Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai sunkusa zama nawa ko don haka kicire kunya kawai don watarana har a tsakiyar hannu na zasu kwana,


"Na bani yau ta fada, mikewa yayi yana dariya a hankali "ki fara sabawa don rayuwar wayewa zamuyi a gidan mu baby na,



"Kituromin a text Ina jira ya fita tareda barmata kamshin shi ta yi Ajiyar zuciya tareda kallon kirjin nata tana tuna lokacin da MA ya shafasu tayi shiru tana tunanin maganganun shi
Na jiya,



"Baby zanje wuri mai nisa yanzu bazaki iya zuwa koda sau daya bane inganki? Baby inashan wahala tsawon rayuwata bantaba jin irin Abinda nakeji akanki ba Kowa tanbayata yakeyi lfy ta kalau kuwa?



"Ni nasan banda lfy a jikina ki taimakeni ki bani kulawa koda kalma daya ce mai dad'i guda daya kifada min inji sanyi please



Wayarta ce da tayi Kara tasa ta dawo hankalinta ganin numbar shi ce yasa tayi picking tareda sanya hands free ta Ajiye tana mai kankare kunbarta da nail cuter



Shiru yayi Kamar kullum nadan lokaci kafin ya fara magana, "yaushe ne Zaki fara daga waya ki kirani? Yaushe Zaki fara bude baki kibani Amsar tanbayata,?


"Yaushe ne Zaki sama min natsuwar da zuciya ta ke bukata? Jibi zantafi baby please do something kafin mahaifiya ta tarasa ni,



Tsayawa tayi kawai tana nazari kafin ta daga wayar ta cireta a hand free ta fara magana cikin natsuwa, " me kake so da rayuwata? Meye tsakani na dakai? Kai ba saurayina ba ba d'an uwana ba you are nobody to me please free me ka barni in fuskanci masoyina mai burin Aurena mai nufin raya sunna dani bawai mai shirin zaman BARIKI dani ba,


Kai ba sona kakeyi ba kawai rayuwar banza kake burin yi dani kuma bazai faruba da ikon Allah aniyarka ta bika,


Toh ni ko a tarihi bantaba jin irin rayuwarka ba ba kalmar so ko daya sai mugun nufi a kullum "kai Wallahi nakara tsanar rayuwar ka da duk wani Mai halin BARIKI irin naka,



"Hmmm Meye so? Ya ake agane mutum nason wani? Meye jin dadi A soyayyar bayan Ajiyar da juna dad'i ? Kit ta katse kiran idanun ta na zubar da ruwa tana mai jin wani sabon bakin ciki MA ya gama da rayuwar ta Wallahi sai Allah yasa ka mata gashi ta Kasa fadawa Kowa halinda take ciki,



Ya takura mata duk da tun ranarda ya bata waya bata kuma ganin shiba, number yayarta ta Kira,


"Aunty na tafada cikin murna bayan ta daga "Wai YASMIN kin manta dani ko bayan kin gudu kinbarni gashi baban Auwal ya wuce gambiya jibi ogan Shima zai wuce sai sunyi wata shida zasu dawo,


Ajiyar zuciya ta sauke haka kawai taji Dadin tafiyar zataso ma kafin ya dawo Adaura mata Aure da ismail sai taga yanda zaiyi,


"YASMIN ki dawo don Allah kinga nakusa haihuwa kuma kinga baba bazai taba Bari indawo gidaba ki taimaka kidawo kodan yaronki yana kewarki,



Wani irin tausayin y'ar uwar tata taji nan take ta canja shawarar zuciyar ta na kin komawa BARIKI bayan ga rabin jinin ta a ciki,


*****************
Karar wayar ta tayar da ita daga dogon baccin datakeyi mai cikeda mafarkai masu dadi ta Sa hannu ta janyo wayar batareda ta duba ba tayi picking tareda kangawa a kunne ta cikin muryar bacci tace,


"Hello, wani irin Ajiyar zuciya ya sauke a hankali cikin natsuwa "hy baby' ya fada cikeda kasala, ba arziki ta bude idonta don jin muryar shi da tayi,



"Baby please say something sweet Gobe fa zantafi ki fadamin kallama mai dad'i da zanrika tunawa da ita,




Shiru tayi mai don tasaba da jin wa innan kalamai daga gareshi basa wani damunta, "um ki fadamin me kikeso inkawo miki kafin intafi,


"Banason komai naka nagode, "hmm dole kiso Abinda yake nawa baby kuma kidaina hawa machine natsani mace na hawa machine,


"Yanzu nafara hawa kuwa tunda dole inje school kuma Ina ruwanka ba,? "Niko keda ruwa harma da tsaki aciki yazaki rika kwanciya a bayan kowane irin kazami da jikinki mai matukar muhimmanci,



"Zankawo miki mota ki koyi driving, "banaso haka kawai kajamin bala'i wayar nan ma nasha question akanta bare ka kawo wata mota ince wa ya bani?


"Kice Muhammed Abdullah ne yabaki wani Mai nacin ki, "bakaji da kyau ba, a wane dalili zai bani mota Meye relation din mu dashi,?


"Blood relation inajinki har cikin jini na baby give me chance zanzo infadawa baba sai inkawo miki motar,



"Karufamin Asiri don Allah kabarni ingama lfy da iyayena ni yanzu banason duk wani Abinda zai dagamin hankalin su ta sanadiyata,



"Ni ai hankalina ba akwance yakeba tafiyar nan da zanyi ji nake kamar bazan dawo inganki ba wata shida kamar shekara shida nake hangosu please take care of your self



Zan nemi napep personal ya rika kaiki school please don't say no to this one, sannan ki kiyaye Wallahi ba a sake zantafi inbarki ba zansa tsaro donni ba sakarai bane idan wani namiji ya kusanta ki zaisha wuya I promise don haka ki kiyaye,



Wani irin tsoro taji ya shigeta ita kam ta hadu da rayuwa itada ke murna zai tafi shine zai hada ta da wani tsaro, wayarshi ma tana dauka ne saboda kawai a rabu lfy batason yana zuwa Unguwar su da tawagar shi,


"Baby' yakirata cikin kasala tareda yin mika mai karfi har bones dinshi na amsawa
"Zanzo inganki kafin in wuce please karki mun musu zanzo gidan ku,


"Aa karka zo don Allah katafi tunda muna waya, "I can't inason ganinki please allow me,



"Zanzo idan baki fitoba zan shigo gidan, saurin tashi tayi zaune tareda fara rokonshi da ya rufawa rayuwarta asiri, Gobe zanje school mu hadu a can ka ganni don Allah karkazo nan gidan baba na nan,



"Is OK to kifito da wuri saboda karfe tara jirgin mu zai tashi, shiru kawai tayi don tasan ita Allah ya jarrabeta da ala k'ak'ai a rayuwa,



"Kazo kai kadai karka kwaso yaranka kaga yanda kuke janyo idanun mutane a kanku banaso, "as you wish ya fada tareda katse kiran,



Kwance yake yana maijin bugun zuciyar shi na karuwa ga wani uban feelings dake taso mai kamar Yayi hauka sai mulmula yake a gado,



Bacci ya gagareshi ya mike tareda nufar durowar gadon shi ya ciro magani ya jefa a baki tareda daukar ruwa ya kora ya koma ya kife,




Yana cikin wannan halin Yaji ana shafashi tareda kissing wuyan shi da yatashi duk wata tsiga ta jikinshi ya wani irin juyowa tareda runtse idon shi gam yana mai ayyana Ina ma YASMIN ce tazo,



Jin an Dora baki akan lips dinshi yasa shi saurin bude idanun shi ya zuba mata ido batareda ya motsa ba ya dauke kanshi don kiss idan ba YASMIN ba baya bukata



Zuby ce ta marairaice fuska "haba MA yanzu da Emanuel bai fadamin zaka tafiba da saidai inji lbr ko, "Muhammad Kasan Ina matukar kaunar ka meyasa kake wahalar da zuciya ta,



Kallon hawayen ta kawai yakeyi kafin ya tashi kamar ba akan jikinshi takeba ya juya tareda zuba mata ido,



"Me ya kawoki,? "Nazo muyi sallama ne nakasa daurewa yau ko zaka kasheni bazan tafiba Allah sai kabani natsuwa Kasan munriga munsaba da juna yanzu kakeson ka juyamin baya bazan iya rayuwa dakowane namiji ba sai kai please marry me '



Tafada tana riko hannun shi ya bata wani irin mugun kallo"you are insane nine zan Aureki? Nataba fada miki Ina son Aure? Muntaba Alkawarin Aure dake?




"To me kakeso dani? Bana bukatar komai a wurin ko wace mace please leave me alone, kuka tasa sosai tareda fadawa jikinshi tana lalubarshi,



Gim ya tsaya kamar dutse ta Karachi fitinarta ta mike ta koma gefe tana kuka don jikinshi ko motsawa baiyi ba, "bakada lfy MA kaje kaga doctor



Mikewa kawai Yayi tareda komawa can karshen gadon Yayi kwanciyar shi bai kuma komawa ta kanta ba,



******************

Cikin Sauri YASMIN ta gama shirin ta ta fito tana rike da Jakarta ta Yayi irin wadda Y'an mata ke son ratayawa yanzu mai doguwar igiya bakomai aciki sai wayarta da ID dinta na school da kuma Y'an canjin ta,



Tsayuwar napep agaban ta ya bata tsoro tayi baya kadan ya leko da kanshi "Hajiya shiga muje umarnin Oga ne, batada zabi ta shiga ya tukata,



Wayarta ta fito da ita tafara dannawa tana mai bude sakonni a watsp bata kuma dago kanta ba saida yace munzo Hajiya,


Ta dago kanta taganta bakin tafkeken gate din dake dauke da manyan rubutu a jikin shi, GAMJI tagani,


"Yazaka kawoni nan? Maganarta ta kafe lokacin da tayi ido biyu da kyakkyawar fuskarshi yana sanye cikin shigar shi ta kaki yau Como flag ne a jikinshi Yayi matukar yin kyau gayen akwai fitinannen kyau a tare dashi kuma shine sojan da ta taba gani fari sosai kamar baya aikin wahala Abin tsoro atareda shi bai wuce muscles dinshi ba kamar wani roman reigns,



Matso da fuskar shi Yayi gab da ita tareda hure mata idanu tayi saurin dawowa hayyacinta,
"Wannan kallon fa karkiga munina baby ya fada yana dariya da gefe daya irinta muiskilayen maza,


Hannun ta ya riko tareda cewa ''let go kamar wata magnet haka ta biyo shi ya bude gaban katuwar motar da yazo da ita ya zaunar da ita kafin yazagaya ya shiga,



Facing dinta Yayi sosai ya zuba mata ido kamar zai hadiyeta kare mata kallo yake ta ko Ina ya sauke idanun shi ya gaban hijabinta ya sauke ajiyar zuciya



"Baby kintara komai da nakeso I love your body and your beautiful face bansan y'anda zanfada miki ba, katuwar wayar shi ya janyo tareda saita ta ya fara daukarta Hoto kafin yasa hannu ya janye hijabinta kamar wani mai tsafi batareda ta ankareba, har saida ya cire ya ajiye a kafar shi,



Wani irin zabura tayi tareda zubamai ido ita tarasa dalilin da yanzu Sam take Kasa fada mai mugayen magan ganun ta gashi yau ya mata wani irin mugun kwarjini duk ya cika mata motar


Sarkewa idanun su sukayi ta yi saurin sauke nata batareda ta ce mai komai ba don kamar ya daure mata baki yau,


"Ni dai kamar bakin nan bashi bane mai tsiwa? Kodai kinbada kaine infasa tafiyar nan baby mu gwangwaje?


Dauke kanta tayi gefe ya zubawa sajen dake fuskar ta ido tareda cewa wow domin ta kwantarda shi da gel Yayi wani irin kwanciya mai ban sha awa ga sumar ta tufke ta da katon ribbon ja ta nannade shi kamar kwallo jelar baisan lokacin da hannun shi yakai kantaba ya fara shafa shi tuni lafiyar shi ta motsa,


Tayi saurin dafe hannun shi domin kokarin cireshi akanta ya ware idanun shi akanta wa inda suka sauya launi harda wani ruwa ruwa suka tara a ciki,


Ya Kara riko hannun ta gam yanajin wani dadi yau ne karon farko da mace ta rike hannun shi haka Yaji wani iri har tsakiyar kanshi hannun ta kamar magic,



Baisan sanda ya fisgota kan cinyar shiba, wata y'ar Kara tasa tareda kokarin sauka tana dukan kirjinshi mai kamar dutse take duka,



"Meye haka Wai kaga shi yasa natsani halayenka banason iskanci,

Wani irin ajiyar zuciya kawai yake sauke wa duk da ta cure jikinta wuri daya amma he is feeling the hug he gave her deep down,



Saida Yaji yana shirin sumewa ya saketa ta koma gefe ta dunkule tareda sakin kukan da tarasa dalilin shi, "meyasa kakemun haka kaje wurin Y'an matan ka da suke nema mana saini kakeson kazo ka batamin tarbiya Allah sai ya sakamin,


Kanshi ya Dora akan sitiyarin motar na dogon lokaci kafin ya dawo dai dai wayar shi tayi Kara ya yi picking "OK kawai yace ya kalleta,


"Am sorry for making you cry ni zan tafi, saka hannu ya ciro wallet dinshi ya ciro ATM guda uku ya zube mata su akan laps dinta "gashi if needed kiyi duk abinda zakiyi dasu zantura miki pin din duka a text



Wani irin kallo tabishi dashi tareda ajiyemai kayan shi "bana bukata inada maiyi min, Kasa cewa komai yayi kawai ya mika mata hijabinta tareda kallon kirjinta for the last time yai ajiyar zuciya tareda fesar da huci mai zafi yaja motar saida ya kaita kofar school din kafin ya bude dash bord ya ciro rafar Y'an dubu dubu ya Ajiye mata guda biyu ganin bazata karba ba ya fisgo Jakarta ya bude tareda sakawa ya ajiye mata,


Bude motar yayi ya fita saida ya zagaya ya bude mata ba bata lokaci ta fito ko sauraran shi batayi ba tayi wucewar ta yabi bayanta da kallo har ta bace ya fada mota ya tafi,




**************
Yau kimanin kwana biyu kenan da tafiyar MA tunda ya tafi bai kirata ba kusan duk bayan minti goma saita duba wayar tarasa me yasa ta damu da rashin kiran nashi


Gashi yanzu data zauna sai tunanin shi ya fado mata wani iri takeji d'an gane dashi tarasa meke damunta,

Mama ce ya shigo dakin ta kalleta "YASMIN Wai meke damunki ne kwana biyu duk bakida walwala gashi sai aukin kwanciya kamar mara lfy,


"Ki kitafi y'ar uwarki nata kirana kije kitaimaka kitsaya da ita kinga mahaifinku ya Riga yayi ratsuwa tunfarko bazata dawo mai gidaba ta haihu,


Tashi tayi saida ta gyara ko Ina a gidan kafin ta fada wanka ta shirya cikin atanfa mai saukin kudi Riga da sket tayi kyau sosai ta sanya hijabi tareda daukar akwatin da ya shirya Kayanta,



Ismail ne ya shigo gidan cikin shigar alfarma ya karbi jakar ya fita da ita mama ta fito da Wasu kayan data shirya mata ta karba ta ce "ki kaimata zankirata inyi mata bayanin yanda zatayi dasu,




Tunda suka Kama Han ya batace mai komai ba sai shine keta zuba yana bata labarin yanda ya tsara musu gini da kuma tanbayar ra ayinta,



"YASMIN meyake damunki kwanan nan ba yadda kike ba nake ganin ki you are too silent this days
"Bakomai ta fada, bata kuma cewa komai har saida ya kaita har kofar gidan ya fitar mata da kayan kafin ya mata sallama batareda ya shiga ba ya wuce don Sauri yakeyi,



Tunda ta fito idanun ta ke kallon kofar gate din gidan nashi yana nan fes kamar koda yaushe sojoji na wurin kamar yana nan aciki,


Ji tayi dama ta ganshi yanzu ta kalli saman dai dai wurin da yataba ganin ta da Oga umar wurinda ta lura yafi zama a wurin saboda nan kayan training dinshi suke,


Saida ta dauki lokaci cikin tunani kafin ta dauki akwatin ta ta nufi kofar tayi nocking sannan ta dawo ta dauki katuwar jakar kayan da mama tabata ta kawoma Aunty MARYAM,




Maryam tayi Farin ciki sosai da zuwanta saidai taga canji a wurin kanwar tata sosai, duk da haka bata fasa taya ta duk abunda ta sabayi mata ba,


*************
Rayuwa nata tafiya yau tayi sati daya a Barrack amma har yanzu bataji daga MA ba tun tanasa ran zai Kira ta har tafara cire rai takai matukar damuwa akan rashin jin wayar shi,



Takira amma layin baya zuwa har kuka takeyi idan ta samu kebewa adaki ita kadai ya tafi ya barta da mugun tabo Wanda tasan shine ajalinta idan tayi wasa


MA ya sanya mata mugun guba a zuciya domin ita tasan ta kamu da kaunar wannan bawa Wanda ita tasan shi ba kaunar ta yake ba tunda ya fada mata clearly rayuwar da yake son suyi da ita,


Gaskiya Ashe ba laifin matan dake binshi bane yanada qualities da idan ya fara nunawa mace kulawa dole ta manne mai don ya hadu ne karshe gayen,



Tundawowar ta BARIKI bata kuma leka ko waje ba don bata son ganin Kowa MARYAM ta tanbayeta ba adadi meke damunta saidai tace mata bakomai,



Yau kusan karfe goma sha daya na dare tana kwance tana sans ar wayar ta tayi Kara tayi banza da ita domin tasan ismail ne kuma ita yanzu Sam bata son jin muryar shi kwanan nan


Saida taji kiran yaki karewa yasa ta fisgo wayar da nufin kashewa taga international call ne mai plus ta samu kanta da daga kiran don har wani rawa jikinta keyi,



"Hmmmm yayi doguwar Ajiyar zuciya jin ta daga mai kiran saida ya d'an dauki lokaci kafin yafara magana,
"Baby bakya kewata ko? Nasani ai dama nadameki Addu a kike intafi,



Tunda taji muryar shi gaba daya muryar ta ta fara rawa sai wani irin kuka ne ya zo mata mai zafi, tafara shashsheka,
"Subuhannallah baby Meye na kuka please ki daina karki jamun ciwon zuciya a nan,



"Kasa yin shiru tayi ya yi shiru tareda runtse idanun shi yakasa cewa komai saida ta dauki lokaci tana yi kafin tayi shiru,


"Hmm am Sory nakasa rike kaina dole saida nakiraki muryar ki nakeson ji kamar inyi hauka please inkiraki video call? Nayi kewarki da yawa,.......... 🖊️


*afuwan hannu na ya gaji ku biyoni domin jin ya zata kaya masoya ismail kuzo jaje YASMIN ta afka komar soja ko ya zata Kasan ce shin rabon waye YASMIN ya zakuyi da baba masoyan MA?*



*Matar soja*
[8/30, 2:56 PM] Feenerh Wrtr: PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09



🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
*BARIKI*
_Auren Soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻



_written by FENERH_
Maman Ammar


*Dedicated to*
Fiddausi mainasara feby



*wow Fans kunyi ruwan comment yanda ya kamata Ina Alfahari daku agaskiya kun faranta min rai sosai da zafafan comment wann ya nunamin kuna biyeda wann littafi nawa 100pcnt godiya dubu agareku masoyan MA da Yasmin*


21&22

Datse kiran yayi batareda ya jira umarnin taba ya kirata kai tsaye, ba bata lokaci ta dauka domin zuciyar ta na mararin ganin kyakkyawar fuskar shi tayi kewar shi fiye da tunanin kanta,



Wata irin doguwar Ajiyar zuciya ta sauke ganin fuskar shi data bayyana ya zuba mata ida sai kare mata kallo yakeyi kamar ya janyota ta wayar yakeji,



Ita kanta tatafi da yawa don ganin tayi yayi mata mugun kyau yakara fresh sati daya kawai da bata ganshi ba, "baby haka kike daman Ashe bana ganin komai' yafada idanun shi kamar suyi aman wuta,


Nan tadawo hayyacinta tayi saurin kallon jikinta ta waro ido tareda kife wayar ta dafe kirji shikenan takarawa kananzir fetur dama ya lafiyar kura,


Best ce kawai ta mugun kamata pink gashi tamugun fitoda shape din kirjinta da kyau tasaman har ana hango fararen na shanun ta da suka kunburo kamar su fito,


Saida taji karar wayar ta tuna da abinda takeyi tayi saurin janyo hijabi tasaka kafin ta juyo fuskar wayar, wani irin huci yaja tareda jan numfashi ya ce,


"Why baby please kicire ingani don Allah karkiyi min rowa nariga na gama yawo kin tada abinda bazai taba kwanciya ta dad'i ba please do something kicire hijabin if possible ma harda rigar kicire mun pleas..... Kit ta datse tareda kashe wayar baki daya ta jefar,


Ta kife a gadon tana jan numfashi "ya Allah ka yayemin son bawan nan naka kar ya jefani ga halaka, Allah ka rage min kaifin soyayyar shi a zuciya ta kar inyi rauni ya Allah karka nufeni da fadawa halaka, "Astagfirullah tafara nanatawa har saida taji tasamu natsuwa kafin ta wuce ta dauro Alwala ta tada salla domin Addu ar neman sauki,



Shikuwa MA ai yau yayi mugun gani domin yau sai Allah shida lfy wani irin juyi yake akan gadon nashi yana hango irin romon dake kirjin YASMIN "wayyo ta karasa ni,


Sai faman rike ciki yakeyi ga wani gumi dake fesomai na wuya dakyar ya tashi ya nemi magani ya watsa ko ruwa bai iya dskko wa ba,


Saida ya dauki dogon lokaci kafin ya d'an samu natsuwa ya kuma gwada kiran ta Amma akashe haka ya hakura tareda jin matukar jin haushin kashe mai wayar da tayi,




YASMIN bata kunna wayar taba sai washe gari tana kunnawa kiran ismail ya shigo ta dauka ba bata lokaci "gimbiya nakira jiya busy daga baya kuma naji akashe Ina fatan wayar ba matsala?


"Bakomai caji na yayi Kasa shiyasa na kashe nasa caji, "OK idan kina bukatar wata kifada inkawo miki, "aa nagode yasu mama? "Lafiya lau suke,


"Kinsan me? "Aa. "Wallahi sai yanzu naji dama baba bai daga Auren mu ba NA k'osa sosai inganki a gidana,
Shiru tayi kawai tana sauraran shi ya mugun bata tausayi,


Tasan yanason ta fiyeda yadda yaso Aunty maryam don haka dole ta yaki zuciyar ta kodan gudun fadawar d'an uwanta cikin damuwa ta tallafeshi ta kuma cusa soyayyar shi koda ta karfi ne ta cire Wanda ba kaunar ta yakeba saidan Wasu Albarkatu na jikinta,



"YASMIN yakira sunan ta "Na am Yaya, "please Meye kuma na wani Yaya keda zaki zamo matata yakama ta abani wani sunan mai dad'i mana, "wane irin suna ne mai dad'i?


"Kice sweetheart ko darling ko my love ko habeebi kidai zaba min inji, dariya ya bata sosai har taji bata tareda duk wata damuwa cikin second kadan yasanyata cikin nishad'i "Yaya ka koyi surutu,


"Badole naba tunda ina tareda ke bazaki san irin tanadin da nakewa rayuwar Auren mu bane YASMIN ' wani irin faduwa gaban ta yayi don sai taji Sam bata son yin Auren kuma,




"Bakice komai ba kobakya dokin Auren ne YASMIN? "Inayi Yaya ai lokaci ne "hmm bazan boye mikiba Allah ina cikin wani hali kullum da ciwon ciki nake kwana, ina fada Lafiya kinsani dole inji abinda nakeji yanzu, tanajin y'anda yake mata nishi a kunne yana groaning, Amma ba abinda taji itada ke tareda MA karshen BARIKI ai ita bataga kuma namijin da zai daga mata hankaliba don duk wani d'an iska bayan Muhammad ne,



***********
Wasa wasa ta daina daukar wayar shi koda zai Kira Sau d'ari a rana ko yayi fushi zai kuma gwadawa a haka aka share kwanaki,



Duk ya firgice don ma jarumini ba Wanda zai gane yanada damuwa har Ahmed dasuke tare har yanzu baisan tsakanin shi da Yasmin ba,



Yakai kololuwar karshen hakuri yau ya tura mata text _rashin daukar wayata ba Abinda zai rage akan kuduri na koda bana nan Wallahi zantura gidanku baba yasan komai Abinda zanyi bazai taba yimiki dad'i ba don haka be careful_


Ya tura mata lokacin tana zaune da Aunty maryam ta ji karar shigowar msg ta kalli fuskar wayar da kamar karta daga Amma tasamu zuciyar ta da bude sakon,


Tsaki tayi bayan ta gama karantawa tana mai ayyana ba abinda zai iyayi, "Lafiya kike tsaki sis? "Bakomai Aunty, "nifa bangane miki bane Yasmin naga tun zuwanki kinki ko fita waje saikace bake ba nasan ko Emanuel baisan kina nan ba, "banason surutun shine Aunty kinsan shi da gulma, hhhh dariya tayi "kodai nasan ku ai duk daya keda shi to ai Oga baya gari gulmar me zai kawo miki? Koda yake ance budurwar shi kusan kullum saitazo gidan watarana har kwana take a ciki,



Wani irin takaici da kuma mugun kishine ya rufeta tasamu kanta da jin zafin Abin sosai saboda jaraba har da bai gari yana basu damar shiga gidansu, samun kanta kawai tayi da shigewa cikin dakin ta ta kwanta tareda runtse idanun ta Wasu irin hawaye

Please Login or Register in order to submit comment