Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gyara tareda kallon YASMIN "zo nan mama na, ya fada cikin natsuwa, jiki na rawa ta matso tareda tsugun nawa tana jiran hukunci,


"Saude' baba ya kirata, ta fito tareda janyo kujerar mata ta zauna "malam Wai meke faruwa ne naganku kamar gidan mutuwa Nifa bangane ba?


"Toh ai nima saudatu bangane komai ba sai wadda tayi jagorar komai tayi mana bayani' wake nan? "Yarki mana waye in banda YASMIN,


"Yaya mubi a hankali muji komai a natse don ni koda yaron nan ke magana bangane komai ba, "toh mamuda idan banbi a hankali ba garaje zanyi?


"Yo ko zafi nayi ina zai kaini kana ganin y'anda ya zagaye mana unguwa kamar masu laifi kaduba ma kota har a katanga suna leko mu irin wannan bala I har ina?


"Mama na Meye wanna ina kikeso ki jefa mu shikuma wanna don girman Allah ina kika tsinto shi? Abarikin? Ku Kuma haka Zaku kare a jajubo mana masifa ita maryam ta makale tace sai soja kema ji me kika kwaso,


"Mamuda daga gani wannan yaron bazaiyi mutunci ba, don haka ka dauketa kawai ku wuce zango idan andaura Aure Sa dawo da mijinta


'Yaya ai wanna ba shawara mai kyau bace ai ko birnin sin zamuje banjin wannan yaro bazai biyomu ba Kuma ai nida natafi da ita ni kwabata zatayi ruwa,


"Kai samaila dama kanada zainabu sai ka hakura kawai da mama na, "Aa mamuda banson Abinda kakeyi meyasa kakeson rabashi da y'ar uwar shi?


Tashi kawai baban Zango yayi ya saba malum malum tareda gyara zaman hula" toh nidai nafada muku inkuma dai nine waliyin Yasmin to ban daura mata Aure da kowa sai in wanna sojan yazo yace ya fasa zancen Auren ta don haka ni nayi gida Saude Allah bamu Alkhairi,


Ya wuce kawai batareda karawa waigowa ba, baba zuba mata ido kawai yayi kafin yace "tashi ki wuce ai ke kanki kinzama Abin tsoro Fatima Kuma nasan komai da sanin maryam zamu gauraya da ita,



Ciki ta wuce tarasa me ke mata dad'i tarasa madafa tarasa ina zata tsoma ranta tana hango bacin randa ya tafi dashi ya mugun tsaya mata a rai,

*****************
Bayan ya tashi aiki ya nufi gidan su dama Hajiya tasan da zuwan shi don haka ta shirya mai dish Kala Kala da kanta ta jera mai a dadduma ya iso da tawagar shi kamar gwamna,




Saida ya koshi ya fara bata hakurin rashin zuwan shi da wuri, "aa bakomai nasan aiki ne ya rikeka, riko hannun ta yayi cikin damuwa,


"Akwai magana kenan yau don nasan ka tun kana yaro daka rikeni hakan akwai babbar magana, "eh mama akwai, ina cikin damuwa , narasa mafita bansan yazanyi ba,?



"Tell me what to do kaina ya kulle, "kayimin bayani badai matsalar wurin aiki bace ko? "Akan yarinyar da nakeso ne, ya fara yimata bayanin komai akan YASMIN, Amma banda zancen Auren ta ya boye wannan,



Hamdala tafarayi kafin tace kai nagodewa Allah yau kaine ke zancen Aure? Lallai wannan yarinya ta ciri tuta Ashe soyayya ta da ita akwai Abinda Allah yaboye,


Kai nayi farin ciki sosai baba na Allah yasa rabonka ce, ya Amsa da Amen, yaushe zakuje nema min Auren ta?


"Banson garaje Ai gobe zankira kannin mahaifinka sai muyi magana inyaso sai mu tsara komai,


"Don Allah kar ya wuce jibi zuwan su 'ya ciro ATM ya mika mata gashi asiya komai da ake bukatar kaiwa akwai kudi sosai a ciki zasukai 2milion idan basu isa ba kifadamin inturo muku Wasu,


Sakin baki kawai Hajiya tayi tareda mamakin d'an nata yau ba mafarki takeyi ba kuwa? Muhammad ke son Aure kuma cikin sauri haka? Lallai mahakurci mawadaci



Allah ya ma wannan yarinya Albarka ita kam koda Asiri YASMIN tayima MA tana farin ciki da hakan kuma sai takara mata kudi takaiwa malamin,



Ma kuwa a gidan ya yi wanka ya shirya domin yanada daki na musamman, ya sallami yaranshi kafin ya fito cikin shigar manyan kaya shadda ce fara kar ya murza hula kamar wani sabon Ango ya fito yana zabga kamshi fadin haduwar da yayi bata bakine,


Waya ya dauka yakira tareda bada umarni kai tsaye,
"Mu hadu a Unguwar Dosa da wannan motar harma da kayan cikin duka,



Ya fita Hajiya nakara godewa Allah da Yau take ganin irin wannan farin ciki,

***************
Yasmin dai yau a daki ta wuni bayan tafiyar ismail , ya gama yi mata bori ko kallon shi batayi ba kuma tasan da bai bullo da zancen Auren Zainab ba bazata taba yimai hakan ba,



Yama raina mata hankali Wallahi kuma ta shirya ko baba zai Yanka ta bazata taba y'arda da Auren shi ba,


Baba kuwa yakasa cewa komai ya zubawa sarautar Allah ido yaga ta ina wannan rikici zai kare?


Karfe takwas na dare YASMIN ta samu tsalki ta sheko wanka tareda yin Alwala ta shiga dakinta ta shirya kanta tsab cikin wata rigar baccin ta guntuwa dai dai guiwa tareda daura zani ta Dora hijabi tareda tada salla,



Tana sallamewa baba ya kirata falon su ' ta zauna kamar wadda tayiwa sarki karya gefe guda tareda dukar da kanta,


"Mama na kimun bayani ina sauraren ki " me kikeso ki fadamin? Kema bazaki Auri d'an uwanki ba kike nufi? Dake da y'ar uwarki kun gama watsa min tsarina baki daya ko,



"Haba malam yakamata ka barwa Allah wannan lamari ita maryam da kake magana Ina zamukai wa innan rabon kana ganin cikin shekara biyu Yara biyu ai sai mu yarda da yin ubangiji,



"Haka ne saudatu yanzu kina so ki fadamin bansan Allah keyin komai ba kome? "Toto yanzu nasan komai ma da sanin ki sukeyi tunda ba danginki bane shiyasa kike zuge ya'yan ki su ki Auren shi ko?


"Haba malam ya zaka fadi haka bayan kasan irin y'anda na reni ismail da hannu na kamar ni na haifeshi bai dace wannan kalma tafito daga bakinka ba,


Toh kusani keda Yasmin indai nine mahaifin ta to bazata taba Auren wannan yaron mara tarbiya ba, ya mike fuu ya fita,


YASMIN tashiga tashin hankali najin yau saboda ita iyayen ta na misayar yawu, abinda bata taba jiba tsawon rayuwar su,
Kuka taji ya kwace mata mama ta kalleta,



"Toh Allah ya biyaku ya'yan Albarka Wato dai kullum sai kunja mun magana idan zancen Auren ku yataso haka y'ar uwarki tayi kema gashi Abu yazo gab shine kika bullo da naki iya she gen,


"Kuyi kokari Kuyi Auren ku inda kukeso ni kuma sai ku kashe min nawa kunji nagode muku, itama maryam yanzu zankirata inji don nasan da sanin ta komai ya faru,


Kukan tane ya Kara sauti tareda girgiza kai cikin Kuka" mama don Allah kiyi hakuri Wallahi ni ban turoshi ba kuma Aunty batasan komai akai ba, ni wallahi na yarda da Auren ya'yan karkuyi fada akaina don Allah,


.
"Tashi kije ni nagama magana kuma, tashi tayi kamar wadda kwai yafashe mata ta nufi dakinta,


Baba na fita yaci karo da motoci sababbi dal a kofar gidan daya fara sai kuma ja y'ar Kara ma mai shegen kyau kirar Volvo sabuwar fitowa ya tsaya cak tareda makakin ko suwaye a ciki,



Fitowa MA yayi daga cikin farar ga kayan jikin shi farare yayi mugun haduwa ga kwarjini da haiba da ya cika ko Ina, baba bai gane shiba saida ya matso tareda mika Mai hannu,


"Salamu alaikum baba barka da dare' baba ya Amsa cikeda ganin girman yaron yace wa kake nema yaro?


"YASMIN nine dazu nazo da safe "toto nagane soja ko? "Eh baba sunana Muhammad Abdullah, to Sannu muhammadu bismillah shigo,



Tana kwance ta Dora wayar ta saman kirjinta tana tunanin rashin kiranta da yayi yau kardai fushi yakeyi da ita?


Kamshin jikinshi tajiyo tun shigowar shi taji domin turaren nada mugun kamshin da da mutum ya doso zakasan mutum na zuwa,




Wani irin faduwa gabanta yayi kardai shine ya dawo? Tashiga uku, kuwa MA zai jefa ta a damuwa,



Kiran baba yasa tayi saurin zabura cikin tsoro batareda ta tsaya daukar hijabi ba ta fito ta gyara sumar ta ta nannade ta sai zanin da ta Dora a kugunta saman rigar baccin ta mai guntun hannu Mai dauke da hoton frozen a jiki,



Kirjin nan na MA ya fito da kyau gwanin burgewa saida tasawo kanta wajen ta ganshi cikinta ya Kara d'urar ruwa,
Idanu ta zuba mishi cikeda tsoro gashi wannan ne karon farko data fara ganin shi cikin shigar manyan kaya yayi mata kyau sosai kamar Ango,



"Kije ki fito mana da kujera kintsaya kina kallon mutum kamar zaki cinyeshi, saida taji kunya tareda shigewa dakin mama tafito da kujerun roba guda biyu ta ajiye jikinta narawa ta koma daki cikin sauri,



Tunda tafito ya zuba mata ido kamar ya cinyeta yakeji tayi mugun yimai kyau gashi kanta ba dankwali yaga y'anda sirrin sumar ta yafito

Wani iri yakeji kamar ya bita cikin dakin ya turmushe ta yakeji,....... 🖊️




*hmm fan's yau hakuri zakuyi dani wallahi nayi typing ya goge tas by mistake don haka Kuyi manage gobe zan wanke muku zuciya da yardar Allah*



*Matar soja*
[8/30, 2:56 PM] Feenerh Wrtr: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
*BARIKI*
_Auren Soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻



_written by FENERH_
Maman Ammar


*Dedicated to*
Fiddausi mainasara feby



*Ina son ku ina kaunar ki kuna faranta min ina matukar jinjina muku Allah yakara dankon zumunci yakaro kauna my real fan's AISHA BABAYO, HUSSY ALI MAMAN ABDULLAH UMMI ZARIA, MOMYN KIDS, MOM HUSNAH,* _WA INDA MA BANKIRA BA ZAKUJINI A NEXT PAGE, AP NAYI TUYA NA MANCE DA ALBASA AISHA DAHIRU UWAR GAYYA MAJI D'ADIN M. A JINJINAR BANGIRMA UWAR DAKIN YASMIN ALLAH YABAR KAUNA DA AMANA_



29&30


Yaudai taga Rayuwa, kirjin ta har wani irin tsalle yakeyi kamar zaifito tsabar tsoro "MA zai kasheta kwanan ta bai kare ba,



"Bari inkira mahaifiyar ta ku gaisa, baba ya fada tareda mikewa ya shiga dakin mama, wayar shi ya janyo tareda tura mata text _kifito kefa nazo gani kin wani shige ciki kinbarni da yunwar idanu_



Saurin dubawa tayi tareda cewa "naboni yau, kasa motsi tayi ta koma lafewa a katifar ya kuma turo mata wani _wallahi zan shigo ciki kuma sai nayi Abinda nakeso zanfito inbarki da kunya kinsan ni bansan Abinda ya dace ba_



Zabura tayi ta mike cikin sauri ta saka hijabin ta tareda fitowa, wani irin kallo yake binta dashi tundaga sama Har kasa ya matse fuska "me kike boyemin?



Marai raice fuska tayi tareda matsowa kadan" don Allah me kazoyi? "Bansani ba kicire hijabin sai inbaki Amsa,


"Don Allah muh'd ka rufamin Asiri ka bari inji da tashin hankalin da ka jefani, "banajinki saikin cire wannan hijab din sai muyi maganar,



Cikin sauri ta koma dakin domin jiyo maganar su baba Zasu fito, gyara zaman shi yayi da kyau ya zubawa fuskar mama ido cike da farin cikin ganin inda YASMIN din shi ta gado kyau da fari,


Ya zame kasa tareda cire hula cikin bada girma irin na soja "mama barka da dare, ta Amsa cikin farin ciki da natsuwa bayan ta d'an zauna kan karamar kujera "ya aiki,? Yace Alhmdulillah, "to Allah ya tsare ku ya kuma kare ku, Amen Amen nagode mama,


Yaji dadin Addu ar ta har cikin zuciyar shi ga Matar nada kwarjini da kamala ga tsafta don tunda ya shigo gidan karan farko yasan Matar gidan nada matukar tsafa don sumintin tsakar gidansu tsab Abu zai fadi ka dauka ka jefa a baki,


Saida suka gama gaisawa ta mike tareda cewa" kaga Yasmin din? "Aa ya fada cikin sauri "mama tagan ni Amma taki fitowa kuma tasan saboda ita nazo, mama don Allah kiyi mata magana tana wahalar dani bayan itama fa tana sona sosai,


Wata irin kunya ce ta rufe mama naganin y'anda yake mata magana kamar wani Kara min yaro, shikuma harga Allah jinta yake kamar hajiyar shi,


Ya koma kan kujera ya zauna da kyau tareda dukar da kanshi kadan ya kalli baba yasan baba baya ra ayin shi sarai don yasan yanda Akayi akan Auren maryam don haka yasa shi nuna iko kota karfin mulki sai Anbashi Yasmin sunyi Aure su sami jikokin sunnah ko kuma su tarbi jikokin soyayya,


"Toh Nima bari inshiga ciki sai tafito Kuyi magana, baba yayi magana, "eh dama baba inaso infada maka jibi iyaye na zasuzo nan sukawo kudin gaisuwa,



Tsit baba yayi na d'an lokaci kafin yace "tom muhammadu nidai banine mad'aurin Auren Fatima ba Amma gobe zan Kira kanin nawa infada mai sai kuyi maganar komai a tsakanin ku,


Kara dukowa yayi kadan yayi godiya kafin ya koma mazaunin shi, shigewa sukayi ciki tareda barin shi a wurin bayan baba ya kwala wa Yasmin Kira ' kuryar daki suka shige domin su tattauna magana atsakanin su,


Alokacin ya mike zuruf ya nufi kofar dakin nata cikin hanzari,

Dai dai tana canja kayan jikinta domin rufawa kanta a siri domin tasan bazata iya fita da kayan jikinta batareda hijabi ba kuma a tsakar gidansu,



Riga da sket ne ta fito dashi na material ja domin canjawa, bata taba tunanin MA zai shigo cikin dakin ba shiyasa ta tube daga ita sai pant da bra ta saka sket din ko guiwar ta baikai ba ya shigo,
Da yake tabawa kofar baya yasa yaja ya tokare tareda nannade hannun shi a kirjinshi,



Wani irin trumbling marar shi tayi naganin ta a tsaye sanye da pant da bra farare duk da bata juyoba he can see ha awesome hips dai dai jikinta masu daukar hankali ga bombom dinta wow,


Ai tana zuge sket din ta janyo rigar yayi wuf ya karasa kusa da ita tareda rungume ta ta baya ya Dora hannayen shi akan westdinta tareda sauko da kanshi daidai wuyanta ya Dora mata kiss a wuyan,



Lamarin MA yadai na bata mamaki saidai tsoro don haka koda taji hannun mutum tasan shine, cikin tsoro tayi saurin juyowa bayan ya sauke mata hot kiss a wuya,


Tama manta da ba Riga a jikinta ta zuba Mai ido jikinta NA rawa tareda dafe bakinta da hannu cikin rasa mafita,


"Wai meyasa kakemun hakane? Don Allah kafita kajirani ina zuwa please kaje waje karsu mama su fito suganka muh'd ka rufa min Asiri don darajar iyayenka,



Aikin banza domin shi yayi nisa tunda ya Dora idanun shi akan boosty boob dinta ya rikice idanun shi suka juya Kala yayi wani irin kalar tausayi tareda kokarin rikota taja baya da sauri tareda kare kirjinta da rigar, cikin tsoron Abinda tasan zai iya yi,


Baya baya yakoma ya fada kan katuwar katifar tata mai cike da kamshin ta mai dadin gaske ya runtse idanun shi tareda kokarin natsa kanshi,



Gaskiya yau yayi namijin kokari DA bai yi striping dinta a cikin gidansu ba don ta mugun kunnashi sosai d'auriya iya d'auriya yau yayi,


Ganin y'anda ya runtse idanun shi yasa ta yi saurin saka rigar tareda janyo d'an karamin mayafin ta ta yafa ta matsa kadan kusa dashi' katashi mutafi don Allah karsu mama sufita inshiga uku,




Bude idanun shi yayi tareda zuba mata su cikeda shaukin zazzafar soyayyar ta "love you baby more and more, ya fada cikin kwantar da murya kafin yabi dakin nata da kallo,


Bayan katifar sai walldrp mai kofa biyu da mirror dinta dake dauke da turaruka da kayan shafa gefe data akwatunan tane guda shida pink masu kyau domin su ba talakawa bane don duk Wanda keda maganin lalurar yau da gobe ya wuce talaka, don Albashin baba ya ishesu suji dad'i har ma suyiwa Y'an Uwa Alheri,



Kan bangon dakin ya sauke idanun shi dake dauke da hotunan su Kala Kala ita da maryam tundaga na kuruciya har zuwa yanzu,



Murmushi yayi mai kyau ganin wani hoto nata tana sanye da kayan ta na nurse tayi masifar kyau, yatashi tsaye tareda kakkafe shaddar shi data fara squzing ya nufi wurin tareda ciro hoton ya rungume yasaka hannu ya ciro wani datake sanye da wata doguwar Riga pink kamar babie kanta da crown daga gani na wani occasion ne,



Kallon shi kawai takeyi, ga kamshin shi yacika dakin nata tab ya matso gab da ita" tank's for this beautiful pictures muje inbaki tsarabarki tana waje,



Bai jira komai ba ya fita tabi bayanshi cikin sauri domin ganin ko ba Wanda ya fito, tayi Ajiyar zuciya har suka kai kofar gidan bakowa,


Yana rungume da hotunan kamar kwai saida ya bude gaban motar ya ajiyesu kafin ya dawo wurinta,

Baki Yasmin ta saki wurin kallon motar da tagani y'ar karama tayi mugun yi mata kyau tana sheki duk da dare ne akwai d'an hasken wutar nefa a Unguwar kota ina,


Matsowa yayi tareda sanya hannun shi cikin pocket din Aljihun shi ya d'an rankwafo ta fuskar ta kadan "hope you like it? Idan kuma batayi ba a canjo miki'


Wani irin kallon shi tayi cikin tsoro, " me kake nufi? "Motarki ce akwai tsarabarki ma a ciki ya bude motar tareda bude bayan boot din ya Wasu irin akwatuna ne guda uku Kala daban daban manya duka girma daya blue red da kuma purple ya fito dasu kamar bakomai a ciki ya dauki biyu ya shiga dasu cikin tsakar gidan kafin yadawo ya dauki dayar ya shiga da ita,


Takasa cewa komai saida ya dawo yace "zomuyi magana kai tsaye ya riko hannun ta suka shiga gaban motar,


Juyowa yayi dakyau ya dafe kumatun shi ya zuba mata ido "baby nasan kinfi karfin wannan y'ar kyautar Amma kiyi hakuri zamuje kasuwa insiya miki komai ya d'anka mata key din motar a tafin hannun ta,



Gaba daya tarasa nayi ita yanzu ta ina zata fara tasan kotace mai bazata karba ba Aikin banza zatayi don ta lura dashi mutum ne mai ra ayin rikyau idan yayi niyyar Abu ba Wanda ya isa ya hana shi, don haka kallo kawai take binshi dashi,


Saida ya bata key din ne tayi saurin girgiza kai" aa nidai ka bar ni banason mota ta ina zanshiga da wannan key din incewa su baba me? Bayan kayan da kashiga dasu nidai don Allah kabari ingama dasu Lafiya,


"Hhhh yayi dariya sannan yace "tom idan bakyaso sai ki yi sadaka nidai nakawo kuma bazan koma dasu ba don kiji,


Matsowa yayi tareda riko hannun ta ya kashe mata ido, "baby kinfa dauki alhakina yau, kiri kiri Kinyi min kwalelen Abin kallo na inaji ina ganin su kin hana ni morewa,


"Tun fa shekaran jiya rabon da in rage ruwan Marana kinga yau Kim in wani Abu Inba hakaba yau bazan iya bacci ba,


Kallon nariga nasaba da halinka kawai takemai kafin tayi magana, "wannan ne soyayyar taka da kake fadar kanamun?


"Sosai baby da banasonki da na danne ki wallahi na rabaki da wannan y'anar dakike yanga da ita tuntuni, "dama kasaba yiwa yaran mutane '


"Point of correction, yaran dake ra ayi dai ko yanzu zuby najirana a gidana zanje ta ragemin wannan ruwan dole yau sai sun zuba zan iya bacci ya fada tareda shafo marar shi,


Cikin takaici ta bude motar ta fita, yana kiranta ta shige abinta Allah yagani tana tareda aiki don KO Auren MA tayi to sai tasamu hawan jini domin shi mutum ne mai yin Abinda yaga dama ba Wanda ya isa ya hanashi,


Fitowa yayi tareda rufe mata motar ya shigo gidan bai koma takanta ba ya ajiye key din akan akwatunan ganin karfe goma harda rabi yasa ya wuce gidan shi,


**********************

Tundosowar shi kofar gate din ya ga motar zuby a wurin ya matse fuska kafin ya shiga cikin gidan, tundaga falon yaci karo da Emanuel,


Yafara yimai ruwan bala'i akan yadawo zai fara barin mai gida kamar gidan karuwai ko, ya fara bashi hakuri jiki na rawa "Oga sory sir I no go do one again, ys fada yana sarawa kamar koda yaushe,



Dakin dake kasan falon ya nufa tareda kullewa gam da key ya fada kan katon gadon ya kife tareda runtse idanun yana tuno Abincin zuciyar shi Yasmin,


Kasa daurewa yayi ya kirata, lokacin tana kwance cike da kishin Kila yana can wurin karuwan nashi har Wasu hawaye takeyi na bakin ciki taga Kiran shi,



Ba jan Aji ta dauka domin tanason tasan halin da yake ciki, "babyyyyyy ya furta yana nishi "ad'aura min Aure zuwa jibi kar inkara lalacewa, I can't sleep Marana babyyy, ya fada cike da bukatuwa tareda sauke mata huci mai zafi a kunne,


Ajiyar zuciya kawai ta sauke tareda fara magana, "kana ina ne yanzu? "Ina gida na a BARIKI, "kaida waye agidan? "Nida zuby ne tana sama ni kuma ina kasa nazo nasame ta agidan,



Wani kululu ne ya tokareta yanzu don iskancin MA yake fada mata shida wata ne a gidan? Tsaki taja mai karfi, ya dago da kanshi daga kwancen "baby ina fatan tsakin ba nawa bane?


Banza tayi mai "Hmm you must pay that, ya katse Kiran, minti biyu ya kuma kiranta again "karki kuma yi koda badani kike ba banaso zan shigo gidan da safe injira baban mu da zai mana Aure,



Ajiyar zuciya tayi tareda rike wayar gam a kunne. "No matter how he is she love him to the extend da bata taba iya fushi dashi tana jin son MA kamar fitar numfashin ta,



"Baby barci kikeji? "Aa tace cikin sauri tareda Kara rungume wayar kamar shi ta rungume "kaifa bacci kakeji? "Aini idan ina tareda ke banajin bacci baby banki mukai safe ba ahaka,



Tuni ta baje idanun ta bude ido tarai domin zataso su kwana tana jin shi kar yaje wurin zuby don jitake ina ma tana barikin yau sai takoreta a gidan, ko yanzu jitake kamar tace ya koreta Amma ita a wa?



Haka suka kusan kwana yana zuba mata sambatu har karfe hudun Asuba kafin ya katse "baby bari inje inyi wanka inyi salla kafin akira asuba kinsani zubarda ruwa jin numfashin ki kawai "baby kema kinajin me nakeji kema kin yi yo yo? Kit ta katse Kiran tana dariyar halin muh'd , shidai baruwan shi saidai inbaiyi niyayyar magana ba duk abinda yafito abakin shi sai ya fada,



Saida tayi Alwala tafara nafila tareda yin Adduar neman zabin Alkhairi a rayuwar ta kafin akira salla tayi ta d'an karanta qur ani kadan tarufe ta haye katifa domin biyan bashi don yau gaskiya saidai mama tayi mata hakuri, Aikin gidan nan saita tashi,



Saidai karfe shida baba ya doki kofar ta ta zabura ta mike idanun ta cike da bacci ta fito waje tana hada Han ya, idanun ta a waje ganin baba ya zubawa akwatuna ido, mama na gefe rike da carbi,




"Fatima wa innan kayan fa ga mota nagani awaje tun jiya ga kuma makulli a anan? Bakin ta na rawa tafara in ina" baba shi ya kawo min Wai tsaraba,



"Harda mota? Inji baba cikin karaji, Amma y'ar nan me kikeso kimayar dani ne karamin mutum? Aurenki saura kwana uku ki karbi kayan wani kato haka akeyi me kika bashi zai miki irin wannan kyauta haka harda motar da har in mutu kudin Albashina bazasu

Please Login or Register in order to submit comment