Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sati biyu acell dan ubanta, jarabar nan tata ya isheni a gida... Masifar yau daban gobe daban


Mamaki yahana minal magana sai zaro ido take yawunta yakafe tama rasa me zatace



Annur yatashi saudat ya tallafeta suka nufi toilet ta gaggayara jikinta tana kukan karyar zubewar cikinta.



Ran annur yakare bacewa yakira policawa akayi arrest din minal data kasa kukama sai kukan zuciya


Ran saudat yayi fari kal ,tanacin karenta ba babbaka,bayan sati biyu saudat ta takurawa annur yaje yayi belling ta

Saudat har daki ta biyota tace oh su salihai ansha zaman cell
Murmushin takaici minal tayi tace kisani aunty duk abinda kashuka shi zaka girba komin daran dadewa gaskiya zaiyi halinta ko bana numfashi aduniya zamu tsaya agaban Allah yamana hissabi tsakanina dake



Tsawa saudat tadaka mata tace yimun shiru jaka aladiya dabba munanan dake ni yar jinin sarautace donhaka mu family dinmu ba,a mana kishiya asannu zanfuddaki daga gidan annur in mallake annur da dukiyarsa gabaki daya










Haka minal ta dinga fama a gidan sharrin yau daban nagobe daban har cikinta yakai wata bakwai lokacin damuna ne. kullum cikin yi mata azaba suke,tarame tayi baki ,kullum cikin tunani da damuwa take,ranar tana fitowa daga wanka daure da tawul da katon hijab

Mutumin ranar tagani azaune dagashi sai singlet akan gadonta yace babyna ykk

Cikin mamaki minal tace wai menama bawan Allah kakeson shiga rayuwata



Annur ne yashigo da belt yana dan ubanta ina take saudat tana biye dashi,mutumin yana ganin haka yabi ta dayan gefe yafita aguje


Annur yace lalle minal kin tabbata yar iska to wallahi yau sainamiki abinda bazaki manta daniba




Minal tana kuka tace annur ka yarda dani wallahi bansan wani namiji arayuwataba inbakaiba wallahi bansanshiba


Saukar duka tadingaji ajikinta ihu take gami dagare jikinta,wani wawan duka annur yamata aciki,saudat kokari take a kashe abinda yake cikinta

Annur yace minal bazan iya zama dakeba nasakeki saki daya


Minal taji cikinta ya murde wani azababben ciwon mara yakamata,kara tasaki

Saudat data fuskanci minal nakuda ne yakamata da kissa taja annur suka fita daga dakin suka banko mata kofa



Nakuda mai tsanani minal take tana ihun neman ceto dariyarsu takeji a main falo,haka minal tanajan gwiwa ta je wajen sif tadauki reza din data tanada ,tanajan ciki tanufi toilet sai nishi take

Kaffara tayi jariraya santalelliya ta fado kyakyawa da ita,cancara kuka tadingayi,mahaifa mata fado,minal tagyara jaririyar tadora ruwa zafi tamata wanka tasamata kayan da annur yasiya guda daya tal,awani super market dasukaje
Dama yace a dubai za,akawo kayan jaririyar


Wanka minal tayi,tafara harhada kayanta tana kuka,


Wani zoben gwal tadakko tasawa jaririyar ahannu,ta nanadeta a shawul


Minal ta dauki jaririyarta ta sa mahaifar a leda babba,tagyara dakin tsaf


Tanajin kaunar jaririyar harcikin kogon ranta ta dauketa ko tsinke minal bata dauka gidanba kuka take tazo ta iskesu afalo




Annur dayaji kukan yar ji yayi kamar ya kwaceta ahannun minal danso


Saude ta kalli minal tace ashe an haifar mana shegiya ko shege agida to a kaita gidan ubanta in bata da uba a nufi gidan marayu

Minal tace hmmm saudat kenan burinki yacika nabarmiki gida yanzu meye ribarki ,kaikuma annur sai nangaba zaka gane gaskiya inka shirya nemana saika nemeni kazo ka karbi yarka inkuma ka yafe na rungumi kaddara in riketa.


Tafiya tafarayi,annur jiyake kamar yadawo da ita ya anshi yar Amma daya tuna wani


Amma tayi nisa,tafiya minal take a tsakiyar dare shiru,ga hadari ya hadu yayi baki kirin


Kuka minal tasa tana ya Allah ka dubeni da idon rahama ,ya Allah ka taimakemu



Ruwa aka barke dashi tamkar bakin kwarya,jaririyar sai cancara kuka take

Kuka minal take tana adu,ar Allahya kawo musu agaji


Kwatsam saiga mai adaidaitasau ya haskesu da fitila,tsayar dashi tayi tace gidan marayu zaka kaini


Dasauri tashiga,sai rawar sanyi take ,muryar jaririyar ya dashe takasa kuka da alamu mura ya kamata

Rudewa minal tayi aiko mai adaidaitasan ya nufi gidan marayu da ita ,abakin gate din ya ajiyeta

Shiru tayitana tunanin ina zata samu kudi tabashi ,kamar mai adaidaitasahun yasani yace kibar kudin nasan ke marainiyace ku abin tausayawane


Godiya minal din tayi ta gaishe da securities din tace tanason a kaita office din shugabar gidan marayu



Aiko wani hadadden office aka kaita,wata hadaddiyar matace zaune sanye take da glass tana bawa wasu yara abinci abaki tana musu wasa,dago da kyawawan idanuwanta tayi,ta kafa akan minal tayi murmushi tace sannunki da zuwa baiwar Allah



Ahankali minal ta amsa mata tagaisheta zama tayi


Matar tace ke wacece meya kawoki gidan marayu




Labarin rayuwarta minal tabata,matar ta dunga zubar da kwallah ta karbi jaririyar tace wa minal daga yau kinzama yata karki damu zan kula dake sosai,zan gayawa duk wandayake gidannan ke yatace ,zan hadaki da kawaye nagari Du husna da khadijah suma marayune



Kuka minaltasaki tana godiya yayinda hajiya mairo takira docton yara akayi treating din jaririyar minal.



Watan minal biyu agidan marayu tacanza ta murmure,hajiya mairo ta maidata tamkar yarta ita take raba abincin marayu,kowa yana bala,in son minal






Wani hamshakin attajiri matashi yazo yana bawa yara dubu goma goma


Minal ce tafito suda hajiya mairo da sauran shugabannin gidan marayu da niyyar yimai godiya,yar minal da sukawa lakabi da malika tana hannun khadeeja yarinyar ga kyau dashiga rai sai dariya take da wangale baki tana kallon hajiya mairo



Dagowar da minal zatayi abin da kwakwalwarta yakawo mata shine *safwan*tabbas shine tsaye yana rabawa yara kudi ya kara kyau ya goge




Shima juyowar dazaiyi da mamaki a fuskarsa yagoge idonsa yace kamar minal masoyiyata nake gani






By
Ur perfect writter
Maryam yarmama[21/03 6:34 pm] salmah pinky💅🏼💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*71-75
By
Maryam yarmama

*IN DEDICATION TO*

_MY SALMA ALI WADAH_


_*MASOYANA KUYI HAKURI SAKAMAKON SHIRUN DA KUKEJI,KUNSAN SHA,ANIN JIKI DA JINI*_





malikace tafara cancara kuka,ansarta minal tayi ta jijjigata

Tunanin safwan ya tsaya cikin mamaki gami da tsoro da fargaba yace minal badai kinci amanata kinyi aureba,minal ina kikeso insa raina,to mai yakawoki gidan marayu ina umma da aziza?



Ihu minal tasa ta fashe da kuka

Hajiya mairo tace a a minal meye abin kuka tunda kinsansa saiki bashi amsa,kije wani wuri indai akwai sirri a tsakaninku



Safwan yace tabbas maman marayu akwai sirri a tsakanina nida minal munyi alkawarin aure da ita,kuma nazo naganta da ya'kuma sunyi kama sosai shiyasa abin ya dauremin kai


Hajiya mairo tace kabiyoni office akwai magana,hajiya mairo taja hannun minal dake shesshekar kuka suka nufi office,safwan yana biye dasu




Zama sukayi minal ta zauna a kujerar datake fuskantar safwan malika na sharbar barci acinyar hajiya mairo

Hajiya mairo tace alhaji safwan naji anacema gaskiya minal ta auri dansarki

Dafe kirji safwan yayi yace nashiga uku minal badai kinci amanataba yazanyi da rayuwata


Kuka minal tafashe dashi tafara bashi labari har batan umma


Safwan ya zubda kwallah ajiyar zuciya yayi ya durkusa agabanta yace minal dan Allah zaki aureni ?nayi alkawari ni zan zame uban yarnan,zan nuna miki gata zan taimaki rayuwarki zan nemo umma duk inda tashiga


Kuka minal take tana girgizakai tace bazan iya aurenkaba maza
Macutane .

Hajiya mairo tace haba minal da hankalinki da tunaninki,ki tuna aure ibadane,akwai wanda suka fiki shan wuya,inma baki auri safwanba,ai kuka hadu da wannan dan iskan tsohon mijinki zaiyi takamar shine dama wanda yake sanki


Safwan cikin kalan tausayi yace minal ki tausayamin kin san yau nakai shekara shida inadauke da sonki karkimin haka kitaimakamin kinji


Minal tana kuka tace safwan nagoge da kaunar daka nunamin,kayi hakuri kozan iya auranka sai malika tayi shekara biyu,kayi hakuri


Hajiya mairo takasa magana itama tana tausayawa minal,hawayene yakefita a idon safwan yatashi yana gogewa yafita yaje yadauka bandir bandir din kudi ya aje a teburin hajiya mairp yace maman marayu ga wannan dubu dari uku ne asiyawa malika madara da dubu dari biyu sannan dubu dari nakine


Godiya hajiya mairo tafara tana shimai albarka

Juyawa yayi da niyyar tafiya muryar minal yaji tace mallam kazo kadauki kudinka bama bukatar taimakon kowa yatace itakadai banson kowa yatabamin ita ni nasan wahalar danasha wajen haihuwarta

Murmushin takaici safwan yayi,yadawo yace,hmmmm minal kenan ashe kinada tsiwa


Minal tace eh inadashi kuma sanadinkune maza .


Safwan yace good ai shedanne yake mayar da hannun kyauta baya nidaina bawa yata bake nabawaba



Sallama sukayi da hajiya mairo,yayinda minal tabishi da harara,hajiya mairo itama yabitada wa,azi




Washegari malika tatashi kowa da kuka,minal tabata nono takisha sai rusa kuka,take anyi lallashi ankaji kukanta sai daduwa yake


Minal itama ta rushe da kuka,hajiya mairo ta ansheta amma sai kara cancara kuka take



Motar safwan ne ya danno kai,parking yayi da sauri yafito daga mota



Kukan malika yaji,dasauri yanufi office din da kowa yayi cirko cirko anrasa mai za,a bata tayishiru


Sallama safwan yayi


Amsamai sukayi,dasauri ya anshi malika daga hannun hajiya mairo,cillata yayi sama,ahankali kukan ya ragu ,jijjigata yake yana hura mata kunne,aiko yarinya ta murmusa


Abin yaburge kowa,minal tashagala a da kallon safwan tana inama shine uban malika dataji dadi

Khadijah ce ta dakkowa safwan kujera yazauna,yakarbi feedern dayake cike da milk yafara bawa malika,harta koshi tafara wasa


Hajiya ta kalli dayar shugaban tace hajiya hanne kinga ikon Allah lalle kam malika tasamu uba




Hajiya hanne tace i wallahi bari in koma bakin aikina tunda uwata tayi shiru,dukansu suka koma bakin aikinsu


Office yarage daga hajiya mairo sai minal da safwan






By
Maryam yarmama
[21/03 6:34 pm] salmah pinky💅🏼💍: ●●●●●●●●●●●●●●●●●●●

*🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*76★80

By

Maryam yarmama


*dedicated to*
_my salma Ali wadah_←


*®H.O.W*♣

_wannan shafin sadaukarwane ga kawaye na yan *HIQIYA ONLINE WRITTERS*_
_Shugabarmu *billyn abdul,classic feedoh,first lady,salma Ali wadah,eshart saleh,sweet jiddah,sunhera,Allah yakara mana dankon kauna da soyayya ,Allah yarabamu daga sharrin mahassada_






→☆Safwan yace hajiya mairo amin alfarma inaso aban aran minal da malika zanje muwa malika shopping din kaya


Minal ta dakamai harara tace ba inda zani ,kuma wallahi ko kasiyo bazatasaba


Hajiya mairo tace minal indai kin daukeni uwa kije kiyi wanka nizan shirya malika kuje


Jikin minal ne yayi sanyi a hankali tatashi tana gallawa safwan harara,shiko murmushi yake mata tawuce gidan hajiya dake xikin gidan marayu katan gida ne wanda babu abinda babu aciki,tayi wanka tasa atampa,tadanyi makeup maishiga rai,tasanya hijjabinta mai hannu tayi masifar kyau



Mota sukashiga safwan nadauke da malika,minal nabiye dashi sunyi matukar dacewa dajuna


Zama minal tayi agaban mota,maman marayu da sauran kawayen minal da yara suna dago musu hannu,minal ma dago musu takeyi,suka fita daga gidan marayun


Minal sai gunguni take ita kadai ambi an takurawa mutum saikace shi kadaine,


Safwan yace hmmm matata kina burgeni wallahi zanso muyi aure mu tallafi rayuwar yarmu malika


Minal tadakamai harara tace minal ba yarka bace yatace,gwandama kayi shiru kadaina zancenta

Safwan yadanyi dariya yace amma tafisona kuma dazu kinga example.


Shiru minal tayi har akaje tafkeken shop mall dinnan wanda sai dan wane da wanene ke shiga mall din M&H & UMMAH SHOPPING MALL

Safwan ne yafaka mota,yafito anata chaje mutane ,amma shi dayazo wucewa security suka dinga risinawa suna kwasar gaisuwa

Safwan yace minal yakikaga shoprite dinnan


Tabe baki tayi tace yayi kyau mana aiko makawo yashafa yasan kyanshi balle ni


Dariya safwan yayi yace yanzu in akace nakine yazakiyi ?

Minal takara tabe baki tace zanji dadi in taimaki marayu

Safwan yace to minal dawowana nigeria nagina shoprite dinman danaje gidanku naga anzamr dashi tafkeke nayi tambaya bawanda yace yasan inda kuke,nayi kuka da bakinciki,shine nazo abuja nagina shoprite mall mai sunanku nayi alkawari duk randa na ganku yazama mallakinku dake da ummah da aziza yanzu shoprite dinman ya habaka,bankinki dana bude muku shima yahabaka,har kamfanin motoci da gidan gona na bude muku,gashi ana ana siyar muku da gwala gwalai akasar waje ,kudin dayake bankinku,har jikkokinki sai sun mallaka,kuka duk acikin shoprite dinnan kuka samu daukaka yanzuma shirein bude muku asibitoci nake


Hawaye ne zirara suka fara zuba a idaniyar minal tarasa kalmar dazatayi amfani dashi


Safwan yadanyi gaba yace karkice komai banson godiyarki,ya miko mata hankerchief mai bala,in kamshi yace gashi ki share hawayenki kar mushiga ma,aikatanki su rainaki.


Dariya minal tayi,suka shiga katon short din bangare bangarw suna zagawa,malika tana kafadar safwan minal nabiye dashi,ma,aikata sunata aikinsu da kwasar gaisuwa,harda cinema da katon restaurant da wajen ice cream da wajen wasan yara a shoprite din


Su annur ne saudat suka shigo,minal tana wa annur magana,safwan yana waya,minal ta juya tana kallon kaya,ba abinda babu aciki
Malika tasaki kuka,annur ne yajiyo yakalli safwan sukayi musahaba yace a a abawa uwarta mana,kasan niko inason yara

Saudat tace eh wallahi dama kubamu

Minal takasa juyowa sakamakon muryar annur dataji wanda yanzu tafi tsana aduniya shi yakewa safwan magana.

Cikin harzuka ta dauki wata riga maikyau tajuyo tana yake tayi kamar bataga annur ba tacedarling kaga wannan rigar zaiwa babynmu malika kyau.




Annur ya cire gilashin dake manne a idonsa da mamaki akan fuskarsa yace you?minal dama kinanan

Minal ta kallesa ido cikin ido tace mallam bansankaba kai waye dazakamin magana?


Annur yace annur nefa minal dama yar dake hannun wannan yatace bansaniba?


Saudat tayi rau rau da ido nan take taji kaunar kyakyawar jinjiran ya shiga ranta(Allah da iko,to kwalelenki) yayinda minal tace au har wani yarka kake kiranta? ta nuna safwan to ga uban daya dace da ita ,shine mijina,wanda yasadaukar da rayuwarsa akan malika,kai ko kunyar fadar cewa yarkace bakajiba



Annur yace wallahi sai anban yata ko mutuwa zakiyi saina karbi yata

Safwan mamaki da kishi suka cikashi fal ,ji yayi minal takamo hannunsa tana honey zomubar nan mahaukacine ,wani shock safwan yaji ya kankame malika sosai bayason kowa yarabashi da ita


Shan gabansu annur yayi yana zakuban sana kosaina kwata da karfi

By
Maryam yarmama
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
*🦋MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦋*
(81)
*BY MARYAM YARMAMA*
_(QUEEN MEERAH)_



*After a long break am back... Ina godiya ga tarin masoyana... Bisa kaunar da suke nunamin, duk lokacin da naga sakonku.. Ko kuma kiranku, sai inji tamkar inyi kukan farinciki*

_GARGADI_

_Ban yarda a juyamin littafina ba, ko canzamin suna... Baiwa ce ubangiji Allah yabani.... Don haka a guji juyamin littafina_

Da sunan Allah mai rahama, mai jinkai






Cikin bakin kishi game da zafin nama annur ya fincike hannun minal, daga rikon da tayiwa safwan, yarfar da hannun yayi yana

"Kina da hankali,? kina matata zaki dinga rike hannun wani kato, har kika barshi yana rikemin baby ta

Murmushin takaici minal tayi cikin bacin rai ta kalli Annur tana"bawan Allah ka rabu damu, mu bamu sanka ba, ni wallahi bamma bantaba ganinka sai yau yaza'ayi kazo kana mana shouting akan abinda ba naka ba "..... Ka haukace ne... Tana gama fadin haka ta juya ta kalli safwan tace darling kaga zomu tafi inada abinyi... Safwan yabita zasu fita a shopping mall din , shi yama rasa me zaice saboda mamakin daya rufeshi cikin zuciyarshi yace tabbas wannan shine Annur mijin minal nada. ranshine ya kara baci

Annur ne ya dakatar dasu ta hanyar magana Cikin zafin rai yace "karya kike minal kinsanni, kece mace ta farko da kika soni dan Allah, kika soni a haukace, ki ka zauna dani batare da kin kyamaceni ba, bakisan asalina ba haka kika zauna dani, kika kula dani... Idan har akwai wacce zanso a duniya kece yakamata inso... But saboda rudin shedan na kasa yarda bazaki ci Amanata ba.. Minal baiwar Allah kenan, wannan babyn jini nace"...

Cikin kakkausar murya hawaye ya wanke fuskar minal ta kalli annur sannan ta maida kallonta ga kan saudat wanda tayi tsuru-tsuru, cikin sheshekar kuka minal tace" lalle mutum mugun icene, ban cancanci haka daga gareku ba... Ko ba komai ni marainiya ce wacce tasha wahalar rayuwa😭😭na zauna da dan sarauta, ban duba Asali ba..nayi rayuwa da mutumin danafi so a duniya... Annur bakada da kunya? Har kanada bakin magana innalillahir wa'innailaihir rajiun.... Malikar daka sheganta? Kukayimin shedar zina, kuka koreni gami da yimin saki a ranar danasha wahalar nakuda... Annur kasan maiya faru dani a ranar? .. Kabi son zuciyarka... Zamana dakai bantaba kokarin cutar dakai ba... Amma ka cutar dani da diyata malika, ubangiji Allah ne kawai zaiyi mana hissabi.... Fashewa tayi da kuka ta runtuma a guje sannan tayi Hanyar waje.....

Safwan dake rike da Malika yabi bayanta.... Yayinda annur ya fashe da kuka mai tsuma rai yana" please minal ki dawo gareni, ina bukatar in kara rayuwa dake, nine mahaukacin masoyinki, ya Allah ka yafemin, idan na mutu mezan je nace maka" durkusawa yayi yana sharbar kuka mai tsuma rai...

Saudat dake tsaye nan take taji tsanar minal yakara shigarta cikin zuciyarta tace " nadauka na kauda wannan tsintacciyar magen, nadauka bazan sake ganinta ba, na dauka Nida ganinta sai A lahira, gashinan yanzu tazo tafara kokarin rusamin farinciki.... Ina bazaiyuba. Murmushin mugunta tasaki cikin zuciyarta ta kara fadin " wannan Karon kam lahira zatayi bako... Mutum biyu zasu ziyarci lahira.... Minal da shegiyar yarta... Ku jira ni 😰

_wannan kenan_



Minal har taje gida tana kuka mai tsuma rai a duniya idan har akwai wanda ta tsana bai wuce Annur ba..... Kallon diyarta take cike da kauna, yarinyar sai wasanta take a hannun safwan wanda yayi shiru yana nazarin abu....

Hajiya Mairo ce ta katse wa safwan tunani da cewa " ashe haka tantirin yaron nan ya muku, lalle bashida kunya tom wallahi baza'a bashi yarinyar ba, saidai inda karfinmu yakare, shi ko kunya baiji ba irin cin mutuncin da yayi wa minal, don yaga tanada hakuri wannan karon kam zan tsayawa minal, saidai ayi yakin duniya".....
.

Hajiya hanne tace "Kinga uwar marayu, yaron nanfa dan sarautane akwai karfin mulki zasu iya yin komai don suga sun karbi diyarsu don haka kawai minal a daura musu aure da safwan yau _yau subar kasar nan "

A razane minal ta dago da idanuwanta da suka rine sukayi ja tace" ba inda zani, ina tare da momy bani da kowa saiku ba inda Zanje yanzu kune dangina kune gatana "....

Shiru wajen yadauka safwan yace" minal ina bayanki ba inda zaki kunanan, kuma nayi miki alkawarin sai munga umma... Ki shirya gobe zamuje kano, muje gidan baffanku....

Gaban minal ne yafadi yabada rass! Ta furta baffa


* * *



Kwance annur yake likita yana dubashi.... Yayinda saudat take gefe tana mishi sannu

Gyada kai kawai yake iyayi... Saboda yanda zuciyarshi yake mishi zafi tamkar zai tsage tunanin minal yake da kyakyawar babynshi, da yanzu babynshi tana hannunshi yana mata wasa, minal kuma tana kusa dashi tana mishi hidima da kalaman soyayya, kara ya saki yana "ina bazai yuba dole a bani matata da diyata".....
Likitan ne yace "calm down Aboki ka kwantar da hankalinka a yanzu jininka yahau sosai ba'a bukatar ka dinga sa damuwa a ranka...

Saudat ce ta Turo baki tace" doctor safwan rabu dashi, yasa kanshi a damuwar yarinyar da taci amanarshi, diyarfa ba yarshi bace.... Karuwanci Mina...... Kafin ta karasa annur ya daka mata tsawa"karki kara zagin minal idan ba hakaba Saina dau mummunar mataki a kanki, kinga get out kawai

Cikin bacin rai saudat ta tashi ta fita tana magana kasa-kasa, sama tahau ta dau wayarta ta yi danne-dannen minti takwas sannan ta danna wani number ringing biyu aka dauka

Daya bangaren akace "hello hajiya ranki shi dade da Alama samuwa ce tunda naji kiran nan ".....

Saudat ce ta amsa da"Eh boss wallahi kwangila nakeso nabaka... Na tura maka hoto ta watsapp dinka(dama ta Turo hoton minal daga wayar annur, saboda tun a Mora tagama shirya plan dinta) , inason ka nemomin ita duk inda take, Akwai jaririya a hannunta ka hadasu ka kashesu, nasanka boss akan kudi bakada imani

Amsawa yayi yadau babbar wayarshi yabude data yana duba hoton yayi zooming "cikin kasa-kasa da murya yace ai hajiya aiki yazo gidan sauki don yarinyar ma gatanan tsaye a bakin gate din gidan marayun HUTU... Su uku da wasu yan mata, kuma dayar tana rike da jaririya.. Kuma wallahi danayi zooming itace....


Cikin jin dadi saudat tace"boss meya kaika hanyar gidan marayu kuma,
Amsa yabata yana fadin". Ai yarinyata da Mamanta ta rasu Wanda kowa Yaki amsarta ai nan nakaita, to shine yau nazo visiting, saikuma Kika kirani, hajiya kwantar da hankalinki, ai bindigata tana kwankwasona... Bari ma in Turo miki da hotonta ki tabbatar itace ko ba ita bace.... Zooming din minal yayi yadauke ta daga nesa bata saniba

Ihun murna saudat tayi tace "yes! Yes itace wallahi... Yi maza kayi shooting dinta da duka yanmatan har babyn, kanada kyautar miliyan biyar da visa na barin kasar nan.....
Katse wayar saudat tayi ta dire akan katifa tana "Alhamdulillah


Pls a dinga sharing
*🦋MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦋*
(82)
*BY MARYAM YARMAMA*
_(QUEEN MEERAH)_



*After a long break am back... Ina godiya ga tarin masoyana... Bisa kaunar da suke nunamin, duk lokacin da naga sakonku.. Ko kuma kiranku, sai inji tamkar inyi kukan farinciki*

_GARGADI_

_Ban yarda a juyamin littafina ba, ko canzamin suna... Baiwa ce ubangiji Allah yabani.... Don haka a guji juyaminv littafi a kowani siga_


Boss ya seta bindigarsa daga can nesa cike da murmushin mugunta yace yara taku ta kare.... Hannun yasa akan kunamar bindigar yana kokarin Harbawa, diyarsa abin sonsa yagani tafito daga gate din gidan marayu aguje... Cikin shaukin so ya sauke bindigar yafasa Harbin yamaida bindigar kugunsa..... Nufar wajen yayi, kafin yakarasa yar tashi ta taho tana murnar ganinsa... Nan minal da khadija suka dago da kansu daga dubar wayar da sukeyi suna murmushi, boss ne yadauki yarshi yakarasa wajen yana gaishesu da fara'a akan fuskarsa, Amma cikin zuciyarshi yana "bari ingama da yata zan dawo gareku "..... Amsawa sukayi sannan suka shiga cikin kofar gate din. Boss ne ya kalli yarshi yace " kaunata wannan kyau din da kikayi waye yake kullarmin dake"... Cikin farinciki yartashi ta kalleshi tace "Abba Aunty minal ce, tana da kirki sosai ita yakeyimin wanka tabani Abinci abaki sannan ta koyamin karatu har goyani take. cike da farinciki yace wacece minal kuma, amsa tabashi tace "wannan wacce suka tsaya anan kuka gaisa ai tanada yarinya, wannan jaririyar yarta ce".... nan take yaji tausayin kanshi Dana yarshi ya kamashi da tuni yanzu yakashe wacce take sa yarshi farinciki, nan tsoran Allah ya shigeshi, wayarshi yadauka ya turawa saudat kalamai na nasiha Sannan yasakata a black list.... Sallamar yartashi yayi yace idan tashiga tacewa minal yana godiya Allah yasaka mata da Alkhairi 😭😭😭😭.
Saudat dake zaune a falo tana shan lemo cike da annashuwa karar shigowar sako taji ,da hanzari ta dauki wayar sakon boss tayi arba dashi tana gama karantawa cikin bacin rai ta danno wata uwar asharr tace"lalle boss kagama sanina ,dole ka rainani tsiyar yiwa talaka halacci kenan ,aiko zakayi bayani wallahi ".............. cikin fushi ta fara kirar numbarsa saitaji wayar akashe,tsaki tayi tana nashiga uku wallahi bana burin minal tadawo gidan nan ,idan tadawo wallahi asirina zai tonu ,aikam bazai sabu ba dole minal tabar duniyar nan gaba daya,karar intercom taji alamun tayi bako .saida tagama shan kamshinta sannan tatashi ta nufi hanyar babbar falo taje ta bude kofar. momy tagani tare da aziza fuskarsu ba annuri ...................................................................dam!dam!gabanta ya yanke yafadi amma dayake ita yar duniyace ta saki murmushi tana "oyoyo mummy saukar yaushe ..aha tafe kuke da auntyn minal"...mummy tace dakata bani zakiwa makircin nan ba,zuwa nayi inyi muku godiyar abinda kukayi wa minal keda mijinki Annur ina london nasami labari amma saboda corona yasa ban dau wani mataki ba,bansami hanyar dawowa ba sai jiya nadawo... ,amma hankalina a tashe yake musamman yar uwarta Aziza saboda halin datashiga first semester akayi withdraw dinta daga makaranta,kun kyauta ina mara kunyar nan ,butulu yake wanda bai san hallaciba ,yazo ya nemomin inda minal take ko kuma in tsine mai. "......

Please Login or Register in order to submit comment