Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga bedroom a bakin gado suka d'an tsaya cikin tsokana yace.
"Yarana 'yan al'barka sun bar Abeehnsu ya samu salama da sakaliyar uwarsu mai raki."
dariya suka d'anyi kana suka wuce bathroom.

bayan sun fitone sukaci abinci kana,
Zahra tace to zata koma,
agogon jikin gini ya nuna mata da idonshi da sauri ta ware ido ganin,
k'arfe hud'u na asuba tayi cikin sanyi tace.
"Shi kenan naji kunya Mama zatace na gudu na biyo ka,
gashi nasan zuwa yanzu ta tashi daga bacci."
jawota yayi suka haura gado kana yace.
"Kwanta abinki Maman Yusuf ba ruwanta."
sai ya kuma d'aga mata gira yace.
"Saida kika gama moreni ne kika tuno kunyar."
cikin jin kunya ta kifa fuskarta tayi a k'irjinshi daga nan sukayi bacci.

Aiko washe gari tun kafin su zo Mama ta tura Sharifa ta kai musu breakfast nasu.

kana tace ta karb'omata su Aryan tayi musu wanka.
haka kuwa akayi
Wasa-wasa dai kunya ta hana Zahra zuwa part d'in Mama ganin haka Mama ta tarkata musu tarkacensu Abu da Sharifa suka kaimusu,
shiko oga ko a jikinshi wani lokacin ma in yana son sakewa sai ya kwashi yaran ya kaimata ita da Sharifa da Abu suyi ta fama da raino.

Bayan kunyar ta d'an ja bayane,
yau sati guda da komawarta side nata,
da yamma tayi wanka taci kolliyarta cikin ratsetsen lace mai taushi red and white sai mayafinta shima fari,
kana ta nufi part d'in Mama dan ta gaji da zama shiru tunda Yusuf ya kwashesu da la'asar bata kuma ganinsu ba gashi nononta sai tsastsafowa sukeyi alamun suna neman masu tsotsarsu.

A kunyace tayi sallama kana ta shiga a parlour ta samesu bisa dukkan alamu fita zasuyi dan ga Mama da mayafi a hannu kana tana ruggume da Aryan yayinda Yusrah ke hannun Yusuf tana k'ananun kuka,
cikin nuna ba komai Mama tace.
"Yauwa zo zauna ki bawa rigimemmiyar taku ta tsotsa kafin mu tafi."
cikin d'an sakewa ta amshi Yusrah kana ta azata a cinya tare da fidda mamanta,
ai da sauri ta karb'a harda wawura.
dariya Mama tayi kana tace.
"Oh wannan d'iya badai fitina ba, shi kuma wannan sarkin hak'urin ba ruwanshi."
Murmushi sukayi Duka sai kuma Zahra ta d'an kalli Mama tare da cewa.
"Ina zamuje?."
sab'a Aryan tayi a baya kana tace.
"Zamuje Girei Saliman Aunty Shuwa ne Allah ya mata rasuwa."
cikin tsananin firgici da tsoro ta mik'e tsaye tare da cewa.
"Innalillahi Mama Salimana kike nufi yaushe meya sameta?."
Allah sarki Zahra gaba d'aya ta gigice ta fita haiyacinta kamar ta mance abinda su Aunty Shuwa suka mata suka gujeta duk da sabon da sukayi ko mgna tawa Salima baza ta amsaba wani irin kuka ne mai tsuma zuciya ya kubce mata.

Yusuf ya jawota kana yace.
"Kiyi hak'uri Ummu Aryan kiyi mata addu'a shine abinda tafi buk'ata daga gareki.

A haka dai suka tafi girei gida suka fara shiga saida suka gaisa tukun suka wuce gidan Aunty Shuwa har da Yusuf d'in
bayan sun gaggaisa, su Mama sun mata ta'aziya ina ita kam Zahra sai kuka da ker ta bud'i baki tace.
"Allah ya jik'anta da rahama."
cikin tsananin kuka Aunty Shuwa tace.
"Amin Amin Zahra Ngd Allah ya bar zumunci.
Salima ta rasu da burin in ta haihu zataje gareki tace in dai ta haifi 'ya mace ke zatayiwa mai suna har mijinta ta gayawa tace ya mata al'k'awari ko bayan ranta in dai mace aka samu a samata Zahra."
sai kuma ta sharte hawaye tare da ci gaba da cewa.
"Kullum Salima sai tamin magiya akan na barta ku koma k'awancenku jahilci ya hanani gane abinda ya dace na kasa gane ba son ranki bane k'addarace ta fad'a min, koda Aryan ya rasu tazo tana kuka tace min zataje ta miki ta'aziya na hanata. nan take cemin Mommy duk cikin k'awayena nafi son Zahra amman kin rabani da ita kawai dan tsautsayi ya fad'a mata."
sai kuma ta mik'owa Zahra jaririyar tare da cewa.
"Ga takwrarki mijinta ya cika mata al'k'awarin da ya mata an sawa yarinyar suna Zahra, Zahara ki yafe min nayi watsi da zumuncinmu kan aikin jahilci."
Hamma Yusuf kanshi yaji tausayin Aunty Shuwa kana Zahra tafi bashi tausayi wato babu irin k'alu balen da bata ganiba,
kud'i masu yawa Yusuf ya basu kana suka sallamesu suka tafi.


**************************
Bayan Shekaru Goma sha biyu.

Lokaci ya tafi komai ya dai-daita shekaru sun ja abubuwa da yawa sun wakana,
yanzu Zahra da Yusuf sunada yara bakwai, Aryan, Yusrah, Haiydar takwaran Daddy kenan sai,
Muhammad tokwaran Abba suna kiranshi Rayyan sai Jabber takwaran M Jabeer sai kuma Abdulkareem sai kuma yar lele yar auta Mimi takwarar Maman Yusuf.

Sakina kuwa matar Sulaiman basu sake samun ko b'atan wataba haka yasa,
suka karb'e Adnan d'insu suka ruggumi d'ansu kamar kowa,
sai Aryan yaranshi uku Yusuf da Asma'u sai autansu Sultan wanda Sultan d'in sokoto sukawa mai suna.

kana Affan yaranshi hudu Anisa sai Anish sai kuma takwarar Aunty Amarya Maryam kenan sai autansu Zahra.
Abdulkareem kuwa yaranshi hud'u,
Hayatuddeen sai Saifudden Yusuf kana auta Safiya.

Jafar ma da Dija sunyi yara biyu babban Sulaiman sai k'aramar Zulaihat yayiwa yayunshi tokwarori.

Sultan kuwa yaranshi biyu Amira sai Amir,

tuni Ibrahim da Sadik sunyi aure,

Sharif ma tuni an girma anyi aure.

idi mai caji ma ya tara iyalai babban d'anshi Yusuf yawa mai suna.

Yusuf kuwa rayuwa tayi dad'i.



Yau Monday bayan sallan azahar,
Yusuf ne zaune a parlour Abba shida yaranshi da Abbanshi da Maman Yusuf kana Zahra na daga gefe Aryan ne zaune a tsakiyarsu ya babbaza kyaututtukan daya samu da yayi haddar qura'an da akayi,
Mimi ce mak'ale a gefenshi tanata shak'o wuyanshi wai zata takashi ta haura saman kujera wurin Abeehnsu.
cikin tsuke fuska Aryan ya d'an mareta tare tureta.
cikin had'e fuska Zahra tace.
"Bani son mugun hali dan kawai tazo kusa da kaine zaka daketa."
kai ya rusunar kamar bai jitaba,
Yusuf kuwa murmushi yayi tare da jawo Mimi jikinshi kana ya kalli Aryan d'an matashi mai kama da mahaifinshi sak da sak komansu iri d'aya cikin nitsuwa Yusuf ya kalli Abba tare da cewa.
"Abba Aryan dai dole jami'atul madina zamu kaishi ko?."
cikin gamsuwa Abba yace. "Sosai ma kuwa haka yafi dacewa dashi."
cikin zumbura baki Yusrah tace.
"Abeeh ni kuma fa."
Haidarne ya d'an harareta tare da cewa.
"Yoh ke ai sai dai a kaiki India ki k'ara koyo rawa ko Hamma Aryan?."
murmushi Aryan yayi tare da gyad'a kai alamar eh.
ita kuwa Yusrah Zahra ta kalla tare da cewa.
"Ammi ba kin jisuba."
murmushi tayi tare da cewa.
"Sharesu kema can zamu kaiki."
Jabeer ne ya kalli Zahra tare da cewa.
"Ammi ni mafa na kusan Kamota a hadda."
dariya suka d'anyi kana Mama tace.
"Ai Yusrah ita rawankanta yayi yawa bata meda hankali kan karatunta."
Yusuf ne ya d'an kalli Zahra kana yace.
"Yoh ai kema kin sani Maman Yusuf itafa Yusrah gado tayi."
jin haka Zahra gane da ita yake shi kuwa Yusuf mik'ewa yayi tare da cewa.
"Eh duk da haka Yusrah na zatayi karatu yadda na dage uwarta tayi itama zatayi."
Abba da Mama dai dariya sukayi,
ita kuwa Zahra bayanshi tabi da sauri.

A bedroom ta sameshi yana konce dan so yake yayi bacci tsakanin azahar da la'asar d'in.

tana zuwa ta rab'a gefenshi kana tace.
"Allah ko gwara Yusrah da Aryan sam ya fiye miskilanci ni mmki ma nakeyi yadda yake karatu dan ni kainafa sai na zageshi yake bud'e baki yamin mgn shi kullum body language,
daya gadoka saida ya fika iyawa."
Murmushi yayi tare da janta jikinshi kana yaja blanket ya rufesu..

************

Bayan wasu shekaru.

Faiq dan Adda Zulaihat ya auri Yusrah

kana Aryan ya auro Safiya d'iyar Abdulkareem.
Yusuf d'an Aryan kuwa ya aiuri Mimi.

Haidar kuwa ya auri Maryam d'iyar Affan,
kana Auwal d'an Amira kuwa ya auri Asina,
sannan Jabeer 'arami kuwa ya auri d'iyar Zeenat,
toh al'amura dai sun tafi yara duk sunyi aure tuni Yusuf da Zahra sun fara jikoki.
dan Yusrah ta haiku haka Safiya matar Aryan k'arami d'iyar Abdulkareem balarabe Kena,
kana Rayyah kuma ya auri Zulaihat d'iyar Jafar,
Adnan kuma ya auri d'iyar Raihana.

Yauda yamma hadari ya d'an taso,
haka yasa Zahra ta kalli Zayyad d'an Aryan kenan dake gefenta wanda baifi shekara d'aya ba,
cikin yanayin nitsuwa da haiba da alamun girma yazo ta mik'e tare da cewa.
"Taho Zayyad zo in goyeka naga kamar bacci zakayi."
da saurinshi yazo ta goyashi,
mintu goma tsakani yayi bacci,
kana ta kontar dashi sannan ta mik'e ta shiga bathroom wonka tayi mai rai da lfy kana taci ado da kolliya ta nufi side Oga,
shiru parlour ba kowa haka yasa ta wuce bedroom tana shiga ta sameshi bisa sallaya,
gefenshi ta zauna tana bin sautin muryarshi suna karatu a tare,
sun jima suna karatun kana suka shafa,
Yusuf ya rufe qura'an d'in tare da ajiyeshi a ma'ajiyinshi sannan ya juyo gareta tare da jawota jikinshi cikin sanyi yace.
"Rayuwa tayi dad'i kuka ya zama dariya zafi ya zama sanyi Allah mai jujjuya lokaci da lmri ya juya mana rayuwarmu yau gani ga Zahra da tarin zuriya 'yaya da jikoki,
lallai da nayi sake na rasa *Yar Fulani* da *Nayi nadama (MI WASMITI* lallai na yarda na tabbatar *Namiji baya kad'an* domin gashi hikimar Aryan d'inmu ya had'a aurenmu, gashi munyi dace a cikin *Tausaya wa juna* da mukayi ya zame mana al'khairi , koda yake dama ke *Bandirawo* ce a gareni dole kawai tausayin juna,
duk da munga *Rubutaccen al'amari* a rayuwarmu amman munyi imani da *HUKUNCIN ALLAH*
muna kuma rayuwa tare da tsumayin *RIGAR KOWA*".
ruggumeshi tayi kana tace.
"Hamma Yusuf in ban fad'a nauyin kalmar zaimin illa, Hamma ina sonka, mi yid'ima i love you ana uhhbbuka hubban azeem ya Habibi laisa li misluka abadan."
cikin tsananin farin ciki yace.
"Allah na gode maka da jin wannan zazzafar soyayya da akayi ta b'oye min tsawon shekaru.
Alhamdulillah!
Alhamdulillah!!
Alhamdulillah!!!."



Uhummmmmmmmmmmmmmmmmm...... Alhamdulillah nima Aysha Aliyu Garkuwa na godewa Allah daya bani iko da rai da lfy da damar fara littafinnan da gamashi Lfy.



*Kuskuren dake ciki Allah ya yafe min nida na rubuta daku da kuka karanta, Allah ya had'amu akan ladan dake cikin abinda nayi dai-dai, Allah ya rabamu da munana kuma zafafan k'addarori ya kuma bamu ikon cinye dukkan jarabawar da Allah zai mana, Allah ya baku ikon amfani da kyawawan abinda ke ciki, Allah ya bamu ikon tarbiyartar da yaranmu rabbi ya shirya mana ahlinmu baki d'aya*

*Godiva tamu samman a gareki Ummu yahaya Musa Ngd matuka Allah bar zumunci da qauna dear.*

*Ban mance da keba k'anwata Ummi Garkuwa Allah ya bar zumunci da qauna*


*Dija Chiroma ke ta damance a cikin makaranta zan iya cewa duk online kinfi kowa son littafin Hukuncin Allah kina d'aya daga cikin mutanen da suka zaburar dani da nacin tambaya na k'arisa littafin*

*Hauwa A Usman Jiddah na kina cikin mutanen da suka cire min k'iwuyar typing ngd Ngd Ngd matuka Allah bar zumunci da qauna my dear Jiddu*

*Shi na dabanne kullum shike tabayata ya kinyinyi typing kuwa? ki fara posting mana me amfanin kinyi typing kin tara baki fara posting ba Godiya ta musamman gareka k'anina Hayatuddeen (Yaya Hayat*)

*Hamma Muhammad Allah ya bar zumunci d'an uwana shine mai sama min karsashin inci gaba da typing a kai a kai*

*Afwan! Afwan!! Afwan!!! Ina neman yafiyarku mace ko namiji Babba ko yaro wacce na tab'a mgna da ita da wanda ban tab'a mgna da suba na nesa dana kusa wala Allah na d'an cutar daku da zuk'atanku da wani abu da ban saniba kuyi hak'uri ku yafe min ku gafarceni musamman wasu na min mgna basu amsa ya zama aiki. Sai kuma Allah ya had'amu a sabon littafina mai zuwa. mai taken BABU NAKASASSHE SAI RAGO*

🤗🤗🤗😊😍😘




By
*GARKUWAR FULANI*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment