka gaya musu

Annur yace haba anty ai abokainane dasu muke wasan langa awaje,shiru minal tayi ,annur yace anty ina kazar da ake bawa angwaye tunda nima angone,minal ta kyalkyale da dariya tace ai amare ake bawa badai angwayeba



Annur yacewa yaran abokaina ku fita ku tafi gida gobe ma hadu ayi langa,ku zo gobe muci abincin anty


Ihu yaran suka dingayi suna sai gobe sai gobe

Minal tatashi taje ta rufo kofa,ta cire hijjabin tace ana zafi,wlh baxan iya jurewaba


Annur ya kalli shayeeda ya kawar da kai ,matsowa daf dashi minal tayi tana kallonsa,shafo fuskarsa tayi tace haba dear meye nacemin yar iska bayan kasan ni matarkace sai yanda kayi dani na zamo mallakinka,ina kaunarka kai nake mafarki kaine uban yayana



Matsawa gefe annur yayi ya murtuke fuska yace a a anty ki daina shafani karki iskantani,nidai yarone badan iskaba


Minal taji dariya ya subuce mata ta dingayi harda tsugunawa tace ai kai ba yaro bane ka wuce shekara talatin


Annur ya zaro ido yace amma ummata tacemin shekara biyar nake shine take bani biyar,tunda yanzu shekarata talatin nera talatin za,a dinga bani daga bisa ya kwanta a gado ,nan take barci ya daukesa.


Dariya minal tasa tace oh na hadu da masoyi,gyara mai kwanciya tayi itatama ta kwanta tana shafamai laulausan gashin sa daya kwanta kamar indi,a



Washegari minal ta tashi ta hura wutar murhu ba kalanzir a risho tanason daura wa annur shayi


Iccen danyene ,duk gidan ya kaurw da hayaki sai hawayene yake ta zuba a idanunta


Annur ne ya fito daga daki, ya nufi wurin ya kalli idon minal duk yayi jajur,kamar, gauta yace sannu anty in nemo miki makamashi
Murmushi minal tayi. Tace daka kyauta my dear


Da gudu annur ya shige dakin ya dauki wuka ya yanki rabin sabuwar taburman minal😂😂 dagudu ya fito ya cusa a murhun nan wuta ya tashi fuuuuuu


Tambul minal tayita koma gefe dafe. Kirji minal tayi tace dagaskene gizo idona yakemin taburmata a wuta?


Annur yace ai anty saiki godemin , nasha wuya wajen yanko taburman,ma



Ko daya minal bataji haushiba,ta yi murmushi tacenagode ta dora tunkunya akan wutar dake ci

Tahadamusu. Shayi sukasa,



By
Maryam yarmama
[11/03 11:45 am] salmah💍💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*-16
By
Maryam yarmama


*wannan shafin nakine maman hafsat(sayyada hajara)i love you so much*



Minal ta kara rushewa da kuka tace yar uwa mijina ya yanke wlh ya yanke,ki taimakamin kar,in rasashi,kinga jini yanata zuba a hannunsa ,minalta dago hannun annur masu laushi da taushin bala,i



Aziza ta rike ciki😂ta rinka sheka dariya harda hawaye saida tayi mai isharta ta kalli minal da ranta ya sosu tace dame ya yanke,banza minal tayida ita,yayinda aziza ta dauki tsumma,ta kulla a hannun annur

Ihu annur ya kwalla anty a cire zafi ,aziza ta kara kyalkyalewa da dariya harda faduwa kasa tace haba angon minal kaifa namijine ba mace ba ko kunya bakaji ga minal azaune kana kuka aisaita rainaka


Rufe ido annur yayicikin alamun kunya yace nidai anty ki bari nadena kuka,yanzuma wasa zamu tafi


Zaro ido aziza tayi tace la ai ango baya wasa,sai amaryarka ta rainaka ta dingama wanka,ai azamanin nan ka dinga zama agida tana koyawa a.b.c d

Annur yace la aiko inason in iya a.b.c d.don yanamin dady duk abokaina sun iya nikadai na rage ban iyaba


Aziza tace laaikwa gwara ka koya donwata rana in baka iya a.b.c diba ba wanda zai yi wasa dakai



Annur yace. Dagaske anty bari in dawo daga wasan taya,sai antyna ta koyamin


Aguje ya fyace yayinda abokansa suka rufamai baya



Aziza tace lalle kam minal sannu da hakuri



Minal tace ai abinda kakeso shi yake wahalar dakai sai hakuri haka duniya ta gada mu dingahakuri, wai ya ake ciki har ne


Aziza tace ai nasiyar da duk wata abubuwanmu na amfani,najena bude mana account na zuba,bakiga akwatina a wajeba,na dawo gidannan. Da zama na barwa. Baffa gidan

Gobe su hajiya ma zasu yafi abuja final
By
Maryam yarmama
[11/03 5:31 pm] salmah💍💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*-17
By
Maryam yarmama

*After a long break yarmama is back,for the countinuty of this novel,my fans thanks you for ur patience*


Minal tace ayyah yanzu hajiya tafiya zasuyi,sune fa yanzu gatanmu,ya takene abba ya tafi,umma bawanda yasan inda take,su hajiya zasu tafi,shikenan namu ya kare mun zama marayu karfi da yaji,bamu da kowa


Annur ne ya bankado labulen ya shigo yace anty ki daina kuka kuna dani ni jarumine,innayi kudi zan siya miki mota


Aziza tayi dariya tace nifa annur

Annur ya noke kai yace a a banda ke ke,bakya dariya saina mugunta


Aziza dariya takarasa saki tace oh munada catoom a gidannan,tabbas annur shine farin cikinmu yanzu,yusif kona bugamai waya bata shiga,inagama a black list yasani


Annur yace anty anty ki koyamin a.b.c d

Aziza tace a a nidai kace minal ta koyama badai niba,ni bacci nakeji


Annur ya murtuke fuska yace anty dama kinzone ki cinye mana abincinmune?to bamu yardaba ki tashi ki koma gidanku

Minal tace a a yar uwatace anan zata zauna tare damu

By
Maryam yarmama
[11/03 5:31 pm] salmah💍💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*-18
By
Maryam yarmama



Annur yayi murmushi yace hmmmm anty dafatan ba taci kamar shanuko

Aziza tace aini buhun shinkafa nakeci arana
Kuma acikina yake dafuwa


Annur ya zaro ido yace anty mekike nufi kina nufin hadiyewa kikeyi kamar gara iye kai anty ki dai rageci


Aziza tayi bamza dashi tayi kwanciyarta,minal ma ji tayi tanajin bacci itama ta haye kan gado ta kwanta


Annur ya tsaya ya kurawa kyakyawar fuskar minal ido,yana godiya ga Allah,dariya ya kece dashi

Kuka ya fara kuma yana anty yunwa nakeji zanci abinci anty zanci abinci


Aziza ta tashi tace ohhjj kaidai kafiya takura wollah,zama kusa dakai gwanda zama kusa da toilet

Annur ya dinga ihu wayyo anty minal,ki tashi ta kirani da mahaukaci


Minal ce tatashi ta fara aikin lallashi tace haba nawan jaruman maza basa kuka,ka koyi juriya


Annur kokari ya fara ya tare kukan,amma chan ya kara fashewa da kuka yace anty anty bazaki gane bane,buhun shinkafarmu nake tunani,yanzu muka yi bacci,anty zata hadiye,niko wallahi bazanci tuwoba

Fashewa da dariya su minal sukayi harda tafi minal tace ai bazata cinyeba,tasanni zaneta zanyi sosai

Ka kwanta anjima na dafa mana shinkafa mai dadi



Dariya annur ya fashe dashi ,ya rufe ido da tafukayen hannunsa,ys fita a guje kamar zai tashi sama


:::::::::::::::;;;;;::::::::::::;::;;;;
Abbane zaune awajen boka yana fadin ya bokana kamar yanda nayi sanadiyar mutuwar babansu ,nawa uwarsu kuruciya tabi duniya,ta shige daji,nasasu sukayi bakin jini,nasa kanwar ta auri mahaukaci
To haka nakeso awa fitsararriyar nan asiri,duk wanda ya nufeta da niyyar auranta fuskarta sai ya zamemai wata dodanniya,kuma inason tayi bakin jini awajen kowa,inason dukansu daga ita har yar uwarta suyi bakin jini kowa yakisu


Kyakyalewa da dariya bokan yayi yace angama kasan yaran akwai ibada,inason ka debo kasar kabarin mahaifinsu da gashin yaran,in sunyi tsifa sun taje sai ka dakko warin takalminsu,shikenan an gama,zasuga bakin cikin da basu taba ganiba a rayuwarsu;a wahala zasu kare


Abba yace gaskiya saidai kasa aljani kamus ya dakko amma ni bazan iyaba

Boka ya sheke da dariya yace wannan ba damuwa bace,ajiye kudi kaga aiki da cikawa.


Damin kudi abba ya aje yana murmushin mugunta,



By
Maryam yarmama
[11/03 5:31 pm] salmah💍💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYYAYEN MASOYI🦁*-19→20
By
Maryam yarmama

Minal ce zaune a tsakar gida tanawa wa aziza tsifa,tajewa aziza kai takeyi,wata guguwa ta taho,gari yayi bakikirin
Takalminsu da gashin dasuka taje yayi sama,

Aziza da gudu tayi daki,yayinda minal taja baya bakinta ya furta ayoyi

A hankali guguwar ta lafa ,ta tafi da takalmarsu


Aziza ta fito daga daki tace minal kenan ta tafi da takalmarmu lalle da sake wannan guguwa haka

Minal tace hmmmmm Allah zaimana maganin komai,zomuci gaba da tsifar da mukeyi saimu dora girki


Wani almajirine yazo yayi sallama wai aziza tazo inji yusif

Ihun murna aziza tayi tace da gaske?

Yaron yace eh
Tace jeka cemai ina zuwa,kawai yanzu shafshaf


Aziza ta shiga cikin dakin tasa hijjab ta shafa hoda daman lebe

Minal ma murmushin murna take tana kallon yar uwarta yanda take dokin,ganin sahibinta tace Allah yasa a fita asa,a


Aziza tana taku daidai tana fita taci karo da yusif.

Yusif kara yasaki yanufi mota da gudu,ya ja da karfi yabar layin

Ran aziza ya bace tace aha,yusif dama zuwa yayi yamin wulakanci lallema bari inkirashi


Daukar wayarta tayi ta kirasa bugu daya ya dauka,
Aziza ta haushi da masifa yusif wannan wani irin wulakancine daga ganina saika kama guduwa saikace kaga dodo

Yusif yace haba aziza yazakiyimin wasa da fuskar dodanni ba kyan gani


Aziza ta cika fal da mamaki tace wallahi ba abinda nasa a fuskata ina ganin gizo nama


Yusif yace wannan ba gizo bane gaskiya indai hakane to kina da shafar aljanu


Aziza tawani lankayo ashar ta duramai tace yusif inkasamu wata basai ka tsaya kanamin wulakanciba,


Yusif yace bawa minal wayar nasan zatafi fuskantata

Gida azixa tashiga ta mikawa minal wayar a sanyaye,tace yar uwa gashi inji yusif


Minal ta amsa bayan gaisuwa yusif ya kora mata bayani

Mamaki ya cika minal ta tuna mafarkin datayi da abba shekaran jiya ya biyosu da wuka yana nuna aziza itada samun aure har abada,sudajin dady har abada


Kashe wayar minal tayi tana zubda hawaye ta kwashe mafarkin datayi ta gayawa aziza

Wani ihu aziza tayi tace shikenan burin abba yacika ya lalata mana rayuwa,aziza tashiga daki ta dakko kalanzir a galan,ga maganin kwari a hannunta


Minal ta kuka ta tashe tsaye ta tashi tace yar uwa mezakiyi,dashi

Ran aziza a bace tace sha zanyi inmutu in huta da wannan wahalar,wai me mukayiwa abba bayason ganinmu iyeh,wallahi gwanda nasha kalanzir na mutu,in huta,galan ta dauka ta kafa abakinta tanata kwankwada.


Ihu minal tafara ta taho da gudu,amma tayi latti aziza ta sha mai isharta,tafadi akasa kumfa na fita abakinta.


Kuka minal tasa tana aziza karki mutu kibarni awannan duniyar,mu biyu muka rage aziza ,,jama,a taimako yar uwata

Da gudu ta tashi da niyyar fita karo sukaci da wani yaro,hannunsa rike da madara caton yace wai gashi inji *boyayyen masoyi*


Ayar tambaya shin wanene boyayyen masoyinman mai taimakansu,
Shin aziza tamutune?

Jama,a labari yanzu aka soma kuta bibiyarmu


By
Maryam yarmama
[11/03 5:31 pm] salmah💍💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYYAYEN MASOYI🦁*
By
Maryam yarmama

Minal ce zaune a tsakar gida tanawa wa aziza tsifa,tajewa aziza kai takeyi,wata guguwa ta taho,gari yayi bakikirin
Takalminsu da gashin dasuka taje yayi sama,

Aziza da gudu tayi daki,yayinda minal taja baya bakinta ya furta ayoyi

A hankali guguwar ta lafa ,ta tafi da takalmarsu


Aziza ta fito daga daki tace minal kenan ta tafi da takalmarmu lalle da sake wannan guguwa haka

Minal tace hmmmmm Allah zaimana maganin komai,zomuci gaba da tsifar da mukeyi saimu dora girki


Wani almajirine yazo yayi sallama wai aziza tazo inji yusif

Ihun murna aziza tayi tace da gaske?

Yaron yace eh
Tace jeka cemai ina zuwa,kawai yanzu shafshaf


Aziza ta shiga cikin dakin tasa hijjab ta shafa hoda daman lebe

Minal ma murmushin murna take tana kallon yar uwarta yanda take dokin,ganin sahibinta tace Allah yasa a fita asa,a


Aziza tana taku daidai tana fita taci karo da yusif.

Yusif kara yasaki yanufi mota da gudu,ya ja da karfi yabar layin

Ran aziza ya bace tace aha,yusif dama zuwa yayi yamin wulakanci lallema bari inkirashi


Daukar wayarta tayi ta kirasa bugu daya ya dauka,
Aziza ta haushi da masifa yusif wannan wani irin wulakancine daga ganina saika kama guduwa saikace kaga dodo

Yusif yace haba aziza yazakiyimin wasa da fuskar dodanni ba kyan gani


Aziza ta cika fal da mamaki tace wallahi ba abinda nasa a fuskata ina ganin gizo nama


Yusif yace wannan ba gizo bane gaskiya indai hakane to kina da shafar aljanu


Aziza tawani lankayo ashar ta duramai tace yusif inkasamu wata basai ka tsaya kanamin wulakanciba,


Yusif yace bawa minal wayar nasan zatafi fuskantata

Gida azixa tashiga ta mikawa minal wayar a sanyaye,tace yar uwa gashi inji yusif


Minal ta amsa bayan gaisuwa yusif ya kora mata bayani

Mamaki ya cika minal ta tuna mafarkin datayi da abba shekaran jiya ya biyosu da wuka yana nuna aziza itada samun aure har abada,sudajin dady har abada


Kashe wayar minal tayi tana zubda hawaye ta kwashe mafarkin datayi ta gayawa aziza

Wani ihu aziza tayi tace shikenan burin abba yacika ya lalata mana rayuwa,aziza tashiga daki ta dakko kalanzir a galan,ga maganin kwari a hannunta


Minal ta kuka ta tashe tsaye ta tashi tace yar uwa mezakiyi,dashi

Ran aziza a bace tace sha zanyi inmutu in huta da wannan wahalar,wai me mukayiwa abba bayason ganinmu iyeh,wallahi gwanda nasha kalanzir na mutu,in huta,galan ta dauka ta kafa abakinta tanata kwankwada.


Ihu minal tafara ta taho da gudu,amma tayi latti aziza ta sha mai isharta,tafadi akasa kumfa na fita abakinta.


Kuka minal tasa tana aziza karki mutu kibarni awannan duniyar,mu biyu muka rage aziza ,,jama,a taimako yar uwata

Da gudu ta tashi da niyyar fita karo sukaci da wani yaro,hannunsa rike da madara caton yace wai gashi inji *boyayyen masoyi*


Ayar tambaya shin wanene boyayyen masoyinman mai taimakansu,
Shin aziza tamutune?

Jama,a labari yanzu aka soma kuta bibiyarmu


By
Maryam yarmama
[12/03 9:33 pm] salmah💍💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*26-30
BY MARYAM YARMAMA

_IN DEDICATION TO_
*MY BESTY SALMA*




aziza ta dauki kudin taje ta biya,

Akayi treating din minal,
Minal ta shafe saati uku tana jinya,kamar bazatayi raiba
Itadai burinta taga. Sanyi idaniyanta annur


Aziza tayi fadan tagaji,ta fidda damuwa,ahaka aka sallamesu

Abin mamaki suna dawowa gidasukaga gidan ya kone kurumus


Minal da azizasuka fashe da kuka dasuka shiga gidan sukaga komai ya kone

Minal ta dora hannu aka tace nashiga uku annur dina

Harara aziza ta dankara mata tace kekika damu dawani annur ni ta kayana nake


Minal tace haka aziza raifa akace miki,ko kiyashima yana darai balle mutum,niban damu da in rasa rainaba indai annur zairayu wannan ba matsalata bane,kafin ta karasa maganar ta taga yara suna shigowa dadirka dirkan akwatuna guda hudu,ga kayan masurufi da sauransu

Ajewa suka farayi ,minal tace kuko wani irin sabani kukayi haka?

Dayan yaron yace basabani mukayi ba wanine waishi boyayyen masoyi yace in kawo muku

Dayan yaron yamika wasikar yace wai gashima yace abawa wata minal


Sahannu minal tayi ta ansa,ta sallami yaran,bubbude kayan sukafarayi,kayanemasu shegen kyau adinke suke,ko wanne da gyallensa,harda bedshit

Rawaa azizata fara tana murna,yayinda minal tayi tsaki tace aini bai burgeniba.



Fara karanta wasikar tayi kamar haka
Assalamu alaikum


Kiyi hakuri dear natafi da mijinki,amai aikin kwakwalwa nanda sati biyu zan dawo miki da mijinki;lafiya kalau,saiya sakeki ni in aureki


Kuka minal tasatace. Wallahi bawanda ya isa ya rabani da mijina har abada,

Aziza dariya ta sheke dashi tace aigwanda ki auri *boyayyen masoyi* ya fiye miki alkhairi akan wannan mahaukacin,ki godewa Allah ma yamiki hallaci

Minal tace wallahi ba abinda. Yamin wani hallaci yamin bayan yarabani da abin kaunata?



Kwalin chocolate aziza ta bude ta dauki daya ta faraci tana santi



Yayinda minal tayi tsaki tayi tagumi.



Aziza tace inmazaki dauka ki dauka kici inta mutuwane mu mutu tare.



Minal tayi. Rau rau da ido itama ta dauka suka. Dinga ci.

Shigar dakayan sukayi daki,suka kulle,dakin suka fito tsakar gida kamar sunsan abba zaizo
Suna hira abba,ya shigo gidan yana tafiyar kasaita


Kallo daya sukamai kowacce ta dauke kai,aziza harda guntun tsakinta


Abba yace,to shedanun bariki saiku shirya kubar gidannan domin nasiyesa zan gyarasa sabuwar amarya zanyi



Aziza tace kutumar chan wai abba mai mukama bakason ,kaga mundan fake,kafiso mu zauna atitin Allah to wallahi kayi karya ubangiji Allah yafi karfinka tsohon najadu

Tattabata minal take alamun tayi shiru aziza tace ke dallah sokuwa kyaleni inciwa wannan wanda yafi fir,auna muganci mutunci kuma in kwana lfy ,kasan ba tsoranka mukejiba wallahi ko yanzu akan wuka saina lumama



Tafi abba yayi yace good niko nayi rantsuwa saina ga bayanku,keda aure har abada,kekuma minal ke dajin dadi kinyi hannun riga dashi


Minal ta fashe da kuka ta durkusa tana ta rokan Allah ya yaye masu bakin cikinan


Yayinda aziza ta dauki tabarwa tawani duro uwar ashar ta nufi wajen abba ta kwalamai akafa

Ihu abba yasa yayinda aziza ta kara kwalamai akafa tace bari in karya kafar zuwa gidan boka,


Da gudu abba ya fice rai abace aziza ta nufi daki tana kuka

Minal ce tashigo tace aziza meye kike kuka


Aziza ta hargitsa gashin ganta tace minal bazaki gane yanda nakeji bane naso ace na kashe abba a take inyaso nima a kasheni


Subhanallah minal ke fadi tace haba aziza ki dinga sawa ranki ruwan sanyi,mekike ci nabaka na zuba,karki manta watara sai labari ,God time is the best


By
Maryam yarmama
[12/03 9:33 pm] salmah💍💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*31-35
By
Maryam yarmama

This page goes to my unique fans,i gave you a vote of thanks for ur love and caring about this novel






Aziza ta share hawayenta tace shikenan yar uwa nabarwa Allah,in umma ta raye Allah ya bayyanata
Minal tace ameen sannan ta dora da ya Allahu,ya rabbi mai sammai da kassai,mai kowa da komai,ina rokanka da sunanka tsarkaka kuma kyawawa,ka kare umma duk take,in tana raye ka bayyanata,inya mutu ya ubangiji ka mata rahama kasadamu da ita a aljannah firdaus,ya ubangiji ya Allah ka nuna ikonka akan mijina ka warkar dashi,kabawa aziza miji nagari wanda zaizamo gatanta nikuma ina rokanka ka dawomin da mijina




Shafa sukayi a tare,yayinda ,aziza ta fara danne danne awayarta,a group dinsu sai hirar prince ake



Kullum minal cikin kuka take Allah ya dawo mata da mijinta lfy


Kwatsam tana zaune atsakar gida tana zaune ta wanke kayanta ,wani yaro yashigo ya bata wasika ya tafi,karba tayi ta fara karantawa

*daga boyayyen masoyi*

_ki godewa Allah mijinki ya warke_
_garau yake yanzu,sai sunanki yake ta ambata_
_gaskiya yana masifar sonki, sati daya masu zuwa zai dawo,don haka ki dingacin abinci ki maida jikinki,kiyi kwalyar tarbarsa_

Minal bata karasa karanta wasikarba tayi ihun murna,aziza dake chatting ta fito tana tambayar meye faru?


Rungume aziza minal tayi tana wayyo dady kasheni annur ya warke ya warke nanda sati daya zai dawo


Itama aziza cike da murna tace dan Allah kai Allah abin godiya,wayayi wannan sai Allah


Minal tace kwarai kwarai farincikina yadawo amma naso umma tananan


Nan jikinsu yayi sanyi, aziza tace Allah yabamu hakurin jure rashin umma


Minal tace ameen yar uwa


Minal mikewa tsaye tayi tana ta adu,a dacin abinci tayi kyau,da kiba tayi bul da ita



Saura kwana daya mahaukacin masoyi yadawo,minal anje an shiga saloon anyi gyara,anyi lalle


Tayi masifar kyau,tun dare suka fara toye toye,dama akwai raguwar kudin da boyayyen masoyi yabasu


Minal sai walwala take jira take gari ya waye,amma daren yayi nisa


Aziza sai tsokanarta take amaryar annur ,sai doki kike


Minal tace nadole inyi dokiba inason in ji muryar mijina,muyi magana mai dadi ta fahimta,mu shaku da juna,annur din da da yanzu ba daya bane;annur din da yaro karami ne but annur din yanzu babban mutum ne mai hangen nesa



Dariya aziza ta sheke dashi tace lalle kam


By
Maryam yarmamat
[12/03 9:33 pm] salmah💍💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*36-40

By
Maryam yarmama
*DEDICATED TO*

_SALMA ALI WADAH_♥





Yau take sallah awajen minal,ta chaba ado cikin wani material mai shegen kyau


Itama aziza taci kwalya cikin wata atampa an kashe dauri

Minal tun safe take zuba idon ganin annur,harta fara fidda rai da zuwansa,harta fara fitar da kwallah
Aziza tace ke meye haka saikin bata kwalyarki?


Kara da horn din mota taji

Hadadden gayene yafito a motar ya nufo gidansu minal


Tsaye yake kekem ,suit ne blue ajikinsa,yayi masifar kyau,
Tashi minal tayi kamar tasha ruwa akasa

Miko mata hannu annur yayi alamun tazo

Kunyane ya rufe minal a hankali ta taho ta shige jikinsa ta fashe da kuka mai tsuma zuciya

Kara

Please Login or Register in order to submit comment