Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwartona!".

Yana jin ta faɗi haka ya tashi daga jikinta da sauri yayi hanyar toilet ya shiga.

Cikin bacci Mumy taji ƙarar Hansa'u dan haka ta tashi a firgece ta ƙarasu wajan Hansa'u , irin yadda taga Hansa'u ba komai a jikinta yayi masifar ɗaga mata hankali, jikin na rawa tafara faɗin,

" Ba abinda ya sameki ƴata?".

Hawaye ne suka riƙa zuba a idon mumy lokaci ɗaya.

Hansa'u kasa magana tayi ba abinda take faɗa sai

" Mumy na bani mijinki shine kwartona".
Tana faɗin haka itama tana kuka.

Duk wannan abin da ake yana toilet zaune yana tunanin mafita.



Hauwa ce tafito riƙi da wani figigin mayafi sai rangwaɗa take, Alhaji Abu yana ganinta ya washi baki yace,

" Hauwata Hauwata, Hauwa anfito, yanzu sai ina?".

Hura cigum ɗin dake cikin bakinta tayi sannan tace,

"Gidan ƙawata zanje Baba".

Inna Maryam ce ta kalleta kana tace,

" A haka zaki fita Hauwa duba shigarki, ke yanzu kodan yaranki bazaki wa kanki faɗa ba Hauwa, idan aure kike so dan Allah kizo kifitar da wani cikin waɗannan yaran ki aura, wallahi koni zan riƙa samun abinda zakuci ni dai burina ki daina wannan yawo".

Har Hauwa zata buɗa baki tayi magana sai wayarta ta fara rura, da sauri ta duba haɗi da ɗaga wayar tana faɗin gani zuwa.

Dube lnnarta tayi da Alhaji Abu tace,

" Inna bari idan na dawo muyi magana yanzu akwai waɗanda ke jirana kuma munyi alƙawari dasu gasu can suna jirana".
Tayi wannan magana tana tafiya domin ta fice.

Inna Rabi ce tace,

" ɗan gado sai ɗan gado, barewa bazatayi gudu ba ɗanta ya rerafa, Hauwa ai ke bakiyi komai ba idan za'ayi dubi da tsatson da kika fito"....Alhaji Abune ya buga mata tsawa dan haka ba shiri ta kama bakinta bata ƙarasa abinda taso ta yaɓawa lnnar Hauwa ba.

Inna dai batace komai ba ta tashi ta shiga ɗaki.


Hauwa na fita daman akwai wani yaro mai napep wanda ke ɗaukarta duk inda zata je, dan haka tana fitowa ta ganshi ƙofar gida yana jiranta, shiga tayi yaja suka kama hanyar zuwa inda zata haɗa wannan matar da yaro matashi mai sabon jini kuma yaro wanda iyaye suka jima sunabawa tarbiya, Ahmad yaro mai hankali ga kyau ga iya wanka.

Kai tsaye wajanda tasan yana zama suka dosa, kuma da zuwan su suka ganshi zaune shi kaɗai yana duba wani littafe na arbiya, kallonshi Hauwa tayi tsaf sannan ta ɗaga waya takira wannan matar tace akawo mata hijab mai girma haɗi da gayawa wannan matar wajan da zata kawo mata, ba ɓata lokaci wannan matar ta kawo mata, bayan ta saka ne ta fito daga cikin napep ɗin ta fara tafiyi cikin na tsuwa kace ita ɗin wata malama ce, sannu ahankali har ta ƙaraso wajan da yake, sallama tayi masa, bayan y ƙarɓa ne ta gaishe dashi cikin natsuwa, sannan tayi gyaran murya tace,

" Daman wajanka nazo ina so ne zaka koyar da yaran aunty na karatun islamiya koda awa ɗaya ce, saboda yaran naga basu ɗaukar karatun islamiya shiyasa akace asamu maiyi musu muraji'a idan sun dawo gida, to gaskiya najima ina ganinka anan kuma duk na wuce kana karatu to shine abin ya birgeni kuma nasan tabbas zaka iya shine nace bari na tambaye ka".

Murmushi Ahamd yayi dan koshi ya gaji da zama ba aikinyi dan haka yace,
" ba damuwa zanyi, ina ne gidan nata?".

Murmushi Hauwa tayi tace,

" Zo ga mai napep can sai na nuna maka gidan da take".

Bai tsaya wani tunani ba ya tashi suka tafi suka shiga, kai tsaye gidan wannan matar suka tafi.

Babban falon gidan suka sauka, bayan anci kasu da kayan mutsa baki sannan wannan matar tazo sai fari take da ido, kyaukyawace bata da wani jiki, amma itama irin Hauwace, akawai ɗaukar hankalin duk wani ɗa namiji wanda ya kallesu zaiji bayani a jikinshi.

Bayan tayi masa bayani ne haɗi da bashi kuɗi masu yawan gaske wanda zai riƙe kafin gobe ya dawo, bayan tafiyarshi ne Hauwa ta tsara mata yadda zata bin komai a hankali har tasamu kan yaron dan da alamu akwaishi da taurin ka, amma idan kika bi ahankali har kika samu yashiga gari to wallahi sai yadda kikayi dashi dan irin yarannan har kuka sukeyi muna, haka dai Hauwa ta riƙa bata shawara daga baya tayi mata sallama tayi tafiyar ta haɗi da cikata da shatara na arziki.

Tana fitowa suka wuce unguwar da ta ɗau ɗaki haya saboda hutawa da samarin ta.....





*Comment and share*



*SUMMY M NA'IGE✍️*
*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*




*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

*Z.W.F.🏝️*



*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*


*Marubuciyar*

*Ƙawar ƴata ce*
*Umarnin saurayi*
*Ƙawaye ne sanadi*
*Auren biyayya*
*A chating muka haɗu*
And now
*Mijin Babata ne*




*_INA MIƘA GAISUWA GAREKU ƳAN UWA KUMA MASOYAYA KUMA MASOYAYAN WANNAN LITTAFE NA MIJIN BABATA NE, COMMENT ƊINKU NA ƘARA SANI FARIN CIKI FIYE DA TUNANINKU, INA GODIYA SOSAI IRIN YADDA KUKA ƘARƁI WANNAN LITTAFI, ALLAH YA BAMU IKON KAMMALASHI LAFIYA YA_🤗*




*SHAFI NA 12*



Ƙara shigar da ita jikinta Mumy tayi haɗi dayi mata tofi, tana rarrashinta, kayan jikinta ta mayar mata haɗi da ƙara rarrashinta itako sai surutai take tana faɗin Mumy mijinki shine kwaetona ki taimake ni ki rabani dashi!.

Tana cikin faɗar haka shiko dai-dai lokacin da yashigo ɗaki haɗi da rai kamar bai taɓa dariya ba, kallon mumy yayi irin kallon nan na tsana kana yace,

" Naji sharin da ƴarki take kullamin, to bari kiji idan gidan ubanta ne bata son na zauna ba sai ta naɗamin sharri ba, wallahi zan barshi har abada, ke koke zan iya rabuwa dake da tazo ta naɗamin sharri, dan haka yanzu basai anjima ba zan bar gidannan wallahi bazan kwana acikinshi ba, kuma da safe zan rubata ta karda akawo miki sai ƴarki taje ta tada ubanta cikin ƙabari yazo kuci gaba da zaman aure tunda ta nunawa duniya kishi take taya ubanta".
Yana faɗar haka yayi cikin ɗaki ya fara haɗa kayanshi.

Jikin Mumy na rawa ta ture Hansa'u daga cikin ta ta shiga bedroom cikin tashin hankali.

Riƙishi tayi haɗi da sanya wani marayi kuka tana faɗin,

" Dan Allah kayi haƙuri wallahi ina tunanin mafarki ne take dan har yanzu idonta rufe suke bata buɗe, dan Allah ka tausayamin wallahi ina matoƙar sonka".
Ta kai ƙarshin zanci tana kuka haɗi da durƙusawa ƙasa ta riƙi ƙafarshi.

" Nizata nunawa bariki sai tagama iskancin ta waje maza sun gama lalubarta tazo tana cewa mafarki ne take wallahi banyarda cewa mafarki bane, tabbas akwai wanda ke shigowa gidannan yana anfani da ita, da zaran sunji mutsina ko naki sai ta koma ta kwanta tana ƙara tana cewa ƙarto yazo mata, dan haka datayi ciki ace nine gwara na bar gidan nan tunda na lura ke tsoronta kike ji ".
Ya kai ƙarshin maganar rai haɗe kamar abinda ya baɗa da gaske ne.


Wata ƙara mumy ta sanya lokaci ɗaya ta tashi da gudu ta isa falo wajan da Hansa'u take zaune tana kuka saboda taji duk abunda yake cewa Mumy.

Mumy da zuwanta wajan Hansa'u bata tsaya komai ba tasa hannu tashaƙo wuyan Hansa'u haɗi da faɗin,

" Ni zaki cin amana kici amanar mijina, to wallahi kinyi ƙarya, ashe kice ke kawo ƙato yakwana dake dan kina shegiyar yarinya ki ce wannan bawun Allah ne, to bari kiji ƙarshin zamanki gidannan ya ƙare, dan wallahi da aurena ya mutu gwara nakasheki, dan haka ba sai gari ya waye ba, ki tashi kihaɗa duk wani abu wanda yakasance naki ne ki barmin gidana dan ubanki ko ƙwandala tashi babu lokacin da zan sayin wannan gida dan haka yau kinji gida nawa ne ni kaɗai, dan haka kitashi ki kama hanyar zuwa gidan ubanki, dan ko wace ƴar tana tutiya ne da gidan ubanta ba na uwa ba".

Tana gama faɗar haka ta tukuɗa Hansa'u waje, Mumy kamar wata mahaukwaciya sabon kamu , haka taje ta ɗauko duk kayan Hansa'u tajefo mata su waja kana ta roƙon Hannun Hansa'u ta fitar da ita waje sannan ta maida ƙofar gida ta rufe.


Wajan mijinta ta dawo wanda abinda tayi ma Hansa'u ba ƙaɗan yayi mishi daɗi ba, amma bai wani nuna ba yaci gaba da haɗi fuska waishi a dole fushi yakeyi.

Rugumeshi mumy tayi tana bashi haƙuri akan dan Allah yaci gaba da zama tunda yanzu Hansa'u ta koma wajan kakarta Hajita Sa'a, da ƙar Mumy ta samu ya yarda yace ya haƙura, saboda daɗin da yaji wannan dare kwana yayi kanta yana mata abinda yasan tana so, lokaci ɗaya Mumy ta manta da abinda ya faru bare wata Hansa'u.

Hansa'u kallon Mumy kawai takeyi har tafitar da ita waje kuma ko waje cikin dare, wasu Hawaye ta shafe a fuskarta dai-dai wannan lokaci wasu samari suka ƙarasu wajanta sai hura sigari sukeyi, suna wata tafiya da alamu cikin maye suke.

Hauwa ba ita ta koma gida ba sai dare, bayan ta shiga gida kai tsaye ɗakinta tashiga tayi wanka tana shirin bacci sai ga Innarta tashigo riƙi da fitila a hannunta tace,

" Hauwa tun ɗazo sai nemanki muke, wai ina kike zuwa ne?".

" Kai Inna wallahi kin fiye tambaya, ai ni ba yarinya bace da zaki tsareni da tambaya".

" Allah ya shiryeki Hauwa, daman gaya miki ne zanyi ɗazo aka aiko akace agaya miki Ubanki na can kwance babu lafiya kuma babu mai kula dashi shine nace bari nagaya miki".

Tsaki Hauwa tayi tace,

" To ni Inna mi zan mishi? ko lokacin da ina ƙarama ya taɓa taimakona? ko yasani makaranta, ko ya taɓa bani wani taimako wanda zai nuna cewa shi ubanane? dan haka ki rabu dani, can ƴan uwanshi da uwarshi su kula dashi".

Inna kallon Hauwa tayi haɗi da haɗi wani baƙin ciki wanda ya tokare mata wuya tace,

" Indai kin amice nice na haifeki, to gobe ina so ki tafi ki ganshi ko bai taɓa miki komai ba shine yayi sanadin zuwanki duniya, kuma wallahi kar nasaki jin irin wannan maganar ta fito daga bakinki".

Inna nagama faɗar haka tayi tafiyarta saboda zuciyar ta dataji zata fara mata cuyo.

Tsaki Hauwa tayi kana tace,

" Bai taɓa kullamiki komai ba amma kice sai nabishi, bawani nabishi na kula har yanzu sonshi takeyi".

Tsaki taja haɗi da jawo abin rufa tayi kwanciyar ta......





*Comment and share*




*SUMMY M NA'IGE✍️*
*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*




*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

*Z.W.F.🏝️*



*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*


*Marubuciyar*

*Ƙawar ƴata ce*
*Umarnin saurayi*
*Ƙawaye ne sanadi*
*Auren biyayya*
*A chating muka haɗu*
And now
*Mijin Babata ne*




*NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFI DAGA FARKONSHI HAR ƘARSHE ZUWA GA MASOYIYATA KUMA ƳAR UWATA MUMY KULSUM, (Zakiyya).*




*SHAFI NA 13*



Asalin labari.

Malam Bashar shene Mahaifin Hansa'u, Sunyi aure da Mumy wato Yasira cikin so da ƙaunar juna, Malam Bashar Malamine a wajan Yasira wato malamin su ne na islamiya, malam Bashar mutumin kirkine kowa nashi ne haka yasa kowa ke ganin girmanshi, bayan sun dai-dai ta da yasira yaje ya sanar da Mahaifiyar shi ya samu matar aure, da yake mahaifinshi ya jima da rasuwa, Hajiya Sa'a tace yanzu Bashar kai da baka da baka gama gini ba, ina kai ina wani zanci ka fitar da matar aure, nuna mata yayi shi ba yanzu za'a aure ba, kawai yana so ne iyayenta su san dashi dan kar ayi mata miji, ba yadda Hajiya Sa'a ta iya haka taje ta samu ƙanin mahaifinshi yaje ya nemar masa auren Yasira wajan ƙanin Mahaifinta, dan ko ita mahaifinta ya jima da rasuwa.

Bai sha wuya wajan bashi Yasira ba, Saboda kowa yasanshi mutum ne wanda yasan darajar mutane kuma ya iya zama da mutane.

Haka Malam Bashar da Yasira suka cigaba da soyayar su har zuwa wani lokaci , ƙanin Mahaifin Yasira ne ya aikowa Iyayen Bashar yace yana so ya aurar da ƴarshi idan har Bashar bai tashi ba shikam ya tashi aurae da ƴarshi sai dai yayi haƙuri zai bawa wani, shi kuma Allah ya haɗashi da wata.

Bashar najin haka sosai yashiga tashin hankali shida Yasira, da mahaifiyar taga haka ta bashi shawar tonda yana son Yasira ya je ya ɗauke haya zuwa shekara ɗaya dai-dai ya ida ginin gidanshi sai ya koma.

Haka kuwa aka Hajiya Sa'a tasa mishi hannu har ya samu aka ɗaura mishi aure da Yasira.

Wani ƙaramin gidane yasamu haya amma Yasira tace shi take so ba komai nashi ba, dan haka koda aka kaita gidan bata damu ba suka cigaba da zamansu cikin so da ƙaunar juna.

Sai da yasira ta shakara ɗaya sannan ta samu ciki mai wahala ga kuma laulayi, ko yaushe ba lafiya, suna cikin haka kuɗin haya ya ƙare mai gida yace tabbas sai sun bar masa gidanshi idan basu bashi kuɗi ba, kuma dai-dai wannan lokaci Bashar bashi da kuɗi ga ɗawai niyar iyali kuma gashi koda yaushe suna asibiti saboda cikin bai bawa yasira lafiya ba.

Irin walaƙanci da yasira taga mijinta anayi mishi ne yasa tace bari ta sayar da kayan ɗakinta suje a gina mata ko room and parlour da toilet yafi musu shan walaƙanci, bayan ta gayawa iyayenta shima ya gayawa mahifiyarsu ne aka sayar da kaya yayi gini sannan suka koma ciki abin sai wanda ya gani.

Koda suka koma ko katifa bata da ita, haka suka riƙa bacci a ƙasa har cikin Yasira ya tsofa.

Lokacin da cikin ya cika wata tara Allah ya azurtasu da samu ƴa mace, sosai sukayi farin ciki da kyautar da Allah yayi musu.

Bayan suna Bashar ya tashi tsaye wajan nema, ko kafin Yasira ta dawo wanka ya saya mata kayan ɗaki irin na zamani, sosai tayi farin ciki da haka, haka suka cigaba da zamansu cikin rufin asiri har Yasira ta kai shekara huɗu amma babu wani labarin samun wani ciki dan haka suka cigaba da kula da ita, dan ko makaranta ta kuɗi mahaifinta yasa ta, Shekar Hansa'u sha huɗu Allah yayi wa Malam Bashar rasuwa, mutuwar da ta gigita ala'uma da ƴan uwa musamman ita kanta yasira, dan ba wata jinya yayi ba motace ta kaɗeshi.

Bayan akammala kwana uku kowa ya koma gidanshi aka bar yasira da Hansa'u cikin kunci da takaici.


Bayan Mumy tafita takaba ne ta fara sanar ta, kuma cikin ikon Allah Allah yasawa sanar albarka, Kabir shike kai Mumy kasuwa ya mayar da ita gida, kuma duk jimawar da zatayi sai ya jirata har ta kammala ya ɗaukota ya mayar da ita gida.

Kabir yaro ne matashi dan ko aure bayi ba, amma irin yadda yaga mumy na sana'ar ta kuma tana da gidan kanta dan haka yasawa rainshi ai irin su Mumy sune musu daɗin aure, mace mai sana'a da gida ai daɗin aure ne da ita, dan haka ya fara nunawa Mumy soyayya cikin hikima batare da ta fahinci mi yake nufi ba.

Ita koma a lokacin Mumy aure bai gabanta, burin ta Hansa'u tayi karatu mai zurfi, danshi ta fara faɗi tashi wajan neman nakanta.

Lokacin ana fitowa Mumy da zanci aure, amma sai tace ba yanzu ba, iyayenta ne da suka ce dole ta fitar da miji tayi aure dan baza su zuba mata ido suna kallonta ba, shi koma Kabir na ganin haka ya ƙara matsawa da nuna mata soyayya zallah babu wani ɓoye-ɓoye, tun Mumy na haɗe mishi fuska har tazo taɗan fara sakin jiki dashi, a lokacin Hansa'u bata wani fahinci abinda ake nufi ba, amma irin yadda yake shigowa gidansu kai tsaye bala'i haushe yake bata, dan wani sa'in ko sallama bai zaiyi ba zai shigo gidan yariƙa kallonta musamman nashanunta da suka fara fita.

Ko Mumy bata tsakar gida kai tsaye zai shiga ɗaki ya sameta koda kuwa babu kaya ajikinta haka zai shiga suyi ta buga soyayya suna guje-guje suna ihu, haka zai zauna gidanmu har cikin dare suna ɗaki shida Mumy wata rana ma zata koreni naje wajan kakata, kai Mumy tayi soyayya wadda ko lokacin da zata aure Babana basuyi irinta ba, irin wannan soyayar da sukeyi ne mutane suka samusu ido saboda Kullum Kabir yana gidanmu ko a caɓar da yake zuwa ya daina saboda yaci yasha ya kwanta saman gado sai kace wani mijinta.

Irin yadda naga kowa yasama Mumy ido ne yasa naje na gayawa Innarta halin da ake ciki, bayan Innarta ta kirata ita da ƴan uwanta sukayi mata magana tace ita ba abinda ke tsakaninsu sai ya kaita kasuwa ya ɗauko ta, amma tunda mutane sunce haka to tabbas sai ta aureshi, iyayenta da ƴan uwanta ba yadda basuyi karta aureshi ba tace a'a ita tabbas shi take so kuma shi zata aura.

Ba dan son suba haka aka ɗaura auren Mumy da Kabir wanda bawata wahalar da yayi ina ba sadaki da ya biya ba, ranar da aka ɗaura musu aure ranar banyi bacci ba saboda ihun da suka kwana sunayi shida mumy, haka gari ya waye gabana ya goyota yaje toilet yayi mata wanka ya fito da ita.

Koda zanje makaranta da kyar nasamu ganinta ta bani kuɗi na tafi, to tunda ya ga kuɗin da Mumy ta bani lokacin da zanje makaranta to tundaga lokacin ya fara haɗi rai shi wallahi ko ƴaƴa gareshi ba zai bari suyi karatu mai zurfi ba saboda yanzu lalaci yayi yawa, tun mumy bata ɗauka ba har ta ɗauka yasa duk ta aje wani kuduri nata gyafe na son taga nayi karatu.

Wannan kenan.



Koda Safiya ta waye Hauwa kamar baza taje ba, haka dai tashirya ba dan ranta yaso ba ta tafi batare da tayiwa kowa magana ba na gidan, dan ko Alhaji Abu da suka haɗu hanu kawai ta ɗaga masa tayi tafiyar ta rai ɓace.

Kai tsaye gidan Babanta ta tafi.

Kwanci ta tarar dashi shi kaɗai guda sai biyarshi suke saboda warin da ɗakin keyi, hannu tasa ta rufe hancinta haɗi da wowa baya.

Dubanshi tayi sama da ƙasa tace,

" Ina fatar ka gane kowace ce".
Ta kai ƙarshin zancin da sake harararshi.

Hawayen da suka zuba a dunshi ya goge yace,

" Ɗiya tace Hauwa'u".

Ya kai ƙarshin zanci da sanya wani murmushi mai ciyo.

Bata ce dashi koma ba, tafice, bata jima ba sai gata tazo dawasu matasan maza, nuna musu wajan da yake kwanci tayi, ba ɓata lokaci suka ɗaukeshi suka kai toilet suka yi mishi wanka aka gyara mishi jikinshi da ɗankin da yake kwance, bayan sun kammala ne ta sallamesu sannan ta ajema Baban kuɗi ko kollonshi bata sakiyi ba tayi tafiyar ta yanata famar kwala mata kira amma tayi mishi banza, dan sarai tajishi.........



*SUMMY M NA'IGE✍️*
*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*




*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

*Z.W.F.🏝️*



*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*


*Marubuciyar*

*Ƙawar ƴata ce*
*Umarnin saurayi*
*Ƙawaye ne sanadi*
*Auren biyayya*
*A chating muka haɗu*
And now
*Mijin Babata ne*




*NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFI DAGA FARKONSHI HAR ƘARSHE ZUWA GA MASOYIYATA KUMA ƳAR UWATA MUMY KULSUM, (Zakiyya).*




*SHAFI NA 14*



____________📝 Kanta ta haɗe da ƙafafunta tana kuka har suka ƙaraso wajan da take, har sunyi gaba sai suka ji sautin kukanta, juyowa sukayi a tsorace dan ba shakka sun tsorata.

Yarinya ce suka gani zaune ta haɗe kai da kakafafu sai kuka take.

Har zasu wuce saboda tsoro dan sun zaci aljanace, sai ɗayan yace wallahi ba aljana bace sai munyi mata magana, jin maganarsu yasa ta ɗago kanta a tsurace, ganinsu datayi ne yasa gabanta dukan uku-uku, dan haka cikin hikima ta tashi zata gudu, da sauri ɗayan ya riƙon hannunta yana ƙara mata kallo, kallon da yake mata ne yasa ta buga wata ƙara wadda da ace Mumy na cikin hankalin kanta da zata ji.

Ɗayan su ne yayi sauri ya ɗauko wani farin ƙyalle ya ɗaura mata a fuska, lokaci ɗaya ta rufe idonta kamar wata matatta.

Murmushi ɗayan yayi yace,
" kozo na kaita mota dan wallahi yau nayi gamu da katar dan tabbas nasamu irin kalar yarinyar dana ke so".

Jinjina mishi hannu sukayi haɗi da faɗar,

" Dole muyi fati tunda har yau ka iya furta cewa ga wata mace da kake so".

Murmushi yayi musu kana suka fara tafiya har suka kai wajan da suka aje motar su.

Buɗewa sukayi yasata sannan ya rufe kana suka shiga suka bar unguwar sai kiɗa suke sha suna tafi haɗi da rangwaɗa kai.

Koda gari ya waye Mumy bata wani damu ba, tunda tana tare da masoyinta sai famar buga love suke hankali kwanci, saboda tasan ba inda Hansa'u zata je sai gidan Kakarta wato Hajiya Sa'a.

Tare sukayi wanka, bayan suyi ne tashirya shi sannan ya zauna ta riƙa bashi abin kari har sai da ya ƙoshi sannan ya jawo ta jikinshi sosai.

Ajiyar zuciya suka sauki lokaci ɗaya sannan ya buɗa baki a hankali yace,

" Baby gaskiya na gaji da zama gida ba aikin dana ke fita komai kece keyi, wallahi nima ina so nayi miki abinda zai saki farin ciki Baby , shiyasa nace idan har babu wata damuwa ina so ki bani kuɗi na saki sayin mashin in yaso sai na rika cire miki kuɗinki duk sati har na biya".
Ya kai ƙarshin zancin da ƙara matsita jikinshi haɗi da yimata wani zazzafan kiss.

Jikinta ne yayi sanyi lokaci ɗaya dan haka itama ciki da ƙwarewa ta mayar mishi da martanin kiss ɗin da yayi mata kana tace,

" Ba koma Baby duk abinda kake so shi zan maka, burena ako da yaushe ka kasance cikin farin ciki".

Wani ihu yayi haɗi da ƙara rugumeta yana sa mata albarka, kai saboda jin daɗi ɗaukar ta yayi ya goya yafito tsakar gida sai rawar murna yake...

Kai tsaye Hauwa gidan Ƙawarta tatafi dan jin yadda zanci Ahamd ya kasanci ko ya bada kai, inko bai bayar ba asan yadda zaa ɓullowa lamarshin.

Ta jima zaune cikin falon amma shuru kamar babu kowa har zata tashi ta tafi sai kuma ta ɗauko waya takira ta, kamar baza aɗauka ba kuma sai can aka dauka Hauwa tace,

" Halan baki gida gani zaune falon amma kamar ba kowa".

Kashi waya tayi bata re da taba Hauwa amsa ba.

Mamaki ne ya kama Hauwa tabi wayar da kollon tana kallon ikon Allah.

Tana cikin haka sai ga wannan matar ta fito sanyi cikin wasu kananun kaya, dubin Hauwa tayi a ɗan ya tsani tace,

" Lafiya naganki da safiya nan?".

Murmushi Hauwa tayi irin na ƴan duniya tace,

" Yanzu ne da safe? daman zuwa nayi naji aiki yayi kyau ko yaya?".

Sai a lokacin matar ta ɗanyi murmushi tace,

" Aiki yayi kyau Hauwa dan yanzu haka gashi can sai bacci yake a ɗaki".

Ido Hauwa ta zare tace

" Kenan komai yana tafi yadda ya dace".

" Eh".
Itace ansar da taba Hauwa ataƙaice, dan bata son zanci yayi yawa ya kai har lokacin da Habibin nata zai tashi bacci, dan an bata labarin Hauwa ance ko ɗanta zata iya zama dashi idan taga yayi mata, dan ita ɗin akuya ce kowani bunsuri biyarshi take.

Kuɗi ta ɗauko taba Hauwa tace,

" Gasu ki sha ruwa kuma nagode sai idan lokacin nemanki yayi zaki jini".

Murmushi Hauwa tayi haɗi da karɓar kuɗi, sai da tasa jika sannan ta tashi ta dubeta tsaf sannan tace,

" Ba komai nasan zaki nemeni nan bada jimawa ba".
Tana kai ƙarshin zanci ta tashi tayi ta fiyar ta.


Gida ta wuce sai tunanin abinda zata kullawa wannan matar take, lokacin da taji tasamu mafita tayi murmushi irin nasu na ƴan duniya kana tace,

" Hauwa ce fa! ba'a gwada mata kan duniya, gada nayi ba tsintar tanayi ba".

Dai-dai lokacin tashiga ɗakin ta...




*Comment and share*




*SUMMY M NA'IGE✍️*
*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*




*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

*Z.W.F.🏝️*



*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*





*SHAFI NA 16*


Sai da suka ɗau lokaci a haka sannan ya ɗago da kanta da murmushi a fuskarshi yace,

" Baby na kimin afuwa kinga sai yanzu na dawo ko?".

Murmushi tayi mai nuna tsantsar so da ƙauna sannan tace,

" Tunda ka dawo lafiya ai mun wuce wuri".
Kiss ya bata mai

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment