Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jawo jallabiyarshi da ya cillah kan dressing stol zurawa yayi tare fara tafiya cikin takunshi na nitsuwa,
bakin k'ofar yazo tare dasa hannu,
har zai bud'e sai ya kuma juyawa bathroom ya shiga brush yayi sannan ya fito.

Aryan kuwa tuni ya koma wurin Sulaiman inda Jafar kuwa yaketa jera musu kulilin a tsakiyar parlour bisa tattausan carpet d'in,
tuni sun buge da hira.
yana isowa ya zauna kan 2 str tare da k'ara tsuke fuska dan shi babu abinda yafi tsana a mishi da safe irin ya maida baccin nan azo a tasosho,
hannu Sulaiman ya mik'a mishi,
cikin k'ara tsuke fuska shima ya mik'a mishi hakama Jafar daya gaidashi madadin ya amsa da baki sai ya amsa mishi da kai,
shi kuwa Aryan cikin watstsakewar daya samu ya kalli Jafar tare da cewa.
"Matso mana da abincin nan dama na d'an kwana biyu banci girkin Mama ba."
"To".
Jafar yace dashi sannan ya matso da kulolin tsakiyarsu sannan ya bubbud'e,
gaba d'ayansu a tare suka shak'i k'amshin girke-girken
shikuwa Yusuf ido ya lumshe tare da zamewa ya konta kan kujerar da bata gama d'aukar tsawonshi ba,
k'afa d'aya ya d'aura kan d'ayar sannan ya hard'e hannunshi a k'irjinshi sai ya k'ara lumshe ido tare da karkad'a k'afafunshi,


Aryan, Sulaiman, Jafar, kuwa su kam sai zamewa sukayi suka zauna a tsakiyar parlour,
sannan Jafar ya turo musu pellets and Cups
kowa ya zuba abinda yake so,
Aryan couscous ya zuba da miyar daddageggiyar hanta sannan ya had'a tea mai kauri,
Jafar kuwa kunun gyad'an nan ya zuba tare da zazzafan k'osai d'in,
Sulaiman kuwa kura tea ya had'a tare da zuba ferfesun jan naman.
gaba d'aya a tare sukayi gyaran murya tare da lumtse idanu a lokacin da sukayi lomar forkonsu,
jin sautin gyaran muryarsu a tarene yasa Yusuf bud'e ido,
kallonsu kawai yakeyi ganin yadda sukecin abinci tare da lullumshe ido alamar dad'inshi na gamsar dasu,
haka yana kallonsu su kuwa shiru kakeji sai sautin cokula da akeji ket-ket,
sun d'an jima suna harrak'awa
murmushi yayi ganin duk sun kuma jawo kulolin suna k'ara abincin,
cinyewa sukayi tas wanda suka zuzzubawa a karo na biyun,
cikin mmaki ya kalli Aryan daya kuma Jawo kular ferfesun yana zubawa,
aiko zubawa yayi da yawa sannan ya fara ci tare da lumshe ido yana wani shihht-shihhht.

ido suka zurawa Yusuf daya mik'e tsaye bedroom nashi ya koma,
jimawa kad'an ya fito
rik'eda phone d'inshi gefen Aryan ya zauna tare da kara phone d'in a kunne tare da cewa.
"Raihana kizo parlour na."
a can d'aya gefen kuwa Raihana daketa kiciniyar had'a musu breakfast tace.
"Toh Hamma Yusuf gani nan zuwa."
gyaran murya ya d'anyi tare da cewa.
" Ina jiranki yanzufa".
"Toh." tace tare da katse wayar ta nufi side d'in nashi.

A bakin k'ofar ta tsaya tayi sallama,
har saida aka bata izinin shiga sannan ta shiga,
gefenshi taje tare da duk'awa tace.
"Ina kwanan Hamma?."
a tare suka amsa da.
" lfy lau."
shi kuwa Yusuf da sai yanzu ya bbud'e kulolin da filas d'in Cup ya d'auka mai d'an girma kunun gyad'arnan mai zuma a madadin sugar nan ya zuba har bakin cup din sannan ya jawo pilet ya zuba k'osai kusan guda 13 kunun ya fara kurba.
ido ya lumshe tare da gyara zama ya had'iye kunun a hankali sannan ya samu damar amsa gaisuwar Raihana,
cikin seconds 58 ya shanye kunun dan kafa kai yayi bai cire cup d'in a bakiba saida ya shanye tas,
sannan ya sake cika cup d'in ya fara cin k'osaid'in yana d'an korawa da kunun,
saida yaci kusan kosai 7 sannan ya kalli Raihana daketa hira da Jafar yace.
"Yauwa Raihana d'aukar muku abincin nan ki kai muku keda Kaka da Rafi'an kawu kuji girkin Mama dan naga alamun a rumbud'a oga Aryan zai cinye bai tuna da kuba."
to tace tare da fara karb'ar kulolin da yake mik'o matan,
ta kai na Couscous da ferfesub d'in ta dawo amsar na
na k'osai da filas d'in kunun da tea din da pepper chicken d'in kenan ta hangi motarsu Zahra ta iso harabar gidan, da sauri ta nufi gunsu ruggumesu tayi dukansu suna cikin haka,
suka hangi motar Affan ga ta fadawa a gefenshi,
ganin haka sukayi cikin gida,
shi kuwa Yusuf sake kiranta yayi dan ganin bata dawo da wuriba,
cikin girmamawa tace.
"A a Hamma Yusuf naga kunyi bak'ine kuma dama nimafa nayi muku girkin,
barima in kawo muku dan naga harda fadawa."
da sauri ya kalli Aryan tare da cewa.
"Affan ne yazo kenan."
katse wayar yayi lokacin da yaga Affan ya shigo,
ai kuwa nan sukayi ta ciye-ciyensu da hira shima Affan yasha kunun sosai,
sannan Yusuf ya d'auke filans din ya hana Aryan sha wanda saida sukaga santin da Affan keyine ya sasu cewa zasu sha d'in.
Dariya Aryan yayi tare da cewa Yusuf.
"Yaseen ka daiyi sa'a kasan ni dama can kunu ba cimata bane,
shiyasa ban kulaba kaje kayi tasha har gobe da safe kayi ta faman sintiri fitsari."
Sulaiman ma dariyar ya d'anyi tare da turowa Affan pilet d'in daya zuba mishi dankali da k'wai d'in,
shi kuwa Yusuf Affan ya k'arawa kunun tare da cewa.
"Kaima daga wannan ka gama shanye rabonka."
jawo kofin Affan yayi tare da cewa.
"Hmmmm ai cikin nawa nema ya k'wansa min dan ya cika amman dai bari in shanye wannan d'in kam,
sauran kuma sai da dare zanzo mu shanye."
Jafar ne ya danna gyatsa tare da gyara konciyarsa yace.
"Ba damuwa gobema ai sai Zahra ta sake dama mana tunda kunun ya samu shiga."
cikin gyad'a kai Affan yace.
"Gskya kam, da ta kyauta mana dan wlh ban tab'a shan kunun daya min dad'in wannan ba."
daga nan sukaci gaba da hira,
sun dad'e sosai kafin Affan ya tafi,
suko su Sulaiman koda suka tashi fita saida suka jira Yusuf da Aryan sukayi wanka,
sannan Yusuf yasa Jafar ya shigar musu da filas d'in kunun har cikin bedroom tare da na tea sai kulan pepper chicken d'in sannan suka fita a tare.

Raihana kuwa kai tsaye d'akinta taja su Zahra inda suka fara da k'arisa aikin dilken da sukayi tsawon wata d'aya,
sannan ta d'auko tand'un tsumi ta bata nan ta fara sha tare da ruwan kankana,
sai kusa k'arfe 11:23 Am suka zauna zaman fara zanen lalle inda Zahra ta cancand'e amarya ta fito ras kamar amaryar indiyawa,
bayan ta gamawa Raihana sai tayiwa Rafi'a yar kawunsu Aryan d'in daga nan tayi tayiwa k'awayen amaryar wanda yawancinsu yan makarantarsu Raihanarce,
Amira, Adda Zulaihat, Aunty Amarya, Aunty Madina, suma duk sun zo,
sai kusa k'arfe uku na yamma ta samu suka kammala da yake na k'awayen mai d'an sauk'i-sauk'i tayi musu ba mai kyau da wahala kamar na amaryarba ne.

K'arfe 5:00 pm farfajir gidan su Aryan cike mak'il da jama'a matan aure yan mata da yan saffa-saffa yayinda wani shararran malami keyi musu nasiha mai ratsa jiki akan zamanta kewar aure,
sai gabanin margin akayi addu'a tare da ciye-ciye da lashe-lashe aka tashi.


Su Yusuf kuwa suna fita kai tsaye cikin Jimeta suka fara shiga gidansu Ummi sannan gidan Goggo Aisha,
daga nan dai suka d'an jejje gidajen yan uwa,
suna gamawa da cikin jimeta kai tsaye cikin girei suka nufa,
gidansu Aunty Amarya suka fara zuwa,
a bakin mashigar gidan sukayi parking,
cikin mamaki Aryan ya kalli Sulaiman yace.
"Kai Sulaiman haka gidansu Aunty Amarya ya gyaru?".
kai Sulaiman ya gyad'a mishi tare da cewa.
"Kasan Uncle Gambo ya samu aiki ai,
shine ya gyara gidan yayiwa Tattinsu gyara sannan yayiwa Aunty Amarya ma side d'inta mai kyau ya ginawa k'aninshi ma kaga gida ya zama kamar ba shiba."
tsaki Yusuf ya d'an ja tare da cewa.
"Gskya ni dai da gidan yafi burgeni."
Aryan ne yace.
"Gskya kam da gidan yafi kyau yafi kama da lambu kana shiga zakaji yana k'amshin furanni sannan zakayi tajin kukan tsuntsaye da zirga zirgansu,
uwa uba ga k'amshin bishiyoyin ayaba mangoro gwaiba da dabinansun nan mai d'an karen zak'i ga ruwan rijiyarsu nan mai gard'i da sanyi kamar ruwan FARO,
gashi da suna da tattabaru."
sai ya kuma yin dariya tare da lumshe ido yace.
"Kai Yusuf gskya fa munyiwa Tatti rashin ji a zamanin da muke ganiyar k'uruciyarmu,
dad'ina da matar ga tsabta da iya girki."
Shima Yusuf ido ya lumshe tare dayin sakalin murmushi yace.
"Lokacin kana nan kamar biri in kaga ayaba ko bai nunaba sai kaci."
Sulaiman ne ya tuntsure da dariya dai-dai lokacin da suka shiga tsakiyar gidan yace.
"Hahaha tarihi zai maimaita kanshi kenan ai har yanzu lambub nan yana nan,
barema yanzu kuma da Uncle Gambo ya k'ara k'awata wurin,
rijiyar nan ruwanta na kwaranya ta tsakiyar lambun ga k'arin shuke-shuke da yayi yanzu harda inabi akwai a ciki." suna cikin hirarsu tare da kutsowa har tsakiyar part d'in da suka nufan.
wata bak'ar tsohuwa na gani mai wani irin sihirtaccen kyau lallai kam Tatti bak'ace amman iri bak'ak'en nanne masu azabar kyau hancinta zuwet har kan d'an k'aramin bakinta yayinda gashin girarta yake konce lif-lif har sun had'e akan karan hancita ga bisa dukkan alamu a gunta Zahra ta gaji irin gashi girar.
Fad'ad'a fara'ata tayi yayinda tayi kansu cikin tsananin farin ciki take cewa.
"Kai yau ashe amarya nake lale-lake marhabin daku manyan bak'ina."
sai ta kuma juyawa tayi parlournta tare da cewa.
"Ku shigo ku shigo maraba da jikokin kirki."
a tare suka shigo tare da zama kan tim-tim d'in dake tsakiyar parlour a bisa carpet dan babu kujeru a parlour sai tim-tim d'in.
zama sukayi yayinda ita kuma ta kasa zaune ta kasa tsaye sai hidima takeyi dasu,
ruwa ta d'ebo musu a kwanon sha ta kawo musu, sannan ta koma cikin wani d'an bukka mai shatin kobo wanda dacan nanne d'akinta yanzu kuma ya zama kitchen d'inta sai gadon bono dake gefen kitchen inda kamar shine kond'on wanke-wonketa dan ga kwanuka a kife a kai sannan ga tukwanenta da zaka iya duba hak'oranka a jiki,
cikin kitchen d'inkuwa wata tukunyar k'asa naga ta bud'e wanda taketa nason mai mamaki nayi ganin cikin tukunyar na bul-bul alamun yana b'ararraka ne,
sai lokacin na lura ashe kan rushi yake,
wani irin k'amshi dahuwar takeyi,
ido na bita dashi lokacin da ta d'auko wani akwashi wanda sai k'yalli yakeyi
ludayin ice naga tasa tare da d'ebo tand'enrun nan da yaketa fesar da wani azabebben k'amshi
naman ragone wanda ya dahu yayi luguf,
duk k'asusuwan sun sab'ule sun bar jikin tsokokin,
kusan cika akwashi tayi sannan ta fito,
tana hauro barandar tare da kiran.
"Sani! Sani!!."
Sani k'anin Aunty Amarya dake d'akinshi ne wanda yanzu ya fito wanka dama yana sauri ya shigo dan yaji tana kiran sunan Yusuf.
"Na'am Tatti ganin nan zuwa."
yace mata lokacin daya fito part nashi ya nufo part d'inta,
ita kuwa gabansu Yusuf ta ajiye akwashin sannan ta zauna gabansu cikin tsakin fuska tace.
"Kai Aryan nayi fushi da kai,
wato sai da Yusufa ya dawone zaka lek'oni ko?."
dariya Aryan yayi tare da cewa.
"Yoh ai tare muka dawo."
haharanshi tayi irin na tsoffi tace.
"Ai tun randa ka dawo Sulaiman ya gaya min,
har ka samu aiki amman bakazo ka gaya minba ko dan in d'an sanya al'barka."
murmushi yayi tare da d'an sosa k'eya yace.
"Tuba nakeyi Hajia Tatti."
Yusuf ne yayi saurin cewa.
"Karki yafe mishi Tatti,
ai nima kullum Jumma'a sai nace yayi k'ok'arta yazo ya dubaki keda Kaka amman da yake shi baya son sada zumunci sai yak'i zuwa."
cikin dariya Sulaiman yace.
"Toh Yusuf had'asu kasa rabasu."
Jafar kuwa sai murmushi yakeyi dan ya tuna dama haka suke kuma in zasuzo in yace zai bisu sai suyi ta tarfa mishi rashin mutunci,
dariya suka kumayi jin Yusuf na cewa Tatti.
"Na dawo kanki ke kuma tsohuwarnan in baki dena cemin Yusufa ba zamu b'ata."
dariyar Uncle Sani ne da sukaji ya sasu meda kallonsu baki k'ofar,
da sauri ya k'arisa gunsu,
hannu suka mimmik'a mishi sukayi musabaha,
cikin sakin fuska yace.
"Kai lallai munsan Yusuf ya dawo tunda ga Aryan da Jafar ma mun samu ganinsu a gidanmu."
cikin murmushi Jafar yace.
"Uncle ina zuwafa ni yawanci nike kawo Zahra ai."
da sauri Tatti tace.
"Kuma in kazo baka shigowa ba."
dariya suka d'anyi
har Uncle Sani zai zauna Tatti ta kalleshi tare da cewa.
"Yauwa d'auki k'oryarcan mana ka shiga cikin lambu ka tsinko musu abin motsa baki."
to yace tare da mik'ewa ya fita,
Yusuf ne ya yunk'ura zai mik'e ya bishi Tatti tace.
"Dan Allah d'an zauna kuci abinci,
na sanka yanzu zaka kama zagaye cikin lambun har abincin yayi sanyi."
komawa yayi ya zauna tare da cewa.
"Kin dai had'ani da Allah kin hanani tafiya amman ni a k'oshe nake."
turo musu akoshin tayi tare da cewa.
"Ai kuwa sai kunci,
tunda rabanku ya shiga ciki,
tun shekaran jiya fa nake aikinshi in d'a sa wuta sai in d'an sauk'eshi sai washe gari in kuma azashi,
toh d'azu da safe na k'arisa mishi had'in muka d'anci,
toh dama Zahra dasu Nana sunce in ajiye musu kunga ashe rabankune."
dariya Aryan yayi ganin tuni Sulaiman ya jawo akwashin a tsakiyarsu tare da wonke hannunshi cikin k'waryar da ta kawo musu da ruwan wanke hannun.
shima Aryan ido ya lumshe tare da had'iyar yawu muk'ut,
dan dama abincin da sukaci da safe tuni ya narke,
kuma koda sukaje gidansu Ummi kakannin su Sulaiman kenan,
basuci komaiba kuma daga nan sun bi gidajen Goggonnin su Yusuf inda suka samu su kuwa duk sun tafi gidansu Aryan d'in walimar Raihana
toh sai bayan la'asar har 3:35 suka iso nan d'in,

shi kuwa Sulaiman k'ananan akwashin yajawo sannan ya d'ibi iya cinsa ya fara ci tare da lumshe ido shima Aryan da Jafar d'iba sukayi sannan suka fara ci cikin akwashi d'aya,
ita kuwa Tatti hannu tasa ta turawa Yusuf babban akwashin tace.
"Yau to kaima maza kaci,
sai muyi mgnar yaushene aurenka."
kai ya jinjina tare da wanke hannunshi ya fara ci.
jimawa kad'an sai ga Uncle Sani ya kawo musu yayan itatuwan,
haka suka zauna a tare sunaci sunata hira,
har Uncle Gambo ya dawo shima yayi farin ciki da zuwansu sannan yayi tayimusu nasiha tare da nuna musu yanzu dai lokaci yayi da zasuyi aure,
ita kuwa Tatti sai binsu takeyi da Addu'a,
sai biyar na yamma suka bar gid'an,
inda Sulaiman da Jafar sukayi gida,
Aryan da Yusuf kuwa suka wuce bayan p, z, dan Mama tace mishi ya bari kar yaje gidan Innartan dan Abba ya hanata zuwa kuma itama Innar bata nan.


Haka dai Yusuf ya d'an lellek'a dangi,
tare da Aryan wanda an d'aga shariyar da zai jagoranta sai ran monday shiyasa sukayi wunin ziyararsu tare.

Koda suka dawo da dare gidan ya kacame ya cika da b'aki yan uwan Ummarsu Aryan ma sun zozzo daga Chadi,
maza da mata,
an sauk'i mazan a side d'in Aryan,
nanfa su Yusuf suka shiga cikinsu akayi ta hira,
sai kusan 11:12 Pm Yusuf ya koma part d'inshi wonka yayi tare da shirin bacci harya konta kuma ya tuna da kununshi,
tashi yayi ya d'auko filas d'in ya tsiyayi kunun da yawa sannan ya jawo kular pepper chicken d'in ya fara ci yana d'an korawa da kunun,
wayarshi yaja tare da kiran Aryan yazo yaci abinci,
to Aryan d'in yace sannan ya fito ya nufi side d'in Yusuf d'in.
A harabar gid'an ya d'an tsaya dan ganin wata mota da take tsaye a bakin gate bisa dukkan alamu fita zatayi amman tana tsaye alamun akwai mai fitowa cikin motar
matsowa ya d'anyi ta gefen da yaga an bud'e k'ofar gaba in da mai zaman banza yake.
ido ya zaro tare da k'ara motsowa ganin abinda akeyi a cikin motar,
idonshi ya kuma zarowa ganin idiris yana yiwa Zahra wani irin.....!!!







*By*
*GARKUWAR FULANl

*HUKUNCIN ALLAH*

*Page 2⃣8⃣*

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



Idi mai cajine ya gani wanda yanzu suke ganinshi a mutumin kirki idiris
ido Aryan ya kuma rumtsewa jin wasu irin kalamai da Idris d'in yakewa Zahra.
"Ni dai na san in kina sona bazaki hanani tab'a jikinki ba,
kinfa san kece burin rayuwata,
fatana in ganmu k'ark'ashin inuwar aure."
cikin tsananin takaici da jin tsanar idris d'in a cikin ranta, a zafafe ta fizge hannunta daga rik'on da yayi mata yayinda take jin wutar tsanarshi na ruruwa a ranta ji takeyi tamkar ta shek'e wuyanshi sai yayi sanyi,
ko kuma ta kikkifa mishi maruka.
shi kuwa kai ya luggob'ar cikin yaudara ya fara mgna murya na rawa kamar zaiyi kuka.
"Kiyi hak'uri my dear in sha Allah bazan sakeba,
amman yana da kyau kisan irin mijin da zaki aurafa,
dan ki shiryawa amsar buk'atusa."
fuska ta tsuke tare da watsa mishi wani mugun kallo cikin fad'a tace.
"Ni ba yar iska bace,
wallahi Allah kenan na tsaneka bani ba kai har abadan."
cikin tsananin b'acin rai tace.
"Ka bani wayata da mayafina zan tafi cikin gida dan ni bana buk'atar zama da kai."
murmushin ha'inci yayi tare da kallon fuskar wayarshi ta yadda ita bazata ganiba yace.
"Du du du dai 9:37 Pm ne ki bari goma ta cika mana."
cikin tsantsar tsanarshi ta yunk'ura alamar zata fita,
sai ta kuma dawowa ta zauna jin yace mata.
"Gashi amshi tunda kin gaji da ganina."
harara ta watsa mishi tare da jan dogon tsaki,
ganin yadda yayi kamar zaiyi kuka muryarshi sai ta mata kama da muryar Dream Guy d'inta,
cikin zafin nama ta fudge mayafinta dayake d'an rik'e da gefenshi,
hannu tasa ta wabce wayarta da yake hannunshi,
a dai-dai lokacin ne Aryan ya iso wurin,
hasken wayarshi ya danna dan sam baya ganin abinda sukeyi a cikin motar kawai dai muryarsu yakeji.
shi kuwa Idi sai k'ok'arin kamo hannunta yakeyi,
ganin haka tayi maza ta bud'e marfin mortar,
yayinda shi kuwa yaketa wani irin lumshe ido yana fidda numfashi tare da jawo wani irin numfashi dake sark'afe da tsananin sha'awa danna kan joystick d'inshi yayi da k'arfi yana mai k'udurta aniyar saifa ya kai ga cimma gashi,
ita kuwa Zahra cikin wani irin azabebben tsoro da k'arfin daya zo mata ta zuro k'afafunta woje,
Aryan kuwa gyaran murya yayi tare da cewa.
"Salamu akaikum,
waye ne a cikin motar nanne kam?."
da sauri Idiris ya zare hannunshi daga matsar da yakewa jikinshi,
sannan ya gyara zaman wondonshi cikin firgita yace.
"Allah rene Ya Aryan surkinka ne Idiris."
tsuke fuska Aryan yayi duk da yasan Idris zai girmeshi matsowa yayi tare da cewa.
"Ke Zahra fito kiyi cikin gida."
cikin rawan jiki da firgita ta k'arisa fitowa daga motar da sauri tayi cikin gida har tana tuntub'e sai haki takeyi gaba d'aya taji ta tsani Idris.
shi kuwa Aryan juyawa yayi tare da cewa.
"Toh saida safe ko,
sannan please dokar gidanmu ba'a zuwa zance da dare."
bai tsaya yaji ta bakinshi ba ya juya gun Baba mai gadi yace.
"Kai Baba."
mik'ewa yayi da sauri yazo gaban Aryan shi kuwa Aryan cikin bada umarni yace.
"Karka sake barin motarna ta shigo cikin gidannan da dare,
kuma har a gama bikin nan karka sake barin a zauna a nan ana hira."
to yace tare da bud'e gate d'in,
shi kuwa Idi jan motarsa yayi ya fice yana cewa.
"Hmmmm Aryan kenan ai kun makara in sha Allah gobe iwar haka kuna nan kuna cikin tashin hankalin duniya dan na gama shirina,
gobe da yamma zan fasa budurcin Zahra zan keta tsakiyar cinyoyinta,
tabbas sai nasa Yusuf kuka kamar yadda ya sani kuka."
murmushin mugunta yayi tare da cije lips enshi yace.
"Hmmm har yau ina jin azabar da Yusuf ya shayar dani,
ina tuna yadda yayi ta dandatse mini yayan Marenana,
badan kwanana na gababa da tuni na mutu,
yamin tsirara da ranar Allah nayi ta gudu a tsakiyar garin girei wai duk yamin hakane dan kare budurcin Zahra ko!!?,
toh ni kuwa nayi al'k'awari sai na fasa budurcin Zahra...? duk wanda zata aura sai dai yabiyo bayana."
haka dai Idi yayi ta cin al'washin raba Zahra da budurcinta.

In baku mantaba masu karatu Idi mai caji fa yanada sana'arsa,
toh bayan Yusuf ya mishi d'an banzan duka da dandatsar nan,
akan sonyiwa Zahra fyad'e da yayi,
sai daga baya yazo ya kwashi kayan shagonshi inda,
ya koma k'auyesu inda yasa mahaifiyarshi ta seda shanu biyu ta bashi kud'in yazo ya had'a da kud'in hannunshi
ya kama hayan shago a shopping complex ya saro woyoyi sabbin samfura daga nan ya zama d'an saye da sayarwa,
kuma yana samun ci gaba domin har gida ya saya,
inda yakeda burin d'auko mahaifiyarshi daga k'auyensu amman ya bari sai yayi k'udurinshi nayiwa Zahra fyad'e kafin ya d'auko Mamanshin.


Ita kuwa Zahra tana shiga cikin gidan kai tsaye d'akin Raihana ta shigo inda ta samu su Mami tuni sunyi bacci sai k'awayen Aunty Raiha da suketa hira,
Rafi'a ce tace.
"Yauwa Zahra wai sai yaushe ne zakuyi kitson kin sanfa ance gobe anayi sallan la'asar za'a zo d'aukan amarya."
Raihana ta kalla wacce ke rik'e da tandun tsiminta tanata lasa,
mayafinta ta jefar gefe tare da cewa.
"Bari in d'an watsa ruwa sai mu fara kawai tunda naga alamar kwanan zaune zakuyi."
Fadila ce d'aya daga cikin k'awayen tace.
"Yauwa Zahra kahan yayi."
bayan tayi wonka ta fito tasa yar doguwar riga,
sannan ta zauna bakin gadon,
ita kuwa Raihana ta dawo k'asa gaban Zahra sannan ta mik'a mata kifiya,
nan ta fara tsantsara mata wasu irin kitso masu azabar kyau,
yayinda suketa hira da k'awayen amarya hira dai irin wacce k'awayen amare keyi in sun samu sarari,
duk da Zahra bata kaisuba a k'alla zasu fita da shekaru 5 bai hanasuyi hirar a gabantaba da yake suna ganin yanayinta na kaud'i gata da girman jiki zakayi zaton sa'arsuce.
Fadila ce ta mik'o mata wayarta tare da cewa.
"Please dan Allah Zahra ki amsa kiran wayarnan ko ki kashe wayar tunda shi wannan mayene bazai bar kiranba."
Rafi'a ce tayi dariya tace.
"Yoh yaga zuk'ek'iyar yarinya d'anya charab ai dole yayi ta zuba naci."
Amina ce ta d'an tab'e baki tace.
"inji shine suke tare tun d'azu,
sannan yanzu yayi ta azalzalarta gskya nima bani son saurayi mai nacin tsiya."
ita dai Zahra amsar wayar tayi tare da katse kiran da idi ya mata a karo na 17 banda text 6 da yamata na tayi hak'uri ta amsa kiranshi taji menene damuwarsa,
Raihana ce ta juyi lokacin da kiranshi na 18 ya shiga wayar cikin lallashi da shak'uwarsu da Zahran tace.
"Dan Allah, na rok'eki da girman Allah ki amsa mishi kiranshi kinji k'anwata".
kai ta gyad'a tare da amsa kiran ta kara wayar a kunnenta,
shiru tayi tana jin yadda yake wani irin nishi da alamun kuka gaba d'aya sai taji tausayinshi
cikin sanyi jiki murya can k'asa ko Raihana da takewa kitso bata jinta tace.
"Ka konta kayi bacci mana."
k'ara narkewa yayi tare da kele baki yace.
"Bazan iyaba ai Dear."
tana maici gaba da kitson ta tsuke fuska tace.
"Sabida me?."
cikin yaudara yace.
"Sabida kina fushi dani gashi bani da lfy."
a tak'aice tace.
"Meke damunka?."
kukan munafurci ya d'anyi har saida yaji tana ce mishi.
"Sorry dan Allah ka bar yin kuka gaya min meke damunka".
cikin izaya yace ki bud'e data zan gaya miki ta what's app."
ba tare da ta tuna komaiba ta katse kiran tare da bud'e datar sannan ta shiga whatsapp d'in kan numbershi ta shiga.
murmushi tayi jin voice message daya tura mata yanata kukan shogoba sannan yace ta bud'e video dayake k'asan voice message d'in,
yatsarta tasa ta danna kan video inda nan take ya bud'u,
hannunta ta meyar kan kitson da takeyiwa Raihana yayinda wayar ke kan cinyarta,
ido ta zaro da sauri ganin abinda ke cikin videon,
Idin ne konce a kan gado yayinda yake cikin blanket
sai taga ya kuma tashi zaune yana cewa.
"Shhhhhhh My dear kalli fa halin da nake ciki."
kawai sai ya yaye blanket d'in,
joystick d'inshi ta gani yana karkad'awa tare dayin wani irin kukan fajirci,
bata bari taji me zaiceba ta kashe wayar gaba d'aya tare da cilla wayar cikin hang bag d'inta dake gefenta,
gaba d'aya jikinta rawa yakeyi.
zamewa tayi ta konta tare da cewa.
"Aunty Raiha ki bari saida safe zamu k'arasa yanzu kaina ke ciwo."
cikin bacci-bacci Raihana tace.
"Nima na fara jin bacci."
ita dai Zahra tini ta konta wani irin azabebben tsinkewar tsuciya kawai takeji,
lokaci d'aya ta fara jin alamun zazzabi zai rufeta,
sai k'amk'ame jikinta tayi tare rufe idonta hawaye masu azabar zafi na zubo mata, tunani takeyi duk lbrin

Please Login or Register in order to submit comment