Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta datayi " kiyi hakuri Maman Auwal bazan kuma fitina dake ba insha Allahu,



Koda ta shigo gidan kasa ce mata komai tayi saidai idanu kawai don tasan halin y'ar kanwar tata idan ta matsa sai yanzu tace zatayi mata yaji gwara ta bari idan tayi niya zata fada mata da kanta,



*tushen labari*
2years back,


Tafe suke a kan hanyar su ta dawowa daga makaranta sanye suke a cikin fararen kaya da d'an karamin hijabi sai bakin low pass a lamar dai malaman jinya ne su



Kyawa wane su sosai duk da kana ganin su kasan yaya da k'anwa ne Amma Akwai shakuwa mai girma a tsakanin su



Saidai kanwar tafi yayar nesa ba kusa ba kuma kirar jikin su Akwai banbanci domin Maryam nada jiki kadan ita kuma Yasmin jikin ta d'an dai dai ne,



Zasuyi matukar burgeka idan kaga y'anda suke tafiyar su kamar wasu kawaye,
Motace tasha gaban su fara tas kirar Lexus sukayi saurin tsayawa cak,.



Fitowa yayi sanye cikin kakin shi yayi matukar yin kyau kanshi ba hula ya fara basu hakuri,


"Y'an mata Kuyi hakuri na tsayar da ku akan hanya, wani irin mugun kallo Yasmin ta watsa mai " kadai yi niyyar kashe mu Allah ne baiyi ba saboda ka ganka soja to Allah ya fika , ta furta tana mai murguda mai baki,


Saurin riko hannun ta Maryam tayi Alamar ya isa mana, dariya yayi ya kalli Maryam "kibawa kawar mu ko kanwar muce hakuri naga tanada tsiwa,



" kayi hakuri ba komai ta rikota suka kama hanya da niyar wucewa yayi saurin shan gaban su " don Allah meye sunan ki ? Ya fada yana kallon Maryam, ta fada mai kai tsaye yayi "suna mai daraja don Allah wane unguwa kuke ne yau nakai kwana uku ina ganin ku a dai dai nan hanyar kuma saboda ku nake biyo wa yau nakasa hakuri ne a yimin uzuri inzo gidan k....



...karma ka fara wallahi don Aunty nada mijin Aure ni kuwa ko maza sun kare ban Auren soja don haka bamu hanya ko inbangaje ka wallahi,



Finciko hannun Maryam tayi sukayi gida batareda ta kuma kallon inda yake ba, Maryam na wai wayen shi domin gayen ya matukar burgeta ga kakin ya karbeshi sosai,



Shiga motar shi yayi ya rika binsu har saida yaga gidan su ya koma barrack w'anda su kuma suna isa kofar gidan su sukaci karo da Ismail wato w'anda. Maryam din zata Aura,



Karo na farko da taji takaicin Amince was Auren da iyayen su keda burin hadawa,
Tasowa yayi yana musu barka da zuwa,


Yasmin ce tayi carab tace " ai wallahi ya sama'ila idan baka dakko mu sai anyi ma fashi a hanya wataran kaga wani mayen soja yau ya biyo ma mata,



Dariya yayi "kai Yasmin kin cika mita nasan meye matsalar ki daga yau na gama interview dina ni zanrika dakko ku insha Allah,



Maryam dai wuce wa tayi batare da ko gaishe shi ba, yasan halin ta na rashin son magana don haka bai cika damuwa da shariyar ta ba,





Karfe takwas na dare suna zaune a tsakar gidan nasu dai dai na rufin Asiri aka aiko ana kiran Maryam, saida gaban ta ya fadi ganin irin kallon da Baban ta yayi mata kuma suna matukar tsoron mahaifin nasu bayason wasa,



" Maryam waye kika bashi izinin zuwa gidana bayan kinsan kinada miji a kasa? "Wallahi baba bakowa, " to bari inga kowaye,




Yana fita Mama ta ce "Yasmin waye yazo wurin y'ar uwarki? " mama ni yazan San ko waye ? "Nasan tare kuke ai koma waye zaki sani,



" nidai bansan waye ba, "to ku kiyaye kafin ku hadu da fushin babanku Kunsan burin shi akan ku ita kuma tasan tanada mijin Aure don haka ta kiyaye,



Shiru kawai sukayi har Baban ya dawo ya ce wani soja ne wai sunan shi Ahmed ya mun bayanin wai yana son Maryam ne toh nabashi hakuri bayan nayi mai bayanin tanada mijin Aure,



Wani iri taji har cikin ranta zataso ace ta Auri wannan bawan Allah mai suna Ahmed ya tafi da ita lokaci daya gashi ita bamai iya magana bace,




Kwana biyu Abin ya tsaya mata arai sosai har wani zazzabi ke shirin kamata gaba daya tayi sukuku da ita Yasmin tayi tanbaya har ta gaji Amma ba Amsa,




Shima gefen shi hakan take domin ya mugun damuwa soyayyar Maryam ta yi mai mugun kamu bayajin zai iya hakura da soyayyar ta gashi baida ko numbar wayar ta bare yaji muryar ta,


Damuwa tayi mai yawa har takai ga ogan shi ya tanbaye shi lafiya?

Jin juna suke kamar yan Uwa ko Abokai don haka bai boye mai komai ba " hmm saboda mace kake hana kanka natsuwa? Toh ita y'ar gidan uban waye da Baban ta zai ce ya bawa wani ita?




"If you really love her get her pregnant sai muga y'anda zata Auri wani kaga dole su baka ai, kallon ogan yayi " sau daya fa nasamu damar magana da ita,



"Ina gidan su yake ? Suna unguwar Dosa ne " ok karka damu I will help you get her,



Bayan sati daya ta dawo daga makaranta ita kadai ce saboda Yasmin bata jeba tana fama da ciwon ciki, ta fito daga cikin school din nasu dake tudun wada,



Ganin motar ranar a gaban ta yasa tayi saurin daga idanun ta ta zuba mai yana zaune a cikin motar kamar zai cinyeta da idanu,



Kafin ya fito ya dawo dayan gefen da take tsaye ya bude mata tareda bata umarni, "ki shiga Muyi magana Maryam,



Ba musu ta shiga tareda rufe kofar da yake tinted ne bamai hangosu,
Ya shiga shima tareda riko hannun ta da yakusa sata suma saboda wani irin shock da taji,


Wannan ne karon farko da wani namiji ya taba rike mata hannu haka
" Maryam ya kira sunan ta dago kanta kawai tayi idanun ta na cikowa,



"Kinga halin da soyayyar ki ta jefani' ko Abinci bana iya ci kawai tafiya nakeyi Amma bana cikin hayya cina Maryam bazan iya hakura dake ba banason wani ya Aure ki I want you,



Ki taimaki marayan Allah k'arki sani cikin gararin Rayuwa, kuka ta fashe dashi da yasa baisan lokacin da ya rungumota zuwa jikin shi ba gaba dayan ta tadawo kan kafar shi,



Wani irin rudewa yayi jikin shi ya fara rawa, " Maryam ki Aure ni don. Allah, ya dago fuskar ta ya zuba mata ido "kina sona?


Kai ta daga mai kawai " to ki fadawa baba ni kikeso ya barni na Aure ki zakiyi farin ciki, "bazan iya ba '
Ta furta mai. A hankali, Ajiyar zuciya ya sauke



" zan koma wurin baba yau bazan iya hakura dake ba ina sonki sosai ko bakyason Aure na?
",inaso, ta fada kissing goshin ta yayi kafin ya maida ita mazaunin ta kamar wata baby ya gyara belt din sit dinshi,

" muje inkai ki gida, tace "aa kar baba ya ganni a motar ka kabarni zan hau napep, " aa bazan bar matana na hawa motar haya ba, ya hau kan titin batareda ya saurare ta ba,.




Tun daga nesa ta hango mahaifin ta a kofar gidan jingine da jikin y'ar karamar civic dinshi yana magana da Ismail, wani irin faduwa gaban ta yayi ta fara juya kai "don Allah mu koma kaga baba da ya Ismail a tsaye,


Jin sunan w'anda takira yasa ya bude motar cikin fushi ya nufesu Dukawa. Yayi ya gaida Baban kafin yayiwa Ismail wani irin mugun kallo,
" Ahmed Kaine yau a gidan mu ya aiki, baba ya fada tareda bashi hannu,


Yace "Alhmdulillah naga Maryam ne a hanya na rage mata hanya nakawo ta gida yafada yana nuna mai Maryam din data fito jikin ta narawa ta gaida Baban nata dake. Binta da kallo,



Ismail kuwa dukar da kanshi kawai yayi batareda yace komai ba,
Gaishe su tayi ta shige jikin ta narawa,



A tsakar gidan ta tarad su suna hira Yasmin tayi filo da kafar Mama, ta gaida mama ta wuce da sauri cikin dakin su,


Yasmin ce ta mike tareda binta dakin " Aunty lafiya? "Me kika gani? " naga kin shigo a sittin ne ko kallo na bakiyi ba,


"Ba komai ya jikin ki? " naji sauki, ya lectures yau me Akayi?
"Ki duba jakata ina zuwa in watsa ruwa zafi ta fada tana fita dakin zuwa waje,




Tanajin Shigowar Baban nasu ta ki fitowa cikin bandakin domin tasan sauran saidai maganar da taji yanayi ce yasa ta fashe wa da kuka, saurin rufe bakin ta tayi da hannu kar su jita,




" nace Ismail ya fara shiri watan da zamu shiga zandaura musu Aure da Maryam, yake fadawa mama,


"Alhaji bayan kace sai sun gama school of nurse din kuma me yasa ka canja Shawara?
" gani nayi Maryam na shirin kaini ga kunya shiyasa nace zanyi mata Auren ita Yasmin idan ta kammala sai tafito da miji tayi Auren,



"Allah yasa Alkhairi tafada batareda lamarin yayi mata dad'i ba saidai halin girma irin na iyayan my mata nagari da kara yasa bata nuna maiba,


Ita kanta Yasmin jikin ta yayi sanyi duk da tasan wannan ne burin Baban su a Rayuwa hada Auren Maryam da Ismail,


Alhaji lawal mai turare shine sunan mahaifin nasu shi dan Asalin garin Zango ne su biyu iyayen su suka haifa shida kanin shi Mahmud sun taso cikin kaunar juna har lokacin da Alhaji lawal ya kammala karatun shi ya fara aiki da ma aikatar nipost dake nan Kaduna ya dawo cikin gari tareda Auren Matar shi guda daya da kuma d'an kanin nashi tilo,




Tun Ismail na karami Allah ya dorawa Alhaji lawal kaunar yaron tun ma bai haifi nashi ba, kuma d'an uwan shi ya mallaka maishi halas malak


Mama saudatu ita ce Matar shi daya mai halin kwarai ta rike shi Amana tun bata fara haihuwa ba har Allah ya bata haihuwar Maryam,




Bayan shekara biyu Allah ya kuma bata Fatima wato Yasmin kenan kasan cewar ta ci sunan kakarta ta wajen uba,



Rashin son maganar Maryam ya faro tun tana karama zaka d'auka kurma ce shiyasa ma bata fara karatu da wuri ba har saida Yasmin ta isa shiga makaranta aka hada su,


A gurguje sunyi karatun su tundaga primary har matakin secondary kafin su shiga makarantar koyon Aikin jinya wato school of nurse,


Wanda a nan ne suka hadu da Ahmed bayan maganar Auren ta da Ismail tayi karfi sosai,


A haka kwanaki ke tafiya har lokacin da baba yasa ya yi a lokacin Maryam duk ta tsiyaye a tsaye tsabar tunani da damuwa kullum mahaifiyar ta tanbayar ta takeyi duk da tana kara irin ta y'ar farko Amma saida ta cire kunya ta sata a daki,



"Ki fada min Abinda ke damun ki nice mahaifiyar ki Bakida wanda ya fini kuka tasa mai cin rai kafin ta bude baki " mama Ahmed nakeso banason ya Ismail ki sa baki baba ya barmu Muyi Aure dashi ina son shi sosai,



Shiru mama tayi tareda zuba mata ido tama kasa cewa komai tasan cewa maganar babbace tunda duk karar Maryam ta bude bakin ta fada lallai kuwa tana son shi sosai,


Tashi tayi fita dakin megidan ta sameshi ta zauna cikin ladabi,

Baban Ismail Alfarma nake nema don girman Allah, juyowa yayi sosai ya zuba mata ido "ina jinki saude wace irin Alfarma ce?



" akan zancen Auren nan ne don Allah ka hada Ismail da Yasmin tunda ita batada w'anda takeso ka bawa Yarinyar can zabin ta,



Zuba mata ido yayi kafin ya mike kawai ya nufi dakin su Maryam din tana ganin shi ta zabura jikin ta na rawa "Maryam baki y'arda da zabi na ba ko?



Kina so ki watsa min kasa a ido har zaki iya aiko uwar ki wurina ta fada min bakyason dana sai wani bare kuma soja

" toh shi kenan kije ki Aure shi Amma ki sani ba hannu na a ciki kuma bada yawu na ba kuma na gode wa Allah da yasa bake kadai bace Yata don haka zan hada mama na da Ismail nasan ita bazata bani kunya ba,


Wani irin kuka tasa jikin ta na rawa "baba kayi haku.." Ki yimin shiru kuma ranar Aurenki da nasa ba fashi kije ki nemi wani uban ya daura miki Auren Amma nidai kin gama zama a gidana,




Ya fita Abinshi ranshi matukar bace ya kira Yasmin tareda neman Alfarmar ta y'arda da Auren Ismail,


Abin yazo mata a bazata Amma kodan ta taimaki y'ar uwar ta dole ta y'arda, saidai ta nemi Alfarmar Baban ta ya barta ta karasa karatun ta kafin ya mata Auren ya kuma Amince,


Gefen Ismail kuwa ba wata matsala domin shi a yanzu tuni dama yafara son Yasmin din don Bazai iya furtawa Baban bane don haka canji yafi yimai dadi sosai,




Baban su Mahmud shine yayi ruwa yayi tsaki har aka daura Auren Maryam da Ahmed kuma mahaifin ta yace bashi baita kuma karta tako mai gida bai kuma y'arda kowa yayi hulda da ita ba duk da irin lallashin da kanin nashi yayi ta yi Amma fur yaki,



Shiyasa Yasmin take sato jiki tazo wurin y'ar uwar ta , sai bayan ta haifi Auwal ne baba ya fara sakko wa jin labarin ta kuma samun wani ciki ba tareda d'an ya shekara ba yasa ya fauwala wa ubangiji yasan cewa rabon haihuwa ne sanadi da yanzu yayi jikoki a kan titi,


Wannan shine d'an taka'i taccen tarihin Abinda ya faru sai kuci gaba da biyoni domin jin yazata kaya da Auren Yasmin din taku"



*Matar soja*
[8/30, 2:56 PM] Feenerh Wrtr: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
_*BARIKI*_
_Auren soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻


_written by fenerh_
Maman Ammar



*Dedicated to*
Fiddousi mainasara

(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)



тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09


9&10


Wanene Muhammad Abdullah M.A? Dana ga major Abdullahi Kudan yan Asalin Zaria ne mahaifin shi yayi Aikin soja tun ana Yakin basasa lokacin sune suka yiwa Nigeria hidima,



Mahaifiyar shi Hajiya Hauwa kuwa yar Asalin katsina ce fulanin Asali shiyasa ya gado fari sai dai kirar jikin shi ta mahaifin shine kowa yasan mallawan Zaria da tsawo kamar samu dawa



Ya gaji kyau gaba da baya yanada yayyi biyu mata duk sunyi Aure da yaran su manya ata kaice shine karamin su mahaifin su ya dade da rasuwa saura mahaifiyar su kawai,


Yan uwan shi mata duk suna Auren wasu kusoshin gwamnatin Nigeria ba wadda take nema a wurin shi mahaifiyar su na cikin gata sosai shiyasa take daukar yaran jama'a tana tallafa musu,



Tun mahaifin shi nada rai yakeda burin danshi ya yi Aikin soja kuma cikin ikon Allah ya samu gurbi a NDA har ya kammala tareda nasarori da dama har zuwa yanzu,



Da yakai matakin da yake kai na general a kananun shekarun shi domin ba duk soja ne zaikai wannan matsayin ba a under fourty,




Matsalar shi shine rashin yin Aure wanda shi baida burin yin Auren ma A rayuwar shi Sam domin duk abinda yake nema ya mallake shi kudi mulki mata kuwa da kudinka sai ka zaba wasu ma kyauta zasu kawo Kansu,



Saidai har yau baiga macen da ta zauna a rayuwar shi da har zai iya Auren ta ba sai dai zuby itama kawai shakuwa ce da kuma hidima da take mai da Aljihun ta kasan cewar ta y'ar gidan minister saidai wulakanci daban daban take gani akoda yaushe wurin MA,




Saidai bata sani ba yana ganin kimar ta fiye da duk macen da yake Hulda da ita domin yafi sakewa da ita ko a wurin harkar su yana dan samun gamsuwa da ita,



Cigaban labari

Kwalliya tayi sosai cikin wata doguwar rigar shadda blue kamar zataje fati ta daura dankwalin a sittin tareda yafa farin mayafi a gefen kafadar ta kana iya hango irin Aikin da gaban rigar yasha da stones suna sheki ga kirjin ta sunyi wani irin cika suna daukar hankali wani farin takalmi ne da kuma y'ar karamar pos dinta ta rike,


Hot 8 dinta take dannawa tana tura sako sai murmushi take fitar wa mai kaya tarwa,


"Yasmin har kin shirya? Taji muryar Maryam " eh Aunty ina Auwal da Baban shi nifa na matsu bamu tafi ba wallahi,


"Wai d'okin zuwa gidan Momyn MA ne haka? " bazaki gane ba Aunty Matar nada kirki kamar ba ita ta haifeshi ba wallahi sainayi sanadin da zatazo taga iskan cin da yake tsulawa a bariki d'an iska kawai,



"Nashigesu don girman Allah Yasmin kirufa mana Asiri ina ruwanki da rayuwar shi ? Nidai inkin San Abinda zakiyi kenan ki hakura bari infadawa Baban Auwal kinfasa,



" aa bazan yiba karki hana ni tafiya ai inada hankali yazan hada Uwa da d'an ta,


Fitowar Ahmed da yaron shi yasa shi tsayawa kallon ta "aa kanwa ta irin wannan wanka karkisa ace Amarya na karo wa maman Auwal,


" to dafa? Ai nice Amaryar dama, ta fada tana dariya, haka ne fa Kece ta karfen muje yamma nayi ko,



Fita sukayi tana dauke da Auwal a hannun ta Maryam ta rakosu kofar fita kafin ta koma taci gaba da Aikin ta,



Yana hango Fitowar su yana daga saman gidan nashi idanun shi a kafe akanta tana tafiyar ta a natse jikin ta na juyawa kamar tarwad'a



Gaba daya ta gama wucewa da imanin shi ya kasa koda kifta ida nunshi akan ta har saida ta shiga motar yayi Ajiyar zuciya kafin ya janyo wayar shi yayi dialing numbar Ahmed,



Yana d'auka yace "where are you? Muryar shi can kasa Alamar cike yake da kasala,
" oga ina gida yanzu dai zamuje gidan momy ne mu gaishe ta ta ce inkai mata Yasmin,



"Wait for me nima gidan zanje, yafada yana mai mikewa, shiru Ahmed yayi domin yasan Akwai matsala yanzu kam idan taji zasu tafi tareda oga,




Juyowa yayi tareda kallon ta tana wasa da yaron " kanwata tafiyar mu ta canja salo fa tareda oga zamu tafi bari in dakko babbar mota a ciki,


Ya fada yana fitowa batareda yaji Amsar ta ba, katuwar Hummer jeep din shi Army green ya fito da ita ya faka tareda jiran Fitowar oga kwata kwata,



Cikin shigar kana nan kaya kamar zashi training ya fito tree quarter da kuma wata riga mai hula kalar kaki ya bude gaban motar ya shiga saida suka fito yayi mata horn ta fito kamar bataso ta fara takowa kanta a kasa ta bude bayan motar ta shiga,




Yi yayi kamar bai sanda zuwan ta ba saida Ahmed ya tayar da mota yace "Yasmin ga oga baki gaishe shiba,


" dago kanta tayi cikin shirin daukar magana ta watsa mai harara kafin tace "la shine ogan naku? Wallahi da naga yana kwaso mata n.......



"Yasmin shine. Ahmed ya tari numfashin ta da sauri kafin ya kunna radion motar yasaka wani kida mai taushi na wakar Angel of my life,



Janyo earpiece tayi ta sanya a kunnen ta tareda sanya best wakar da take so ta Ado gwanja wakar shi ta a hayye matan Arewa kun kai mata,



Har wani lumshe idanun ta takeyi tsabar jin dad'in wakar shi kuwa tunda tayi magana yaji muryar ta mai zaki ya lumshe idanun shi batareda yaji kalamin ta ba,



Wakar dake tashi ce a cikin motar ga kamshin turarukan su ga na motar sai jin shi yake cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara,



Auwal wasan shi kawai yakeyi a gefen ta hannun shi rike da lollipop yana sha,

Saida ya tsaya kofar tafkeken gate din yayi horn sojojin suka wangale mai ya sa hancin ta,



Suka rugo tareda bude mai motar ya fito fuskar shi a daure ya basu umarnin su koma bakin Aikin su kai tsaye ya koma gefen da zata fito ya tsaya ya kare ta daga kallon masu gadin nashi,




Saida tayi gaba dauke da yaronta ta bi bayanta tareda Ahmed wani irin kallo yake binta dashi mai cike da ma'anoni kala kala,




Kamar koda yaushe dattijuwar na zaune akasan Capet din ta dora hannun ta akan tun tun din dake kasan hannun ta rike da carbi gefen ta zuby ce zaune kanta akasa,




Gaban ta kayan motsa baki ne a Jere, tun Shigowar shi falon gaban zuby ya fadi shi kuwa hade fuskar shi yayi tareda bata rai sosai,



Yasmin kuwa baki ta saki hango wannan mayyar wato uwar shi ma tasan d'an iska ne tunda ga karuwan har cikin gidan su,


"Abin nashi Ashe har da licence ta furta a fili kuma yajita sarai, fuska Hajiya ta saki sosai ganin Yasmin,



" a maraba da Yata Fatima Lale marhabin, ta fada cikin jin dadi yau ga Fatima kai Amadu ka cika Alkawari,



Matsawa tayi kusa da ita tareda zubewa ta gaisheta cike da kunya, shi kuwa gefen zuby ya nufa fuska a matse "what the hell, why did you come hare?



Shiru tayi jikin ta na rawa ta mike tareda daukar Jakarta tace " momy zan tafi, "A sauka lafiya ta fada ba yabo ba fallasa, don ita dai Yarinyar bata yi mata ba,



Mace ba kamun kai haka ki kwaso kafa kizomin gida duk da ina son ganin Auren shi bazan so ya Aure ki ba ta fada a zuciyar ta,



Bin bayan ta yayi suna fita ya fisgo ta ya hada da bango " kina hauka ne kika zo gidan mu? Fisgewa tayi da karfi "eh ina hauka Muhammad,


" haukar sonka haba ya kakeson inyi najira ka for so long yanzu kana shirin juya min baya akan wannan Yarinyar da a haihuwar kaji tsab zaka haifi kamar ta wallahi kaban kunya,



Shima Ahmed munafuki yace kanwar shi ce what ever wallahi sai naga bayan ta ba macen da ta isa ta rabeka in kyale ta,



"Kin makaro baby kuma wannan Yarinyar da ki taba ta gwara ki tabani yafi miki sauki kinga y'anda tayi dake ranar ki kiyaye nafada miki I don't take rubbish from women you no,


" kayi Abinda zakayi kuma Anjima gidan zanzo wallahi sai na dauki mataki akan ka Muhammad "zakiyi babban kuskure kuwa,




Ya fada yana mai juyawa cikin gidan ya samu Yasmin ta baje sai hirar su sukeyi kamar sun dade da sabawa




Auwal sai wasan shi yakeyi a jikin ta daga gani tanason yaron sosai ya Ayyana,

Ko kallon shi momy batayi ba domin tana ciki dashi akan zancen Aure,

Zama yayi a gefen ta tareda riko hannun ta " sory mama na ki taya ni Addu'a karkiyi fushi dani Kece garkuwa ta,


Dawo da hankalin ta tayi kanshi da kyau"kayi Aure inka naso mu shirya, "momy zanyi in lokaci yayi ki yimun Addu'a,


Uwa da da' sai Allah ta saki ranta harda samai Albarka tana mai fatan samun mace ta gari,


A zuciyar Yasmin kuwa cewa take " ogan yan iska mace ta gari? Saidai a mafarki kila d'an iska sai y'ar iska irin shi,




Sai kusan magrib suka bar gidan Hajiya tayi mata kyautar super da kayan kwalliya masu tsada harda turaruka



Tayi matukar jin dad'in ziyarar saida suka biyo ta ostrich oga yayi take away na dambun nama dasu pizza sannan sukayi bariki,



Zaka d'auka bai damu da ita ba a cikin motar nan kuwa duk wani motsin ta idanun shi na kanta,


Suna tsayawa itace farkon fitowa ta wuce bako sallama da ledar kayan ta Auwal kuwa yayi bacci a kafar MA saida Ahmed ya shigar da motar sannan ya karbeshi ya bashi ledojin take away shima ya je su ci da iyalin shi yayi godiya,




Tana shiga ta fara bawa Maryam labari "Aunty Gaskiya mutumin can katon d'an iska ne " wane mutumin kuma Yasmin sarkin yan daukar magana?



"Ogan ku mana kinsan dashi mukaje gidan maman shi Hmm Abin mamaki karuwar shi muka samu a cikin gidan da gani baiso taje ba......




" ya isa labarin nan Yasmin ina mijina? "Hmm masu miji yana nan zuwa shida my boy ni natafi in watsa ruwa tunda bakyason hirar ga kyautar da na samo ta fada tana mika mata ledar kayan,




Karfe goma yana kwance akan tafkeken gadon shi idanun shi a lumshe ya kasa bacci Yarinyar nan ta tsaya a zuciyar shi sosai




Yarasa me yasa ya kasa cire ta a cikin ranshi shidai ba

Please Login or Register in order to submit comment