Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zafi sannan suka ƙarasa cikin ɗaki.
Bayan ya zauna ta kawo masa abinci tare lemo mai sanyi, zama yayi yaci saida ya ƙoshi sannan ta ɗago da kanta ta dubeshi tace,
"!Baby ina mashin ɗin ko baka sayo ba naga kadawo haka?".

Sai da ya gyara zama sannan yace ,

" kuɗin ne basu isa na sayi mashi saboda mashin ya tashi, ko yanzu akwai cikon nera dubu ɗara".

Ido ta zare kana tace,

" Yaushe abu ya lalace, kai duniyar nan wallahi koma ya lalace, to yanzu ya za'ayi my baby?".

Jikinshi ya jawota kana yace,

Baby bansan yadda zanyi ba, kinga yanzu ba kowa ki aramaka kuɗi ba bare naje nasamu rance".
Ya faɗi haka cikin wata murya maisa kasala tare da shafar duk wani sashe na jikinta.

Ahankali ta buɗa baki tace,

" karka damu insha Allah gobe zan baka ciko, ni burina duk bai wuce naga kana farin cuki ba".

Sosai yaji daɗi har ranshi dan haka ya ɗauketa bai dire ko ina ba sai kan gado.
::::::::::::::::::::::::::::

Kai tsaye hotel suka nufa wajan da ake patin abokinsu shida budurwarsa, suna zuwa kowa ne daga cikin abokinshi ya ja budurwa suka keɓe gyafe ɗaya, shi waje ɗaya ya samu ya zauna ya kunna sigari ya na zuƙa.

Yana cikin haka sai yaji wayarshi tayi ƙara alamu saƙo ya shigo, tsaki yayi kamar ba zai ɗauko wayar ba kuma sai ya ɗauko wayar ya duba, ido ya zare , dan har ga Allah ya manta da wani zancin meeting ɗin da zasu shiga garin abuja gobe ƙarfe ta kwasa na safe, kuma kamata yayi ace acan ya kwana saboda kafin ashiga meeting akwai abinda zasu gudanarwa nan ma'akatarsu, cikin hanzari ya miƙe tsaye wajan da abokanshi suke da ƴan mata ya ƙarsa yace su zo shi zai tafi gida dan yanzu cikin daren nan zai wuce abuja.

Fatan alhairi sukayi mishi sannan ya kama hanya bai tsaya ko ina ba sai gidansu, kai tsaye part ɗinshi ya wuce ya haɗa duk abinda zai buƙata yasa mota kana ya kama hanyar abuja batare da ya tashe iyayenshi.
Abdulrazak kenan.

AbdulRazak ɗane ga Alhaji Muh'd kuma da Hajiya Hadiza ɗa ɗaya tilo, shikaɗa suka haifa kuma tunda suka haifeshi Hajiya Hadiza ko ɓatan wata bata sakiyi ba, sosai suke son yara, amma tunda Allah bai basu da yawa ba suka yi haƙuri da ransu suka cigaba da bawa yaronsu tarbiya, Abdulrazak yayi karatun islamiya da na zamani har ƙasar waje yafita yayi karatu kuma yasamu cigaba dan yanzu haka yana aiki abuja birnin taraiya, ganin yana samun kuɗi ko ta wani fanni yasa abokai suka riƙa liƙe masa dan ma iyayenshi basu cika bari yana ma'amala da kowa ba, amma duk da haka sai da ya haɗu da wasu abokai suka ɗaurashi akan hanya, amma har yanzu yaƙi saboda tun farko bai sababa, abu ɗaya sukayi galaba akanshi itace tabar da yake sha yanzu, iyayenshi sun so yayi aure amma har yanzu yace bai ga yarinyar da kemasa ba, har iyayenshi sun so su haɗashi da wata ɗiyar abokin Dady shi, amma Kakarshi tace a'a bata so a takurashi a barshi har lokacin da yaga waca tayi mishi, ai aure lokaci ne dashi da lokaci yayi babu wanda ke hana ayi sai anyi, akan haka ne suka saka mishi ido badan ransu ya so ba .


Cigaban labari.

Koda gari ya waye Hajiya Hadiza ita da Dady suna zaune suna breakfast sai ga wata matashiyar dadcijowa tashigo bakinta ɗauke da sallama, amsawa Hajiya Hadiza tayi kana tace ta ƙaraso, bayan ta ƙaraso ne ta gaishe da Alhaji sannan ta gaya musu cewa ga Baba mai gadi nan yazo nemanshi, bata izini yayi da abarshi ya ƙaraso cikin gidan, bayan ya shigo ne haɗi da gaishe da Alhaji da Hajiya sannan yayi gyaran murya yace,

" Alhaji daman akan aikin da kasani ne nazo na shaida maka cewa jiya kusan ƙarfe sha biyun dare tabbas yashigo da wata yarinya shida abokanshi, ina ma tunanin kamar koda suka ɗauko yarinya bata cikin hankalinta saboda ko tafiya bata iyaye shi da kansa ya ɗauketa zuwa sashinshi".

Ajiyar zuciya Dady yayi lokaci ɗaya ya dafe zuciyarshi saboda wani zafi da take fitarwa.

Kallon Mumy yayi da kyau, yace,

" Kinga yaronnan ko? abinda yasa yaƙi aure kenan saboda yasan yana da ƴan mata waja, wallahi yanzu bazan zuba ido ina kallon yaron nan ba, tabbas ƙarshin watannan zan ɗaura mishi aure da kowace yarinya nasamu, ko yana so wallahi ko baya so".

Ya faɗi haka ciki da zafin rai.

Dubin Baba mai gida yayu yace,

" Yanzu ita yarinyar tana ina? ko har yanzu tana nan gidan?".

" Eh Alhaji tana cikin gidan yasa ɗakinshi ya rufe".

" Tashi mutafi Baba mai gida".

Ya faɗi haka tare da tashi tsaye, itama Mumy mayafi ta ɗauko ta biyushi dan taga shin da gaske ne, dan itakam tasan ɗanta na tsare sallah cikin lokaci tabbas abu ne mai wuya ace yana biyar mata.

Mota suka shiga direba yaja suka kama hanyar gidan.....


Sai da Hauwa tagama miƙa sannan ta tashi tashiga toilet tayi alwala tayi sallah sannan ta fito zuwa ɗakin Babarta.

Koda tashiga yaran sun farka daga bacci, yara ne kyawawa, babban yanzu shekarshi goma, mai binshi nada shekara shida, ƙaramin shine da shekara huɗu.

Kallonsu tayi tsaf, sannan ta ƙarasa wajansu ta zauna, gaisheta sukayi shi ƙaramin shine ya faɗa jikinta ya na kuka.

Sosai taji son yaran na fizagarta, tana cikin haka wayar ta ta fara rura, kamar bazata ɗauka ba sai kuma ta ɗauka haɗi da karawa a kunninta tun batayi magana ba aka ce,

" Hauwa kizo yanzu ga Ahmd nan bashi tare da kowa, ko minti ɗaya karki ƙara kizo".

Cikin hanzari tace,

" Yanzu kowa".

Yaronta dake jikinta ta ɗauke ta aje ƙasa cikin sauri ta zaro kuɗi ta basu tace susha minti ko sallama bata tsaya sukayi da kyau ba ta fita jiki na rawa........




*Commen and share*



*SUMMY M NA'IGE✍️*
*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*




*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

*Z.W.F.🏝️*



*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*




*_INA MIƘA GAISUWA GAREKU ƳAN UWA KUMA MASOYAYA KUMA MASOYAYAN WANNAN LITTAFE NA MIJIN BABATA NE, COMMENT ƊINKU NA ƘARA SANI FARIN CIKI FIYE DA TUNANINKU, INA GODIYA SOSAI IRIN YADDA KUKA ƘARƁI WANNAN LITTAFI, ALLAH YA BANI IKON KAMMALASHI LAFIYA_🤗*



*SHAFI NA 15*


Bata jima dashiga ɗaki ba sai ga Inna mero tashiga ɗaikin bakinta ɗauke da sallama, amsawa Hauwa tayi haɗi da tashi daga kwanciyar da take.

Kallonta lnna tayi da kyau kana tace,

" Ɗiyar nan dan kar nace kije ki dubu mahaifinki ne kika sa ƙafa kika fita yawonki, to shikenan tunda bazaki ji magana taba kije kiyi duk abinda kika ga dama, amma kisani ko bayan raina ne sai kin gane cewa maganar dana ke gaya miki gaskiya ce".... Wai lnna waya gaya miki banze ba? ko kinje dubiyarshi ne yake gaya miki banje ba? ina fita gidannan ban tsaya ko ina ba sai gidanshi, na dubushi ban dai jima ba na fito".
Ta kai ƙarshin zanci tare da murguɗa baki.

Ajiyar zuciya lnna ta sauke kana tace,

" Dama na zaci baki je bane amma tunda kinje ai shekenan, idan kin koma samu lokaci sai ki riƙa zuwa kina ganin halin da yake tunda duk duniyar nan bashi da wata ƴa in ba ke ba".....a'a karki ce ni kaɗai ce, ina ɗiya matan da yake tare dasu wallahi an tabbatamin yana da yara kusun uku to su miyasa bazasu zo suga halin da yake ciki ba sai ni!".

" To ke duniya tasan kece ƴarsa, kuma idan kingama gayamin magana ki tashi ga yaranki can mahaifinsu ya kawosu tun ɗazo, har sun ci abinci sunyi bacci".

" Lafiya dai ya kawo su ko lnna?".

" Lafiya ƙalau, ya kawo sune suga mahaifiyar su, kuma ko ba komai ni yau nayi farin cikin ganin su".

" Tau bari nayi sallah gani fitowa sai mu gaisa".

Duban Hauwa lnna tayi da kyau kana tace,

" Yanzu Hauwa har yanzu baki daina lattin sallah ba, ashe duk iskanci da kike yana da nasaba da rashin ƙinyi sallah cikin lokaci, wallahi ɗiyar nan kiji tsoron Allah , kisani duniya ba matabbata bace".

Inna na kawai ƙarshi ta bar ɗakin saboda kar ciyon zuciyar ta ya tashi.

Murguɗa baki Hauwa tayi haɗi da komawa ta kwanta.
===========
Kuɗi maso tsoka Mumy ta bawa mijinta tace yaje yasaye mashin saura kuma ya shamai yayi musu cefeni da saura.

Sosai yaji daɗin abinda tayi mishi, dan haka yinin ranar ba abinda yake mata sai kasheta da soyayya mai shiga rai, a halin yanzu Mumy tana jin tabbas idan babu Kabir bazata iya rayuwa ba, dan yanzu ta zaɓi zama dashi akan kowa, a koda yaushe burinta ta ganshi tare da ita suna kwasar soyayya, danshi bata jin shayin mallkamasa duk abinda ta mallaka ba muddin baifi ƙarfinta ba.

Sai da gari ya waye sannan yayi wanka yace yaje ya sayo mashin ɗin, har ƙofar gida ta rakashi sannan ta dawo gida zuciyar ta fas dan farin ciki saboda sahibin ranta na cikin farin ciki.


Da fitarshi bai tsaya ko ina ba sai gidan Yayarshi, bayan sun gaisa ne yace mata daman kuɗi ne ya kawo mata dan a haɗa mishi lefe, washa haƙura tayi lokacin da ya ɗauko kuɗin ya bata, kana ya shaida mata cewa wani sati yake son akai mishi wannan lefen, tace karya damu tun yau zata fita wajan sayayya, godiya yayi mata yace shi zai tafi dan yau yake so akai mishi ƙarshin ginin da yakeyi saboda wata mai kamawa ne yake so yayi aure.

Sosai Yayarshi ta nuna masa jin daɗi akan haka har da faɗin ko kai fah, yanzu zakayi auren shiga tsara da nunawa dangi, dan wallahi sai munyi biki sosai, sai mun nunawa duniya yanzu kayi aure, za mu wankeka tas kamar sabon jariri.

Dariyar jin daɗi yayi sannan ya tashi ya tafi kasuwa ya sayo kayan abinci ya raba buyi ya kaiwa iyayenshi rabi sannan yabawa wani almajiri ya kaiwa Mumy rabi sannan ya wuce gidanshi da ake mishi gini, shine bai dawo ba sai ƙarfe goman dare, lokacin duk inda hankalin Mumy yake ya tashi saboda rashin ganin sahibin ranta.

Yana shigowa gida ko rufe ƙofa bata bari yayi ba ta fito ciki da zumuɗi sai ƙamshin turari take tayi ado cikin ƙananun kaya masu bayyana da jikin mutum.

Rugumeshi tayi haɗi da sauke wata ajiyar zuciya.

*********
Tuƙi yake a hankali, su kuwa abokanshi sai shan sauti sukeyi suna rangwaɗa kai.

Hanyar da ya ɗauka ne yasa ɗaya daga cikin aboksnshi yayi saurin yimishi magana yace,

" Baba yana ga ka ɗauke hanya , ba hotel zamuje mu huta da wannan yarinya ba?".....tun bai bari ya kai karshin abinda zai faɗa ba ya taka birki ciki da tashin hankali yace,

" Kai wani irin bunsuru kake? angaya maka yarinyar nan kalar hotel ce? to bari kuji na rantse duk kwaɗayinku akanta ku haɗiyeshi dan wallahi duk wanda yayi gigin taɓa koda ɗan yatsarta ne wallahi sai na rabashi da rayuwarshi kun san halina idan zan iya ko bazan iya ba, duk matan da kuke nema akwai wace nace muku ina so? to dan haka kukiyaye ni wallahi".

Ya ƙai ƙarshin maganar tare da kunnan motar ya fara gudu kamar zai tashi sama.

Tunda ya fara magana gabaki ɗayansu sukayi shuru suka kasa magana saboda sanin halinshi.


Dai-dai get ɗin wani fantamemin gida ya tsaya, horn yayi, ba ɓata lokaci mai gida yazo ya buɗe masa jiki na karkarwa.


Wajan da ake aji motoci yazo yayi parking, fitowa yayi batare da yayi wa ko wanin su magana ba, ya ɗauke ta yayi da ita hanyar da zata sadashi bedroom ɗinshi, kwantar da ita yayi kan gado sannan ya fito ya samesu parlour suna jiranshi, bai ce dasu komai ba ya fito suma suka bi bayanshi, mota suka koma shiga suka fita.....




*SUMMY M NA'IGE✍️*
*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*




*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

*Z.W.F.🏝️*



*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*




*SHAFI NA 17*


Suna isa gidan bayan diraba yayi parking suka fito, kai tsaye part ɗinshi Dady ya nufa ya buɗe ɗakin ya shiga.

Tunda suka kawo ta gidan ba itace ta farka ba sai da garin Allah ya waye, sosai tashiga tashin hankali ganita cikin wannan ɗaki kuma ba kowa a cikinshi, hawaye ne masu zafi suka fara zuba a idonta, lokaci ɗaya ta fara tunanin abinda Mumy tayi mata wato Mumy tafison mijinta akanta, to wallah tunda har ita da kanta ta koreta wallahi tayi ma kanta alƙawari bazata koma gidan ba sai dai tabi uwa duniya, taje gata ga mijinta tunda ta nuna tafison shi akan kuwa, hawayen da ke zuba a idonta ta goge, ɗakin ta fara bi da kallo har ta gano inda ban ɗaki yake, cikin sanyi jiki ta tashi tashiga, alwala ta ɗauro kana tazo ta gabatar da sallah, azkar ta farayi tanayi tana tuna abinda Mumy tayi mata, lokaci ɗaya ta kife kanta a ƙafafun ta tafara rera wani kuka mai ban tausayi, a dai-dai wannan lokaci Alhaji da Hajiya da Baba mai gida suka shigo ɗaki, mutuwar tsaye sukayi lokacin da idonsu ya gane musu abinda basuyi tunani ba ko a mafarki .

Tana jin mutsin kamar anshigo ne yasa ta ƙara sautin kukan da take, da sauri Mumy taje ta ɗago kanta dan ta ƙara tabbatarma idonta gaskiya.

Idon suka haɗa da Hansa'u da Mumy, ita ko Hansa'u tana ganin mace kuma uwa da sauri ta faɗa jikin Mumy tana faɗar,

" zasu kasheni dan Allah ki taimakeni".

Ƙara sakata jiki Mumy tayi haɗi da bugun bayanta alamar tayi shuru kenan, ajiyar zuciya Hansa'u ta farayi a hankali har tayi shuru, sai da tayi shuru ne Mumy ta sake ɗago kanta tayi mata kallon tsaf, ƙaramar yarinya ce kyaukyawa son kowa ƙin wanda yarasa to ina suka samu ta.

Mumy na cikin wannan tunanin Dady ya ƙaraso wajan da suke yace,

" Yarinya wace unguwa kike? kuma ina suka ganki ya ɗauko ki? miya haɗinki da su?".

Duk yayi mata wannan tambayar lokaci ɗaya.

Ajiyar zuciya ta sauke batayi magana ba, sai da Mumy ta sake tambayar ta kana ta buɗa baki a hankali tace,

" Ni ba ƴar garin nan bace, iyayena sun rasu, wadda ke riƙona ce ta ƙoroni saboda mijin da ta aura baya sona, kuma ƙoƙarin yake yayi min fyaɗe, to dan nagaya mata shine yasa ta ƙoreni cikin dare, to ina cikin tafiya ne wasu mutane suka sace ni, wani abu suka shaƙamin a hanci, tundaga wannan lokaci ban sake sanin inda kaina yaki ba sai yanzu da safe".

Ajiyar zuciya Mumy ta sauke ita da Dady lokaci ɗaya.

Dady ya buɗa baki yace,

" Kuma baki san kowa naki ba?".

Kai ta ɗaga masa alamar eh, hawaye ne suka riƙa zuba a idonta saboda ƙaryar da tayi musu.

Dady ne ya kalle Mumy yace ko zata iya raƙata har agane inda dangin ta suke?.

Mumy daman ita tunda taga yarinyar tashiga ranta, ai Dady ko baki bai rufe ba Mumy tace,

" Ai ɗa na kowa ne, Allah ya tayamu riƙo".

Da Ameen suka amsa, sannan Mumy tariƙa hannun Hasa'u suka fito dan su koma gida.

******
Koda gari ya waye mijin Mumy yacewa Mumy ta bashi kuɗin saboda baya son ya makara, ko beark batayi ba jiki na karkarwa ta tashi tace yayi mata izini zata je gidan ƙawarta ta dawo, izini yayi mata tare dayi mata kashedi karta jima, tace yanzu bazata jima ba zata dawo.

Mayafi ta ɗauka bata tsaya ko ina ba sai gidan wata ƙawarta wato Hajiya Suwaiba mai adashe.

Sosai Hajiya Suwaiba tayi mamakin ganin Mumy dan ita kan rabonta da Mumy tunda ta aure tsinanin yaro nan, kallon Mumy tayi sama da ƙasa tace,

" Amarya kece yau agidan? ina ango yake yabarki kika fito yanzu da sassafin nan, ko har kungama cin amarci ne?".

Mumy tace,

" Ke ni banso haka daman ko yana nan ai zan fito".

Wani kallo Hajiya Suwaiba tayi mata kana tace,

" Kedai Allah ya kyauta, ina ƴata Hansa'u?".

Gaban Mumy ne ya faɗi dan wallahi ita har ta manta da wata Hansa'u, kawar da tunanin Mumy tayi tace,

" Keni ba isakanci nazo kimin ba, daman kuɗi ne nazo ki aramin har zuwa ƙarshin wata, saboda mashin zan saya na basuwa haya, kuma jiya koda aka je ya ƙara kuɗi, shine nace bari nazo wajanki nasan zan samu".

Da yake da Hajiya Suwaiba da Mumy akwai amana, ba musu Hajiya Suwaiba ta tambaye Mumy nawa take so, gaya mata tayi ta ɗauko mata, haɗi dayi mata fatan alhairi.

Mumy ana bata kuɗi jiki na karkarwa tayi ma Hajiya Suwaiba sallama ta kama hanyar komawa gida.


Koda tashiga gida yana waya da budurwarsa yana gaya mata yau yake son su haɗu da ƙawayenta shi ya salamesu yasan ya gama da komai amaryarshi kawai yake jira, jin Mumy tayi sallama ne yasa yayi mata sallama akan sai yazo .

Amsawa Mumy sallama yayi yana faɗin,

" Oyoyo Baby kin dawo, sannu da hanya kinji ƴar aljannah, dan indai nine to na janye miki ƙafa kishiga aljannan mosoyiya".

Sosai Mumy taji Daɗi, dan haka cikin shagwaɓa ta faɗa jikinshi tana faɗin,

" Baby andace ka gansu nan".

Bakinshi ya haɗe da nata ya fara tsotsa, har yayi nasarar rabata da kayan jikinta, wasa yashigayi da ita son ranshi yana nuna mata zallah soyayya, amma tabbas idan yana tare da Mumy tunanin Hansa'u ce yake tare da ita shiyasa yake zaucewa wani lokaci.

Sai da yashayar da ita ruwan soyayayya, sannan daga baya yayi wanka yayi beark kana ya karɓi kuɗi yafita.

Kai tsaye gidan iyayenshi ya nufa, koda yaje yasamu Yayarshi da ƴan uwanshi ana taganin kayan lefe akwati biyar akayi mata, sosai yaji daɗi shida ƴan uwanshi, shaida musu yayi ko gini yau za'a kammala koma na gidanshi amarya kawai suke jira, daɗi suka ji kamar su zuba ruwa a ƙasa susha.

Kuɗi ya bawa Auntyn shi yace a sayo ma Babarshi kayan da zata sa ita da Babanshi ranar aurenshi, aikuwa sun jidaɗi ba abinda suke samasa inba albarka ba, daga bisani yayi musu sallama ya fita.

Yau duk wani abu wanda ya rage sai da ya kammalashi na aurenshi har kayan da zai sakawa sai da ya saye ya kai ɗinki, sauran kuɗi ya kai ajiya saboda idan Amarya tazo yasamu abinda zasu kashe.

Bayan ya kammala sannan yaje wajan abokinshi yace dan Allah sutafi wajan mai gidanshi mashin yake so abashi yana acaɓa.

Haka kuwa akayi suka je mai gidan abokinshi yace yaje gobe za'a bashi mashin amma fah shekara ɗaya ne zai gama, sosai yaji daɗi yayi masa godiya sannan ya koma gida wajan Mumy ya shaida mata gobe za'a bashi mashi.


===================

Babu ɓata lokaci Hauwa ta isa wajan da aka shaida mata Ahmad na can, koda taji ta sameshi, yana ganinta yayi murmushi yace,

" Rai kanga rai, tun ranar bansake ganinki ba?".

Murmushi Hauwa tayi tace,

" Koni bansake ganinka ba , ko yanzu hanya ce ta haɗa mu, saboda har zan wuce na ganka zaune shine nace bari na zo mu gaisa".


Murmushin jin daɗi yayi yace,

" Gaskiya kin kyauta kuma nagode".

" Bawani ka gode zo karakani wallahi daman ina ta tunanin yadda zanyi tafiya ni kaɗan, hala ina Hajiyar ka ta barka kai kaɗai?".

Hauwa tafaɗi haka haɗi da ruƙo hannusa suka fara tafiya.

" Wallahi yau biki garesu, ai jina nake duk ba daɗi".

" Ayya ai tunda kasaba kullum kana jikinta dole kaji ba daɗi".

Ta faɗi haka dai-dai lokacin da suka tsayar da mai napep.

Shiga sukayi basu tsaya ko ina ba sai unguwar da ta kama hayar ɗaki, kai tsaye ɗakin ta buɗe suka shiga sai wani rangwaɗa take mishi, shiko sai kallonta yake yana murmushi birgewa.

Lemo ta kawo masa mai sanyi ta aje gabansa, zama tayi kusa dashi kamar ta mayar dashi ciki sosai Hauwa ta birgeshi dan yanzu shima yasan sirrin gari, gwara ya tsaya ya kwashi gara, suna ciki haka Hauwa sai daɗi takeji tarkonta yayi, wayarshi ta fara rura, kin ɗauka yayi saboda ya shagala sai wasa suke shida Hauwa.

Sai da aka saki kira sannan yayi ƙarfin halin ɗauka, koshi dayaga sunan Mamarshi ya bayyana.

Tun baiyi magana ba Mamarshi tace,

" Duk inda kake kazo wallahi ance ga mahaifinka can rai hannun Allah, dan Allah Ahmad kaje ko dan albarkar haihuwar dana maka".

Ta kai ƙarshin zanci da fashewa da kuka.

Bai ce da ita komai ba ya tsinki wayar kana ya dube Hauwa yace,

" Bari naje na dawo?".

" Ina zaka tafi?".
Tafaɗi haka tare da zare ido.

"Wallahi mahaifina ne ba lafiya shine zanje".

" Ayya to in ba damuwa ko zamu iya zuwa tare".


Yace muje bawata damuwa........




*COMMEN AND SHARE*



*SUMMY M NA'IGE✍️*
*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*




*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

*Z.W.F.🏝️*



*MARUBUCIYA*
*UMMU JA'AFAR✍️*




*SHAFI NA 19*


Har Hauwa zata ɓuda baki ta yi magana sai Inna tace

" karki kuskura ki gayawa mijina magana ai ko ba komai ubanki ne".

Abinda ke damunta ne yasa ta kyalesu ta fara ɗaukar kaya tana kaiwa ɗakin da yace, sai da ta kammala sannan lnna tashi ɗakin haɗi da zama gyafin katifa, kallonta Hauwa tayi idonta taf da hawaye tace,

" Kaicona lnna! lnna bakimin zaɓin uba ba wanda zan nunawa duniya nace shine ubana, kisana yau ina cikin ƙunci da ta kaicin kasancewa ta ƴa ga Babana, ashe lnna Baba na da ɗa Ahamd shine baki taɓa gaya min ba?".

Kallonta lnna tayi ciki da mamakin ta tace,

" Wani Ahamd kuma? ni dai nasan tunda mahaifinki ya sakeni bansanshi da wani ɗa ko ƴa ba wadda akace yau ya aure ya haifa, sai dai idan na matan da yake tare da sune, to wani abu ne ya faru?".

" Barshi kawai lnna bazaki gane ba, danshi ake so mutum yasan wanda zai aura".
Ta faɗi haka lokacin da take tashi ta bar ɗakin.

Tana fita dai-dai lokacin da ake shigo da kayan amaryar Alhaji Abu mata sai kuɗa suke, tsaki Hauwa tayi kana ta dube matanshi da ƴaƴanshi dake tsakar gida kowa na sabgar gabanta tace,

" An daiyi asara, ni banyi dacin uba ba wasu basuyi dacin uba da miji ba".

Tana faɗin haka tasa ƙafa ta bar gidan saboda taje ta samu mafita.


Sosai hankalinshi ya tashi ganin Hauwa ta tafi kodan halin da taga mahaifin shine, wata ƙila haka ne, amma har ga Allah Hauwa tashiga ranshi dan shi yanzu burinshi bai wuce yaganshi tari da ita sona shan soyayya ba, amma gaskiya Mamarshi bata kyauta ba, da yanzu yana can yana hutawa da Hauwarshi mai kayan ni'ima, yajima tsaye yana tunanin yadda zaiga Hauwa sannan ya samu wasu almajirai manya ya gaya musu aikin da za suyi musu sannan ya dawo wajan mahaifinshi, gyaran jiki da ɗaki akayi haɗi da sanya turare aka sauya mishi ɗaki sannan ya biya su suka tafi.

Bayan ya bashi fura yasha ne yasamu ya buɗe baki da ƙar yace,

" Amadu ina Hauwa'u, ba yanzu nagan ku tare ba, amma gaskiya naji daɗi da kuka san juna".

Kallon Baban Ahamd yayi tsaf sannan yace,

" Baba daman kasanta ne?".

Murmushi yayi irin na ƴan duniya yace,

" Kamar ya nasanta Ahamad, na haifita sannan kace na san ta"......." mikace Baba!".

" Nace nasan wannan aikin iyayenku ne suka haɗa ku, ko dai kun je gidan lya gaishta ta haɗaku, dan haka kasani baka da ƴar uwa kamar Hauwa, duk nine na haifeku , amma kuyi haƙuri da yadda rayuwa tazo".

Jikin Ahamd ne ya ɗau karkarwa kana yace,

" Kana nufin Hauwa Yaya tace?".

" Eh wallahi hala kai ka ɗauka kaine yaya, saboda ka ganta da ƙaramin jiki ko, kai ko ka biyoni da Babban jiki".

" Nashiga uku, amma Baba kacutar damu dan wallah a halin yanzu Hauwa budurwa tace!!.

Da ƙafi uban ya tashi zaune abinda yajima baiyi ba, kullum yana kwance saboda ya kasa koda tankwashi ƙafar bare asa ran zai iya mutsi yau shine ya tashi zaune saboda razana.


A hankali yake taka ƙafarshi har ya isa parlour da yake tunanin zai sami mahaifiyar tashi, zaune take tama kallon labarai tayi kyau abinta da ka ganinta ba abinda

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment