Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

assalamu alaikum a d'an saurara munada d'aurin aure a nan yanzu."
jin haka duk aka koma aka zazzauna kana cikin sanyi Daddy Ya matso gaban Abba kud'i ya zaro a aljihunshi kimanin dubu hamsin,
cikin sunkuyar da kai tare da zubda hawaye,
murya na rawa yace.
"Yaya ina nemawa d'ana Yusuf auren d'iyarka Zahra?."
cikin wani irin mmki Abba ya zubawa Daddy idanu cikin tausayin hak'urin k'anin nashi sai gashi idanunshi na zubda hawaye,
jin haka Malam Jabeer kuwa shima ya gyara zama cikin tsananin jin dad'i yace.
"Alhamdulillah ba matsala ni na bada auren Zahra ga Yusuf."
Cikin jin dad'i Daddy ya kalli ya kalli Malam Jabeer domin ya musu halacci,
jin haka kawai sai ya juya ya fuskanceshi shi kuwa Abba kai ya jinjina mishi alamar suyi abinda suke shirin yi ba matsala.

A nan a wurin a wannan yamancin na wannan ranar a wannan shekara ta 2020 wanda yayi dai-dai da Yusuf ya cika shekara 30 Zahra kuwa shekara 20 aka d'aura aurensu bisa sadaki dubu hamsin tare da shaidun mutane anguwa bisa waliccin Malam Jabeer wa Zahra Daddy kuma wa Yusuf.
to fa wannan abu shine Hukuncin Allah,
kowa ya cika da alhini da mmkin wannan lamarin.
bayan an gama d'aurin auren kamar yadda shariya ta koyar,
kana aka raba horon nan da sweet d'in aka bawa mutanen cikin masallacin Alhamdulillah kuma ya ishi mutane da yake goron yanada d'an yawa.

Shifa Yusuf baya fahimtar abinda akeyi domin shi baya cikin nitsuwarshi,
haka itama Zahra sam batama ji me aka fad'a a masallacin ba.

Maman Yusuf kuwa sujjada tayi tare da godewa Allah tanayi tana murmushi still hawaye na bin fuskantar,
Hajja innama hamdala yayi cikin jin tausayin jikokin nata.
Aunty Amarya kuwa tafi kowa jin dad'in wannan al'amarin.

A masallacin kuwa bayan an gama komai na d'aurin auren sai Daddy ya kuma fuskantar Man liman cikin sanyi da rauni yace.
"Man Liman ayi mana gayyar jana'iza yanzun nan,
Allah yayiwa Aryan rasuwa."
cikin tsananin kad'uwa da firgita Man Liman ya kalleshi tare da cewa.
"Aryan kuwa yanzufa shi yazo ya d'udd'ura ruwa a butocin nan."
cikin sanyi Daddy ya jaddada mishi tabbas shi d'in dai.
gaba d'aya jikin Man liman rawa yakeyi sai tambyar Daddy yakeyi yana yaddada mishi har baki uku,
sannan ya koma ya zauna tare da gyara zama cikin raunin murya yace.
"Al'amarin ubamgiji ya wuce wasa."
sai ya kuma rumtse ido hawaye na zuba tare da cewa.
"innalillahiwa'inna'ilaihi rajiun."
sai ya kuma yi shiru dan kukan da ya subuce mishi,
yayinda gaba d'aya mutanen cikin masallacin dama unguwar gaba d'aya aka kasa kunne domin in anji haka dai to anyi rashine.
shi kuwa man liman goge hawayenshi yayi tare da ci gaba da cewa.
"Innalillahiwainnailahirajiun, ana gayyar jana'iza a k'ofar gidansu Alhaji Aliyu Allah ya yiwa jikansu Aryan rasuwa."
sai kawai tsohon nan ya kife kanshi jikin guiwarshi ya saki kuka mai rauni wanda har mutanen uguwa sunajin sautin kukanshi can k'asa-k'asan las fik'an
ganin haka yasa Malam Jabeer kashe las fik'an kana ya kayo cikin rauni ya kalli inda Yusuf ke zaune yana bitar karatu inda yake karanta arrahaman,
yanayi muryarshi na rawa, gabanshi yaje tare da karb'ar qura'an d'in ya ajiyeshi kana ya mik'ar dashi tsaye ruggumeshi yayi tare cewa.
"Kayi hak'uri Yusuf dukkan tsananin yana tare da sauk'i kayi mishi addu'a,
cikin kuka da tausayin kanshi ya gyad'a kanshi alamar gamsuwa,
daga nan duk suka firfito,
inda suna fitowa suka samu Aryan babba da Affan duk sun zo sabida tun kan a shiga masallaci Jafar ya kirasu ya gaya musu rasuwar Aryan.

kai tsaye Malam Jabir Affan Aryan Babba da Daddy duk cikin gida suka wuce.
yayinda Jafar da Ibrahim suke biye dasu a baya suna rik'e da makara.

Bayan sun shiga ne Daddy da M Jabeer suka sakashi cikin makarar kana suka rik'o da nufin zasu ita zasu k'ofar gida cikin,
sanyi Yusuf ya durk'usa gaban gawar kana ya lumshe idonshi hawaye masu zafi suka rink'a tsastsafo mishi murya na rawa ya fara yi mishi addu'o'i saida yayi mai tsawo kana yaci gaba da cewa.
"Koda baka raye alk'awarin da nayi maka yana raye,
duk da Allah bai maka tsawon rai da zaka cika min Al'k'awarin da kayi min ba,
insha Allah ni zan cika maka naka."
ganin kamar Yusuf bai cikin haiyacinshi ne yasa suka d'aga makarar shi kuwa Ibrahim cikin rauni da muryar kuka ya kalli Daddy tare da cewa.
"Daddy a kira Zahra tazo ta ganshi mana."
cikin sanyi Daddy yace.
"A a barta ganin nashi tashin hankali zai k'ara mata."

Haka aka fita da gawar Aryan aka sallaceshi kana aka wuce dashi gidanshi na gaskiya,
bayan sun dawo daga binneshi ne,
Daddy ya kamo hannun Yusuf kai tsaye ya nufi cikin gida dashi,
yana shiga ya wuce parlour Hajja inna dashi ajiyeshi yayi kana ya koma part d'in Maman Yusuf inda ya samu suna zaune a parlour Zahra nata kuka,
ba mgna kawai sai kamo hannunta yayi,
kai tsaye ya juya da ita parlour Hajja inna.


Suna shiga sai ya kamo hannun Yusuf tare da sa mishi hannun Zahra cikin nashi cikin sanyi da tausayi ya kallesu
tare da cewa.
"Alhamdulillah Yusuf yau dai ga Zahra a matsayin matarka ta sunna,
Allah ya baka ikon rik'eta da haqurin zama da ita.
Ke kuwa Zahra ga Hamma Yusuf d'inku a matsayin mijinki kiyi biyeyya a gareshi in har kina son faranta min rai Allah ya baku zaman Lfy da zuriya ta gari.
Dukanku biyu babu wanda na nemi shawararsa na yanke hukunci ne dan ra'ayin kaina na d'aura muku aure kuma ku dukkanku ina kyautata zaton zakuyi min d'a'a kuyi na'a da matakin dana d'auka a kanku,
ina fatan haka ya zama sanadin k'arshen bak'in cikinku,
ina fatan kuyi hak'iri da rashin Aryan kada kuyi ta zubda mishi hawaye kuyi fata da addu'ar Allah ya baku wani d'an da zai maye muku gurbin nagartarshi, ku sani Allah da ya bamushi ya fimu sonshi,
shi daya rasu baiyi gaggawaba hakazalika muma da muke raye bamuyi jinkira zamu amsa kiran mahaliccinmu a ko wanne lokacin,
dan haka kuyi hak'uri Yusuf ka d'auki matarka ku tafi gidanka."
sai ya kuma saki hannayensu da ya had'e wuri d'aya tare da juyawa hanyar fita yace.
"Allah ya yiwa rayuwar aurenku al'barka."
Yana fad'in haka ya juya ya fita k'ofar gida inda ake karb'ar gaisuwar makokin,
inda Abba, Affan, Aryan Babba Malam Jabeer, Jafar, Ibrahim, Man liman Bappa Njagirde, Bashir d'an liman abokin Yusuf,
tare da uncle Sani k'anin Aunty Amarya dan ta kira ta shaida musu,
suke zaune nan suka zauna akaci gaba da amsar gaisuwa.



Cikin gida kuwa Mama da Hajja inna duk suna parlour Maman inda tuni mak'ota suna shigowa domin kowa yaji rasuwar tana ratsashi.


Hamma Yusuf da Zahra kuwa tunda Daddy ya fita Zahra ta saki wani marayan kuka mai ban tausayi,
shi kuwa Hamma Yusuf sarkin hak'uri sai idanunshi ya limshe yayinda tuni hawayen ciki suka samu damar sauk'a,
lips enshi ya had'e duka biyu ya taunesu kana ya rink'a sa babbar yatsar k'arfashi yana danne mai binta,
yana jin kukan Zahra na cika mishi kunne,
so yake ya yi mata ta'aziyar rashin gudan jikinta domin yasan duk yadda yakeji a ranshi fin haka takeji a matsayinta na uwa.
ita kuwa Zahra kukan abu da yawa takeyi ga rashin d'anta ga auren bazata,
wanda bata san matsayinta a wurin wanda aka aura matanba ga rabuwa da gida da Mama,
sai ta kuma saki wani nakatsasshen kukan da yasa Yusuf juyowa ya kalleta,
hannunshi yasa a hankali ya rumtse hannunta dake cikin nashi,
idon ya k'ara zuba mata ganin gaba d'aya fuskantar ta kumbura tayi jazir hatta lip's nata sun haye sama,
ida nuntama duk sun kumbura cikin farin yayi jazir,
uwa uba ga jikinta da yayi tsananin zafi alamar zazzab'i mai k'arfi,
cikin sanyi yasa hannunshi duka biyu ya rumtse tafin hannun nata,
yatsarshi manuniya ya saka cikin tafin hannun nata yana murzawa a hankali cikin salon rarrashi,
kana ya d'an matso da k'afarshi kusa da ita tare dasa tafin k'arashi kan rufar k'afarta yana d'an d'agawa yana d'an bubbuga saman k'afar tata a hankali hankali alamar rarrashi da kuma tausayawa,
cikin kukan ta kayo ta kalleshi jin abinda yake mata,
gashi ya matsota har cinyarshi na gogartata cinyar,
kwayar idanunshi ya jujjuya mata alamar tayi shiru,
kana ya k'ara matse hannunta,
ita kuwa ganin kamannin Aryan a fili a kan fuskarshi sai kawai ta sunkuyar da kai tare da rushewa da kuka,
k'ara rik'o hannunta yayi cikin tausayawa ya d'ago hannunta da nashi dake sark'afe da juna,
kan fuskarshi ya manna tafin hannunta dake manne da nashi ya fara goge hawayenshi dake bin fuskarshi da bayan hannunta,
ido ta zuba mishi cikin tausayawa kanta da rayuwarshi,
sai kawai ta manna kanta a gefen kafad'arshi taci gaba da kukun.
shi kuwa yana maici gaba rarrashinta da mata body language enshi.


A k'ofar gida kuwa ganin mak'ariba ta gabato yasa,
M Jabeer mik'ewa tare da kallon Affan da Aryan kan ya kalli Jafar cikin sanyi yace.
"Muje cikin gida mu gaisa dasu Mama,
zamu wuce gida."
To Jafar yace tare da yi musu jagaro,
parlour Mama suka fara zuwa sukayi mata ta'aziyar kana suka wuce parlour Hajja inna dan ta shaida musu Zahra na can.

Sallama sukayi kusan sau biyu amman ba amsa sai shesshek'ar kukan Zahra da sukeji,
saida Jafar ya kuma sallama a karo na uku sannan Hamma Yusuf ya bud'i baki a hankali ya amsa,
jin an amsa musune yasa suka shiga.
ganin sunada yawane yasa Zahra tayi saurin janye kanta da kiciniyar zame hannunta daga nashi,
amman ina ta kasa sabida gyara rik'onma yayi,
kana ya d'an kalleta ta gefen ido tare da tattab'a k'afarta da tashi alamar ta nitsu.
haka yasa dole ta nitsu tare da sunkuyar da kanta,
M Jabeer kuwa cikin tausaya musu ya amsa gaisuwar da Yusuf ya mishi kana yace.
"Allah ya jik'an Aryan yasa ya huta,
ku kuma Allah ya baku madad'inshi."
cikin sanyi murya can k'asa Hamma Yusuf ya amsa da Amin Amin kan lip's enshi,
Aryan babba kuwa ya gaza mgna sai hawaye yaketa zubdawa,
Affan ne yayi k'arfin hali kallon Zahra murya a sanyaye yace.
"K'anwata kiyi hak'uri kibar kukannan haka kiyi mishi addu'a fatanmu Allah ya baku wani madadinshi,
Allah ya jik'anshi."
kai ta gyad'a mishi alamar gamsuwa kana tace Amin,
shi kuwa Aryan murya na rawa ya kalli Yusuf tare da.
"Allah ya jik'anshi da rahama yasa ya huta."
murya can k'asa Yusuf yace.
"Amin my Aryan."
sai kuma duk suka fashe da kuka mai sanyi tausayin Yusuf yana ratsa zuciyar Aryan shiyasa ya yunk'ura ya fita yana zubda hawaye,
kana Affan da Jafar suka bi bayanshi.
M Jabeer kuwa cikin nitsuwa ya kalli Yusuf tare da cewa.
"Kayi k'ok'ari ka taushi zuciyarka,
ta hakanne zaka taushi tata zuciyar,
dole ka zame mata Garkuwa,
har zuwa lokacin da mantuwa zata danne zafin dake cikin zuciyarta,
Daddy yace ku fito ku tafi gidanku."
Kai ya jinjina tare da motsa baki alamar zaiyi mgna dan yasan M Jabeer bashi son wannan d'abi'a nashi na body language,
murya can k'asa yace.
"Ngd Malam kayi min godiya wurin Daddy."
sai ya kuma k'ara rumtse hannunta jin ta saki shesshek'a.

Shi kuwa M Jabeer salama ya musu sannan ya fita.

Bayan ya fitane ya sallami su Abba dan lokacin salla nata k'aratowa kuma shine limamin masallacin fadar jiha so shiyasa yake sauri ya tafi.

Bayan ya tafine Daddy yayi cikin gida,
daga tsakiyar gidan ya tsaya kana ya d'an d'aga murya yace.
"Yusuf! Yusuf!! fito ku tafi."
Daga cikin parlour ya amsa tare da mik'ewa tsaye kana ya jawo hannun Zahra,
yana gaba tana biye dashi suka fito,
suna zuwa tsakiyar gida,
sai ta ratsa tayi part d'in Maman Yusuf da sauri Daddy yace.
"Ina kuma zakije?."
cikin rawan murya tace.
"Wurin Mama zanje."
kai ya jujjuya mata alamar a a,
sannan ya nuna mata hanyar fita tare da cewa.
"wuce kibi mijinki."
cikin sanyin jiki ta kayo hawaye na zuba tace.
"Please Daddy a barni mana in zauna kusa da Mama."
kauda kanshi yayi dan tausayinta da yaji tamkar ya tasata a gaba yayi ta kuka to amman ya zaiyi dole ya nemar mata mafita,
yasan tabbas in tana gaban Mama zatafi sakewa to amman dole tabi mijinta.
cikin d'aga sauti yace.
"Nace kibi mijinki ko."
kai ta sunkuyar hawaye na zuba kana taje gefen Hamma Yusuf d'in ta tsaya.

Ita kuwa Maman Yusuf tun mgnar Daddy na forko itama ta sako hijabinta kana ta fito tsakar gidan bata kalli inda Daddy yakeba tabi bayan Yusuf da Zahra,
cikin mmki Daddy ya biyo bayansu tare da cewa.
"Maman Yusuf ina kuma zakije?."
ba tare da ta juyoba tace.
"Zanbi d'ana tunda dama Abbanshi yace duk randa yasa k'afa ya shigo gidannan a bakin aurena,
to yau sanadin rasuwar Aryan ya shigo dashi shiyasa zan bishi shida matarsa nasan zasu rik'eni iya rai da mutuwa."
cikin mmki suka kalli Abba da yake tsaye gefen motarshi da suka rab'a dan wucewa,
bai kalli kowaba bai kuma ce komaiba,
sai kawai yasa hannunshi ya kamo na Maman Yusuf kana ya juya da ita cikin gida.

Shi kuwa Daddy murmushi yayi tare da cewa su Yusuf ku tafi.

haka suka juya suka tafi.


Bayan sun isa Dau Girei yana shiga cikin gidan ana kiran sallan magrib,
parking yayi kana ya juyo a hankali ya zuba mata ido ganin har yanzu hawaye take zubdawa cikin wani irin sanyin jiki ya roggofo kan kujerar da take bikinshi ya saita kan kunnenta ido ya lumshe tare dasa hannunshi ya kamo nata murya can k'asan mak'oshi yace.
"i......!






By
*GARKUWAR FULANI*
[30/01 6:11 PM] My 2nd Mtn: *HUKUNCIN ALLAH*

*PAGE 18*


NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*



"in Allah ya jarabceki da abu ko wanne irine,
walau dad'i ko akasinshi,
kamar yadda ya jarabcemu a yanzu,
godiya zamuyi gareshi mu karb'i k'addaratmu da hannu bibbiyu muyi imani a cikin lamarin muyi hak'uri domin Allah shi ya bamu Aryan kuma ya fimu sonshi kuma shiya d'aukeshi garemu a lokacin da yaso,
Kiyi hak'uri ki dena zubda mushi hawayenki a matsayinki na uwa,
ki shiga cikin gida kiyi al'wala kiyi sallah kiyi mishi addu'a shine kad'ai gatan da zakiyiwa Aryan,
dan Allah kibar kukannan haka kinji fa jikinki zafi alamar zazzab'i."
cikin sauk'e numfashi da rumtse ido ta janye hannunta kana tasa hannu ta bud'e marfin motar ta fita.
Fitowa yayi shina kana ya mata jagaro zuwa cikin gidan,
kai tsaye har bedroom d'in dasuka kwana shida Aryan jiya ya kaita kana ya juya ya fita,
ita kuma bathroom ta shige kana tayi al'wala sannan tazo ta tsaya kan carpet d'in dake tsakiyar d'akin,
ta kabbarta sallan.

Shi kuwa Hamma Yusuf daga nan cikin parlour yabi wani d'an corridor tafiya kad'an yayi sai gashi ya bud'e wata k'ofa mai azabar kyau,
cikin wani tamfatsetsen parlour ya ratsa wanda yasha kayan k'awa na jin dad'in rayuwa,
komai na cikin parlour white and red color ne sai d'an ratsin pink color a cikin white d'in,
kama daga sofas d'in da labulayen carpet d'in,
har fentin kusan haka yake kama tayis da saman d'akinshi,
can gefen dama kuwa wani k'ayataccen dinning area ne Wanda aka d'an rabashi da tsakiyar parlour da step duga 4 sai wasu irin ziran igiyoyi masu shek'in ruwan garai-garai wanda suka kasance labulen wurin sai kuma dinning table mai azabar kyau,
kana daga gefenshi kuwa ga washing hand baby,
sai d'aya kusurwan da yake manne da irin firij d'innan mai marfin glasses wanda yakeda d'an tsawo a gefenshi kuwa wani d'an show glass ne mai d'auke da cups kala da iri,
can cikin parlour kuwa
kayan kallone na zamani wanda sai masu hannu da shuni.
shiru parlour ba motsin komai,
illa hasken daya kunna,
gefen ginin ya ratsa inda yaje gefen AC rimot d'in Ac ya d'an zaro daga ma'ajiyarshi kana ya kunna AC sannan ya medashi wurin zamanshi,
a hankali yake taku tamkar mara lakka a jiki,
ido ya lumshe jin sanyin AC ya fara ratsashi kana yana jin sanyi tayis d'in na ratsa tattausar fatar k'afarshi,
still wani d'an gajeren corridor ya ratsa kana ya bud'e wata k'ofar sai gashi cikin wani bedroom wanda za'a iya mishi inkiya da aljannar duniya,
gadone shimfide a cikin d'akin wanda tamkar zai motso ya d'auki mai konci a kanshi sabida tsabar kyau da gyara da yasha,
komai na ciki irin na palon ne a kala hatta beshit da blanket dake kan gadon.

kai tsaye bathroom wanda yakai girman d'aki komai na buk'atar mutun akwai a ciki acan d'aya sashin kuwa wata durowace madaidaiciya wacce take cike mak'il da kaya kama daga rigunan wonka towel boxers vest 3 qtr,
sai d'aya sashin kuma wanda turaruka ne kala-kala,
masu sanyin k'amshi.

Jiki a mace ya zura k'afafunshi cikin wasu tattausan takalma kana ya wuce cikin bathroom d'in,
uzurinshi yayi na 3 minutes kana yayi alwala sannan ya fito gaban mirrornshi yaje inda wasu turarukan ke jere,
biyu daga ciki ya fesa kana,
yaje gaban durowarshi zare rigar jikinshi yayi sannan ya d'auko jallabiya fara k'al ya zura ba tare daya cire dogon wondon shaddar dake jikinshi ba,
yar hular tab'a kaji hadis d'inshi ya d'auko ya kifa kan sumar kanshi kana ya zari jarbinshi dake kan durowar mirror sannan ya juya ya fito.
Madadin yabi ta inda ya shigo sai naga ya bud'e wata babba k'oga wacce kai tsaye ta sadashi da wani d'an fili mai matuk'ar kyau wanda yafi kama da lambu,ta cikin nan d'in ya kuma bi wata hanya sai gashi a farfajiyar gidan,
inda
kai tsaye masallaci ya nufa,
inda yaja mai gadinshi da mai mishi girkin nan sukayi salla,
kana ya zauna a wurin yayi ta karatu har saida lokacin isha'i yayi sannan ya sake jansu jam'i sukayi salla,
bayan sun idar sun fito kenan sai ga Jafar kuwa ya iso,
bud'e mishi gate akayi,
kana ya shigo ganin Hamma Yusuf d'in a wurinne ya sashi fitowa da sauri,
kulolin dake baya ya bud'e ya dauko kana ya matso inda yake.
har zasuyi cikin gida Mai gadin ya d'an matso tare da cewa Jafar.
"Yau ina aboki baka kawo mana shiba."
juyowa Jafar yayi cikin sanyi ya kalli maigadin kana yace.
"Allah sarki ai Aryan ya rasu d'azu da yamma."
cikin tsoro Mai gadin ya zaro ido tare da cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajuun.
Allahu Akbar rai bak'on duniya Allah sarki yaro mai hankali."
k'anin mai gadi kuwa shima rasuwar Aryan ta girgizashi dan a cikin kwanakin da sukayi a tare d'innan yaron ya shiga rashi,
matsowa sukayi kusa da uban gidan nasu sukayi mishi ta'aziya,
kana sukayi cikin side ensu.

Shi kuwa Jafar bin bayan Hamma Yusuf d'in yayi har parlour shi cikin sanyi yace.
"Hamma Yusuf ga abinci Adda Zulaihat tace in kawo muku."
cikin sanyi ya kalli Jafar tare da cewa.
"Kaje gidanta ne ko dai taji rasuwar Aryan taje gida ne?."
ajiye kulolin yayi a gabanshi kana yace.
"A a Ibrahim ne ya gaya mata a woya,
so kuna fita ita da Amira duk sun zo,
sunema sukayi abincin dare,
shine tace in kawo muku,
tace kuma tanata kiranka baka d'agawa,
Zahra kuwa tama bar wayarta a gida."
kai ya sunkuyar tare da cewa.
"wayata tana cikin mota d'ayar kuma tana gida dama na bawa Aryan ita,
ga k'aramar kuma tana can d'akin."
cikin jin tausayinshi Jafar yace.
"Toh Hamma inje in d'auko maku woyoyin mana."
kai ya jujjuya mishi alamar a a. Kana ya turo mishi kulolin tare da cewa.
"D'auki abincin ka kai mata,
ka nuna mata inda kitchen yake."
to yace kana ya zari kulolin ta inda Yusuf ya shiga shima ta nan yabi ya nufi side d'in da Zahra take,
a kan dinning table d'in parlour ya ajiye kulolin kana,
ya shigo tsakiyar parlour kan sofa ya zauna tare da d'an d'aga murya ya kira Zahra.

Ita kuwa Zahra tunda ta idar da sallan isha'i tana zaune a bisa carpet d'in tana karatun Qura'an zuwa yanzu muryarta ta disashe sai dai hawaye shiyasa Jafar baiji tana amsa mishi kiran da yake mataba,
jin yanata kiranta yasa ta mik'e ta fito parlour,
cikin sanyi ta zauna gefenshi murya a disashe tace.
"Ya Jafar ina amsawa fa bakaji bane."
sai ta kuma sa hannu ta share hawayenta.
shi kuwa Jafar zamanshi ya gyara cikin girma da kaifin basira yayi gyaran murya tare da cewa.
"Zahra kukan me kikeyi ne har yanzu?.
kukan Allah ya karb'i rayuwar Aryan ko kukan gatan da mahaifinmu ya miki? ko kukan rabuwa da mutanen gida kikeyi mutanen da in banda Mama babu mai tausaya miki."
cikin sanyi ta girgiza mishi kai tare da cewa.
"Ya Jafar nima ina son in bar kukan,
to amman in na rufe idona sai Aryan nake gani,
kuma Ya Jafar Daddy baifa tambayemu ba dukanmu kawai yasa aka d'aura aure,
yanzu shi Hamma Yusuf ce musu yayi zai auren ko yana sona, mutumin da ko mgna baya minfa."
gyara zama yayi kana yace.
"Kina tuhumar Daddy ne da ya muku ba dai-dai ba?."
kai ta jujjuya alamar a a,
shi kuwa ci gaba yayi da cewa.
"Zahra ke Daddy yayiwa gata wlh rufin asiri ya nema miki,
zamanki a gida me yake haifarmiki banda bak'in ciki, inafa sane da abinda Ummina keyi miki, hakama Aunty da Hajja Inna,
Zahra ki rik'e aurenki ki rufawa kanki asiri,
bance Hamma Yusuf yana sonkiba kuma bazance yana k'inkiba,
lokacine zai nuna hakan,
kuma batun mgna kinfa san shi Hamma Yusuf tun fil azal haka yake halittarshi ce baida yawan mgna,
ko Mamanshi zakiga suna mgna sai tayi mgna biyar ya bata amsan biyu uku daga ciki kuma ya amsa da gabb'an jikinshi,
musamman kanshi shifa Hamma Yusuf komai na jikinshi zai mgna dashi kama daga Baki ido hanci kai hannu k'afarshi kai harda kafad'anshi haka Allah ya yishi yafi yawan yin body language akan mgnar fatan baki,
so duk lokacin da kike tare dashi dole ki zama mai lura da motsinshi domin zai amsa miki dukkan mgnarki da jikinshi koma ya miki mgna da jikinshi".
cikin zubda hawaye tace.
"Ya Jafar ai yana mgna da Aryan kam."
kai ya jinjina mata tare da cewa.
"Wani lokacinba, wani lokacin kuma suyi ta mgna da jikinsu, dan shima Aryan yanada d'abi'un Hamma Yusuf,
shin kin mance a gabanki yake koyawa Aryan mgna da girarshi."
kai ta jinjina kana tace.
"Dan Allah ya Jafar a kawo min Sharifa mu zauna tare."
mik'ewa yayi tare da cewa.
"Ya Abubakar ya hana yace kada a baku ko tsuntsu a barku ku kad'ai in kunga da hali ku saki ranku in kinga zaki iya tabbata kina kuka kuwa sai kiyi tayi."
sunkuyar da kai tayi cikin zubda k'olla shi kuwa Jafar k'ofar da zata sadata da kitchen ya bud'e kana yace mata in tanada uzuri ga kitchen ga kuma abinci ya kamo mata,
sannan ya dawo ya zauna ya rink'a yi mata nasiha mai ratsa jiki,
tare da nuna mata mutuwar Aryan hutune a gareshi tunda ya tafi tun yana yaro baida zunubin komai a kanshi,
kana yarone da yayi alkhairai da halin nagari,
ya k'ara da ce mata irinsu Aryan sune d'aliban Annabi Ibrahim.
hannu tasa tana share hawayenta kana tana sauk'e ajiyan zuciya,
haka dai ya mata nasiha da tunasarwa har saida yaga ta saki ranta kad'an kana ya fita.

kai tsaye harabar gidan ya nufa da nufin d'aukar wayar Hamma Yusuf dake cikin mota ya mayar mishi,
to amman sai ya samu motar a rufe take,
kawai sai ya shiga motarshi yayi tafiyarshi.


Ranar dai Zahra bata rumtsa ba domin tana rufe idonta sai taga Aryan,
gaba d'aya tsoro ya rufeta gashi gidan shiru babu motsin komai sai kuka tsuntsaye.

A b'ank'aren Yusuf ma haka ranar ya kwana babu bacci a inda Jafar ya barshi a nan ya kwana.


Mama kuma da Abba lokacin da Abba yaja hannunta,
bai ce da ita komaiba haka ya jata har cikin bedroom nata ya kaita kana ya wuce side dinshi yaje yayi al'wala,
to yana fitane ya had'u da Zulaihat inda Abubakar ma nan ya zauna akayi hirar karb'ar gaisuwa dashi,
ana idar da sallan ishane Amira ma mijinta ya kawota.
hakama Zeenat da Mami da Aunty Madina da Goggo Aysha da Goggo Maimuna.
So nan sukayi hirar karb'ar gaisuwar sai kusan k'arfe 10 mazansu suka d'aukesu suka tafi.
Ummi kuwa bata gari ne wai taje auren yar bappanta Maiduguri.


Shiru gidan bayan duk bak'in sun tafi,
kusan

Please Login or Register in order to submit comment