Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuka,
shiyasa ya jawoshi cikin gidan.
shi sam Yusuf bai lura da itaba da yake tana bayan Zulaihat,
shiyasa ya ratsa gefe ya zauna kan sofa tare da kwantar da Aryan a gefenshi still kanshi na kan cinyarshi,
ita kuwa Zahra sai ta rab'a gefe.
haka nan sai taji kuka ya kubce mata,
sautin kukantane ya tada Aryan kuma daga baccin daya fara,
mik'ewa yayi tare da cewa.
"Abeeh Ammina tana kuka."
jin kukan ya k'aru ya sashi juyowa gareta,
ai yana ganinta ya mik'e da sauri da gudu yayi kanta,
cikin kukan ta durkuso k'asa dai-dai tsawonshi kana ta bud'e mishi hannu,
da k'arfi ya abka jikinta tare da cewa.
"Oyoyo Ammina."
ita kuwa ruggumeshi tayi gam tare sunkuyowa tana sumbatarshi tako ina murya na rawa take ce mishi.
"Miss you my Aryan, ka tafi ka barni bana iya bacci ko kad'an."
shi kuwa Aryan sai share mata hawayen yakeyi,
Abubakarne yayi gyaran murya tare da cewa.
"Toh yau dai zakiyi baccinki gaki ga Aryan d'inki."
mik'ewa tayi tare da cewa.
"Zomu tafi gida Abba zaiyi fad'a in yasan bana gida."
da sauri Zulaihat tace.
"A a ai yau kam sai dai mu kwana."
kai ta jujjuya tare da cewa.
"A a wlh ni kam zan koma gida dudu dai k'arfe bakwai da rabine,
in ban koma gida wa zaiwa Mama aikin safe."
shi kam Yusuf tunda ya kalleta sau d'aya bai kuma kallonta ba,
sai da yaji tace in bata komaba wa zaiwa Mamanshi aikin safe,
nanne ya d'an kalleta ta gefen ido,
cikin wani irin yanayi ya mik'e tare da nufar hanyar fita murya can k'asa yace.
"Ni na tafi saida safe."
Aryan ne yayi maza ya kwace hannunshi yaje gabanshi da gudu ya rik'o hannunshi tare da cewa.
"Abeeh ka cewa Ammi tazo muje gidanka mu kwana a can."
Yusuf kuwa rusunawa yayi tare da jawoshi ya ruggumeshi yana jin k'aunar yaron na ratsashi,
can cikin rashi kuwa yanaji bazai iya rabuwa da yaronba,
sai dai kuma yana jin wani sashi na zuciyarshi na tausayawa Zahra,
ita kuwa Zahra cikin sanyi tace.
"Aryan zomu tayi ko."
jin haka Abubakar ya mik'e tare da cewa.
"To tunda bazaki kwanaba kije Yusuf ya kaiki gida."
sai ya kuma juyowa ya kalli Yusuf da tuni ya fita cikin d'an d'aga sauti yace.
"Yauwa to Yusuf ka sauk'eta gida,
kafin ka wuce."

"Uyhummmm." yare da k'ara jan hannun Aryan suka fita,
shi kuwa Aryan sai tsalle yake yana cewa.
"Ammi ki fito kizo mu tafi gidan Abeeh na,
yafi gidan Abbanku kyau."
ita kuwa Zahra sai tsuke fuska tayi sabida takaicin yadda Aryan ya saketa yabi Yusuf,
cikin jin dad'i Adda Zulaihat tace.
"Toh ai sai ki tashi ku tafi".
cikin jin haushi tace.
"Ni na fasa zan kwana kuma kice mishi ya kawa min yarona."
cikin hima Adda Zulaihat tace.
"Ai kuwa wlh sai kin koma tunda da fari cewa kikayi bazaki kwana a gidana ba,
so dole kije ya meda ke."
sai ta kuma mik'e tare da tsuke fuska cikin nina girma tace.
"Maza tashi ki bishi."
rau-rau tayi da ido alamar zatayi kuka,
murya na rawa tace.
"Please kiyi hak'uri Adda ki barni in kwana a nan."
cikin kalato hatsala Zulaihat tace.
"Ke kije yana jiranki."
ganin yadda Zulaihat ta mata yasa ta mik'e cikin fushi da zubda kollah tayi woje,
Abubakar kuwa dariya yayi tare jinjinawa Zulaihat domin shi yasan manufarta shiyasa sukayi murmushi tare jinjinawa juna alamar tsarinsu zai tafi dai-dai.

Ganin yadda take tafiya tana saib'i yasa Abubakar biyo bayanta tare da cewa.
"Kiyi sauri mana."
cikin sanyi tace.
"Ayyah Ya Abubakar dan Allah ku b'arni in kwana a gidanku."
cikin had'e fuska yace.
"A a ba'a gidana ba kam,
in ma kwannan kikeso sai dai watarana,
so maza muje."
dole ta d'aga k'afa tare da sakin sassanyan kuka ita a zatonta ko kuma kyawanta da hantararta suke irin yadda Ummi ke nuna mata.

Suna isa gaban motar Abubakar da kanshi ya bud'e mata motar tare da cewa.
"Zo ki shiga."matsowa tayi jikin motar yayinda k'irjinta ke duke tara-tara,
lokaci d'aya zuciyarya ta shiga tuno mata abubuwa da dama,
tanajin Aryan na cewa.
"Ammi shigo mu tafi."
amman ta gaza motsawa saida taji Abubakar ya daka mata tsawa.
"Ke! tafi daga nan ana miki mgna kina tsaye, maza ki shiga."
jiki na rawa ta shiga,
kana shi kuma ya rufe musu motar tare da cemusu.
"Allah ya kiyaye hanya ki gaida mutan gida."
a saman lips Yusuf ya amsa da Amin,
kana yaja mota suka fita gidan.

Shi kuwa Abubakar cikin jin dad'i ya kalli Zulaihat tare da cewa.
"Allah dai ya dai-dai ta tsaka ninsu."
"Amin Amin Ameeeeeeeeen ya rabbil izzati."
tace sannan suka koma cikin gida.




Sukuwa su Yusuf,
tunda ta shiga bata kalli inda yakeba sai kanta ta kife kan cinyoyinta taci gaba da kukanda ita kanta bata san dalilinshi ba,
hakanan take jin kukan nacin k'arfinta,
Allah sarki Aryan kuwa sai shima ya zame jikin Yusuf sai ya koma jikinta,
jawoshi tayi kan cinyarta,
ta zaunar dashi suna fuskantar juna,
kana ta rungumeshi tare da manna kanshi tsakiyar k'irjinta,
sukaci gaba da kuka, shi dai Aryan kukanta ne ya sashi kuka,
cikin kukan yaketa tambayar. "Ammi meya sameki."
rashin abin fad'i sai kawai tace ba kai bane ka tafi ka barni ina kwana ni kad'ai."
sai ta kuma kife kai tana kukan rashin dalilin.

a haka har suka isa dai-dai masallacin k'ofar gidansu inda shima Yusuf sai zuciyarshi ta karaya,
yana tuno abubuwa da dama a rayuwarshi,
gashi yanaji yana gani shiga gidan mahaifinshi yafi k'arfinshi gidan ya zubawa idanu yayinda kukan Zahra da Aryan ke ratsa mishi jiki da zuciya,
itama Zahra yanzu tausayinshi ne ya k'ara k'arfin kukanta domin tasan yadda yake k'aunar Mama amman gashi a waje ita kuma tana ciki kuma bashi da damar ganinta,

Lumshe idanunshi yayi tare da taune lips enshi,
ita kuwa Zahra hannu tasa da nufin bud'e motar ta fita sai taji a rufe take,
hakan yasa ta juyo kanta ta kalli inda yake,
sai daga ita ya zubawa idanu yayinda yakai hannunshi kuma kan cd motar,
yatsarshi ya dannan a wani sashi na jikin cd,
sai ya kuma juyowa gareta sosai kanshi ya sunkuyar kan Aryan dake zubda hawaye,
goshinshi ya manna kan na Aryan,
yayinda sajenshi ke gogar tamtsen hannun Zahra data tallabe kan Aryan d'in,
ita kuwa Zahra gaba d'aya jikin tsuma yakeyi,
yayinda ta tsurawa gashin kawunansu ido.

Shi kuwa Yusuf hancinshi ya goga kan na Aryan tare da k'ara matsowa jikin Aryan d'in hannu yasa bisa fuskarshi kana yasa 'yar yatsarshi ma nuniya yana share mishi hawayen.
ita kuwa Zahra har yanzu hawaye da kuka mai cin rai takeyi yayinda hawayenta ke d'iga kan goshin Yusuf,
a hankali ya taso tare dasa hannunshi kan cd ya murd'a wani wuri alamun sautin mgnar ya k'ara,
cikin wani irin sanyin sauti mai ratsa zuciya da ruhi sautin wata wak'a ya ratsa cikin motar inda Yusuf ya bud'i baki a hankali murya can k'asan mak'oshi tamkar maiyin rad'a yake bin bakin mawak'in.
"Ehh rana wata shaida suke ni nakine!."
sai ya kuma lumshe ido tare da sunkuyowa kan Aryan murya can k'asa yaci gaba da bin wak'ar,
"Da za'a tsaga jinin jiki sunanki ne."
sai ya kuma rangwafowa kansa kad'an kana ya lumshe idanunshi,
sai ga wasu zafafan hawaye masu k'una suna bin fuskarshi,
k'ara rage sautin muryarshi yayi tare da k'ara volume d'in wak'ar,
kana ya d'an juyo fuskarshi saitin kunnenta,
tare daci gaba da bin wak'ar inda yake fad'in,
*"In mutuwar fuju'a tazo sanad'inki ne."*
sai ya kuma d'oro hannunshi kan Aryan tare da ciga da cewa.
"Maza kama hannuna, ki taho ta damana,
in dai na rasaki nayi rashin masoya na damana."
sai ya kuma sa hannu ya kamo Aryan tare da dawo dashi jikinshi ya rungumeshi.
ita kuwa Zahra,
kife kai tayi a cinyarta ta saki wani zazzafan kuka mai tono tsohon tab'o dake cikin zuciyarta tsawon shekaru hud'u da suka wuce,
tana cikin kukan taji,
hannunshi bisa......!






By
*GARKUWAR FULANI*
[24/01 7:30 PM] My 2nd Mtn: [1/22, 11:09 AM]


*HUKUNCIN ALLAH*

*PAGE 13*

Ta saman bayanta jin hakan sai jikinta fara karkarwa,
shi kuwa Yusuf k'ara masowa yayi tare dasa hannushi ya bud'e marfin motar kana ya gyara zamanshi tare da tallabe Aryan daya fara maida baccinshi,
ganin ya bud'e marfin motar ya kuma koma ya zauna tare yin kamar baisan da wani a wurinba hakan yasa ta fahimci ta fita yake nufi,
fahimtar haka yasa ta d'ago kanta daga kifuwar da tayi kan cinyarta,
tafin hannunta tasa tana share hawayenta still kuma wasu na korar wasu,
cikin muryar kuka ta kalli inda suke,
yayinda ta tsada idonta kan fuskar Aryan kana tace.
"Aryan taho mu tafi."
kafa d'arshi ya mak'e tare da cewa.
"Ni gidan Abeeh na zamu tafi,
muje can kiji Ammi zai d'oraki kan dokifa."
ganin bazai zoba ga dare na k'ara gashi Yusuf yayi kamar kurma sai tasa hannunta ta fara k'ok'arin jawo Aryan tana cewa.
"Don ubanka tunda aka haifeka ai nand'in dai kake, yau babu inda zakaje."
shi kuwa Aryan kuka ya fara don shi dam sam baya so a zagarmishi uwa ko uba,
shi kuwa Yusuf ido ya zuba mata,
tare da tsuke fuska,
gaba d'aya duk motsin da tayi sai taji idanunshi na yawo a jikinta,
haka yasa ta k'ara jawoshi shi kuwa sai mak'ale Yusuf yakeyi,
suna cikin haka taji Yusuf yana mishi mgna k'asa-k'asa.
"Aryan ka bar kukan ya isa, bita kaje gida nima yanzu zanzo."
cikin tashi zaune ya fuskanci Yusuf d'in tare da cewa.
"Abeeh kacewa Ammi ta dena zagin Ubana."
kai ya sunkuyar tare da had'e goshinsu wuri d'aya kana yayi guntun murmushi tare da cewa.
"Hmmmm ai ba zaginka taiba,
don ubanka tace,
toh kai kuma don uban naka zaka bita,
ba don k'arfinta ba,
ai zakaji mgnar ubanka ko?."
kai ya gyad'a tare da cewa.
"Ehh zanji."
murmushi yayi tare da sunkuyowa cikin kunne ya rad'a mishi wata mgna,
sai gashi yaro ya sauk'o da kanshi tare da mik'a mata hannu alamar ta d'aukeshi,
d'an guntun tsaki taja tare da jawoshi ta kikkimeshi a jikinta,
sannan ta juya ta fara kiciniyar fita,
ina sai abun kuma ya gagara domin Aryan dai ya girmi ta mishi irin wannan rik'on gashi motar irin masu tudunnane, ga takalmin k'afarta irin mai d'an tsini ne,
jin abun bazaiba karsu fad'i garin fita yasa,
ta midashi sannan ta fita,
shi kuwa ana ajeshe a d'ale cinyar Yusuf tare da cewa.
"Abeeh kace Ammi na tayi hak'uri kaga fushi tayi."
murmushi Yusuf yayi cikin son yaron komanshi da nitsuwa yakeyi,
d'agoshi yayi tare da cewa.
"Kai fita ta nan, sai kace mata inji Abeeh tayi hak'uri."
tsayuwa yayi a bakin k'ofar kan wani d'an abu da ake takawa yayin shiga ko fita motar,
juyowa yayi yana fuskantar Yusuf kana ya mak'e kafad'a tare da cewa.
"Pleesee Abeeh kace tayi hak'uri,
kar tayi fushi dani
in nine na fad'a cemin zatayi ubana."
ido ya zuba mishi tare da sauk'e numfashi,
ita ko Zahra ganin zasu b'ata mata lokaci yasa ta zagaya tare da zuwa ta gabansun ,
matsoshi tayi sosai ta yadda zata ciccib'oshi ta samu ta sauk'ar dashi,
hakan yasa duk suna fuskantar juna,
yunk'ura tayi tare da d'agoshi,
sai ta kuma sakeshi jin abida Yusuf ke fad'i
fuskar Aryan yake kallo kamar dai shi yakewa mgnar murya can k'asa yake cewa.
"Ubanshi dai ba sa'anki bane, so ki dena zagar mishi uba,
kuma yace kiyi hak'uri kar kiyi fushi dashi."
da sauri ta rumtse idonta tare da kauda kanta ganin ya kawo kanshi garesu,
shi kuwa kai tsaye bisa goshin Aryan ya dire lips enshi tare da sumbatarshi,
shima Aryan sumbatar kumatun Yusuf d'in yayi tare da cewa.
"Abeeh kazo da wurifa."
kanshi ya sha sannan yace.
"Toh zanzo."
cikin kauda kai ta d'agoshi sannan ta sauk'eshi,
hanninshi ta rik'o sannan sukayi cikin gida.


Suna barin wurin Jafar dake cikin harabar masallaci yana hangosu,
shiyasa tunda ya fito bai koma gidaba saida yaga tagiyarsu,
hamdala yayi tare bin bayansu,
dan shima Yusuf tuni yaja mota ya tafi.



Suna shiga gida a parlour ta samu Mama cikin kula tace.
"Au dama ba kwana zakiyiba?."
cikin sauk'e numfashi tace.
"Toh Mama in na kwana wazai miki aiki."
ta bud'i baki zatayi mgna kenan sai ta kuma kalli Aryan da ya shigo tare da Jafar,
cikin wasa tace.
"Oh Aryan wato tun ba'aje ko inaba har ka mancemu, wato Abeeh dad'i."
da gudunshi ya k'arisa wurinta kana ya zauna gefenta tare da cewa.
"Yauwa Maman Yusuf, Abeeh na yace wai ince miki Yusuf d'inki ya gaisheki,
wai yana kewarki,
nace mishi ya nuna min Yusuf d'in sai yace min wai Maman Yusuf d'in tace Yusuf d'inta ya rasu baya duniya."
ido ta d'ago da sauri ta kalli Jafar yayinda shima ita us kalla,
ita kuwa Zahra jan gannunshi tayi tare da cewa.
"Tafi daga nan fad'i ba'a tambayeka ba,
muje kayi wonka kayi al'wala ka konta."
bin bayanta yayi tare da juyowa yana kallon Mama tare da d'aga mata hannu ya mata alamar zai dawo.

Jafar kuwa cikin sanyi ya juya tare da cewa.
"Mama saida safe ."
numfashi ta sauk'e kana tace.
"Allah ya bamu al'khairi."
Amin Amin yace lokacin da yabar wurin,
ita kuwa Mama ta dad'e a wurin tana tubka da worwara,
shi Yusuf zato yakeyi ko fushi takeyi dashi har yanzu.


Ita kuwa Zahra bayan sun gaba shirin kinciyarsu,
sannan tayi musu addu'a kana ta jawoshi jikinta,
ido ta lumshe tare da sauk'e nannauyan ajinyan zuciya,
idon ta kuma bud'ewa ta kalli fuskar Aryan d'inta sai ta kuma juyawa tare da cewa.
"Hmmmmm."
can kuma sai ta kuma juyi kana tace.
"Uhummmmmmm."
gaba d'aya ta kasa bacci sai juye-juye takeyi,
shi kuwa Aryan tuni yayi baccinshi.

Hamma Yusuf kuwa,
haka nan ya kwana a zaune a parlour domin tunda ya dawo ko bedroom d'in bai shigaba,
konciya yayi kan 3 str yayinda ya kwana ido biyu,
gaba d'aya zuciyarshi ta raunata a kan lamarin uwa da d'anta,
yanaji to ya zaiyi ya rabasu,
yadda suke son juna haka.

Haka dai yayi ta zama,
da tunanin har zuwa asuba kana ya,
yaje yayi salla sannan daya dawo ya samu bacci ya d'an saceshi.

8:00 Am ya farka daga baccin , mik'a yayi tare da yin salati kana ya rumtse idonshi ya tashi zaune,
numfashi ya sauk'e a hankali yana mai jin bugun zuciyarshi na harbawa da sauri-sauri,
idon ya bud'e a hankali jin sautin cida alamun hadari ne keyin gaggamin had'uwa,
mik'ewa yayi ya nufi bedroom,
yana shiga ya zare jallabiyar jikinshi kana ya fad'a bathroom,
tsawon 47 minutes yana bathroom d'in kana ya fito d'aure da towel yayi irin d'aurin nan da ake a zagaye wuya da gefe-gefen towel d'in kana ya daureshi ta bayan wuyanshi.
sai d'an k'aramin da yake rik'e dashi yana goge sumar kanshi.
gaban dressing mirror ya tsaya,
wani mai ya fara shafawa mai tsananin k'amshi saida ya shafe jikinshi kab sannan ya kuma bud'e wani mai ya shafe sumar kanshi,
kana ya d'auki kum ya fara gyara zaman gashin,
yana kontar dashi,
sai ya kuma gyara sajenshi, saida ya gama sannan ya fesa wani turare mai sanyin k'amshi,
sannan ya juya zuwa gaban tamfatsetsen durowar,
wasu riga da wondo ya fidda masu tsananin kyau farare k'al,
sai boxer da vest suma farare k'al,
kana ya fara kimtsawa,
saida ya gama shiryawa sannan ya d'auko hula mai kyau bak'a tare da zura bak'ak'en takalma,
sosai shigar tayi mishi abu da farin mutun ga kyau,
ga tsajen da yayiwa fuskarsa k'awanya sai ya k'ara fito da haibarshi,
parlour ya fito woyoyinshi dake kan sofar da yayi bacci ne,
ya d'auka sannan ya zaune yana mai jan tsaki,
cikin rashi yake tunanin.
"Shi Jafar meya hanashi kawo Aryan har yanzu,
sun barni ni kad'ai a gida kamar maye."
tsaki ya kuma ja tare da yin mgna a fili yace.
"Zanyi mgnin abin."
wayarshi ya zaro daga aljihun sannan ya kira Jafar,
shi kuwa Jafar lokacin yana gida tare da Zahra dan ta k'irashi yazo ya kaita gidan Tatti,
so sun fito kenan suna cikin mota kiran Hamma Yusuf d'in ya shiga woyarshi.
Jawo Aryan yayi tare da cewa.
"Aryan ga Abeeh na kira".
aifa da sauri ya bar jikin Zahra tare da amsar wayar cikin farin ciki yace.
"Hello Abeeh."
wani irin murmushin jin dad'i Yusuf yayi tare da gyara zamanshi cikin k'aunar yaron da begenshi yace.
"I miss you so much My happiness."
cikin jin dad'i Aryan yayi tsalle tare da fad'awa jikin Zahra kana yace.
"Miss you too my Abeeh."
murmushi yayi tare da cewa.
"Ban yardaba."
da sauri yace.
"Allah ko Abeeh nayi missing enka, tun d'azu nake cewa Ammi na ta kiramin kai kazo ka d'aukemu,
sai ta cemin wai zataci ubana in banda dena damunta da mgnar wanda bai damu da niba."
cikin fidda nannauyan numfashi yace.
"Hmmm yanzu ina kake?."
dariya yayi tare da cewa.
"Muna cikin motane Uncle Jafar zai kaimu gidan Tatti,
zanje inci banana."
sai ya kuma yi saurin juyowa ya kalli Zahra da ta d'an tureshi tare da cewa.
"Ubanka Aryan karyani zakayi ne,
ji yadda kaketa tsalle a kaina."
fuska ya kwab'e tare da yin muryar kuka kana yace.
"Abeeh ka cewa Ammi ta dena cewa zataci Ubana fa."
sai ya kuma yi maza ya manna mata wayar a kunnenta,
Jafar kuwa sai dariya yake musu,
shi kuwa Yusuf jin Aryan na cewa.
"Abeeh ka gaya mata tana jinka."
fuska ya had'e tare da taune lips kana cikin izza yace.
"Baki iya gaisuwa ba ko?."
kai ta jujjuya alamar a a kana cikin sanyi da jin bugawar zuciya tace.
"Ina kwana."
kai ya juya tare da lumshe ido ba tare da ya amsa gaisuwar tataba yace.
"Zakici ubashi ko?."
kai ta jujjuya tare da yin k'asa da murya tace.
"A a."
murya can k'asan mak'oshi yace.
"Hmmm irin tarbiyar da na rok'a ki bashi kenan,
koya mishi zagi ko?."
gaba d'aya jikinta macewa yakeyi da tsuma duk sanda yake mata mgna,
cikin sanyi da rawan murya tace.
"Hamma Yusuf k'aryafa yake min."
da sauri ya katseta tare da cewa.
"Karki k'arya tamin yaro, kece mak'arya ciya,
dan tun kafin yau na sanki ke babbar mak'aryaci ce,
ai na jiki yanzuma kince ubanshi,
shin Uban nashi sa'anki ne?."
a hankali tace.
"A a."
shi kuwa Yusuf mik'ewa tsaye yayi tare da cewa.
"Toh tunda kike cewa zakici ubanshi ai sai ki shirya cinsa d'in ko."
hannu tasa ta dungure kan Aryan tare da cilla mishi harara kana ta tura baki tare da cewa.
"Bazan sakeba."
cikin yin k'asa da murya kamar bazaiyi mgnaba yace.
"Kima sake mana in kin ganshi kusa dashi,
naji har ce mishi kikeyi ya damu da wanda bai damu dashiba,
irin zaki samishi tsanata a ranshi ko?."
da sauri ta rink'a girgiza kai domin ita dai bata fad'awa Aryan hakaba,
Jafar kuwa sai dariya yakeyi domin shi ya kitsawa Aryan haka,
dan samar da mgna a tsakaninsu,
cikin d'an d'aga murya tace.
"Allah ko Hamma ban gaya mishi hakaba."
tsaki ya d'anja kana yace.
"inma kin fad'a inma baki fad'aba, kin dai san baki fini sonshiba,
kuma kin sani ba ke kad'aice kika haifeshi ba,
don haka ba ke kad'ai ke sonshiba,
dan haka kima dena kuka in yana wurina,
don zan d'aukeshi,
shekara nawa kina tare dashi."
jin zai d'aukeshi ya sata jawoshi ta ruggumeshi kamar yanzun zai d'aukeshi cikin sanyi tace.
"In ba mutuwaba babu abinda zai rabani da shi."
baibi ta kantaba ya katse kiran kana,
ya mik'e ya nufi kan dinning table enda isa k'anin mai gadinshi ya shirya mishi d'an abin tab'awa domin shine mai mishi girki.



Ita kuwa Zahra mik'awa Jafar wayar tayi.
daga nan babu wanda ya kuma mgna har suka isa,
shi bai shiga cikin gidanba yace sai yazo d'aukarsu.

Tatti kuwa tana ganinsu ta cika da farin ciki dan dama tayi kewarsu,
cikin sauri Aryan ya k'arasa inda take cikin jin dadi ya fad'a jikinta tare da cewa.
"Tatti zanci Banana."
cikin jin dad'i tace.
"To zauna bari in kira Kakanka Sani yazo ya baka dan naga ya nika wasu shekaran jiya."
to yace tare da yawo roban zuba dake gabanta ya fara lasa.
ita kuwa Zahra cire laffayar jikinta tayi tare da zame d'an kwalin kanta,
kana ta konta kan 3 str,
tare da lumshe ido.
ganin duk yanayinta ya sauya yasa Tatti matsowa gareta tafin hannunta ta kife kan goshinta,
dan ita a zatonta ko ciwon kai ke damunta ganin idanunta sunyi ja,
jin kanta ba zafinne yasa Tatti gyara zama tare da fuskantar ta cikin kula tace.
"Zahra."
shiru bata amsaba,
sai hawayen da yabi gefen kunnenta,
kasancewar a konce take kuma rigingine tayi,
cikin tausayawa Tatti tace.
"Kiyi hak'uri kinjiko Zahra komai yayi tsanani zaiyi sauk'i watarana."
still ba mgna sai hawaye wani na korar wani,
ita kuwa Tatti a zatonta Aunty Amarya ce tayiwa Zahra wani abu da yake in ta yawaita hantarar in ta gayawa Tattin inta kuma ta kirata tai mata fad'a tana ragewa,
cikin kula tace.
"Aunty kene ta miki wani abun?."
sai yanzu ta samu damar yin mgna tare da tashi zaune cikin muryar kuka tace.
"Hamma Yusuf ne."
cikin mmki ta kalleta alamar neman k'arin bayani kana tace.
"Hamma Yusuf kuma?."
Kai ta gyad'a mata alamar eh
cikin danne dariyarta ta tab'e baki tare da cewa.
"Toh meya miki, kuma ina kika ganshi?."
kukun ta saki tare da rik'o hannun Aryan tace.
"Ba cewa yayi wai zai d'auke Aryan ba."
kai ta jinjina cikin jin tausayinsu dukansu tace.
"Toh kiyi hak'uri,
dan ya nuna yana son d'anki sai kiyi kuka,
inji yanzu ga Sulaiman da kuke uba d'ayama ko inda kuke baya gani bare yace zai d'auki d'anki."
kife kanta tayi kan cinyarta tana kuka sabida tasan Tatti bazata fahimci komai a kan lamarinba,
kuma wani abun sirrinta ne,
babu wanda zata gayawa sirrin d'an uwanta,
dashi sai ita sai Allah daya haliccesu.
haka dai Tatti tayi ta rarrashinta.


Shi kuwa Jafar yana sauk'esu kiran Yusuf ya kuma shiga woyarshi,
cikin girmamawa ya d'aga tare da cewa.
"Barka da safiya Hamma."
cikin kula yace.
"Barka dai Jafaru, ina Aryan d'in."
dariya ya d'anyi kana yace.
"Na barosu gidan Tatti."
"Meyasa baka kawo min shiba yau,
kuma naga ka kawo min breakfast."
hankalinshi ya maida kan titin tare da cewa.
"Na shigo na samu kana bacci a parlour shiyasa na fita dan kar in tasheka,
kuma dama Zahra na jirana zan kaita gidan Tatti,
kuma itace ta hana in je da Aryan."
Kai ya jinjina kana ya tashi ya matsa daga jikin dinning table d'in inda tea kawai ya d'an sha,
bedroom ya nufa tare da cewa.
"OK kun samu Uncle Gambo a gidane?."
cikin mamaki Jafar yace. "Uncle Gambo kuma?."
"Eh". ya bashi amsa a gajarce,
cikin kad'uwa yace.
"Hamma Yusuf kaddai baka san cewa Uncle Gambo ya rasuba."
cikin kad'uwa yace.
"innalillahi Uncle Gumbo ya rasu? yaushe? banjiba? wa zai gaya min to tunda baka gaya minba,."
a take ya jero mishi tambayoyin tare da rumtse ido yana jin wasu zafafan hawaye na tsastsafo mishi cikin jijiyoyin idanunshi,
tausayin Tatti ya rufe mishi zuciya,
Allah sarki su Aunty Amarya da uncle Sani da Tatti sun rasa gatansu jigonsu Garkuwarsu,
cikin sanyi Jafar yace.
"Wlh na mance yamin na gaya maka rasuwarshi,
ai yanzu yafi shakara biyu da rasuwa."
cikin sanyi da taune lips enshi yace.
"Allah ya jik'anshi da rahama,
in sha Allah zanje in gaida Tatti."
da haka sukayi sallama,
shi Jafar ya wuce wurin aikinshi.

Shi kuwa Yusuf key d'in motarshi ya zara tare da juyawa a sanyaye ya fita harabar gida,
jiki a mace ya shiga mota ya, ya fita,
kai tsaye bayan P. Z ya nufa,
yana zuwa k'afarsu Aryan mai gadin ya bud'e mishi gate,
ganin Yusuf ne yasa Baba mai gadi fad'ad'a fara'arshi tare da cewa.
"Lale marhabin da Yusufa bawan Allah."
cikin girmawa suka gaisa tare da cewa.
"Baba har yanzu kana aikin nan?."
Kai ya d'an juya tare da cewa.
"Toh ya za'ayi ana neman na rufin asiri,
gashi shima kanshi Aryan d'in yanzu baya aiki."
cikin mamaki Yusuf yace.
"Baya aiki kuma?."
Kai ya jinjina tare da cewa.
"Ai tun bayan gama shariyarku ya bar aiki,
yace ya bar aikin law har abada,
ya barshi kamar yadda ya bar nonon uwarshi,
to kuma har yanzu bai samu wani aikinba."
cikin mamaki da kullewar tunani Yusuf yace.
"Yanzu yana gida dai ko?."
"Eh yana nan ai yanzu bai fiye fitaba."
cikin motarshi ya koma tare da,
d'auko rafan kud'i yan dubu-dubu guda biyar dubu dari biyar kenan,
mik'awa Baba mai gadi yayi tare da cewa.
"Baba ga wannan ka fara jari,
in sha Allah in na huta na samu sukuni zan zo har gidanka,
mun gode Allah ya bar zumunci."
Allah sarki Baba mai gadi kuka ya rinkayi tare da samishi a'lbarka
shi kuwa Yusuf kai tsaye part d'in kaka ya nufa,
inda a bakin k'ofar shigan yayi kicibs da yan tagwayen Aryan, mace dana miji,
d'aya Yusuf d'ayar kuma Asma'u sunan mahaifiyarsu kenan,
cikin k'aunar yaran ya sunkuyo tare da ciccib'arsu duka biyu kana ya nufi cikin parlour yana cewa.
"Kai me Rafi'a take baku kukeyi k'atti haka."
cikin fara'a Hajia kaka ta fito daga kitchen tana cewa,
"Muryar wa nakeji kamar Yusufa."
hararar gefe ya mata tare da cewa,
"Yusuf dai ba Yusufa ba."
murmushi tayi tare da cewa.
"Bazance Yusuf d'inba Yusufan zance."
dariya yayi tare

Please Login or Register in order to submit comment