Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sakin linzamin tare da zabura cikin d'aga murya Yance.
*Guramm!!.* inda nan take *Guramm* yayi wani tsalle da sufa ya tsallake katangar da akayi da niyyar duk wanda ya tsallaketa shine yaci gasar, tuni aka d'auki tafi da sowar taya murna ga *BARDE* Inda Safwan 2 da Prince dawakan nasu sukazo a tare masu kula da dawakai ne sukazo suka rik'e musu linzamin dawakan ko wanne ya sauka.



Yusuf ko cikin zafin nawa ya diro daga saman dokin hannunshi d'aya ya saka ya rik'e k'ugunshi had'i da cusa d'aya hannun cikin gashin kanshi tare da maida numfashi, sannan ya sunkuyo tare da yin sujjada da mik'ewa duk a lokaci d'aya,
yayinda duk motsin da yayi aketa daukarsa hoto da video, mutane sai ihu suke da sowa tare da tafi suna. "BARDE! Barde!! BARADEN Adamawa!!!."
Cikin tsananin farin ciki Malam Jabir ya taho yana farin ciki shine yazo na d'aya rungume Yusuf yayi inda shiko Safwan cikin ciccin magani ya karaso ya mik'awa Yusuf hannu sukayi musabaha had'i dace mishi. "Congratulations". shima rungume shi Malam Jabir yayi nan Prince ma yazo yayi masa congratulations had'i dayin musabaha, nan suka k'arasa rumfar da aka tanadar dan hutawar su.



A sannu sauran yan tseren suka k'araso Aryan da Affan sun taya Yusuf farin cikin nasarar dayayi musu.



Kano Team da Jos team aka had'a inda suma nan d'aya daga cikin yan kano ya samu nasara sai aka k'ara had'a partercot Polo team da Lagos polo team nan ma d'aya daga cikin yan Lagos yaci daga nan aka tashi inda nanda kwana 2 za'a k'ara kara dawowa cikin wadanda sukayi nasara zasu k'ara fafatawa har ko wacce jaha a fitar mata da gwarzo guda 1 da zasu hadu kuma su fafata a fidda gwarzon shekara a cikin su.



Bayan komawar su masauki ko wannen su yayi wanka, Yusuf ne kwance yana huta gajiyar da suka kwaso knocking d'in k'ofar d'akin su akayi Aryan ne yaje ya bude saboda Yusuf da Aryan d'akinsu d'aya Safwan da Affan kuma d'akin su d'aya, Malam Jabir ne ya shigo tare dasu Safwan Affan jin sallamar shi shine ya saka Yusuf bud'e idanuwan shi da suke lumshe kallo 1 zaka masa ka tabbatar akwai tsantsar gajiya da damuwa a tattare dashi, gefenshi Malam jabeer ya zauna cikin kulawa da k'aunarshi yace.
"Tabbas kunyi bajinta kunyi k'ok'ari da k'wazo haka kuma akeso ga ko wanne d'an wasa yanuna iya bajintar shi kuma Alhmdllh kun nuna."
sai kuma yayi shiru tare da zubawa Yusuf ido cikin nazartan yanayin shi Yance. "Yusuf!". ya k'ira Yusuf da kanshi ke k'asa d'ago idanuwan shi yayi ya sauke akan k'wayar idon Malam Jabeer da yace.
"kai Allah ya bawa nasarar zaka wakilci jahar ka duk da inada yarda a kanka amma kallo 1 za'ayi maka a hango tsantsar damuwa a tattare da kai ka sani firgici ko damuwa suna tauye samun nasara ina rok'arka kayi fatali da damuwar nan taka ka aro jarumta da karsashi har mukai ga nasara duk da nasara daga Allah take amma muna fatan Allah ya bamu". Ajiyar zuciya Yusuf yaja had'i da had'iye wani yahu daya tokare mak'ogaron shi sai daya lumshe idanuwan shi ya bud'esu yace "insha Allah duk da ba wayona ko dabarata bace ya sakani samun nasara a yanzu ba face Allah ne yaban amma ina fatan gasar gaban ma Allah ya bamu nasara". had'a baki sukayi wajen fad'in "Ameen" inda Malam Jabeer yaci gaba dayi musu nasiha da nuna musu amfanin da nasarar da suka samu zai haifar musu a gaba ana haka aka kawo musu abinci ci sukayi kasancewar akwai gajiya a tattare dasu kuma lokacin 10:00pm tayi ya saka su Malam Jabeer sukayi musu sallama suka tafi makwancin su su kuma suka kwanta.




Washe gari da suka tashi bayan sunyi wanka sanadin maganin gajiya da suka sha gajiya tabar jikin su sai wadda ba'a rasa ba nan Malam Jabir ya shirya musu fita suje su zagaya gari.

Suna fita kai tsaye M, M, P, S, C , K, suka nufa.
Suna isa bakin Gate d'in sukaji anyi wani irin....!




*BY*
*GARKUWAR FULANI*

πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*HUKUNCIN ALLAH*

Page 1⃣5⃣

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*




πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡



~Kada dai ku manta kuna cin bonus d'in free page ne, hahaha kuma saura k'iris su k'are donma kunci sa'a wata baiwar Allah ce ta rok'eni Allah manza ta nema muku Al'farman in k'ara muku free page's din to saura kadan su k'are~


*Ga masu buk'atar biyan kud'in shiga group d'in Hukuncin Allah domin samun damar karanta littafin har k'arshe, zaku turo katin MTN na 200 kacal ta wannan layin 09097853276 ko kuma ku turo d'ari biyun ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai kiyi screenshort na shaidar kin biya ki turomin ta dai wannan layin da nakeyin what's App dashi 09097853276.*



```πŸ€¦πŸ»β€β™€πŸ€¦πŸ»β€β™€yaseen kuna sani ciwon kai masu tambayata tsoffin littatafaina da littatafan wasu marubutan, dan Allah ku sakarmin mara in huta, in littafin wata kukeso ita zaku tambaya bani Garkuwa ba, dan Wlh ni bana karanta littafin kowa bare in ajiyeshi, nawa kuma in dai kin nema a groups in sha Allah zaku samu.
πŸ‘ŽπŸΏMasu yimin transfer ta layin etisalat d'ina yaseen ku dena katin MTN nace muku zaku turo ta layin etisalat d'in ba cewa nayi kumin transfer ba hakama masuyin BTU ku bari, katin mtn zaki saya ki kofi number ki turomin ta what's app numbe 09097853276 ko kuma ta message inbox na, na kusafa na dena sakaku a group na duk masu turo katin etisalat, yaseen ba ruwana in kin turo na etisalat d'inπŸ€—β˜Ί
Ina yinku sosai Hukuncin Allah fans one & two, duk da yan fans one kun cika surutu, ko ya yan fans 3 kuma zasu kasance~ πŸ˜€. Toh fa kada ku manta gyaran jiki na amare da uwargidaye inadasu meda tsohuwa yarinya in da masu buk'ata kuyi min mgn```


Kai tsaye harabar hotel d'in M M S P C K, suka fita wani guri da aka k'awata kamar lambu an saka kujerun hutawa a cikin gurin ga bishiyu sun yiwa gurin rumfa inda kuma korayen ciyayi sukayiwa k'asan wurin k'awanya, sosai gurin zai saka nishad'i da nutsuwa a zuciya,
zama sukayi suna tab'a hira inda Malam Jabir yake dad'a koyar dasu dabarun tseren doki.


Kiran sallar magriba shine ya tashe su daga gurin suka wuce masallacin dake cikin hotel d'in sai da sukayi sallar isha'i suka fito daga masallacin kowa ya duke suka shige d'akunan su dan yin shirin bacci.



Washe gari ya kama ranar da za'a koma a kara fafatawa dan fiddawa ko wacce jaha gwaninta.

10:00am su Yusuf suna cikin *Murtala Muhammad square polo club kaduna* amma yau zuwan nasu da banbanci tunda su ba tseren zasuyi ba, nan aka gabatar da yan tsere sukayi inda aka fitarwa da kowacce jaha mutum 1 da zai wakilci gasar k'asar gaba daya da za'a gabatar nanda kwana uku.




Shiri sosai su Yusuf sukewa gasar dan kullum sai sunje training kuma Alhamdulillah akwai alamun nasara a gurin su, dan sun zage sosai dan fidda ogansu daga jin kunyar horaswan da yake musu, sannan shiko Malam Jabeer ya kafa ya tsare addu'a yake tayi ba dere ba rana dan neman cin nasara.

Yau ne ranar gasar fidda gwarzon shekara na k'asa, Yusuf kuwa tun asuba da ya tashi yakejin alamun ciwon marar shi kad'an-kad'an yana kartanshi daurewa kawai yakeyi kuma bayaso ya sakewa Malam Jabir gwiwa da yake ta karfafa mishi gwiwa da ganin shid'inne zaiyi nasara kuma gashi ya manta maganin shi a gida dan baiyi zaton ciwon zai tasar masa ba haka dai suka gama shiri suka fito driver ya kwashe su a mota zuwa *MURTALA MUHAMMAD SQUARE POLO KADUNA*.



Su gaba d'ayansu da zasu wakilci gasar ne a jere akan lafiyayyun dawakan su Adamawa polo team Yusuf zai wakilce ta sai Kaduna polo team Mahmoud zai wakilcesu, Kano polo team Hashim zai wakilcesu Lagos polo team Juidehrn ne zai wakilcesu ko wanne jaha dai wakilinta, kuma kusan gaba d'ayan su kwararru ne zakaru a cikin team d'insu anaji dasu, sannan duk sun d'an girmi Yusuf.
Yusuf dake zaune kan dokin shi kallo d'aya zakayi masa kasan ya shiryawa gasar kamar yadda sauran yan jahohi ma hakanne daga garesu duk suna rirrik'e da Polo stick d'insu a hannayensu na dama yayinda hayensu na hagu ke rirrik'e da linzaman dawakan masu da kyau,
a zuciyar Yusuf kuwa addu'a yake akan Allah ya basu nasara dan samun nasarar su tamkar wata d'aukaka ce data samu jahar su gaba d'aya.



Bayani aka farayi acikin loudspeaker din gurin akan 'yan tsare su shirya nan ko wannen su ya shirya ya daidaita zaman shi akan doki cikin abinda bai gaza minti 5 ba aka fara basu umarnin fara tsere yayinda d'aya daga cikin Al'k'alan gasar ya cilla musu d'an mulmulellen polo ball d'in.



Ko wanne mahayi cikin karsashi da k'warewa yake sarrafa dokin shi dawakan kuma suna bawa mahayan su goyon baya suna gudu yadda ya kamata tare da sassarafa polo stick d'insu da ciccila polo ball d'in cikin k'orewa,
saura baifi suyi tseren minti 20 ba marar Yusuf tayi masa wata d'amka tare da murd'awa da k'arfi ya saki polo stick d'inshi tare da saka hannunshi ya tallafe marar tashi lokaci d'aya jikin shi ya d'auki rawa gumi yahau karyo masa tako ina tuni ya saki linzamin dokin nashi dan tsananin rawa da jikinshi keyi rasa yadda zaiyi yayi gashi shine a gaba ya tserewa duk sauran yan tseren, dokin shi ya rage gudu ganin mahayin shi ya rage sarrafa shi runtse idonshi yayi da sakin yar k'ara ga zafin ciwo ga kuma yan tseren daya tserewa sunzo sun wuce shi, dabarar fara addu'a ce tazo masa a sannu ya fara karanta duk addu'ar da tazo bakin shi.



Cikin k'idima da fargaba Malam jabeer da yake kallon abin dake faruwa ta allon majigin da aka saka a kowanne kusurwa ta cikin studio din mik'ewa yayi cikin tashin hankali bakin shi d'auke da zikiri danya zame masa jiki inhar ba magana yake ba tom bakin shi ambaton Allah yakeyi,
su Aryan ma da hankalin su yakai kan abinda ke faruwa damuwa suka shiga da tashin hankali ganin sunga samu sunga rashi ga k'oshi ga kwanan yunwa addu'a suka farayi akan Allah ya basu sa'a.

Daddy kuwa hannu yasa ya tallab'e kanshi tare da jero Addu'o'i,
yayinda wurin dubban jama'a da dama suka rik'e kai ganin na gaba ya dawo baya


A sannu marar Yusuf ta fara saki k'ullewar da ciwon da take ya tafi tamkar an zare gashi daga cikin nono ajiyar zuciya yaja mai karfi dan zuwa lokacin har likitocin da suke kula dasu sunje sun tsareshi suna shirin fara bashi temakon gaggawa, zabura yayi da daka wani mugun tsalle abin kamar almara su kansu likitocin ba zasuce ga lokacin da sukaga sauk'anshi kan dokin da rarumo sand'arshi ta Polo stick d'inba sai kawai hawan shi dokin suka gani sai sukuwar shi suka fara gani cikin tsananin zafin nama, zuwa lokacin wasu sauran dawakan sun tserewa nashi da wajen 15 kilometers gudu yake cikin kwarewa dokin kuma da yake tafiyayye ne yasan sirrin tsare shima saiya k'ara gudu tamkar a sama yake tafiya.



A sannu Yusuf ya taddo yan baya-baya a tseren ai suna kan dawakan su amma dokin Yusuf sukebi da kallo ganin abin kamar magic kamar wanda ake sarrafawa da computer a sannu yakai ga dawakan da suke gaba Kano, Lagos, da kaduna sai katsina nan suka farayin taeren wuta-wuta kamar kiftawar ido suna hango jerarrun sandunan da aka jera kusan guda 7 a kurkusa inda su dokin zaina tsallakewa cikin k'warewa har yakai ga cinye gasar tseren kuma ba tare daya ture sanda ko d'aya ba, dokin Yusuf ne yayi wata sufa da sukuwa duk saiya wuce nasu dawakan yakai gab da gurin sandunan saiya rage gudun a sannu Yusuf ya fara sarrafashi yana tsalleke sandunan har yakai na k'arshe.
Ihu da sowa da tafistudio d'in ta d'auka kamarzata dare dan cikar jama'a da hayaniya, sai gefen da manyan bak'in sukene yake a nitse wurinda su maimartaba da wakilanci sannan duk jiharda sukazo gasar masarautarsu ta wakilto wasu sun zo, so shiyasa wurin ya had'a taron manya,
Malam Jabir kuwa sai cewa yayi.
"Allahu Akbar Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!."
sai kuma yajan wata doguwar ajiyar zuciya, Aryan da Affan da kuwa a kuje suka fara sakkowa daga matattakalar kujerar da suke suka nufi gurin Yusuf,
wanda cikin k'warewa ya diro daga dokin da durk'ushewa kan gwiwoyin sa yayi sujjadar godiya ga Allah daya bashi nasara tare dayin hamdala yayinda yan jaridu suke turuwar d'aukarshi hoto akan duk motsin da yayi,
su Aryan ne suka d'ago shi sai sukaga hawayen farin ciki a idanuwan shi suma dariya suka kyalkyale da ita da rungume shi a sannu matasa suka sassauko cak Yusuf yaji an d'aga shi ana ihu da juyi dashi ana.
"Sai *BARADEN* Adamawa, kaga d'an na koya ya zarta y'an na gada".
shi kuwa sai murmushi yake yana d'aga hannunshi sama tare da mik'a gaisuwarsa ga masoyansa.




A sannu sauran yan tseren suka k'araso inda Kaduna team sukayi na 2 Kano team na 3 Lagos team na 4 Katsina team na 5 Jos Team na 6 sai sauran yan state d'in suka k'araso daga baya.




Bayan gama murna nan aka jera duka yan tseren a layi da daddaya suna zuwa mai girma Sarkin Zaria na saka musu sarkar silver a wuya mai tambarin doki had'i da basu wani d'an a word mai alamar doki, har aka k'araso kan 'yan Kano aka basu kyautar su a matsayin sunzo na 3 sannan aka bawa yan kaduna ma tasu kyautar a matsayinsu sune na 2, sannan akazo kan Yusuf bayan an saka mishi tashi sark'ar ta gold a wuya aka mik'a mishi aword d'inshi nan aka bashi k'aton kofi inda aka fara d'aukar pic d'inshi ta ko ina sai flasher ke hassakawa nan matasa suka k'ara daukar shi cak suna zagaye cikin filin dashi hannunshi d'auke da Cup d'in.



Lokacin da taro ya tashi nan su Yusuf suka shiga mota dan tafiya masaukin su amma matasa haka sukayi dafifi wajen rakasu saida suka rakasu har masaukin su,
hotel d'in dasu Yusuf suka sauka dai bai samu nutsuwa ba har saida dare yayi.



8:37 pm Yusuf da ya fito a wanka d'aure da towel inda d'aya ke rataye a wuyan shi, inda siffar shi ta k'arfafan maza ta fara bayyana kasancewar shi matashi dan kimanin shekara 18 amman cikar haibarshi da kimarsa sun zarta haka Yusuf kyakykyawa ne farine k'al mai madaidaicin tsawo fuskarsa gwanin sha'awa sajenshi da yayi fuskar k'awanya shi k'ara mai cikar haiba da dottaku dan Yusuf irin mazannane masu halittar gashi mai kyau da tsulb'i bak'ik'k'irin dashi sai Shek'i yakeyi hanshi har baki lips enshi kuwa yan sirara masu d'an fad'i haka nan ida nunshi irin siraran idanun ne masu kyau basuyi k'attiba sai gashin girarsa da yabi saman idanshi yayi lunch hakan damtsen hannunshi da sharab'anshi da k'irjinshi da cikinshi k'asan cibiyarshi duk gashine a kwance lub-lub mai sulb'i da shek'i, gashin kanshi kuwa kamar na matashin balarabe,
hannun shi ya saka yayi baya da jikak'k'en gashin dake kanshi dabai gama tsane shiba ya fito cikin takun shi na zaratan samari ya k'arasa gaban mudubi had'i saka towel d'in dake rataye a wuyan shi yana goge gashin k'ansa dan tun safe bai samu nutsuwa da kad'aita ba sai yanzu,
zama yayi akan stool d'in dake gaban mudubin ya shafa mai had'i da fesa body spray a jikin shi sannan ya saka singlet ya zura jallabiya ya fesa turaren shi mai tsanyin k'amshi na TomFord .



Hararar Aryan yayi wanda tunda suka samu kansu in banda amsa call da yakeyi bashi da aiki sai daya tsuke fuska tamkar mace had'i da taune lips d'inshi na k'asa danya zame mishi d'abi'a cikin fad'a yace.
"Wai ba zaka tashi kaje kayo alwala kazo muyi sallah bane kadai san bamuyi sallar magriba da isha'i bako?". dariya Aryan ya shek'e da ita tare da juyawa Yusuf fuskar wayarshi yace.
"Kasan Allah ko *BARDE* yau handle d'inka ya samu k'arin fan's a k'alla sunfi dubu 11 kaga yadda ake ruwan comments and likeng da shearing pictures naka a duniyar media kuwa".
tsaki Yusuf yaja yace.
"Ina maka zancen sallah kana wani shirme daban, please kaje kayo alwala kazo muyi jam'i".
mik'ewa Aryan yayi had'i dayin mik'a yace.
"Toh wai kana nufin ni bazanyi wankan bane bayan kai ka shege cikin bayin kayi ta sama kamar mai canza fata, koda yake nasan wanka biyu kayi manza mai jabar tsiya da masifa".
cikin zafin zuciya Yusuf yace "Allah bazan jiraka ba, da kasan zakayi wankan ka tsaya biyewa shirme da shiririta, sannan in naga dama inma yi wonka shabiyu ba biyunba, banza d'an sa ido kawai".
dariya Aryan yayi yace "maida wuk'ar *BARADEN* Adamawa".
hannu Yusuf yakai da niyyar naushin Aryan d'in gocewa yayi ya shiga cikin bandakin da gudu, sanin halin Yusuf bayason jira ya saka shi yo alwalar da fitowa.
Yusuf ne ya jasu sallar cikin k'ira'a mai dad'i sukayi sallar magriba da isha'i nan Aryan ya tashi ya shiga wanka Yusuf kuma ya zauna fara Azkar nan akayi knocking k'ofa yaje ya duba abinci aka kawo musu k'arba yayi ya dawo yaci gaba da Azkar d'inshi koda Aryan ya fito wanka sai daya idar da azkar d'inshi gaba daya ya dad'e yana kwarara addu'a Allah ya kawo daidaito tsakaninshi da mahaifin shi sannan ya tashi jallabiyar jikin nashi ya cire ya zama daga shi sai singlet da boxer nan suka fara cin abinci suna tab'a hira cikin rumtse ido Yusuf yace.
"Aryan naso ace yau nasarar nan dana samu mahaifina baya fushi dani da nafi kowa jin farin ciki a cikin raina". shiru Aryan yayi tsahon minti 2 sai kuma ya sauk'e numfashi tare da cewa.
"Sorry Yusuf shi kuskure inya faru ba'a tuna shi hanyar gyarashi kawai za'a nema munanan muna addu'a in sha Allah zuciyar Abba zatayi sanyi ya yafe maka abin daka aikata".
cikin jin dad'in maganar Yusuf yace.
"Allah yasa".
bayan sun gama cin abincin nan Yusuf ya d'auki wayar shi ya shiga facebook ganin Aryan duk yayi posting pic d'in da akayi a gurin gasar kuma anyi comment da yawa dad'i ne ya kamashi kwanciyarshi ya gyara had'i da lumshe ido yace.
"Maman Yusuf Addu'a da Albarkar da kike sakawa Yusuf d'inki tana tare dashi a koda yaushe".
sai kuma yaji k'wallah ta cika masa a ido bayan hannu yasa ya goge nan ya fara yi musu godiya saiya shiga Instagram nanma abin ba Damara nanma yaga yawan fans d'in daya samu Allah ya k'ara yiwa godiya ganin ba wayonshi ko dabarar shine ya saka ba gashi ya samu d'aukakar dabai tab'a tunani ba a cikin k'ankanin lokaci satukan da suka gabata babu wanda ya sanshi sai iya yan garinsu Adamawa amma cikin abinda bai gaza kwana 5 ba kusan duniya kowa yasan da zaman shi babu wanda ya isa yayi maka wannan baiwar sai Allah, nan ya shiga whatsap groups shima magana d'aya ne anata comment akan gasar tseren da sukayi
murmushi kawai yakeyi tare da amsawa fan's nashi addu'o'in da suke mishi.



Hutun kwana 2 sukayi babu inda suke zuwa suna d'aki duk da haka kuma masoya suna kawo musu ziyara yau Malam Jabir yace ya kamata su shirya su fita su zagaya gari kasancewar gobe zasu bar kaduna zasu koma Adamawa.



3:30pm Yusuf da Aryan sanye suke cikin shadda gizna brown colour inda suka sanya hula zanna bukar milk da ratsin brown sai takalmi zira k'afa milk agogon silver ne d'aure a hannunsu sai zuba k'amshi suke sosai sukayi kyau cikin shigar fitowa sukayi daga d'akin su suna tafe suna hira Yusuf yana rik'e da sabuwar laptop and phones nashi yayinda shima Aryan yake rik'e da sabuwar wayarshi wanda aka rarraba musu.
Tsaye suke k'ofar d'akin Malam Jabir suna knocking Affan ne yazo ya bud'e musu kasancewar suma suna d'akin musabaha sukayi nan suka shiga sukayi musabaha da Safwan da Malam Jabir duk da Safwan sai wani dojewa yake dan rabonsu dashi tun ranar gasar amman shi a Affan yana zuwa susha hira,
dan haka yanzu ma hannu ya mik'away Yusuf da Aryan suka tafa tare yajo hannun Yusuf ya ruggumeshi irin ruggumar gayu ta gefe d'aya ido ya d'an kashewa Yusuf tare da cewa.
"Hi guys, hege Baraden Adamawa kana ceiling fa, matsalarka ka yad'e sajen nan ka kuma saki fuskar zakafi fitowa new blood, amman yanzu wallahi kayi kwarjini da yawa zaka ke hana mata ganin wasu mazan sai kai".
dariya sukayi dan Affan akwai rawan kai da abin dariya,
Malam Jabeer kuwa hannu yasa ya komo kunne Affan tare da matsewa yace.
"Ya salam Affan rawan kanka yayi yawa please ka koyi nitsuwa irinta Yusuf".
tsalle Affan yayi tare da yarfa hannu yana cewa.
"Gaskiya bazan iya zama ustazai irinku ba".
Affan yana matuk'ar Yusuf a ranshi shiyasa yake zuwa gunsu akai-akai
su gaisa su kuma sha hira dan yana matuk'ar son Yusuf da Aryan a cewarsa Yusuf ya zama sanad'in d'aga darajar masarautarsu.

Sosai Affan da Yusuf da Aryan ke raha,
yayinda tuni Safwan ya fice a parlour dan tsananin tsanar da yakewa Yusuf ji yake kamar ya baddashi a doron k'asa,
Malam Jabeer kuwa tuni yayi cikin bedroom dan k'arisa shirinsa,
Bayan ya fito cikin shiga ta alfarma sanan suka fito Malam jabir, Affan, Aryan sai Yusuf masallaci suka shiga saida sukayi sallah sannan suka fito driver ya d'auke su, a bakin gate suka samu Safwan suka d'aukeshi.

Kai tsaye gamji suka nufa, suna isa bakin gate d'in Yusuf yayi wani irin juyowa tare da zaro ido yana kallon gefen da Safwan yake, da sauri yasa hannunshi ya.







*BY*
*GARKUWAR FULANI*

[02/01 12:45 PM] My 2nd Mtn: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*HUKUNCIN ALLAH*



Please Login or Register in order to submit comment