Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaki saudat tayi cikin rashin kunya ta hada girar sama dana kasa tace"to ai mummy bani zaki balbale da fadaba ,wannan kuma ai tsakanin danki da minal ne,ni bamma san mai akayiba cikin shege ta kawo cikin gida ,shine ya koreta"....Aziza cikin bacin rai tace"wallahi karya kikeyi yar uwata bazata taba yin hakaba ,nayi imani da ubangiji na.kuma yau asirinki yana gab da tonuwa ,yau zaki shuka abinda kika girbe,.....tsaki saudat tayi tace"au tafiyarki kasar waje tare kuke yawo kenan ,Ashe ke kika koya mata halin ai bazanyi mamaki ba saboda yayan talakawa haka suke ,shidai annur yace ciki ba nashi bane tuni ya seta mata hanya,duk munafikin daya gaya muku wulakanta minal mukayi to karya yake ciki dai bana Annur bane karuwanci tayi ta samoshi,juyawar da saudat zatayi tashiga ciki ...taci karo da annur ya wanke ta da mari kyawawa guda biyu ...cikin bacin rai yace "duk ranar da kika kara aibata minal a idon duniya sai na sakeki ,Albarkacin mahaifina kikeci .....muryar dady sukaji yana"Annur idan har ka haihu a cikina,idan ni mahaifinka ne, ,inason kasaki wannan mara kunyar yarinyar wanda yau Allah ya tona mata Asiri,dagowar da annur zaiyi saiyaga hawaye a fuskar mahaifinshi ,tunda yake bai taba ganin mahaifinshi yana hawayeba sai yau .....tunkaro inda mahaifinshi yake yayi ,ya rungumeshi yafara kuka tamkar karamin yaro ......saudat ce tashige falo aguje,tayi hanyar kitchen ta dakko wuka tana yau zan kashe annur ,na kashe kaina kowama ya rasa...ba macen da ta isa ta rabi kota zauna da annur 👦fitowa tayi daga kicin din ta nufi hanyar falo ..sannan tayi wajen kofar falon inda tabar su momy nan tasamesu kowa yana kuka ,annur kuwa yana rungume da mahaifinsa ..."yana dady na rasata"......ji yayi an chaka mishi wani karfe ta baya,kara yasaki ya zube a wanwar "..................................
*MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI*
BY
MARYAM YARMAMA
83


Saudat tsaye taja wan dogon numfashi da ajiyar zuciya ta dawo daga duniyar tunanin data shiga... Furtawa tayi shedan kayi karya, da kake so inje kurkuku... Tana gama fadin haka dakai dubanta ga aziza wacce suke tsaye Suda mommy, harara aziza ta daka mata sannan suka white falon... Suka barta tana kallon annur rungume da mahaifinsa... Annur ne yakamo hannun mahaifinsa yace" dad idan har sakin saudat shine BURINKA tom zanyi abinda kace duk da bansar hujjarka ba na cewa na saki saudat".....amma daddy meye hujjarka, saudat yar gidan amininka ce, kuma ku kulla Alaka da sarkin gombe mai karfi dadi meyasa kake so ka yanke wannan karfin Amintakarku?..

Cikin hawaye daddy ya kalleshi yace son muje ciki Labari ne mai tsaho... Takun kasaita sukeyi, wuce saudat sukayi tana tsaye jiki a sanyaye..ciki ya duri ruwa. Shigewa falon sukayi sannan suka zauna, cikin sauri saudat ta rufa musu baya itama yashiga babban talon tazauna tana wani daman yatsine da hararar dady, shiru wajen yayi yayinda daddy yafara magana da cewa "Yabo ya tabbata ga ubangijin talikai,Annur dafarko kayi kuskure mafi girma a rayuwarka, ka cuci rayuwarka"ina karatunka, ina iliminka da har kayi saurin yanke hukunci akan matarka minal wacce ta soka tun batasan kai waye ba, yarinyar nan bata cancanci haka daga gareka ba.... Duk Abinda yafaru naji ta bakin wanda yazo gidanka ya nuna shine mallakin cikin minal, sannan hotunan daka gani editing akayi, shi mutumin yazo ya sami maigadin gida yace yanason magana dani mai gadin yahanashi, sai ya kama kuka shifa yanason ganin mai martaba saboda yana cikin tashin hankali... Tom cikin ikon Allah na fito ina zagayawa, ina exercises bisa umarnin likita sai naji wannan hayaniyar, sai nace maigadi yabarshi yashigo, damai gadi yabarshi yashigo... Sai na umarta akawo mishi abinci, yacemin shi bazai iyacin abinci ba saiya furta abinda yake damunshi "tom cikin kuka gafara gayamin irin kulla kullan da matarka saudat tasakashi sannan yace shi yake mata aiki" duk abinda akace minal tayi duk Sharri ne, kuma saudat ce ta kulla sharrin sannan rana daka kori minal, sai datasa yabi sawun minal domin ya kasheta da jaririyar Amma Allah bai basu dama ba
Kalmar Innalilahir wa'innahir laihi rajiun annur yaketa nanatawa, gumi ya tsofo mishi ta ko'ina a jiki,. Yayinda saudat sai zazzare ido take jiki na kyarma....

Daddy ne yace "Annur mutumin nan ya gayamin abinda yasa ya kasa samun kwanciyar hankali shine yace duk lokacin daya kwanta sai yaji kukan jarirai ta ko'ina, sannan yadinga yin mafarkin gashi yana wutar jahannama, shine da kwatance ya gano gidana domin yace yakasa zuwa wajenka bayason ku hada ido... Yana gama fadin haka, ya dakko MAGANIN kwari ya kwankwada, Kafin inyi magana ya kurma wani ihu, yayi hanyar gate yafita, fitar shi keda wuya mota ya bigeshi sai mutuwa....
Kuka Annur yasa yayi kan saudat ya shaketa yana saudat kinci Amanata, kin rabani da abar sona abar kaunata, bazan taba yafe miki ba..... Kije na sakeki saki uku... Ihn neman cero saudat take kurmawa, dakyar mommy ta amsheta a hannun Annur..... Ana amsarta ta saki kuka mai tsuma rai tayi hanyar saman benen falo da gudu, tafara hada kayanta yau shine karo na farko da tafara nadamar abinda ta aikata a rayuwarta kuka tasaka mai tsuma rai tana"minal kiyi hakuri na cutar dake na rabaki da abin sonki....

By maryam yarmama





*💥MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI💥*
84
By maryam yarmama

*KANO CITY*

nifa Abban haseeya nagaji da ciyar dakai, nagaji da jinyarka gwanda ka mutu kowama ya huta da wannan wahalar naka... Mamace take fada cikin zagin rai gami da tsananin tsana...

Kwance Abba yake cikinshi ya kumbura tamkar mai cikin wata Tara... Sai mishi yake dakyar hawaye masu zafi nabin idonuwanshi ya Kali mama yace"ladi kiji tsoran Allah a rayuwar na nayi komai ne donke da yaranki, Domin kuji dadin rayuwa, Amma dayake duniya ta juyamin baya shine kike tsanata,kike hantarata?
Cikin masifa mama tace"dakata malam karkace kayi saboda ni wallahi karyanka kawai son zuciyarka kabi, ka yi ajalin danuwanka sannan ka cutar da marayun yaransa, gashi Kaga sakayya, ita haseeyar dakayi auren jari da ita, gashi tadawo gida, ga uwar danfarar da mijinta ya mana yasa muka zuba hannun jari, kaine harda saida kadarorin marayu, hatta Gidan da muke ciki ka daga ka siyar ka kawo mu rubabben gida.sannan kadai kudade kabashi... Karshe ai mijin haseeyar guduwa yayi ya barta da ciki da ciwon kanjamau . Tana gama zubo jawabin nan ta fashe da kuka tana wallahi ka cuceni, Allah ya isa tsakani dakai
Wani irin Zafi Abba yakeji ga zagin ciwo shiru yayi yana zubar da hawaye shi yanzu burinshi kawai yaga umma da yaranta ya nemi yafiyarsu.. Kwalla mash dumi ne suka zubo mishi




*ABUJA CITY*

minal ce zaune dauke da wani karamin Hoton dasuka dauka annur yayi mata kiss suna Dariya ta kura mishi ido tana kallo..tana zubar da hawaye... Charaf taji an warce hoton juyawar da zatayi taga safwan tsaye yana mata kallon tuhuma, kunyane ya kamata tafara kokarin share hawayenta

Hade girar sama dana kasa yayi yace"bana ce kar inkara ganin kukanki ba? Haba minal save ur tears,Dama ni nasan kinason Annur, saboda da wuya ki dena sonshi.....dakatar da safwan minal tayi ta hanyar cewa"enough safwan kawai ina kukane idan na tuna Abinda Annur yayimin, baiji tausayin diyar nanba haka ya wulakantamu... Bazan taba yafe mishi....
"Shiiiiiiiiiii" safwan yayi mata Alamar tayi shiru sannan yace "minal, Annur yana sonki Duk Abinda yafaru nasan ba laifinsa bane, sharrin macene and kuma wallahi Ranar Dan Ganshi a mall dinnan nasan yayi nadamar abinda yayi, karki manta shi gwarzon namiji ne kuma yarima dan sarauta, Amma ya dunkusar da kanshi yana kuka tamkar karamin yaro, tun daga Ranar na fara giving up nasan zaku dawo, kuma nasan kunfi dacewa dajuna,
Cikin kuka minal ta Kate zancen safwan ta hanyar cewa " safwan ni dakai na dace bashiba, kai mutumin kirki ne

Amsa safwan yabata yana"minal shima mutumin kirki ne, saboda sonki ya kwaikwayi hauka, yazauna dake acikin talauci don kawai yasameki, yayi rayuwa acikin talakawa saboda ke, Maman malika kiyi hakuri ki koma Gidan mijinki, ni na sadaukar da soyayyata, namiki Alkawarin auren yar uwarki Aziza, Dama tun da basona kike....
Jikin minal ne yayi sanyi shiru tayi sannan tace "hmmm safwan inaga Mubar maganar nan sai mun dawo daga kano"....

Hajiya Mairo ce ta shigo office din bakinta dauke da sallama tana murmushi tace"minal kinyi baki fa Kafin minal tayi magana Aziza tashigo hannunta rike da baby malika.. Tsaye minal ta tashi kukan murna tafara tayi wajen yaruwarta ta rungumeta tsam, itama Aziza kuka tasaki tana"yar uwa Ashe zamu sake haduwa a rayuwa"kuka suka kara fashewa dashi... Momyn annur ne tashigo tana"haba daughters ya isa kar kanku yayi ciwo, sakin Aziza minal tayi ta nufi wajen momyn annur ta rungumeta tana gaisheta... Aziza dake rike da baby malika ta hangout safwan yana tsaye sai murmushi yake nan ta shaidashi tace"kamar safwan nake bani".... Cikin Myrna safwan yace bakiyi karyaba nine safwan dai na minal, Dariya tayi tace "kaikam akwai zolaya"...

Nan aka bude sabon shafin hirar rayuwa, sai raha ake cike da annashuwa yau Gidan marayu kowa sai farinciki yake minal sai rarraba ido take ko zataga Annur (Allah sarki minal sarkin hakuri, haka akeso mutum ya kasance a rayuwa, ga yafiya)...
Momyn Annur ce ta shiga lallashin minal da tayi hakuri ta koma dakin Annur... Inda harda su safwan

Kuka minal take tana itafa bazata komaba,Aziza ce tace minal idan har don safwan ne karki damu mun daidaita kanmu... Dukan wasa minal ta kawo mata cikin kunya tace"wallahi kefa yar uwa sai a hankali,bakida dama dama

Dariya da murna kowa yafara, nan dai mony suka roki hajiya Mairo da tabar su sutafi da minal, dakyar hajiya Mairo ta yarda nan... Momyn annur tayiwa su hajiya Mairo da hajiya hanne dumbin Alkhairi da Alkawarin kowani wata zata dinga taimakawa marayu... Kuka kam Yara da manya na Gidan marayu sun sashi minal kuka takeyi saboda tasan zatayi kewarsu... Haka Yaran kowa ya dinga Aunty zanbiki.. Minal sai takara fashewa da kuka tamkar karamin yarinya... Har kasa ta durkusa tana godewa hajiya Mairo da sauran matan Gidan... Nan suka shiga motocin Alfarma sai Gidan annur,tafkeken gate din aka bude musu suka yada zango cikin Gidan.... Annur dake kwance a falo da drip a hannunsa yanajin karar motocin ya fincike drip din ya nufi kofar dazai sadashi da harabar Gidan.. Fitowar sa keda wuya, aka budewa minal mota...santalelen chocolate color kafartane yafara fitowa daga mota... Sannan tafito tafiya take cike da nutsuwa , ta kara kyau,kalar skin dinta chocolate yakara fitowa tayi kyau sosai har wani sheki take... Turus Annur yaja ya tsaya yana kare mata kallo.itama cal ta tsaya azixama da mommy suka tsaya..hawayene yafara shatata a idanuwanshi, blue eyes dinsa yajuye yazama brown... Doso inda minal take yayi, wacce tuni ta hade rai itama zubar da hawaye take... Yana zuwa ya zube agabanta tamkar zaiyi shige kasa cikin muryar kuka yace"minal! Wallahi kunyarki nake, narasa yanda zanyi na Kali idanuwanki ince ki yafemin na rasa da wacce kalma zan baki hakuri... Minal I just know I can't leave without you.. Ruhina, rayuwarta, jinina, dukiyata fansace a gareki, kiyi hakuri ki yafemin ko bazaki komo gareniba pls minal kice kin yafemin"... Yana gama fadin haka ya rushe da kuka maicin rai.... Minal ji tayi an dafota tabaya juyowar da zatayi saudat tagani tana zubar da hawaye cikin muryar kuka tace

"Na dauka dan talaka Ba mutane bane, nadauka mulki da sarauta sune jin dadin rayuwa, Amma sai na lura bisa tunani na Duk shirmene, komai na duniya banzane, Duk abinda yafaru tsakanunku da Annur nice sanadi, ni nayi kulla-kulla... Da ace mata da Dama zasu zama kamarki da sun morewa rayuwa.. Minal kiyi hakuri ki koma dakin mijinki,na gayawa annur Duk irin abubuwan Dana mulla miki, ki koma ki zauna ke kedai badanmu ba ko dan yarinyarki.. Ki yafemin domin duniya ta koyamin darasi yanzu narasa mahaifana kuma narasa annur har abada "....
Cikin kidima minal ta Kali saudat... Sannan ta fashe da kuka tace"wallahi Aunty bakiyimin komai ba, kuma na yafemiki idan harma kinyimin... Rungumeta saudat tayi tana godiya sannan tace'"ni nabawa su Momy da Aziza address din inda kike, Tunda sun samoki Alhamdilillh, zan iya yafiya yanzu Tunda kun yafemin... Nan daisukayi bankwana inda Saudat tahau motarta aka bude mata gate tafice daga Gidan....

Aziza ce takaraso wajen tace Haba ya Annur dan Allah katashi ba girmanka bane kana rokar wannan kwailar...
Minal ce ta kalleta tayi wani dakuwa t share hawayenta... Da hannunta masu taushi ta durkusa ta tallafo annur ta rungumeshi tana "sugar kaima bakayimin komaiba ka yafemin..Allah ma Muna masa laifi yana yafe mana balle mu, na yafe maka"... Farinciki ne yarufe annur yakara rungumeta cikin muryar dady yace"omg dagaske kike matar mahaukacin masoyi, nagode Allah ya biyaki da Aljanna"... (Summa manta da awaje suke)....dasuka Ankara nan kunya ya kamasu annur ya waske ya saki minal sannan ya karbi babynshi a hannun momy... Yarinya tazo hannun ubanta sai Dariya take... Nan annur ya ga Kama tayi dashi sak har fatarshi... Nan yafara kissing dinta sannan yayi mata adu'oi a kunnenta... Ya rungumeta suka shiga ciki....

*KANO CITY*

jikin Abba yakara Zafi ya rikice, hasiya da luba sai kuka suke rizga yayinda mama saicin tuwonta take tana"yo to ai kudena wahalar da kanku kuna zubar da hawayenku a banza ai mahaifinku abinda ya shuka shi yake girba.. Ke kuma luba saboda Allah da annabi duk mazajen da kuka aura Duk tsinannu ne, kinje kin auri dan dambe, gsshi ya ragargaza miki fuskarki kin dawo harda saki uku kema, yanzu gashi kin dawo gida, to wallahi kowacce takama sana'a bazan iya ciyar daku ba... Cikin kuka haseeya tace"mama yanzu da tsohon cikin zankama sana'a"
Cikin fada mama tace yo Dama dan ubanki haka zan zauna dake ina ciyar daku da cikin dan danfarar nan.. Ai duk ke kika jawo mana wahalar nan.. Gashi yanzu gidansu minal mike ciki, Gidan Dama yafara rushewa, yanzu idan sun dawo wayasan inda zamu dosa? Aiko cikin gobe zaki haihu ne wallahi sai kin Kama sana'a.. Matar madamfari kawai haihuwarku wallahi batayin ranaba..... Bata gama rufe bakinta ba taji sallamar..mai sallamar ce tashigo
Kara mama tasaki tana"umman Aziza"


💥MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI💥
85


By maryam yarmama





*masoya daga Cameron, niger, chad da sauran garuruwa, ina mika sakon godiya musu kaunar dakuke nunamin, nagode Allah yabar zumunci*

*SHAFIN KARSHE*


*ABUJA CITY*
Nan aka kara maida auren minal da annur, zokaga irin farincikin da suka shiga...bikin gargajiya akayi inda su minal da annur suka zaka kayan sarauta.. Minal taga gaga wajen dangin annur dayake da daya tilo, kuma ga dangi masu tarin tawa... Ana gama da kwana daya aka daura auren safwan da aziza... Bawani buduri akayiba saboda safwan yace shi bayason ayi wani buduri, Aziza kam taci burin akwana bakwai ana budurin bikin amma sagwan yaki haka ta hakura, su Aziza anshiga sawun manya, sunsha kuka suda minal lokacin da akazo daukar aziza domin akaita gidanta

"Cikin shekshekar kuka minal tace"Allah sarki umma, inama kinanan, kizo kiga yanda yaranki suka zama, rushewa tayi da wani irin kuka maicin rai sannan itama aziza tadinga kuka, su hajiya mairo ne da momyna annur sukata basu baki, dayake agidan su annur akayi taron biki.... Dakyar aka banbare aziza daga jikin minal inda aka kaita gidanta dake abuja crown exculisive gida tamkar Aljannar duniya.. Aziza ta tsorata da ganin wannan gidan...(dama gata da uwar buri aranta)...... Nandai amarai suka tashan amarcinsu... Inda annur da minal suka kara kyau da gogewa, annur baya zuwa ko'ina, kitchen tare suke shiga, komai tare sukeyi sun zamto abin sha'awa ga kowa.... Annur kam yazama tamkar cingum yace bayason borori a gidansa

Kwance minal take akujerar falonta tayi matashi da cinyar annur, shafa kanta annur yake cikin so da kauna yana kallon kyakyawar brown din fuskarta yace "babyn yakamata ace munje kano, mun binciko gidanku sannan mufara binciken inda zamuga umma".... Nan idon minal yakawo ruwa tace" heartbeat wallahi ba irin binciken da bamuyi ba, kaga umma har yanzu, amma ni a raina kullum inaji zamu sake haduwa da umma, sannan ko badon umma ba inason inje kano in nemi numbansu ummi kawata, domin mu dinga sada zumunci,.... Kuka ta fashe dashi yayinda annur yafara lallashinta cikin salon riritawa ya mantar da ita duk wani kunci da take ciki........ Annur da minal kenan... Mahaukaci da mahaukaciyar masoya.... Nan dai suka yanke zasu rankaya kano gobe, harda Aziza da safwan........

KANO CITY

Cikin hawaye umma tace"ladi nice ba wata ba, yanaga kun dawo nan, meyasu Abbansu haseeya, ina kuma yarana innalillahir wa"inna ilaihir raji"un,... Ina kuka kaimun yayana? Badai kun koresu a gidan daya rage shine gatanmu ba...

Cikin kuka mama ta kalli umma tace" umman minal kiyi hakuri, ki yafe mana, muma bamusan inda sukeba, tun lokacin da Abba ya daurawa minal aure da wani mahaukaci, sannan ya kori aziza daga gidan bankara jin labarinsu ba... Kiyi hakuri.... Kara umma tasa ta sunkuya a wajen tana"Abba ka cuceni! Me mukayi maka a rayuwa da zaka saka mana da irin wannan abin, dan uwanka imran mijina ya kaunace ka da zuciya daya, ya jawoka jikinshi, amma ka kasa rike mishi yaya"nashiga uku nawa yakare, nikam bazan iya rayuwa ba yarana ba.... Zaman dirshin tayi... Yayin abba dake kwance yake kallonta yana matse hawaye ga cikinshi sai kara kumburi yake"...... Dakyar ya iya cewa... "Dan Allah kiyi hakuri, nima nemansu nake in nemi yafiyarsu, kiyi hakuri ni nayi miki kurciya kika fita hayyacinki, ki kabar gida da yaranyi... Mijinki ma ni na kasheshi don in mallake dukiyarshi.....na zalunceku, nasan Allah bazai taba yafemin ba.
Salati umma tasa yayinda inna ladi ta fashe da kuka... Kowa kuka, lubaba dake tsaye itama tayar da butar hannunta tafashe da kuka tana"Abba baka cancanci zama mahaifinaba, nayi nadamar saninka a rayuwa kanayin komai cikin son zuciyarka, to yanzu ai kaga karshenka
Dakyar umma ta tashi da niyyar fita daga gidan,inda ta yanke shawarar gwanda tashiga gari ta nemo inda yaranta suke... Nan taji duniyarma yana juyi da ita, zubewa tayi a wajen sumammiya...


Annur da minal rike suke da hannun juna, inda malika tana hannun yar aikin maisuna hajara, tafiya suke acikin airport ga bodyguard da dogarai suna take musu baya.. Annur sanye yake da blue din suit wanda ya amshi farin fatarsa, itama kuma minal sanye take da dogan rigar abaya dark blue, sannan tayi rolling, sunyi masifar kyau duk inda suka wuce sai an gaishesu domin prince annur sananne ne, Gashi kuma dan wasan kallon kafan da akeji dashi ne.... Nandai suka wuce inda passenger suke zama kafin jirginsu ya tashi.... Basu dade da zamaba Aziza da safwan suka tawo suna rike da hannun juna... Su Aziza anzama manyan mata sai takun kasaita ake, ita sanye take dadogan riga amma nata red ne, shikuma safwan sanye yake da shadda shampo, sunyi kyau sun kara gogewa... Suna zuwa aziza ta rungume minal cikin farincikin sannan ta karbi malika a hannun hajara tana"thats my baby".... Sannan ta kalli minal tace"matar mahaukacn masoyi yayane".... Dariya duka suka fara yayinda annur ya kalli aziza yace"yayarmu ai wannan tsohon labari ne"gaskiya kina kwafsa mana

Azixa tace"ai nikam bazan mantaba yanda nasha bulala, a hannunka, inw zan manta, wai bakaji kunyar zamanka acikin dattiba"

Sosa kai annur yayi yace"ai sone ya kawo haka, kuma nason yanzu duk duniya bawata mace da zata soni kamar my heart minal, shiya duk wani dukiyata, rayuwata komaina na mallaka mata and yau shine ranar dazan gaya muku nine boyayyen masoyin da kuke nema.... Mamaki yacika minal,, kafin suyi magana amfara kiran passenger... Nan suka shige cikin jirgin sai kano, ba wanda yasamu damar yiwa kowa magana har suka sauka a Aminu kano Airport



KANO CITY
Haseeya da tsohon ciki tana suyar awara a kofar gidan yayinda lubaba ke siyar da kunnun tsamiya... Mama ce ta leko tana musu masifar kar wacce ta karo aiko abata ruwa acikin gida, su siya da kudinsu.. Jiniyar dankara-dankaran motoci sukaji... Nanda motoci kusan guda goma suka faka a layin... Nancikin mama ya duri ruwa tana fadin"munshiga uku, kardai gwamnati ne tazo ta fitar damu daga gidan...duk da unguwarsu minal dan babban layine haka bai hana makota fitowa su ganewa idonsu meke faruwa.... Lubaba da hayakin iccen murhun ya balbalesu, tashi sukayi tsaye suna karewa motocin kallo,kowa da abinda yake aiyanawa a ranshi, cikin sauri bodyguard suka fito suka fara bude motocin tsakiya... Dogarai ne suka fito suna "takawarku lafiya, jinin sarauta, takawarka lafiya dan sarki, magajin sarki.... Bude wata hadaddiyar mota ash colour sukayi... Annur ne yafito hannunsa dauke da malika yana, kissing din goshinta"nan akafara binsa da kallo yayinda dogarai suka bude dayan part din suna wa minal kirari"takawarki lafiya, matar yarima kuma surkar sarki, Allah yaga bayan makiyanki, Allah yaja kwana hajiya minal".... Dabadan ance minal bace to tabbas da lubaba da haseeya sun karyata.... Mama ce tasaki baki tana goge idonta wai shin gaskene ko ba gaske bane"wannan kamar minal, Amma kuma ai taji ance matar sarki kodai batan kai akayi"..mama sai kara raba ido take .. Aziza da safwan aka budewa mota suma suka fito.... Nan minal ta sanya fara'a a fuskata tana kallon kaskon awaran suyarsu minal tace "Ahaba wa nake gani kamar su lubabatu da haseeya "ai sunajin ta ambaci sunansu suka karaso suka rungumeta suna fadin "minal kece".fashewa sukayi da kuka mai tsuma zuciya... .... Cikin mamana ne yabada wani sauti"kurrrrrr bashiri ta shige gida tadau buta, tashiga bandaki domin tasan wannan bakomai bane fyace gudawa.........

Aziza ce ta karaso wajen tana musu kallon hadarin kaji tace"ai saiku saketa karta shafa muku warin talauci, kunga ai karuwanci yayi rana, tunda gashi munsami maza a bariki.... Maganarce ta doki dodon kunnensu, shiru sukayi duk jikin kowa yayi sanyi.... Lubaba tace "Aziza dan Allah mu yafi juna, Adaina dawo da hannun agogo baya"......

Aziza tayi yar dariya tace"haba matar manya, au kinyi laushi kenan, ina mijin naki yake,ke kuma haseeya ina biloniya din naganki da ciki kina sana'ar awara a waje, anya lubabar dana sani ce kuwa..... Cikin bacin rai lubaba taso kawar da zancen da fadin.... Minal ummanku tana cikifa,... Kukan dadi minal tasa, tayi cikin gidan yayinda kowa ya rufa mata baya...... Abbane kwance a tsakiyar gida akan taburma, rana sai dukansa yake, tundayafara rashin lafiyarnan daga mama har su lubaba wulakantashi suke, ko abinci zasu bashi saiya roka, saukin abinma tunda umma tadawo gidan ita takedan kula dashi, itama tace tanayine don Allah......... Muryar minal da aziza yaji suna kiran umma! Umma ina kike.... Turus sukaja suka tsaya ganin wani tamkar Abba yana kwance, ga ciki ya kumbura suntum......

Ummq ce ta fito daga daki hannunta rike da carbi, kuka tafara... Minal da aziza suma kuka suka fara... Suka nufi wajenta ta rungumesu, sunata kukan farinciki... Safwan yana gefe suda annur suna kallon matayansu yanda suke cike da sha'awar yanda suke kaunar mahaifiyarsu.... Saida su minal da umma sukayi kuka mai isharsu.... Muryar Abba suka tsinkaya yana "waye nakejin muryarsu tamkar su minal

Minal ce ta juyo tana "Abba mune, bakada lafiyane... Cikin dauriyace minal nine kunga yanda Allah yazamar daniko, hakkinku shike dawainiya dani, naci amanar mahaifinku minal dan Allah ku yafemin.... Zama sukayi a taburman da luBaba ta shinfida musu... Abba yakara fadin minal dan Allah ku yafemin"cikin kuka minal tace wallahi ni dama Abba ban rikeka a zuciyaba ni na yafe maka, kullum adu'a nake maka Allah yasa kagane, har yanzu ina kaunarka kuma ina kallonka a matsayin abbana, kuma duk nasan rudin shedane ne yake dawainiya dakai, wallahi

Please Login or Register in order to submit comment