Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na yafe maka, annur dake zaune a gefe da safwan a wani taburmar cikin murmushi ya kalli minal yana godiya a ranshi BISA wannan babbar kyautar ...

Abba Godiya yayi yayinda ya kalli Aziza dake ta faman harararsa tana tsaki kamr ta dokeshi takeji yace"Aziza na cutar da rayuwarku, nasan kona mutu bazan sami rahamar ubangijiba "..cunno baki Aziza tayi tana"yo ai wannan tsakanikane da ubangiji, Amma nikam bazan taba yafewa macuci irinka ba, kuma Allah ya isa bamu yafeba, duk abinda kayimin kabuga kirji kace bazamu cigaba ba, yo yanzu kirjin waye yake ciwo... Gashi kafara gani, kaine ka daurawa minal auren mahaukaci domin mu tozarta, Amma Albishirinka ka tona ramin mugunta ka fada aciki, kullim tunaninka yanda zaka kuntatawa marayun Allah, gsshi yadawo kanka domin mijin minal dan sarkine kuma jinin sarauta, kuma dan wasan kallo na africa ne... Sannan nikuma ina auran shararren doctor wanda ya shahara ciki da wajen kasa, to yanzu daka buga kirji kace saidai mu kare a karuwanci da kaskantarcyar rayuwa, tsakaninmu dakai waye yanzu yake jin jiki... Nikam wallahi ban yafe makaba, kuka aziza ta fashe dashi yayinda ta kalli umma tace"umma kiyi hakuri idan harna bata miki rai, inajin zafi a raina akan abinda mutumin nan yayi mana.....

Jinjina kai umma tayi tana"Aziza nayi tafiya ta kwana daya baci basha, kafafuna sun kunbura, hankalina ya gushe, karshe wasu yar rugane suka tsinceni, sukatayimin magani, harna warke kullum, kuka nake ina kiran sunanku kuda minal, karshe dai dana gama warkewa, nace zan taho kana, dakyar suka barni nataho nakarbi addreshinsu inda suke, zuwana gidan nan shine nagasu abba sukecemin basu san inda kuke ba... Nandai nafadi na suma! Karshe dai na hakura ina adu'ar Allah yadawomin daku duk inda muke, ni kaina na yafewa abba ko bakomai yaci darajar abbanku daya rikeni amana".... Nan kowa yadau kuka, mama tana kuka itama ta dinga rokar gafara

Aziza ce ta juyo ta Kali mama tace"ai mama kece da abin kuka yanzu, kuma duk dan hakkin daka raina shi zai tone maka ido, mamah billionaire nake aure yanda KUKAYi fata ba haka ya kasance ba.....
Su lubaba da haseeyan da kuka dau buri a kansu ina musu fatan Allah ya sakasu a danshinmu... Kasa dakai mama tayi gumi yafasa zubo mata, ba shiri takarajin cikin yabada wani sauti kurrrrrr, nadamar abinda tayi takeyi nan tafashe da kuka ta tashi tadau buta tayi bandaki ta dinga zawo 😂😂shikam safwan tsiwar matarshi Aziza ne yake burgeshi



Nan dai umma takara yiwa Aziza fada domin tasan halinta tun tana yarinya da lafiya nan dai aka yafewa juna... Inda har hira ta barke tsakaninsu, har Abba ya tsomo baki, anata raha...

Su annur ne, suka koma gefe sukayi shawarar fitar da abba waje.... Da su Abba sukaji lamarin, nan Abba ya fara matsar hawaye yana "ai da baku wahalar da kankuba, da kun barni na mutu... Nan dai suka dinga kwantar mai da hankali.... Inda nan take safwaan ya Kira masu aikin Gina, inda za'a rushe gidan ayi ginin zamani... Kukan kunya mama ta dingayi tana godiya, inda su aziza dasu lubaba ana gefe ana hirar bayan rabuwa, har luba take basu labarin abinda yafaru...... annur dake tsaye sai ido yakewa minal da su taso su koma masaukinsu ya gaji.... Kamar umma tana zuciyanshi ta kalli minal da Aziza tace "yakamata Kuje ku huta, saboda gajiyar hanya, Aziza kamar jira take dama umma tayi magana, inda tayi wuf ta tashi tana eh umma nima barci nakeji, minal kuma tace"Aini umma yau a wajenki zan kwana"...... Dakuwa umma tayi mata tace "tunda ni kike aureba... Kibi mijinki... A hankali ta tashi, su luba aka rakosu kofar gida har wani yanga ake, dama tuni sun kashe sugar awarar sukayi sadaka... Nan dai minal suka shige mota... Luba ta mika mata Malika dake barci tace "sister minal bazaki barmin daughter dina ta kwana anan"..... Annur ne ya chafe cikin sarauta yace"ina, diyata bazata iya kwana mosquito ya cizeta ba ... Just gobe zamu dawo ai karku damu, nan ya dakko kudi masu yawa yabasu, suyi cefenan yau.... Sallama sukayi, suka wuce masaukinsu, dama guest house ne ... Inda minal tana zuwa ta kwantar da malika, ta hada musu ruwan wanka, suka shiga wanka tare..... Suna fitowa ta shafa mishi mai, ta taje mishi kai, sannan ta fito mishi da kana nun kaya, itama dressing tayi cikin wani gown mara nauyi... Annur tsaye yake jikin madubi yana murmushi... Inda minal ta rungumoshi ta baya tana "thanks you sweetheart for everything, samunka a rayuwa alkhairi ne, nagode da abubuwan da kayimin a rayuwa... Ashe kaine mahaukaci kuma BOYAYYEN MASOYI, wonderful... Ubangiji Allah ya biyaka da gidan Aljanna lalle, nayi dacen miji, mr blue eyes, now nazama MRS ANNUR, KUMA MAMAN MALIKA,.... murmushi annur yayi ya juya ya rungumeta yana fadin "ni nayi dacen mata kamila, mai tausayi, mai tafiya, komai Allah yabaki.... Ubangiji Allah ya barmu tare, inason mu rayu tare mu mutu tare baby...... Hawaye minal tafara, itama ta rungumeshi tsam.... Nan labari yasha bam bam.... 🏃‍♀️🏃‍♀️basu farka ba sai da sukaji kukan Malika. Kowa so yake ya dauketa.. Annur ne ya goya malika... Yana lallashi, inda minal ta zauna tana mishi dariya🤣🤣🤣.....


****†"


Abubuwa sun faru, an Gina wa Abba tamfatsesen gida a cikin kwana, sannan harda rasuwar Abba ana gobe za' a tafi dashi india... Kuma a ranar luba ta gigice ta haifi danta namiji.... Nan hankali ya tashi, yan uwansu Abba sunzo dai koke-koke suke, inda sukaga su minal, nan kunya ya dinga kamasu... Gida yacika da su minal anata karbar gaisuwa, harsu Maman marayu dasu iyayen safwan duk sunzo.... Aziza kuwa saida ta wanke yan uwan babanta da soso da sabulu, wasu harda kuka, dakyar umma ta basu hakuri... Sannan tasa aziza a daki, tayi mata fada.... Minal ce ke kula da luba,saida akayi sadakar bakwai sannan kowa ya watse,wanda wasu yan kauye sun ga gida sukace ai sufa sunzo bazasu komaba, mama ce ta koresu, inda minal tace zasu dau umma su tafi da ita, umma tace subarta anan... Zasu zauna da mama dasu lubaba... Annur ne yasamo yan aiki guda biyu da tsohuwa da budurwa, sannan da maigadi, aka siya mota, aka nemi driver zai dinga zansu mama duk inda zasuje... Nan sabon kuka yadawo.... Godiya kam ba wacce ba'ayiba.......

Minal saida suka nemo inda MUTANEN da suka taimaki umma suke, sukayi musu Alkhairi mai tarin yawa.. Sannan ta nemo gidansu kawarta ummi, shima annur ya Gina wa Maman ummi dankareren gida, sannan yabawa ummi jari, tana gidan mijinta da tsohon cikinta......

Minal da aziza anzama manyan mata, inda sukasa taimakon marayu da marasa karfi agaba... Inda suka dau umma, sukaje umrah daganan suka wuce wajen danginta sunyi murna sosai da GANINSU... Nanma minal yayi musu abin alkhairi
*TARIHIN ANNUR*
(Kiyi hakuri, ina sane bansa da wuriba)

Annur da daya tilo a wajen sarkin zaria..... Wato mai martaba sultan abdullah.Wanda shima gada yayi a wajen mahaifinshi Dayake duk yan uwanshi matane, kuma shine dan fari.. Annur yayi karatunsa a UK.... Baisan komai kan sarauta ba, yafi maida hankalinsa akan kwallon kafa inda yayi suna... Kuma ya karbi lambar yabo.... Annur mutumin kirkine, kuma mai tausayi ya gado kyawun mamanshi wacce ta kasance yar gidan sarautar Agadaz... Yar dangi kyakyawa sunanta Hauwa... Ga kyawun hali.... Duk shima mai martaba yanada nashi kyawun
Mai martaba ya hada auren annur da saudat yar sarkin gombe.wanda saudat tanada shekara 26 a lokacin, tanada Jikin girma, kyakyawace ba laifi . Dayake tun suna yara sukayi alkawarin aurar dasu, annur shi bayaso, saboda tun yana yaro, yasan saudat bata da junta amma haka yabi umarnin iyaye, ita kuma saudat tana mutuwar sonsa. . amma batada Halin kirki ko kadan ga nuna tsanar talaka da bakin kishi.... Kuma batason yara.... Haka ta tashan kwayoyi tana zubar da cikin, tun annur yana kokarin cusata a ranshi, harts fice mishi a rai, Domingo fitsararta, shiyasa yadau alwashin auren yan talaka, .... Rayuwar annur ya canza lokacin da yaje kano ya tsalla ido yaga minal, nan yace zai iyayin komai don sonta, don kuma ya zauna da ita.... Haka yasa kanshi a hauka, ko bikin luba shine prince din da akata Kira yazo baizo ba... Saboda lokacin bayason asirinsa ya tonu... Duk lokacin dayaga minal sai ya canza kayansa zuwa mahaukaci, tana tafiya zai dawo normal... Hatta kudi ya bawa yara suyi masa wakar hauka..... Kuma shine boyayyen masoyin nan.......


*Bayan shekara uku*

Minal tanada yara uku Malika da twins Sultan da imran inda sukaci sunansu mahaifin annur amma suna cewa sultan, yerima while imran kumma Abba.. Kyawawan yara dasu... Lokacin haifuwarsu, har hawaye annur yayi da yake rike hannunta tana nakuda, sai cewa yake thank you baby, Allah yayi miki Albarka...... Yanzu dai dukansu suna gudunsu ko 'ina...... Inda yaran sunfi jin turanci ma... Aziza ma tanada yaranta biyu mata duka... Fatima da Hindu.... Rayuwarsu suke cike da sha'awa... Dangin safwan suna son Aziza duk da tanada fada har yanzu.... Don ita bata barin ta kwana.... Suna kula dasu ummah da gidansu amaru.... Inda suka dawo da umma da mamah abuja, suke zaune a dankararren gida harda masu aikinsu... Da wasu yan uwan mamah.... Rayuwa tayi dadi....

Minal tazama babbar mace, inda taso komowa makaranta amma fafur annur ya hanata.... Wai sunada kudi Tunda tanada ilimin karatu da rubutu ai shikenan... Business kawai takeyi wanda suka hada hannun jari da Aziza suka bude kamfanin takalmi da kaka, wanda yayi fice daga Nigeria har kasar waje.....

Su luba ma duk sunyi aure, suna zaune a kano... Suma annur da safwan sun bash jari....


Annur da minal suka aje yaransu a Gidan mommy, suka tafi honeymoon kasar germany.... Inda suke ta dizzar soyayyarsu tamkar sababbin amare... Ko rabuwa da juna baso so suyi... Kullum suna makale da juna, suyita daukar selfie da videos.... Hatta kitso annur yake zama yayiwa minal...... Sai da minal tafara laulayi sannan suka dawo gida Nigeria..... Annur ne yake kula da ita... Har takai watan haihuwarta ta haifo diyarta santalleliyar mace inda taci sunar momyn annur hauwa... Suna ce mata "beauty"..... Suna kam anyi taron suna, inda anyi gayyata..hardasu saudat, da tayi wani auren Amma ba haihuwa, kuma cikin kishiyoyi take, sai gori suke mata. Nan minal takara suna taxama tauraruwa wanda matan gwamnoni da ministoci suke son kulla Alakar kawance da ita.....
Duka family dinsu sukaje umrah, sukayi wasu Abba adu'a, sannan sukaci gaba da taimakon Gidan marayu....


Rayuwa suke cike da so da kauna.... Inda nake musu fatan dorewa har abada......



Alhmdlh
*nan na kawo karshen littafin mahaukaci ko boyayyen masoyi, inda nayi kuskure, ubangiji Allah ka yafemin*
Allah yasa sakon da yake ciki ya isa inda Akeso...

*MASOYA INA GODIYA, DA BAZARKU NA TAKA RAWA.... KUMA NAGODE BISA ADU'OINKU.... NAGODE BISA KAUNAR DA KUKA NUNAWA LITTAFIN NAN... WANDA YADAU LOKACI, KUKAYI HAKURI KUKE BIBIYATA... HARDA MASU KIRANA A WAYA DA WAYANDA NA GA KYATUTUKAN JIN DADI DA BAJINTA, WALLAHI BANSAN Hka littafin nan yayi suna ba har yafita kashashen waje, har kirana mutane daga chad! Cameroon, ghana, 🇳🇪 niger, da dai sauransu.... Nagode Allah ya bar zumunci, sai kun kara kina a sabon littafina mai suna "LOKACINE"
(Rikicin cikin gida) Labari wanda yasha babban da sauran litattafaina... Is coming very soon......

Ga MASU fatan Alkhairi ga num 07030772637
Pls a dinga sharing, saboda WAYANDA suke neman complete samu nagode



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment